Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar Ƙauna Complete Hausa Novel by Hadiza D. AUTA

Author :  HADIZA D. AUTA Category :  African Stories & Novels

Chapter   24 / 29

69K to 72K   out of 85.8K words

haifar
masa. Sai da ya nisa sannan ya yi magana cikin raunin zuciya ya ce,

"Tabbas ke 'yar halas ce A'isha kuma mai ƙoƙarin rama halacci. Sannan kin yi gadon mahaifinki tun daga
kan kamarsa har zuwa kyawawan halayensa. Saboda kin so wa Amina abin da kike so wa kanki, kuma kin
guji abin da zai lalata mana farin ciki duk da abin da uwarta ta yi miki a baya, sannan kuma tana ƙoƙarin
ɗora sabo a yau. Allah Ya yi miki albarka A'isha, sai dai abin da na kasa ganewa, shin ya ya aka yi da auren
da kika ce za ki yi yanzu, bayan matsalar da kike tare da ita? Ko shi ma.."

"An yi bincike Baba, wannan zancen duka ƙage ne ko kuma na ce an yi komai ne a bisa kuskure da
ƙaddara. Amma ba ni ce asalin wadda abin ya faru a kanta b..."

"Alhamdulillah! Allah mun gode maka!"

Baba ya yi maganar tare da kai goshinsa ƙasa yana sujudar godiya ga Ubangiji. Zuciyarsa wasai ya yi
maganar da ta saka ta hanzarin kai kallonta gare shi baki buɗe. Bayan bugun da ƙirjinta ya shiga yi babu
ƙaƙƙautawa.

"Halinki na kirki ba zai taɓe ba A'isha, don haka a yanzu na yanke hukuncin aura miki mijin Amina ko da
kowa ba ya so. Da ma can na yi wannan alƙawarin saboda ganin yadda hankalinsa ya tashi a kan rashinki
sannan da auren Amina. Don ina da iko a kan aurar da ke, saboda mahaifinki Alhaji Haroun ya ba ni
wannan damar da kansa kuma a bisa yardarsa. Saboda haka ba zan bari ki rasa wanda kike so yake son ki
tsakani da Allah ba, ko da a garin yin hakan zan rasa raina matuƙar ke za ki samu farinciki."

"Baba.."

"Yi shiru kawai A'isha, Allah Ya sani ba zan bar rayuwarki ta yi tangal-tamgal ba. Dole ne ke ma a samar
miki da farin ciki ko da hakan zai jawo matsalolin da suka fi waɗanda ake hasashen faruwar su."

Shiru Nur ta yi masa, saboda ganin ya fiddo wayarsa a aljihu cikin rawar jiki hannunsa yana rawa ya
danna wa Jamal kira. Sai dai har ta gama ringing bai ɗaga ba, yana ƙoƙarin sake yi masa wani kiran ta
durƙusa gabansa tana magiya, hawaye yana zuba bayan ta haɗa hannuwanta ucealamun roƙo.
"Don Allah Baba, don Allah kada ka bari a a jefa Amina cikin tashin hankali. Allah Ya sani na bar mata
Jamal har abada, kuma zan yi ƙoƙarin raba zuciyarsa da sona ko don ta ji daɗin zaman aurenta....na yi maka
wannan alƙawarin Baba, don Allah ka bar Amina da mijinta su rayu su kaɗai ba tare da na shiga tsakiyarsu
ba."

Tashi kawai ya yi ya fice daga ɗakin ba tare da ya ce ƙanzil ba. Ya bar ta zugum ta tagumi tana nazari. Har
ya dawo ɗauke da kwanon jalof ɗin shinkafa ya ajiye mata gabanta yana faɗin, "Fara ci, bari na je na kawo
miki ruwan sha." Nur ta kalli abinci kawai amma ko kaɗan zuciyarta ba ta buƙatar cin komai. Baba ya dawo
da kofin ruwa a hannunsa yana waya. Kai ɗaga tana kallonsa cikin wani sabon tashin hankali saboda saƙon
da ta ji yana miƙa ga Jamal.

"E, ka zo na amince zan aura maka auren A'isha gobe idan Allah Ya kai mu."

