Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Fansar Ƙauna Complete Hausa Novel by Hadiza D. AUTA

Author :  HADIZA D. AUTA Category :  African Stories & Novels

Chapter   16 / 29

45K to 48K   out of 85.8K words

yawo da ke bayan har yanzu bai san darajarki ba."
Ta ɗan tsahirta da maganar kafin ta sake cewa, "Dole ne ki iya jan aji idan kina son ki ƙwato martabarki ta
mace, wadda yake ƙoƙarin wofintarwa a iska. Don haka ki daina sakar masa fuska har zuwa lokacin da zai
gano amfaninki."

Kai kawai Minal take ɗaga mata alamun gamsuwa da shawarar da take ba ta, ba tare da ta iya haɗa ido da
ita ba tsabar kunya da muzantar da ta yi a gabanta.

Sallamar da maigadin ya yi a bakin ƙofar shiga cikin gidan, ya sa Hajiya ta amsa tare da miƙewa ta nufi
ƙofar. Minal ta kasa motsin kirki ballantana ta tashi wurin har Hajiya ta dawo da wayarta a hannu ta miƙa
mata tana faɗin,

"Ga wayarki, ki je ki yi arwala ki kwanta. Ni ma na shige Allah Ya tashe mu lafiya."

"Amin." Ta amsa cikin maƙoshi jiki a sanyaye ta yi ɗaki da ledar don Hajiya ta bar ta da ita a hannu ba ta
karɓa ba. Ta jima zaune a bakin gadon da tagumi tana nazarin halin Jamal da shawarar Hajiya. Sai da ta
fahimci dare ya ƙara yi sannan ta koma buɗe ledar tana kallon chocolate da kalolin biscuits da ke ciki.
Murmushi ta yi babu shiri saboda tuna Jamal da birkitaccen halinsa mai wuyar fassara. Sannan ta mayar da
ledar gefe ta ajiye bayan ta ƙulle, da nufin sai Hajiya ta ga abin da ke cikin ledar kafin ta taɓa. Daren ranar
ma ta yi bacci mai ɗauke da mafarkan Jamal a cikin yanayin da dole sai da ta yi wankan tsarki kafin ta yi
sallar asuba. Saboda sabon abu ne da ya zamo mata tamkar almara, wanda take kallon sa tamkar wani
babban zunubi, don ta kasa yardar wa zuciyarta aurenta da shi mai inganci ne kamar kowane auren da ake
ɗaurawa.

Ta yi lattin tashi bayan ta koma barci bayan asuba. Don har Umma Ade ta zo gidan ba ta tashi daga
nannauyan barcin da ya kwashe ta ba.
Hajiya da Umma Ade a falo bayan sun gama gaisawa ta miƙa mata lambar mai kayan matan tana cewa,

"Na sanar da ita za ki kira ta. Ashe ita ma tana rubuce-rubucen littafai a cikin waya. Ni ma a bakin matan
su Nura na ji labarin kuma sunanta Surayy, su ma sun yaba sosai da ingancin kayanta. A cewarsu babu
asara ga sayen kayanta saboda amfaninsu ya linka ma ƙudin da za a kashe."

"Allah Sarki, Ubangiji Ya ci gaba da dafa mana gabaɗaya. Kuma na gode miki sosai Ade, bari na kira ta
tun yanzu saboda yaron can ya fara wuce gona da iri a kan yarinyar nan. Ga shi kuma ba na so ya same ta a
yadda take, don zai fi raina ta idan bai kamu yadda ake so ba."

Umma Ade ta yi murmushi bayan ta ce amin, sannan ta ƙara da cewa, "A dai bi mini yaro a hankali Hajiya
kada a yi masa mugun kamun da zai kasa zuwa gaishe mu."

"In dai ta riƙe mana shi da kyau to ya sha zamansa mun yafe zuwan, mu za mu dinga zuwa har gidansa
ganin shi. Don ya fi alheri a kan ya ɗebo mana wata wutar da za ta gagare mu kashewa."

Suka yi dariya gabaɗaya, saboda sigar da Hajiya ta yi maganar tare da kai wa Aden hararar gefen ido.
Kafin ta ƙara da cewa, "Ai Ade yaron nan naki babban riƙo kawai ya dace da Shi, saboda kansa rawa yake yi
ba ya shayin yin gaban kansa. Wannan dalilin ya sa na jinjina wa budurwarsa Aisha, saboda ba ƙaramin aiki
ta yi ba kafin ta raba shi da shashancin da ya mayar ba a bakin komai ba."

