Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

NUR FIRDAUS Imanin 'Ya By Anne-Aurora

Author :  Anne-Aurora Category :  African Stories & Novels

Chapter   51 / 52

150K to 153K   out of 155.7K words

tozarci da muzantawa haka ya dinga dawo mata tay kuka bana kadan ba.



yaudai babu kalar tunanin da batay ba,



Mrs haseena tuni duniya ta zame mata sabuwa dan duk kudin na zasu isheta har ma su fiddata akunya inta juyasu zuwa naira, ga wann shegun jeweries da bridal veil da shoe da clutch komi ya zama musu deidei yau din nan sun samo abunda zai fiddasu a kunya saidai harynxu mrs hasina bata dena jin matsanancin mamakin inda nur ta samu wann uban kudin hartake ajesu a jakarta batare da saninta agidan ba..



Da yamma suka shirya tsaf suka bar gidan ita da layla, mrs hasina takai result ma hajy mairam dake nuna cewa cikin Nur firdaus din yama fita shikenan kuma komi ya dawo musu dede aka tsunduma hidimar biki, gobe zaa fara event za'ama laylan wankan lalle da turare na yan meduguri.



anata shiri basu dawo gidan ba sai wajajen 12pm na dare tazo ta samu nur firdaus tana tattara duka important files dinta tana saka su agefe, basuce ma juna komi ba sai can layla tafara cema nur ai yanxu kam cikin shegen dake jikinta ya zuba sai ta dena guilt tripping dinsu da emotional face ta saki jiki ayi hidimar biki dan kar ace sisternta batazo bikinta ba.



aidama itace tasha gaya mata cewa bazata rabu da ita ba komin rintsi inde hakane kawai gobe tabisu wajen sakun lallen.



laylah tanata zuba maganganu yadda kasan nur bata dakin haka tay banza da ita har tagaji tay shiru.



hanklin nur sosai ya dan dawo jikinta da taji cewa ai dukan da hasina tay mata tayta zubar jini jiya yasaka cikin ya zuba atleast now she can make a move dan tagama tunani taga babu amfanin zamanta da su inba de kashe kanta takeso tayi da baqin ciki agidan ba.



washe gari da asubahi

ta dauki wani jakarta na baya, acikin wanda Adnan ya taba kawo mata dayajeshi dubai siyayyar sport wears na shi. gucci schl bag ce me kyau amma tana da dan xurfi da girma. tana kammala karatun qur'ani ta kwashe muhmmn files dinta na schl da komi data ware tunjiya da dare ta shiryasu acikin jakar da duka inne wears dinta da farin rigar javeed.



snn ta hada duk wani abu da babanta ya siya mata sai few abaya datasan kudin mrs haseena bai shiga ciki ba ta saka aciki basufi kala biyar ba,sauran duk wanda tasan idon laylah nakai tabarsu a wadrob din da dukkan wani abu data mallaka nakayan duniya da layla take saka mata ido akai tana kishinta, harma da wanda mrs hasina ta siya musu duk bata daga ko daya ba. acikin manyn hadadun hijabanta ma befi kaloli biyu kawai tadauka ba sai wanda ta'aje akan gado zata saka ajikinta.



karfe takwas ta fita basu san inda ta nufa ba, da kafa taje cikin wani 24/7 jeweries store a anguwarsu

takai tallan wani abun wuya da dan kunne na gwal da ta siya da kudinta da aka bata kyauta awani gasar makaranta..



kudinsa ya kama 400k a lalace, bata damu ba ta karbi kudi ta saka a hijabinta ta boye snn ta siya abinci da pain relievers around 9:30am tadawo gidan saida ta tabbata suna can dakin snn ta boye kudin acikin kaya tay wanka taci abincin snn tasha magani ta shirya kanta tsaf...



can ta ta fito daga ita sai jakar bayanta sai handbag dinta, kai tsaye taje dakin Mrs Haseena wanda ko sallamarta bata amsa ba,itama hakanan taqi ta gaisheta tace musu wayarta tazo abata.



