Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar Ƙauna Complete Hausa Novel by Hadiza D. AUTA

Author :  HADIZA D. AUTA Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 29

27K to 30K   out of 85.8K words

tamkar a lokacin take furta su.

'Ba za ka san darajar Amina ba sai ranar da ka yi gangancin rabuwa da ita. Kuma daga lokacin haukar da
ke cikin kanka za ta sake ka ka gano ka cuci kanka.'

"Ya Salam! Hajiya me ya sa kike ƙoƙarin Yi mini baƙin baki koyaushe?"
Zancen da ya yi kenan dafe da kansa cike da takaici, tsaki ya buga mai ƙarfi sannan ya buɗe murfin motar
ya fito ya fisgi jakar da ke gabanta ya wurga bayan boot cikin fushi, sannan ya zagaya yana faɗin,

"Malama ki shigo mu je kin ɓata mini lokaci."

Minal ta buɗe bayan motar za ta zauna ya yi hanzarin faɗin, "Ba ki isa na zamo direbanki ba! Idan har ba za
ki zauna gaban ba ki fita na ba ki kudin adaidaita sahu mu haɗu can. Ƙauyanci kawai ke a komai sai an ci
gyaranki..mitsss."

Wani kallo ta yi masa na tsawon sakonni ba tare da ta ce komai ba, ta buɗe gaban ta shiga ta zauna cikin
tsuke fuska. Sannan ta koma danne kukan da yake ƙoƙarin bayar da ita a gabansa. Don ta ci alwashin daina
kuka a gabansa duk tsananin ƙuncin da ke ranta kuwa.
A haka suka fice gidan, yayin da suka bar maigadi da tunanin rabuwa auren ne ya yi ko wata tafiya ce za
su yi su dawo. Kowanensu fuska a cure har suka ci rabin tafiyar, kasanacewar akwai tazara a tsakanin
Nasarawa da Jogana. Amma har suka isa babu wanda ya ce da wani uffan illa wayar da Jamal yake ta
karɓawa lokaci bayan lokaci.

Dam-dam ƙirjin Minal ya shiga bugawa a lokacin da motar ta tsaya bakin lugun gidansu. Tana ƙoƙarin
buɗewa ta fice ya yi hanzarin riƙo hannunta yana cewa,

"Ko da wasa kada ki nuna akwai wata matsala a tsakanina da ke, idan ma kin faɗa ni ban san komai ba
kuma babu ni a cikin masu shaidu. Yanzu gaishe su muka zo yi zuwa daré zan dawo na ɗauke ki mu koma
gida, tun da kin amince za ki iya zama da ni a kowane hali."

'Innalillahi! Wai wannan wane irin mutum ne shi?'

'Ni mutum ne kamar sauran mutane aminiyar matata. Kuma na san darajar mahaifiyata kamar yadda kike
ƙoƙarin yi wa taki biyayya."

Ya ba ta amsa kai-tsaye tamkar ya shiga zuciyarta ya ji abin da take faɗa. Sai dai kallon da take yi masa ya
nuna zahirin ƙullewar kan da maganganunsa suka yi mata. Hannunta da ya riƙe gam ta kalla, inda ta yi
maganar ido a kan ya taimaka ya sake ta.

"Babu abin da zan ji ko da na kwana da ke a jikina ballantana riƙe hannu. Don haka ki je ki sanar da su zan
shigo mu gaisa sauri nake yi akwai abin da zan yi."

Sororo Minal ta yi ta kasa motsawa, tsabar ya gama kai ta maƙura ta yadda ba za ta iya fassara manufar
abin da yake nufi da ƙoƙarin aikatawa ba. Tana yunƙurin fita ƙannenta da yaran unguwar, suka baibaye da
motar. Yayin da wasu suka biyo su tun shigowarsu cikin layin har suka tsaya bakin gidan. Tsalle suka fari yi
suna ihu saboda ganin Minal tare da faɗin sunanta suna yi mata oyoyo.

Tsaki mai ƙarfi Jamal ya ja a daidai lokacin da ya hango yaran sun yi wa motarsa dafifi, har da masu shafa
jikin motar suna leƙen sa. Kasanacewar tintac ya sa ba su gano ita ce cikin motar ba har sai da ta fito suka
gan ta. Da murmushin yaƙe ta tarbi yaran tare da kiran sunayensu tana amsa gaisuwar da suke yi mata
ɗaya bayan ɗaya. A haka ta shige gidan suka bi bayanta ɗiii har da masu tirereniyar shan gabanta da niyyar
su riga ta shigewa.

