Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
zauna da shi mu yi masa irin bayanin da na yi miki saboda fitar haƙƙi. Da ma
aikinmu shi ne gano cuta da neman hanyar waraka. Kuma idan an bi ƙa'idojin asibiti sau da ƙafa za a dace
da yardar Allah."
"Hmmmmm! To Ubangiji ya shiga cikin lamarinsa da namu bakiɗaya. Kuma in sha Allahu zuciyar Jamal
ba za ta buga ba, kuma zai rabu da ciwon lafiya ya ci gaba da rayuwarsa kamar kowa."
Ta miƙe har za ta fice ranta a jagule ta waigo, tana tambayarsa za ta iya ganin sa a daidai lokacin. Likitan
ya nufi hanyar fita ofishin yana cewa ta biyo shi.
Jugum Hajiya Mama ta yi a lokacin da ta yi ido biyu da Jamal, saboda likitan ya yi mata jagora har gaban
gadonsa, cike da sharaɗin kada ta yi dogon motsin da zai damar da marasa lafiyarsu da ke cikin ɗakin.
Hawaye ta shiga sharewa da gefen hijabinta, saboda ganin yadda ya rame a dare ɗaya tamkar wanda ya yi
kwanaki yana jinya. A ranta tana tuno kalaman likitan da suka gama tsinke mata jijiyon jiki da na zuciya.
Ƙarfen gadon ta riƙe daidai kansa tana tofa masa addu'o'i tana hawaye, kafin likitan ya gama zagayen
marasa lafiyar da yake dubawa. Fahimtar ta shiga yanayi mara daɗi ya dawo kanta da kalaman kwantar da
hankali a kan Jamal zai farfaɗo cikin lafiyarsa da sabon kuzari. Da ma ƙarin ruruwar wutar ciwon nasa har
da zazzafan zazzaɓi. Don haka ta kwantar da hankalinta babu abin da zai sake samun sa.
Hakan ya ƙara mata juriya ta fito daga ɗakin zuciyarta cike da gamsuwa da maganganun likitan. Kiciɓis
ta yi da Amna a bakin ƙofar shiga a hargitse, raɓa gefenta ta yi ta faɗa tana wara idanuwanta a kan gadajen
masu jinyar da ke jere har ta hango shi a kan gadon ƙarshe.
Bakin gadon ta ja ta tsaya tana rufe bakinta saboda sabon kukan da ya zo mata babu shiri. Hannunsa ta
yi hanzarin kamawa ta ɗora kanta a saman hannun tana kuka mai sauti cike da tausayin sa a ranta. Sanyin
hawayenta da ya ji a hannunsa ya ɗan motsa tare da buɗe idanuwansa kaɗan, sannan sake rufewa tare
hanzarin dafe kansa yana faɗin,
"Nur, ki matso kusa da ni."
Amna ta saki hannunsa tana murmushin farinciki hawaye yana zuba a kan fuskarta ta ce,
"Auncle J Amna ce.."
Juyo kansa ya yi saiti da fuskarta yana kallon ta kamar zai yi magana kuma ya ja bakinsa ya yi shiru bai ce
komai ba. Amna ta fice da sassarfa cike da jin daɗi ta sanar da Hajiya ta zo ya tashi. Tare suka dawo har
direbanta suna murnar ganin sa a raye kuma ya farfaɗo a cikin hayyacinsa. Da ido kawai yake bin su ɗaya
bayan ɗaya kafin ya yi ƙarfin halin furta abin da ke cizon ransa.
"Hajiya, har yanzu Nur ba ta dawo ba ko?"
Uhum🥲
D. AUTA CE✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA IBRAHIM D. AUTA*
*LAMBA TA BIYAR.*
Shiru Hajiya mummy ta yi masa, saboda babu wata amsar da za ta iya ba shi a daidai lokacin. Hakan ya
sa ta kawar da kanta gefe kawai tana share hawayen da ke bin fuskarta, zuciyarta cike takaicin abin da ya
faru, wanda ya yi silar ciwon da ke barazana ga lafiyarsa.
