Author : HADIZA D. AUTA Category : African Stories & Novels
kalar murya
ya ce, "Kada ka shanye tunaninka, yana da kyau a matsayinka na namiji ka dinga aiki da hankali kafin ka
aiwatar da komai. Saboda mahaifiya ba abin wasa ba ce, kada zuciya ta ɗebe ka ka aikata abin da Allah zai
yi fushi da kai a sanadin bijire mata."
Sai da ya ɗan tsahirta bayan shirun sakonnin da ya ratsa bayan dire maganarsa ya sake cewa, "Ban hana
ka mayar da A'isha gida ba, amma ka ji tsoron Allah, ka tuna cewa marainiya ce kuma amana ce a
hannunmu gabaɗaya. Sannan ka yi imani a kan wani ba ya auren matar da ba tasa ba, duk tsanani idan
matarka babu mai hana ka aure ta idan lokacin ya buga. Don haka ka daina garaje, kuma ka nemo hanyar
sasanta kanka da Hajiya cikin sauƙi har ta aminc..."
Shigowar Innarmu cikin gidan ya sa Baban yin shiru kowa ya mayar da hankalinsa a kanta. Don tun kafin
ta ƙaraso ta fara maganganun da ke nuna a shirye take da yin komai aka shiga gonar Amina. Tsam Jamal ya
miƙe tare da bai wa Nur umarnin ta tashi su je, Baban ma ya miƙe fuskarsa a cure yana jaddada masa Nur
amana ce a wurin su. Jamal bai ce komai ba ya yi gaba ba tare da ya kalli Innarmu ba ballantana ya gaishe
ta.
Nur ta ƙi motsawa daga inda take saboda ta gama kaiwa maƙura a kan halin da take ciki. Saboda
zantukan Jamal sun taɓa ta, sannan yunkurin kai ta gida ya saka ta jin wani faɗuwar gaba, duk da a ranta
tana buƙatar hakan ko don wanke kanta daga laifin da za ta aikata idan aka tabbatar ba ta nan. Sai da
Baban ya yi magana sannan ta miƙe cikin sanyin jiki ta bi bayan su, yayin da zantukan Innarmu suka raka ta
da cewa,
"Sum-sum da ita baƙar munafuka wallahi sai na nuna miki ke ƙaramar 'yar duniya ce. Ban da zalunci kin
gama ƙulla abu daga baya ki dawo kwancewa saboda mugunta. To dole ne ki bar Amina da mijinta! Don ko
za ki mutu ba zai taɓa auren ki ba!"
Babu wanda ya bi ta kanta har suka fita ƙofar gidan, Nur ta durƙushe a gaban Baban tana wani irin kuka har
muryarta tana sarƙewa. Baban Amina ya dafa kanta yana faɗin,
"Ki yi haƙuri A'isha, Allah zai zamo gatanki a duk inda kike."
Ya ƙare maganar tare da ɗaga ta sama ya ja hannunta zuwa bakin motar, Jamal ya yi hanzarin buɗe mata
gaban motar, amma ta ƙi shiga kamar yadda ya so ta buɗe baya ta faɗa tana ci gaba da rera kukanta. Ƙur
da ido Jamal ya yi mata tsawon sakonni kafin ya zagaya ya zauna cikin sauri fuskarsa a cure. Yana ƙoƙarin
tayar da motar adaidaita sahu ta kunno kai a cikin layin, sai da ya ja gefe motar Jamal ta wuce sannan ya
isa ƙofar gidan ya tsaya. Kan Amina a duƙe tana ajiyar zuciya wata bayan wata kamar an ba ta umarni ta
ɗago kanta. Ƙirjinta ya shiga bugawa babu ƙaƙƙautawa ganin motar Jamal tana fita daga cikin layin nasu.
Mamaki fal zuciyarta ta fito cikin adaidaita sahun tana ƙoƙarin shigewa gidan cikin sassarfa, saboda
zuciyarta cike take fal da son sanin abin da ya kawo shi gidansu, bayan ya gama tozarta rayuwarta.
"Malama ba ki sallame ni ba fa!"
Mai adaidaita sahun ya yi magana, sai a lokacin Amina ta tuna babu ko ficika a hannunta, asali ma ko jakar
hannu ba ta ɗauko ba ballantana jakar kayanta. Gidan ta shige ko waigensa ba ta yi ba, haushi hakan ya
sake ɗaga murya yana faɗin,
"Malama idan kin shiga ki aiko mini kuɗin sauri nake yi."
