Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

NUR FIRDAUS Imanin 'Ya By Anne-Aurora

Author :  Anne-Aurora Category :  African Stories & Novels

Chapter   43 / 52

126K to 129K   out of 155.7K words

gidansu..



tana daga kai da niyyar masa magana caraf sai ta hango taron mutanen dake a kofar gate dinsu koda taga mrs haseena atsaye da su maman saeid atake taji ta birkice gabaki daya zuciyanta ya hau buga kirjinta na dukan tara tara, ahnkli tasunkuyar dakai kamar mara lfya data kalli time a wayarta kawai sai idonta yafara fidda sabbin ruwan hawayen tausayin kanta dan ta riga tasan me zai biyo baya.



Javeed ya gama kare masu mrs haseena kallo yaga suma nan din suke satar kallo

duk da yasan ba lallai sugane waye a motar ba sabida tinted dinsa amma tuni jikinsa ya bashi sudin su wayene.



juyowa yay kalleta ganin tafara kuka sosai da muryansa mai taushi yace you scared? bata amsa shi ba kawai tamasa innocent kallon ai bazai gane komi ba..



dan kyabe baki yay yace duk duniya za a iya taruwa ayi magana akanki amma ke ki tsaya kan gaskiyar ki kawai mana..



Ta girgiza kai a hankali hawaye na gangarowa daga gefen fuskarta bata ma sanda bakinta ya kufce cikin kuka me sanyi tace masa mummyna bazata fahimce ni ba, Nide dan Allah ka dan tsaya, Bazan iya fita yanxu ba, sungan ni a cikin mota da kai ynxu zasuce min wani abu da ba zan iya jurewa ba.



Javeed ya tsaya yana kallonta can yasauke numfashinsa ahnkli ya matso kusa da wata iriryar salo na kwarjini da kwantar da hankali



cikin kwayar idanunta yake kalla kafin nan yay calming voice nasa cikin lallami yace Dont worry, ki manta da su kawai ki fita da kwarin guiwa, u're a brave gal, rembr u fought seven boys to save ur own sister, u've taken risk againts ur ownself kuma nasan Wnan bashine farkon yakinki da duniya ba."



kallonsa tay cikin ido a shaukance tana jin kamar duk duniya shine kawai ya dan fahimceta, batace masa komi ba ta saka hannu tafara share hawayenta Ahankali tabude kofar motar Veil dinta ya makale a bayan kujera bata lura ba tafita waje da sanyin jiki suman kanta ne ya wani irin kwantawa akan gadon bayanta da wani irin nauyin zuciya ta rufe masa motar snn tajuyo tanamai kallon lumsashun idonsa..



he is so damn cute sai yanxu ta kara kare ma fuskansa kallo sosai.



sihirtaccn ajiyan zcya tay da sanyin murya tace masa "thank you...dan kadan yabude idon ahankli yay kamr be jita ba da wata sexy voice nashi me kashe jiki yce 'what did you say?? yan yatsunta take fidgeting tare dadan shagwabe masa fuska tace 'Thank you, for everything...murmushinsa me tsada da baifiye yi wa kowa ba ya mata snn ta juya sai anan ya lura da veil dinta dayaga tafara tafiya da sumanta abude



Haseena da tuni ta soma jin jiri jiri tana ganin nur ta fito a motar wani babu ko dankwali wani irin kunya ya gumeta ta dan lumshe ido tana kokarin boye fushinta. ranta amugun bace ta juya da fushi cikin sauri ta shiga gidan ba tare da cewa kowa komai ba su layla na biye da ita



Su Maman Sa id abun nema ya samu ai take suka tsaya kallon juna ita da mama hauwa



tace dubi dubi yar gwal din ta fito yawon tada saurayi ko veil din ma bata yafa yau ba...



mama hauwa tace "Ni fa dama tunda farko nace muku akwai wata babban matsala agidan haseena dan haka kawai polisawa bazasu zo neman yaranta da asuba ba.