"Hmmmm! Allah dai Ya ƙara shirya mana su Hajiya. Amma yaran zamani kowa da kalar taɓararsa. Shi ma
in sha Allahu daga wannan lokacin ya gama tasa kalar ƙurciya."

Hajiya tana 'yar dariya ta ce, "Ke dai ba kya so a ga laifinsa, tafi ki yi aikinki lokaci yana tafiya."
Umma Ade ta wuce kitchen, yayin da Hajiya ta nufi ɗakinta da takardar lambar Surayya a hannunta.
Wuri ta samu a bakin gadonta ta zauna, bayan ta jawo wayarta ta fara saka lambobin kamar haka
08032773332, zuciyarta cike da ɗokin samun biyan buƙatarta cikin sauƙi.

Ɗii! ɗii! Wayar ta shiga ringing a lokacin da Hajiya ta danna kira, aka yi sa'a babu jinkiri ta ɗaga. Bayan
sun gaisa Hajiyar ta gabatar da kanta tare da bayanin ita ce wadda ta saka Ade ta nemo mata lambarta.
Suka sake gaisawa a mutumce kafin Hajiya ta yi mata bayanin dalilin neman ta. Ajiyar zuciya Surayya ta yi
kafin ta ce,

"A shawarce, kafin a ba ta kayan matan da ta yi amfani da su, yana da kyau ta fara shan maganin
infection kafin su. Saboda wani lokaci ko an sha maganin mata idan akwai infection ba zai bari a ga
amfanin kayan yadda ake so ba."

"To, babu damuwa. Yanzu a cikin magungunanki bayan na infection wane da wane kike da shi? Kuma
nawa ne kuɗin kowanne?"

Surayya ta yi murmushi mai sauti kafin ta ce, "Akwai ingantattun kayan gyara na Chad daga Bojuwa
Herbals. Sai Sanyi flusher mai wanko dukkan sanyin da yake maƙale a mahaifa da jijiya. Sannan akwai
ingantacciyar kazar sababi ta saiwowin Chad mai ciko da mace ta haɗe tamkar sabuwar amary..."

"Ita fa wannan amarya ce kuma sabuwar. A ganin ki babu wata matsala idan ta yi amfani da maganin da
zai ƙara haɗe ta?"

Hajiya ta yi hanzarin tambaya saboda jin ƙara matsewa gudun Jamal ya ji wa yarinyar mutane ta shiga
uku. Surayya ta yi murmushi sannan ta sake cewa, "Babu wata matsala Hajiya, ai duka cikin gyara ne irin
wanda kowace mace ake so ta yi tun daga kan budurwa har wadda ta taɓa haihuwa. Kada ki damu zan
haɗa mata da hakin daka mai kama jiki na mussaman. Tare da tsumin saiwowin da sai isassum mata ke
shan su. Don kayanmu duka na Chadi ne masu matukar inganci da rashin illa."

Cike da jin daɗi Hajiya ta ce, "To, ma sha Allah, sai ki faɗo mini kuɗin nawa ne gabaɗaya? Sannan sai ki
turo account na ba ki kuɗin gobe Ade ta zo mini da kayan, ko kuma na aika direba ya karɓo mini a
hannunta. Ubangiji ya ba mu ladar gabaɗaya."

"Amin-amin Hajiya. Allah Ya ƙara rufa asiri." Daga haka suka yi sallama, Surayya tana ƙoƙarin ajiye wayar
Hajiya ta sake cewa, "Mun gama magana amma ba ki faɗa mini sunanki ba."

"Sunana Surayya Dee, marubuciyar littafin HALIN YAU."

Sai a lokacin ta tuna ta ji sunanta a bakin Ade. Cike da jin daɗi ta ce, "Madalla Surayya, Allah Ya yi albarka,
in sha Allah zan haɗa ki da wata ɗiyata idan ta shigo garin. Ita ma tana son irin kayanku sosai, daga nan har
Sokoto ana aika mata kaya har zuwa Yobe. Amma tun da ga ki a cikin garin Kano idan muka ji daɗin kayanki
zan ba ta lambarki ku dinga zumunci, don na yaba da kirkinki duk da ban taɓa ganin ki ba."

