Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar Ƙauna Complete Hausa Novel by Hadiza D. AUTA

Author :  HADIZA D. AUTA Category :  African Stories & Novels

Chapter   13 / 29

36K to 39K   out of 85.8K words

kasa furta ko
kalma ɗaya. Hannuwansa a baya yana kallon ƙasa ya ji muryar Minal tana faɗin,

"Jakata da ke motarka nake so."

Ta yi maganar a hankali saboda ba ta so Hajiya ta ji me take faɗa, gudun ta fahimci abin da ya kai jakar
kayan nata cikin motarsa ya ƙara yin wani laifin. Amma sassauta muryar da ta yi bai hana Hajiya yin
magana cikin ɗaga sautinta ta ce,

"Ke fa muke jira? Tsayuwar me kike yi a wurin?"

Inda-inda Minal ta fara yi tana sosa ƙeya, kafin Jamal ya yi hanzarin barin wurin ya isa inda motarsa take
ajiye yana faɗin,
"Ashe ta saka jakar kayanta a motata ba tare da na sani ba."

Wani kallon mamaki Minal ta bi shi da shi kafin wata kalar dariya ta so kufce mata. Saboda ganin ya
fuske ƙiri-ƙiri alamun da gaske abin da yake faɗa. Idon Hajiya a kansa har ya buɗe boot ɗin ya ciro jakar ya
nufi bakin motar Hajiyar ya ajiye yana sunne kai tare da kumbura fuska. Cike da mamakin abin da ya kai
jakar kayan a motarsa ta ce masa,

"Kai Jamal! Dube ni mu haɗa ido! Za ka faɗa mini dalilin zuwan jakar a cikin motarka ko sai mun raba
'yan kallo da kai? Saboda jikina ya ba ni akwai abin da kake shiryawa ba tare da na sani ba."

Gefe ya ja yana zarar ido tare da shafa bayan kansa yana faɗin,

"Ki tambaye ta Hajiya, idan ni na ce ta haɗa kayan ta saka a motar."

"Ba zan tambaye ta ba kai na tambaya! Amma ka bar amsarka don na gama gano komai. Kuma hakan da
ka aikata ba ƙaramin burge ka yi ba. Don haka na hutar da kai rage mata hanyar zuwa gidansu da ka yi
niyya. Da ma can zamana take yi kuma daga yau ta koma hannuna. Kuma ko da wasa kada na ga ka taka
ƙafarka zuwa inda nake....wuce mu je ke kuma! Tun da ba za ki iya faɗa mini abubuwan da ke faruwa ba sai
da idanuwana suka ganar mini komai."

Ta ƙare maganar a daidai lokacin da take shiga motar, bayan ta zuba wa Minal ido har ta shige motar ba
ta daina furzar da abin da ke bakinta ba.

"Hajiya don Allah ki yi haƙur..."

Jamal ya yi maganar a lokacin da ya zuro kansa ta gilas saitin Hajiyar bayan ya marairaice kamar mara
lafiya.

"Ni matsa ka ba ni wuri! Gida ne an bar maka ka kawo duk wadda kake so. In dai gindi ne kullum safiya
sai an kawo sabon samfur a cikin duniya. Kuma duk ƙwarewarka ga iskanci wata macen sai dai ka hango ta
daga nesa ka bar ta. Don haka ya rage naka ka zaɓi rayuwar da duk ka fi hangen za ta fisshe k....tafi mu je
Malam Habu tun kafin zuciya ta ɗebe ni na yi abin da zai dame ni daga baya."

Tana maganar tana zuƙo gilashin motar da ƙarfi ta rufe har tana ƙoƙarin dantse wa Jamal hannu da
gangan.
Minal dai ta sha jinin jikinta, har suka bar gidan maigadi yana ɗaga musu hannu ba ta daina mamakin
Hajiyar ba. Saboda ba ta taɓa tunanin ita ma ta iya masifa kamar Innarmu mu ba. Ganin lokacin auren ba
ta tsaurara wa Jamal kamar yadda ta yi masa yanzu ba.

Jamal kam ya jima tsaye a inda suka bar shi kansa a ƙasa, hannuwansa zube cikin aljihu yana nazarin
abin yi. Saboda ko kaɗan bai ji daɗin abin da Hajiyar ta yi wa Zee ba, hakan ya sa ya ji ba zai iya neman ta
ba ballantana ya tafi ganin halin da take ciki.

