Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

NUR FIRDAUS Imanin 'Ya By Anne-Aurora

Author :  Anne-Aurora Category :  African Stories & Novels

Chapter   22 / 52

63K to 66K   out of 155.7K words

alatu grizzy brown sleek morden furnitures ne kawai aka kawata ko wani daki da falor dashi babu wani hayaniyar tarkace, kalar da akayi amfani dashi na grizzy brown yasaka sashen ya zama yanada high sense of tranguility nd relaxation.



motar yana tsayawa still saida dr simran ta dau tsawon mintina biyar tana baza shan qamshi snn ta hakura ta sauko kallo isasshe batay wa tsakar gidan ba ta saka kai izuwa hadadden sashen data saba zama idan sunzo kadunan da hjy zuby.. tana shiga tun a falo ta fara cire kayan jikinta tana yardawa nan kasa ayayin da take cat walking like a goddess cos she think she has the perfect curvy body dan haka batajin shayin komi.



Kai tsaye ta shiga cikin part din dake cikin babban main mansion din, private Apartment ne mai dauke da private parlour nasa, sai fankacecen princess theme bed room da walk in closet inda ke lode da kayan sawa na designers kala kala masu dan karan tsada da kyau wanda ake ajiyewa sabida baki.



Daga nan akwai small passage da zai mika ka wajen wanka wanda shima tamkar daki ne mai zaman kansa, Tana isowa wajen tasa hannu ta wafce clean pink towel ta dora akan kirjinta ta fada wajen wanka sai kace ba itace ta bata awanni tana wankada kwlliya a lagos ba.. cikin sanyin taku ta fada cikin hadadden ruwan wanka tanamai sauke ajiyar zuciya jin an hada matashi so warm nd relaxing daidai yadda jikinta yake muradi...



nan ma Sai da ta kusa hour guda cikin bathroom babu abinda take sai Wake wake daga karshe dai ta hakura ta fito daure dawani sabon towel din sai kuma daya datake goge kanta dashi..



gabaki daya hjy zuby

tasaka angaya ma maaikatan gidan cewa simran zatazo dan haka tana fitowa ta tarar da mai aiki tsaye wanda tana jin fitowarta kirjinta ya hau bugawa da sauri



daga kai tay suka hade ido tay saurin kawar da nata snn ta sunkuyar dakanta cikin ladabi ta ce"



Ure welcome back maam"..



Da wani irin yanayin kyaliya ta wuceta kmr bataji taba dan kaf nuna musu takeyi kamar itace matar javeed mufasa and she is an important part of the mufasas



kasar wuya ta ja tsaki A kasaitance tadan lumshe idanuwanta slightly tana tunanin kayan daya dace ta saka dan tasan hajy mamy ya gargajiya ce

jininsu tuntuni bai wani hadu ba.



gashi ta tsane duka maids din gidan dan maids suna irritating dinta dan kuwa sosai takejin kyamar su arayuwanta....



da kakkausar murya marar sanyi da dadinji tacema maid din ta matso kusa ta fara tayata shiryawa



Da sauri maid ta matso kusa ta fara aikinta na kimtsata tanayi tana kafa mata dokoki akan karta taSa mata nan kar ta tabamata can oil ta shafa mata a jikinta daga sama har zuwa kasa tayi mata light nd cheek make up ta fetsa mata turarrukan ta data saba shafawa masu tsada da dadin qamshi sai da ta gama sann tadauko mata doguwar riga na atampa amma haka fiiir taki sakawa wai yana mata nauyi..



karshe dai wata figgyr Dior gown iya gwiwa ta saka with small skiny short daga ciki ta sakale kafafunta cikin fenty sleepers mai laushi ta dau wani shararar veil tadan yafashi akanta wanda takejinshi kamr an mata dole.



Bayan mai aiki ta kammmala aikinta cikin sauri ta fice sai can da kamar mintina arbain sann Dr simran othman din ta samu fitowa



kamar bazata taka kasa ba take tafya tana isowa katafaren falonsu taga dayar maid dinsu a tsaye dauke da chemonille tea set a hannunta..



