Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

NUR FIRDAUS Imanin 'Ya By Anne-Aurora

Author :  Anne-Aurora Category :  African Stories & Novels

Chapter   3 / 52

6K to 9K   out of 155.7K words

murmushi gabaki daya hanklinta nakan abubuwan da ayoyin ke magana akai dan Allah ya azurtata da ilimin fahimtar ayoyin qur'ani ba zallan iya karantashi ba.



Drivernsu malam liman dake tukasu time to time yake juyowa yana dan satar kallonta yana murmushi dan ilimin addinin da nur din take dashi bakaramin burgeshi yakeyi ba...



Laylaah dai ta lumshe Idanunta throut batace komi ba..



Wani shararren titi suka bi inda zai mi™ar da su har Plot 322 3rd avenue dake gwarimpa housing estate dake abuja inda fitaccen makarantansu na ICICE Al-noor academy international secondry school yake...







wajajen karfe 7.40am na safiya lkcin Sun karyo kwanan estate din kenan Gaban laylah yafara bugawa da wani irin matsannancin karfi da itakanta batasan musababbinsa ba...



Da wani irin sauri ta daga kanta sama tana lekan ta window dan batajin irin wann bugun zuciyar face sai ADNAN SHEHURI yana daf da ita. dada jingina kanta tay da seat dan bayan bugun zuciyarma gabanta fadi yakeyi sosai. sede ganin babu kowa dake bbiyar byan motarsu yasaka tabi ta dawo kan seat dinta ahnlkl ta lumshe idonta tay shiru tana jin sautin kirjinta kamar zai faso waje, duk dai ta rasa wani irin zazzafan so take ma Adnan din wanda azahiri ya kasance saurayin Babban dadarta NUR FIRDAUS ne, wanda kaf makarantan nan nasu da kuma angwansu babu mahalukin da zaice baisan irin zazzafar soyayyar dake tsatsafa tsakanin Adnan shehuri da dadarta nur firdaus ba.



"But why is the forbiden fruit is alwys the sweetest"...???



itade Tanada babban buri nason taga tamori rayuwarta to the fullest tai sakalci, taji dadin rayuwa, batace tana son awards ba, snn batace sai tay porpular ansanta da ilimin addini kamar yayarta nur firdaus..itade kawai she just want attention irin wanda kowa yake bawa dadartan, like a full time celebrity kowa yanaso ace yay shiga irinnata dan yau in nur firdaus tasaka takalmi ko jaka toh gobe zakaga yara dayawa a makrntar suna neman irinsa dan suma su suka ace sun saka irin nata, Hakama turare, style din kitso, yadda take saka hijab da sock.



Every girl want to adopt Nur firdaus's unique style and signature dress codes tsabar yadda take bala'in farinjini nitsuwarta yake kuma burge kowa. Ga wann uban farinjinin nata na kawaye da kuma mugun yawan kwarjinin datake dashi a idanun kyakwawan maza masn ma masu dukiya.,



A fannin laylah kuwa she is chronic attention seeker itade she just want to chill and have all the fine fine rich guys chasing her around kamar dai yadda taga maza masu kudi da aji suna bibiyar yayarta nur tana basar dasu itama tanason taga tana wann kalar rayuwar sosai sabida aganinta itama din kyakkaywace sosai babu abunda bata dashi dan harma tafi nur firdaus zaunannen diri me daukar hankli..



iya kkrinta tanayi akan daukar wanka da kuma karatu dan kullum itace na daya a ajinsun itama sede duk ayanxu tana neman watsarwa sabida damuwar kishin yawan farinjinin yar uwarta data fara daurawa a aranta



duk dama tana kkri wajen yaki da hakan saidai kassshhh haryau ta rasa mesa kullum dai nur firdaus din kawai ake kallo ba ita ba.





Tun da suka taso suna yan kanana kusan ince haka abun yake, its like she is living under her shadow kowa nur fidaus din ce abakinsa, she is evrybodys favourite and everybodys good example duk dama bata dauke rayuwa komi ba sam bata da hayaniya amma sosai Allah ya daukakata.



ita sam sam laylah bata da wnn uban farinjinin bare kuma muhibba na samun daukakar mutane bare kuma maza dan ko me aikin gadin gidansu da anguwansu basu taba mata kallo na biyu ba kamar wacce akama mugun baqi.



dacan zama a inuwar yar uwartan datakeyi be darata ba duba da yadda noor firdaus din take matukar son ta tamkar ita ta haifeta dan a duniya bayan mahaifinsu daya rasu Babu Wanda nur firdaus take mugun so arayuwarta sama da 'yar uwarta laylah wadda takewa kallon tamkr amanrta Allah ya damka mata ba zallan 'yar uwa ba.



