Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
fara sauyawa har yana ƙoƙarin haɗa jikinsa da nata cikin nutsuwa ba tare
da kyara ko hantara ba.
Sallamarsa da ta ji ya sa ta miƙe tana cewa Hajiya za ta shiga ɗaki ta yi wanka ta yi sallah. Ta so hana ta,
amma ganin ta fi son tafiyar ya sa ta yi 'yar dariya ta ce,
"Jamal ka daina tsorata mini 'ya, ba na son tana ƙin sakewa a duk lokacin da ta gan ka."
Bai ce ƙanzil ba sai murmushin da ya yi yana sosa kansa tsawon minti biyu sannan ya ce, "A taƙaice dai
na zama dodo."
"Kusan haka, don haka ko ka bari ko na ɗauki mataki a kanka."
"Ai da ma na san kin fi son ta da ni. Ga shi ma ko lafiya ban da..ina jin kamar a gidan nan zan kwana yau
Hajiy..."
"Ka je gidanka gaskiya! Ko ba komai za ka sha maganinka a can kafin ka kwanta."
Bai ba ta amsa ba sai da ya baje kan kujerar sannan ya ce, "Matsalar jikin ne nawa babu ƙarfin da zan iya
yin tuƙi a yanzu. Kuma gidan babu daɗi daga ni sai maigadi."
Wani kallo ta yi masa cike da jin daɗin ganin ya fara damuwa da kewar Minal ta ce, "Ji wani sanabe,
yanzu duk shekarun kwanakin da ka yi kana kwana a cikin gidan ba ka san babu daɗi ba sai yau da kake son
kwana a gidan nan?"
"Kawai ki yarda Hajiya, za. Jaraba kwana a nan ɗin, gobe idan na samu ƙarfi sai na koma can."
Farinciki fal zuciyarta ta ce, "Ba kwanan ba, ba na son ka takura mini yarinya, saboda haka tashi ka je
ɓangarenka ni zan rufe ƙofarmu gudun na manta ta kwana a buɗe ban sani ba."
"Idan na tashi zan sanar da ke ki ruf.."
"Ba fa zan bar ka a nan ba! Tashi ka je na rufe ba za ka saka ni surutu a cikin dare ba."
Ta yi maganar tare da tsare gida alamun babu wasa, haka ya miƙe ba don ya so ba ya koma ɗakinsa da ke
harabar gidan. Sannan ta rufe ƙofarta ruf ta bar makulli a jiki tana tofe ko'ina da addu'a. Jamal kam barci ya
yi cikin kewar Minal, sai da ya kira Zee a waya suka yi abin da suka saba yi sannan ya rage zafi. Amma a
zuciyarsa bai fasa shan alwashin yi wa Minal muguwar mamayar da zai koya mata hankali ba.
Da safe bai tsaya kari ba ya fice gidan a gaggauce saboda kiran da aka yi masa wurin aiki. Kasancewar
yana da wasu kaya a gidan bai koma gidansa ba daga nan ya zarce ma'aikatarsu.
***
Tsawon kwana bakwai Hajiya tana tsaye a kan Minal, sannan da takatsantsan a kan kusancinta da Jamal
har ta kammala shan magungunan ta cinye kazar sababi. Don tun daga ranar da ya kwana gidan ya tare a
nan bai koma gidansa da kwana ba. Hakan ya sa Minal ta shiga feshin wanka da kalolin shiga cikin sababbin
kaya tamkar tarwaɗa. Saboda Hajiya ta sa an yi mata dilka da halawa fatarta ta ƙara murjewa har da haske
sai da ta yi.
Gyaran da ya ƙara susuce Jamal ya zama bita-zai-zai, Hajiya tana korar sa yana mannewa. Wani lokaci da
gangan yake naɗewa a cikin ɗakinsa, saboda kawai ya ce bai da lafiya a kawo masa abincinsa a nan. Don
kawai ya yi amfani da damar ya rage zafin da ke ƙona masa jiki tsabar fitinanniyar sha'awar Minal ta yi
masa mugun kamu.