'Gud evening maam"



maid din ta fadi vry politely



Da miskilallen kallon banza tabita snn tace

"maaam??



mai aikin tay saurin sauke kanta kasa ahnkli snn tace sorry Mrs.. mufasa".



wani mahaukacin tsaki taja mata harta karaso kasa tay wucewarta agabanta tana wani irin masifa.



mtss can you imagine i have to be reminding ppl on how to Adress and respect me in dis house.. hmm an rainani agidan nan wallh kuma duk sai naci ubanku...



mai aikin kuwa tun dataji simran tana masifa jikinta tuni ya soma rawa duk da sude basuji ta inda akace musu Javeed ya aureta ba, amma duk sanda tazo haka zata takura kowa sai wai dolene sai an kirata da mrs javeed mufasa ko mrs mufasa izuwa ynxu su kansu masu aikin sunsha gulman cusa kanta datake ma javeed din har sun gaji..



Muryan me aiki na dan rawa kanta na kallon kasa tabiyota har falon inda take tsaye



"Mrs mufasa ur tea, gashi kiji in baiyimiki ba sai in koma in sake wata...cikin dauriya da danne tsoronta tafada tana mika mata mug dake dauke da nicely made chemonille tea.



Shiru simran tay na tsawon mintina kaman bazata ma amsa ta ba kusan mintina goma maid din tana tsaye bata motsaba can dai ta amsa ta Dan kai cup din saitin bakinta bata sha ba ta shunshuna tana juyowa dashi ta watsa mata tea din a fuska a bazata snn ta mike tsaye Tin kan ta farfado daga raxanan datayi tabikanta da hatsallen masifa tana cewa "How dare u how dare u make dis boring tea who asked u for it?



"Am..am.. sorry ma'am its my mistake..pls forgive me.



cikin rolling eyes simran tace maam again?? please "Get lost.. "cikin daka mata tsawa tay comanding dinta a rikirkice maid din ta kama hanya zata fita da ihu tace

mata get me a Black cofee in 5 scnds nd dont waste my time. yar iskan yarinya..



jiki na Sari maid din tawuce kitchen ta kunna coffe maker fuskanta jike da ruwan shayin da tsabar tashin hankli bata samu daman sharewa ba.



A cikin sauri sauri ta hada mata black coffe ta kawo mata ta samu dede ta kammala magana da hajiya zuby kenan, kafin nan ta karba..cikin yatsina

tace how comes banji motsin kowa agidan nan ba. cikin ladabi me aikin ta gaya mata cewa ai hajiya mammyn bata jin dadin jikinta kwana biyu kenan tana mafarke mafarke tana firgita yanxu haka tanacan gidan dabbobinta ana mata jinya sai gobe jumua ne zata dawo.



tunda taji hakan sai tasaka aranta cewa hala da javeed kenan zasu dawo, dan haka ta dada bararrajewa dan bazata iya zuwa gidan dabbobi ba tana da kyankyami zasu iya sakata amai.



anan gidan hjy mamyn

tay zamanta abunta tanamai baza dan banzan mulki da isa wa masu aiki tana kuma shirya yadda zata tarbe javeed agoben in suka dawo.

#SURAYYAHMS

08060712446

#BOOK1#

[24/02, 09:38] Anne-Aurora>Ø‹Ý: NUR FIRDAUS....22

SURAYYAHMS

Daga conference hostel kuwa rayuwa medadi tareda nishadi su nur firdaus sukeyi tareda kawayenta, tun ran da sukazo akanyi hira ayi wasa da dariya time to time haka nur zata zame taje can baya inda babu surutu snn tay bitan karatunta ko tay waya da adnan acan agefe dan tun da jadidah tafara saka idanunta sosai akan reactions din laylah akan adnan sai abubuwa dayawa suka fara bayyana musu a fili, wanda yajefa nur firdaus cikin tunanin ko da gaske ne laylan bata son soyayyarsu da adnan.

gabaki daya sai ta dan rage daukar wayarsa agabansu yakansace chatting kawai suke yawan yi dashi batare da tabari laylahn tana lura da hakan ba....

aranta tabari akan sai sun koma abuja snn zata lallabi laylan taji meye matsalarta da Adnan privately batare da tasako opinion din kawayenta acikin maganan ba sabida batason ta zargi yar uwarta akan namiji snn bata son laylan taji babu dadi.



