Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
har ba ki tauna ta ba. Ita
rayuwar nan da kika gani komai mai sauƙi ne idan aka ɗauke shi mai sauƙin. Saboda Jamal namiji ne, ko ba
ita ba zai iya ganin wata ya ce yana so, idan kina irin wannan furucin sai ki jefa kanki cikin matsala, idan har
tsautsayin illar furucin ya biyo kanki, Allah Ya kare. Don ita magana zarar bunu ce da ta fito ba ta komawa
ciki, sannan magana mai daɗi ma babbar sadaka ce, kuma Manzon Allah S.A.W ya ce; a faɗi alheri ko a yi
shiru. Idan kin san kina cikin fushi bakinki ba zai iya faɗar magana mai daɗi ba to ki daina yin magana har
sai kin huce. Ina roƙon Allah Ya ƙara miki haƙuri, kuma in dai Jamal ne zai zo gidan ya same ni ki ga yadda
za mu yi da shi, don ga ni cikin gidan naku ina jiran dawowarsa komai dare. Kuma ko a waya ban ce ki ce
masa komai ba, ki bar ni da shi kawai har sai ya zo."
Ajiyar zuciya Inna Ade ta saki kafin ta ce, "Ai wayar tata ma ta buga ta a ƙasa ta fashe gabaɗaya. Don ina
ganin kamar ba za ta sake moruwa da ita ba, bari na ɗauko miki ita ki ga yadda ta koma."
Inna Ade ta fice daga ɗakin cikin sauri, mintuna a tsakani ta dawo da watsattsiyar wayar ta miƙa wa
Hajiya. Hajiya ta karɓa zuciyarta cike mamakin mahaukacin kishin Minal, wanda ba ta taɓa tunanin hakan
za ta faru a kurkusa ba, duba da yanayin auren nasu da kuma yadda ta sha fama kafin a samo kansa, kuma
ta san ita ma ba ta son auren dole aka yi mata."
"Shi dai namiji ba a cin alwashi da shi, koyaushe ki saka wa zuciyarki cewa mijin mace huɗu ne. Kuma
idan Allah Ya nufa zai tara matan sai dai ki kai zuciyarki nesa ki bar wa Allah komai. Amma idan kika ce za ki
yi ta nuna masa irin wannan zafin kishin gaskiya akwai matsala a gaba, don wani a lokacin da kike haukar
kishin a lokacin yake ƙara zaburewa. Saboda sun fi son ganin mace tana kishi a kansu idan za su ƙara aure,
kuma suna jin haushin mace ta nuna musu ko-in-kula a lokacin da suke neman auren. Don wani a sanadin
hakan yake rage rawar kai idan ya fahimci auren ba ya gabanki. Saboda zai yi tunanin anya ma kina son sa
kuwa? To da irin waɗannan kissa ake samun kan miji a riƙe babu faɗa babu tashin hankali. Don haka don
Allah ki daina abin da na ga kin yi a yau, inda hali ma kada ki sake yi saboda mutuncinki zai zube a gaban
duk wanda ya ga abin da kika aikata."
Inna Ade kenan da jerin maganganunta da suka ƙara rura wutar takaicin da Hajiya ta cusa wa Minal. Don
ba ƙaramin haushi ta ji ba, a lokacin da take jefo mata tambayoyi sannan kuma babu wani tashin hankalin
da ta ga ta shiga a sanadin jin abin da Jamal ya aikata. Don ba haka ta so ba, ta so ta dinga masifa ita ma ta
ɗauki zafi sosai fiye da yadda ita ta ɗauka.
****
Ɓangaren Jamal kuma, minti biyar a tsakanin wayarsu Baban ya fito. Turus ya yi a lokacin da ya yi ido biyu
da Nur, don tun kafin ya ƙaraso motar ta fita cike da jin nauyinsa ta durƙusa har ƙasa tana gaishe shi.
Mamakin ƙarara a kan fuskarsa, amma hakan bai hana shi gayyato murmushin dole ba ya yaɓa wa
fuskarsa. Cikin sakewa ya yi magana tamkar babu abin da ya faru.