nan Haseena ta mike tsaye da mamaki tace wa nur ina zataje da jaka? tafara kkrin zata kwace jakar tava meye aciki, nur ta ture hannunta da karfi

cikin tsaurin ido ta fara mata magana da wani irin busashen ido

tace karsu taba mata jakarta ita bata dauke komi nasu ba suje daki gasucan kayan duniyar datay yawon karuwanci ta samesu tabar musu su siyar suyi hidiman biki in hakan zai saisaita musu zuciya.



then she begin to tell mrs hasina everything na yadda ta samu kudaden da kayan datake zaginta akai, yau nur taki ta rufawa layla asiri, duk wani abunda ya wakana wanda Mrs haseena bata sani ba nur ta fayyace mata tace mata kuma bata damu da ko ta yadda da ita ko bata yadda da ita ba, itade kawai wayarta tazo karba zataje kaduna dan bazata iya zama da uwar da take nuna mata tsana a fili snn take tozarta ta ba.



baki bude kuma akangare mrs hasina ta dinga kallon nur ganin yadda yau ta tsaya agabanta take gaya mata magana masu zafi with no filter or ounce of respect, nur ta bushe idon ta gaggaya ma mrs hasina kalaman da inaji harta mutu wasu kalaman bazata iya mancewa dasu ba.



..sann ta dada jaddda ma mrs hasina cewa tabbas mijinta saadat shine ya aikata musu hakan kota ki, kota so wata rana zata gani.



layla duk ta rude da hayaniyarsun tana ta kuka tana karyata nur amma ko ajikinta.



kusan cacar baki sukeyi da mrs hasina

akan karda nur taje kaduna inma barinsu take so tay taje yola kawai wajen didi amma nur ta tubure tace inda taga dama zataje kuma wallh ba'a isa ahanata ba.



ganin baza'a bata wayarta bama yasa ta wuce afusace ta fara wargaza kayan mrs hasina tana watsi dasu a tsakar dakin kamar ba nur din ba har saida ta tsamo wayarta acikin wani drawar tadauki abunta batay wata wata ba ta kama hanya zata tafi



har waje Suka biyota mrs haseena tanata masifa kamar zata daga gidan...



wallh nur inkika fita agidan nan karki sake ki sake dawowa dan bazan karbeki ba...



dama can baki da kunya gashi yau halinki na boye ya fito fili, butula, duk abunda nake miki da rashin kunya saki sakamin? har nine kike cewa zakije kaduna konaki konaso to dan ubanki kije su kasheki kamar yadda suka kashe ubanki...inhar kika tafi nide wllh karki sake dawomin..



nur firdaus bata ko juyo ta kallesu ba

kuma ko hawaye bata sauke ba itakanta tasha mamakin kalar bacin ranta tun jiya kawai tasa aranta mrs hasina ta mugun tsanarta hakan bazai taba canzawa ba inta cigaba da zama da ita wata rana hala zata kasheta gara kawai ta tafi inda zata rayu.



har bakin gate layla tabiyo nur tana ririketa tana kuka tafara rokonta wai karta tafi kaduna shikenan yanxu bazata tsaya taga aurenta ba.



a fusace nur ta fincike hannunta a tsawace tace wani auren naki da kullum sai kince min ina miki baqin ciki akai layla? tou ai nice kika dauka a matsayn babbar maqiyanki kuma be kamata na kasance aranakun farincikinki ba dan haka kiyi aurenki lafya

kayan duniya kuma gasu can nabar maki

a daki, all the shoes jeweries harma da abayan dana saka a kd..take them. let them give u the happiness and love dat i cudnt give you.



tana gama blasting din layla ta fita abunta

mrs haseena ta dinga ihu tana masifa tana kwala mata kira kamar kanta zai tsage yau bakaramin mamaki nur firdaus ta bata ba dan bata taba tsammanin haqurin yarinyar nan zai kare hartay behving haka ba.