Innarmu riƙe da buta a hannu tun lokacin da ta ji ihun yaran suna oyoyo, tare da kiran sunan Aminar. A
gurguje ta fito bayin kuma ta kasa ajiye butar har ta yi ido biyu da Amina. Saboda dukan da ƙirjinta yake yi
tsabar fargaba da tashin hankalin da take ciki tun bayan wayarta da Amina. Hakan ya jawo cikinta ya dinga
murɗawa tana faɗa bayi cikin gaggawa a duk lokacin da ta tuna suna kan hanyar zuwa gidan. Saboda ba ta
san da wace Jamal ɗin ya zo ba.
Sai dai kallo ɗaya da ta yi wa Amina ta ji sanyi ya ratsa zuciyarta. Ganin sauyin da ta yi a cikin 'yan
kwanaki, fatarta ta sauya saboda zama wuri ɗaya, kuma alamun hutu da jin daɗi ya fara kama jikinta.
Amma ko kaɗan ramar da ta ga ta yi ba ta tayar mata da hankali ba, ta ɗora hakan a kan fitinarta ce da
rashin danganar da ta ɗora wa kanta.

"Innarmu ina Babanmu?"

Maganar da Minal ta tare ta da ita kenan, wadda ta dawo da ita daga duniyar nazarín da ta afka.

"Ke ma kin sani a daidai wannan lokacin ba za a tarar da shi a gida b..."

"To, ki saka hijabinki ya ce a faɗa zai shigo."



SANARWAR!
INA NEMAN MUTUM 20 MASU SAYEN lLITTAFIN DAKAN ƊAKA.. COMPLETE BOOK 1-2 PRIZE 1K GA MAI
BUƘATA YA TAƁA NI TA NAN; 08022014771 ZAN SAKE SHI A RANAR 3 GA WATAN FEBRUARY.




D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

Follow this link to join my WhatsApp community: https://chat.whatsapp.com/I6nbHRDfqd05VKHdFpnfeB

*Assalamu alaikum*
*Na ce kuna neman inda za ku saya wa yaranku da kuma kanku kaya cikin sauƙi?*
*Shin kina neman kayan kitchen da bedsheet masu quality da sauƙi?*
*Tom ki shigo ki gane wa idonki idan price ɗin bai yi miki ba ki fece. Shaharariyar 'yar kasuwa; Rukayya
Musa Mahmud. Business name; Maman Suhaila. Dealers of all kind of kids clothes. Kitchen Ware's.
Necklace. Bedsheet. Shoes and bags.*
*Muna Kano Muna tura kaya ko'ina a cikin aminci da kula da amanar kayanku.*


*LAMBA SHA UKU.*

Wani kallo Innarmu ta yi mata kafin ta juya, jiki babu kuzari ta jawo hijabi ta saka tare da ɗauko
tabarma ta shimfiɗa. Sannan ta nemo 'yar tsugunno ta dasa a bakin ɗakinta, waton nesa tabarmar. Minal
kam tsaye kawai take rike da igiyar shanya a tsakar gidan nasu, kanta a ƙasa tana zana haruffan sunanta da
takalmin ƙafarta.

"To hamshakiya mandiya, ga ni na na shirya har na shamfiɗa masa tabarma, kice ya shigo na ji da wace ya
zo."
Zancen Innarmu kenan tana ɗage kai tare da aika mata hararar gefen ido. Minal ta saki igiyar shanyar ta
nufi hanyar fita gidan ƙirjinta yana bugawa. Cike da mamaki ta bi motarsa da kallo, saboda ganin har
lokacin bai fito ba. Tsaye ta yi bakin gidan tana aika wa motarsa harara tsawon minti biyu, kafin ta isa jikin
motar ranta a ɓace ta fara ƙwanƙwasawa. Duk da ta sani yana sane da ita kuma tana da tabbacin ya gan ta
sarai ta gilashi.

