Author : Bilyn Abdull ce Category : African Stories & Novels
matan Tajwar? Shike kashesu?
Ko akwai lauje cikin naɗi a kashesun?. amsoshinku duk suna a
cikakken littafin nan na DAUƊAR GORA CIKI KA SHATA, dan
cakwakiyarfa yanzune ma zata fara😉 .
13
.........Ta ko'ina bayine masu hidima ga wannan basarakiyar
daula. Yo basarakiya mana, dan itace masarauta dake mulkin
ƴan ƙasa dama sarakunan ƙasar baki ɗaya. Sun sake wuce
gate na biyu inda anan ɗin ma dai katafaren wajene da
misaltasa babban aikine ga mai hasashe. Ta ko'ina hadimai ne
ke kaiwa da komowa maza da mata. Ga wasu irin gine-gine
na alfarma da ɗaukar hankalin mai kallo tamkar ba'a cikin
ƙasar Ruman ba. dogayen gine-gine ne da abaya sai dai su
hangosu daga nesa tamkar yanda suke iya kallon jirgi yayinda
yake keta giza-gizai. Ga wasu irin korayen shukoki tako ina
tare da shimfiɗaɗen lafiyayyen titi da za'a iya rantsewa yafi
kowanne titi dake a cikin ƙasar Ruman. Kasancewarta farin
shiga a ganin wannan shimfiɗaɗɗiyar daula saita fara tunanin
anyama kuwa a duniyar mutane take? Kokuwa dai mafarki
takeyi ne? Dan sam inda take yafi kama da anguwanin
ƙasashen turawan da a tv ne kawai suke iya ganinsu cikin film
ko labarai da makamantansu...
Har motocin suka samu wajen tsayawa aka fito da ita sam
ba'a hayyacinta take ba, bawai ƙawatuwa da tarin ƙyale-
ƙyalen da aka zubane kawai ke ɗibar hankalinta ba, akwai
wani ɓoyayyen tunani acan ƙasan ruhinta da ƙahon zuciyarta
mai alaƙa da tabbatar da abinda mutane ke faɗa akan Daular
Ruman ɗin...... Saukar sautin busar sarewa mai zaƙi da daɗin
saurare da ya fara tashi a cikin daular Ruman ya sauka cikin
kunnenta tare da katse tunaninta ya maidota hayyacinta.
Wannan saƙone dake isa zuwa kunnen duk wanda ke a cikin
masarautar cewar an iso da _Zawjata almilki_.
Tsawon lokaci sautin na tashi har sai da saƙon ya isa ga
kunen kowan da ake buƙata. Daga Iffah dai bata san
ma'anarsa ba, dan haka bata ɗaukesa komai ba. Sai ma share
hawayen fuskarta data cigaba dayi, dan har yanzu fuskar tata
na lulluɓe ne da hular ƙawatacciyar rigar jikinta da zamu iya
kira alƙyaba. Sai dai zuciyarta cike take da alwashi mai ban
tsoro ga duk wanda zai iya jinsa a kunne. Ta sadaukar zata
mutu, amma ba ita kaɗai ba harda Shahan-shan na Daular
Ruman, idan an hanata damar bayyanama duniya a ƙwato
musu ƴancinsu, sai ya mutu aga wanda zai cigaba da kashesu.
A karan farko ta saki murmushi mai ƙayatarwa, irin
murmushin data jima batayiba kuwa........
Babu wanda ta ɗaga kai ta ko kalla a cikinsu har suka
gama bushe-bushen algaitunsu dana sarewa. Cikin
girmamawa ɗaya daga cikin matan da suka ɗakkota ta matso
gab da ita.
“Ran Zawjata-almilki ya daɗe, nan shine sashen Malikat
Bushirat. Mahaifiya ga Zakin wannan daula Shahan-shan,
Uwa ga duk wani ɗan ƙasar ruman”.
A karo na farko Iffah ta ɗan ɗago idanu ta dubeta kaɗan
daga cikin alƙyabar, kanta a ƙasa yake ita a dole bazata iya ko
haɗa ido da ita ba domin girmamawa. komai batace da ita ba,
sai dai ta dubi katafaren ginin da ya tabbatar mata da
maganar matar. Idanunta ta maida ta risinar kawai batare
data nuna alamar tama jita ba. Abin mamaki bai nema tsaida
bugawar zuciyar Iffah ba sai da suka shiga wannan katafaren
gini, bayi sai zubewa suke akan gwiyawunsu tamkar wasu
masu neman gafara ko kuma Tajwar Eshaan ɗinne da kansa.