Surayya ta yi murmushi cike da jin daɗi ta ce, "Babu komai Hajiya, in sha Allah za ku yaba da kayan fiye
da yadda kuke zato. Saboda bayan abubuwan da na lissafa miki har da haɗin amarya (Bridal package),
haɗin maijego da uwargida duka ina yi."
"Allah Ya ƙara dafa miki, kuma ya tsare ki da sharrin da ke ciki. Kada ki manta ki turo mini account zan
sa a tura miki kuɗin yanzun nan."

Daga haka suka yi sallama kowa ya ajiye wayar. Hajiya ta yi jim tana nazarin yadda za ta tsayu a kan
Minal ta yi amfani da kayan daki-daki. Ƙir shigowar saƙo a wayar ya sa Hajiyar ta duba, a fili ta furta,

"Ma sha Allah, saura kai uban rawar kai, kai ne za ka biya kuɗin ko nawa ne daga aljihunk...."
GARE KU MASU TAMBAYA!
Littafin FANSAR ƘAUNA na kuɗi ne. Ku biya ₦500 kacal ga wannan account. 9032685442 Opay. Waɗanda
tura kuɗi ta opay yake bai wa wahala ku tura ta Bank Account; 1230094555 Access Bank Hadiza D. Auta
Ibrahim.

DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. Mai buƙata 9032685442 Opay. Shaidar biya ta nan
08022014771.

10 February zan sake shi da yardar Allah.



D.
✍🏼 AUTA CE
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*

*HADIZA D. AUTA*

*AREWABOOKS: Princessdija.*

https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa


*LAMBA ASHIRIN.*

sallamarsa ta sa ta hanzarin kai kallonta a bakin ƙofar. Ta amsa masa fuskarta a cure tare da amsa
gaisuwar da ya yi mata a gajarce tana kawar da kai gefe. Kansa ya shiga sosawa bakinsa ɗauke da 'yar
dariya ya ce,

"Wurin aiki zan je Hajiyata. Shi ya sa na zo ki saka mini albarka."

"Wani kallo ta yi masa kamar ta ce wani abu amma kuma ta fuske, tare da komawa miƙa masa wayarta
sannan ta tashi tsaye. Nufar bakin wardrobe ɗin ta yi idonta a ciki kamai mai neman wani abu, daidai
lokacin ya yi magana cikin murmushi mai sauti ya ce,

"Wayar fa Hajiyarmu?"

Ba tare da ta kalle shi ba ta ce, "Kuɗi za ka tura, dubu hamsin da shida a cikin account ɗin da ka gani. Sai
arba'in da huɗu a cikin nawa account."

Ido ya zaro tare da marairaice fuska yana faɗin, "Hajiy..."

"Ba na son wata doguwar magana! Tura kuɗin ka miƙo mini wayata."

Ta katse shi cikin sauri tare da kafe shi da ido har ya tura kuɗin sannan ta ɗauke kallonta daga kansa ta
koma binciken da take yi. Ya tako a hankali idonsa a ƙasa ya damƙa mata wayar cikin hannunta yana
ƙumshe dariya. Ganin yadda ta haɗe fuska alamun babu wasa amma kuma tana so ta yi dariya.

"Yanzu fisabilillahi laifin me na yi da aka caje ni waɗannan kuɗin a matsayina na almajiri Hajiyarmu?"

Ya yi tambayar a lokacin da ya koma bakin gadonta ya zauna cikin sanyin jiki yana haɗe fuska. "Sa ranka a
inuwa, ni ma ba amfani zan yi da su ba, matarka ce take buƙatar kuɗin saboda biyan buƙatarku gabaɗay..."
"Amma dai yarinyar nan ta jaza mini aiki! Yanzu Hajiya saboda Allah duk me za ta yi da waɗannan kuɗin?
Yarinyar da ko dubu goma wataƙila ba ta taɓa riƙewa a hannunta b..tsakani da Allah Hajiya ki daina sake
mata damar da za ta lalace da son kuɗi a samu matsal..."

Juyowa ta yi a fusace tana faɗin, "Tafi wurin aikinka ba na son doguwar magana! Kuma daga yau babu
kai babu fita da ita yawo ban sani ba, ko da rana ballantana a cikin sulusin dare."

Ta yi maganar a fuske, sannan ta juya ta rufe wardrobe ta bi ta gefensa cikin sauri ta bar masa ɗakin. Jim
ya yi a tsaye riƙe da ƙugu kafin ya sauke numfashi mai ƙarfi yana faɗin,

"Shikenan Hajiya ta fi son ta a kaina."