Zuge gilashin ya yi tare da aika mata wani kalar kallo ya yi guntun tsaki. Sannan ya mayar da gilashin ya
ɓalle murfin ya fito yana aika katsa wa wasu yara tsawa tare da aika musu daƙuwa. Saboda dukan bayan
motar ɗaya yake yi da bulala, yayin da wani yake dafe da boot yana leƙen ƙasan motar.
Kiran sunansu Minal ta yi tare da faɗin su bar wurin, saboda ranta ya yi babu daɗi. Duba da halin Jamal
tare da halin yaran ba za a jitu ba. Don tun da suka shigo layin da yaran suka biyo su da gudu yake ta tsaki.
Bai yi magana ba amma alamu ya nuna jin haushinsa ƙarara a kan abin da yaran unguwar suke yi masa.
Shigewarsa kawai ya yi ya bar ta tana yi wa yaran faɗa. Saboda ya ƙagu ya yi abin da ya kawo shi ya tafi
sabgogin gabansa.

Tun daga sallamarsa Innarmu ta fara rawar jiki da ganin sa, hakan ya sa ta shiga gaishe shi bayan sannu
da zuwan da yi masa baki washe. Ba tare da ta jira shi ya fara gaishe ta ba a matsayinsa na suruki. Minal ta
yi kasaƙe a ɗaki ranta a ɓace zuciyarta cike da jin haushin rawar jikin da Innarmu take yi a kansa. Shiru
kawai ta yi tana sauraron su har suka gama gaisawa kafin kafin Jamal ya fara magana.

"Da ma na zo ne na gaishe su ku, amna na ga kamar Baban ba ya gida."

"E, ya fita kasuwa tun da safe. Amma idan ya zo za a sanar da shi zuwanka."

Jamal ya sunkuye kai yana faɗin, "Babu damuwa, sai a gaishe shi kafin na dawo a lokacin da zan same
shi."

Daga haka ya ja bakinsa ya tsuke yayin da yake mutsu-mutsun fito da kuɗi aljihunsa. 'yan dubu sababbi kar
ya ajiye mata a gabanta yana faɗin,

"Wannan naki ne, a yi haƙuri babu yawa."

Sannan ya mayar da hannun yana ƙoƙarin lissafo wasu suka ji sallamar Baban Amina. Dukan su suka amsa
a tare, yayin da Amina ta fito daga ɗakin cike da jin daɗin ganin sa tana gaishe shi.
Baki har kunne ya amsa mata, sannan ya nufi inda Jamal yake zaune ya miƙa masa hannu suka gaisa cikin
mutumta juna.
Da murmushi ɗauke a fuskarsa ya ce, "Kun zo ganin mu ashe?"

"Mun zo Baba. Fatar mun same ku lafiya" Jamal ya amsa cikin ladabi.

"To madalla, dukan mu Alhamdulillah! Ya wajen Hajiyar ita ma?"

Jamal ya sake amsawa cikin sakin fuska ya ce, "Tana gaishe ku Baba."

"Muna amsawa, Ubangiji Ya yi albarka."

Daga haka shiru ya ratsa, yayin da Jamal ya miƙe yana ƙoƙarin saka takalminsa Baban ya ce, "A dai ƙara
haƙuri, in sha Allahu alƙawarin da na yi maka yana nan matuƙar A'isha ta dawo gare mu. Don haka kada ka
ji komai da sannu Allah zai kawo mana mafitar da za ta warware matsalolin gabaɗaya."

"Babu damuwa Baba. Ubangiji Ya bayyana ta cikin gaggawa."

'Ba Amin ba wallahi.'

Zancen zucin Innarmu kenan a lokacin da Baba ya dire nasa zancen. Amma daga Minal har Jamal sun karɓa
da 'Amin.'
Don dukan luguden da ƙirjin Minal yake yi bai hana ta saurin amsawa ba. Kai-tsaye wani sashe na
zuciyarta ta ji ina ma Nur ba ta tafin ba, wataƙila da halin da take ciki ba zai riske ta ba, ballantana ta ci
karo da abin da zamo mata barazana a gaba.

"Ke Amina! Me kike jira da ba za ki bi shi ku koma ba?"

Innarmu ta yi maganar tana zare mata idanuwa. Ganin Jamal yana ƙoƙarin fita Amina kuma tana ƙoƙarin
komawa cikin ɗakinta.

"Ta zauna, sai dare zan dawo na ɗauke ta."

Jamal ya yi maganar cikin sauri saboda bai shirya komawa da ita a lokacin ba. Innarmu ta yi saurin washe
baki tana faɗin,

"To ai shikenan. Tun da ka bar ta yi mana wunin. Amma da ba ka bar ta ba; ƙafa da ƙafa za ka koma da
ita."