"A'isha, yaushe a garin namu?"
Nur ta yi fiki-fiki da ido cike da jin kunyarsa a idonta ta ce, "Ka yi haƙuri Baba."
"Tashi mu je gidan, mutane suna kallon mu."
Ya yi maganar tare da yin gaba yana sake gaisawa da Jamal. Gaban motar ya buɗe wa Baban sai da ya shiga
sannan ya rufe, ita kam Nur tsaye kawai ta yi zuciya tana yi mata gargaɗin kada ta shiga motar, inda hali ta
samu ta zille kawai musu kawai sai dai su shafa su ji babu ta.
Amma umarnin da Baban ya ba ta a kan ta shiga motar su tafi, hakan ya sa ta jingine abin da ke ranta ta
faɗa motar zuciyarta a cunkushe. Jamal ya ja motar cikin sanyin gwiwa tare da tunanin yadda zai kaya
tsakaninsa da Baban. Don ya gama sanin matsayar Innarmu yanzu tasa kawai ta rage, kuma ita ce mai
babban muhimmanci a wurin sa. Har suka isa gidan babu wanda ya sake yin magana, sai dai tun kafin su
shiga cikin gidan Innarmu ta sha gabansu tana muzurai. Baban ya raɓa ta gefenta ba tare da ya ce komai
ba, har ya yi gaba ya juyo yana cewa da su Jamal su ma su shigo. Dole Innarmu ta ba su hanya suka wuce
sannan ta bi bayansu da ƙatuwar harara tana faɗin,
"Wallahi A'isha daga ni har Amina ba za mu taɓa yafe miki ba! Kin san kina son sa tun farko uban waye
ya saka ki dole a kan sai kin bar wa Amina shi? To ku gama duk wani ƙullen-ƙullen da ya kawo ku mu yi ta a
ƙare ni da ku."
Ta ƙare maganar tana ƙwafa ta nemo kujera ta dasa a tsakar gidan tana muzurai da tsaki jefi-jefi. Baba
kam bai bi ta kanta ba, kamar yadda Jamal da Nur ba su nuna ma sun ji me ta faɗa ba. Wuri Baba ya nuna
musu suka zauna, sannan shi ma ya raɓa jikin bango ya zauna idonsa a kansu ya ce,
"Na gan ku tare, duk da ban yi tunanin hakan ba. Duba da yadda aka sha faman neman A'ishar ba a gan
ta ba. Ina ka haɗu da ita?"
Jamal ya gyara zama ya ce, "A wani gidan cin abinci muka haɗu. Duk da ta so tafiya ta sake bari na Allah
bai ba ta sa'a ba. Inda matsalar take dai na ji tana zancen gobe ne ɗaurin aurenta. Bayan kuma ka mini
alƙawarin duk ranar da ta dawo za ka aura mini ita da hannunka."
Shiru ɗakin ya ɗauka tsawon minti biyu kafin Baban ya sauke ajiyar zuciya ya ce, "Tabbas mun yi haka da
kai, kuma ina kan bakana a kan aura maka ita a duk lokacin da ta dawo. Sai dai zancen auren da ka ce za ta
yi, shin su wane ne suka bayar da aurenta ga wanda za ta yi auren da shi?"
Kallon Nur Jamal ya yi cike da son ƙarin bayani, amma ba ta ce komai ba. Sai da Baban ya kai kallonsa gare
ta yana cewa ,
"Gare ki A'isha, muna son ƙarin bayani." Hakan ya sa ta cire tagumin da ta yi tana faɗin,
"Baba, bayan tafiyar da na yi, abubuwa da yawa sun faru. A cikin su har da haɗin aurena da ɗan'uwana
Sulaimane, wanda ya zamo ɗa a wurin yayan Babana, uwa ɗaya uba ɗaya. Shi ne ya ba shi ni, kuma shi
saka ranar auren da komai, bayan an sake samun saɓani a kaina, tsakanin dangin Babana da mahaifiyat..."
