Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

NUR FIRDAUS Imanin 'Ya By Anne-Aurora

Author :  Anne-Aurora Category :  African Stories & Novels

Chapter   11 / 52

30K to 33K   out of 155.7K words

only my heat my entire soul is all urs habibty.



nur tay murmushi

kalaman soyayya masu zafi ke yawo acikin iskan dakin atsakaninsu



inda nan take Layla taji zuciyarta tana bushewa dajin mugun haushin yadda yar uwarta Nur Firdaus ta ri™e hankalin Adnan sosai.



Ta yi ™o™arin ri™e kanta dake juyawa amma inaa wani radaWi tadingaji na kishi na caccakarta da ™arfi. Cikin zafin zuciya ta juya cikin sauri ta bar wurin da sauri ta wuce kitchen tana ™o™arin Soye abin da zuciyarta ke haifarwa



akasa kan tiles ta zube a kitchen dafe da kirjinta tana jin kamar zata mutu aranta take cewa na shiga uku hala Ba zan taSa samun wani abu daga gare shi ba muddin yaa nuri tana raye ni din tamkar wata fuska ce."



ahnkli ta jingina bayanta da bango tana jin radadin ™iyayya da sha'awar Kwace duk wani abu da nur firdaus ta mallaka a zcyar Adnan shehuri, Duk da cewa ta haWu da kalaman qaddara da jinkiri, da na nuna ™aunarta ga yar uwarta Nur Firdaus, ta kuma san cewa babu abin da zata iya yi sai ci gaba da wasan kwaikwayo....





tajima a kitchen din har sai dataji alaman motsi snn ta mike ta wanke fuskarta ta rasa me zatay kawai sai tahau hada musu shayi, jim kadan nur firdaus ta fito duba ta, sukayi yar hira a kitchen din ayayin da suka sha shayin, babu abunda ke yawo a ran layla face yadda taga mood din nur firdaus ya sauya sosai, baqin cikin da suka qumtsa mata dazu duk ya gushe snn hanklinta ya dan kwanta.





yau din baccin kirki laylah bata iya samu ba tsabar ydda take imagining inama ace itace take soyayya da Adnan yake sakata irin wann farincikin

gashi kyakkwawa, young, ga kudi, ga familynsa sunyi suna a siyasa sosai. this is exctly how she want to end up. Adnan shehuri is her wildest fantasy amma kuma ba ita bace acikin rayuwarsa gabaki daya duk sai taji baqin ciki me tsanani ya gumeta sam ta kasa runtsawa..





wanda kusan hakane yake faruwa ata fannin mahaifyarsu mrs Haseena, wanda acikin daren itama babu abunda take yi sai juyi akan gadonta da tunanin abunda ya faru ayau dake duk hanklinta yana ga kan mijinta ne, sam bata kaunar abunda zai rabata da sadaat sabida bakaramin biya mata bukatarta yadda take so yakeyi ba...



she just cant bear to loose him, daren nan sam be mata dadi ba, hakanan ta dinga tura masa text a wayarsa tanajiran taga ya kira ko ya amsata amma inaaa har tay bacci be kulata ba..





bangarem sadaat din kuwa a club ya tare da abokansa suna tana taba yan shaye shaye da yan matan da zasu kwana dasu ko sau daya be tuna da wata haseena ba.







***** washe gari da safe.



gidan ya dauka da wani irin shiru, nur firdaus tun bayan sallan asubh ta fice tana can waje tanata bitar karatun qur'anin ta kamar dai yadda ta saba.



ko kadan bata da masaniya akan yadda yar uwatta layla da kuma mahaifyatta suka karace daren su da ita a zuciyarsu.





inda layla take ganin kamar itace barrier da raba ta da samjn babban mafarkinta na kasancewa tare da Adnan shehuri, mrs haseena kuwa ta kwana da haushin rashin mijinta sadaat wanda take alakanta sa da lefin nur firdaus ce.







yauma sassafe layla tay wanka ta taho dakin maman nasu da wani sabon salon makircin, sosai ta lura da cewa mrs haseena tana cikin damuwa game da fushin da sadaat yakeyi akansu, dan haka tadauki wann damar tadinga kwantar ma mrs haseena hankli tana mai wanke kanta da kuma shigar da tsanar nur firdaus aran mahaifiryarsun sosai cikin wata iriyar makirtaccen salo na yaranta.