*******Friday...

yau ranar jumu'a da asubahi javeed ya farka da wani irin zazzabi me tsananin zafi sosai wanda da kyar jikinshi ya dena rawa..



bangaren nur firdaus anan kuma bayan sun karya aka sanar musu cewa karatun gasa ta farko zaa fara saurara ne da ga ranar asabar daga 8.00am- zuwa 8pm na dare, amma sabida hidimar sallar jumu'a da sauransu yau din za a kaisu cikin gari suyi yan gaishe gaishe da ziyara ma excos din su.



they where all very excited sabida baba driver yace musu duk su shirya da wuri yau zai kaisu babban masallaci suyi sallahn jumuar dukansu acikin gari dan kowa yaga gari kafin su dawo su shirya zuwa wajen gaisuwa.



Dan haka tun farkawarsu suka hau shirin fita da zabar irin kayan da zasu saka kusan dukansu sun fitone da abayu masu kyau kuma bakake.



javeed bai bari ciwon sa na daren jiyan ya bayyana wa kakansa ba sabida yariga da yasan maganin matsalar aransa.



Da safe tunda suka gaisa ya barta da likitan ta bai sake lekowa ba sai da ya gama shirinsa tsaf



wajajen 12 ya fito a kimtse Cikin sauri tareda ™warjini irin na soja,.. da sallama Javeed A. Mufasa yashigo dakin kai tsaye ya nufi gadon da kakarsa ke kwance. Yana sanye da wata pure black slim fit suit data mugun amsar jikinsa fiyeda da wadda ya saka jiyan as usual fuskarsa a da™ile yake babu alamar wata rauni ko damuwa sai dai idanuwasa suna nuni da wani nau in tausayi da ba a saba gani a tare da shi ba.



kallo daya yama likitan ta tashi cikin sauri da girmamawa ta basu waje, snn ya kalle kakarsa dake kwance muryansa atausashe sosai yace "hajiya likita ta gaya min cewa jikinki yay kyau yau. tana dan murmushi ta riko hannunsa cikin lumshe ido tace "Babu laifi jikina ya warware, all thanks to you. tana kallonsa da kulawa take maganan, Javeed ya dada dur™usawa kusa da gadon, yana saka hannunsa cikin nata kamar yaro mai neman nutsuwa daga wajen uwarsa. ahankli yace zan tafi amma ba lallai bane ki sake gani na.



cikin datsar numfashinsa tareda lumshe ido muryanta me cike da rauni tace "Javeed bana jin daWin zuciyata tun daga ranar da aka naWa ka Brigadier General. Na san da kaunar dakakewa aikinka da dakuma sadaukarwarka ga cigaban kasa amma ka san wani abu?"



yana kallontan amma ya mata shiru cikin sakin ajiyan zuciy tace ba ™asar da kake bautawa ce matsalata ba, tuggun Zubaida da Simran ne. Javeed ya dada yin shiru bai ce komai ba dan shi sam wayn kananan kwarin basu gabansa.

hjy mammy ta cirkita laSSanta tana kallon yadda jikinsa ke daWa samun ™amewa da girman basira duk dama tasan yana rayuwane da dumbin nauyin zuciya da kuma damuwa.



tace "Kai ba ™aramin yaro ba ne, Javeed. and very soon zaka kawo mana matar aure. Idan kana jin magana ta, ka zauna ka Wauki matakin kare kanka nide Ina jin cewa akwai wani abu da ke yawan faruwa a bayan idonka dan Zubaida ba mace bace da na yarda da ita snn yar uwartan can kuma tana da mugun nufi irinnata, ni dai na shaida hakan bana kuma fatar sharrin su ya shafe rayuwrka."pls do not trust them javeed, ta karashe magnan cikin tari me dan kara, nan ya dau goran ruwa ya bata tasha cike da kulawa snn ya dan kwace hannunsa anata alamun ba ya son su ci gaba da wann zancen..



adan takure da kuma yanayin basarwa yace hajiya karki damu ina sane da komai tun ma kafin a faWa min, kedai kidena yawan tunani akansu, duk wanda yake tunanin zaiyi wasa da ni zai sha mamaki nan gaba



dan shiru hajya mamy tay na dan wani lokaci snnn ta cirkita yatsun hannunta, tace "toh shikenan "Na yarda da kai amma bana son ka yarda da mutanen da suke kewayenka. "Ka sani, duk da kai soja ne, kana bu™atar kariya ta ruhaniya. yau ko gobe zanje ni wajen malamai sumin istihara da adduoi dan masu iya magana sunce Kada ka sake ka bar duniya tariga ka sanin kai waye ne."



