Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

NUR FIRDAUS Imanin 'Ya By Anne-Aurora

Author :  Anne-Aurora Category :  African Stories & Novels

Chapter   8 / 52

21K to 24K   out of 155.7K words

haka nakeji huuhhh huhhhhh.





kansa a mugun daure cikin rashin jindadin kananan maganganuntan yasauko kasa da guntun wandonsa ahannu baiko kalleta ba sabida wani irin harararsa takey da tsananin baqin cikinsa aranta, da har zai yi magana ta wurga masa wani kallo cikin dakamai tsawa tareda tsananin jin haushinshi tatsaresa,



"sadaat kafita kawai. banason nagaya maka wata maganar da harka mutu bazaka manta ba "meye amfanin auran dana maka da haseena ehh? gindinta kawai nace kaje kaci cant u keep her away from all this??? sam bakay amfani da brain dinka ba, da ace ka iya takunka da tuni ka iya daukemin hanklinta daga harkan siyasan nan haba da Allah sai kace ba namijin dana raineshi da hannuna ba?..



da wani irin zzafan frustration take masa maganan cikin masifa tana diri sosai duk

kaikake jawomin koma baya a harkan siyasata, sadaat u cause dis mtsss sam baka cika namiji ba, i gave one simple job to do.. marry dat bitch and screw her, amma haryanxu nadaman aura maka haseena sharif kawai nakeyi, dat evil slut haseena sharif is getting on my nerves.. toh wallh dukanku daga kai har ita baku san wuta ba saikun taka dani farida bala ake ja..





sosai ransa yay baqi kirin da yadda take nuna masa kamar bai taba mata kokri ba amma baice mata komi ba yagama saka kayansa zaifita tawani rikeshi tanamai balla masa wasu munanan harara



cike da takaici ta dau waya tawurga masa ajikinsa tana mai cewa bangane ina magana kamin shiru ga yar iskanka ko?



ransa a harde yace mummy ni club zanje



wani irin mari takai masa abazata "wato ma zakaje club kasha giya ni ka lalalata min komi ko, toh babu inda zaka, u will "fix dis.. ga waya nan ka kira dukka yan jaridun mu a kano kabasu kudi konawa ne sumin aiki mekyau awajen taron da haseena zatayi yanxu, sumata wasu irin munanan tambayoyin da zai jawo hanklin jama'a akan makricinta..



karbar wayar yay adan fixge baice mata komi ba yafita dashi yana kukkuni tabi bayansa da wani irin kallo mai zafi me tafe da takaici



...wani tukukin tsaki taja ta bude drawer ta dauko hodar cocaine ta zuba kadan akan table tare da zubewa agabansa ahankli ta fara shaka saida taji yaje har cikin kwakwarlta





******

Ata daya bangaren daga mallam Aminu kano intl Airpot kano da misalin karfe 8:00 am dede nasafe nan take filin jirgin ya cika da hayaniyar manya manyan yan jarida da masu watsa labarai

ayayinda da jirgi me dauke da tawagar jaijtacciyar yar gwagwarmarya Mrs. Haseena Sharif wacce takasance wata gwarxuwa kuma shahararriyar mai fafutukar kare hakkin jama'a ta bayyana a garin kano domin zantar da live show a wani shiri mai taken "ina Adalci Ga Mata da Yara??..



live show ne da ake iya watsawa kai tsaye a gidan kowanne talabijin afadin nigeria daga bakin mai ita, wanda Taron ya karkatane a kan batun cin zarafin jinsi musmn na mata (GBV) akan wani sabon al'amari mai tayar da hankali dayake faruwa a kano state kai tsaye



yanxu lokaci ne na ganganmin yaqin siyasa dan haka mrs haseena shareef ta jajirce sosai wajen fidda salo salo na makircin siyasa tare da ganin tasamu shigar da sunan uwar dakinta hajiya mariam kanem shehuri me neman kujerar takarar ministan jinkai nakasa gabaki daya a xukatan talakawa batare da ta nuna a haka a fili ba.





tunkafin jirginsu daya taho dasu daga abuja yasauka a kano tuni manyan jami'ai data gayyata daga hukumomin kare haqqin dan adam kamarsu amnesty, Unicef, kano state ministry of women children and disabled, Citad, NHRC, IRC da kuma UNFPA ta kano duk suka hallaro.