bayan Layla tay nasarar kwantarwa mahaifiyarta hankali da kalamai masu dadi ta koma dakinsu tahau shiryawa hanklinta kwance.



mrs Haseena kuwa sosai ta ji tamkar ta samu sabon karfi don fuskantar sauran matsalolin ta nayau. nan ta mike tsaye da sauri bayanta kimtsa kanta da wasu uban sun manyan kaya tadauki jakarta me tsada, snn ta fice don dawowa bakin aiki kan shari'ar Ummi.



kusan a kofa suka ci karo da nur firdaus sanye da hijab ta riko qur'aninta ahannunta

wani irin takaitaccen kallo tamata sai kuma ta tuna mijinta marigayi haroun shima fa aikinsa kenan kullum cikin karatun qur'ani da sassafe, wani tsakine ya kufce mata taciki data tuna duk halin sa ne ajikin yarta nur firdaus.. and no wonder she is soo annoying..



cike da sanyin girmmawa nur firdaus ta gaisheta, kallon kirki bata mata ba ta amsata ciki ciki tayi wucewarta. nur din ma bata kula ba ta wuce ciki dan ta shirya zuwa makarnta



yau zaay screening na zuwa gasa zasu karbi ID cards,competition customes dinsu, da sauransu, dan babban tarone da ake asalin gayyatan manya manyan mutane dake bada gudumawa wa addini bana kadan ba.





qamshin jikin haseena ya bule gabaki daya ilahirin tsakar gidan gata da son publicity tasan makwabtarsu da dan uban gulma dan haka har waje bakin gate ta fita da motarta tana amsa waya hankali kwance.



aikuwa hamshiyar magulmaciyar wato maman saeed tana hangota ta windown gidanta tay saurin dirkowa ta fito.





kafin mrs haseena ta gama amsa waya ta shiga mota, ta ji wata murya daga gefe, murya mai cike da tsokana da hassada, Tana daga ido taga Maman Saeed din ce, wacce takasance mai yawan barbada surutu da tsangwama ga mrs Haseena saboda kiyayya da hassada.



yi tay kamar ta fitone duba wani abu cikin tsokana da basarwa tace Haba Hajiya Haseena kin dawo gida shine babu magana,...



mrs haseena ta mata wani irin kallo kasar wuyarta tace.."uhum toh Sannu ramatu.



wani makakallen dariya maman saeed tay yawwa sannu haseena daman ko ina son nagaya miki dan wallahi shirinki na jiya ya tabo inda yake mana kaikayi har munasa rai kema hala kiga girman abun a nan gidanki kya bar kwayawwan yan mata da katon saurayi agida sukadai?? toh amma dai Bari mu gani idan 'ya'yanki ma ba zasu kawowa duniya abin kunya ba..



Haseena ta tsaya cak, ta kalli Maman Saeed da murmushin takaici. dantasan cewa makwabtanta basa son ganin tana samun cigaba,kuma kullum suna amfani da duk wata dama don bata mata suna.



hankli kwance cikin jan aji tace "Maman Saeed kenan abun kunya ya wuce mace dake zama da namiji agidansa suna zaman dadiro bayan duk ansan saki uku ne a tsakaninku???



maman saaed ta hade rai sosai mrs haseenan ta fashe da wata muguwar dariya mai cin rai ahhhahaha

yanaha kin canza fuska ohh toh abar wann maganan, ke yanxu ramatu me kike nufi da wannan maganar taki ehhh? Ko dai ke ma kin fara shiga cikin wnn hirarce ta makiya da ba ta da ma'ana?"



cikin jin haushin abunda haseena ta goranta mata tace

in ma na shiga hirar maqiyarki Ai ba hirar banza ba ce, Hajiya haseena Na dai ga kamar kece kike fitowa a talabijin kina magana kan tarbiyyar yara musmmn ma yara mata. Amma inaa aimu sai mun ga abin nan da gaske awajenki, kuma Muna addu'ar 'ya'yanki su zama abin koyi, amma fa idan sun rushe ki, kar ki manta kema ki bayyana wa duniya komi kamar yadda kika bayyana maganar Ummi a idon kowa."



dede nan Haseena ta fusata tace Na san ke da sauran makwabtan nan nawa baku taba farin ciki da ganin na ci wata nasara ba. Kullum ku kuke nan zaune cikin hassada, matsiyata, yan dorin dosino a gwarimpa, jahilci ya kafe ku waje guda..kudai kuna jiran ganin na fadi kasa. Amma bari in fada miki, babu wanda zai iya rushe ni a duniyan sai ubangijin daya daukaka ni. Kuma idan kinada wani abu da za ki fada game da 'ya'yana, ki bari sai lokacin da abin ya faru, idan har zai faru kenan."



