Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
mabuƙaci.
Minal ko wani kallon 'yan duniya ta yi masa tana 'yar dariya ta ɗaga hannu sama alamun sara masa ta ce,
"Ok sir!" Sannan ta juya ta shige ɗaki .
Sai a lokacin Zee ta samu kuzarin zuwa inda yake ta faɗa jikinsa tana rera waƙoƙin kuka kala-kala. Ya ja ta
jikinta ya rungume tsantsan sannan ya sauke ƙaƙƙarfar ajiyar zuciya mai sauti. Haƙuri ya shiga ba ta bayan
sun isa kan kujera sun zauna, tare da yi mata alƙawarin ba zai taɓa son Minal ba.
Mintuna a tsakani bayan Jamal ya shawo kan Zee ta daina kukan tana masa shagwaɓa Minal ta fito cikin
wata sabuwar shigar ƙananun kayan. Inda ta saka riga mai hannun best iya cibiya da dogon wandon da ya
ƙara fitar da halittar jikinta, don ko bra cirewa ta yi ta bar kan nipples ɗin ta suna maraba da mai kallo.
Sannan ta saka wata kwantacciyar hula kamar ta 'yansanda ta saki jelar kitson burazil da ƙanwarta ta yi
mata a gida, wanda ya saje da gashin kanta kuma ya sauka gadon bayanta yayin da ta zubo wasu a gaban
fuskarta. Da takalmi mai mugun tsini a ƙafarta ta fara taku cikin nutsuwa har ta iso gabansu. Sannan ta
shiga fareti tana juyawa tare da buga ƙafa bombom da ƙirjinta suna ta aikinsu na rangaji.
Ganin abin da take yi ya ja hankalin Jamal Zee ta fashe da wani sabon kuka tana kai masa duka tare da
kiran sunansa. Minal kam ko kaɗan hargowar Zee ba ta saka ta daina abin da take yi ba, sai da ta gama iya
juyin da take so sannan ta ƙame ƙam a gabansu ta ƙara sara wa Jamal ta ce,
"Me za a dafa mata 'yar laɓai?"
Takun ƙaniya🫣
*SANARWAR!*
*INA SO KU NUNA MINI KARA RIN WADDA ZAN TABBATAR KUNA JIN DAƊIN BIYA TA A CIKIN LITTAFIN
FANSAR ƘAUNA. MUTUM 50 KACAL NAKE SO MASU SAYEN lLITTAFIN DAKAN ƊAKA.. COMPLETE BOOK 1-2
PRIZE 1K GA MAI BUƘATA YA TURO KUƊINSA TA NAN; 9032685442 OPAY. SHAIDAR BIYA TA NAN
08022014771. ZAN SAKE SHI A RANAR 3 GA WATAN FEBRUARY. LABARI NE MAI ƊAUKE DA RIKICI,
HARGITSI, TASHIN HANKALIN DA RIKITA-RIKITA BAYAN ZALLAR TSAGWARON SOYAYYA MAI ABIN MAMAKI.
NI CE DAI MARUBUCIYAR ABOKIN AIKINA. KUN SAN KALAR ALƘALAMINA BA NA RUBUTA ABIN DA BA ZAI
DAMƘO ZUCIYA BA*
*SAURA KWANA HUƊU KACAL YA RAGE GA MASU BUƘATAR SHIGA CIKIN WANNAN TSARI. GA WAƊANDA
SUKA SAYA SUNA DA KYAUTAR LITTAFAINA BIYU. RUWA DA ƘANƘARA DA BAKAN GIZO.*
SAI KUN ZO.
D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*LAMBA SHA BIYAR.*
Ƙaƙƙarfan tsaki Zee ta ja sannan ta zame daga jikin Jamal ta miƙe a fusace ta nufi ɗakinsa, tana goge
hawayen da ke malala a kan fuskarta.
Kallo Jamal ya bi ta da shi, hakan ya sa Minal da ke tsaye gabansa rungume da hannu ta ce,
"Ka tambayo ta mu ji abin da take so na je na dafa mata lokacin breakfast yana ta ƙurewa. Ina so na
gama da wuri sai na ɗora mata girkin rana kafin na dare ya zo shi ma."
Wani sakaran kallo Jamal ya bi ta da shi cike da mamakin da ta ƙara jefa shi a ciki. A gefe ɗaya kuma
kukan Zee yana shiga kunnuwansa, gabaɗaya zuciyarsa ta hautsine. Zumbur ya miƙe ba tare da ya tsaya ba
ta amsa ba, cikin sauri ya nufi ƙofar ɗakinsa saboda hango Zee da jakar kayanta tana ƙoƙarin fitowa daga
ciki.
