Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

NUR FIRDAUS Imanin 'Ya By Anne-Aurora

Author :  Anne-Aurora Category :  African Stories & Novels

Chapter   36 / 52

105K to 108K   out of 155.7K words

are you okay? ina kikaje ne kinje kin jima munata nemanki, Did you know that your mum is here??



a mugun mamakance nur tace what? are you serious tun kan jadida ta amsa ta tafara murmushi dan wani irin farinciki taji ya rufeta...da murna ta riko hannun Jadida tace muje suna ina?



jadidah tafara dariya tace suna can suna zaune akan chair har nakai mamanmu sun gaisa, nur tanata murmushi tace hakan

yayi, cikin sauri suka karaso wajen duk yadda tazo da murna tana zuwa annurinta ya sauya ganin yadda haseenan take mata wani irin kallon tara saura kwata gashi ta mugun dore fuska layla na nanike agefenta dan suka daine awajen suna zaune akan motarta suna hira



suna tahowa jadidan tamusu sallama ta koma wajen iyayenta



acikin ladabi nur firdaus ta rusuna har kasa da sanyin murya tace mummy ure welcome..i am so sorry bansan kinzo ba..mummy ya hanya? i am so happy that you came for us.



Haseena tadan jaaa karamar tsaki uhum uhum Nur i knw ure not happy to see me karkiy wani karya dadai ace ubanki ne dayake daure miki gindi toh, ai bazaki ma ajesa ya jiraki haka ba,

so, dis is what u want hun?sarauniyar masu ilimi da tarbiya, u want to be the talk of the town to gashi nan kin samu congratulations.



Nur ta rasa me zatace tana ta kallonta da sanyin jiki..m



cikin dauke kai akanta haseena ta kalli layla tace Autata jeki kira Dr surayya kice mata an same nur din tazo dan Allah mu wuce Abuja ive got better things to do with my life.



Wani irin shiru nur tay kanta na kallon kasa batace uffan ba har laylah tazo ta wuceta



tana barin wajen haseena ta mata wani irin kallon raini a mugun dakile tace wnn kayan jikinkin fa?



tunkan ta budi baki ta daga mata hannu ke

nur ure alwys not telling me where ure getting this expensive designer abayas, snn karki sake kice min adnan ne ya baki wann najikinkin sabida layla ta riga tagayamin bezo nan wajen ba...kifadi min gaskiya, kode akwai wani Abunda kikeyi ne nadaban sani ba?..did u knw how much ure wearing ryt now? ure wearing a 90million naira handwoven abaya gown from safiya Abdallah dan ubanki ki gayamin sanaar da kikayi anan kika samo wann tsadadden kayan...





hawaye ya cika idanun nur harya fara zuba dan harga Allah bata san ma kudin abayar ba, muryanta harya fara rawa rawa zata fadi gaskiyan kenan sai ga Su dr surayya taredasu antyn aysha da ayshan da layla abayansu suna karasowa..



cikin sauri haseena ta watsa mata harara tace ke kiyi maza maza ki share wann munafukan hawayen naki tunkan sukaraso, amma kisani zamuje mu karasa maganan abayan nan agida inma iskanci kikey da uztan nan aboye dan su nasaki agaba agaba zaki sani, danni ban kashe uwata ba ke bazakizo ki kasheni ba saidai ki kara tada ubanki akabari ki kasheshi akaro na biyu dan shine yake daure miki gindi.



nur dake jin kuka me yawa na tason mata hakanan ta dannesa da karfi ta shanye ganin handkyn da javeed ya bata ne kawai a hannunta saita tay saurin share hawayentan dashi batay tsammani ba amma sassnyr qamshin turarensan kawai data shaka sai taji yay wani irin calming dinta sosai.