Ya taka a hankali cikin sanyin jiki ya fice daga ɗakin shi ma, a ransa yana faɗin, 'Wayyo kuɗina! Wannan
muguwar yarinya ta san hanyoyin haɗa ni da Hajiya kala-kala. Kuma babu damar na gwada ta sai ta ɗauki
fansa...ba dai ni ba za ki shigo hannuna ne.'

Ya ƙare zancen zucin da ƙwafa, sannan ya fice falon ba tare da ya sake bi ta kan Hajiyar ba. Harabar gidan
ya nufa kai-tsaye ya isa wurin motarsa. Saboda irin kallon da Hajiyar ta wurga masa a lokacin da suka yi ido
biyu bayan fitowarsa ɗaki, hakan ya saka shi tafiya babu shiri da niyyar ya bar musu gidan tun kafin ya ƙara
yin wani laifin. Har ya isa wurin aiki bai daina tunanin hanyar da zai bi ya huce haushin da Minal take
ƙoƙarin ƙumsa masa ta hanyar Hajiya.

Hajiya kam yana fita ta ƙwala wa Ade kira, daidai lokacin da Minal ta fito daga ɗaki a ɗarare da niyyar yi
mata ina kwana. Ga shi lokaci ya ja ba tare da sun ga juna ba, saboda jin motsin Jamal a cikin gidan ya sa ta
ƙi fitowa daga ɗaki har sai da ta ji alamun tafiyarsa. Karin safiyar ma a ɗaki Ade ta kai mata, saboda sanin
Hajiya ba ta karyawa tun da safe ta bari sai ta nema da kanta.
Har ƙasa Minal ta durƙusa gaban Hajiyar ta gaishe ta kanta a sunkuye, cikin sakin fuska Hajiya ta amsa
mata tare da faɗin,

"Idan kin karya ki shirya direba zai kai ki gidan lalle da kitso. Saboda na sa Amna ta yi wa mai lallenta
magana ta ce ki je cikin lokaci saboda a kammala miki da wuri. Zan ba ki kuɗi idan aka gama ko nawa ta
faɗa sai ki biya ta. Amma ki tabbatar an yi mai kyau, ba iya irin wanda Amna take yi ba."

Minal ta yi dariya saboda tuno zancen Amnar a lokacin da take ba su labarin rikicinta da Hajiyar a kan
lalle koyaushe. Don ta fi son a yi mata na gargajiya ita kuma ko kaɗan ba ta son shi, shi ya sa ko ta yi lallen
ba ta yabawa sai faman kushen da take yi da harare-harare. Saboda ko zanen fulawar ma kaɗan Amna take
so ba ta son a cika mata lalle a jiki.
Minal tana ƙoƙarin miƙewa ta ga Umma Ade a gefe tana murmushi, ta raɓa ta gefenta ta wuce ita ma
fuskarta ɗauke da murmushin kuma cike da jin nauyin su duka. Don tun da Hajiya ta fara magana Aden ta
iso wurin amma ba ta ce komai ba har suka gama gudun ta katse su. Sai da Minal ta bar wurin sannan
Aden ta ce,

"Ga ni Hajiya."

"Yawwa Ade, da ma sanar da ke zan yi mun yi magana da Suraira ɗin..."

"Surayya take Hajiya."

Ummu Ade ta yi maganar tana 'yar dariya, saboda jin yadda ta sauya sunan alamun ba ta gama riƙewa ba.
"To..to haka nan fa Surayya! Na ba ta kuɗin abubuwan da za ta harhaɗa mana, kuma idan direba ya dawo
daga kai Aminar zai kai ki ki karɓo mana sauran kayan kafin ta gama dafuwar kazar sababin. Don ina so a yi
komai a gaggauce gudun yaronki ya kawo mana matsala ba tare da an gama gyaran ba.
"Mutum da matarsa Hajiy..."

"A hakan kuma zai bar ta duk nacinsa tun da har ya yi laifin da ta dawo gabana."

"Ni dai ina raba ki da yaran zamani. Kin san kuma farinjinin yarona ko bai nema ba mace za ta neme shi
da kanta. Kada kina bin bayanta ta zagaye ba tare da kin sani ba ta gane mijinta."

