Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

NUR FIRDAUS Imanin 'Ya By Anne-Aurora

Author :  Anne-Aurora Category :  African Stories & Novels

Chapter   30 / 52

87K to 90K   out of 155.7K words

arabian coffee, taga gashin idanunta suma bakakene dogaye wara wara dasu ga lips dinta dakenan karami dan tsut dashi pinkish peach colour da yakara haskaka kyallin fuskarta da bata shafa mai komi ba. gefen fuskarta shatin dogayen sajene lub lub a kwance duk dama kanta na sanye da bakin hula, kunenta babu ko dan kunne sai wata manne kana ganin yarinyar basai amfada maka ba zakasan tana da suma, kayan jikinta da komi nata saida razia ta duba tamusu cikakken kallo dan bana tsammanin akwai wani wanda ya taba karewa nur firdaus irin kallon kwaf kwaf da razia abu ta mata acikin dan kankanin lokaci.



sede kuma tunda taji babanta yanata musu bayanin yadda mutuwar bazata yaxo ya raba nur firdaus da mahaifinta dayake matukar kaunarta sai kuma jikinta ya danyi sanyi sosai sabida akwai ababen tausayi dayawa aciki.



Razia tana da gigin miskilanci da taurinkai amma bata taba hadashi da kaskanci da walakanta jama'a ba. Snn best part of her shine tana paying attention sosai ga Addininta duk dama a kasar waje din take karatu, awajenta ta san cewa addininta nada muhimnci ba kamar yadda wasu suke kallon Addinin islam a matsayin addinin kauyanci da takurawa ba. She is ambitious abt so many things in life musamn ma film ko harkqn fashion dan arayuwanta tana son kullum taga takai wani babban matsayi a careerta a duniya da za'a na buga misali da kwatance wa mata da ita.



a fuska dai zakayi zaton Razia mace ce mai rawanin girman kai sabida tana da wann zubin miskilanci da rashin sake fuska ga kuma wnn kyantan da yanayinta da' ya kai matsayin ace tayi mulki da izza ma uban kowa dashi sai dai ita hakan duk be rufe mata ido ba dan muddin ka samu caurage din iya shiga rayuwarta zaka gane cewa she is d most wildest and kind hearted being u wll eva meet in ur life.



saidai ganin nur firdaus sosai ya dan tabata taciki duk dama tasan akwai alaqa na jini atsakanin su but she is sumhow conflicted taya ma zata jata ajiki bayan ita kanta tasan taji kishin daya kasance Nur din tanada wasu abubuwan da yazo dede da nata wasu ma yafi natan wanda datake tinkaho dasu kamarsu kyau, kyan jiki ga dogon gashi, ga wani dan uban sanyin aji da kwarjini dake fallasa kansa atattare da ita,she honestly dont knw weda to like her or not yet, sabida ganin nur yasata taji kamar her personality has meet it challenge.



haka nan har suka gama cin abincin cikin raha iyayen suka tashi suka bar wajen dan su tattauna, Razia Abu ce kawai batace ma nur firdaus uffan ba duk dama fuskarta looks normal and emotionless abt her.



komawa palor tay ta dan zauna ita daya tana latsa wayarta can saiga nur firdaus ta karaso wajen



Miskillalliyar Ajiyar zuciyar da Nur ta saki shi yasata juyowa a dan takaice Suna hade ido nur ta dan sakar mata murmushi mai sanyi snn tace "salam alaikum, Hi sis. kallo daya Razyn ta mata snn ta dauke kanta tanamai kawar da idanunta can gefe like she dont even care, dan haka ko murmushi bata iya mayar mata ba.