Maman Saeed ta kalli Haseena da wata irin murmushi mai cike da tsokana da tsananin haushin jin baqaqen kalaman data yafa mata.



"Ai gaskiya zata fito fili Haseena. Kuma fa sai mun ga yadda za ki kare kanki idan duniya tagane ke ma ba kida da cikakkiyar tarbiyyar da kike kokarin yada wa al'umma."



Haseena cikin zafin rai tace "Idan kika gama magana ramatu kike ko Mman Saeed, sai ki koma gida ki ci gaba da rayuwar ki ta dadiron ci. Ni baki kai nayi musayar yawu dake ba, kuma ba ki isa ki tsayar da tafiya ta ba. duk wanda yake bina da sharri dai Allah ya isa!"



Ta juya cikin fusata, ta shige mota tare da murda tayar cikin sauri tana barin wajen Maman Saeed tabi ta da kallo mai cike da cin fuska da haushi.



gidan dayan makwabcyarsu wanda tadan tsufa maman saeed ta wuce cikin huci da fushi dan taje ta barbada mata labarin komi..



dagata dayan bangaren kuwa Haseena tana tuki cikin hanzari zuciyarta cike da zafi da takaici.



"Wadannan mutane ba su da wani buri sai na ganin na fadi," ta fada a hankali tanajiin ranta na tafasa sosai.



seidei tariga taayi alkawari a zuciyarta cewa ba za ta bari su yi nasara akanta ba. Matsalolin cikin gida da waje duk ba zasu hana ta kai ga cikar burinta ba.



aikuwa nan da nan Ta sake mayar da hankali kan maganan shari'ar Ummi. tanamai tabbatar makanta da cewa wannan yarinyar zatasamu adalci kodan maqiyanta su mutu Kuma idan suna tunanin zata rushe saboda 'ya'yanta cikin karkda kai tace muje zuwa ba su san iya karfina ba....

SHARE AND COMENTS



FOLLOW ME AT SURAYYAHMS



08060712446

[10/02, 19:38] Anne-Aurora>Ø‹Ý: NUR FIRDAUS...13



SURAYYAHMS





bayan tafiyar haseena aiki bada jimawa Nur firdaus tashigo cikin dakinsu da hadaddn qur'aninta rungume da lallausar kirjinta tana tafiya ahankli kamar wacce bata da laka, cikin sanyin jiki ta aje qur'anin akan desk dinta tabi ta kashe wayarta snn ta zauna ahkli a gefen gado tay yar tagumi.



har cikin kokon zuciyarta takejin wani irin nauyi da damuwa dan kokadan bataji dadin yadda jiyan bacin rai yasata maida magana mezafi da kuma tsawa wa mahaifyartan ba, duk da yawan rashin adalci da tunxirata da mrs haseena tay ders dis kindest part of her heart dayake tuna aya daya tak a cikin qur'a ni daga cikin Suratul Al-Isra tun daga 23 da Allah yace karka daga ma iyayenka murya koda kafurta musu kalman "uff", kada kuma kamusu tsawa..



sede tafi jin nauyin ayata 24 inda Allah yake cewa  Wa khfid lahuma janaahaz zulli minar rahmati wa qur Rabbir ham huma kamaa rabbayaani sagheera.", And lower to them the wing of humility out of mercy and say,  My Lord, have mercy upon them as they brought me up{when I was] small. haka kawai inta tuna ayar ya ambace humility saita dingajin kamar bata kyauta makanta data amsa ma uwarta magana a cikin rauni da tsawa ba, duk sai tarasa ya zatay, dan bata da wani dalilin tsaurara makanta duk dama tasan kowani dan adam a duniya raunataccen halitta ne sede ita din karamar yarinyace sosai data rike ilimin addininta amtsayin madogarar rayuwarta bana wasa ba.