saukowar mrs haseena sharif kadai ma abun kallo ne dan atsakanin kyaun sura da iya daukar wanka tare da confidence din dake tafe da mrs haseena bansan mezance yafi daukar hankalin jama'a ba.



dake hukamar human right na America ne ta dau nauyin shirin yasa tataho har garin kano da english wear wato peach versace suits dinta daya wani irin mata masifar kyau kai bazakace takai maka shekaru arba'ain da shida a duniya ba. saukarta ke da wuya kenan jami'ai tare da yan jaridu kala kala suka yanyaneta kowa na kkrin tofa iyakan albarkacin bakinsa akan shirin da tazo zantarwa wanda abune wanda basu sabayi a kano sosai ba.





Cikin nutsuwa amma da takaici Mrs Haseena sheriff ta fara jawabi tana cewa "kowa ya kwantar da hanklinsa, Yau mun zo nan ne domin tattauna wani abin da nasan zai girgiza zukatan al'umma. munsami labari cewa Yarinya 'yar shekara 13 mai suna Ummi ta fuskanci abin da babu wata yarinya da ya kamata ta fuskanta a rayuwarta. Wannan yarinyar an zalunce ta, an karya mata zuciya, kuma mafi muni, mahaifinta ne ya aikata wannan abin kunya...dani da mabiyana zamuyi iya bqin kkrinmu domin muga mun ceto ummi daga wann ukubar.



tambya ake jefa mata kota ina amma Mrs. Haseena bata kula ba ta cigaba da magana da karfi da kuma karfin zuciya Mun taho kano ne don tattauna yadda za mu dakatar da irin wannan zalunci a cikin al'umma. Ba zamu yarda wannan abin kunya ya zama ruwan dare ga mata ba.



sauran manyan mata mabiyanta da suke gudanar da aikin social activist din tare nan suka fara mata amshi in atare suna daga muryoyi.



wanda zuwansun sosai ya mugun daukar hankalin jama'a kai tsaye ita da tawagarta da jamian suka kama hanya zuwa wani anguwa dake cikin wata karamar hukuma a kano inda akaje har gidansu ummin aka fito da ita sarari snn aka fara fitar da bayanai kai tsaye daga bakinta, tare gabatar da shaidun abin da Ummi ta fuskanta live da kuma yadda za a dauki mataki kan mahaifinta daya mata fyaden shima wanda yanzu haka yana hannun hukuma...



Duk abunda akeyi kai tsaye ake nunasa agidan talabijin honourable farida bala ta gama kilewa da kwaya tana kan kallon haseena a tv tana kan dura mata ashariya manya manya.





misalin karfe 2 na rana Daga gidansu ummi aka wuce Dakin taron dake ministry of women children and disable na kano state wanda yana cike da jajirtaccun 'yan jarida, kowannensu dauke da littattafan rubutu, na'urorin daukar sauti, da kyamarori, suna jiran su tambayi Mrs. Haseena Sharif tambayoyi masu zafi. A gefenta, Ummi na zaune cikin nutsuwa amma da tsoro, tana makale da hannun Mrs. Haseena lkcin ko kanta bata iya dagawa





Bayan Mrs. Haseena ta kammala jawabin ta na farko mai karfi, nan take wani sanannen dan jarida mai suna Ibrahim Yusuf ya fara magana cikin muryar tambaya wanda daga ganinsa kasan shima hayansa akayi yace "ranki dade Mrs. hasena Sharif, kina bayyana wannan lamarin ne a matsayin fafutukar kare hakkin yara, ko kuwa wani kokari ne don inganta yakin neman zaben shugabar ki, Hajiya Mariam Kanem Shehuri, wanda ke neman kujerar ministar Abuja?"



Mrs. Haseena ta gyara zaman ta da murmushi sannan ta dubeshi da fuskar dake nuna karfin hali. tace " kusaurara, zan yi magana a sarari. Wannan batu na Ummi ba ya da alaka da kowanne irin tsari na siyasa. Batun kare yara daga zalunci da cin zarafi wajibi ne da ya wuce kowanne tsarin siyasa. Ko da kuwa ba ni tare da Hajiya Mariam Kanem Shehuri, zan tsaya tsayin daka don ganin an yi wa Ummi adalci."