Dan Qaunar datakewa laylah qaunace irin wadda Allah ne kawai ya isa ya cire mata shi cikin ranta musamman ma da mahaifyarsu ta watsar da su batawani fiye damuwa da tsabgar data shafe rayuwarsu ba.



tun suna kananu itace tamkar uwa kuma abokiya wa yar uwarta layla, ko kadan bata bari laylahta taso da tulin baqin cikin abunda mahfyarsu take musu ba.



Nur fidaus kusan itace ta raine layla ayayinda ita kanta take neman kulawar iyaka dai tana Jin dadin rayuwarta ne sabida kulawa da abokantaka na gari datake samunsu wajen masoyinta Adnan shehuri dakuma sanin cewa Allah ya mugun daukakata shiyasa Batada abokin fada Bata saka komai na damuwa aranta itadei kowa natane. duk inda kaga noor firdaus toh tabbs zakaganta tare da yar uwarta laylah sabida yadda take alfahari da ita sun matukar shakuwar da ko bacci baiya rabasu dan akan gado daya suke bacci.





....sede ayanxu Da laylahn ta fara dan girma izuwa siffar cikakyar ya mace sai taji kmar daukaka da farinjin yayartata yanason ya dameta aranta, she just cant stop thinking of how she lost her long time secret crush wato "Adnan shehuri" wanda babu abunda take bukata ajikin Wa namiji da adnan baidashi kai tun batasan kanta ba take fama da wata irin mahaukacin kaunarsa aranta sede kuma Adnan is all about nur firdaus soyayya sukeyi me tsayi me kuma tsafta tun na yaranta.



tun suna kanana sosai suka taso da shakuwa wanda akalla izuwa yanxu shakuwarsun ta wuce wanda za'ace zaa iya rabasu cikin sauki





ga kuma very sexy and hot mijin mummynsu agida shimafa talura kamar yaa noor din kawai hanklinsa ke kai, kai hatta drivernsu yafi sakewa da ita duk dai laylah tarasa meyene aibunta da kyawawan maza masu kyau da aji da uban kudi ire iren su Adnan shehuri basuson su tunkareta da zancen soyayya haryanxu..



She wants soo much attention amma bata taba nuna hakan a fili ba amma kuma abune dake cinta aranta bana wasa ba, she wants to be heard and seen awajen maza masu kudi, kuma kyawawa kamr nur firdaus.



toh amma, haryau dai ta kasa tantancewa ko badluck dinta daga silar farijinin yayarta nur firdaus ne ko kuma wani boyayyar aibune take dashi wanda batasani ba.



..cikin saurin kauda wnn tunanin aranta ta bude lumsashun idanunta ahnkli wanda atake kuwa yasauka akan wata mahaukaciyar baqar sport car Audi8 dake kkrin dososu in classic front view, jikin deck din motar kawai takalla saiji tay kamar numfashinta yatike yakai caan sama sararin samaniya yanamai barazanar zaibar gangan jikinta



wani sihirtaccen numfashi ta sauke musmmn ma dataga sunan ADNAN dinne ajiki dan atake taji lkci guda tarasa duk wani nitsuwarta kirjinta na daka tsalle yana rawa kamr zai faso waje..



irin masifar son datake masa shi ake kira da makahon so dankuwa duk yadda taso ta haqura dashi baiyuwa daga zarar sunyi ido hudu saitaji gabaki daya gangan jikinta ya dauka da mahaukacin tsumayin sonsa.



what can be more painful kamar kaga abunda kake matsanancin so agabanka bayan kasan bazaka taba samunsa ba har Abada...





tun da tay ido hudu da motar adnan taji gabaki daya ta rasa nitsuwarta wanda tun kan malam liman ya karasa dasu school parking lot Adnan din ya cimmasu cikin sauri sauri yay parking motarsa ya sauko kasa tsadadden agogonsa ta wittels bach pure diamond ita tafara daukar idon jama'ar dake wajen., acikin sanyin takunshi me mugun daukar hankli ya nufo motarsun sanye da wata lallausar Brown Pants me kamar gold na aldo bianci wanda ya dora wata cool maroon raymond Tshirt data masa chif chif ajiki tanamai bayyana burgewan dake tafe da danyen shekarun samartakansa.