Javeed ya tsaya daga cikin motar Yanata kallon Nur tana tafiya ahankli harta karasa bakin gate dinsun taji wayarta na ringing da wata private number akan screen tana daukawa taji muryan sa yana cewa 'wait for me der". cak ta tsaya batace uffan ba sai gashinan ya taho ya kawo mata veil din hannunta mika zata amsa hannunsu ya dan gogi juna wani uban zafi yaji jikinta yayi, tana karba kanta na kallon kasa tawuce cikin gidan da sauri kuma cikin sanyin jiki..



wani irin shewa su maman saeed suka buga dede lokacin javeed ya juya ya koma cikin motarsa yazauna aransa yanajin kamar yabita ciki sede yasan bazai taba iyawa ba



after like 5 mins bayan iyayen gulma sun bar wajen javeed ya sauko kasa ya bude booth dinsa na baya ya dauko wani jaka yakoma motar ya bude jakar yahauciro Bunch bunch na new dollar note yanemi envelope sama da kasa a motar bai samu ba ya tuna riga biyune ajikinsa akwai irin farin inner shirt din nan hakan ya cire T shirt dinsa kafin nan ya cire inner rigar cikin ya shimfida akan seat ya zuba dolla notes din nan kusan guda biyar aciki, akan note guda daya ya cire pen dinsa ya rubuta mata "get drugs" ajiki yay wrppig dinsu dakyau acikin white shirt din.



kafin nan ya mayar da na saman ya fito ya kwankwasa gate sai ga malam liman ya fito suka gaisa cikin dattijantaka yace

masa ga aika ya bawa nur firdaus amma zai kirata zatazo ta amsa dakanta basai yakai mata ciki yanxu ba. Dattijan takan da javeed din yay masa maganan dashi ne ya saka malam liman bai masa musu ba dan sosai shima yke son nur dan haka baya zarginta da komi kawai saiya karba ya aje a dakinsa.





mrs Haseena tana shiga gidan ta tsaya a falo tana na huci me zafi Layla kuwa na tsaye da hawaye dan aranta tasan itace ta jawo ma nur firdaus haka sede yadda taga hasseena na tafasa tasan cewa dolene ta fidda kanta tay denying komi if posble ta nuna cewa bata san da zancen partyn ba kwata kwata ......



aikuwa Nur tana shigowa gidan Mrs haseena ta tareta da buhun barkwanon masifa dama acike take da ita tam, yai taki sam tabarta tay bayani kawai tafara sheka mata ruwan zagi da kalamai na zargi ta inda take shiga bata nan take fita ba kawai nur saita sunkuyar dakanta tayi shiru tana famar zubda hawaye.



ji kawai take mrs haseena na cewa zaya iya disowning inta inde rayuwar bin maza tasako agaba dan Bazata taba amincewa ta jawo mata abun kunya ba



agaban haseena layla ta nuna cewa ita bata san da maganan wani party ba ita kam ma bata da lafya tana gida tana kwance irin dai ta nuna aima bata san cewa nur din bata gidan ba.





Da kuka me cin rai nur tawuce daki dan duk furucin layla yafi bata baqinciki, As usual laylan ce tazo daga baya tay kneeling agabanta ta dinga kuka har tana majina wai tana ba noor haquri...



nur tay fushi sosai taki kulata zazzabin period ma yazo ya rufeta ranar tanata murkusu a daki sai can da yamma dataji dama dama sai taga text din javeed da private number akan taje ta amsa abu awajen me gadinsu



mamaki ne kawai ya sakata daurewa ta fita waje aikuwa malam liman bai ja ba ya bata aikan da bata san meyene aciki ba dai ta saka a hijab dinta tazo dakisun dashi wann shegen qamshin turaren san ne ajikin rigar duk ya cikata sai taji kawai tana Allah Allah tabude abun tagani nan kuwa ta shiga warwarewa sai taga ashe ma kudi ne da note din daya rubuta akai tadau lokaci tanata kallon fine italic and bold hand writing dinsan dayay mata mugun kyau dan ita kudi bai dameta ba.