"Maigida akwai wani abun ne?"

Zancen maigadin gidan kenan yana 'yan duƙe-duƙen alamun girmamawa. Duk da zuciyarsa cike take da
son sanin abin da ke wakana a cikin gidan. Tun lokacin da Jamal ya zo da Zee har zuwa lokacin da Minal ta
dawo, kashe yake da kunne yana so ya ji wace irin waina ce ake toyawa a cikin gidan.
Ganin zuwan Hajiya da fitar Zee a yanayin da take jikinsa ya ba shi babu lafiya. Ya shiga tsumayin jin wani
abu da zai fallasa komai har ya gano kalar wainar da ake toyawa. Duk da zuciyarsa ta gama ba shi satar
amsa a kan Jamal ne kawo abin da duk ya haddasa komai.

"Aikin bincike na na ɗauko ko aikin tsaron ƙofa da gadin gida?"
Jamal ya yi maganar a fusace saboda jin haushin shisshigin da yake son yi masa a cikin gida.

"A'a ranka ya daɗe?"

Ya yi hanzarin amsawa yana ja baya tare da ranƙwafawa alamun girmamawa gare shi.

"To ka tsaya iya aikinka."

Jamal ya yi maganar cikin haɗe girar sama da ta ƙasa tare da barin wurin ya koma cikin gidan zuciyarsa a
ƙuntace.
A kan babbar kujerar falon ya faɗa yana shafa kansa cikin matsananciyar damuwa. Sai dai duk ya rufe
idanuwansa Minal yake gani a cikin shigar ƙananun kayan da ta yi wa Zee barazana. Idan ya buɗe idon
kuma ta koma yi masa gizo yana hango ta da towel iya cinya tana taku bom-bom ɗin ta suna ta juyawa.

"Ya Salam! Wai me ke shirin faruwa da ni ne?"

Ya furta maganar a kasalance a lokacin da ya isa inda yake hangen ta da sassarfa da nufin kamo ta ta
ƙarfi, ko da zai rage nauyin abin da yake ji a cikin zuciyarsa. Sai dai wayam ya ji ya kamo banza babu komai
a wurin sai ginin da ya ci karo da shi ya buge hannunsa da Zee ta gatsa wa cizo.
Babu shiri ya bar wurin dafe da hannun ya faɗa ɗakinsa. A gurguje ya yi wanka ya fice gidan zuwa wani
babban Chemist. A nan aka yi masa dressing czon, saboda shatin haƙoran Zee ruɗu-ruɗu har fatar ta tashi
sosai.
Bayan an gama rasa inda zai nufa ya yi, dole ya ƙare rabin wuninsa a wani restaurant. A can ya ci abincin
rana har dare ya zo ya sake cin abincin sannan ya nufi gidansa.

Daren ranar kwanan takaici ya yi yana tsaki, saboda ganin ya yi uku babu. Zee ta tafi Minal kuma Hajiya
ta ɗauke masa ita, Nur kuma ta yi masa nisan da bai san ina zai je ya nemo ta ba. Juyi ya shiga yi saboda ji
yake yi kwanciyar ba ko kaɗan ba ta yi masa daɗi.

***
Minal kam kwana ta yi mai daɗi har da minshari. Saboda zuwanta gidan cikin wuni ɗaya ta gano
tsabagen kirkin Hajiya. Don gaba ta saka ta a kan sai ta cinye abincin da ta zuba mata, dare ma haka aka yi
ita ta bai wa zaɓin abin da take so a dafa. Cike da jin nauyin Hajiyar ta yi shiru tana sunne kai ta ce,

"Babu abin da ba na ci, kuma komai aka dafa zan ci."

"Kada fa ki takura kanki. Sannan duk abin da kike so ki faɗa mini kada ki ji nauyi."

Bayan sun gama kallo a falo Hajiya ta kai ta ɗakin Amna inda aka ajiye mata jakar kayanta. Ta ce ta zauna
a nan tun da Amnar ta koma makaranta. Kuma ta yi duk abin da take so a cikin gidan babu mai takura ta,
sannan ta ɗauka tamkar cikin gidansu take gaban Innarmu. Kuma duk abin da take so idan ta yi ra'ayi kawai
ta dafa, idan ma babu kayan haɗi ta sanar da ita za a nemo a kawo mata. Fitaa idan ta yi sha'awa yi ta
sanar da ita ba sai ta nemi Jamal ba.