"Ina za ki je kuma? Ba sati ɗaya za ki yi mini ba?"
Ya furta maganar bakinsa yana rawa tsabar ya gama ruɗewa, kuma yana hangen Minal ta lalata masa duk
wani tsari.
"Ba zan iya zaman b...zuciyata za ta iya fashew.."
Ta yi maganar tana murza idanuwanta cikin shesshekan kukan da ta yi har idanuwanta suka sauya. Cikin
sanyin jiki ya isa daf da ita ya riƙo jakarta yana faɗin,
"Ki yi haƙuri zan ɗauki mataki a kan duk abin da ta aikata miki. Amma ki sani babu inda za ki je har sai kin
gama mini kwanakin da muka tsar...."
"Tun farko ban san da wata a cikin gidan ba da ban yarda na amince da zuwan ba. Amma tun da
idanuwana sun ga komai ba zan yarda a fasa mini zuciyata a banza ba...sakar mini jaka ni ba zan zauna
ba.."
Ta ƙare maganar tare da fisge jakarta ta yi gaba. Ya bi bayanta yana magiyar ta yi haƙuri ta zauna har suna
ƙoƙarin ficewa daga falon, daidai lokacin da suka ji Minal tana faɗin,
" Ke! Hajiya kwartuwa, ga shi har za ki tafi ba ki faɗa mini abin da zan girka miki ba."
Daga Zee har Jamal kallon mamaki suka bi ta da shi, saboda sunan da ta kira kuma ta bi da zance kamar
wadda ta yi abin arziƙi. Babu shiri Zee ta ƙara fashewa da wani sabon kuka tana nuna ta tare da kallon
Jamal ta sake cewa,
"Babe, kana jin me take faɗa kuma ba ka ɗauki matakin komai b...to na rantse da Allah ni kuma ba zan
ƙyale ta b..."
Ta yi maganar cikin hargowa tare da sakin jakar ta nufi kitchen da gudu tamkar wata mahaukaciya. Minal
da ke tsakiyar falon a tsaye rungume da hannuwa a ƙirji, babu shiri ta fashe da wata mahaukaciyar dariya.
Saboda kalar gudun da Zee ta yi ga ta ɗunɗumemiya kamar ta kifa ta faɗa zuwa kitchen. Hakan ya saka
Minal dariya sannan da farincikin Zee ta ji haushin sunan da ta kira ta da shi. Ta ƙara sakaws ranta kaɗan ta
gani kuma sai ta koya mata hankali.
Zee da ke kitchen kamar wata mahaukaciya ta shiga neman wuƙa ta dinga ɓarin kaya, amma duk neman
ta ba ta samu ko ɗaya ba. Saboda tun lokacin da Jamal ya kwashe su ya ɓoye a ɗakinsa bai dawo da ko
ɗaya ba. Ita ma Minal da dubara take amfani da cokali mai yatsu har ta yanka abin da take so.
Ganin babu wuƙar da gaske kuma neman zai ɓata mata lokaci, ta fisgo cakali mai yatsu ta fito a
haukace tana ƙoƙarin isa kan Minal idonta rufe. Cikin sauri Jamal ya sha gabanta tare da riƙe ta yana
ƙoƙarin hana ta abin da zuciya ke ingiza ta, ita kuma tana ƙoƙarin kufce wa riƙonsa don ta yi kan Minal da
nufin ƙaddamar mata, ta huta da takaicin baƙin kishinta da ke cin zuciyarta.
Minal dai har lokacin tana tsaye a inda take ba ta fasa dariyar ba, kuma idonta a kansu suna ta kokawa a
ƙarshe abin ya koma faɗa a tsakaninsu. Saboda haushin Jamal ya hana ta isa wurin Minal ta yi abin da ta yi
niyya; ta ware haƙoranta ta gatsa masa wani mahaukacin cizo a damtsen hannu. Zafin cizon ya saka shi yin
tsalle tare da fasa ihu kafin ya sauke mata wani lafiyayyen mari da bayan hannu. Cike da mamaki ta riƙe
gefen fuskar tata inda naman kumatunta ke rawa tsabar ƙarfin saukar marin tana kallon sa. Ta jima idonta
a kansa bakinta a sake kamar wata gaula, kafin ta ɗora hannu a ka ta fasa wata uwar ƙara ta faɗi ƙasa tana
birgima. Saboda takaicin tozarcin da ya yi mata a gaban Minal bayan don shi ta zo gidan, saɓanin tunanin
da ta yi a kan ya ci zarafin Minal kuma ya sauke mata ƙananun iskancin da ta hango a tsakiyar kanta.
