Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

NUR FIRDAUS Imanin 'Ya By Anne-Aurora

Author :  Anne-Aurora Category :  African Stories & Novels

Chapter   24 / 52

69K to 72K   out of 155.7K words

ta dauka ahankli cikin lumshe ido tsammmm tare da dauke numfashinta cak, tace oh my God

Nur a ina kika samu wann qamshin turaren



nan jadida ta fara shunshuna kayan sosai har tazo tagane ashe a hannun nur ma kamshin yake fita dede inda javeed ya riken wani shegen daddadar qamshin turarensa na mufasa noir ya kama wajen ya mannu da fatarta..



wani irin bugawa kirjin nur yai da mugun karfi tarasa me zatace sai uhmm uhmm mm jadidah batace komi ba tajuya tabarta a tsaye taje takawo mata ruwa ta bata tryng to calm her self down, bayan tasha ruwan tadan ri™e gaban goshinta ahnkli snn tace ya salam..i cant believ i was soo caried away, dat man is sooo..ta fadi hakan cikin wata bataccyar shauki tanamai lumshe idanunta sosaiiii cikin wani irin rikitaccyar yanayi mai tsananin wuyar fassarawa.



ahnkli ta furta batai tsammanin jadida taji ba sai taga jadidan ta kafeta da ita da ido ta na murmushi, da sauri tadan dauke kai,. nan jadidah tay krmin dariya babe kodai kin hadu da Adnan dinki ne kike boyemin?"did he left his mum in london and flew to you? ehhh masoyan asali laila and majnun



da sauri nur tace no no a'a ba shi bane.



da mamaki jadidah tace hmm to why are u panting bazaki fa bar nan batare da kin gaya min komi ba.



wani nannauyar ajiyar zcyace ya kufce mata tanajin kamar duk wani hanyar jini dakebin sassan jikinta yana neman daskarewa.



zamar da kanta tayi ahnkli jikin gadonsu tanamai lafar dakanta dataji yana neman yin mata nauyi saitaji gaba daya jikinta tayi laushi jikintan yayi wani mashak ya mutu murus duk tabi ta langwabe fuskar ta sake tamkar wacce batada laka, aynzu duk wani kofar yin tunaninta a toshe yake babu abunda takeji ajikinta face sauyawar yanayi mai rikitarwa jin kamar bazata iya boyewa ba ta kalli jadida cikin ido ganin itama ita take kallo ahnkli tace i met sumone jadidah, its kind of complicated but he is too damn handsome to be true baki gansa ba ne JD i froze like zaifa iya kasancewa gamo nayi kuma gashi naje na maresa sabida ya rike min hannu na..and i think the smell on my hand is his scent..ta karashe maganan kamr zatay kuka



cikin gwalo ido jadida tace "u slaped him??



cikin fashewa da kuka me sanyi tace 'i swear nd am so scared ryt now jadida na banu what if he is not human being and i called him an ass wipe.



jadida ta kara gwalo ido waje tace what???



ganin hankalin nur ya kara tashi saikuma ta riko hannunta tace its okay kidena kuka, so what if he is not human being, kawai ki gayamin asalin meyafaru daga haka zamu gane ko shi din mutum ne ko ba mutum ba.



nan nur firdaus ta share hawayenta tun daga farko ta fara bawa jadida labarin javeed, da wani irin mamaki taga jadida na famr kyaklkawa mata dariya., "oh my god ure so funny nur, amma dai zanso nagansa bantaba jinki kina describing wani haka ba lallai kin kalleshi kam..weee huu huhu am dyieng to meet a real life mafia...ure so lucky nur...da karfi nur ta kwace hannunta tace "jadida are u mad?? ya ina miki maganan serious kina dariya

wllh acikin makabrtan muka hadu kikasan ko daga daya cikin grave din nan ne ya fito??



jadida ta kara fashewa da dariya tace "no i am not mad, kawaide kece haba nur just chill, inda ace yana son ya rama marinsa da by now yasa an samoki kuma ba ghost ko aljani bane tunda bai hadiyeki awajen ba...nd you knw what, i just love the way you described him..its giving like love at first vibe...