Nur ta dan tsaya ta rasa me xatay sai can razian ta dago kai ta kalleta cikn sanyin kyabe baki tace " Sit. zauna mana...kin xo kin tsayamin akai...



ahankli nur ta taho kafafunta harna yar hardewa tazauna a dan dofane kanta na kallon kasa tsabar yadda razian ta kafeta da wani irin bold nd piecing looks kamar wani abu na daban take kallo ajikinta.



after like 3 scnds of awkward silence tsakaninsu nan razy ta ajiye tsadadden wayarta akan cinyarta takalle sunkuyayyn kan nur snn tay karamin murmushi

ahnkli tace "Cousin sister huhn? Nur tana dago kai taga razian tamika mata hannu a sanyaye nur ta kama hannun nata ahankli sukayi musabaha nan ne razian tadanne komi aranta tay ma nur firdaus din ssnyr murmumshi snn tace " "i Am Razia Abubakar ciroma. friends call me Razzy, in law schl i am B-razzy, bt you can call me Razia Abu. calmy Nur tay nooding snn tace "got it,I am Nur firdaus haroun ciroma,i am pleased to meet you Anty razia...ahnkli razia ta kwace hannunta cikin katseta tace A'a, no tags pls waye Anty kuma?Razia abu is enuf, kidanga cemin Razia kinji..i am still in my prime u knw.. nd i love my name.



kallonta nur ta dingayi tana murmushi sabida burgeta dataji razyn tayi musmn yadda take wani irin daukaka kanta da wata iryar sanyin kasaita da tsananin wayewa.



dan shirune ya ratsa wajen sai can snn tace "so Nuriii, How old did u think you are? cikin sake ajiyan zucyan bazata nur tace "uhmm, i am 17.. i think. razy ta juyo ta mata wani irin kallo cikin dan kwalo ido.. "haa 17?, bt u look bit matured for ur young age kin wani tuttula kaya ajikinki kamar wata matar aure,bt its good sha, i bet ure a virgin ryt??



wani iri nur taji atake dan bata sn me take nufi da hakan ba dai kawai ta sauke kanta kasa tay shiruuu batace komi ba.



ita kuwa razy tafadi hakan ne sabida mamakin yanayin dataga tsantsan modesty da kuma sanyin nitsuwar nur din wanda ya balain kasance mata kamar wani sabon abu nadaban da bata saba gani a wajen yara yan 17yrs din ba dake ita a kasar waje cikin turawa take rabin rayuwarta.



dan tasan wann age din ne ma teenagers like her age sukejin kansu suke kuma fallin tashen balaga.



kafin nur ta dago kai taga wai har razia ta mike tsaye, suna hade ido ta daga wayarta ta saka a kunne snn tace "i got to go, Excuse me. daga nan bata hira tacewar nur din ba tahaura sama kan step walking calmy and majestically nur tadinga binta da ido harta bace ma ganin ta dan bata taba ganin yadda tsantsan aji, kwarjini da wayewa yake fallasa kansa ajikin mace kamar yadda yake kwaranya ajikin razia abu ba.



dan ajiyan zuciya ne yakufce mata takalle agogon hannunta ganin tara saura ta mike tsaye ta karaso wajen iyayen nasu ta samesu sunata waya da lawyernsu akan ko za'a barsu su rufa mata baya gobe a wajen gasarta amma haka fir aka hanasu.



acikin sanyin ladabi ta rusuna snn tace musu zata tafi.



saidai Daga yanayin yadda dukansu suka amsata kai zakasan sam basuji dadin tafiyar da xatayin ba, bayadda suka iya the case file againts them bai basu damar shiga rayuwarta ba harsai ta kaiga cika 18yrs old wanda lkcine da ta mallake hanklin kanta bisa tsarin kundin shariar bature sann zata iya deciding dakanta but for now haseena ce take iko da yaranta and she forbade any one daga familyn ubansu ya kusancesu sabida shaidoji data gabatar wa kotu cewa zasu cutar mata da yaranta kamr yadda suka cutar mata da mijinta.



hankalin hjy sa'adatu da na hajya bilki sosai ya tashi ganin lawyer yace musu bazasu ko samu daman halartan wajen gasar nur firdaus goben duk dama su ba jininsu bane. Alhaj Abubkar kuwa dama already ya riga ya danne xafin abun aransa dan yasan haseena tafi tsanarsa fiye da kowa a dangi kuma tana jirane yay wani abu game da yaranta ta lalata masa sunansa akoina.....