nur kuwa har saida tay nisa takai bakin titi sann ta fashe da wani irin kuka me radadi dan abunda tay kusan abune me matukar wuya ita bata iya raini da rashin kunya ma babba sai yau gashi tay ma mahaifyarta

sann ta raba kanta dasu fatan ta shine kar Allah ya kamata da lefi, saidai kuma in ta tuna cewa Allah ya baka cikaken dama raba kanka ko nisanta kanka da mutanen da suke cutar dakai sai taji wani sanyi.



ta tari mota kenan ta kunna wayarta wanda har hooking yake yi tsabar sakonnin da suka shishigo da sauri ta dudduba da bataga wanda yay kama dana javeed ba sai kawai ta maida wayar jakarta ta aje. basu ko yi nisa ba taji tafara bleeding jini na shirin wanke mata kafa duk sai taji tamugun tsorata haka tafasa tafiyar taje ta kama wani motel 20k per night ta zauna anan ta hada ruwan zafi ta shiga ciki ta wanke kanta snn tasha maganinta da tazo dasu, Rigar javeed datazo dashi ajaka shine mata kadai marar nauyi haka tacire tasaka ajikinta tasaka pad ta dan kwanta tay bacci me dan nauyi sai yamma ta farka taga jinin be dauke duka ba tasake wanka snn ta fita ta siya abinci tazo dakin ta zauna taci





ata daya bangaren kuwa tunjiya mutanen sanata farida suka samu rigar sadaat daya gama wankuwa sa jininsa ya turmushe sa datti ya bushe da kyar ma suka gane nashi ne, tun anan ka tabbatar mata cewa da wuyane in sadaat yana raye babu tantama tunda an samu rigarsa ajeji to hala har anjima da kashe sa. bakaramin baqin ciki da haukan gaske sanata farida tay ba, ji tay kamar asarar datayn ya mata yawa, ita bata ci kujera ba, bata samu ta tozarsa haseena yadda ranta ke so ba gashi kuma ta rasa shakikin yaron gidanta sadaat. zafin hakan yasa kawai ta bawa ussy oder akan duk inda akaga yaran mrs hasina abisu a akashe su karma abarsu su raye..



yau da safe ussy ya fito farautarsa saidai bai samu damar samun mrs hasina da layla ba dan tunda Nur firdaus ta rabu da su suka gama jimamin su na lkci kalilan snn suka share kashinta suka tsunduma hidimar biki dan mr haseena ta hau dokin zuciya tace sam bazata sake bata lkcinta akan ryuwar nur firdaus ba tunda tazabi taje wajen dangin ubanta in sha Allah bazata taba nemanta ba harsei tazo ta nemi gafaratta a abuja.



abun nadan sosa mata rai amma ta danne dan yau akwai kudi da abubuwan duniya a hannunta sai kawai ta tsunduma wajen harkan karya da nuna ma dangin Adnan cewa itama watace dan ta goge abun kunyar datay awajen karban kayan lefe da akaga tanata barin kudi akan layla duk sai anata mamakinta.



ussy yasan be isa yaje ta wajen hidiman ba sabida security dan haka yazo kofar gidan ya tsaya daga nesa ya samu dede maman saeid ta fito zataje gidan mama hauwa



samunta yay da magana yana son ya san ko nur firdaus haryau tana kumshe a gida koma ta mutu.



maman sa'iid tace masa ai yau din nan da safe taji suna hayaniya nur firdaus

ma ta wuce kaduna

wajen dangin ubanta

har maganan da be tanbayeta haka ta dinga zuba masa



yaji dadi sosai data masa wann barbadan harya dau dubu talatin ya bata kyauta sann ya tafi



tun ahnya ya gayama sanata farida cewa ai nur bata tare dasu mrs haseena awajen biki dan haka itace first target, nan danan kuwa tay amfani da mutanenta aka fara neman nur basu samu excat location dinta ba sai can da yamma ana daf da magrib nan da nan kuwa yazo shi gate djn motel din ya tsaya yana jiran dare ya dadayi da wata silencer ajikin bindigarsa yadda zai harbeta ta mutu basai anji karar bindinga ba.