Minal ta shiga jin daɗin asirin Jamal da ya tonu da wuri Hajiya ta ga komai da idonta, sannan da gatan
da take nuna mata tamkar 'yar da ta haifa da cikin ta. Hakan ya sa ta ci alwashin kafin ta bar gidan sai ta
ƙara wa Hajiya ninkin ƙaunar da take yi mata a cikin ranta.

Tun da asuba ta fara gyaran ɗakin Amna sannan ta wanke toilet ta koma gyaran babban falon Hajiyar. Sai
da ta share ko'ina ta ƙwalƙwale tsaf sannan ta sauya zaman kujerun daidai tsarin da take so. Gari yana fara
washewa ta faɗa kitchen cikin zafin nama ta shiga haɗa musu abin kari, saboda ganin komai yana ajiye a
mazauninsa, babu abin da za ta tambayi Hajiya.
Ko da Hajiyar ta fito riƙe da baki tana mamakin ayukan da Minal ta yi a cikin duhun asuba zuwa ƙarfe
takwas na safiya.
Ƙamshin da ke dukan hancinta ya sa ta nufi kitchen ɗin zuciyarta cike da jin daɗi, saboda halin kirkin Minal
ya burge ta matuƙa. Har ƙasa Minal ta durƙusa cikin ladabi tana yi wa Hajiya ina kwana, fuskarta cike da
walwala ta amsa mata tare da saka mata albarka, kafin ta gyara tsayuwarta da carbi a hannunta ta ƙara
cewa,

"Kin hana idonki barci kina ta wahalar da kanki Amina."

"Babu komai Hajiya. Ai kaina na yi wa."

"To, Allah ya yi albarka."

Hajiya ta juya ranta fes ta koma falo ta zauna tana nazarin gyaran da Amina ta yi wa falon. A ranta ta ce,

'Yarinyar kirki.'

"Hmmmmm!" Ta sauke ajiyar zuciya saboda tuno Jamal da irin sagegeduwar da yake ƙoƙarin yi wa kansa.
Amina ta haɗa komai a tire ta kawo wa Hajiya, daidai lokacin da 'yar aikin Umma Ade ta shigo gidan suna
gaisawa da Hajiya.

Amina ma cikin girmamawa ta rusuna ta gaishe da ita, sannan ta koma kitchen ɗin. Umma Ade ta biyo ta
tana faɗin,

"Amarya, da kin jira na zo wannan duka aikina ne. Yau ma wani jikana ne muka tashi da shi babu lafiya
shi ya sa ban yi sammakon da na saba yi ba."

Amina tana harhaɗa kayan da ta ɓata da nufin wankewa ta ce, "Ki yi zamanki kawai Umma Ade, tun da
na zo gidan ai ni ce mai yin komai.."

"Ba za a yi haka ba! Ba ni kwanonin kawai na ƙarasa aikin, ke ki je ki huta ai kin yi mai wuyar."

Ganin da gaske Umma Aden ba za ta bari ta yi aikin ba ta ɗebi nata abin karin ta shige ɗakin Amna cike
da jin kunyar Hajiya. Saboda ba ta son zamanta falon ya takura Hajiyar, kuma ita ba za ta sake ta yi karin
yadda ya dace ba.
Bayan ta gama karin ta faɗa wanka, cikin ɗan lokaci ta shirya da ɗaya daga cikin kayanta na gida.
Saboda lokacin da ta haɗa kayan gabaɗaya babu kayan Nur ko ɗaya a cikin jakar. Iya nata kawai ta ɗauka,
don ta ci alwashin bar mata kayanta kamar yadda suke har zuwa lokacin da za ta waiwayi abin ta.