Ya yi maganar ba tare da ya kashe adaidata sahun ba, tsabar saurin a biya shi ya ƙara gaba.
Next page
FANSAR ƘAUNA
31.
Babu sallama Amina ta faɗa gidan, kai-tsaye ta shige ɗakin Innarmu ganin ba ta tsakiyar gidan. Zumbur
Innarmu ta yi cike da kaɗuwa tana ƙoƙarin ɓoye abin da ke hannunta. Fahimtar Amina ce ta shigo ba
Babansu da ta yi tsammani ba; hakan ya ta sa ta sauke ajiyar zuciya dafe da ƙirjinta da ke bugawa fal-fal ta
ce,
"Ke ko me ya kawo ki gidan nan a a wannan lokacin? Kin wani shigo babu sallama haka kawai kin ba ni
tsoro!"
Zama Amina ta yi a bakin gado duk da tana jin sautin odar da mai adaidaita sahun yake ta zubawa
alamun ita yake jira. Ta rushe da wani zakin kuka saboda rage nauyin da take ji a ƙirjinta.
"Ke! Dakata! Dakata don Allah! Shin kin zo ne don ki tara mini jama'a ko kin zo don ki ƙara mini wata
damuwa a kan wadda nake ciki?" Ba ta jira amsarta ba idonta a zare ta ci gaba da cewa,
"Sawunki a likkafa ki tashi ki koma gidan mijinki tun kafin Babanku ya dawo gidan nan ya tarar da ke.
Saboda a kan aurenki har barazana ya yi mini da saki muddin na yi sanadin mutuwar aurenki har da faɗin
bakin aurena. Uwa-uba ni kaina ba zan so a ce aurenki ya mutu ba har sai kin haifa masa ɗa ko ɗiya a
gidansa, ko don na ga ƙarshen iskanci da rashin mutuncin da ake ƙoƙarin yi mana daga ni har k..."
"Assalamu alaikum!"
Sallamar da suka jiyo a ƙofar gidan ta sa Innarmu yin shiru tare da ficewa daga ɗaƙin cikin sauri ta isa ƙofar
gidan tana gyara zaman kallabin da ta ɗaura, wanda ya faɗo ƙasa garin duƙawa saka takalmi tsabar firgici
da fargaban da take ciki a lokaci ɗaya.
"Kuɗina za a ba ni, sauri nake yi akwai inda zan je tun ɗazu ake jira n.."
"Idan ka saka haƙuri tare da ita ma za ku koma, don ita ma ba zama ta zo yi b..." Innarmu ta yi maganar
cikin sanyin jiki, tare da juyawa gefe jikinta yana rawa ta cusa hannu cikin aljihun bujenta. Kuɗi ta ciro tana
haɗa kansu ba tare da tsayawa tantance nawa ne ba ta miƙa masa, kansa a sama hannunsa a aljihu alamun
ya gama yin fushi a cikin fusata ya ce,
"Gaskiya ni sauri nake yi a dai biya ni na wuce! Ba zan iya komawa da ita b.."
Karaf idanuwansa suka hango masa dubu-dubu da ɗari biyar-biyar bayan ɗari biyu da naira ɗarin da yake
hange. Babu shiri ya sauya fuskarsa daga fushi zuwa murmushi ya karɓe kuɗin tare da yin gaba yana cewa,
"Ki ce ta fito na sauke ta jira na ake yi."
Innarmu ta koma ci shi ya shige cikin adaidatar sahun zuciyarsa cike da jin daɗin haɗuwa da irin Innarmu.
Saboda ya gama fahimtar a ruɗe take kuma ba ta tantance adadin abin da ta miƙa masa ba. Shi ma baki-
alaikum ya soke kuɗin aljihu, cikin rawar jiki ya dinga faɗin,
"Ta fito fa! Kada kada ta ɓata mini lokaci."
Hakan ya sa tun kafin Innarmu ta isa bakin ɗakin ta shiga ƙwala wa Amina kira tana faɗin, "Fito! Fito ke
kaɗai yake jira don ya ce sauri yake yi."