A farko Hajiya ba ta gano lagonsa ba, sai a wata rana da ta ji Minal shiru ba ta dawo daga kai masa
abincin ba, babu jinkiri ta bi bayanta cikin zullumin kada ya samu kanta tun kafin ta gama gyaran. Saboda
haka Minal tana shiga ya rufe ɗakin ya shiga luguiguita ta son ransa, don ita ma magungunan da take sha
sun fara aiki a jikinta. Ta yadda babu abin da ta fi so a lokacin kamar ya yi mata abin da ya koya mata a cikin
'yan kwanakin. Ko boren da take yi masa da zabura idan ya taɓa ta gabaɗaya ta daina yi, wani lokacin ma
har ɗoki take yi da dakon sa a kan cewa a kawo masa abincin don kawai ta je ya ɗora mata sabon darasi.
Ranar da Hajiya ta rutsa su a cikin yanayin da ba ya faɗuwa, dole ta tattara mata kayanta ta kai ta
gidansa da kanta ta ce Allah Ya ba da zaman lafiya. Da ma Umma Ade ta ba ta shawarar ta miƙa masa
matarsa tun da ya kasa haƙuri ya biyo ta gidan ya tare. Amma Hajiya ta kafe a kan babu inda za ta je sai ta
gama gyara ta tsaf kuma sai kayan matan sun bi jikinta.
Kasancewar bai san Hajiya za ta mayar da ita ba, sai bayan ya dawo gidan bayan magrib cin abinci. Yana
zancen abincin, Hajiyar ta ce masa ya je gidansa matarsa ta yi masa girki sai ya ci a can. Sake da baki ya
dinga kallon Hajiya sannan ya ce,
"Shi ne aka mayar da ita ba tare da na sani ba?"
Wani kallo ta yi masa kafin ta ce, "Da na zo da ita izininka na nema?"
Sosa kai ya shiga yi yana 'yar dariya saboda har zuciyarsa ya ji daɗin damar da aka ba shi don ya ci
karensa babu babbaka. Amma sai ya koma alayen jan Hajiya da hira kamar ba ya son tafiya, har da cewa
shi a nan gidan zai kwana bai tashi komawa can ba.
Gaba Hajiya ta saka shi da abin bugu ta koro shi har harabar gidan tana yi masa Allah Ya tsare. Cikin wani
ƙumaji a ransa ya fice gidan aguje maigadi yana ɗaga masa hannu da addu'ar sauka lafiya. Bai zame ko'ina
ba sai Yahuza suya, a nan ya zaɓi ƙosassun kaji biyu da sauran tarkacen ci da sha ya buga motarsa zuwa
gida. Zuciyarsa cike da ɗokin zama ango a daren ranar, ranar da ta zamo daidai wata biyu da aurensu.
Yanzu wasar za ta fara.
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda
tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta
Ibrahim.
JERIN LITTAFAINA GA MAI BUƘATA!
1. ABOKIN AIKINA 1K
2. BAƘON YANAYI 1K
3. DAKAN ƊAKA 1K
4. AMFANIN FITILA 1K
5. JIKI DA JINI 1K
6. GIDAN AURE ₦700
7. TARTSATSI 1K
8. MAKANTAR SO 1K
9. ZUBAR HAWAYENA ₦700
10. RUWA DA ƘANƘARA ₦700
11. BAKAN GIZO ₦700
12. MUSAYAR ZUCIYA ₦500
13. DIJE ƘARANGIYA ₦500
14. DACE DA JUNA ₦500
D.
✍🏼 AUTA CE
[2/20, 22:17] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*ASHIRIN DA BIYU.*
Minal kuwa, tun bayan gama sallar Isha ta kwaɗa wanka tare da feshe jikinta da fitinannun turaruka,
waɗanda Hajiya ta yi mata kyautar su a matsayin tsarabar zaman aure. Ta sha gayunta cikin wani
tsadadden lesi fari mai adon golden. Bayan ɗan kunne da sarƙa har da agogo da 'yan hannu ta saka. Ta fito
shar da ita ta ko'ina sai juyi take yi zuciyarta cike da jin daɗin yanayin da farincikin zuwan ranar. Saboda
jikinta ya ba ta daga ranar farincikin da Hajiya take hasashen zuwansa zai wanzu, matuƙar Jamal ya gano
darajarta.