Misalin ƙarfe goma zuwa sha ɗaya na safiya, Jamal ya yi parking motarsa a harabar gidan Hajiya.
Zuciyarsa cike da fargaba a kan irin tarbar da za ta yi masa, bayan ta yi masa kashedin kada ya zo mata cikin
gida ba ta buƙata. Fuskarsa babu yabo babu fallasa ya shiga babban falon, a inda ya fara yin tozali da Minal
ita kaɗai zaune a cikin falon tana kallo, gabaɗaya hankalinta ya tafi a kan wata diramar da ake yi Bollywood.
Ƙirjinsa ya buga dam-dam, amma cikin basarwa ya raɓa ta gefenta ya wuce zuwa ɗakin Hajiya fuu tamkar
bai gan ta ba.

Ita ma sai da ta ji motsin mutum hankalinta ya kai kansa yana ƙoƙarin shigewa ɗakin Hajiyar. Ƙirjinta ya
dinga faɗuwa don ta firgita sosai da ganin sa tsidik, saboda sallamarsa ma a ciki ya yi ta ballantana ta ji shi
ta amsa.

"Ummmm!" Ta yi wani abu da baki sannan ta ci gaba da kallon amma hankalinta ko kaɗan ba ya wurin.
Don ta rasa nutsuwar da take da ita kafin zuwansa. Haka kawai ta tsinci kanta da tausaya masa don a kallo
ɗayan da ta yi masa ta fahimci babu walwala a tattare da shi kuma ba ya cikin jin daɗi.
Mintuna a tsakani ta fara jin sautin Hajiya tana faɗa, kafin ta ji ƙarar buɗe ɗakinta tana ba shi umarnin
ya fice mata daga ɗaki ba ta buƙatar ganin shi. Kamar an ingiza Minal ta zabura cikin rawar jiki ta isa gaban
Hajiyar ta durƙusa tana faɗin,

"Don Allah ki yi haƙuri Hajiyarmu. Kuma ki yafe masa ba don halinsa na san ba zai sake b...."

"Yi mana shiru baƙar munafuka bayan duk ke ce kika haɗa komai! Ai ina sane da ke kika kira ta don ta
tsine mini ki ji daɗi. To wallahi idan kika sake na riƙa ki sai na kakkarya mini ƙafafuwa baƙar almura mai
fuska biyu."

Idon Hajiya a kansa amma sai da ya gama amayar da abin da ke cikinsa. Saboda tunaninsa gabaɗaya ya
tsaya a kan Minal ce ta kira Hajiyar ba tare da ya sani ba. Minal ta shiga rantsuwar ba ta kira Hajiya ba har
da ƙwalla a idonta. Hakan ya sa Hajiyar ta yi hanzarin faɗin,

"Daina yi masa rantsuwa! In dai har da gaske ke ce kika kira ni na je kamar yadda ya faɗa; to shi kuma
dole sai ya yarda ke ce kika ɗauko masa hayar macen banzar, don kawai na gani ki ɓata masa suna...wallahi
Jamal ka fita idona na rufe! Kuma ka fice mini daga gida ka koma wurin waɗanda suka fi mu daraja a
idonk..."

"Hajiy..."

"Yi mini shiru sakaran banza! Allah Ya rufa maka asiri kana ƙoƙarin tona wa kanka....tashi ki tafiyar ki don
na fuskanci kwata-kwata ba gaskiya yake so ba."

"Ni dai don Allah ki yi mini haƙuri na tuba ba zan sake b...ke! Je ki faɗa wa Umma Ade yunwa nake ji a ba
ni abin kari."

Ya yi maganar alamun da Minal yake yi, tare da komawa kan ɗaya daga cikin kujerun falon ya zauna
yana canza channel daga Bollywood zuwa MBC Action. Wani kallo Hajiya ta yi masa bayan wucewar Minal
sum-sum kamar wadda ƙwai ya fashe wa a ciki ta nufi kitchen. Ita ma Hajiyar ta ƙarasa cikin falon ranta a
jagule tana faɗin,

"Yanzu Jamal matar taka ta sunnah kake kira 'Ke'?"

Kansa kawai ya shafa, ba tare da ya ce komai ba. "Kowa dai ya yi mai kyau ya sani, kuma hanyoyin zubar
da girma da yawa suke, waɗanda duk mutum ya zaɓi bi a can zai ci karo da gamonsa. Ina tausaya maka duk
ranar da ka cika yarinyar nan ta fara boƙare maka za ka yaba wa aya zaƙin ta."