Javeed ya lumshe ido dan Bai saba da jin irin wnn maganganun ba, ta Waga hannunsa a hankali to zan wuce ki kula dakanki. da sauri tace ka tsaya mana Javeed...acikin maraice murya tace jiyafa na maka mgana akan zuwa wajen gasa amma bakace min komi ba,..jikana ina sonka yi min alkawari cewa zakazo muje tare dakai dan Allah it wll mean alot to the family..ance min gobe ne yaran zasu fara gasa, sann marigayiya mamanka fa babban exco ce a wann organisation din nasu na kkrin daukaka ilimin addinin islama da karatun al'qur'ani musmn wa yara da suke tasowa. cikin murya me cike da rauni ta kallesa ahnkli snn tace please and please u shud honour her choices javeed nasan baka da lkci amma tunda dai sun gayyace mu yakamata muje wajen kodan sabida mamanka..



shiru yay baice mata komi ba dan saida yadau minti kamar uku kafin can ahnkli ya dawo hayyacin sa tare da bata amsar a murde.. yace zan dawo in ganki, Zan tabbata kin koma gida lafiya..yana furta hakan yajuya ya fice ayanyinsa na nitsuwa securitynsa suka rufa mai baya har waje.



bin bayansa ta yi da murmushi mai cike da godiya tasan tun da yace zaizo din toh zaizo, dan tasan javeed baya taba sabawa magananta it doesnt really matter if he says yes or no directly.



bayan tafiyarsa bada jimawa masu aikinta suka fara shirin kaita wajen malamai kamar yadda ta bukata dan tunda mahaifyar javeed ta rasu ta saka aranta cewa zubaida ce kawai ta kashe mata surkuwa wanda duk duniya takejin kamarna ita ta haifeta sabida tasota fiye da yadda taso danta Alhaj attah mufasah,



lkcin da mahaifyr javeed take raye rayuwa me tsafta da dadi sukayi bazaka taba iya tantance ko ita da surkuwanta ba yan uwan juna bane.



shiyasa mutuwar mahaifyar javeed din yafi mata ciwo fiye da yadda suke zato amma haka ta cije ta danne dukkan zafin aranta sabida lamarin ciwon kwakwalwa me tsanani da javeed yayita fama dashi dayake karami.



yau fiye da shekara talatin da shida kenan amma itakam tarike fushi aranta, tanajin bazai taba wuce cewa zubaida bace ta kashe mata surkuwa shiyasa duk sanda javeed din yazo wajenta toh sai ta gargadesa akan zamansa a lagos tareda su zubaida.



wata private masallacin jumua javeed suka wuce kai tsaye sede har sukayi sallahn zuciyarsa bai daina tunanin tarin maganganu kakarsa ba, ji yake kmr yana bukatar cikakken nitsuwa kafin ya iya yanke wani hukunci

akan request din nata

na zuwa wajen gasar

dan har yanxu bai san ko zai iya daurewa ya iya zaunawa acikin taron mutane irin haka ba cos most of his life schedules are really private and mysterios





aftr jumuat pryr basu bar masallacin ba har saida yay sallahn asr daga nan kai tsaye shida convoy dinsa guda biyar din suka wuce hanyar wata makabarta, wajajen 4pm saura na yamma suka iso wajen inda masu gadin harsun riga da sun saba in javeed yazo akan dan katse zirga zirgan masu shige da fice

dan shikadansa yake takawa da kafafunsa har ya isa inda kabarin mamansa yake while all his security men remain outside by the car.