Jamal kam ɗakinsa ya nufa riƙe da hannun da ta gatsa masa cizon ransa a ɓace yana tsaki. Minal ta ƙara
fashewa da wata mahaukaciyar dariya tana tafa hannuwa, kafin ta faɗa a kan ɗaya daga cikin kujerun falon
tana ta dariyar mugunta har da riƙe ciki. Musamman da ta kalli Zee a dunƙule tana gunjin kuka ta koma
kallon jakar kayanta da ke yashe ga banza. Sannan ga Jamal ya shige ɗaki, zogin cizo ya hana shi tsayawa a
ƙarasa wasar.
Dariyar da Minal ke yi ta ƙara ziga Zee ta fusata, idanuwanta a rufe ta zabura tamkar wata kububuwa
tana huci ta yi kanta da duka babu ji babu gani.
'An zo wurin.'
Minal ta faɗa a ranta, don da ma can a shiryenta take a kan duk yadda ta faɗi rataya. Saboda ganin Jamal
ya bar ta daga ita sai ita jikinta ya ba ta Zee za ta kawo mata wani raini. Babu ɓata lokaci ta saki ƙwanji suka
yi ta kai wa juna duka.
Kaf! Kif! Kakakaf! Sautin doke-doken da suke yi kenan. Dambe ya kacame suka dinga neman makasar
juna, kowace da ƙudurin ta illata 'yar'uwarta. Kasancewar Zee tana da ƙiba, Minal tana samun sa'ar kai ta
ƙasa da ƙyar ta haye ruwan cikinta tana kai mata duka ta ko'ina. Duk ƙoƙarin Zee da ƙarfin halinta; bai sa ta
ɓanɓare Minal daga maƙalewar da ta yi mata ba tana aikin jibgar ta inda duk hannunta ya je. Dole ta sa
Zee fasa ƙara tana jera kiran sunan Jamal babu ƙaƙƙautawa ganin da gaske Minal illata ta take son yi ƙarfi
da yaji.
Ko da Jamal ya fito baki a sake ya dinga kallon abin da yake faruwa, kafin ya isa wurin a fusace ya fisgo
Minal cikin fushi ya wurga ta gefe tana haki. Ransa a matuƙar ɓace ya dinga aika mata kallo cike da takaicin
ganin ɓarnar da ta aikata wa Zee. Domin gabaɗaya ta sauya mata fuska, bakinta jini hancinta jini. Hatta
idanuwanta ajin jini ne a ciki saboda yakushe mata fatar ido da Minal ta yi. Bayan kumburewar da fuskar ta
yi sumtum a cikin ɗan ƙanƙanin lokaci.
"Ke wace irin mahaukaciya ce ban sani ba? Kina ganin yadda kika mayar da yarinyar mutane kamar babu
imani a zuciyarki! To wallahi duk abin da ya biyo baya babu ruwana duk inda take ta kai ƙarar ki za ta ja
haƙƙinta a kan wannan rashin imanin da kika gwada mata... wannan ai rashin hankali ne mai lasisi..kai
jama'a!"
Ya ƙare maganar a firgice bayan ya ɗago fuskar Zee da ke kife cikin tashin hankali, ganin jinin da ke zuba
daga hancinta har ya ɓata gaban rigarta.
"Wallahi! Wallahi ko gobe wata kwartuwa ta zo gidan nan, kuma ta nemi ta dake ni sai na yi mata abin da
ya fi wannan..."
"Ko me ta yi miki ai bai kamata ki yi mata irin wannan aika-aikar ba! Don taƙamar ta zo cikin gidan nan..ni
na kawo ta kuma ba gidanki ba ne!"
Wani kallon uku kwabo ta yi masa kafin ta mayar masa da amsar cewa, "Kai da ka kawo ta ma ka kwaɗa
mata mari saboda ta cije ka. Sai ni zan zuba ido na ƙyale ta dake ni a banza? To duk matakin da za a ɗauka
kaina a ɗauka amma wallahi ban yi danasanin sauya mata fuska ba...kai ko mutuwa ta yi a sanadin hakan
Allah ba zai kama ni ba don kare kaina ne na yi. Tun da ita ma ta so kashe ni ba don ka karɓe cokalin ba da
ba a san me za ta aikata mini da shi ba...to ta yi duk abin da za ta yi ina jira! Tun da ita kaɗai ce mai gata ni
ce ba a bakin komai b..."