Turus Innarmu ta yi ganin Amina kwance a kan gado ta juya baya tana rera wani kalar kukan da ya sa
Innarmu isa bakin gadon cikin sassarfa tana faɗin,
"Ko kukan jini kike yi wallahi sai kin koma gidan mijinki ko za ki mutu ƙarewar kuka da ruwan hawaye! Za
ki tashi ki je ya sauke ki cikin mutunci ko sai na haɗa miki da duka za ki fahimci da gaske nake y...?"
Takaicin Amina ya ƙara yawa, saboda furucin da Innarmu ta yi a kan sharaɗin da Babansu ya gindaya
mata a kan mutuwar auren nata; shi ne abin da ya ƙara lalata mata kuzarin bayyana rashin mutuncin da
Jamal ya shuka mata. A ranta ta kitsa ba za ta bayyana mata sakin ba, gudun ita ma Babansu ya aiwatar da
abin da ya shirya a kanta. Duk da babu hannunta a cikin sakin ballantana dalilin da ya kawo shi. Amma ba
za ta so fallasuwar sakin ba gudun abin da ba ta fata ya kasance a tsakanin iyayenta. Hakan ya sa ta sauko
daga kan gadon salun-alun da shessheka tana ajiyar zuciya ta ce,
"Don Allah ki bar ni na zauna ko iya kwana biyu ne a gidan nan... Innarmu...zu...zu...zuciyata wani irin zafi
take y... zan..zann..iya mutuwa idan na koma gidansa a wannan lokacin."
Yanayin yadda ta yi maganar muryarta tana sarƙewa dafe da ƙirji; ba ƙaramin karya zuciyar Innarmu ta yi
ba, amma hakan bai hana ta riƙo hannunta cikin zallar tausayin ta ta ce ba,
"Ki yi haƙuri Amina, komai da kike gani muƙaddari ne daga Allah. Yanzu haka daga wurin Malam Shazaƙi
na fito, kuma ya tabbatar mini aure tsakanin mininki da A'isha babu shi har abada. Kuma ke da mijinki
mutu ka raba takalmin kaza mutuwa ce za ta raba ku. Yanzu haka kin ga abubuwan da ya ba ni...ya ce idan
kika yi komai a yadda yake uwarsa ma sai kin so ya kula ta ballantana A'isha, wadda idan ban da tsoron
Allah a dare ɗaya zan sa a kawar da ita kowa ya hut..."
"Innarmu..." Amina ta yi maganar cikin wata murya saboda ƙirjinta da ke dakan luguden uku-uku a kan
furucinta na ƙarshe. Tana ƙoƙarin sake yin magana Innarmu ta damƙa mata layu da magungunan da ta
ɗaure a cikin leda tana faɗin,
"Yi sauri ki tafi, gobe idan na samu dama zan zo da kaina na nuna miki duk yadda za ki yi amfani da su
kamar yadda malamin ya faɗa mini. Don haka ki kwantar da hankalinki A'isha ba ta isa ta saka mu jin kunya
biyu ba."
Amina ta fice daga ɗakin jiri yana kwasar ta ta fice gidan Innarmu tana rarrashin ta, da kanta ta shigar da
ita adaidaita sahun duk da ƙwallar da take sharewa tare da shessheka. Saboda sun tarar har ya kunna
adaidaitasahun da niyyar tafiyarsa, don ya gama kitsa wa ransa cinye kuɗin duka a matsayin ladar zaman
jiran da ya yi tsawon lokaci. Har adaidaitasahun ta fice daga layin ta hau kan titi Innarmu ba ta bar kallon
su ba, zuciyarta cike da tunanin hanyoyin da za ta bi Amina ta zauna lafiya a gidan Jamal, sannan ta yi
mulki irin wanda babu macen da za ta kai ta ballantana a ce ta fi ta wurin sa. Ta yadda ba zai ji maganar
kowa ba sai tata, kuma ba zai ga kowace mace a cikin idonsa idan ba ita ba.
Amina kam sautin kukanta ya ƙaru a daidai lokacin da ta ga an kama hanyar mayar da ita gidan Jamal,
saboda tuna sakin wulaƙancin da ya yi mata bayan kishin Nur da ke cin ranta. Don a duk wani motsin da ta
yi sai ta hango su rungume da juna suna faɗa wa juna kalaman soyayya. Idanuwanta a runtse suka isa ƙofar
gidan tana ajiyar zuciyar kuka kala-kala. Ƙafafuwanta suna harɗewa ta isa bakin ƙofar gate ta ƙwanƙwasa,
sai da ta kwashi minti biyar zuwa shida tana bubbuga gidan kafin Baba maigadi ya buɗe mata, bayan ya
leƙa ta ƙaramar ƙofa ya hango ta tsaye tana ajiyar zuciya da zuƙar majinar kuka.