Dr surayya tana isowa da murna nur taje ta rungumeta sosai da murmushin murna a fuskanta itama ta shafa kan nur din tace Sannunki Nur hasken Al'umma Allah yayi miki albarka Allah yasa kifi haka yar lelen babanta i just wish he is here yau da kinga gata sede Allah baya barin wani dan wani



nur tana murmushi tace hakane anty nagode da kikazo min Allah ya saka da alheri



tace we are all proud of you, jst keep it up", murmushi tasa sannan tace "Thank you anty, da murmushi ta koma jikinsu antynsu ayshe tace ina wuni anty matar tace"Lafiya kalau,congratulations, yar nan kinyi k'ok'ari sosai, Allah ya bada sa'a. duk da bata wani sansu ba da faffadan murmushi tace musu Nagode anty. bayan sun gaggaisa aka sake sabon photo session, haseena kam kin shiga tayi wai flash din cameran na reflecting idonta yana sa mata ciwon kai duk ta takura akan su wuce gida duk ta matsu, hakan yasaka Dr surayya jin mugun takaici tay fushi tace suje kawai da yayanta ita zata kwana a kadunan sai gobe zata zo abuja ta jirgi. ..

SURAYYAHMS 08069712446

[05/04, 22:26] Anne-Aurora>Ų‹Ż: BONUS.



Dagata dayan bangaren kuwa

tunda su javeed suka dau hanya ya lafar da kansa akan seat yay tsammm zuciyarsa na bugawa da wani irin ™arfi kamar wani abu mai nauyi na kokarin ballowa daga ciki



Da akwai wani abu game da yarinyar nan da bai iya jurewa Wata annurice mai ban mamaki da ke zuwa masa tare da ita kmar hasken alfijir bayan dare mai duhu ya wanye. Ya lumshe ido, yana jin kamar sanyin muryar ta na masa yawo akansa.



"Na rasa dalilin da yasa zan so ki haka, "Nur Firdaus& "he finally got her name



yay juyi zcyrsa yaji tanacewa duk duniya, kece macen da nakeji hala zanso na har abada Kuma zan same ki ahankli bada garaje ba Zan gane ko wacece ke a hakika.



ahankli ya bude lumsashun idanunsa sann ya kunna Wata naura agabansa me kamar mini telepad wanda atake ta hadashi da hajya mammy a video call, da murmushi ta tarbe sa suka fara magana cikin raha shide ba wani amsawa yake ba amma dan yasata farin ciki yadan sake fuska suka fara bankwana.



muryanta kamr na wacce zata masa tace ka kula dakanka javeed, karka manta da maganan da nagaya maka akan zubaida da kanwarta



nikaina ina son ace ka aure wacce tafi sonka amma ba mace me karamin kwakwalawa irin simran ba, Hajiya Mammy ta sake kallonsa da fuskan tausayi tace  javeed, ka dinga tunawa cewa Aure yana bu™atar rabon Allah inafatan idan zuciyarka ta gane sakon wata zuciya, bazakay wasa ba, ba lallai bane a Wauki lokaci wajen neman aure. just make sure u find ur own wife ba wacce zaa cusa maka ba. aurenka kawai nake jira a duniyan nan dan haka karka ja lokci,kar kabari harse na mutu kafin nan pls this is my last wish kay kkri kacika min.



murmushi me sanyi kawai ya mata sai yay pause kadan snn yace

"Farewell grandma.



dan Dan guntun hawayenta tay masa mumurshi me sanyi sann tace sai na sake jinka Allah ya maka albarka javeed.



ahnkli yace Ameen hajya nan ya katse wayar



Ya koma baya idonsa a lumshe yana tunanin maganguntan yasan dolene kawai ya nitsu yay auren nan kodan ita duk dama hankalin sa ba a nan yake sosai ba he just want to get to know dat girl



Zuciyarsa na ta juyi da tunani kala kala can yay murmushi tuna yadda ta cije tace mai Aswipe din dazu, ga tsoro ga tsaurin ido

"what the hell is aswipe& lols she cant even insults properly, Yafurta hakan jokingly a hankali kamar yana jin sautin kalmar a kunnensa har yanzu.

Sai kuma ya lumshe idanunsa sosai yace



"Ba komai& na cancanci hakan."

