Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
gare shi ba gudun ya gano halin da take ciki ya nemi cutar da ita babu
mai ceton ta. Don a cewar Gwaggon idan ya fahimci tana mugun tsoron sa zai raina ta yawa ta yadda zai
dinga yi mata abin da ya ga dama koyaushe. Hakan ya sa shigowarsa bai sa ta kai duban ta gare shi ba duk
da hankalinta yana kansa. Sannan bai yi sallama ba ballantana ta amsa, sai jin sa ta yi ya saki ledodin da ke
hannunsa suka zube ƙasa, bakinsa yana rawa ya kira sunan Nur cikin ɗaga murya yana cewa,
"Nur! Yaushe kika dawo ban sani ba?"
Wani kallo ta yi masa kamar ta yi masa babu yabo babu fallasa, amma a zuciyarta sosai ya ba ta tausayin
da ya so karya mata zuciya. Sai dai hakan bai hana ta waige gefe da gefe ba cikin basarwa ta ce,
"Ina ka ga Nur a nan?"
"Ya Allah!"
Jamal ya faɗa cikin wata irin murya yayin da ya yi hanzarin dafe kansa da ke sarawa babu shiri. Saboda
hango Minal a matsayin Nur ya tayar masa da mikin da yake ƙoƙarin dannewa a ransa. Saboda gizon da ta
yi masa sak Nur da ƙamshin turaren Nur da ya ji a cikin falon, wanda tun asali shi ne ya fara yi masa
maraba kafin ya isa bakin ƙofar shiga falon. Ƙirjinsa ya hau bugawa babu ƙaƙautawa ya shiga nuna ta da
hannu yana faɗin,
"Ko da wasa kika sake saka turaren Nur a cikin gidan nan sai na sauya miki kamanni...kuma kin ci sa'a na
yi wa Hajiya Mummy alƙawarin zama da ke da a yanzun nan sai kin bar gidan nan wallahi...ahhhh!"
Ya ƙare maganar yana dafe kansa ya wuce jiri yana kwasar sa ya faɗa ɗakinsa. Kamar da gayya a ɗakin ma
turaren Nur ne ya fara yi masa oyoyo. Gado ya yi hanzarin kwantawa dafe da kansa yana murza goshinsa
tare da bubbuga kansa a hankali. Ya bar Minal da ƙamewa wuri ɗaya tamkar an dasa ta, saboda furutansa
sun ƙara lalata ƙarfin halin da ke zuciyarta.
Zumbur ta miƙe gudu-gudu sauri-sauri jikinta yana rawa ta faɗa ɗakinta, babu ɓata lokaci ta hau cire
kayan Nur da ke jikinta. Sannan ta nufi bayi da sassarfa ta shiga darzar jikinta da sabulu tana haɗa kumfa, a
ƙoƙarin ta na son raba kanta da ƙamshin Nur saboda gudun ta shiga haƙƙinsa da yawa ciwonsa ya ƙara
tashi ta yi sanadin sharri. Don Hajiya ba ta ɓoye mata komai ba ta sanar da ita duk abin da likita ya faɗa a
kan ciwon nasa tun kafin ya dawo gidan. Kuma ta nemi alfarmar ta kula da shi tare da juriya a kan
halayensa har a shawo kan matsalolin da ke cure su warware.
Sai da ta ji fatar jikinta ta fara zafi sannan ta haƙura da wankan ta fito daga bayin. Jikinta a mace ta sake
shiri ta fice saboda tuno abincin da take son yi masa ta yi kada ya kwana da yunwa. Ta ɗauki minti biyar a
bakin ƙofarsa tana tunanin yadda za ta shiga ɗakin da irin sakamakon da zai biyo bayan shigarta. Kamar
wata mara gaskiya haka ta shiga ɗakin nasa tamkar wadda ƙwai ya fashewa a ciki ƙirjinta yana harbawa.
Nesa da shi ta tsaya tsawon minti biyu ba tare da ta iya furta masa ko kalma ɗaya ba. Alamun mutum da ya
ji a kansa ya yi hanzarin tashi zaune yana ƙare mata kallo cike da mamaki. Kafin ya haɗe girar sama da ta
ƙasa ya yi magana cikin kakkausar murya ya ce,
"Malama lafiya kika shigo mini ɗaki ko sallama babu!"
"Abin..ci...abin...cin...na ce.."