a fanninsu nur firdaus

kuwa dukansu sunsha wanka sunyi kyau all in black abayas yau itace kawai batayi kwalliya ba tabar fuskarta soo natural and charming baka ganin komi sai baqin kajol data shafawa idonta yay baki da kuma chapette din ta goga ma lips dinta wanda baiya nunawa sosai shima.



bfr 12.30pm na rana suka fito daga hostel aka kawosu msallacin cikin gari bayan an idar da sallah aka fara zagawa dasu garin suna mika gaisuwa wa excos kowa yana saka musu albarka dan wani babban international islamic organisation ne a kadunan yake sponsoring din competion din tare da few secret indivisuals kamar top families irinsu mufasa's, king sujamal of hadejiya and safeey Allah foundation a abuja da dai sauran great great generational wealthy billionaire families wanda suka fi bada himma akan dukkan wata hidima na addinin musulunci.



gasar ya zama yana da muhmmci saboda ana kashe masa kudi sosai wajen shiryashi snn ana kuma bada kyautuka ma yaran da suka halarta masu dumbin daraja da ma'ana.



tunda suka bar masallaci yau gabaki dayansu basu huta ba gaishe gaishe da ziyara kawai suke kaiwa daga nan anguwan zuwa nan anguwan, wajen manyan xcos ana saka musu albarka

wasu suna kara musu karfin gwiwa akan abunda ya kawosu.



wajajen karfe 4:30 suka kamo hanya zasu bi hanyar da zai sadasu gida ta karshe

saidai sabida tension din insecurity da ake fama dashi kasa kasa agarin yasaka baba driver yayita zagaye dasu har yabiyo dasu tahanyar makabarta sabida samun cikakken tsaro.



lkcin kusan kowa ya gaji amma surutu kawai daliban suke anata hira a mota can basu hankara ba motar tay wani kara inda baba driver yay saurin jan burki suka sauka akan titin dake daf kusa da babban makabarta aka paker su..



sama sama nur firdaus ta bude lumsashun idanunta dan ita kadaice ta bige da bacci bayan ta toshe kunnenta da karatun qur'ani data kejinshi da earpiece dinta.



..motar yana jan burki tabude ido ayayinda taji jadidah ta dafa kafadunta tana cewa

"ki fito kisha iska ko abarki aciki tayan motar mu yay faci.



'ahankli nur tace subhanallah garin yaya...?? duk suka mike tsaye da yar jakar hannunsu aysha tana cewa toh Allah yasa dai yana da extra tire dan wallh nagaji ni yunwa nakeji..agajiye laylah tace Ameen ta riko hannun nur, har suka sauko kasa suka tsaya atare, laylahce tafara kallon kofar gate din grave yard din dan basu da wani nisa da wajen tace laaaaaa big sis kuga yau gamu ga wani babban makabarta...cikin katseta da wasa jadida tace "toh sai akayi yaya? badama kuga makabarta sai kun nunawa nur..



ikon Allah."ohh toh me hadin nur da grave yard ni ya su?? aysha ta tambya cikin tuntsirewa da dariya...



nur firdaus ta danyi murmushi tace kibari kawai aysha kinsan ko wani jummua a abuja nasaba nakan kai sadaqa maqabarta shiyasa in sukaga makarbata ako ina sai su fara tsokanata..



Dariya sukayi atare ayshan tace Lallai nur firdaus sai kace wata tsohuwa? kakata ce fa me aikata irin wann dabiar har wani burga take ma mutane wai taje makabarta kai sadaqa,nikuwa nace mata Allah sa wata taci karo da fatalwa su sakata gudu zata gane.. jadida da layla suna dariya, nur tace toh ai harkan samun lada babu wani tsufa ko yaranta..kaiwa sadaqa maqabarta yana da amfani bayan hakama ai da shi ake toshe wasu abubuwan ake kuma inganta wajen da yan uwanmu musulmai suke kamar kabarukan da suke fadawa ko rushewa ko wata matsala na security kunsan fa akwai grave robbers, ga natural disasters etc indai zaku bayar kawai kuzo muje tun yanxu mu bayar kuma kudan samu lada tun kafin baba driver ya gama gyara mana mota, dan naji ana cewa wai saima an

22 / 52