ita kuwa nur tun bayan dataci abincin yamma takara shan magani tay wankan ruwan zafi takunna Data a wayarta tanata kallon hidimar bikin layla sai hawaye dake zuba a idonta, ga wajen ya dau shiru har wani tsoro tsoro takeji na shiga jikinta not knwing dat tun data bar gidansu she is being surounded by spys na javeed mufasa dan suna ganin signal din trackerta ya dawo suka hau aikinsu na bibiyarta duk inda tay motsi batare da saninta ba.



wajajen 10pm bacci ya fara damunta ta aje wayar ta saka karatun qur'ani tayi shiru tanaji dede wann lkcin ussy ya fito cikin sanda baiko lura da spy suna binsa ba



dake sun kware atake suka gane cewa akwai bindiga ajikin sa daya acikinsu ya kira javeed

ya sanar masa cewa sunga wani guy dat looks suspicious a motel din har sun dau hotonsa sunyi bincike sunga cewa stray dog din politcal rival dinsu mahaifiyar nur firdaus ne.



atake javeed yace musu inhar wajen nur ya dosa karsu bata lokci kawai su harbeshi.



aikuwa kamar antunxira su hanklin ussy akwance ya shiga ta baya zaije dakin nur ya kasheta



baiko hankara da takun gayun abyansa ba yana miko hannu zai saka master key yabude kofarta yaji saukar wata shegiyar military riffle akansa



koda ya juya ya kalle gandama gandaman gayu masu damatsu ajiki saida yaji cikinsa yay kuuuu dan kamar zaitsaki fitsari ajikinsa haka ya tsomare jikinshi yana rawan dari zai magana dayan gayen yace masa "shushhh..kakr sake ka jawo hanklin madam lets go to your car ryt now.



dama gashi awajen duhu duhu ya aje motar tasan, suna kaiwa wajen dayan gayen ya wani buga ma ussy gindin bindigarsa aciki sai dayay aman jini atake



suka matseshi suka fara tambayrsa meyake nema da yarinyar bakinsa na bari yace shima besanta ba cewa kawai akayi yazo ya kasheta by her mums political rival...yafara rokonsa akan su masa rai karsu kashe shi. aikuwa da bindigarsa daya saka silencer suka karba sai dau dayan gayen yaharba masa shi akansa, suka dauke gawansa cak suka bude booth dinsa suka sakashi aciki



nan ya kira javeed ya gaya masa, javeed yace su rubuta sako su hada da gawar akai ma sanata farida let her know dat in ta sake turowa akashe yarinyar nan she will be the next person to die and he wont mind wasting her entire generation wnn gargadine ya mata danma wai ita mace ce.



aikuwa yadda ya fadi haka suka aikata sanata farida tana zaune a daki da dare aka kirata da wayar ussy akace tazo ta amsho sako akofar gidanta...tana fitowa ta samu motar ussy a bude amma babu kowa aciki ta mugun tsorota tayta dube dube har takai both a mugun kangare ta koma baya dataga gawan ussy da takardan gargdi ajikinsa a mugun tsorace ta dauka ta karanta..



tsabar ta tsorata acikin daren ta tattara inata inata tabar nigeria saida taga ta tsira snn ta turo sako acikin yaranta suka dauki gawan ussy akaje aka toni rami aka binneshi..



Duk wann hidimar da akayi nur firdaus bata san anayi ba, bayan data gama jin karatun qur'aninta she slept peacefully hartay mafarki babanta yazo mata sun zauna suna tahira har tana famar kyalkyala dariya.



hakan yasa washe gari koda ta farka taji zuciyarta yay fayauu batajin wnn damuwa da baqin cikin dake kumshe a ranta.



koda tay wanka sai taga jinin kamar ya dauke duk da haka dai ta saka pad abunta ta dawo dakin ta shirya tsaf snn ta dauki wani baqin abaya plain acikin jakarta ta saka

tanata tunanin ko zata kira kawunta ne ta sanar dashi zuwanta amma kuma tana tsoron karyace mata a'a sabida case dinsu na kotu dan takulla aranta cewa inhar be karbeta ba, da ta dawo gidan mrs Haseena gara ta kira lambar hajiya mammy snn taje gidanta ta roketa akan kome aikin shara da wanke wanke a dauketa xata mata har sai ta cika 18yrs din.