****
Ɓangaren Jamal kuma, yana barin gidan kai-tsaye wani masallaci ya tsaya ya yi sallar Asr, lokacin ƙarfe
biyar har ta gota, sannan ya yi gidan ƙanen Babansa ya tsinke zuciyarsa a ƙagauce da son ƙaddamar cikar
burinsa. Cikin sa'a ya tarar da shi gida suka gaisa sama-sama. Don ya fahimci Jamal ba ya cikin nutsuwarsa
tun daga kan kallon farko da ya yi masa.

"Baba wurin ka na zo!"

"To, ga ni Jamal, Allah Ya sa lafiya?"

"A kan maganar yarinyar nan ce da na so aure a farko aka musanya mini da 'yar'uwarta...."

"To, to na dai gane."

Ya gyara zama yana faɗin, "Baba ta dawo yau. Kuma a yadda na ji ta faɗa gobe ne ɗaurin aurenta da
wani. Sannan wallahi Baba na sani ba za ta so kowa bayan ni ba...don ina da tabbacin ba ta son ko ma
wane ne auren haɗi ne za a yi mata. Baba don Allah..."

"Dakata Jamal." Baba Hassan ya katse shi tare da ɗaga masa hannu kafin ya sake cewa, "Ka manta da
abin da aka ce ya hana ku auren tun a farkon da aka so yi Allah bai nufa ba?"

"Ban san komai ba Baba, babu abin da na sani a kai don ba a sanar da ni ba."

"To ka je ka tambayi Hajiyata, ita ta sani don ta san komai tun kafin a aura maka yarinyar da ke gudanka
a yanzu. Kuma idan ta amince ka auri yarinyar a yadda taken, ka ce ta kira ni da kanta ni ta sanar da ni zan
je na yi wakilcin auren."

Baba Hassan ya ƙare maganar yana miƙewa tsaye saboda sanin abin da ya zo da shi ba zai taɓa karɓuwa
a wurin su ba. Kuma da gangan ya ce sai Hajiya ta amince don ya san ba za ta amince ya auri Nur a yadda
suka san ta ba. Har ya fara yi masa magiya Baban ya katse shi da cewa, ya je kawai ya roƙe ta idan ta
amince a cikin daren ma zai nemi a ɗaura auren kafin safiya.

Jiki babu kuzari Jamal ya nufi gidan Hajiyar, daidai lokacin kiran Baban Amina ya shiga wayarsa, a nan ne
yake sanar da shi batun amincewarsa. Farinciki fal zuciyarsa ya dinga tuƙi wani sanyin daɗi yana ratsa masa
zuciya. Bakinsa a washe ya isa ƙofar gidan Hajiyar, sai dai tun kafin ya shiga maigadi ya sanar da shi ba ta
nan. Waya ya ɗaga ya kira ta, a lokacin ana ta kiraye-kirayen sallar magrib. Babu ɓata lokaci ta sanar da shi
tana gidansa tun da rana. Katse wayar kawai ya yi ya nufi gidan zuciyarsa cike da tunanin abin da ya kai ta
gidan duk da zumuɗin da yake yi a kan sanar da ita abin da ke ransa. Sai a lokacin tunanin halin da ya bar
Minal ya faɗo ransa, kansa ya dafe tamkar ya kwarara ihu ya ce,
"Ya Salam! Minal kin ɓaro mini aiki tun da kika kira Hajiya."

Gudun motar ya ƙara tare da buga wani uban tsaki yana faɗin, "Me ya sa ba ta bari har na dawo ba za ta
kira Hajiya? Bayan kuma ta sani dole ne sai ta yi mini faɗa.... mitsssss! Wannan tonon asiri har ina? An yi
mace babu sirri ita a komai sai ta yi abin da zai sa Hajiya ta ga laifina."

Haka ya dinga sambatu masu ɗauke da ganin laifin Minal a kan tunanin da ya tsaya masa a zuciya. Don
ya tabbatar wa ransa ita ce ta nemo Hajiyar don jin haushin ya bar ta tsawon lokaci bai dawo ba. Sai da ya
tsaya masallacin unguwarsu ya yi sallah sannan ya nufi gidan ƙirjinsa yana bugawa.
Gunjin motarsa da Minal ta jiyo ƙirjinta ya buga dam-dam, tsam ta yi da ranta, abincin da Hajiya ta saka
ta gaba sai ta cinye ma ta ji ya gundure ta. Fahimtar hakan ya sa Hajiya ta yi magana cikin haɗe fuska tana
cewa,

"Ki ci abincinki, kada ki ce komai ki bar ni da shi na ce."