He is a 300 level petroleum engineering student in Base university wanda duk dan nur firdausn ya tuburewa mahafyarsa ya nace cewa saiyay karatu a nigeria kuma a garin Abuja dan kawai suna kasancewa tare.



Adnan shehuri kyakkwane wanda a shekaru bazai wuce 23 ba duk dama jikinshi bai nuna hakan sosai, he is the real defination of tall, cute and calm guy, dan yana da wani irin tsiririn jikine wanda baza'a kirashi da rama ba kaidai kallo daya zakamai kasan acikin niimar dukiya me amsa sunansa dukiya ya taso, dan tundaga kalar yauqin fatarsa har yananin tafyarsa zai fallasa maka hakan, duk inda yaratsa kuwa sai anjuya anzuba ma karan hancinsa dake nan har baka wane na sharukh khan,couple with his silky smooth saje da Allah ya kawata farin doguwar fuskansa dashi. har wani kyalli fatar jikin nashi yake kamar na dan jinjiri.



Adnan da gudane tamkr gwal awajen wata cikakkeya kuma shahararriyar yar siyasa da ake kira da HAJIYA MAIRAM KANEM SHEHURI. wanda basai anja dogon zance ba kunsan sunan cikakkun yan garin maiduguri ne kabilar kanurai da sukayi mixing da yan uwansu shuwa arab ta hanyar auren dangi da kwarya tabi kwarya.



Mahaifinsa Adam shehuri is a senior ambassador of nigeria to Qatar shibaiya cika zama kasar nigeria acan qatar din yake rayuwa dan ya tsufa dan saida yakai almost 50yrs kafin Allah ya bashi haihuwa aka samu Adnan din.



dan haka Adnan din atare da mahafyarsa dayafi mugun shakuwa da ita yake rayuwarsa anan nigeria duk da kasancewarta wata jajirtacciyar yar siyasa da ake damawa da ita sosai aharkan siyasan kasa bata gaza wajen saka ido akan rayuwarsa ba.



hjiya mairam ta rike manyan matsayi kala kala tun daga kan high ranking director har accountant general na crude oil sector har izuwa minister of humanatarian affairs na kasa datake kkrin komawa kan kujerarta ayanxu.



a duniyan nan Duk abunda danta Adnan yake so bata hanashi shiyasa duk dama ajinsu da matsayin dukiyarsu ba iri daya bane dana iyayen nur fidaus amma haka ta amshi soyayyar tasu hannu bibbiyu snn ta jawo mahaifiyar Nur fidausin acikin tawagar siyasanta dan kawai danta Adnan yaji dadi....

*ME KIKE TUNANI ZAI FARU A WANN NOVEL DIN???*?

SHARE UR TOTS AND COMENTS everywhere ure my dear ego reach my desk=ØLÜ<Øûß



or VIA

=ØGÜ<Øûß

CONTACT 08060712446 CHAT KAWAI BANDA KIRA ORG

FOLLOW WATTPAD OR AREWABOOK APP AT *@SURAYYAHMS*







COMEBACK SERIES OF SURAYYAHMS 2024/25

[30/01, 13:48] Anne-Aurora>Ø‹Ý: *NUR FIRDAUS.....4*

_Arewabooks@surayyahms_





ayayinda Adnan yake karasowa zuciyar laylah kamar zai tarwatso waje tsaban bugawa ayanayin da takasa iya dauke kwayar idanunta akan Adnan din har ya karaso tawajensu batare dayama lura da ita a seat din bayana motar ba.



kkrin bude motar take domin tafito koda ace ita zata fara yin ido hudu dashi saikuma taji murfin motar ya tike gam tawaje takasa budewa taciki acikin sauri tadaga ido harzatai wa drivensu malam liman magana saiga Adnan dinhar ya karaso.



saukar nutsatsiyar muryansa taji ayayinda yay sallamawa malam liman wanda yanamai amsa masa ya dauke kansa izuwa kan nur firdaus yahau binta da kallo.





cak laylah taji magana ya dauke a bakinta ayayinda kirjinta yake tsananta bugawa ta tsaya baki bude tanata kallon karamar tashin hanklin dayazo da ita akan kyakkwan fuskan tasa me dauke da kwarjini me daukar hankli...



kai tsaye ya dora hannunsa bisa murfin gaban motar yabudewa Nur firdaus kofa ahnkli dan ta fito. wani irin zararriyar so yake mata wanda shikansa bai san iyakansa ba danko da ta katse masa wayar ji yay kamar ransa ta datse shiyasama hanklinsa bakaramin tashi yay dayaji wayarta akashe ba.