kusan duk duniya babu wanda yakaishi jiran yaga nur tacika 18yrs din,sabida ya nuna ma haseena ita bakomi bace a duniyan nan dan yasaka aransa zai kwato yaran dan uwansa ya rainesu har ya aurar dasu wanda alkwari ne daya masa tun suna yara amma haka haseena tay amfani da surkullenta na political influence ta hanashi cikawa..



tun yanaganin abun nata kamar bazai taba yuwa ba yanaji yana gani hakanan sharrin bakin haseena yazo yafi karfinsa dan a farkon abunma kamar bazai taba hakura yabarta da yaran ba amma dake kowa yasan haseenan ta kware wajen iya zubar ma mutum da dukkan mutuncinsa akanson ranta shiyasa yay haquri akan case din wanda haqurin nan ya jima yana masa ciwo da radadi aransa dan gani yake kamar rashinshi acikin rayuwar nur da layla ai kamar yaci amanar dan uwansa harona ciroma ne..



Badon ransu yaso ba suka haqura suka fara bankwana da Nur firdaus kowa na mata nasiha akan tay haquri wanda tun tana murmushi har ta fara hawaye sabida sun tausasata sosai da kalmomi masu sanyi.



Nan hjy bilki ta debo kudi sabbin yan dubu dubu na 100k da turmin zani me tsada da original turarrukan meduguri kala kala guda biyar masu azaban qamshi dake ita kanurice ta bawa nur din harda wasu turarunka gashi dana wanka,uwargidan sa hjy sa'adatu kudade kawai ta debo ta bata one rapper na dollar notes da golden sarka me tsada da wata hadadden red nd golden mayafi set yake da clucht purse da shoes dinsa ayar jakarsa. sun mata goma na arziki snn suka babbata haquri duk jikinta saida yay sanyi, Alhaj abubakr ciroma yace shida kansa zai kaita har hosteln din matansa sunata mamakinsa dan sunsan baya tuka mota dakansa musmn da daddare but it seems he wants to speak privatly da yarsa nur firdaus sai

kowadai ya nuna ya fahimcesa.



wajajen 9;15pm suka rako Nur har bakin kofar mansion dinsu lkcin zasu wuce kenan saiga me aiki ta fito da wani karamin jaka

kai tsaye ta mika ma nur tace madam razia tace inbaki" da mamaki Nur tay murmushi snn ta karba jakar cikin sanyin murya tace ace ma razian ta gode.. iyayen sosai hakan ya musu dadi. daga sama can razia na rike da waya a kunnenta tana hangosu ayayin da takekan bawa babban kawarta me suna MOLLY labarin tsaban kyaun da kuma nitsuwa datagani awajen cousin sistern ta nur firdaus, bawai dan hakan ya wani burgeta ba saidan kawai tasha mamakin ta ne sosai, dacan ma batay tunanin bata komi ba kawartan ce tayta cusa mata raayin akan tabawa nur din wani yar kyauta. tana daga sama tanata kallonsu dan itama mamaki ne yaso ya rufeta ganin wai babanta zai yi tuki dakansa da daddare.



9.30pm saura cikin babban lexus jeep dinsa dayasha tinted suka kamo hanya aciki ya rike stiring yana tukasu ahnkli suna hira, yayi yayi domin nur tagaya masa abubuwan da haseena take musu amma haka taki sam ta furta masa komi sabida tasan duk abunda ta furta anan zai zame musu babban rikici sann haseena zata kara tsanarta bana wasa ba.



shikuma aransa yasan dolene kawai haseena ta watsar da rayuwrsu sabida yanayin yadda yasan tale daukaka political career ta sede kuma dayaga nur ta shashantar da maganan sai kawaide yahaqura dashi ya cigaba da bata gwarin gwiwa tare da gaya mata cewa kofarsa abude take duk sanda taji tanaso ta dawo hannunsa da zama ita da layla zai iya zame musu uwa da uba snn zai karesu daga duk wata ukubar haseena.