"But damn& she had dis fire in her." saurin katse tunaninta yay da cewa Wannan yarinyar zata min illa...



ya jawo wayarsa ya bude yafara latsawa within few minutes tunanin ya dena zuwa masa, hanyar airport direct suka nufa dan ayaune zai wuce Abuja...



dagata bangaren su Dr simran kuwa tun zamansu a motar hadiza ta dinga bata labarin nur firdaus tanamai gaya mata yadda javeed yay behaving agaban yarinyar. simran data fara dariya har tana hawaye, tace sam karyane, ta karyata hadiza karshe ma ta maidata kamar mahaukaciya kawai hadizan saita haqura tay shiru ta kyaleta.



sai dariya take tana cewa kedai hadiza ke babbar munafukace wallah, shekaru na nawa ina tare da javeed kece zaki gayamin halinsa akan wata mace? javeed baya kallon mace sau biyu konima wallhy baya bata lokcinsa ya kalleni bare wata stranger, wai yarinya karama ma for that matter to me zai gani ajikinta, kai amma kin raina ma kanki hankli



hadiza batace mata komi ta ja bakinta tay gum ta shareta har suka isa gidan hajiya mammy nan da nam tahau tayata parking din kayanta dan itadin ma yau zata koma Abujan cikin gaggawa.





daga ta bangaren su nur kuwa kusan gifts din nur dake motar antyn aysha haka mrs haseena taki fir akawosu saima cewa tay acewa jadida ta kwashe ta zuba a motar mum dinta insun koma abuja zaaje akarba ita bata son tarkace a motarta.



hakan dai akay nur batacewa komi sai dai ta zuba musu ido, kaf acikinsu aysha ce kawai tabi schooll bus abunta, haka jadida ta kwashe gifts din duka suka wuce mata dasu Abuja tare da mum dinta, wajajen 4:40pm na yamma bayan an idda sallahn asr anci abincin nan Nur da layla suka shiga motar mrs haseena



as usual haseena ke tukasu suka kama hanyar Abuja layla na gefenta, nur na zauna abaya ita daya, wanda tunda suka kamo kan hanyar batama jin hirar da sukeyi,wani irin kasala da rauni me nunnuke da tsananin kewar mahaifinta kawai takeji na tsagawa har tacikin kokon ranta



kanta ta dan jingina akan seat idanuwanta a lumshe tajima ahaka dan bata ko motsi gashi Adnan ko kirarta awaya beyi ba



atsakanin qamshin turaren javeed da ke mamaye ajikinta yana fita harta numfashinta dakuma dumbin kewar mahaifinta datakeji aranta bata san wanne yafi sgasa mata aya gangan jikinta ba.





sunyi tafiya me nisa sunkai kusan rabin hanyar shiga Abuja lokacin Motar Haseena na tafiya da wani irin speed kamar yadda zuciyarta ke tafasa da haushin bata lokcinta datay akan hidaman Nur din yau wanda duk Dr surayyace ta jawo mata bakowa ba..



Layla na gefe tana tanatq famar mata surutai mai cike da yarinta duk damq Labarin Nur Firdaus daaka tayi yau awajen gasar karatun Qur ani ya™one mata zuciyar ta amma bashi ya hanata bada labarin komi wa haseena ba.





sai can Haseenan ta buWe baki tafara cewa

layla ni wann boring hirar ya isheni just tell me what you want to eat kawai muna shiga abuja sai mu tsaya mu saya



da murna Layla ta ce Zucchini pizza kawai nake so naci mummy

ta juya baya tace yaa nur kema ai shi zakici ko?



tanakan cakalar nur da surutu Kafin ta rufe baki nan sukaji motar tayi wani muguwar kara wanda kanajin sa kasan fashewar taya ne, nan take kuwa motar ta juya gefe da su cikin sauri sukayi jeji sukaje garau suka buga jikin wata katon bishiyar kuka.



kusan dukansu sun rude Kowa ya birkice yana salati wani irin Girgiza motar tafarayi daganan sai hayaki saiga kuma ™amshin man fetur.