"Idan har haka ne, ba zan iya aurar da ke kai-tsaye kamar yadda na so yi a farko. Duk da mahaifinki da
kansa ya damƙa mini ke tare da wasiyyar idan aurenka ya tashi na aurar da ke da hannuna. Amma tun da
danginsa suna raye, kuma har hakan ta faru; to ban isa na yi jayayya da su ba. Saboda sun fi ni ƙarfi a kanki,
kuma ba zan so na yi abin da zai jawo mini matsala daga baya b..."
Cikin matsanancin tashin hankali Jamal ya yi magana tamkar cikin wata kalar muryar kuka ya ce, "Baba,
ka dubi girman alƙawarin da ka yi mini, tun da kana da iko da irin taka dama a hannunka; don Allah ka
taimake ni ka aura mini Nur a yanzun nan ba sai anjima ba."
Wani kalar murmushi Baban ya yi kafin ya ce, "Wallahi, da a ce wannan matsalar ba ta shiga ba; da babu
abin da zai hana ni ɗaura maka aure da A'isha. Amma a haka ina jin tsoron abin da zai je ya dawo, ganin
ban da ƙarfin jayayya da su a kant..."
"Ni zan tsaya a kan komai Baba, ko da wata matsalar ta taso ka bar ni da ita, zan taryi gabanta kuma zan
sha kanta da yardar Allah."
Kafin Baban ya ba shi amsa suka jiyo muryar Innarmu a kansu tana faɗin,
"Na sha ruwan bala'i ba ka isa ka yi wa Amina kishiya tana da wata biyu a gidanka ba. Dole ne ka yi
haƙuri har zuwa lokacin da za ta haifa maka 'ya'ya. Sannan auren ma idan da A'isha aka yi ni da Amina ba
za mu taɓa yafe muku ba daga kai har ita baƙar munafuka..."
Baba ya katse ta a fusace bayan ya miƙe tsaye yana nuna da hannu. "Kin ga...ki yi mini shiru babbar
kwabo! Ina ruwanki da shiga maganar da babu ke a cikin ta? Idan ma auren ne an faɗa miki haukarki za ta
sa a fasa n..."
"Ko ba a fasa ba shi kuma zai sauwaƙe wa Amina. Don babu ta yadda za a yi ta zauna zaman kishi da
A'isha. Wallahi dole ɗaya za a yi! Ko ita ko Amina, amma tun da ba macizai ne ba za su taɓa haɗa zama
cikin rami ɗaya ba ahe!"
Ta ƙare maganar tana riƙe ƙugu tare da jijjigar jiki alamun kaiwa maƙura a kan fushin da take kai. Shi ma a
fusace ya ba ta amsa da cewa,
"Muddin kika yi sanadin mutuwar auren Amina; to ke ma a bakin naki auren. Don na fahimci sai an fito
miki da yaren da kika fahimta za ki hakaltu."
Baki a sake cike da mamaki Innarmu ta ce, "Yanzu Malam a kan wannan feƙaƙƙiyar rayinyar kake son saki
na? A kanta kake iƙirarin bakin aurena idan na kashe auren Amina? To ita ta je ta yi auren mu gani tun da
ta fi kowa a wurin ka. Kuma aura mata shi ɗin ga fili ga mai doki."
Wata sabuwa!
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda
tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta
Ibrahim.
D.
✍🏼 AUTA CE
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*ASHIRIN DA TARA.*
Ta yi maganar tana kumfar baki, bayan ta gama fesar da zantukanta tana huci ta fito daga ɗakin, tsabar
tashin hankalin da ta shiga gabaɗaya ta rasa nutsuwarta. Takalmi ma ware daban-daban ta saka, sannan ta
ja hijabinta a birkice ta fice daga gidan tana surutai tamkar ta tashi sama.
Yayin da ta bar Baban Amina riƙe da baki a kan mamakinta, bayan kunyar da ta bar shi da ita saboda tijarar
da ta yi a gaban Jamal. Don Nur ta saba gani, ko kaɗan ba ta yi mamakin jin ire-iren maganganun da ta
furzar ba, saboda abin ba sabon abu ba ne a wurin ta ba.