motsin takun layla data fara ji yasata sauri tabude jakarta

data dawo dashi daga KD ta juye bunch din dollars din aciki tare da wanda matar kawunsun ta bata ya zama tana da bunch bakwai kenan na Us dollars da bata san worth dinsu ba iyaka

banbacinsu shine kowani tumin na javeed din yana da kauri sosai sann is made with special currency code kana gani kasan dai buga musu kudin nan dai akeyi danasu engine din.



rigarsa dake baza qamshi kawai ta fitar tajefa akan gadonta dede wajen pillow inda take kwanciya dan babu tantama qamshin javeed yana saka mata kasala na musammn da kuma nitsuwa.



cikin kwanakin gabaki daya Ko adnan baiya gane mata gashi case akatayi akansu fahad tasha mugun mamaki da har aka karkare bincike basu ambace sunanta ba bare su bada labarin abunda javeed ya musu, kawai tasan tsoro ne ya cika su but atleast she is now free frm them snn har abada in sha Allah bazata sake kula aysha ba, kusan saida layla tay kwana uku tana bibiyanta da magiya tana rokonta kafin nan ta sauko suka shirya kansu harma fiye da dacan



mrs haseena kam dama satin nasu ne tunda masifarta ya raba polisawa da gidanta tacigaba da kai kawowa wajen uwargijiyata dan babban taron murna sukeso suyi bayan an sanar da jamaa nasararsu.



******



Dagata dayan fannin kuwa baifi jinyar kwana goma akayi a kasar gypts ba saiga Jikin alhaji Abubakar ciroma ya warware sosai saidai shida ahalinsa haryau basu dawo nigeria ba suna egypts din inda kullum ake masa check up na ciwon zucyarsa..



kullum yarsa razia na manne dashi yana kuma lura da furucin bakinta datake yawan yi akan nur firdaus game da ciwon nan nasa shide bai taba ce mata komi ba



har sai ana washe gari za'a sallamesa su dawo nigeria sann ya zaunar da ita tare da iyayentan duka ya hau basu tarihin mahaifin nur firdaus frm the scratch, frm yadda iyayensu suka mutu suka barsu suna yara amma harouna ya zame musu uba da uwa, yace musu sanadiyar da shidin baiyi mugun arziki ya zama me kudi sosai kamarsu ba kenan

sabida he was busy taking care of their lives raising them and shaping them into who they are today.



yace musu secrifices din dan uwansa haroun ne ya kawosa matsayin daukaka da ayau suka gansa yake ciki, ya kuma gaya musu cewa Alhaj haroun din mutum ne me tsnanin tausayi da gaskiya kuma wnn gaskiyarsa ita ta kashe shi.



ba labarin daya daga musu hankli face na babban filin gado da suke gadara dashi da

gwamnati da wasu yan siyasa sukaso su kwace wanda case dinne yay sanadiyar karewar dan arzikin haroun wajen sharia



kuma badon komi ya tsaya akan gaskiya ba saidan yay protecting din future din dan uwansa da kuma na yaran sa daya bari awajen haseena.



duk wani boyayyen tarihinsu saida ya basu jikinsu kaf sai dayay sanyi suka kasa motsi, anan ne suka gane dalilin daya saka yarike rashin samun su nur akusa dashi aransa da tsanani har abun yaja masa ciwon xuciya.



snn yace musu ji yake kamar yaci amanar dan uwan sa dabai raine nur da layla da hannunsa ba sabida dan uwansan haroun shine ya dorasa a duk wata matsayin tarbiya da daukaka da suka gansa aciki a duniya ayanzu..



saida ya gama warware musu wann lamarin kafin nan dukansu suka gane muhimmacin su nur a rayuwansu tare da dumbin baqin cikin dake kumshe a ran alhaj abubakr din da kuma damuwar rashinshi acikin rayuwarsu nur da bazai taba iya cire zafinsa a zcyarsa ba

da wann baganin yay ma razia da iyayenta wasia me shiga jiki sann yace musu koda wata rana ya mutu bai yadda su juya ma su nur baya ko su cutar dasu ba koda awani yanayin rayuwa zasu tsince kansu.