baki a sake nur ta dinga kallon jadida like dis girl is insane, nan ta mike tsaye tace ke naga alaman babu amfanin magana dake

its really really pointless talking to you...



tsaye jadida ta biyota

tace okay fine, amma dai karki bari hakan ya dameki cos is nothng kawai kin mareshi ne sabida yataba miki hannu shikenan, sann kuma karki fadawa kowa most espicially laylah. cikin sauri nur ta kalle jadidahn snn tace and why not?



jadida ta kyabe baki ahnkli snn tace "have secrets of your own nur. i knw u love her amma bakomi bane sai ta sani..keep dis one as a secret kinji.



shiru nur tay tanamai tuna yanayin behrvrs din layla na kwana biyu musmn akan Adnan kawai sai ta gyada kai batace komi ba. cikin sauke ajiyan zuciya jadida tace kije sallahn ki dawo mun zo da taliyar murji da manja daga gidansu

antyn aysha karkiji badai qamshi ba,nur kinsan kuwa bamu bi schl bus ba? sneaking fa mukayi muka bi bayan motarsu malam bello aka shigo da mu shiyasa duk muka dauka kinbisu ne sai kuma muka ga baki nan ashe kinacan da mystery guy dinki



nur firdaus tace hmm u guys are criminals amma ya akayi malam bello yazo wajen aida yasan bama nan da mun shiga uku yau.



jadida tanemi waje ta zauna snn tace maybe they called him, kin san yamma already yay ga tension na security Muna daf da wajen mukaga duk an gama shiga, shikuma malam bello ya debi su ameer da su maryam da'awa anashi motar saina dauka ko kinacikinsu ne saida mukazo naga ashe baki nan.



cikin sauke ajiyan zcya Nur tace thank god they didnt notice kedai bari naje masjid inna dawo sai muci abincin nafara jin yunwa.



tana kammala fadin haka ta bude wadrbe din hostel din ta dau™i gogaggen milk colour hijab ta zura ta fice taje masjid ta samu har su laylah sun fara kkrin yin shelar nemanta sai gata nan

ta iso..



da sauri layla ta karaso da fuskar damuwa muryanta cike da shagwaba tace Big sis ina kika shiga inata nemanki



nur tay murmushi me sanyi ta rikota aysha tace kinje kin buya awani waje kina bitan karatu ko, see nur ure going to win this in sha Allah, i have no daubts.. se ki dena sakamana hawan jini ko...dukansu sukayi dariya ahnkli nur firdaus tace toh ya isa kunsan dai masallAci ba wajen hira bane, so lets focus on prayers

and i promise bazan saka muku hawan jini ba..dariya sukayi suka karaso ciki nur tay sallahn magrib tay ishai, tay bitar qur'ani kadan around 8:30 pm suka dunguma suka dawo hostel ahanya suna ta bata labarin gidan antyn aysha da sukaje ita kuma duk sai ta kasa ce musu komi gameda haduwarta da javeed

duk dama its amusing her har cikin ranta amma tuna maganan jadidah yasata tay shiruuuuu batace musu uffan ba



Suna shiga hostel suka samu jadidah ta gama kimtsa musu ko ina sabida bayan nur itace me tarbiya sosai acikinsu dan kowa saida ta gyara masa gadonsa yay tsaf ta fetsa turare ma kwanansu ta shimfida musu dadduman cin abinci komi ready suna zuwa aka wanke hannu aka fara cin abinci ana hira ana dariya..sama sama tay chat da adnan shima din bata gaya mai taje makabarta ba

bare tagayamai meyafaru, dama can ita ba me far far din magana bane, but cemata da jadida tay she shud be having secrets of her own yasa taji kamar hakan ya zauna dede da ra'ayinta. besides tasan adnan yana da tsananin kishi, iya halinsa kawai dayake bata tsoro kenan, he is very violent in kishi ya tabashi fada yakeyi bayaji baya gani, dan yasha fasa ma yara kai akanta da abu me rauni, wai tun lkcin ma basukai haka ba knan.