"Allah Ya kyauta."
Baban Amina ya yi maganar bayan ya sauke ajiyar zuciya mai ƙarfi. Sannan ya sake kai kallonsa a kan Jamal
yana cewa,
"Kana dai gani tun kafin a je ko'ina wata matsalar ta kunno kai. Duk da ba a fata, amma matsalolin da za
su biyo bayan ƙulla auren sai sun fi haka. Don da a ce zan samu damar ganawa da dangin Baban A'isha; da
zan roƙi alfarmar su ba ni izinin aurar da ita. To ina mai tabbatar maka babu abin da zai hana ni ba ka
aurenta, kamar yadda na yi yunƙuri yi a watannin baya, Allah bai nufa b..."
"Baba ban katsi hanzarinka ba, amma matuƙar ba a ba ni auren A'isha ba; ni kuma ba zan taɓa barin
wani ya aure ta ba."
Yana gama furta hakan ya miƙe yana sake cewa, "Zan tafi na dawo Baba, kuma don Allah kada ka bari ta
je ko'ina."
Baban Amina ya bi shi da kallo kawai har ya fice, saboda bai san mai zai ce da shi ba, kansa ya ƙulle ta
yadda ya kasa gano wane kalar hukunci ya dace ya zartar a kan matsalar. Duba da jin labarin auren da Nur
ta faɗa za a yi mata idan safiya ta waye. Sannan yana jin tsoron dangin Babanta su zarge shi a kan shi ne ya
hure mata kunne ta gudo, bayan bai san komai a kanta ba tun bayan barin ta Kano. Hakan ya sa ya sauke
ajiyar zuciya mai ƙarfi sannan ya kira sunanta.
"A'isha."
"Na'am Baba." Ta amsa kai-tsaye tare da goge hawayen da ke bin fuskarta har a lokacin.
"Me ya dawo da ke garin nan, bayan kin tafi ba tare da kin sanar da ni ba?"
Zama ta gyara, tare da zuƙe majinar kuka cikin wata raunanniyar murya ta ce, "Ka yi haƙuri Baba, ni kaina
na san ban kyauta ba. Amma Allah shi ne shaidar na bar garin nan ne ba don ina so ba, kuma na bar shi ne
saboda na samu nutsuwar zuciya. Sai dai da a ce na san abin da zan tarar a can, da ban yi gangancin yin
nisa da ku ba. Saboda a sanadin bayyanata, bayan na share shekara uku ba na tare da su, hakan ya jawo
mini tashin hankalin da ban yi zato ba. Duk da ba ni ce na kawo kaina a gidan nan ba, kuma ba ni da laifi
don na yi wa wasiyyar mahaifina biyayya. Amma an yi mini hukuncin da ya jawo mini danasanin komawata
hannunsu. Sannan a sanadin hakan na gano gaskiyar abin da ya haddasa mini tarnaƙin zuciya, wanda ba
zai warke ba har zuwa ranar mutuwat..."