Yana murmushi ya yi gaba, Baba ya raka shi har ƙofar gida yana saka masa albarka. Yayin da suka bar
Innarmu dafe da ƙirji saboda ƙaƙƙarfan bugun da yake yi mata babu ƙaƙƙautawa. Sosai hankalinta ya tashi
da jin wata sabuwar magana daga bakinsu, wadda ba ta san da ita ba. Tsabar ruɗewa kuɗin da ya ba ta ma
a nan ta bar su. Jikinta yana rawa ta isa bayan ƙyauren gidan a sukwane. Sai da ta sha jinin jikinta sannan ta
shiga leƙen su ta wata kusufa, tana hangen duk abin da yake faruwa daga inda take. Sai dai ko kaɗan ba ta
jin me suke tattaunawa a kau. Har suka gama magana Jamal ya fito da kuɗi daga aljihunsa, kamar yadda ya
ba ta shi ma haka ya miƙa masa. Cike da jin nauyi Baban ya ƙi karɓar kuɗin sai da ƙyar Jamal ya ci kansa ya
karɓa yana godiya, sannan ya ƙara saka masa wata sabuwar albarka bayan addu'ar gamawa da duniya
lafiya.
Sai da ya tayar da motarsa ya tafi bayan sun yi sallama, sannan Baban ya koma cikin gidan a daidai
lokacin da Innarmu ta isa bakin ƙofar ɗakinta, inda ta fara haɗa kan kuɗin bayan ta bar jikin ƙyauren cikin
sauri gudun ya kama ta. Don sun saba, a duk ranar da ya gan ta tana leƙen wa'azin yake zuba mata, sai ta
gaji da sauraro ta biye shi sun koma yin faɗa.

Yana ƙoƙarin shigewa ɗakinsa, da niyyar ɗaukar abin da ya dawo da shi gidan. Innarmu ta biyo shi baya
tana cewa,

"Ni kam Malam wai wane irin alƙawari ne ka yi wa mijin Amina ban sani ba?"

Juyowa ya yi yana kallon ta kamar ba zai ce komai ba, amma sanin wace ce ita ya yi magana fuskarsa a
cure ya ce,

"Ina ruwanki."

"Uhum, ko ma dai mene ne ai ya kamata na sani Malam. Saboda ko an dafa a ɓoye ai ba za a ci ɓoye ba.
Don yana da kyau a ce duk wani abu da ke faruwa ka sanar da ni. Idan dai har abin nan ya shafi Amina."

Murmushin takaici ya yi kafin ya ce, "Idan kuma bai shafe ta ba fa? Shi ma dole sai kin sani?"

Sum-sum ta bar wurin tana cewa, "Allah Ya ba ka haƙuri, ai da ma can na sani ba ka ɗauke ni a bakin
komai ba."

"Ke dai kika sani."

Ya yi maganar yana ci gaba da abin da yake yi, sai da ya gama sannan ya rufe ɗakinsa yana ƙwala wa Amina
kira. Cikin sauri ta fito ta durƙusa gabansa tana faɗin,
"Ga ni Baba."

Tsayuwarsa ya gyara, sannan ya dafa bango ya yi jim na ɗan lokaci kafin ya ce, "Na so na je har gidanki na
yi wasu maganganu da ke. Amma na ƙyale ganin Salame ma ta isa ba sai na je ba. Don haka kafin na ce
komai zan ce ki ji tsoron Allah, kuma ki sani aure ba wasar yara ba ne. Kada ki yi duba da yadda auren ya zo
ki ce za ki yi wa sunnar Ma'aiki riƙon sakainar kashi. Miji miji ne kuma wajibi ne girmama babba ko da a
gidan mashaya ne, ballantana tsakanin mata da mijinta. Saboda haka ki riƙe aurenki tsakani da Allah kuma
ki riƙe mijinki za ki ga ribar hakan a gaba. Amma ki sani ban ce ki shiga rayuwarsa da bin diddigi ba kamar
yadda kika ga Binta tana yi ba. Saboda kowane namiji da kalar halinsa, idan ita tana yi mini ina ƙyalewa shi
ba lalle ne ya ƙyale ki ba idan kika kwashi halinta. Don haka shawara ce na ba ki, amma ban ce dole sai kin
bi b..."