"Yi mini shiru mahaukaciya! Kin yi laifi kina yi wa mutane surutun banza."
Ya yi maganar a ƙufule yayin da ya tallafo Zee tana layi tare da ɗaga kanta sama yana bubbuga goshinta
cike da zummar jinin ya tsaya idan ma haɓo ne ta yi. Suna ƙoƙarin ficewa daga falon Zee tana gunjin kuka a
jikinsa aka turo ƙofar falon.
Dam-dam! Ƙirjin Jamal ya buga, saboda firgicin ganin Hajiya a irin wannan lokacin. Ita kanta Minal sai da
ƙirjinta ya buga, jikinta yana rawa ta faɗa ɗakinta da sassarfa. Da hanzari ta sauya kayan jikinta da wata
doguwar riga ta ɗaura ɗankakwalinta a ka ta fito. Saboda sautin Hajiyar da ke tashi a sama tana faɗa ko'ina
ana jin ta.
Amma mamakin ganin shu rungume da Zee bai hana ta isa falon ta zauna ba. Fuskarta a yamutse ta
dinga bin su da kallo ɗaya bayan ɗaya. don ganin ta ya yi saurin sakin Zee ya rakuɓe gefe yana muzurai.
Zee kuma ƙasa ta zube saboda ƙafafuwanta sun yi sanyin da ba za su ɗauki gangar jikinta ba. Don ganin
Hajiyar ya sa ta shiga tashin hankalin da ya saukar mata kyarmar jiki, ta shiga haɗiyar yawu tare da ƙara
sautin kukanta wiwi.
"Macen banza har a cikin gidanka Jamal?"
Hajiya ta yi maganar cikin tsurewa, tsabar mamakin ganin abin da idonta ya yi tozali da shi. "Ashe Allah Ya
kawo ni ne rabon na ganar wa kaina irin ta'asar da kake aikatawa ba tare da na sani b..."
"Wallahi Hajiya sau ɗaya ne...kuma yau ne kawai kin ga jakarta ma gida za ta je yanz..."
Jamal ya yi maganar a ruɗe saboda ta gama ganin komai, kuma bai san da wace kalma zai musa mata ba.
Kafin ta katse shi da salati tana tafa hannu alamun ya gama kashe ta da wani mamakin.
"Ana ganin ta fasa mini baki da hanci amma ba za a yi ta kaina b...to wallahi idan na mutu duk sai kowa
ya yi bayani."
Zee ta yi maganar tana ƙara bajewa ƙasa tare ƙara sautin kukanta cikin matsanancin hali ta koma birgima.
"Ke daƙiƙiyar ina ce da za ki zo gidan matar aure da mijinta ki yi tsammanin za ki fita lafiya lau? To bari ki
ji ko kashe ki aka yi ke kika jawo kuma babu wanda zai kai ki asibiti a cikin mu. Ki tashi ki ja jakar kayanki ki
fice tun kafin na haɗa ki da 'yan sanda su tafi da ke wallahi!"
Hajiya ta ƙare maganar cikin matsanancin fushi alamun ta kai maƙurar ɓacin rai. Zee ta miƙe da ƙyar cikin
tashin hankali tana layi ta ja jakarta kamar ta kifa da tangaɗi ta fice ta ƙofar falon. Jamal ya bi bayanta da
niyyar rage mata hanya ganin halin da take ciki.
"Kai kuma ina za ka je?"
Hajiya ta katsa masa tsawa cikin haɗe guyska ta jefo masa tambayar. Muryarsa tana rawa ya ce,
"Rufe ƙofar zan yi idan ta fice."
"Rufe ka zo."
Ta sake magana a taƙaice kafin ta mayar da kallonta a kan Minal da ke rakuɓe jikin kujera tamkar ruwa ya
ci ta.
"Ke kuma..."
Dam ƙirjin Minal ya sake bugawa, saboda ta tsorata matuƙa da ganin yanayin Hajiyar.
"Allah ya yi miki albarka."
Wani sanyin daɗi ya ziyarci zuciyar Minal, saboda ta yi tsammanin ita ma za ta juye mata fushin a kai
ganin yadda ta ɗauki zafi sosai.