Kalmomin da ta yi ƙarfin halin harhaɗawa kenan cikin ininar da ba ta san ta iya ta ba sai a ranar. Saboda ya
kafe ta da ido tamkar wadda ya kama da laifin kisa ko ta yi masa babbar sata.
"Abinci-abinci kika ce me?"
Ya maimaita maganarta cikin sauya murya a sheƙeƙe alamun ya kai maƙura da takaicin ta a ransa. Tana
kallon yatsun hannunta ta mayar masa da amsa fuskarta a haɗe kanta a duƙe ta ce,
"Abinci ne na dafa, idan za ka ci sai na kawo maka."
"Abinci!"
Ta yi hanzarin ɗaga kai a tunaninta ta yi masa gwaninta, amma jin tsawar da ya daka mata da maganganun
da ya baibaye ta da su; ya sa ta yi hanzarin ficewa sum-sum daga ɗakin cike da tsoro bayan rawar da jikinta
ya hau yi.
"Ni ne kike zaton zan ci abincinki? Ke mahaukaciyar ina ce da za ki yi tunanin zan iya cin abin hannunki
ma ballantana ƙazamin abincinki?"
Ganin ta bar masa ɗakin ya fito falon yana ta balbala mata masifa duk da ta shige ɗakinta, amma bai
haƙura ba cikin ɗaga sauti tamkar bai san dare ne ba ya zazzaga mata zafafan maganganu tamkar ana yi
masa wahayin su.
"Idan na sake ganin jemammun ƙafafuwanki a ɗakina sai na saka gitta na sare su gabaɗaya! Daga yau
kada ki sake shiga duk sabgar da ta shafe ni...idan kuma ganganci ya ja ki na illata ki a banza na ga wanda
zai tsaya miki baƙar wawuya bagidajiya! Kuma ki buɗe kunnuwanki da kyau ki ji ni; matuƙar ba ki sanar da
ni inda Nur ta je ba sai na ga bayanki baƙar munafuka mai raba ƙauna!"
Minal ta rushe da wani irin kukan da ba ta san lokacin da ya suɓuce mata ba. Saboda kalamansa na
ƙarshe sun yi matuƙar gigita mata kwanya. Kuma sun shiga jikinta ta yadda ita kanta ta shiga tunanin laifin
me ta yi wa Nur ta yi mata irin wannan sakayyar, ta gudu bayan ta ɗora mata jakar tsaba a ka kaji suna
aikin caccaka. Tun tana kukan da hawaye har ta koma yin na zuci tare da ajiyar zuciyar da babu komai a
cikin ta sai nadamar zamanta gidan ba tare da ta tsere kamar yadda Nur ta yi ba.
'Matuƙar ba ki sanar da ni inda Nur ta je ba sai na ga bayanki baƙar munafuka mai raba ƙauna.'
Maganganunsa sun daki zuciyarta, hakan ya sa suka fara yi mata amsa-kuwwa a cikin kunnuwa babu
ƙaƙƙautawa ta shiga jujjuya kanta tana faɗin,
"Nur ki dawo tun kafin raina ya zamo fansar guduwarki."
Jiki ta ja tana jan ɗuwawu ta isa bakin gado ta jingina bayanta tare da ɗora kanta saman gadon tana
haɗiyar zuciya da shesshekar kukanta a hankali. A haka barci ɓarawo ya sace ta daga zaune tana tunani da
ajiyar zuciya lokaci bayan lokaci har a cikin barcin.
Shi kam sai bayan ya gama sababin da surutan shi kaɗai sannan ya kwanta rigingine yana kallon sili,
zuciyarsa cike da tunanin ta wace hanya zai ci gaba da neman Nur. Zuciyarsa ta tsayu a kan zai bayar da
cigiyar ta gidan rediyo da kuma posting a social media. Ta yadda abin zai zama viral ya watsu a ko'ina ko za
a dace. Da wannan nazarin ya miƙe a lokacin da cikinsa ya fara ƙugin yunwa. Kitchen ya nufa ya yi tsaye
bakin ƙofa yana ƙare masa kallo bayan ya kunna ƙwan lantarkin da Minal ta kashe a lokacin da suka gama
aiki.
Bincike ya dinga yi har ya haɗa kan indomie ya haɗa ta da ƙwai biyu cikin ɗan lokaci ya dafa.
Kasancewar ya iya hannunsa tashin hannun Hajiya ɓangaren abinci abubuwa kaɗan ne bai iya ba. Duk da
gatan da take yi masa hakan bai hana shi koyon wasu ayukan mata ba.