Zaman faɗa muku daula da dukiyar dake a wannan sashe ma
ai ɓata lokacine, dan haka na baku damar ƙiyastama
zukatanku kawai.... (Lol😉😋😆)
★Karan farko na tarihi, karan farko na rayuwa, yau ga
Iffah gaban *_Malikat Busheerat_*. Mace ta biyu ga tsohon
Tajwar Haysam ibn Abdull-Majeed. Mahaifiya ga Tajwar
Eshaan ibn Haysam Abdill-Majeed Shahan-shan na wannan
ƙarni. Hamshaƙiyar mace mai tsananin ƙyau tamkar itace ta
zaɓama kanta ƙyaƙyƙyawar surar jikinta da zubin halittar ta. A
kallo ɗaya da Iffah tai mata daga cikin hular alƙyabar jikinta ta
kasa sake ɗaga idanu ta ƙara saboda kwarjininta. Ta tabbatar
ta isa a kirata _Malikat_ (Sarauniya), Uwa ga fir'aunan sarki
kuma. Kishingiɗe take a ɗaya daga ƙayatattun kujerun
katafaren falon daya amsa sunansa daular duniya, wanda
kafin isowarsu cikinsa sun wuce manyan faluka da suma suka
amsa suna daular duniya bama ta ruman ba kawai. A gefe da
gefenta wasu matanne cikin shiga ta alfarma suma har su
huɗu, sai hadimai dake zagaye da ita kowanne da hidimar da
yake a gareta cikin matsanancin taka tsan-tsan da kai. Dan ko
wadda ke tare da ita suna shigowa zubewa ƙasa sukai jikinsu
har tsuma yake yi, ita Iffah har tsoroma suka bata tare da
mamaki mai girma na wannan ƙarfin iko.
Iffah dai na tsaye har sai da ɗaya daga cikin matan nan
dake tare da Malikat ta miƙe ta kamota ta zaunar ƙasa bisa
lallausan carpet ɗin dake a falon saitin Malikat Bushirat da
har yanzu tana a kishingiɗenta kuma ko sau ɗaya bata ɗago
ta kalla kowaba tunda suka shigo. Kusan minti biyu falon yay
tsitt babu wanda ya sake koda motsin kirki, sai ƙarar na'urar
sanyi dake tashi kaɗan-kaɗan da wani ƙamshi na musamman.
(To masu karatu inhar Malikat na'a haka, yaya shi kuma
Tajwar ɗin zai kasance kenan akan izza da mulki?🤔.)
Iffah da shirun ya isheta kaɗan ta ɗago idanunta ta cikin
hula ta saci kallonsu. Sai taga su duka har Malikat ɗin ashe ita
suka zubama idanu. Haka kawai tasha jinin jikinta, dan
kallone bana a santa ba, kallone dake buƙatar nutsuwa kafin
a bashi fassara. Kaɗan taja numfashin dake neman maƙale
mata a maƙoshi da ƙara yin ƙasa da kanta hular ta sake rufe
fuskarta ruff. A hankali, cikin son ɓoye rauninta da hawayen
dake neman kwace mata ta furta “Barka da yamma ranki ya
daɗe”.
“Malikat ta amsa miki, tare da maraba a gareki”.
Ɗaya daga cikin matan ta amsa a maimakon Malikat da har
yanzu batako motsa daga kishingiɗar da tayi ba. Sai dai ta
ɗago ƙyawawan idanunta farare tas ta sake zubasu akan
Iffah, idanun ta juya a hankali ta dubi ɗaya daga cikin matan
nan dai dake kusa da ita.
“An gama ranki ya daɗe”.
Matar ta faɗa da girmamawa alamar ta fahimci mi take nufi.
Tsam ta miƙe zuwa inda Iffah take, ta kai hannayenta biyu ta
kama hular alƙyabbar tai baya da ita, ƙyaƙyƙyawar fuskar
Iffah datai jajur saboda kukan da tasha abinka da farar fata ta
bayyana. Idanu Iffah ta rumtse sakamakon jin al'amarin a
bazata, ga wani irin harbawa da ƙirjinta yayi har sai da ta
ambaci (Hasbinallahu wa-ni'imal wakil) a zuciyarta sannan taji
numfashinta da yay sama yay ƙasa a lokaci guda ya daidaita.