"Haba Malam! Yanzu shikenan idan ka tashi yi wa 'ya'yanka faɗa ko nasiha ba za ka naɗe tabarmarka
salun alun ba har sai ka saka ni zama bis...?"

Innarmu ta yi maganar ranta a ɓace kafin ya katse ta. Saboda tun da ya fara maganganun ta saka wa
zuciyarta sai sun yi faɗa, don dole sai ya sako laifinta ko kuma ƙarara ya nuna takaicinsa a kan wani halinta
a fakaice.

"Nononki da ta sha nake tsoron ya yi aiki a gidan aurenta. Don muddin ta biye wasu halayen da kike
gwadawa a cikin gidan nan; ba lalle ne halin ya bar ta zama gidan mijinta lafiya ba. Saboda kin fi kowa
sanin yadda aka yi auren, kuma an yi sa'a yaron ya san darajar manya. Ya kamata a ce ita ma an zaunar da
ita an faɗa mata darajar aure ta wuce sanin da ta yi masa."

Ya tsahirta da magana, su ma suka yi shiru babu wanda ya iya cewa uffan. Saboda Innarmu ruwa ya ci kai,
duk da ta gaji da abin da faɗan da yake yi mata a gaban 'ya'yanta. Shi ya sa sau da yawa tana son gyara
wasu abubuwan amma hakan ba zai hana ta sake kwatawa ba.

"Yanzu dai ka yi haƙuri, in dai don na yi tambaya a kan maganar da kuka yi ne; Allah Ya huci zuciyarka. In
sha Allah daga yau ba zan sake tayar da zancen ba. Amina kuma ina fatar ta yi zaman aure managarci
wanda za ta samu aminci tsakaninta da mijinta, ba irin zamana da kai ba. Tun da har yanzu ban wuce cin
fuska da gugar zana a wurin ka ba."

Nufar hanyar fita ya yi ba tare da ya ce mata komai ba. Saboda ya jima da sanin daɗin bakinta, kuma in
da sabo ya saba da halinta. Ta iya yin laifi kuma ta koma yi masa dabaibayi da maganganun da komai yake
son ɗaurkar mataki a kai sai ya sassauta.

Illa maganar da ya yi wadda ke nuna da Amina yake yi. Inda ya juyo yana faɗin,

"Tashi ki je, Allah Ya yi miki albarka."

Daga haka ya fice ya bar su jugum kuma tsaye cirko-cirko a tsakar gidan. Innarmu ce ta kawar da shirun
da cewa, "Ni fa wallahi sai dai Malam ya ga laifina, amma ba na fatar A'isha ta dawo garin nan ta zauna da
mu kamar baya. Saboda muddin ta dawo ba za ki taɓa samun nutsuwar da za ki samu lada a gidan mijinki
ba. Sai inda ƙarfina ya ƙare a kan haka, don ba zan taɓa bari ki zamo bora ba. Wahalar da nake sha a gidan
nawa mijin ta isa, ke kam daɗi za ki ji da yardar Allah."

Fuska a cure Amina ta ce, "Innarmu..."

"Yi mini shiru Amina. Ba fa zan zuba ido a saka mu kunya biyu ba. Kina kallo babu kalar surutun da ba a yi
mini ba a kan auren nan naki. Amma duk na shanye zagi da ƙazafin da ake yi mini saboda farincikin kin
samu gidan hutawa. To a kan me zan zuba ido A'isha ta dawo rayuwar mijinki ki koma bora? Wallahi ba zai
yiwu ba, sai dai a yi duk abin da za a yi amma zama daram ke da shi sai mutuwa. Duk wani ɗan baƙinciki sai
dai ya mutu...ke ko ke kika kawo mini gangancin da auren nan ya lalace wallahi sai na ɗauki mataki kanki.
Shi ma ina ɗaga masa ƙafa ne saboda a zauna lafiya amma ba wai don ina jin tsoron sa b..."

"Don Allah Innarmu ki yi shiru haka nan. Ba na jin daɗin yadda kike sako Babanmu a maganar nan,
saboda shi ma yana so na zauna inda hankalina zai kwanta. Ni ma kuma na yi alƙawarin zama da shi komai
tsanani sai inda ƙarfina ya ƙare. To me ya rage kuma Innarmu?"

10 / 29