Bayan ya cinye indomin ya tuna da kunun ayar Hajiya, ƙaƙƙarfan tsaki ya ja sannan ya fice daga ɗakin ya
nufi bakin ƙofar shigowa babban falon ya kwashe ledodinsa da ya watsar.
Kasancewar akwai wadatacciyar nefa kuma akwai ƙanƙara a cikin frizer da ke kitchen. Wadda ya gan ta a
ƙanƙare wajen binciken da ya gama yi lungu da saƙo har zuwa store da ke ƙuryar kitchen ɗin. Sai da ya
kwankwatsa ƙanƙarar ya jefa a kunun ayar, wanda ya bulbule a cikin dogon jug sannan ya faɗa wanka.
Zuciyarsa babu daɗi ya gama wankan ya fito yana tsane jikinsa yana tsaki cike da takaicin Minal ya sake
faɗin,
"Wawuyar banza mai ƙaton kai! Duk inda Nur ta je ta sani, kuma gobe idan ba ta sanar da ni gaskiya ba
sai na ɗauki mummunan mataki a kanta. Ban san me ta yi mata ba don kawai ta gudu ita ta aure n....don
ubanta ko za ta mutu ba zan yi zaman aure da ita ba tun da ba na son t...mitsssss!"
Ya ƙare maganar da jan dogon tsaki ya ja jug ɗin kunun a tsaye ya kafa masa baki ya fara kwankwaɗa. Garɗi
da daɗin kunun, haɗi da sanyin da ya yi bai san lokacin da ya tayar da jug ɗin ba ya ajiye kofin yana gyatsa.
Bakinsa ya goge bayan ya koma toilet ya yi brush ya kwanta da towel a jikinsa yana haki kamar wanda ya
sha gudu.
Da tunanin Nur bacci mai nauyin gaske ya kwashe shi. Kamar almara cikin dare ya fara jin jijiyarsa tana
miƙewa, zumbur ya zabura saboda kakkarwar sanyin sha'awa da ya shiga yi. Kansa ya dafe yana salati
saboda yanayin da yake ji bai taɓa tsintar kansa a makamancinsa ba. Zarya ya fara yi a cikin falon dafe da
kai jijiyarsa a miƙe kamar mai koyon tafiya. Babu shiri ya yi zaman 'yan bori a tsakiyar ɗakin saboda ya kasa
juriyar tsayuwa da ƙafafuwansa da ke kakkarwa.
"Ya Salam!"
Ya yi ta jerawa a bakinsa yana maimaitawa tamkar wanda aka saka yin hadda. Nan take gumi ya hau keto
masa yana sharewa da hannu har ta kai ya dafe mararsa yana salati. Tsabar harbawar da jijiyarsa take yi
tamkar numfashinsa zai shiɗe yake ji. Halin da yake ciki ya saka shi miƙewa babu shiri ya fara tafiya yana
layi ya faɗa ɗakin Minal jikinsa yana tsuma. Ƙafafuwanta ya jawo da ke shimfiɗe a bakin gado, babu shiri ta
baje a tsakiyar ɗakin tare da farkawa a haukace cikin wani sabon firgici. Saboda mafarkinsa take yi wai ya
zo da wuƙa a kanta yana faɗar ko ta faɗa masa inda Nur ta ɓoye ko kuma ya kashe ta.
Ihu ta fasa iya ƙarfinta ta buge shi ya faɗi ƙasa dabas tare da sakin towel ɗin da ke ɗaure a ƙugunsa.
Wataƙila halin da yake ciki ya mantar da shi babu komai a jikinsa, a haka ya miƙe jijiya miƙe ya nufe ta
gadan-gadan zai kamo ta. Ta sake ƙwalla ƙara tare da zurawa da gudu ta faɗa toilet a sukwane, sai dai kafin
ta rufe ƙofar suka shiga kokawa a tsakaninsu. Yana ƙoƙarin shiga ciki yayin da ita kuma take ƙoƙarin tura
ƙofar iya ƙarfinta a kan ba zai shiga ba, saboda kuzarinsa ya rage ya kasa shigar kamar yadda ya so.