Ta fashe da wani sabon kukan da ya ƙara ɗaga wa Baban Amina hankali. Ya shiga rarrashin ta cikin
kaɗuwa da rawar murya. Tsawon minti biyar kafin ya samu ta sassauta kukan ta sake cewa,
"Baba ba zan iya auren Jamal ba, duk da auren da za a yi mini ba son mijin nake yi ba. Amma na zaɓi
zama da shi a kan zaman da zan yi kishi da Amina. Saboda ba na son duk abin da zai cutar da ita, haka ma
idan ina da iko ba zan taɓa bari Jamal ya auri wata ma ballantana a ce ni na aure shi. Yanzun ma wata ce ta
so lalata musu zama, shi ya sa na zo don na kare su daga sharrinta. Saboda ina group ɗaya da ita, kuma tun
ranar da hatsaniya ta haɗa ta da Aminar na sani, don duk maganganun da suka yi a tsakaninsu ta kwashe
ta tura a group ɗin. Yayin da wasu suke ta zuga ta a kan ta ɗauki mummunan mataki a kan Amina ko don ta
huce takaicin abin da ta yi mata. Tun da na ji muryar Amina kuma na gano da ita ake yin rikicin, sai
hanalina ya tashi. Musamman da na bi diddigin mai son yi musu sharrin, na gano mugun nufin da take son
aikatawa. Don na ƙulla ƙawancen ƙarya da ita, inda na nuna mata ina tare da ita a kan ɗaukar fansar da
take son yi, don kawai na gano komai da take son shiryawa. Ita ma ganin lambata ba ta Nigeria ba ce,
hakan ya sa ta saki jiki da ni ta kwaye mini cikinta gabaɗaya. Don ba ta ɓoye mini komai ba, ta sanar da ni
halayenta da irin tuggun da take shiryawa a kan Amina. Saboda ta sanar da ni a kan Jamal ta nemi aiki
gidan abincin da yake zuwa cin abinci. Don ta yi bincike sosai a kansa da Aminar, kuma babban shirin da
take yi a kansu na farko shi saka Jamal ya bi ta tamkar raƙumi da akala. Ta hanyar asiri don kawai ta raba
shi da Amina, ta yadda zai sake ta saki uku a lokaci ɗaya ba tare da ya yi shawara da kowa ba. Baba, a shirin
da ta yi musu ma, ta ce hatta mahaifiyarsa sai ta so ganin shi da idonta ba ta samu damar ganin sa ba.
Kuma yanayinta ya tabbatar mini za ta iya duk abin da take faɗa, don ta sanar da ni ba a kansa ta fara ba,
kuma ta ba ni labarai a kam mazan da ta afka irin tarkon da take son jefa shi. Sai dai nasa ya fi muni, don
raba Amina da shi da ta ƙudurta ba ƙaramin abu ba ne, wanda ta ce ba ta taɓa raba kowa da matarsa ba,
sai dai ta juya mazan da ta riƙe gam ta yadda duk samunsu yana hannunta. A sanadin wannan babbar
sana'ar da ta riƙa tana tutiya da ita, ta mallaki gidan kanta inda take cin karenta babu babbaka, kuma ta
sanar da ni tana da manyan filaye sama da biyar ba tare da kowa ya sani ba."
"Cabɗijam!" Baba ya faɗa yana jinjina kai. Nur ta ƙara da cewa, "Tsoron ta raba Amina da Jamal ta sigar
da ta so ya sa na baro gida bayan na bugi cikinta na san komai da ta shirya. Sannan kafin na zo na sanar da
Adamu abokin Jamal komai, da taimakonsa aka sa mata ido a kan duk wani takunta da na Jamal idan ya zo
wurin. Sai dai tabbacin da ta ba ni a kan bai zo ba, amma lalle zai je wurin a cikin kwanakin, saboda
kiranyen da ta sa aka yi masa. Hakan ya sa ni ma na kasa haƙuri na biyo hanya babu shiri don a yi komai a
gabana, na manta shaf da matsalar da za ta faru biyo bayan hakan. Duk da ƙaryar da na yi a kan cewa wata
kakata ce ta kira ni, waton ƙanwar mahaifiyar Babana. Da wannan dalilin na baro Niger cike da zummar
komawa cikin lokaci tun kafin asirina ya tonu. Kwanana biyu a nan ba tare da kowa ya sani ba, sannan ina
zuwa gidan cin abincin na wuni tare da Hajiya mai abincin amma ita muguwar ba ta san ni ce ba. Saboda
hoton wata ɗiyar yayan Babana na tura mata a matsayin ni ce kuma ta yarda...."
Daga nan ta kwashe komai da ya faru bayan tonuwar asirin Zulaiha ta faɗa wa Baban Amina. Ya shiga
jinjina kai tare da goge wata ƙwallar da ta cika masa ido tsabar mutuwar jikin da maganganunta suka