Amna ta matsa jikin gadon tare da dafa hannunsa ta yi magana cikin sigar rarrashi ta ce masa,
"Ka yi hakuri Uncle J, ni na sani Nur za ta dawo maka, saboda ita ma tana son ka. Kuma abu ne wanda
kowa ya san da hakan ba za ta iya rayuwar da babu kai a cikin ta ba. Don haka don Allah ka taimake mu ka
taimaki rayuwarka Uncle J, ka kuma ƙarfafa kanka da zuciyarka ka yi ƙoƙarin cire damuwar komai a ranka
Allah yana sane da komai da ya far..."
"Laifin me na yi mata za ta guje ni?"
Ya wurgo mata tambayar cikin sauri saboda ya kasa shanye takaicin, kuma tambayar da ke ransa kenan
tana yawo a ƙwaƙwalwarsa.
"Ka bar zancen nan Jamal. Za a yi shi daga baya idan ka samu lafiyarka."
Maganar Hajiya kenan cikin kakkausar murya, duk da take ƙoƙarin danne da abin da ke cikin zuciyarta.
Saboda ko kaɗan ba ta fatar ta yi asararsa kamar yadda likita ya yi mata mummunan albishir. Daga hakan
Jamal bai sake cewa komai ba, sai kawar da kansa da ya yi gefe tare da runtse ido ƙirjinsa yana bugawa da
sauri da sauri.
Bacci mai nauyi ya ɗauke sa, zuwa lokacin asibitin ta cika da danginsu, 'yan'uwa da abokan arziƙi.
Mutanen nesa da suka kwana gidan Hajiya mummy fiye da rabinsu suna asibitin ana jajanta lamarin.
Gidansu Minal ma Hajiya ta kira ta sanar da su halin da ake ciki, sannan ta bai wa 'yan aikinta umarnin su yi
abin karin safiya su kai wa Minla. Saboda tashin hankalin da take ciki bai hana ta tunawa da amanarta da
aka ba ta ba.
Wannan dalilin ya sa Innarmu da Gwaggo Salame suka dira asibitin ganin Jamal. Daga can suka zarce
wurin Minal bayan sun gama tattaunawa da Hajiya a kan yadda za a shawo kan matsalar cikin sauƙi. Kuma
an bar zancen a tsakaninsu ba tare da an sanar da Minal halin da yake ciki ba, gudun ta ƙara tuburewa ta
bijire wa auren kuma ta lalata musu sabon shirin da suka tsara.
****
Minal kam maganganun Gwaggo Salame sun rage mata kaso huɗu a cikin goman damuwarta. Kuma ta
karɓi ƙaddararta, duk da tana jin ba ta gamsu da ingancin auren ba har a cikin zuciyarta ba. Saboda iya
sanin ta dakalolin tarihin auren da ta ji ba ta taɓa jin kalar abin da aka yi mata ba. A take zuciyarta ta shiga
ziga ta da shawarwari mabambanta, waɗanda ta tsayu a kan wadda zuciyarta ta karɓa, kuma ta riƙe a
matsayin makamin kare kanta daga farmakin da ke cikin auren, sannan da riƙon amincin da take yi wa
alaƙarta da Nur.
Jiki babu kuzari ta ja abincin da Hajiya ta aiko mata ta ƙara ci. Sannan ta fitar da sauran ga maigadi yana
ta godiya. Sai dai abin da ya so ƙara saka ta cikin damuwa zamanta shiru a cikin gidan tun bayan zuwan su
Innarmu, babu wanda ya sake zuwa gidan har dare. Sannan ta kira Amna ya fi sau goma, amma har wayar
ta gama ringing ba ta ɗauka ba. Hakan ya ƙara tunzura ta, ta shiga neman lambobin Nur cike da ƙunar rai,
da zaman turaata saƙonni da zummar ko da za ta buɗe wayar ta gan su. Saboda duk kiran da ta yi a sanar
da ita layukan duka a rufe suke.
Daren ranar ma ta yi kwana rabi da rabi, saboda rashin nutsuwar zuciya da kaloli tambayoyin da take son
amsarsu amma babu damar hakan. Abincin daren da Hajiyar ta sake aiko mata ma sai cikin dare ta samu
damar ci, a lokacin da yunwa ta hana ta sukuni saboda barcin ya ƙi ba ta haɗin kai. Karfe biyun dare ta
duƙufa kai kukanta ga Allah, a kan ya kawo mata sauƙin matsalar da take ciki, sannan ya dawo da Nur ga
mijinta ita ma ta auri wanda take so. Saboda katangar kashedin da Innarmu ta yi mata da Aminunta ya
hana ta neman sa a waya ta ji halin da yake ciki.