nur dai batacewa komi saidai tay murmushi, sosai yaji dadi data masa alkwarin zata sake nemesan, har bakin karamin gate din wajen hostel dinsu ya ajeta snn ya debi kudi yabata yaciro golden card dinsa dake dauke private numbersa yace ta ajeshi safe sabida wata rana snn karta bari kowa yasan tazo gidansa dan karya zama mata tashin hankli.



ya mammata nasiha yayita ta tuna mata da kalaman mahaifinta da yadda mahaifinta yake matsanancin sonta, yayi alfahari da ita har Allah ya dauki ransa, sosai ya mata nasiha akan ta cigaba da rike kanta da mutunci, snn tatuna mahaifinta will be very proud of her duk inda yake snn suma suna tare da ita. sunkai minti sha biyar suna magana kafin suka rabu dan koda ta kama hanyar hostel kuka marar sauti kawai takeyi tana tuna rayuwarsu ta baya cikin sauri tarungume kayan tsarabarta tana tahowa batama kula da uban tsoron da takeji na kar masu gadin hostel su kamata ta fito gari a wann lkcin ba.



kafin kace wani abu hartakawo gate na hostel ana daf zaa rufe kuwa ta samu ta shiga a sadade sabida karfe goma na dare yay. jikinta a sanyaye tashiga dakinsu da sanyin sallama hannunta rike da manyan ledoji guda uku na gifts dinta kudaden da aka bata kuma ta sakasu acikin jaka,isowarta kenan ta samu kawarta jadida hartay bacci, kallon gadon layla da aysha tay dats empty duk sun jibga bargo akai zaka dauka suna nan kwance acikine, a hankli ta sulale gefen gadon ta zauna tay shiruuuu dan saida tayi zaman minti goma cikin kakalo makanta nitsuwa sann ta iya tashi taje tawatsa ruwa tafito daure da towel akirjinta, ko shafa mai batay ba tajawo akwatinta da jadida ta riga ta shirya musu tahau creating space ma gifts dinta dan tasan gobe daga an gama hidima zasu bar kaduna sukoma abuja,



rabi ta raba turaren ta aje wasu awaje dan ta deba ma kawayenta sauran kuma ta zuba ajakar layla tare da kudin da kawunsu ya basu shima ta raba musu shi tsakiya ta aje mata nata ajakarta, ita kuma ta aje dollars din da sauran kudin dayay saura. sai 100k da hjy bilki ta bata tacire na yin sadaqa da wanda zata dan bawa kawayenta goben.



sauran tarkace duk ta zubasu ajakarta, ya rage na razian ne kawai dama bata bude ba dake a cikin wani pack yake a rufe, harta fara kkrin bude pack din sai kuma Adnan ya fado mata arai. jikin ta sanyaye ta ta jawo wayarta dan tasan ba lafiya ba ace Adnan dinta rabin ranta bai nemeta yau ba gabaki daya sai in dan wani abu ya faru dashi. ta dade cikin tunanin hakan itadai batagane komi ba amma kuma sam sam hanklinta yaki kwanciya da shirun nasa gabaki daya.



aje pack din kawai tay ta haura kan gado juyi kawai takeyi da wayarta a hannun ta all this while tana kokonton sake danna numbersa datayi saving da habibi da'iman=ؘÜ,tanata kallon lambar tay wani lamo da sassanyar murmushi, dan inta tuna yadda yake bata komi nashi in suna hira, his mind his soul his spirits he is so soft like an angel,bata taSa ganin mutum mai kirki da kuma saurin shiga rai irinsa ba.



ajiyar numfashi ta sauke rungume da pillownta a kirji.."she wonder what he is going tru right now danta lura yana son maman shin nan sosai, ahnkli ta kuma lumshe idanunta tana mai masa addua at same time wani tu™ikin damuwar rashin samun shi awayar yana damun zcyrta sosai,.."what if he needs me right now,.,zuciyan ta na fadin hakan ta mike zaune tanannade kanta a tsakankanun cinyoyinta cikin jin wani azaban damuwa akan adnan"..