Dariya suka saka gabaɗaya, yayin da Ade ta bar wurin tana faɗin, "Bari na kawo miki abin kari. Ga shi an
manta yarona ya tafi ba tare da ya karya ba."

Hajiya tana dariya ta ce, "Shi ya sani Ade, ya je can ya ƙarata, don zamansa ma saka mutum magana kawai
zai yi."

***
Ƙarfe goma da rabi na safiya a gidan mai lallen ta buga wa Minal. Aka shiga tsefe mata kai bayan an
manna mata lalle. Wanda ta zaɓa da kanta a cikin waya, don tun kafin a shafa jan lallen tsarin jeren salatif
ɗin ya fito da ƙafarta fes. Duk da take baƙar mace amma baƙin nata bai hana jan lallen da zanen baƙin lalle
mai fulawowi fitowa ya yi kyau a ƙafarta ba. Haka ma fuskarta ta washe, saboda tana da cikar gashi tsawo
ne babu, wannan ya ba da damar da aka tsara mata kitso da gashin attach, wanda ta nuna style ɗin da take
so. Don da ma can da shi ta fi auki a koyaushe kitsonta ba ya tsallake na ƙari matuƙar za ta yi fitar kunya.
Kuna sosai kitson ya yi mata kyau kasancewar ƙwararriya ce ta yi aikin, musamman da aka haɗa mata da
na gaba ta ƙara zama 'yar ɗagwas.
Zuciyarta cike da jin daɗi ta cashe kuɗin da aka faɗa babu wata gardama, saboda Hajiya ta ba ta
wadataccin kuɗi har da saka wa kanta kati a waya, don ita ma an gama burge ta. Ranta fes ta kira Hajiyar ta
sanar da ita an gama komai direba ya dawo ya ɗauke ta. Misalin ƙarfe shida na yamma, Jamal ya faka
motarsa a ƙofar gidan lallen sannan ya kira ta a waya ya ce ta fito.
Ƙirjinta ne ya buga dam tun daga ganin kiransa har zuwa saƙon da ya fesar mata kafin ya datse kiran ba
tare da ya jira cewarta ba. Jiki babu kuzari tana haɗe rai ta fito gidan, tare da rakiyar wasu matan da ta
ƙulla ƙawance da su a wurin lallen, har da musayar lamba. Bakin motar suka ja suka tsaya suna yi mata
Allah Ya tsare, yayin da Minal ta buɗe gaba ta zauna tana dariyar yaƙe suka yi sallama, ganin irin kallon
ƙurullar da wata daga cikin su take yi wa Jamal, sosai hakan ya ƙona mata rai. Shi kam bai ma san tana yi
ba, don ita kanta Minal bai sake kallon ta ba har ya hau kan babban titin da zai kai su gida, bayan ya bar
ƙofar gidan.
Ƙirr! Wayarta ta shiga ƙara, cikin sauri ta duba mai kiran, ganin sunan Zulaiha gidan kitso ta ɗauka cike
da mamakin dalilin kiran.

"Ammm...na ce ba ƙawata.." Zulaiha ta yi magana cikin fargaba. Kafin Minal ta amsa a ƙagauce.

"Kika ce me?"

Ta yi maganar a taƙaice cike da zaƙuwar son jin abin da za ta faɗa, "Don Allah wannan gayen da ya ɗauke ki
yayanki ne ko saurayinki?"

"Me ya faru?"

Minal ta jefa mata tambayar cikin gatsali tana yamutsa fuska. "Ya burge ni sosai wallahi, kuma idan har ba
saurayinki ba ne ni ina ciki. Don Allah ki fara kama mini ƙafa kafin na gabatar da kaina idan kin ba ni
lambars...."

"Ke wace irin shashasha ce? Sannu Gantalalliya 'yar iska!"
Minal jikinta yana tsuma ta yi maganar saboda wani tsinin mashin baƙin kishin Jamal da aka caka mata a
tsakiyar zuciya. "Subhanallahi! Ƙawata me ya yi zafi ne daga tambay..."

"Ki je ki tambayi ubanki wataƙila shi ya san amsoshin da zan ba ki!"

Ƙitt! A zafafe ta datse kiran tare da danna mata block. Sannan jikinta yana rawa ta sake nemo lambar
ɗayar ƙawar lallen ta danna mata blocking ita ma. Tana huci fuskarta a cure ta yi

16 / 29