Don abu ne da ta sani dole ne hankalinsa ya tashi a lokacin da ya ji an yi wa neman aurensa ƙarfa-ƙarfa.
Sannan ita ma Nur za ta dawo ga Jamal komai daɗewar lokaci, hakan ya sa ta dinga amfani da kayanta na
gida duk da ba su da yawa. Kayan Nur kuma ta mayar da su akwatunan lefenta da ke ajiye gefen gado.
Saboda ta saka wa ranta zaman wuccin-gadi ne za ta yi a gidan ba zaman dindindin ba, don haka babu abin
da zai ruɗe ta ta saki jiki a inda babu lasisin zamanta.
Ba ta samu bacci mai daɗi ba har sai da ta gama sallar asuba, daga lazumi ta ɓingire a wurin sai barci.
Haka ta ci gaba da rayuwar kaɗaici ita kaɗai a gidan Jamal har tsawon sati ɗaya, babu mai zuwa wurin ta
idan ba Gwaggo Salame ba. Abin da ya fi ɓata mata rai kenan ganin yadda aka wofintar da 'yancinta bayan
an tauye rayuwarta da gingimemen laifi. Hakan ya sa a cikin 'yan kwanakin gabaɗaya ta zuge, saboda
ramar ƙarfi da yaji ta dira jikinta har idanuwanta sun zurma tamkar mai ciwo. Saboda wa'azi da nisihar
gwaggon Salamen, tare da kulawar da Hajiya ke ba ta kowace safiya; ba su cire ta daga cikin ƙuncin da
zuciyarta ke abota da shi ba. Sai ga wani ƙarin tashin hankali, Hajiya ta kira ta a waya tana sanar da ita
Jamal zai dawo ranar ta shirya yi wa mijinta girki.
Shiru kawai ta yi bayan ta sauke wayar daga kunnenta ƙirjinta yana bugawa ta shiga sharar ƙwalla.
Saboda jikinta ya ba ta gara zaman gidan ita kaɗai da rayuwa wuri ɗaya da Jamal. Duba da irin tozarcin da
ya yi mata da yunƙurin kisan tun a tashin farko.
"Ba zan iya zaman aure da shi ba."
Furucinta kenan a lokacin da ta miƙe jikinta yana rawa ta ja dogon hijabi ta zumbula. Da sassarfa ta sauka
ƙasa jikinta yana tsuma ta isa bakin gate, maigadi yana tambayar lafiya ganin yadda ta fito gidan kamar an
koro ta. Amma ƙanzil ba ta ce da shi ba ta buɗe ƙofar za ta fice. Kiciɓis ta yi da gwaggo Salame tana ƙoƙarin
shigowa gidan har kansu ya gwabru da juna.
"Subhanallahi!"
Furucin gwaggon kenan a lokacin da ta yi ido biyu da Minal, nan take zuciyarta ta hasko mata abin da take
ƙoƙarin aikatawa. Fuskarta a cure ta dinga kallon Minal tana nazarin yanayinta, ganin ta ja gefe tana
kumbura fuska bakinta ɗauke da gungunin a saman leɓonta. Fuskarta a cure ta yi mata magana cikin
kakkausar murya ta ce,
"Me ya fito da ke kuma ina za ki je?"
Minal ta ɓare baki kamar ƙaramar yarinya ta yi magana cikin kuka ta ce,
"Wallahi ni ba zan zauna daga ni sai shi a cikin gidan nan b..."
Ta yi maganar tare da rushewa da wani sabon kuka har da buga ƙafafuwa. Baki a sake gwaggon ta bi ta da
kallo bayan ta shigo gidan ta rufe ƙaramar ƙofar. Ta fara fa hannnuwa tana salati saboda ta rasa me za ta
faɗa. Ganin maigadi yana tsaye yana kallon su ya sa ta ja hannunta tana tirjiya da buga ƙafa har suka koma
cikin gidan. A falon sama ta zaunar da ita kan kujera ranta a matuƙar ɓace ta shiga nuna ta da hannu kafin
ta samu damar faɗin,
"Yanzu Amina sau nawa zan ce ki yi haƙuri? Kenan duk abin da nake faɗa a bayan kunnuwanki yake bi
yana wucewa? Saboda Allah duk lokacina da nake ba ki a kwanan nan ashe ba ki gani ba? Ko kin manta ina
da tarin abubuwan da nake jinginewa na zo rarrashin ki? Ashe ban sani ba kallon mara aikin yi kike yi mini
da nufin na yi a banz.."