Minal ta yi marau-marau da ido tana zuƙe majinar kuka, saboda wa'azin da suka saka ta gaba suna yi
mata a kan haƙuri da dauriya ya rage mata zafin da ke ranta.

Da guntuwar sallamarsa ya shigo falon yana sosa kai, ganin Hajiya da Minal a cikin falon, saboda Inna
Ade ta yi gida bayan ta gama girka musu abincin dare. Da muzurai ya isa gaban Hajiyar ya durƙusa cikin
wani sabon ladabi yana cewa,

"Allah Ya huci zuciyarki Hajiya. Na san na yi laifi amma don Allah don girman Ubangiji a yafe mini."

Wani kallo ta yi masa cikin haɗe girar sama da ta ƙasa kafin ta ce, "A yafe maka ka dinga rungumar mata
a tsakiyar titi ana yi maka bidiyo?"

Baki ya rufe cikin tashin hankali, saboda ba zatar da maganar ta zo masa. Don bai taɓa tunanin abin da
ya faru har ya yi watsuwar da Minal z ta sani har Hajiya ta ji labari ba. Ƙoso biyu Hajiya ta yi masa a tsakiyar
kai kafin ta nuna shi da hannu tana faɗin,
"Wai har yaushe za ka daina bar wa rayuwarka abin faɗi? Yanzu mene ne amfanin yin abin da ka aikata
ko daga kai sai ita fanɗararriyar yarinyar ballantana a gaban jama'a?"

"Wallahi Hajiya..."

"Babu abin da za ka faɗa na yarda da kai, yarinyar nan kuma tun da na sanar da kai babu kai babu ita,
muddin aka ce an sake ganin ka da ita sai na tsine maka! Kai ko ƙanwar ubanka ce na raba ka da ita babu
kai babu ita! Idan kuma ka ƙi ji sai dai ka zaɓi ɗaya ko ni ko ita."

Shiru kawai ya yi yana kallon Hajiyar kafin ya miƙe tsaye yana furzar da iska mai zafi a bakinsa.
Hannuwansa duka a cikin aljihunsa bayan kan da ya duƙe yana nazarin abin da zai faɗa, duk ya sani ba
daidai zai yi ba, amma kai-tsaye ya ɗago kansa fuskarsa a cure ya kalli Minal yana faɗin,

"Na haƙura da aure, kuma na haƙura da rayuwa da kowace macen da za ta amsa sunan matata . Don
haka ki haɗa kayanki ki je gidanku na sake ki saki ɗaya."


Cabɗijam! Yanzu littafin ya fara. Kuma daga nan na tsaya ƙarshen FANSAR ƘAUNA BOOK 1. Wanda na bayar
a free tun daga farko har fejin ƙauna.
Sai bayan sallah idan Allah Ya kai mu za mu haɗu a cikin BABI NA BIYUN LABARIN. Wanda nake yi muku
albashir abubuwan da ke cikinsa har ya fi wanda ya faru a farko. Don a cikin labarin akwai ban tausayi, ban
haushi, sannan da ban al'ajabi bayan kalolin abubuwa masu tsayawa a zuciya. Kada ku manta, har yanzu ba
mu san asalin wace ce Nur ba, sannan ba mu ji labarin dalilin da ya sa ta fansar wa Minal Jamal ba.
Ga masu buƙata ku biya ₦1k kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda tura kuɗi ta opay
yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta Ibrahim.


D. AUTA CE
✍🏼

*FANSAR ƘAUNA!*

*BOOK 2.*

*HADIZA D. AUTA*

30.

Dirim-dam-dam! Shi ne sautin bugun da ƙirjin Hajiya ya yi, sannan a lokaci ɗaya ta yi suman zaune bayan
gumin da ya jiƙa mata goshi. Bakinta a buɗe idonta a kansa har ya shige ɗakinsa ba tare da ta iya furta ko
kalma ɗaya ba, don ta kasa matsowa ballantana ta samu cewa wani abu ko don ta rage nauyin da danne
mata zuciya.

Minal kam hannu ta ɗora a ka cikin tsananin tashin hankalin da ya so zauce ta, wata kalar ƙara ta fasa
tare da faɗin,

"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un!"