Suna hade ido murmushi me tsananin sanyi yahau wakana akan fuskanta badon komi ba sai ganin irin kallon tsumammen soyayyar datay niisa a zucya da adnan din yake mata ahnkli tasaukar da idonta can kasa kafin nan tasauko kasa a nitse tatsaya adan gefensa batare da tacemai komi ba.



zucyarta bugawa yake taciki musmn ma dataga gansa ahaka kusan a rikice tasan duk yadda akayi dolene hanklinsa ya tashi da yanayin da ta katse masa waya daxu da safe.





kallonta yake da wata iriyar maitar so akwayar idanunsa da muryansa me tsananin sanyi da taushi yafurta salam alaikum hayaatee..



kanta na kallon kasa tana dan murmushi ta amsashi da same words cikin wani irin sanyin kunya me ratsa gangan jiki....tanajin yadda ya sauke ajiyan zuciya, snn tace meya faru baka wuce Airpot din ba?



wata ajiyar zuciyar ne takuma kufce masa yace "i cundnt go bcos you scared the hell out of me muna magana sai kawai kika katse wayarki inata kiranki kuma baki dauka ba..nan yadan ja numfashi snn yace ynxun ma daga gidanku nafito bansamu kowa ba sai kawai nyo nan direct "ina fatan dai lafya, ince dai ba bata miki ranki nayi ba masoyiyata..?ya karashe magann tasa ahankli cikin sakar mata taushshyr kallo



adedenan ta dagokai tadan kalleshi cikin sanyin murya tace U can neva go wrong with me hayatee. kayi hakuri am really sorry to startle u like this, i didnt mean to make u worry..



Dan kifta ido yay akanta duk saiyaji hanklinsa ya dan kwanta baice komi ba ya cigaba da kallonta kai kace bai taba sakata a idanunsa ba.."



aftr 2 mint suna shiru sai can muryanta dake kasa kasa ya fito Tace amma ai kasan am fine ko you cud have missed ur flight aida basai kazo nan bama.



Cikin katseta yace "are u kidding me??..kinsan yadda hanklina ya tashi kuwa..aida kika kashe wayarma ji nayi kamar daga china nake tahowa wajenki..i d really want to knw what happen?



tanadan murmushi tace "nothing. Muje in rakaka bakin motarka kaje ka shirya kaje inda zaka kawai kar kayi missing sai ka dawo zakaji.



baiko motsa ba yace nop hayatii..hanklina bazai kwanta in akwai wata matsala kawai ki gayamin lets solve it together kafin na wuce .



A duk tunaninsa ko matsalar ta da mum dinta ne akan cmption din nan.



Cikin katse masa tunanin tadago kai takallesa Aranta tana shirin ce masa a'a sedei tunkan ta budi baki amsa daga bayansu yaji saukar dirar wata siriryr

murya data taho da dan rawa rawa.."



"yaa Adnan..

yaa adnan good morning



Saida yadan jaaa kafin nan ya juyo atakaice yaga ashema laylah ce

Kallo daya yamata yadan dauke kansa fuska bayabo ba fallasa snn yace Little sis.. gud mrning yaa Baki wuce aji ba..ya kike..?



Dan karamin murmushi tay trying to hide her intense jealousy da kuma heart beats dinta dake yi kamar zai faso waje duk tagansu tare haka sai tanajin inama ace da itace yayarta Nur firdaus dat this hot rich young handsome guy is crazy about. duk mazan da suke burgeta a duniya kama daga kan mijin mamanta kaf basukai mata Adnan shehuri matsayi aranta ba dan Bakaramin sonshi takey



Tanadan satar kallonsa tace "am Fine..dama..