ranar da wuri nur ta gama chat dashi ta haura sama kan gado domin baccoli danta samu karfin tashi da full energynta dake gobe ne zasu fara gabatar da gasa,



kwanciya tayi a riginge tanata juyi da tunani har batama jin surutun yan dakin, can ta lumshe idanun ta jin wani asirtaccen sanyin dake ratsawa daga windownta harta cikin zcyarta wanda bata taba jin irin zuginsa ba wani rikitaccen yanayi ne maicike da sarkakkiya yake shigarta,a take ta dukunkune kanta tay tsammm saiga fuskar wannan mutumin acikin idanunta wanda ayanzu take kallon halittarsa zar zar zar dashi acikin kwayar idanunta tamkar ma hotonsa ta dauko da cameran idonta tana kalla ahaka har bacci yay awon gaba da ita..



*****

washe gari da safe ranar asabar da misalin karfe 9.am a cikin wani hadadden office din likita mai dauke da kayan gwajin lafiya na mata (gyneacologist) acan saman office din an rubuta Dr surayya muhammad.



mrs Haseena ce zaune akan kujera cikin wata shiga ta alfarma tanata kallon Dr. Surayya wacce ke fuskantar ta da fuskar mamaki dakuma takaici. Bayan da ta gama duba takardun gwajin da aka yi mata, tajefa mata su kan tebur sannan ta kalli Haseena kai tsaye.



"tace Haseena ke kusan ince yar uwarta ce tunda mun jima muna tare, kin san in zan baki shawara bawai a matsayina na likita zan baki ba sai dan domin zai amfane ki," Dr. Surayya ta fara magana cikin kallon reaction din haseena data wani tsime tana kallonta yayinda ta gyara zamanta da shirin jin wani karin bayani da ita kanta ba son ji takeyi



"Na san da haka Surayya shiyasa banje wajen kowa ba nazo wajenki dan kece kawai zaki iya rufa min asiri, Amma me yasa kike son ki hana ni yin wannan abun? waidama Ba ni da hakkin haihuwa ne?surry i told you this was mine and my husbands idea i just want to knw idan zaiyu...



Dr. Surayya ta numfasa Babu wanda ya ce ba ki da ryt akan haihuwa amma fa dole ne ki yi la akari da yadda jikinki zai iya daukar nauyin ciki a wannan shekarun naki haseena. IVF yana da hadari musamman ga mace mai shekaru 46 yar gwagwarmayan siyasa irinki, dan Hakan na iya jawo miki matsaloli kamar hawar jini, ciwon zuciya, ko ma rasa rai yayin haihuwa."



Haseena ta yi shiru na wani lokaci zuciyarta cike da tantama gashi sam bata son taji ance zata mutu cikin sauke murya kasa tace" haba surayya Ke kanki kin san yadda rayuwata take wallhi Ina bukatar wannan haihuwar saboda... saboda..sai kuma tay shiruuu batace komi ba.



Dr. Surayya ta girgiza kai. "Ni Ba zan hana ki ba amma dole ne na fahimtar dake ki fahimci hadarin da ke tattare da hakan Ba wai kuma kawai batun samun haihuwr ba ne batun rayuwarki ne, Haseena Shin kin shirya fuskantar hakan?.."



Haseena ta runtse idanunta zuciyarta cike da ruWani. Ita dai tasan cewa ba za ta iya janyewa daga wannan shawarar ba sabida tanaso taga ta faranta ma sadaat Rai batason wani abu ya rabasu har abada.



saidai maganganun Dr. Surayya sun fara bijiro mata da tunani da bata so ta yarda da su. tana shirin budan baki kenan wayarta yafara ringing nan taciro sa ajaka ahnkli ta kalli screen din sunan Hajiya Mariam Shehuri ne ke bayyana akai, nan ta kalle fuskar Dr surayya snn tace kawata can you excuse me?? Dr surayya tace sure,nan da nan haseena ta mike tsaye cikin sauri jikinta har na rawa ta dan ja gefe kadan kafin nan ta jefa wayar a kunnenta Cikin sauri zuciyarta na harbawa da fargaba da kuma sha'awar jin abin da za'a ce mata.



salam alaikum ranki shi dade.