Salatinta ya farfaɗo Hajiya daga suman zaunen da ya kafce ta, sai da ta sauke nannauyar ajiyar zuciya
sannan ta yi magana cikin sanyin murya.

"Ki kwantar da hankalinki! Babu inda za ki je sai kin gama idda. Duk abin da kike buƙata ki sanar da ni a
waya."

Tana ƙare maganar ta miƙe kanta yana sarawa jiri yana kwasar ta ta fice daga falon, da sassarfa ta sauka
ƙasa zuwa harabar gidan tana ganin komai dishi-dishi. Da ƙafa ta fara tattaki bayan ta bar gidan ba tare da
ta san tana tafiyar ba. Sai daga baya hankalinta ya dawo jikinta ta kira direbanta suka haɗu a hanya ya
ɗauke ta. Kasancewar Inna Ade ta yi gida bayan ta gama rarrashin Hajiyar a kan ta bi komai a hankali
gudun abin ya ƙara rincaɓewa.

***
Minal kam tsabar firgici ya yi mata rumfa bayan fitar Hajiyar ta zabura cikin sassarfa ta bi bayansa zuwa
ɗakin nasa gumi yana feso mata a kan fuska da jikinta gabaɗaya.

"Ka ƙarasa sauran igiyar biyu! Ina son na san babu wata sauran alaƙa da ta rage tsakanina da kai."

Ta ƙare maganar riƙe da ƙugu tana kallon sa ƙur da ido ko ƙiftawa babu, a cikin wani mugun yanayin da
take jin zuciyarta tana fitar da hayaƙin wutar da ƙiris ya rage ta kama da wuta. Jamal ƙanzil bai ce mata ba
har ta gaji da tsayuwa ta maimaita maganar bai kula ta ba, ballantana ya dakatar da haɗa kayan da yake yi
a cikin jakarsa ta matafiya, tsabar sauri cusa kayan kawai ya dinga yi fuskarsa a cure har ya gama zuba duk
abin da yake so ya zuge zif. Cikin zafin nama ya fisgi jakar ya yi gaba, ta bi bayansa cikin wani irin yanayi
mara misaltuwa ganin abin da yake ƙoƙarin aikatawa, don zuciyarta ta tabbatar ƙwaɓarta ta gama yin ruwa
da gaske ba ya buƙatarta a rayuwarsa.

Yana ƙoƙarin ficewa ta sha gabansa cikin dakiya duk da kukan da take faman dannewa yana ƙoƙarin kufce
mata.
"Ba za ka je ko'ina ba sai ka tsinke sauran igiyoyin gabaɗay..." Wata muguwar hankaɗar da ya yi mata ya sa
babu shiri ta zube ƙasa tare da fashewa da wani mugun kuka tana faɗin,

"Wayyo Allahna!"

Babu shiri ya ja birki ya tsaya, tare da hanzarin runtse idanuwansa cikin sauri, saboda ƙarar sautinta ya
shiga kunnensa kuma ya ratsa masa zuciya ta dinga bugawa fal-fal. Amma hakan bai saka shi juyawa ba, ko
kuma ya fasa abin da ya yi niyya. Gudu-gudu sauri-sauri ya isa harabar gidan ya wurga jakarsa a mota ya ba
ta key cikin zafin nama ya fice aguje tamkar zai tashi sama.

Tsawon lokaci Minal tana kuka kafin ta haƙura don kanta ta miƙe tana shessheka ta zumbula hijabi ta fice
bakin gate. Maigadi bai hana ta ba kamar yadda ya saba, saboda fahimtar akwai abin da yake faruwa a
cikin gidan. Tun daga zuwan Hajiya gidan har zuwa fitarta da ficewar maigidan har zuwa tata fitar. Kuma
tuna gargaɗin da Jamal ya yi masa a kan haramta masa shiga sabgar gidan; ya sa ya dinga kallon komai da
ido ba ya shiga ballantana ya sake yin wani laifin.
Don yanayin Minal ya tabbatar masa tana cikin tashin hankali, hakan ya sa bayan fitarta ya jima a ƙofar
gidan yana kallon titin da ta miƙe cike da tausayawa har zuwa lokacin da ta ɓace wa ganin sa.