"Gwaggo ni ba na son zama da shi ne kawai...saboda ya faɗa ba zai mini kallon mace ba kuma ya ce sai
ya kashe n..."
"Ya kamata zuwa yanzu ki fahimci mijinki ba zai iya cutar da ke ba. Don ko kiyashi ba zai iya kashewa ba
ballantana mutum. Saboda duk tsawon kwanakin nan da ba ya kwana gidan yana asibiti ana kula da
lafiyarsa. Ya yi ciwo na tsawon kwanaki a yanzu ta kansa yake yi da abin da ke damun sa. Don haka ki
kwantar da hankalinki babu abin da zai iya yi miki idan ba alheri ba. Idan ma ya yi miki Allah ma ba zai bar
shi ba, kuma hukuma ba za ta ƙyale shi ya ci bulus ba dole ne a ɗauki mataki kans..."
"Idan haka ne Gwaggo a sanar wa da 'yansanda tun yanzu, saboda su san halin da ake ciki su hana shi
kada ya sake yunƙurin kashe ni...don wallahi ranar ƙiris ya rage ya cire mini maƙogwaro."
Dariya Gwaggo Salame ta yi sannan ta zauna kusa da ita tare da janyo ta jikinta, saboda zancenta ya sa ta
fahimci firgicin da ya saka ta ne ya sa take jin tsoron zama da shi tun a daren farkon auren. Hakan ya sa ta
shiga kwantar mata da hankali har ta saki ranta. A gefe ɗaya kuma tana jinjina ƙarfin son da yake yi wa Nur
cikin tausaya wa halin da yake ciki. A ranta kum ta shirya yadda za ta shawo kansa ya daina jin haushin ta
su nemo hanyar da za a gano Nur a duk inda ta shiga.
Saboda kwanansa uku a asibitin aka sallame shi, a kwana na huɗun ne Hajiya ta ce ya kamata ya koma
gidansa da kwana tun da ya ji sauƙi. Amma fafur ya kafe a kan shi da gidan har abada, ta so tirsasa masa
kwana gidan a ranar; amma wasu daga cikin dangin Alhajinsa suka ce ta bi komai a hankali. Hakan ya sa ta
ci alwashin kora shi gidansa cikin dabara, saboda babu adalci a bar Minal ita kaɗai a gidan shi yana kwana
gida.
A son ran Hajiyar ma daga sallamar sa a asibitin ya yi wa gidansa tsinke su sasanta da matarsa, amma
shawarar da likitan ya ba ta a kan a bi komai a sannu har zuwa lokacin da zai warware ya sa ta ɗaga masa
ƙafa. Sai dai kuma a gefe ɗaya ta shiga nata aikin da ta ce idan ya san wata bai san wata ba. Don maganin
ƙarfin maza ta dinga ɗirka masa yana sha ba tare da ya san amfaninsa ba. Ko da ya tambaya kuma ce masa
ta yi maganin ciwon zuciya ne, duk da bai gamsu ba amma hakan bai sa ya yi kokwanto a kansa ba, saboda
cikakken sanin da yake da shi a kan ta fi shi son kansa, kuma ba za ta iya cutar da shi ba.
Abokansa ma ta ba su aikin dannar sa tare da rage masa damuwar rashin Nur. Hakan ya sa suka shiga
nuna masa alfanun haƙuri da kowace irin jarabawa. Saboda iya binciken da suka yi sun tabbatar Nur ba ta
garin, ta yi tafiyar da babu wanda ya san inda ta je. Da taimakon abokan nasa masu ƙarfafa masa gwiwa ya
dinga shan maganin Hajiya. Sai dai inda gizon ke saƙar sauyin da ya fara ji a jikinsa, inda ya fara zargin
maganin da tayar masa sha'awar mace. Saɓanin yadda ya saƙa wa ransa har abada tsakaninsa da mace,
matuƙar Nur ba ta dawo ba babu shi babu kowace irin mace a duniya komai nagartarta.