Ta zauna falo tana kallon Bollywood tare da dakon dawowarsa. Don ta ci alwashin nuna masa ita daban
ce a cikin matan bariki, kuma ta san darajar kanta. Sai dai a gefe ɗaya na zuciyarta yana yi mata gargaɗin
kada ta yi abin da zai lalata musu daren, don ta jima tana tsumayin zuwansa.
Hakan ya sa tun da ta ji ƙarar buɗe gate da ƙugin motarsa jikinta ya hau tsuma. Saboda tsananin bugun
da ƙirjinta yake yi, babu shiri ta zabura ta faɗa ɗaki jikinta yana rawa. Haka kawai ta tsinci kanta cikin wani
matsanancin tsoro, ƙirjinta ta dafe tare da rufe ido a daidai lokacin da ta ji motsin buɗe ƙofar falo. Jinin
jikinta ta sha saboda jin sautinsa yana faɗin,
"Ina matar gidan ne?"
Cikin sauri ta kwanta bakin gado tana rufe ido da nufin yin baccin ƙarya. Amma kuma dukan luguden
uku-ukun da ƙirjinta yake yi, ya tona asirin lamfon da ta yi a lokacin da ya shigo ɗakin ya yi tsugunno bakin
gadon yana ƙare wa fuskarta kallo. Hannunsa ya kai saman leɓunanta yana murmushi ya ce,
"Da ma kin tashi don bugun zuciyarki ya tona miki asiri ba wani baccin da kike yi."
Dariyar da ta so yi ya sa ta yi hanzarin juya kwanciya ta ba shi baya. Bombom ya ɗin ta ya ƙura wa kallo
kafin ya sauke ajiyar zuciya ya miƙe, shi ma ya raɓa ta gefenta ya kwanta tare da rungumo ta jikinsa yana
shinshinar ƙamshinta. Ya shiga goga mata gashin sajensa a wuya cikin shauƙi yana faɗin,
"Wannan amarya so take yi kawai ta ja mini aji."
Ya yi maganar cikin wata kalar murya a lokacin da ya zura hannunsa ɗaya ta ƙarƙashinta, sannan ɗaya a
saman jikinta ya rungumo ta gabaɗaya yana sauke ajiyar zuciya. A lokaci ɗaya ya yi nasarar kai hannuwan
saman ƙirjinta yana aikin da zuciya take ta kwaɗaita masa. Cikin ɗan lokaci daga shi har ita suka fita cikin
hayyacinsu, saboda ya koma samanta yana yi mata wani kalar wasannin da ya jima da sanin su ne
makamar kowace mace. Numfashi ta shiga saukewa tana ɗan kukan da ke ƙara hautsina masa lissafi.
Hakan ya sa ya nemi haukacewa gabaɗaya yana neman kan hanyar da zai ɓillewa a sukwane. A lokacin
nata hankalin ya dawo jikinta cikin tsoro ta shiga ture shi tana ƙoƙarin hana shi abin da yake ƙoƙarin
aikatawa. Kasancewar jikinsa ya yi laushin da ba zai iya komai ba, ba ta sha wuya wurin zare jikinta daga
nasa tare da tashi zaune tana faɗin,
"Malam abincinka yana falo."
Ta yi maganar cikin harɗewar numfashi tare da ƙoƙarin saita nutsuwarta. Kifewa kawai ya yi tare da dafe
jijiyarsa da ke bugawa tsawon mintuna kafin ya samu daidaitar yanayin da yake ciki. Ido ya bi ta da shi a
lokacin da ta sauka gadon ta nufi ƙofar fita tana faɗin,
"Ni na tafi ka same ni a can saboda kai na tsaya jira mu ci abincin."
Ta fice ƙirjinta yana bugawa zuciyarta cike da kwaɗayin ba shi haɗin kai kamar yadda yake buƙace. Sai dai
tuna ba su yi komai na al'adar daren farko da aiwatar da sunnar Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama
ba, hakan ya sa ta haɗiye ƙwalamar ta bar masa ɗakin. Saboda tana son aurensu ya yi albarka kuma idan ta
biye jarabarsa ba zai ɗaga ƙafa ba, ballantana har ya yi abin da ya dace.