Kaf hadiman ƙasa sukai da kansu, dan haramunne a garesu
kallon fuskar *_Zawjata-almilki_* kai tsaye. Yayinda Malikat
Bushirat ta motsa a karo na farko daga kishingiɗar da tai
idanunta akan Iffah. Kusan kallon mintuna biyu tai mata kafin
ta janye idanun cike da ƙasaitar masu isa, yatsun hanunta ta
ɗan murza suka bada sautin (ɗass! Ɗass!!!) har sau biyu.
Tamkar ƙiftawar ido hadimar dake tsaye riƙe da wani
ƙasaitaccen bowl kalar gold da adon stones masu ɗaukar ido
ta iso gaban Iffah da kanta ke ƙasa har yanzu tana ambaton
ALLAH a zuciyarta ta zube tamkar mai neman gafara. Kanta a
ƙasa alamar bazata iya kallon Iffah ba ta miƙa mata bowl ɗin
hannu biyu bayan wata a cikin sauran hadiman ta matso da
sauri ita kuma ta janye farin ƙyalle da aka yana a saman bowl
ɗin tare da murfinsa, tatacciyar madara fara tas ta bayyana.
Cikin rawar murya da tsantseni hadimar ta furta,
“Ya Zawjata-almilki! Wannan madara ce mai daraja daga
hannun Malikat domin nuna maraba da zuwa a gareki cikin
DAULAR RUMAN”.
Shiru Iffah bata da alamar motsawa, har hakan ya bama
duk wanda ke gurin mamaki har Malikat Bushirat. Tsahon
sakanni goma kafin ta ɗago. Manyan idanunta da sukaci kuka
har suka gode ALLAH ta zubama bowl ɗin tare da hadimar
dake gurfane a gabanta tamkar mai neman gafara. Kanta ta
girgiza a hankali tare da sake maidashi ta risinar. Cikin motsa
laɓɓanta a hankali tace, “Wannan karamci abin alfaharine a
gareni da nuna tsantsar godiya ga Uwa gareni dama ƙasar
Ruman baki ɗaya. Sai dai ina mai neman afuwar jinkirtamin
shan wannan madara sakamakon azumtar wannan yini da
nakeyi batare da nasan yau zata kasance rana mafi daraja da
alfarma a gareni ba”.
Kalaman Iffah da tasirinsu tamkar saƙar ƙudan zumace
cikin kuttu a zukatan duk wani mai numfashi dake a wannan
falo. A zahiri da baɗini kuma babu wanda mamaki bai
bayyana akan fuskarsa ba, saboda abune da bai taɓa
faruwaba a cikin daular ruman. Malikat Bushirat tai ƙyauta a
jinkirta amsa tare da biyo jinkirin da sharhin da babu gargada
akan harshen mai furtashi. Wannan abu yakai a kalla Iffah a
sake kallonta dan ko ƴaƴan gidajen sarauta goma cif da aka
kawo daular a irin matsayinta basu samu ƙwarin gwiwar ƙin
shan irin wannan madara ba. Hasalima kowaccensu da rawar
jiki take amsa ta shanye tas ta bada bowl ɗin tana mai
gurfana a gaban Malikat domin yin godiya. Ba'a matsayi
kuma kawai ba hatta a shekaru Iffah itace mafi ƙanƙanta a
cikin Zawjata-almilki goma sha huɗu da aka kawo gidan.
Ɗaya daga cikin matance ta zabura idanunta dake nuna
ɓacin rai akan Iffah. Sai dai abin mamaki Malikat Bushirat da
idanunta ke kan Iffah ko ƙyaftawa babu ta ɗaga mata hannu
alamar ta zauna tare da sakin wani ƙasaitaccen murmushi.
Nuni tai akan a rufe madarar. Ruf aka maidata yanda take
hadimar ta miƙe daga gaban Iffah da tunda ta sake maida
kanta ta rissinar bata ƙara ko motsawa ba.
A karo na farko Malikat ta motsa laɓɓanta, cike da izza da
ƙasaita irin ta manyan masu mulki. “A kaita masaukinta”.
Ƙasaitacciyar muryarta ta ratsa zuciyar Iffah tare da girgiza
gaɓɓanta cikin ikon harbawar jini. Sunan ALLAH ta ƙara
tsarkakewa a zuciyarta dan tabbas Malikat ta cika Malikat ɗin
babu tantama. Saboda muryar tata kanta barazanace ga duk
mai yunƙurin kawoma girmanta wargi da saka tsantseni a
zuciyar duk wani talaka dake a ƙarƙashin mulkinta.