Dole ƙanwar na ƙi Hajiya ta shawo kansa a kan zai koma gidansa da kwana. Daɗin amincewarsa ta aika
wa Minal cefane, tare da sanar da ita abincin da ya fi so ta girka masa da kanta. A nan gidan ma Gwaggo
Salame ce ta taimaka mata da girkin har suka kammala. Sannan ta saka ta yin wanka da ado a cikin ɗaya
daga cikin sabbbin kayan lefen Nur, waɗanda sai da ta sha fama da ita sannan ta saka kayan. Sai dai a a
ranta ta ci burin tana fita za ta cire, saboda ta yi wa kanta alƙawarin zama d Jamal har zuwa lokacin da Nur
za ta dawo.
Kunun aya Hajiya ta haɗa wa Jamal, ta ce ya tafi da shi ya sha tare da Minal, saboda sanin yana mugun
son sa, wannan dalilin ta yi masa tarkon da zai kama shi daren ranar. Bayan ta gama yi masa wa'azi da jan
kunne a kan zama da Minal bisa amana ko da ba ya son ta. Ganin hawaye a idonta ya saka shi karɓar
alƙawarin zama da ita a cikin gidan ba tare da ya yi mata korar karen da ya kitsa wa ransa ba da ya je gidan.
Har ya fice da motarsa cikin gidan tana zuba masa addu'ar tsari da abin ƙi tare da neman kwanciyar
hankali a cikin rayuwarsa. Cike da jin daɗin addu'o'in nata ya baro gidan cikin karfin zuciya, amma bai fasa
hasko hoton murmushin Nur a idanuwansa ba. Hakan ya ƙarfafa masa gwiwar zai ci gaba da neman Nur a
duk inda ta je a faɗin duniya.
Wasar za ta fara🫠
D. AUTA CE✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA IBRAHIM D. AUTA*
*LAMBA TA SHIDA.*
Minal tana zaune falo tana kallon ƙarfin halin da Gwaggo Salame ta saka ta yi. Saboda ita ce ta ba ta
umarnin zaman kallon har zuwa lokacin da Jamal zai shigo gidan, kuma ta ce kada ta kuskura ta bar falon
ba tare da ya dawo ta gabatar masa da abincinsa ba. Tare da jaddada mata kada ta bari wahalar girkin da
suka yi ta tashi a banza. Kuma duk abin da take ji kada ta yi sakacin barin sa ya yi kwana da yunwa. Saboda
Hajiya ta sanar da ita ba ta bari ya ci abinci a wurin ta ba, saboda kada ya ƙi cin na gidansa.
A haka ta zauna tana kallon MBC2 da tagumi har zuwa lokacin da ta ji buɗe gate da shigowar motarsa.
Ƙirjinta ya ƙire ya faɗi a lokaci ɗaya jikinta ya hau rawa ta shiga wara idanuwa tana neman inda za ta ɓoye,
kada ganin ta ya sa haukar son Nur ta motsa masa ya nemi illata ta a banza.
'Ko da wasa kada ki sake ki nuna kina jin tsoron sa. Saboda wannan ne damarki ta farko da za ki yi
amfani da ita ki nuna masa ke ma kin san kanki.'
Tuno kalaman Gwaggo Salamen ya sa ta fara faɗar hasbunallahu wa ni'imal wakil don samun nutsuwar
zuciyar da ta bar jikinta tsoro ya mamaye jarumtar da take ƙarfafa kanta. Saboda sautin huɗubar gwaggon
da take ji a cikin kunnuwanta tamkar a lokacin take yi mata jan kunnen da gargaɗi. Hakan ya sa ta yi
hanzarin gyara zamanta tare da tsuke fuska tana nanata kalmar lahaula wa la ƙuwwata illah billah. Har ta ji
motsin buɗe ƙofar falon ƙasa tare da takunsa yana hawa saman cikin sauri.
Dam-dam ƙirjinta ya shiga bugawa da sauri da sauri a lokacin da ya kunno kansa cikin falon. Idanuwanta
a kan tv ba tare da ta kai kallon ta