***
Jamal gudu yake yi yana dukan sitiyari a lokacin da ya kira wayar Nur sau biyar ba ta ɗaga ɗaya ba. Yana
huci tare da goge gumin goshinsa ya isa Jogana ya yi parking a ƙofar gidan su Amina. A daidai lokacin da
ake ta kiran sallar magrib a masallatai mutane suna ta arwala yayin da wasu ke ta ƙoƙarin zuwa masallaci.
Tun kafin ya fito daga cikin motar Baban Amina ya riga shi fitowa daga cikin gidan yana sauri, wanda
alamu ya nuna a zahiri shi ma masallacin zai je. Duba da yadda yake gyara hannun rigarsa da ruwan arwala
ya gama jiƙewa.

"Ashe ka dawo? Ga ni kuma zan je masallaci."

Baban Amina ya yi maganar fuskarsa babu yabo babu fallasa. Jamal cikin wata kalar muryar da damuwa
ta gama raunta ta ya ce, "I, na dawo Baba, Nur na zo ɗauka, in sha Allahu gobe zan kai ta gidansu har ƙasar
Niger."

Ɗan jim Baba ya yi cikin wani yanayi kafin ya kalli ƙofar gidan yana cewa, "Bari na kawo maka ruwa ka yi
sallah, saboda ita ma sallar take yi, idan muka dawo akwai abin da nake so mu tattauna kafin ku tafi."

"Babu damuwa."

Maganar Jamal kenan saboda ba zai iya yin jayayya da shi ba, duk da a ƙasan zuciyarsa bai so yin ko minti
biyu a cikin garin na Jogana ba. Saboda ba ya son labarin sakin da ya yi wa Amina ya kawo musu tun kafin
ya bar gidan. Don nauyi da kunyar Baban Amina yake ji a ransa, ko babu surukutar Amina akwai ta Nur da
yake yi masa kallon mutum mai daraja a idonsa.

Ba don ya so ba haka ya yi arwalar jiki a sanyaye ya bi Baban Amina masallacin da ke kusa da gidan.
Bayan an gama sallar suka dawo gidan suna tafe kowa shiru sannan da abin da kowa yake saƙa a cikin
ransa. Umarni ya ba shi a kan ya shiga cikin gidan, ba don ya so ba haka ya bi shi da guntuwar sallama har
zuwa bakin ɗakinsa, inda tambarma take shinfiɗe Nur tana kai da carbi a hannunta bayan ta haɗa tagumi
tana share hawaye jefi-jefi. Tsabar fargaba da tashin hankalin da take ciki kala-kala, ji take yi tamkar ta yi
tsuntsuwa ta dira Niger ko da za ta rage nauyin damuwar da ke ƙoƙarin dawo mata sabuwa. Kuma ba don
Baba ya saka ta yi masa alƙawarin zama har ya je masallaci ya dawo ba; babu abin da zai hana ta tserewa
saboda gudun abubuwan da take hangen faruwarsu su wanzu.
Ƙirjinta ne ya buga dam-dam tun daga jin sallamar Jamal har zuwa hango shi da ta yi a bayan Baban Amina
yana ƙoƙarin isa kan tabarmar da take kai. Cikin hanzari ta ja gefen bango ta makure kanta a ƙasa saboda
ba ta son haɗa ido da su gabaɗaya.

"Ƙaraso ka zauna." Baba ya bai wa Jamal umarnin zama ganin sa a tsaye yana kallon Nur ya kasa gaba ya
kasa baya. Cikin sanyi jiki ya jawo ƙafafuwansa ya zauna nesa da ita kasancewar tabarma ce babba. Shiru
ya ratsa tsakani kafin Baba ya sauke ajiyar zuciya ya ce,

"Na ji kana zancen mayar da Nur gida, ya aka yi ka sauya wannan ra'ayin?"

"Ba zan iya ɓoye maka komai ba Baba, amma wajibi ne gare ni Na mayar da ita gida a aura mata wanda
take so, don na gama fahimtar ba ta so na. Rashin son da ya sa Hajiyata ta ji haushi ta hana ni auren ta kai-
tsaye, bayan ta ba ni zaɓin ita ko Nur Na zaɓi ɗaya a cikin su. Saboda Amina ta haɗa ni da ita, koyaushe ni
take ganin laifi kuma komai na yi sai ta ce ban yi daidai ba, to yanzu na zaɓi rayuwa ni kaɗai ba tare da
kowa b..."

Sautin kukan Nur ya saka shi yin shiru yana kallon ta, kafin Baban Amina ya nisa cikin wata

24 / 29