"Haseena!" Muryar Hajiya Mariam ta fito da wani irin izza, "Albishirinki?"



Haseena ta dan lumshe ido tace goro ranki shi dade.



yanxu labari ya sameni cewa Muna da sama da kashi saba'in cikin Wari na ™uri u acan fadar zabe, snn Hajiya Farida Bala ta gama shan kashi ynxu haka an tabbabtar min cewa Komai na nasarar wann kujera yana hannunmu Alhamdullhi.



Wani irin murmushi mai tattare da dadin nasara take ya bayyana a fuskar mrs Haseena tace "Masha Allah! Wannan ai babban labari ce hajiya..



"haha kibari kawai haseena ai duk karyan kada a ruwa fa take karewa Hajiya Mariam ta yi dariya cikin habaici, ke haseena Daga zarar an bayyana sakamakon zaSen nan toh komai ya ™are zamu maida hankli ne kan shirya auren d'ana Adnan daya nace zai auri diyar ki.



Haseena tadan jinjina kai jin ranta yay fari kal Da wannan damar da ta samu dan tasan da gaske zata iya mallakar komi inda ta rike wann damar ssai tana murmushi tace hakane ranki shi dade.. a hankali ta kuma cewa amma Gidana na Gwarimpa har yanzu yana kan mortgage ni duk shi Yafi damuna hajiya ina mai miki tuni zanso a mallaka min kafin auren nan.



"Kada ki damu haseena," Hajiya Mariam ta katse ta.



"Da zarar mun ci zaSe, zan biya miki komai ai nariga na miki alkwarin wann, Ke dai kawai ki tabbatar da cewa ba matsala daga gefenki musmn ma akan batun yarki da adnan yace zai aura dan bana bukatar wani publicity stunt."



da farinciki aran haseena tace in sha Allah babu wata matsala hajy nan ta hau gode mata, Hajiya Mairam din ta Wanyi shiru na  yan dakiku kafin ta ci gaba da magana, tace yawwa dama akwai wata yar matsala fa, malami na ma meduguri ya aiko ace min Wani yana bibiyarki. kuma yana zargin cewa ana bawa Hajiya Farida Bala wasu bayanai."



Haseena ta Wan yatsine fuska tace toh amma Wane ne yake bina?"malamin ya kama sunanshi?



kai tsaye hajy mairam tace "Mijin ki."



Take Zuciyar Haseena ta buga da karfi tace "Me?"..mijina kuma?



"Ba mu da wani tabbaci haseena amma malam akwai hannun wani kusa da ke yi mana kutse Kuma Sadat shine wanda malam yake zargi sosai.."



nan da nan Haseena ta dan daure fuska ta harWe hannayenta cikin jin bacin rai "Hajiya wallahi ba zai yiwu ba i knw Sadat ba zai iya cin amanata ba. yaro ne karami i make sure i study him shi babu ruwansa ma da harkan siyasata.



"Ke dai ki kula," Hajiya Mariam ta furta cikin katse ta. anan kuma zanta kkri har sai mun tabbatar da gaskiyar lamarin.



haseena tay shiru batace komi ba Bayan sun gama wayar ta ja numfashi mai nauyi Zuciyarta na raya mata cewa ba za ta iya yarda da wannan zargi akan sadat ba, sedai kuma ta san tunda aka fara hakan dolene tay wani abu aka sa ba zata iya sakaci ba, dan Idan da gaske Sadat yana aiki da makiya to komai zai iya rushewa mata.



Da wannan tunanin ta juya zuciyarta ta cika da sabon ™uduri na jin cewa zata bincike shi da kanta kuma a Soye



nan ta dawo office din taja kujerarta ta zauna tay shiruuu bayan wasu mintina kadan Dr. Surayya ta kalleta cikin kulawa tareda jingina kai da kujera tana famar nazarin yadda fuskar Haseena ke nuna damuwa da ruWani.



"Haseena, wai yaa maganan yaran ki ne?" Ta tambayeta cikin sanyin murya da son sakata magana.