"..bai barta ta karasa me zatace din ba with a fair dismisal tone yace "good"..Daga nan yadan sai ya dauke kansa akanta gabaki daya ya maida wajen noor firdaus



shiru laylah tay dan Aranta she honestly wish ko da asalin sunanta laylah zaina ambatar ta dashi dan be taba ambatar laylah abakinshi ba sai dai little sis din nn dai daayake ambatar ta dashi kowani lkci wanda harga Allah bason sunan take ba dan sunan yana dada sawa tanajin karsashi da matsanancin zafin tazarar dake shimfide a tsakaninsu wanda tasan Adnan hala bazai taba sanin zazzafar sirrin xucyarta akansa ba nahar Abada dan a taga alama matsayin kanwar budurwansa kawai yake kallonta.



tana tsaye tana jinsu yanamai cigaba da tuhumar masoyayrsa akan katsemai waya datayi dazu da safe tana dan kakkaucewa dan Nur fidaus din yarinyace wacce bata san meye fallasa sirrrin gidan iyayenta ba.



duk irin shakuwa da soyayyar dake tsakanin su da adnan haryau bata taba budan baki ta bayyana masa damuwar da suke ciki ita da yar uwarta akan rashin kulawar da suke samu wajen mum dinsu ba..



shikansa a rade raden gulman mutane yakejin yadda ake fadin yadda mahaifyarsu ta zuba gabaki daya hanklnta da xuciyarta akan harkan siyasa haryau kuma baiji wann maganan daga bakin nur fidaus ba anma sosai ya fahimci mayuwacin halin da suke ciki.



suna tsaka da jayayya akan maganan laylah tay

gyaran murya dukansu suka dan kalleta ta dubi adnan tace yaa adnan am sorry wallh nina jawo ta katse maka wayar.



Girarsa na sama a dage da mamakin ganinta a tsaye haryanxu yace "really? So what happen...ke sai ki gayamin tunda ita taki



Duk da idon da nur firdaus ta mata bata daddara ba..tace nakai ma step dad dinmu letter gasarta ne akan yay mata signing kuma ai kasan batason haka...



cikin datsar numfashinta yana kallon nur fidaus din yace ohhhhh shine kika wani bata ranki kika kashe wayarki ko hmmm sarkin fushi...



turo bakin datay yasashi yay dariya



"anyways koda baki samu signing din bama ive already arrange for that...anjima kadan zan tura uncle dina yay magana da malam bello babu wanda zai hanaki zuwa gasarki muddin ina raye!



Ya kalle laylah atakaice yace little sis thanks but no thanks, kinga tunda batason harka da shi pls karki sakeyin hakan dan banason ranta yana baci i dont like it at all koke kinason hakan?



da dan wasa ya fada amma laylah sai dataji zafin hakan sai Bata amsashi ba ta girgiza masa kai da sanyin jiki tana kakalar murmushi..



Itade nur batace musu komi ba haka ya amshi hadadden school bag dinta na dior yace muje in rakaki chemisry lab din hayateee daga nan saina wuce airpot din ko.



Yana karban jakan ta juya tadan kalli laylah dataki tadaga kai..



gabanta taji na faduwa dan sosai tafara lura da yadda layla take bhving idan adnan yana kusa dasu kodai wani abu na damun laylahn akan adnan din ne oho..



Ahankli cikin wann tunanin ta dafata da sanyin murya tace litlle sis kije class dinku kinji banason nabarki anan u are almost late for class ni practicals zan shiga kuma sai 8.30am.



layla ta kasa iya hade ido da nur firdaus Kan laylahn na can kasa tace okay ...



Ta juya kamar zata tafi but she was expecting Adnan to bid her bye amma hanklinsa duka nakan nur firdaus sai baiko juyo ba.



Batare data sake kallon inda suka dosa ba cikin sanyin fixga taja jakarta tafara tafiya harta haura step ta nufi ajinsu ss2b tanajin zuciyarta kamar zai fita dan zafi kai tsaye ta nufi wajen zamanta dake can baya karshen aji taja seat dinta ta zauna snn ta zuge zip din jakarta ta fidda earpod na Apple ta toshe ramin kunnuwanta dashi nan take tabi ta jonashi da wakokin M sharif dake shake da kalaman soyayyar da suka dace da irin wanda datake yima Adnan tabi takure sautin kidan ta kuma lumshe idanuwan ta batajin komi dake wakana a ajin kamr yadda

3 / 52