"Ranki ya daɗe sannu da dawowa."
Ya yi maganar cikin wata murya, saboda har ransa ya ji tausayin ganin yanayinta da halin da take ciki.
Hannu kawai ta ɗaga masa ta yi gaba jiri yana ɗibar ta, don ƙafafuwanta sun gama yin sanyi da ƙyar ta ja su
zuwa sama kamar ta kifa.
Ikon Allah ne kawai ya kai ta lafiya, idanuwanta a rufe ta faɗa kujera tare da fashewa da wani sabon kuka
cikin shaƙaƙƙiyar murya, saboda tuno Jamal da sakin da ya yi mata a gaban Hajiyarsa babu shayin komai,
sannan da tafiyar da ya yi ba tare da ya tausaya wa halin da za ta shiga ba idan ya guje ta.
'Ko dai Zulaiha ce ta raba ni da shi?'
Tambayar da ta yi wa kanta kenan a zuciya bayan ta tsahirta da rera kukan da take yi, duk da hawaye bai
bar idanuwanta ba har lokacin.
'Idan ma ita ce ribar me za ta ci idan ta raba ku?'
Wani yanki na zuciyarta ya ba ta amsa kai-tsaye, hakan ya sa ta yi tagumi kafin ta cira kai ta hango baƙar
ledar da Innarmu ta haɗo ta da ita. Cikin sanyin jiki ta jawo ledar ta buɗe ƙirjinta yana bugawa, saboda
ganin layoyin da ke ciki sun tuno mata ɗaya daga cikin nasohohin da Babansu yake yi musu ita da ƙannenta
kodayaushe.
'Ko da wasa kada ku bar zuciya ta ingiza ku aikata shirka, wai saboda matsin rayuwa ko wani sauyin
yanayi. Don babu abin da yake tabbace face gaskiya da ikon Allah, don haka ku dogara ga Ubangiji yana
sane da duk halin da muke ciki ba zai taɓa bari mu wulaƙanta ba.'
Maganar Baban ta saka ta jin wani sanyi a gefen zuciyarta, bayan dakiyar da ta zo mata tamkar an yi
mata allurar nutsuwa. Saboda tuno lokacin da ya yi maganar da dalilin da ya jawo nasihar. Kasancewar
kasuwa ta ja masa baya a wani lokaci, abinci ma da ƙyar suke samun na jefawa a bakin salati. Sai Innarmu
ta yi wankau da surfe sannan suke kacancana abin da ya samu. Babansu kuma idan ya samo waje ya ci,
idan ma bai samo ba sai dai ya yi kwana da yunwarsa, don ko ya tarar da abin ci a gidan ba ya ci. A
cewarsa bai ba su ba kuma ba zai yiwu ya cinye musu ba.
Wannan halin matsin da suka shiga ya sa Innarmu ta ba shi shawarar ya tafi wurin malamai su duba masa
matsalarsa, kada a ce wani ne ya saka masa hannu bai sani ba, ganin ɗan abin da yake samu ya tsaya
gabaɗaya sai wahala suke sha.
Kallo ya bi ta da shi tsawon sakonni kamar ba zai yi magana, sai can ya sauke ajiyar zuciya ya ce,
"Duk wanda bai dogara a kan Allah ne mai yi kuma shi yake hanawa ba ya ji haushin rayuwarsa. Ai da na
je gun wani boka ko Malam; gara na duƙufa faɗa wa Allah damuwata don ba gata suka fi ni gare shi ba.
Sannan babu shamakin da ya raba tsakanina da shi, kodayaushe yana tare da ni kuma ya fi kowa sanin
halin da nake cik.."
Innarmu ta katse shi cikin fusata riƙe da tagumi tana ƙura masa kallo da taɓaryar da take daka a hannunta
tana cewa, "Oh Allah! Na jawo wa kaina abin magana daga shawara! Kai kenan kullum idan aka nuna maka
hanya sai ka nuna ka fi kowa sanin Allah. To ka zauna ai, ni dai na san manyan malaman da suka shahara a
duniya ma ana yi musu asiri ya kama s..."
"Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ma an yi masa asiri ya kama shi. Ni ma ban ce ba zai iya kama
ni ba, amma dai ba zan je wurin kowa da sunan neman taimako ba don Allah Ya yi mini wannan jarabawa."
Baban ya amsa mata cikin faɗan shi ma yana ƙwala wa Amina kira tare da sauran yaransu cikin ɗaga
murya, saboda tunaninsa ya tafi tsoron kada Innarmu ta cusa wa yaran nasa irin ra'ayinta. A nan ne ya yi
musu nasihohin, waɗanda bai bari suka tashi ba har sai da ya tabbatar suna kan koyarwar da yake yi musu
ba irin wadda Innarmu take bi da su ba.
"Ya Allah!"
Furucin Amina kenan bayan ta gama nazarin shuɗaɗɗun abubuwa da kalolin rikici da diramomin da ake yi
a gidansu. 'Tabbas ba zan bari imanina ya lalace a sanadin wannan matsalar ba. Gara kowane irin mataki
da wanda Innarmu take so na bi.'
Daga haka ta mayar da layoyin ta ƙulle ledar, tare da ƙulle zuciyarta a kan biye wa sabgar Innarmu,
amma ta kitsa wa zuciyarta sai ta nuna wa Nur ita ba kowa ba ce a wurin Jamal face abokiya, don ba za ta
taɓa zama matar aurensa ba sai dai a yi mutuwar kasko kowa ya rasa.
Kai-tsaye ta jawo waya ta kira Gwaggo Salame. Kira ɗaya biyu ta ɗaga suka gaisa babu yabo babu fallasa,
kafin Aminar ta sauke ajiyar zuciya ta ce,
"Gwaggo kina da labarin ya sake ni?"
"Na ji a bakin Hajiyarsa, ta kira ni ta ce don Allah na ba Babanku haƙuri, kuma ta nemi alfarmar ki zauna
gidan har ki kammala idda. A bisa hakan ni ma na ga dacewar zamanki gidan da barin maganar a
tsakaninmu. Wataƙila kafin ki gama iddar mijinki ya dawo hankalinsa ku sasanta kanku."
Shiru Amina ta yi na sakonni kafin ta sauke wata ajiyar zuciya ta ce, "Don Allah ko Babanmu kada ki bari
ya sani Gwagg..."
"Haba-haba dai...ai ban da niyyar buɗa zancen ga kowa, shi ya sa a inda na ji maganar a nan na bar ta. Ke
ma saboda kin nemo ni ya sa na nuna miki na sani. Allah dai ya shiga lamarin ya kawo sasancinku kusa
kafin lokacin. Sai kin yi haƙuri, ki kalli komai a matsayin ba komai ba, da sannu za ki ga ribar biyayyar da
kike yi. Allah Ya yi miki albarka."
"Amin Gwaggo."
Daga haka suka kai ƙarshen maganar suka faɗa hirar Innarmu, inda Aminar take roƙon ta yi wa Baban
magana su rage zaman doya da manjan da suke yi koyaushe. Saboda tun da ta yi wayo ta fahimci babu
jituwa tsakanin Babansu da Innarmu, kuma abin yana damun ta sosai sannan tana jin takaicin 'yar tsamar
da suke yi. Sun jima suna tattaunawa kafin su yi sallama a lokacin da katin wayar ya fara sanarwar ya kusa
ƙarewa.
Next page✍️
FANSAR ƘAUNA
32.
***
Jamal tafiya kawai yake yi a kan titi cike da ƙarfin hali da jarumta irin ta maza. Amma a ransa da gaɓɓan
jikinsa gabaɗaya ya yi rauni. Don kukan da Nur take yi wiwi ba ƙaramin cusa masa wata sabuwar damuwa
ya yi ba. A ransa yana jin kamar ya yi parking har sai ta gama kukan sannan ya ci gaba da tafiyar, don
bakinsa ya yi nauyin da ba zai iya rarrashin ta ba ballantana ya ba ta haƙuri.
Sannan ya ƙi bin umarnin zuciyarsa da ke nuna masa ya sauka gefen titin saboda abin da yake ji ana yi
masa a cikin kansa, har sai da kukan ya kai matakin da ƙwaƙwalwarsa ta fara juyawa, ganin sa ya yi rauni;
sannan ya yi magana cikin wata