#SURAYYAHMS

COMENTS AND SHARE

[12/04, 19:41] Anne-Aurora>Ø‹Ý: *NUR FIRDAUS...32*

_@SURAYYAHMS_

Arewabooks@surayyahms

wattpad@surayyahms





kwance tashi babu wani wuya game nisan kwana, gashi haryau ana batun cika kwana biyar kenan da faruwar rufe case din partyn nan wanda already har aka gama ba ambace sunan nur firdaus aciki ba.



javeed mufasa kuwa tun aranar daya kawota gida yawuce hidimarsa acan qasar china saidai kuma daga zarar nur firdaus tafice daga gidansu muddin da wayarta ajikinta toh yana iya sani kuma babu tantama spys dinsa suna nan a boye suna bibiye da ita duk inda zata shiga batare da tasani ba. alaqar kawance tsakaninta da aysha gabaki daya ynxu babu shi, yanxu daga ita sai layla sai kuma jadidah suke rayuwarsu a schl din

itade layla bata dena halinta na munafurci da hassada ba amma

kuma tunbayan abunda ya faru a partyn nan ta koyi dannewa, saidai as days pass by tana dada lumewane acikin wani sabuwar tashin hankali, dan bata iya nitsuwa ko runtsawa batare d tunanin cewa kwanan nan labarin Auren yar uwarta nur firdaus dana adnan shehuri dan gidan minister of humntrian affairs zai karade garin abuja ba.



another deep blow da take mugun tsoron gani dantasan bazata taba iya daukar zafin sa a zuciyarta barin ma da tajima tana wahala da dakon boyayyar syyar Adnan shehuri aranta.



acikin kwanakin nan da ake rade raden baifi kwana biyu ayi sanarwa ba sai ta farajin inama ace nur firdaus zata mutu kafin aukuwar wann Al'amari, dan in har nur bata mutu ba toh tanaji hala itace zata hadiye ranta ta mutu dan duk ranar da akace nur ta zama daya da adnan shehuri tasan bazata sake iya samun sauki konada na busar numfashinta adede ba.



acikin kwana biyar innan abubuwa dayawa suna faruwa wasu a boye wasu a abayyane, dan haryau nur bata tsira daga habaice habaice yan hassada ba, snn ga wann mummunan mafarkin daya fara sakota agaba wanda ko tay addua sau nawa wnn same mafarkin sai ya zo mata.



dalilin wnn mafarki yasaka ta aje komi agefe tafara bawa layla extra ordinary care, dan kowani dare sai taga laylan acikin wani mummunan yanayi nacewa wasu mutane sunzo sun dauketa kuma kasheta zasuyi.



bata taba fadawa kowa mafarkin ba sai dai kawai tay addua in kuma taji faduwar gaba ko rashin samun bacci yaki sam ya saketa sai kaga ta saka rigar da javeed da ya bata ajikinta dan qamshin da kejiki na saka mata kasala tuni saikaga tay bacci bazata kuma farka ba sai wann mafarkin nata ya sake dawowa



ata dayan bangaren kuwa sadaat tare da sanata farida bala basu zama dan tun zuwansa suketa shirinsu gashi ta hadasu da wani shegen doctor amma haryau bata fayyace musu dalilin hakan ba tukuna. itade ta basu gargadin su tabbata sai ana washe gari za'ayi sanarwan kujerar nan sann su aikata komi yanxu haka gabaki daya a shirye suke dan baifi kwana biyu ne kacal ya rage ay sanarwan ba.



satin gabaki daya mrs Haseena batama neman sadaat awaya sabida hidiman shirye shiryen samun kujerar uwar gijiyar dana siyasa daya mugun sha mata kai..



and she has put her children under strict survellance akaro na farko kenan data gaya ma malam liman cewa ya tabbata shine zai kai yaranta schl ya jirasu atashi snn ya dawo dasu dan kwata kwata bata yarda da Nur firdaus ba gani take kamar zata iya jawo mata wani matsalar da zai jawo mata cin mutunci ko zagi abainar duniya.