Layla ce tafara danna musu ihun razana da gigita, Haseena ta ri™e cikinta cikin gurnanin zafin bugewa datay amma da ta hango haWarin da ke tafe sai tay sauri ta cafko Layla tabude musu motar ta gaba cikin sauri suka fice tare suka bar Nur Firdaus a baya tanata ™o™arin zare ™afarta da ta makale da jikin seat din gaba.



ganin mrs haseena ta fitar da laylahn waje successfully yasaka nur ta fara kuka tana ihun sunanta Mummy don Allah ki taimaka min kafana ya ki fita mummy wayyo Allah na mummy Nur ta yi ihu cikin rasana da sunan haseena tanata kuka me kara gashi ta mugun razana sosai duk ta rikice.



arikice Haseena ta janye Layla da karfi takaita nesa da motar snn tace auta kiyi sauri kiyi nesa danan this car may explode anytime soon..



amugun rude layla tana kukan tsananin razana tace mummy but what about yaa nur mummy dan Allah kije ki cirota kar ta kone mummy karki bari ya nur ta mutu



wani tsawa ta daka mata tace kedai kibarnan i wll just get us sum help nur ai zata iya fitowa bataga dama bane..



duk rashin hanklin layla yau dakyar ta iya dauke ido akan nur dake ihun neman ceto tay bakin titin tanata kuka kamar ranta zai fita...



haseeena ta matso wajen dede Motar na shirin fashewa lokcin Nur Firdaus ta ciji lebenta kukanta na fita daga cikin kokon zuciyarta sanin cewa Lokaci yana tafiya motsi Waya tak ta karayi da kafarta zai iya jawo explosion da zai iya ya dai dai ta rayuwarta...





haseena nazuwa ta wajen tafara mata ihu tanacewa bazaki cire kafarki ki fito ba??i am not going to kill myself bcos of ur stupidity get out of that car ryt now..kinaji ko bakiji na???



tana cikin wann ihun nur na kuka sosai dan gabaki daya ta gigita ta galabaice.



mummy don Allah kizo kitaimaka min kafana yaki fita mumy

mummmy mummy pls



hawaye suka cika idon mrs haseena tausayin yarta yahanata motsi jikinta na harna rawa rawa ta kuma rude sosai amma ji take wallh bazata kone kanta kurmus akan nur ba



nan sai ga wasu mutane daga titi sunzo wani dattijo me jarumta ne yaje direcr ya ture gaban motar ahnkli sai kujerar daya dannetan ya saki ™afartan da mugun sauri cikin jarumata ta fito waje da ™yar..



tana wullo kanta waje kuwa ko minti uku batay ba motar ta fashe da ™arar gaske wuta ya fara ci, wani irin watsewar zabbi akayi Sai kowa ya rasa ta inda kowa ya nufa...



mutanen dasukaga abun kowa cewa yake alhamdullhi yarinyar nan ta fito Allah ne kawai ya kareta.



da kura ya lafa kowa ya dawo hayyacinsa neman duniyan nan haseena tay ma nur awajen da akayi hatsarin amma bata ganta ba sosai ta rude tana nemanta amma sai shiru..



tunda aka watse nur kuwa tay hanyar titi abunta, tanata jan kafarta dakyar tana dingishi tana sheka matsanancin kuka



dan kuwa abunda haseena ta mata aynxu ya taba mata kwakwalwa har saida tafarajin kamar ba ita ta haifeta ba, sosai tay fushi ta kuma sha mamakinta, sam sam bataga amfanin hade ido da haseena ba, gara kawai tayita tafiyarta koda da kafa ne ta isa Abujar ya fi mata, dan Allah ma yasani babu abunda take tunawa a brain dinta yanxu face sai irin rokonta data dingayi ayayinda take tsakanin rai da mutuwa. and she just cant belive everything ryt now, anya wann matar ita haifeta kuwa, wai ace agaban idonta haseena ta cire yar uwarta layla waje amma ita ta roketa ta taimaka mata haka taki motsawa saima ihu datake mata.