duk wann guilt din datakeji a xcryrta shiyasaka tadenajin radadin ciwon abunda aka mata jiya sai bata tsaya duba yawan rashin adalcin da mrs haseena tamata ba da tunanin yadda Allah zaidubi nata reaction din aranta tahau yi makanta hisabi.



dakyar ta mike tabar tunanin snn tahau shiryawa cikin gogaggen uniform dinta dayake mata wani irin kyau within 30 minutes suka fito ita da layla duk jikin nur firdaus din a sanyaye sam zucyarta baya mata dadi dan hatta layla bata gane kanta ba har suka fito waje suka samu malam liman harya fito musu da mota domin tafya mkarnta.



as usual nur firdaus ta rusuna kadan cikin girmamawa ta gaishe da drivernsu malam liman ya amsata da fara'a, nan da nan layla tadauke kanta tay kamar hanklinta baya wajensu dan bata son yawan gaisuwa.



da fara'a malam liman yabude musu mota nur firdaus ta zauna agidan gaba tare da jingina kanta akan seat tanata tilawar karatunta acikin zuciyarta har suka kai makarntr bata lura ba saida layla taja wani numfashi me shegen karfin daya kusa razata " Yaa nur kiga ikon Allah yau za'ayi emergency assembly am very sure wani abu mummunane ya faru..



nur tay saurin daga kanta sama tana mai duban windon motar

batace komi ba tana observing Duka duka abunda ke faruwa can saiga wata mata da tawagarta a tsadadden mota sun taho tana hura hanci kai tsaye sun wuce offishin shugabar makarntar.



Ayayin da Nur Firdaus da Layla suka sauka kasa tare da sauran Walibai sun lura cewa akwai wani irin yanayi na tashin hankali.



dan Gaba Waya makarantar ta cika da kananan ™orafe-™orafe da kuma hayaniya wanda bai saba faruwa ba.



suna gab da shiga aji, sai wata sanarwa ta fara fitowa ana kira ga dukkan Walibai da malamai su hallara marmaza a filin taron asmbly da alama za'ayi wani gaggan taron gargaWi.



nan sukaji mai gadin makaranta yana jan tsaki yana cewa Wannan abu da akeyi yau akwai matsala Allah de ya kyauta.



Nur Firdaus ta kalli Layla da dan mamaki, amma ba tace komai ba. Layla kuwa tana jin wani irin mugun nishaWi a zuciyarta, kamar tana jin daWin ganin tasowar rigima.



nan da nan kowani dalibi ya isa pavilion nayin asmbly aka jeru yau kowa ya hallara cikin nutsuwa dedeku daga cikin wasu  yan mata da samari suna tayin surutai kasa kasa suna zargin akwai wata babbar matsala data faru a ss2b..



cikin haka saiga nan shugaban makarantar gabaki daya wato Dr. Malam Ahmed Yakubu nan wajen yay wani tsiittt, ya taho cikin shigarsa ta alfarma da kamala yasha farar shadda me tsada yahau saman pavement din ya tsaya tare da duka membobin kwamitin ladabtarwa wato Disciplinary Committe ko ince DC



A gefensu wata shuumar yarinyace da aka fisani da Malika sa'id tana tsaye idonta cike da hawaye amma fuskarta na nuna taurin kai da tsaurin ido. nan Akasa ta dur™usa a gaban Walibai gaba Waya.



shugaban makarntar Malam Ahmed Yakubu dake kallon Waliban duka da daurarren fuska yace

"Ku saurara! A yau mun taraku ne domin mu koya muku wata darasi mai muhimmanci. ya nuna Malika, yace wann Walibar SS2 b ce, wacce ta kasa kiyaye martabarta kuma yanzu haka mun tabbatar cewa tana da ciki batare aure ba, wanda yazama abin kunya ga wann makaranta mai daraja da kima.