Wata yar jaridar rataye da id card ansaka suna Fatima ajiki tadaga hannu tana tambaya cikin muryar zargi.. "hajiya haseena Amma akwai wata tambaya mai mahimmanci, nace, Me ya sa sai yanzu ne aka fara watsa wannan maganar kai tsaye, alhali irin wannan cin zarafi ya dade yana faruwa? Shin kin yi shiru ne har sai lokacin ya dace don amfanin yakin neman zabe?"



Mrs. Haseena ta yi ajiyar zuciya,sannan ta ce cikin natsuwa

"malama, wannan abu ya shafi zuciyar kowa. Babu lokacin da ya fi dacewa don nuna gaskiya da neman adalci. Ba zan iya zura ido na ga yara kamar Ummi suna fuskantar irin wannan zalunci ba. Lokacinmu ne yanzu don mu tashi tsaye."



nan wani babban dan jarida frm no where ya bullo mai suna Ahmed yayi magana cikin harshe mai zafi da karsashi kai tsaye ya miqe abainar jama'a yahau cewa "Amma gaskiya akwai babban shakku ga gudurinku Shin kina ganin idan ba Hajiya Mariam ce ke takara ba, har yanzu ke zaki dage kan wannan al'amari haka? Kila kawai kuna amfani da halin Ummi ne don cimma burin siyasarku."



Mrs. Haseena ta dube shi kai tsaye tana dan murmushi mai nuna jarumta tareda nuna fahimtar inda ya dosa

tariga ta goge a wajen iya toshe caccaka da kuma farmaki daga yan jaridun dake aiki wa makiyanta, tana kan murmushin tace dan jarida kenan shin da gaske kake kayi mamakin irin wannan zargi?? Ummi ba wata alamar siyasa ba ce, ita fa mutum ce, yarinya ce da aka zalunta. Wannan batun ya shafi rayuwarta, ba wani yakin neman zabe ba. Zan yi kowane irin aiki don tabbatar da cewa ta sami adalci, ba tare da la akari da wanda ya tsaya tare da ni ko wanda ya saba da ni ba."



Sai kuma 'yan jaridar suka fara magana da juna wajen ya fara rikicewa nan Mrs. Haseena tamike tsaye ta rike hannun Ummi dakarfi tanamai nunawa al'umma..



"ummi is a symbol of justice to all mothers, sisters, and the society, a woman derseve to be protected..give her the freedom, her right as a women count.. dan haka Idan kun gama tambayar ku game da siyasa, ku tambayi Ummi yadda take ji aranta yanxu Saboda ita ce wannan labarin ke da shi baku ba..



wani irin tsiiiit wajen yayi ayayinda Ummi ta kalli dakin da ruwan idanuwanta da suka cika da hawaye, tana juyawa wurin Mrs. Haseena don samun kwarin gwiwa idonta acike da hawaye yana sauka ahankli tace

"madam Dan Allah nide Kutaimakamini....



Wannan kalami ya sa wani shiru ya mamaye dakin sosaiii yanamai barin tunani mai zurfi ga duk wanda ke wurin.......

SHARE PLEASEEES



SHARE UR COMENTS

AND VIEWS VIA COMENT SECTION



JAXAKALLH KHAIRAN

SURAYYAHMS 08060712446

[05/02, 20:39] Anne-Aurora>Ø‹Ý: *"NUR FIRDAUS..."10*

_Arewabooks@surayyahms_



Abuja.

Dagata dayan bangaren daga cikin karamin falo na gidansu abokiyar nur firdaus wato jadidah bangon talabijin ne ya haskaka fuskar Mrs. Haseena Sharif yayin datake fuskantar tarin caccaka da tambayoyi masu zafi daga 'yan jarida...yarta Layla dake zaune a kan kujera take taje tajawo hanklin dadarta nur firdaus izuwa kan tvn, Suduka biyu suka kalli juna cikin jin mamakin abin da suke gani na live show da mahaifyarsu take zantarwa akan yar yarinya karama wanda hakan yay musu kama da tozarta asirin wnn yarinya wa duk duniya dan abune me zafi da nauyi amma akeyinsa a bayyane



Layla ta kyabe baki ta danna kumatunta da hannu tana girgiza kai ahankli, xucyarta na racing cikin numfashi tace "Yaa Nuri Duba mummy fa, ni Wani lokaci ma nakan manta cewa itadin yar gwawarmayar kare haqqin dan adam ce amma haka dama ake kare haqqin dan adam a bayyane???huhh god, i dont like this.