"Hakan da kika yi ya yi daidai. Gobe ma duk macen da ya sake kawo miki a cikin gidan nan ki yi kaca-kaca
da ita ni na ce! Don babu hukumar da za ta kama ki da laifin dukan macen da duk kika kama da mijinki a
cikin gidan aurenki. Saboda babu babban raini da wulaƙanci kamar namiji ya kawo wata mace a gidansa ko
da matarsa ba ta gidan ballantana tana ciki. Don haka wallah Jamal duk yarinyar da ka sake ɗaukowa ka
kawo ta a cikin gidan nan naka sai na nuna maka haihuwar ka aka yi ba kai ka haifo kanka ba!"
Shiru ya ratsa falon saboda babu wanda ya iya motsin kirki daga shi har Minal ɗin. A lokacin Hajiyar ta
sake cewa,
"Amina kuma, tun da ba ka son ta; ka shiga ɗaki ka rubuto mini takardar sakinta ka ba ni yanzun nan! Tun
da ka isa da kanka sai ka yi duk abin da kake so! Don ba zan juri ganin kana wulaƙanta 'yar mutane a banza
ba. Idan ba ka so akwai dubunka waɗanda ma suka fi ka a komai za su so ta kuma su yi zaman aure na
tsakani da Allah da ita. Idan ka sauwaƙe mata sai ka je ga ka ga matan banzan da ka fi so a kant...."
"Ni dai don Allah ki yi haƙuri Hajiya. Na san na yi kuskure kuma ba zan sake makamancinsa ba. Da ma na
yi ne kawai don na gwada ta."
Wani kallo ta yi masa kafin ta yi guntun tsaki ta sake cewa, "Gwaji? Da irin wannan rashin mutuncin kake
gwada matarka? Yanzu idan da ita ce ta gwada kawo wani a cikin gidanka za ka kalli hakan a matsayin
gwajin? A hir ɗin ka Jamal! Wallahi ina jiye maka tsoron ɓata rawarka da tsalle a kan irin riƙon da kake
ƙoƙarin yi wa Amina."
"Don Allah Hajiya ki yi haƙur..."
"Sai fa ka sake ta yanzun nan ba sai anjima b..."
"Wallahi Hajiya ba zan iya tsallake umarninki ba. Amma ki yi haƙuri zan zauna da Amina tun da kina s..."
Wani kallo ta wurga masa wanda ya saka shi datse maganarsa. Cikin sauri ta miƙe tare da gyara zaman
mayafinta idonta a kan Aminar ta ce,
"Tashi ɗauko mayafinki mu je! Duk ranar da shi ya so auren da ke sai ki dawo gidan."
"To, Hajiya."
Amina ta amsa cikin sanyin jiki da na murya tare da tashi ta nufi ɗakinta. Kafin ta fito Jamal ya isa gaban
Hajiya ya durƙusa gwiwa biyu yana cewa,
"Ki ba ni dama ta ƙarshe Hajiya. In sha Allahu zan gyara duk abin da na ɓata da hannuna."
Banza ta yi da shi, duk da tausayin sa ya sa ta zubar da ƙwalla. Kuma ta so yin jarumtar hana hawaye
zuwa cikin idonta. Amma ƙoƙarinta bai hana ƙwallar zuba ba. Hakan ya sa Amina tana fitowa ta ja
hannunta suka fice. Ya biyo bayansu yana magiya amma ko waige ba ta yi ba ballantana ta tsaya sauraron
sa har suka fita harabar gidan, bakin motar da aka kawo Hajiyar suka isa. Mazaunin baya ta buɗe mata
sannan ta ce,
"Ina kayanki? Idan mun je ba yanzu za ki dawo ba, ki koma duk abin da kika san kina buƙatarsa ki ɗauko
shi mu je, ina jiran ki."
DAKAN ƊAKA..Complete document book 1-2. Mai buƙata 9032685442 Opay. Shaidar biya ta nan
08022014771.
10 February zan sake shi da yardar Allah.
D. AUTA CE
✍🏼
D. AUTA CE ✍️
[2/20, 22:02] Hadiza D. Auta: *FANSAR ƘAUNA!*
*HADIZA D. AUTA*
*AREWABOOKS: Princessdija.*
https://chat.whatsapp.com/Edh59w1Jcgk799uIkP0CFa
*LAMBA SHA SHIDA.*
Minal ta yi gaba da sassarfa a bisa umarnin Hajiyar na ɗauko kayanta. Caraf ta tuna jakarta ma tana cikin
boot ɗin motar Jamal. Cikin sauri ta dawo ta gefen da Jamal yake tsaye yana muzurai don ya