Ganin za ta ɓata masa lokaci ya yi baya da nufin banke ƙofar da jikinsa ko da za ta ɓalle in dai zai samu
biyan buƙatarsa. Sai dai yana yin bayan ta datse ƙofar tare da hanzarin saka makulli ta rufe ruf jikinta yana
kyarma tamkar mazari. Don a iya tarihin rayuwarta ba ta taɓa shiga tashin hankalin da ya kai wannan ba,
don ba ta taɓa yin ido da babban mutum babu tufafi a jikinsa ba, sannan da yunƙurin yi mata fyaɗe ko a
mafarki. Hakan ya ƙara ɗaga mata hankali ta shiga zunduma ihun neman agaji.
Shirun da ta ji tun daga lokacin da ta rufe ƙofar bai nemi buɗewa ta ƙarfi ba; amma hakan bai sa ta fasa
kururuwar da take yi ba. Jamal kam ganin ta yi nasara a kansa ya koma ɗakinsa da sassarfa ya ɗauko ɗaurin
kuɗi 'yan dubu-dubu har bandur ɗaya sababbi kar ya tsaya bakin ƙofar toilet ɗin yana magana cikin rawar
baki tsabar yadda yake ji a jikinsa.
"Idan har ba za ki bari na yi don Allah ba to ga shi zan...bi.. biya ki...tun da...da ma can ke..ba kya... tsoron
Allahhhhh...."
Cabɗijam!🙆
Na yi kudi🏃
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA IBRAHIM D. AUTA*
*LAMBA TA BAKWAI.*
"Wayyo-wayyo Allahna!"
Abin da ta faɗa kenan daga cikin bayin dafe da kanta ta ƙwalla ƙara iya ƙarfinta. Ido ta shiga zarewa tana ci
gaba ihun da kururuwar faɗin ta shiga uku ta lalace a zo a kawo mata ɗauki.
Wannan dalilin ya jawo hankalin maigadin gida ya fito a firgice ya isa bakin ƙofar shiga falonsu yana
bubbugawa babu ƙaƙƙautawa yana kiran sunan Jamal. Bayan ya gama zagayen gidan lungu da saƙo da
zungureriyar addarsa, yana ta neman inda zai ci karo da wani baƙon fuska ko wata alamar da ke nuna an
shiga gidan bai sani ba. Don duk hasken da ke gidan bai hana shi ƙarawa da fitilar hannunsa mai matuƙar
haske ba.
Sosai bugun ƙofarsu ya saka Jamal diriricewa, saboda zumbur ya miƙe daga ƙasan da ya baje dafe da
mararsa yana kakkarwa. Amma dole ya miƙe dafe da ƙugunsa yana tafiya kamar mai tete, a haka ya sauka
daga ƙasan benen da towel a ƙugunsa ya buɗe ƙofar. Don bai tsaya wani jinkiri ba ko ɓata lokacin tambayar
wane ne ba. Saboda jin muryar maigadi ya saka shi shahadar buɗewa babu shiri.
"Baba lafiya?"
Tambayar da ya wurga masa kenan a lokacin da ya gan shi tsaye da addarsa a hannu bayan fitilar da yake
haskawa gefe da gefensa.
"Ranka ya daɗe sautin Hajiya da na jiyo tana ihu tsawon lokaci ya sa na ji tsoron kada a ce wani
mummunan abu ne ya faru ban sani b..."
"Babu abin da ya faru je ka kwanta."
Ya yi maganar ransa a haɗe cike da jin haushin maigadin. Sumui-sumui ya bar wurin yana faɗin, "Allah Ya
ƙara tsarewa." Saboda fahimtar inda lamarin ya dosa babu wani abu sai tsabagen rakin amaryar gidan.
Duba da yanayin da ya gan shi a birkice sannan da sigar da ya fito a yadda yake ba tare da ya ji kunyarsa ba.
Tsaki kawai Jamal ya ja ya rufe ƙofar a maimakon ya amsa masa da amin. Ya koma da sassarfa yana
yamutsa gashin kansa da hannun tare da faɗin Ya Salam a cikin bakinsa ta fi a ƙirga.
Ɗakinsa ya nufa tare da kulle ƙofa ya nufi bayi cikin ƙuncin rai ya yi ta sheƙa wa kansa ruwan sanyi, sai
da ya ji rabin nutsuwarsa ta shiga jikinsa hankalinsa ya dawo, sannan ya fito kansa yana muguwar sarawa
ya kife a kan gado. Ajiyar zuciya ya shiga saki ɗaya bayan ɗaya yana nishi dafe da jijiyarsa da ke harbawa
har komai ya lafa masa barci ya yi awon gaba da shi.