Haseena ta Wan yi murmushi maras kuzari tace "Lafiya kalau suke surayya. Nur Firdaus tana can shirye-shiryen gasar karatun Al-Qur ani da za a yi a Kaduna sun ma tafi can, Layla kuma kamar kullum 'yar nayi na'am ne suna can tare.



Dr. Surayya ta gyara zama. "masha Allah, nur tay gadon ubanta yar albarka ce ina jin yadda ake yabawa da tarbiyanta agari nasan yanxu kam duk sun girma ko...



cikin basarwa da nuna rashin damuwa mrs haseena tace yeahh sun girma sunacan sunatayi kinsan fa ni ba yar son shiga tsabgar yara bane,



Cikin kyabe baki Dr surayya tace tbbas nasani but haseena lets talk serious, in kinje aikinki Kinadan waigowa dan tabbatar da lfyansu kuwa, Kina ma da lokacin su? Ko dai shegen siyasa da damuwar miji suka maye gurbin uwa da ke kula da  ya yanta marayu?"



Haseena ta sauke numfashi tana jin nauyin zancen, kedai surayya Kin san irin rayuwar da nake yi, kinsan wahalarsa Ba abu ne mai sau™i ba bare ince miki zan hada aikina da wani rainon yara ."



Dr. Surayya ta kalle ta ido cikin ido. tace hmmm dat is very typical of you, yanxu de mu aje maganan nan agefe., ranar talata zanje kaduna kuma ranar ne zasu rufe gasar, To me zai hana kema kiWauki wannan damar sai mu tafi Kadunan tare? Gasar nan ba ™aramin abu ba ce a rayuwar Nur Firdaus. haseena dan Allah na rokeki Ki jeki nuna mata cewa kina tare da ita wllh hakan zai ™arfafa ta sosai."



kai tsaye Haseena ta girgiza kai tace Ba zan iya barin Abuja a yanzu ba surayya. kina gani dai Hajia Mariam ta kira ni yanxu tana bu™ata ta, kuma kinsan mun kusa mu ci nasara Idan na bar siyasa a yanzu komai zai ruguje min..."



Dr. Surayya ta dafa hannunta da sanyin murya tace haba Haseena duk wata nasara da kike nema a duniya ba ta da amfani idan  ya yan ki ba sa jin kaunarki aransu, yau Idan Nur Firdaus ta lashe gasar nan waikina so ta tsaya ne a matsayin marainiya saboda ba kizo kin nuna wa duniya ke cikakkyar uwa bace agareta? haba haseena, Kiyi tunani akai mana just this once inkinje me zai cinyeki abu na rana daya ana gamawa ma zamu dawo Abuja tare da su.



Haseena ta yi shiru, zuciyarta na dan bugawa da sauri dan Kalaman Dr. Surayya sun tsunduma ta cikin tunani mai zurfi, can kuma sai ta katse tunanin tareda daure fuska tace toh naji Allah ya kaimu ranar inkin shirya saiki neme ni amma duk tsiya dai gaskiya aranar zamuje mu dawo. Dr surayya tace in sha Allah, daga nan suka tsunduma wata hirar dake anjima ba ahadu ba har kafin nan suka rabu.



Ali akilu road kaduna state 4pm..



A dede ™ofar shiga babban mansion din jifa jifan da sukayi rakiya wa hajy mammy gidan malaminta suka tsaya domin sauketa,nan ™ananan masu aiki da suka rage suka fara tattara mata kayanta suna kaiwa ciki, hjya mamy ta sauka ahnkli da jikin tsufa tana takawa ahankli da azhkar din yamma abakinta.



wani irin shiru gidan yay sabida Dr simran ta ishe wokers din da gadara uwa itace matar gidan saidatasa kaf maaikatan suka gudu suka dena wulgawa.



Bayan dan tafiya kadan hjy mammy takaraso cikin main house, tana shiga cikin hamshakin falonta kuwa ta tarar da Dr. Simran din a zaune tay kane kane tana shan pink smoothie cikin shigar doguwar rigar gucci matar hannu mai shegen tsada.



suna hade idanunsu waje guda Simran din tawani taso da sauri tana baza murmushi da baikai har xuci ba a yangace tace"Hajiya Mammy Alhamdulillah kin dawo

24 / 52