Nur Firdaus wacce ta kasance tana rike da babban wayarta adede wannan lokacin ta ajiyeshi a gefe snn takalli talabijin din da kyau Fuskarta nanuna takaici da rashin jin dadi atakaice tace "Na gani Layla. Amma ki tsaya ki ji abin da take cewa, mummy tana nuna cewa ita tkmr shugabar al umma ce, mace me kare haqqin y'ay'a mata, amma sai gashi bata da lokacin y'ay'anta. wata uku kenan tana yawonta na kulla karfin siyasa bata tare damu amma yau da safe wai har taje kare haqqin wata daban, Ba za ta ma iya tsayawa tambayar yadda muke farka ba, tawuce ta tafi kano duk dai harkan siyasa ne wnn kuma kowa yasani..."



Laylah ta sake kallon fuskar Mrs. Haseena a talabijin, tana sauraron kalamanta game da adalci da kare hakkin yara sai kuma taji kamar maganganun na taba mata xuciya.



tace "Amma big sis duba irin karfin hali da yadda take magana da jajircewa, Mutane sunayi mata tambayoyi masu wuya amma tana amsawa da jarumta. Amma, meyasa mummy ba tanuna wannan kulawar agare mu?"..



Nur Firdaus ta gyara tsayuwarta tana jin zuciyarta tana kuna.



"Wannan shi ne abin da ke matukar damuna Layla. Kullum tana magana akan yadda ake kare haqqin y'ay'a mata, amma mu fa, yaran ta? Bata ma san abin da ke faruwa da namu rayuwar ba. Tabar mu duk saboda ta tsaya wajen wannan yakin neman zabe da siyasa, Adnan ya riga ya sanar dani komi..mahaifyarsa tana bukatar strong advocacy, kujerar datake nema na minister is very competitive sabida akwai wata yar siyasa me hatsari datake son dalewa, shiyasa suka dawo da abun yakin neman zaben kujera, suna neman Votes daga party advocates, da kuma voices of the vulnerables, kuma mahaifyar adnan ta daura mummy akan wann matsayin ne sabida itace kadai zata iya amfani da kowani irin yanayi, dominsu samu kyakwwan advocacy da votes din da sukeso aranar da za'a voting din kujerar a majalisa againts their opponents. shiyasa suka maida abun ya zama kmr makrci cos i wondering ai ba a siyasar neman kujerar minister amma adnan ya min bayanin komi





abun ya taba zuciyar layla amma jin sunan adnan yasaka kawai ta kyabe baki batace komi ba



nan itama nur firdaus ta yi shiru na dan lokaci, tanata kallon talabijin yayin da aka mayar da kyamara kan Ummi da Mrs. Haseena ke kula da ita. dukansu basu ce komi ba dan da sukaji yanayin labarin ummi nacewa mahaifinta ne fa yay mata mummunan fyade ayar shekara 13, duk take dukansu jikinsu sai yay mugun sanyi.



laylah dakejin wani irin rauni tabudi baki ahankli cikin yin kasa da murya, tace "big sis nifa inaga kila mummy tana kokarin gyara kurakurenta ne tawajen temakon wannan yarinyar duk dama nasan yana da kyau muma ta duba rayuwarmu, ba wai kawai mutane na waje ba." dont u think??



Nur Firdaus ta murmusa, amma ba wani murmushi na farin ciki ba."Za mu jira Layla nima ina saka ran haka. Amma har yanzu, zan ce ki guji dogaro da ita. sabida itadin yar siyasa ce, Duniya ce kawai ke koya mana yadda za mu kula da kanmu."



Layla ta kalli 'yar uwarta cikin damuwa, amma ta kasa cewa komai. Suka ci gaba da kallon shirin cikin shiru, kowanne da tunanin da yake yi a cikin zuciyarsa, yayin da tambayoyi game da uwa da yanayin halinta suka ci gaba da mamaye su.





kano state..



taro yayi taro jama'a duk sun rajaa akai musmmn ma da Mrs. Haseena Sharif tayi tsaye cikin nutsuwa yayin da tambayoyi masu zafi daga  yan jarida ke cigaba da harbuwa Fuskarta na nuna jajircewa.



kokari take wajen kare matsayinta da maganarta akan batun Ummi. Sai dai al amura sun canza yayin da ta ji karar wayarta na daukar hankalinta daga abinda ke faruwa.