Asubar farin ya farka ya yi wanka da arwala ya fice masallacin da ke kusa da gidansa. Zuciyarsa cike da
tunanin irin hukuncin da ya dace ya yanke wa Minal idan safiya ta waye. A gefe ɗaya kuma cike yake da jin
haushin kansa, har aka gama sallar ya dawo gida bai daina tunanin dalilin da ya jawo masa shiga halin da
ya tsinci kansa ba. Saboda tun a daren farkon auren da Nur ta karya masa zuciya bai sake saka wa kansa zai
iya shiga irin wannan yanayin a kurkusa ba. Domin ya ci alwashin har Minal ta gama zaman banzarta ta bar
masa gidansa ba zai yi mata kallon mace ba. Amma sai ga shi ya kwafsa tun ba a je ko'ina ba.
Minal kam kwanan toilet ta yi idanuwanta sun yi jajir kamar gautan kaji tsabar barcin da ke idon da kukan
da ta sha tamkar hawayenta zai tsiyaye. A daddafe ta fito daga bayin a daidai lokacin da ta ji ana kiran
sallar asuba. Wayar Gwaggo salame ta shiga kira ana ce mata a kashe take, amma hakan bai hana ta tura
mata saƙon taimakon gaggawa ba, da zummar tana buɗe wayar idan ta gani ta kawo mata ɗauki, idan
kuma zakara ya ba ta sa'a ta aiwatar da nufinta kuma shi kenan. Saboda ta gama tsorata da lamarin Jamal
don ta yi amanna da shaye-shaye yake yi. Shi ya sa da ya bugu a daren jiyan ya so juye mata mayen giyar a
saman kanta. Bayan ya gama cewa idan aka cire shigar matan da ke jikinta babu wani bambanci tsakaninta
da namiji ɗan'uwansa.
'Gwaggo ki zo da 'yansanda Jamal ya sha giya yana ƙoƙarin kashe ni.'
Saƙon da ta tura mata kenan jikinta yana rawa tsabar ta gama tsurewa da lamarinsa gabaɗaya. Kamar
ɓarauniya ta fito daga ɗakin cikin sanɗa ta sauka ƙasa da dabara gudun ya jiyo takunta ya sake ya lalata
ƙudurin da ta kwana da shi a cikin zuciyarta.
Turus Jamal ya yi a lokacin da ya zo shiga gidan ya ji ƙofar a ƙargame. Kiran sunan maigadin ya yi cikin
sauri ya buɗe masa yana faɗin,
"A yafe ni ranka ya daɗe, Hajiya ce ta so tserewa na hana ta fita."
Hango Minal ya yi a tsaye riƙe da ƙugu tana kumbura fuska, bai bi ta kan maigadin ba face kallon sama da
ƙasan da ya yi mata ya watsar, sannan ya wuce zuwa cikin gidan ba tare da ya ce da su komai ba. Hakan ya
saka maigadin ya sake rufe gidan da kwaɗo ya zare makulli saboda ya gama fahimtar yajin amare ne take
shirin dakawa. A ransa ya jinjina lamarin, tare da yin dariyar ashe akwai sauran mutan da masu gudun miji
har zamanin da ake ciki a yanzu na buɗewar ido.
"Ki yi haƙuri ki koma daga ciki Hajiya, ni ma zan je na yi sallah na ɗan matse barcin idona. Sannan ki bai
wa maigidan haƙuri don alamunsa ya nuna bai ji daɗin ganin ki a nan ba."
Harara ta wurga masa a ƙufule duk da girmansa ta juya zuwa cikin gidan ranta a matuƙar ɓace, saboda ta
so tafiya ya hana ta kuma ta so Jamal ya kula ta ta yi masa tijara. Kamar yadda ta so barin gidan ba tare da
kowa ya sani ba. Aka yi rashin dace tun daga lokacin da ta fito cikin gidan a kan idon maigadin. Don yanayin
ta kaɗai ya sa ya gano babu lafiya ya dakatar da arwalar da yake yi. Musamman ganin abin da take ƙoƙarin
aikatawa, kafin ta ƙarasa jikin ƙofar ya kulle gidan da ƙaton kwaɗo cikin sauri. Duk yadda ta so ya buɗe ta
fita cikin magiya; amma kukan da ta yi masa bai saka shi tausaya mata ya buɗen ba. Saboda ya san kan
aikinsa kuma ya tuno lokacin da ta so barin