A nan ma bai ce uffan, sai da Minal ta dawo ɗauke da abin karin ta ajiye masa tana ƙoƙarin barin wurin
ya yi jarumtar faɗin,

"Ko kaɗan ba na jin daɗin yadda kike ƙoƙarin yi mini baki koyaushe a kan wannan yarinyar. Hajiya tun da
ta shigo rayuwata kika daina tausayi na babu ruwanki ko mutuwa zan yi na je na yi. Wannan dalilin ya sa ko
kaɗan ba ta burge ni, saboda a kanta kike yi mini duk abin da kike yi..."

"Ci abincin Kawu Bello! In dai wannan ne matsalarka daga yau ta zo ƙarshe. Da ma rashin jin ka ne yake
sa muke samun saɓani, amma idan za ka gyara ni me zai sa na yi maka faɗa kawuna? Tun da kai ne uban ni
ce ɗiya..."

Baki buɗe ya dinga kallon Hajiyar bayan ya guma lomar dankalin turawa a bakinsa. Babu shiri wata kalar
dariya ta kufce masa saboda kiran sa da sunan Kawunta. Nan take ya sarƙe ya shiga tari cikin rawar jiki
Hajiya ta shiga miƙa masa ruwa a ruɗe tana jera masa sannu. Bayan ya sha ruwan dankalin ya faɗa masa
yana murmushi ya sake cewa,
"Ashe dai har yanzu ɗiyar Kawu Bello tana so na."

Kansa ta dungure tana faɗin, "Kai dai daɗin girkin matarka ne ya ɗebe ka sarƙe."

"Wace matar?"

Ya yi tambaya cikin sauri, Hajiya ma ta amsa masa kai-tsaye ta ce,

"Amina."

Babu shiri ya shiga kakarin amai yana cewa, "Dole na sarƙe na ci abincin mayya."




Kuma dai 🤣


GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda
tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta
Ibrahim.


DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. Mai buƙata 9032685442 Opay. Shaidar biya ta nan
08022014771.

10 February zan sake shi da yardar Allah.



D.
✍🏼 AUTA CE
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa


*LAMBA SHA BAKWAI.*

"Wace irin mayya kuma?"

Maimakon ya ba ta amsa, ya shiga kakarin amai tare da nufar hanyar ficewa falon gudu-gudu sauri-
sauri. Ya bar Hajiya riƙe da baki tana kallon sa da mamaki ɗauke a fuskarta har ya fice. Yayin da wani
zafaffen hawaye ya dinga bin fuskar Minal cike da takaicin tozarcin da yake ƙoƙarin yi mata koyaushe.
Bakin famfon da ke tsakiyar gidan ya tsaya yana ta faman wanke bakinsa, don ya gama kakarin aman
amma ya ƙi zuwa kamar yadda ya so. Sai da ya ja lokaci a wurin yana mayar da numfashi, sannan ya koma
cikin gidan yana ɓata fuska. Sauya mazauni ya yi a cikin falon dafe da cikinsa yana faɗin,
"Wash Allah!"

Hajiya ta yi banza da shi kamar ba ta san ya dawo ba, hakan ya saka shi tsarguwa ya tashi tsam ya koma
kusa da ita ya zauna, tare da riƙo hannunta yana faɗin,

"Don Allah a nema mini wani abu na saka wa cikina Hajiyarmu, kin ga cikina babu komai a cikinsa yunwa
nake ji sosai."

Hajiya ta yi masa kallon uku kwabo sannan ta ƙwace hannunta tana faɗin,

"Me za ka yi da abincin mayu?"

Da hanzari ya rufe bakinsa saboda dariyar da ta kufce masa, saman kafaɗarta ya kwanta cikin marairaice
murya ya ce,

"Yarinyar ce ba ta iya komai ba Hajiyarmu. Shi ya sa ba na son cin abincinta. Amma ki yi haƙuri don Allah
a sama mini wani abin da zan ci fisabilillahi Hajiyarm...."

Hajiya ta ture kansa cikin ƙunar zuciya ta ce, "Wai har yaushe za ka daina halinka Jamal? To daga ni har
Ade babu wanda zai sake wahalar da kansa a kanka! Mu ma abincin mayyar muka gama ci yanzun nan, kai
kuma da kake tsoron a kama maka kurwa sai

13 / 29