Malika ta sunkuyar dakai tana hararar kowa bakinta na motsawa kamar za ta ce wani abu muryan Malam Ahmed Yakubu ya dakatar da ita cikin jawabinsa yace "ICICE Academy ba makaranta bace da za azo mana da wasu shashanci har arena darajar tarbiyya da koyarwar Musulunci. dan haka Mun yanke shawarar korar Malika daga wann makaranta nan take, donta zama izina ga sauran yan mata. da maza, Kuma muna so mu ™arfafa misali ga kowa kowane Walibi daya zama mai tarbiya da hali irin na nitsatsu daga cikinku, babban misali itace Nur Firdaus haroun please where is she, can she come up???.



jikin nur firdaus take ya dau rawa amma dake tana da karfin zuciya hakanan ta sunkuyar dakanta kasa snn ta fito tana tafiya ahankli gabanta na faduwa sosai har takai saman asemblyn cikin sanyin jiki.



lkcin ji take kamar zata nitse kasa dan fargaba, dan kuwa idon kowani dalibi da malami na akanta kirjinta yana bugawa da balain kamar zai ballo waje



shugaban makaranta ya nuna nur firdaus agaban kowa yace ita ce wacce koyaushe take zama abar koyi ga kowace ya mace a wannan makarantar.



tun daga ambatar sunan Nur Firdaus da yay sai gaba Waya Walibai suka fara surututai kasa, Malika tuni ta dago ido da sauri fuskar ta cike da ™iyayya datake kallon nur firdaus din dashi.



Layla kuwa tana tsaye daga nesa tana kallon yadda ake yabawa tarbiyan  yar uwarta a fili tanata murmushi a fili amma a zuciyarta kamar ana zuba mata garwashin wuta haka ta dingaji





daga gefe guda mahaifiyar Malika ta fito tana wani irin huci tareda tawagarta da kuma Malam ibrahim dake shugabantar guidance and counseling session na makarantar.



duk binta da case din a mutunce da sukayi taki sam sabida ita macece mai matukar ji da dukiyarta, tun tana tahowa tawajen cikin fushi takejin abunda ake fada akan nur fidaus,ga yarta malika nan akasa tay kneeling agaban kowa



jitay ranta na wani irin kuna dan Ita mace ce mai alfahari,iko da arzikinta duk dama bata da kyakkyawar tarbiyya ko kunya dan haka bata ganin aibu akan abunda yarta ta aikata. isowarta wajen asmblyn keda wuya ta fara daga murya cikin hargagi da tashin hankli tana cewa "Wannan wace irin hukunci ce? A ina aka rubuta cewa idan yarinya ta samu ciki shikenan sai a wula™anta ta haka? Kun Wauki wann munafukar dalibar ta nuna Nur Firdaus da yatsa cikin zafin rai tace kunsata agaba kamar wata mala ika kuna yabata agaban kowa,..wai har yata ce za'a yi misalin rashin tarbiya da ita tou in sha Allahu watarana za kuga abin da zai faru da naku yayan kuma munafukai mts.



Daga nan ta juya da azama tafizgi takardar korar  yarta daga hannun Malam ibrahim wanda malam bello ne ya mikamai ta jawo hannun malika snnn ta dubi Nur Firdaus kai tsaye, idonta cike da ™yama.



nan ta nuna Nur Firdaus da yatsa tace ohhh waikece me tarbiya ko, toh Idan har rayuwa tana da adalci, kema wata rana za ki san ciwon da Malika ta ji a yau. Wallahi, tallahi sai kin ci karo da abin da ya fi haka muni! munafuka kawai. matsamin mtswww.



malamai mata dayawa suka dau zafi suka amsa amma ko kulasu batay ba ta fizgi hannun Malika, suka fice daga filin taron suna haki da fushi..



malam bello yafi kowa daukar zafi daga Dc comittee shine ya dada tsawatarwa wa dalibai sosai, yace sun yi ma malika haka ne a abayyane badon su tozartata ba, sede dan sun tsorata duk wata yarinya datake ganin zata iya dauko musu wani abun kunya da zai lalata musu darajar makarantarsu.



mafi akasari yay misali da dabiar nur firdaus akowani kalmansa musmn inda take kama kanta snn yayiwa dalibai nasiha sosai saida jikin kowa yay sanyi



Bayan taron ya watse nur firdaus na tafiya da sanyin jiki zataje aji nan wasu  yan mata daga cikin abokan Malika frm no where suka biyosu wata kusurwa wanda kallo daya zaka musu kasan suna cike da matsanancin haushin ta aransu sosai.



wa Layla suka fara magana amma Layla

11 / 52