Tana tsaka da zuba abincin ya iso wurin ya tsaya bayanta, tare da rungumo ta yana shafa mata jijiyarsa
da ke tsaye har lokacin. A tsayen ma sai da suka kwashe minti goma suna tsotse-tsotse kafin ta zare jikinta
ta zauna babu shiri. Saboda ƙafafuwanta sun yi sanyin da suka gaza ɗaukar gangar jikinta. Shi ma ya ja
kujerar kusa da ita yana dafe kansa ya ce,
"Ni fa abincin nan ma da an bar shi na fi son babban abincin."
Wani kallo ta yi masa tana haɗe rai tare da tura masa plate a gabansa tana faɗin, "Ni dai ka ci tun kafin ya
yi sanyi."
Abincin ya kai wa kallo kafin ya damƙo hannunta ya fara shafa fuskarsa cikin wata kalar murya ya sake
cewa, "Ni dai a ba ni wancan abincin na haƙura da wannan ba sai na ci b..."
"Da ma na sani ba ka son cin abincin mayya. Don haka ka bar shi kawai tun da kana tsoron a lashe maka
kurwa."
Ta ƙare maganar tare da zare hannunta tana jan abincin gabanta ta fara ci, tsawon minti biyu yana kallon
ta babu ƙiftawa, kafin ya ja numfashi ya sauke yana faɗin,
"Mayya ta gama kama kurwata, abincin ma zan ci tun da kina so. Amma da za a ba ni babban abincin a
madadin wannan zan fi farinciki."
Wani kallo ta yi masa mai ɗauke da harara, sannan ta ci gaba da cin abincinta kamar ba ta ji me ya faɗa
ba. Ya ja cokalin da ke cikin abincin ya fara kai bakinsa yana cewa,
"Abincin nan bai isa ya sa a yi fushi da ni ba. Ki bar yi mini kallon uku kwabo gaskiya ce na faɗa na fi son
wancan abin da wannan."
Ya yi maganar cikin marairaice fuska da muryar shagwaɓa. Yam tsikar jikinta ya tashi, saboda ita kanta ba
ƙaramar jarumta ta ara ta yafa wa jikinta ba. Kasancewar ita ɗin ma a matse take da shi saboda
magungunan da ta sha sun gama sauya ta koma jarabatu. Don a rana tana sauya pant sau biyu zuwa uku,
tsabar taɓon da take ciki koyaushe jikinta cikin danshin jaraba. Musamman da ya tayar da ita tsaye
gabaɗaya ya buɗe makunnnin famfonta tun kafin ta fito daga ɗakin.
A daddafe suka kammala cin abincin hannunsa ɗaya a cikin nata yana wani irin salon da ke ƙara tayar
mata da hankali. Hakan ya sa daga ita har shi ba su ci abincin kirki ba, don ko kajin da ya siyo sai da ya
gama lallatsa ta sannan ya ɗauko su daga kan Centre table ya kawo saman dinning, a nan ma suka tsakuri
kaɗan suka ture. Da kansa ya kai shi firij ya adana sannan ya fito a daidai lokacin da Minal ta shige ɗaki
tana juya mazaunai. Bin ta ya yi dafe da ƙugu kamar mai tsohon ciki, saboda 'ya'yan jijiyarsa gabaɗaya sun
haye har sun fara yi masa ciwo.
Toilet ta nufa shi ma a can ya bi ta kai-tsaye. Arwala ya ba ta umarnin yi fuskarsa a haɗe saboda zogin da
'ya'yan jijiyar suke yi masa. Babu ɓata lokaci suka fito tare ta shimfiɗa musu sallaya. Cikin minti goma suka
kammala komai tun daga kan sallar har zuwa addu'o'in da ake yi. Sosai ya ba ta mamaki ganin yadda yake
ɓarin ayoyi da addu'a tamkar wani Balarabe. A ranta ta shiga jinjina girman saninsa ga Addini, da girman
kaucewarsa a kan sharholiyar ransa a kan bin mata.
Nan take ranta ya ɓaci, saboda tuno Zee da abin da suka aikata a daren da ya kwana da ita cikin gidan. Ta
miƙe daga kan sallayar ta fara zare hijabi tana naɗewa fuskarta a cure. Saboda wani hawaye mai zafi ya
shiga kwaranyo mata a kumatu.