Wayarta tana ruri a cikin karamar jakarta, kuma idanunta sun sauka kan sunan mai tura sakon wato mijinta Saadat datake mutuwar muradi aranta.



A yayin da take kokarin mayar da hankali kan tattaunawar, ta kasa daurewa saida ta bude sakon wanda ya bayyana cikin sauri,



"Haseena kidawo Abuja kawai akwai matsala. i cant hide this anymore is enuf nagaji nagaji nagaji.. bazan iya ba musmn ma da yarki take fmr kokarin jan hankalina akan zina, nagaji, wallh Ba zan iya ci gaba da boye wnan abun ba. Ki dawo gida kawai don mu taru mu magance shi ko kawai mu raba auren yau yau inyaso kowa ya kama gabansa.." in kuma kece kike turomin yarki dan tanazuwa min tsirara ina wanka tana nema na da sharrin zina, haseena kisani baxan taba yafe miki ba and u have no idea how dis is going to affect ur politics. pts insane!





a tsandare dede kan kalman "Zinan ta kafe idonta dan kanta taji yamugun sarawa Jikinta ya dauki rawa taciki nan take. Fuskar ta, wadda ke nuna karfin hali minti daya da yawuce, ya sauya zuwa wani yanayi na fargaba da mamaki.



ga tambayoyi daga yan jarida sun dau zafi amma zuciyarta ta cika da zullumi.



Ayayin da aka mayar da kyamara kan wani bangaren shirin ana hira da mahaifyar ummi, nan mrs Haseena ta samu daman rike wayar ta sosai sede Kalmomin Sadat sun hanata sakat suna masu ci gaba da maimaituwa a cikin kwakwalwarta.



aranta bata kawo tunanin kowa ba kuwa sai babban yarta Nur Firdaus sabida tasani sam ra'ayinsu baya jituwa, take kuwa ta fara rike haka aranta, dan gani take yarta layla is too naive and young bata san komi game da zina ba tukuna.



amma toh A ina wannan abu ya samo asali? duk da bata kulawa da su amma ai tasan yarta nur firdaus da akwai tarbiyan addini da kuma nitsuwa, wnn halin kuma daga ina ya fito? or..is she doing this to ruin me?

dama nur ta tsane ni



tayi kokarin boye damuwarta daga  yan jaridar, amma jikinta ya kasa boye fargaba da ke bayyana mata, nan Daya daga cikin tawagarta ya zo kusa da ita don tambayar ko tana bukatar ruwa, amma ta girgiza kai cikin hanzari. Ta san cewa wannan ba lokaci bane don nuna rauni. Amma tunanin cewa tana zargin  yarta da irin wannan abin ya fi karfinta, sam takasa cigaba da mai da hankali kan abin da ke faruwa a wurin. Kusan mintuna goma kacal, ta samu uzuri daga shirin, tana mai cewa..."Ku gafarce ni, amma dolene inyi wata kira mai muhimmanci..



nan tanufi wani bangare da ke bayan daki ta tsaya agaban madubi, sannan ta lalubo lambar sadaat saidai switch off ta dingaji, hanklinta ya matukar tashi, cikin danne fushi ta kira wayar Nur Firdaus. Tanasa hannu don kira zuciyarta na bugawa da karfin gaske. Lokacin da ta fara jin ringing din wayar ta dafe goshinta tana jin wani mugun fushin da ke taruwa a cikinta.



lkcin yay dede da time din da Nur Firdaus da Layla suke famr kallon shirin talabijin jikin su duk yay sanyi suna jin yadda tambayoyi masu zafi ke shiga kan ummi da kuma mahaifiyarta abun da taba zuciya sosai..



karar waya ne ya katsesu Da tsananin mamaki Nur Firdaus tadauki wayar ta rike snn ta danna cikin nitsutsen sallama saidai muryar mrs Haseena tayi rauni tana cike da fushi



cikin yanayin daure fuska tace bani da lkcin amsa sallamarki Nur, kawai ki gayamin wai Menene nake ji haka? shin meyake faruwa tsakaninki da mijina, Menene ya sa za a zarge ki da wani abu mai muni haka?..



Nur Firdaus, wacce ta rude tarasa gane abin

8 / 52