Nur takanyi amfani da wann fassarar da Mrs haseena take mata wajen bawa Adnan uzuri dan ya kyaleta dan sosai ya matsa mata akan lallai su fara shirin auren su, yanata zumudi sosai dan he alwys wanted her to be around him acikin kwanakin nan badon komi ba sai dan yana nunata ma yan uwan mahaifinsa dana mahaifyarsa kafin auren amma haka nur tadinga ki mishi sam tacemai ai mahaifyarta tahanasu yinwata motsi ita da layla yanxu daga schl sai gida sabida tsaro.



duk yadda Adnan yay haka zata ki masa sam wata rana har su samu sabani amma ita kanta bata ganewa kanta yanxu zuciyarta da nitsuwarta gabaki daya yanaga wajen javeed ne, ko ina yake, ina ya shiga, duk sanda taji wayarta yana ringing ko karar sako ya shiga she secretly wish zata ga ko private number na javeed ne amma tun ranar da suka rabu bai sake nemanta ba..



Da kyar take danne Abunda takeji aranta domin bata son mare illusions dinta na crushing akan javeed mufasa yazo yashiga tsakaninta da Adnan dantagama lura kmr sosai take bawa adnan din ciwon kai a cikin kwana biyun nan.



wani bin zaizo hira amma kuma hanklinta sam baya kansa har yaji ta bashi haushi sede kuma marmaza zakaga ta lallabashi tareda bashi uzurin cewa tana son ya nitsune ya bawa mum dinsa full attention a wann lkci inyaso in aka gama hidimar murnan sabuwar matsayi zasu dawo daidai. da iyakan wann kalaman ta cire masa damuwar data fara sakashi aciki.



sabida haka wani bin takan daure suyi waya sau biyu arana in taga bazata iyaba kuma sai kaga ta kashe wayarta sai can hanklinta ya dawo jikinta sai ta kunna haka suka dingayi acikin wnn kwanakin haryau ana zancen saura kwana biyu ayi sanarwa.



ranar tuesday duka yaran sunje schl lami lafya sedei tunda suka dawo Nur tafara wani irin ciwonkai me tsanani ga yawan faduwar gaba sai tanaji kamar ana tsorata yaudin da daddare tay bacci sai kuma batay mafarkin datakeyi na laylahn ba kawai babanta tagani waiyafito daga wani lambu me shegen kyau yanamata murmushi yana kirar sunanta tanata binsa abaya izuwa wani tsiririn hanya me wuyan takawa saihar takokarta takusa kamoshi sai yabace mata bat..



ranar Da sunansa ta farka a bakinta harda dan guntun hawaye daya sauka a fuskarta maza tay masa addua sann ta sauka taje kitchen ta bude fridge ta sha ruwan sanyi



tunda ta dawo sai taji ta kasa komawa bacci alwala ta doro tazo ta hau gabatar da sallahn dare, cikin kowani sujuda sai ta roki Allah akan ya jadadda rahama ma mahaifintan, tay adduar samun shiriya wa kanta da layla, da mamansu, snn ta roka musu samun kwancyar hankli, ta roki Allah inhar tsakaninta da Adnan alherine ya tabbatar musu da hakan sann ya cire mata sonshi inde ba alheri bane tarayyarsu...



shima javeed din datakejin wani abu aransa wanda tasan inba Allahn ba wanda yagane me takeji a raaka na karshe gabaki daya akansa tay adduarta.



bayan ta idar ta koma kan gado ta dan rufe ido amma kuma fuskar Javeed dinne ya kuma bayyana mata kamar tumbin dare. can Sai ta tashi zaune tare da pillow akan kijinta Tanamai tambayar kanta Shin haduwarta da javeed anya bazai iya zama jarabawa agareta ba ko wata rubutaccen kaddara? in ba haka ba meyasa zuciyata ke yawan bugawa akansa can ta koma tadan kwanta Amma kafin baccin yazo ta dam dafa zuciyarta da hannunta biyu ta ce ya Allah! Idan wannan mutumin da nake yawan gani ne masoyina na asali to kayi mini jagora. Amma idan zuwansa rayuwata wata fitina ne ka kore min shi daga zuciyata kar a dalilinsa na cutar da Adnan. tana fadin haka tay salatin annabi snn ta shafa snn ta fara kkrin tayar da

43 / 52