Ganin ta a tsaye tana ƙoƙarin sauya lesin jikinta zuwa rigar bacci, ya yi hanzarin tashi ya isa inda take ya
damƙe rigar, tare da fisge ta ya wurgar. Kallo ta ƙura masa daga ita sai pants da bra hawaye yana zarya a
cikin idonta. Babu ɓata lokaci ya ja ta jikinsa yana wani kalar nishi idonsa rufe ya shiga sarrafa ta son ransa.
Duk da ya ga hawayenta amma zuciyarsa ba ta kawo komai a ransa ba, sai da ta zare jikinta tana nuna shi
da hannu cikin muryar kuka ta ce,
"Ba zan taɓa amincewa da kai a matsayin mijina ba, matuƙar ban ga shaidar da ke tabbatar mini babu
wani ciwo a jikinka ba. Saboda ina son kaina ba na son abin da zai sa iyayena su yi asara ta, a lokacin da ka
manna mini wani ciwo a sanadin matan banzan da kake bi."
"Ya Salam!"
Abin da ya faɗa kenan yana dafe kansa da jijiyarsa da ke ta cika tana batsewa. "A tunaninki zan iya cutar da
ke ne?"
Ya jefa mata tambayar ransa a ɓace, kafin ya sake magana cikin haɗe rai ya ce, "Babu wani ciwon da ke
jikina ballantana na goga miki, dalilin hakan ya sa na shirya wa irin wannan ranar don na san za ta zo. Don
haka jira ni minti biyu zan je na ɗauko miki shaidar asibitin da ta tabbatar da ba na ɗauke da kowane irin
ciwo. Saboda Hajiya da kanta ta saka ni awon ba tare da kin sani ba, kuma ba don kowa ta yi hakan ba sai
don ke da kare haƙƙinki gudun a cutar da ke a banza. Amma tun da ita ma ba ta yi gwaninta ba jira ni na zo
ki ga komai da idonk..."
Yana ƙoƙarin barin wurin ta riƙo hannunsa hawaye yana fareti a kan fuskarta ta faɗa jikinsa tana kuka. Jim
ya yi rungume da ita tsawon minti uku kafin ya sauke ajiyar zuciya ya koma rarrashin ta. Jan ta ya yi har
zuwa bakin gadon suka zauna sannan ya sake cewa,
"Yadda kika san ba na son wani abu ya same ni, haka ke ma ba zan so na yi silar wargaza miki lafiyar jiki
ba. Allah shi ne shaidar ban da wani ciwon da ya wuce ciwon damuwar da ke tare da ni. Shi ma ɗin a
hankali ya fara sauka saboda ba na son Hajiya ta rasa ni tun yanzu kafin na ajiye mata jikoki.
Wani kallo Minal ta yi masa mai ɗauke da harara ta ce, "Ba sai idan ina haihuwar ba." Ta ƙare maganar
tana turo baki, ya yi hanzarin kai bakinsa saman nata ya tsotso leɓunanta kafin ya ce,
"A yau zan ba ki cikin 'ya'ya biyu har uku ma idan kina so."
Ƙoƙarin zare jikinta ta yi cike da jin kunya tana haɗe rai ta ce, "Ni dai don Allah ina so ka yi mini wata
alfarma da alƙawari ɗaya."
Duk da ba ta faɗa ba, amma ya fahimci inda ta dosa. Don zuciyarsa ta gama ba shi abin da take so ta
faɗa, hakan ya sa ya yi magana tun kafin ta furta abin da ke ranta ya ce,
"Tun daga ranar da na yi awon nan, ban sake kusantar wata mace ba. Kuma in sha Allahu ba zan sake ba.
Matuƙar za ki dinga ba ni kanki a duk lokacin da na buƙata."
"Saura ɗaya tun da ka gano ɗaya. Ina so ka yi mini alƙawarin babu kai babu Nur...."
Dam-dam ƙirjinsa ya shiga bugawa, nan take ransa ya ɓace saboda ta tuno masa da abin da yake ƙoƙarin
binnewa. "In dai wannan ce matsalarki kuma kike so na yi alƙawari, tuni na yi wa kaina iyaka da