haka dai ta qudura aranta kafin ta fito taje ta siya abincin kryawa

ta zauna taci bayan nan tadan kwanta akan gadon kadan sabida ciwo dataji cikinta yafara mata



ata daya bangaren kuwa Alhaj abubakr yana kwance akan makaken italian bed dinsa har sun gama waya da Agent din Sultan kenan cewa yau da karfe 2 bayan azhar jirgin helicopter zaizo ya dauke Razia izuwa mufasa's private yatch in lagos



komi da suke bukata an tanadar musu tun jiya da dare yay ma yarsa Razia nasiha akan kartaje ta bashi kunya agaban mutane inde tana daraja shi



ya aje wayarsa kenan sai ga wata baquwr lamba na kiransa da can kamarma bazai dauka ba amma sabida yanayin yau din kawai saiya dauka



bakaramin shock ya shiga ba daya ji muryan Didi wato mahaifyar mrs haseena, acikin mutuntawa suka gaisa dan sun balain jimawa basu ga juna ba. hanklin didi ne be kwanta akan nur firdaus ba, sai tana ganin kamar inda aka bar nur agidan ita kadai taredasu mrs haseena hala zasu kasheta da baqinciki



tunjiya ta nemi lambarsa kawai ta yanke hukunci gara ta gaya masa meke faruwa dan yazo ya dauki yar dan uwansa kafin hasina da yarta layla su kasheta.



alhj abbkar yana tambayarta ko lafiya

kawai Didi ta fashe masa da kuka..



jin haka yasaka call din a recoding dan dama yana neman duk wata evidence akan mrs haseena ai kuwa Didi ta fara zuba masa labarin halin da ake ciki bata boye masa ko da full stop ba, tafara rokonsa akan yayi haquri yazo kawai ya dauke nur ya tafi da ita dan itakam tanaji ajikinta cewa nur bazata iya zama agidan can akarkashin haseena ba. tsaban kuka da rokon da didi tay masa har saida jikinsa yay sanyi ya dinga bata haquri yana lallashinta yace mata in sha Allah yau ko aiki bazaije ba zaije ya samu lawyer su tattauna zuwa yamma ko anbashi dama ko ba a bashi zaije ya dauko nur ya dawo da ita hannunsa. godiya ta dinga masa sede suna gama wayar ya fashe da kuka muryan sa harna fita waje jin tsananin baqin ciki da tashin hankalin daya rufesa dayaji wai barayi sunshiga gidan hasina sunma nur firdaus fyade hartay cikin shege kuma ana zrgin wai wawan mijin hasenan ne ma...



salati ya dingayi yana kuka a dakin kamar karamin yaro yana maganganu yana cewa dan uwansa ya yafe mishi...jin ciwon zuciyarsa na kkrin tashi yay sauri ya jawo maganimsa ya sha harya dan samu yay bacci kadan.



matansa sunzo dakin suka samesa ahaka amma gabaki daya ba sugane masa ba, dan Alhaj baiya bacci da safe, duk dai basusan baqin ciki da damuwa bane kawai yasakashi shuting down din kansa for a while..



koda ya farka wajajen karfe goma baiwani kulasu ba kawai ya shirya kansa yawuce offishin lawyernsa kai tsaye sukuma matan suka tsaya akan raxia domin a shirya ta duk sunyi tunanin ko hala sune suke bata masa rai akan maganan su na mufasa duk sai suka damu dake sun san yana da ciwon zuciya.



wann yanayin yasa razia ta haqura ta saki jikinta tay shirinta me kyau danma ta faranta ma babanta rai yau din professionals ta kira suka shiryata tsaf wani kankararen steve meden flowing gown me stones da furrs suka kawata jikinta dashi takalminta da jakarta kuma duka na alexander MC queen



gashi de english wears ne amma babu wani waje ajikinta dake bude face fuska da hannu da kafarta satin scarf me tsada aka

51 / 52