jin abun na neman hanata bacci wayar ta dauka tayi dialling lambarsa this time ya shiga yy ringing saidai har ya katse ba a daga ba, after like 3min sai shiru, dataga baibiyo bayan ™irantan ba saikuma ta karajin damuwan nata akansa ya tsananta



wani abu aranta yanata ce mata Adnan babu lafya and maybe is her turn to be there for him today to be suportive nd comforting.



saida ayanzun dare ne wayarne kawai tasani mafita duk saitabi ta damu tunani kala kala ya shiga gittawa a kwaklwanta sai can ta sauka ahankli ta nufi bathrum ta wanke fuskanta ta da ruwan sanyi snn ta fito snn tadan ji dama dama .kara kwanciya tayi da wayar a hannu ganin kamar yin tunanin bazai ficce ta ba kawai ta bude message ta soma rubuta masa sa™o.





wajajen ™arfe daya saura na dare daga can lodge dinsu na kasar waje Adnan yana kwance amtukar takure akan lallausar gadonsa ya dan lumshe idonsa kamar marar lafiya cikin tunanin mezaice wa Nur firdaus gobe dan bakaramin sawa yay aransa cewa zaizo mata wajen hidimar rufe gasar ba, cos he believe she is going to win kuma yanaso ace ya kasance tare da ita a wann lkcin domin ya nuna mata tsananin son dayake mata da yadda yake alfahari da ita. yau da sassafe ya dauki jakarsa da zumudi zai bar london akan zaizo nigeria ya ma nur dinsa bazata amma haka mamansa tabata rai tahanashi motsawa karshe ma dai tasaka masa tsattsauran security da suka hanasa motsi gabaki daya sashensa ankulle tasaka anyi restricting movemnt dinsa na ranar wanda tsabar fushi da haushi da abun yabasa ko abinci bai iya sawa acikinsa ba kuma har yanxu bai sauko yay magana da maman nasa ba, iyaka kalamanta na kaskanci da cin fuska akan soyayyarsa da nur firdaus sune sukayi ta damunsa aransa dan bakaramin kuntata masa yau tay ba.



tuntunin nan akwance yake yanata juyi cikin tunanin yadda zai tunkare nur firdaus da wann maganan dan gani yake kamar zata saka ran ganinsa awajen hidimarta gobe tunda baizo kadunan tare da su ba, yana bude ido around 2am na dare wayarsa tayi haske da kamar bazai dauka ba yadaure yana dauka wa kuwa yaga sa™on tex messege dinta ya shigo..



kasa iya daurewa yay jikinshi harna rawa ya bude text din yana gama karantawa yay wata kayattacen murmushi mai mugun taushi, mi™ewa daga kwance yay ya jingine gadon bayansa da pillow sannan ya hau rubuta mata amsa

after like 2mins tana rungume da wayarta a kirjinta taji ™arar shigowar sakonsa itama da sauri ta farga ta bude tafara karantawa sai tasha mamaki sosai dataji cewa wai "He is fine".. cikin sauke ajiyan zuciya me nauyi ta rubuta masa wani sakon, "_..just wanna let u knw dat i miss u trout the day, tunda nidai yau baka tuna dani ba ko.."_ sakon nata yana shigowa ya bude tareda kai wayar kan goshinsa ya buga kadan yarasa mesa shibai iya irin karyan nan na masoya ba, atake sai ya rubuta _"can i call u now habibty..please?_

saida tadan ja snn ta maida masa amsa aikwa saiga shigowar ™irarsa sharply bata daga ba sanda ta dan karasa shigewa cikin bargonta ta lullube jikinta har izuwa kan ta snn ta amsa wayar a hankli cikin sanyin murya"tace salam habibi, wani irin maraitaccen ajiyar zucya ya saki snn ya lumshe idonsa sosai

yace..wasalam rabin raina, afuwan nasan nayi laifi but can i go ahead n xplain myself? "dan shiru tayi..shima bai kara cewa uffan ba,wani karamin shiru ne ya gifta tsakaninsu sunadan shakar nunfashin juna,cikin wani irin kasalliyar yanayi mai fitowa da maraitaccen shauki da son yaga ya sakata magana yace waime ya hanamin amaryata bacci ne yau?..bakinta tadan turo gaba a

30 / 52