nur tay kukan baqin ciki da fushin da bata tabayin irinsa a rayuwarta ba, tafiya kawai take tana kuka me zafi, har saida tay nisa sosai sannn ta fadi ta suma, dede lkcin wani motar haya suka tsaya mutanen ciki suka firfito suka dauketa cak suka karasa da ita cikin garin abujan aka kaita asibiti dan batama san inda hanklinta yake ba...ENJOY THE WEEKEDNS WE CONTINUE ON MONDAY AMMA KU SHIRYA SOSAI d'žd'ž





surayyahms/08060712446





[07/04, 19:53] Anne-Aurora>Ų‹Ż: *NUR FIRDAUS...29*

@SURAYYAHMS





Wajajen bayan magrib wata baiwar Allah data kasance acikin motar hayan da suka dauko Nur ta shigo da ita asibitin gwamnati dake Abuja, dake ma matar tadan manyanta sai ba a dau lokaci ba aka karbesu aka shiga da ita ciki aka fara bata taimakon gaggawa lkcin tana sume dik bata sani ba, hatta kafarta inda kujerar ya matse saida suka dubashi da kyau wanda Allahne kawai yaso be karye ba akay dressing dinsa tsaf aka saka masa oitnmt da bandage, sai ruwan drip da aka lankaya mata a hannu, sede kafin ma ruwan ya kare Nur har ta farka ta fara motsawa dan da wani irin kuka me cin rai tafarka yadda zaka sancewa lallai wann abunda haseena tamata ya mugun taba mata zuciyarta bana wasa ba. matar data kawotan ne ta matso kusa tana rarrashinta



Nur tay ta kuka abun nata dawo mata kai harsaida ta tsagaita kukan snn matar tace mata sunanta mrs yvonne christoper dama taje taron addini ne a kaduna sai suka ganta a hanya akasa ta suma suka dauko suka kawota nan tahau rarashinta tanamai tambayar ta abun da ya faru da ita...



tsabar baqin ciki idanun nur na fidda ruwan hawaye sosai amma gabaki daya ta kasa furta gaskiyan abunda ya faru dan gani take hala bame yarda cewa uwa zata aikata haka wa yar cikinta,kawai sai tace hatsari sukayi da ita da su mamanta shine motar yay exploding ya kama da wuta ita ta bace musu.



matar taji tausayinta bana kadan ba haka tay ta rarrashinta tana tambayarta ko tasan lambar mamanta sai akirasu,nur ta sani sarai amma tace mata bata sani ba..



jitake kamar tafi son tay zamanta asibitin dan gabaki daya har ranta ji take kamar bata son ta koma ta zauna a inuwar haseena kuma.



she wanted to pretend that ta samu tabon kwakwalawa ta manta hanyar gidansu ma kwata kwata amma ina har saida wani likita yazo yana kallon fuskarta kuwa yagane ta musmmn dayaga fallasashen kamannin alhaj haroun sosai



yace ma mrs yvonne din ai yasan Babanta nan kuwa yahau kirar lambar mrs haseena akai akai yakai sau uku ajere amma duk sai ace switched off

sabida wayarta ya fashe agarin ceton ransu tun acan wajen hatsarin ya dauke, kkri suke wajen neman mafita sede nur aranta tanajine kamar ta sulale ta gudu ta shiga duniya, haka mutanen nan suka ki subarta tay motsi dan har wani tea me kauri aka mata aka sata sha na dole, matar tanata rarrashinta tana bata haquri ko awa daya basuyi a asibitin ba likitan ya kira wani uber ya bashi adress din gidan mrs haseena akazo aka dauketa dan akaita gida tunda ba asamu lambar haseenan ba...



sunyi tunanin duk inda mrs haseena take yanxu hala hanklinta ya mugun tashi akan bacewar yarta.



haka matar ta riko hannun Nur har cikin mota suka dau hanyar anguwrsu ta cikin gwarimpa wanda tun da suka dau hanyar nur ta kife kanta akan cinyarta ta cigaba da kuka dan ita kadai tasan abubuwan dake mata zafi..





ata bangaren su mrs haseenan kuwa tun Bayan wannan mummunan hatsarin bata sake samun wani sukuni a zcyarta ba musmn ma da sukay neman duniyan basu ga Nur awajen ba.



inkaga yadda haseena ta birkice tana neman nur firdaus awajen tanata ihun sunanta tana yawo taje nan taje nan kamar tababbiya tana kan tambayar mutane saikasha mamakinta



wanda ita kanta layla duk tagane cewa guilty conciense ne kawai yake famar damun mumynsun akan abunda tama yar cikinta ba tsantsan so na uwa ba





bayan an nemi nur angaji mrs Haseena da Layla sunkai kansu gida da kyar Sun isa Abujan bayan

36 / 52