“Ki huta lafiya, cikin aminci da farin ciki”.
Iffah ta faɗa cikin risinar da kanta alamar girmamawa
lokacin da take miƙewa bisa taimakon ɗaya daga cikin matan
nan. Yin hakan ya sake saka zukatansu a mamaki, ita kanta
Malikat Bushirat da kallon ƙasan ido ta bisu har suka fice. A
ƙasan ranta tana mai jin farin cikin samuwar Zawjata-almilki
data dace da gudan jininta tilo kuma Shahan-shan na ƙasar
Ruman gaba ɗaya. A ganinta lokacine daya dace tai yaƙi da
maƙiyanta masu yaƙar Zakinta a yanzu dake zagaye da su.....
★★Kamar yanda Malikat Bushirat ta bada umarni
amarya Iffah (Zawjata-almilki) an isa da ita sashenta dake gab
da sashen matan Tajwar Eshaan su biyu da har yau suke raye,
sannan kuma kusa da katafaren sashen Tajwar Eshaan da yafi
kowanne gini ɗaukar hankali da kayan kyale-ƙyale da
tsagwaren dukiya a cikin Daular Ruman harma da tsantsar
tsaro... Sashen Iffah ya kasance shima sashe dake ɗauke da
nau'in kayan more rayuwa da a kallo ɗaya mai karatu zai
tabbatar da sai dai Zawjata-almilki ɗince kawai kam ta dace
da zama a cikinsa. Kamar yanda al'adar take anyi rakkiyar
Iffah dake kan keken doki tare da busar sarewa mai daɗin
saurare har zuwa sashen nata. Iya masu hurumin shiga kawai
suka shiga har cikin bedroom da suka kira matsayin master
bedroom nata. Sai dai suna fita ta miƙe daga zaman ɗofanar
da tai a gefen gadon, cikin ambaton sunan ALLAH da zubar
hawaye ta jaye hular alƙyabar ta ta ƙarema ɗakin kallo na
tsahon mintuna uku. Komai batace ba ta ɗauka akwatinta da
aka shigo da shi ta fito a ɗakin tare da jawo ƙofar. Bata wani
tsaya kallon falon data fito ba, sai dai tabi kowace kusurwa na
cikinsa domin lissafa adadin ƙofofin dake a cikin. Ƙofar da
lissafinta ya tabbatar mata ta nufa, cikin ɗan jimami da
tausayin kai ta murɗa ƙofar mai kalar ruwan gold. Ɗakin ta
shiga bayan ta leƙa kanta cikinsa. Shima ɗin dai a ƙayace yake
da komai na alfarma. Sai dai komai nasa ya banbanta da kalar
na wancan ɗakin. Amma shima duk abinda ke cikinsa royal ne
irin kayan da suka dace da gidan hamshaƙan masarautu
kamar Daular Ruman. Ajiyar zuciya ta sauke bata samun
nutsuwa ba, sai ta son rage nauyi mai danƙarewa a ƙirji kawai
har numfashi ya gaza samun damar fita yanda ake buƙata.
Jikkar ta ajiye tare da zama bakin gadon ta rushe da sabon
kuka.........✍
14
.........Wannan dare darene na tarihin da har abadan Iffah
bazata taɓa mantawa da shi ba. Badan wani abu ya faru
bayan wanda ya faruba, wanda ya farunne bazai taɓa zama
shiɗaɗɗe a zuciyarta ba. Kwana ɗaya tak ta kasance cikin
ɗimuwa da tsananin kewar ahalinta. Wanda ta riga ta gama
sallamawa ta rabu dasu kenan har gaban abada. Sai dai
bayan mutuwarta suzo jana'izarta batare da ko kan gawarta
an barsu matsawa ba. Sam babu wani barci koda ɓarawo da
yaci galabar ɗaukarta a wannan dare. Hakama abincin da aka
biyo bayanta da shi na buɗa bakin azumin da tace batacisa
ba. Kuka taci ta ƙoshi har kusan rabawar dare kafin ta miƙe
zuwa bayi tayo alwala ta nutsu gaba ɗayanta gaban
UBANGIJIN talikai maji roƙon bayinsa. Duk da tsananin tsoro
da take a ciki na kasancewa ita kaɗai a katafaren sashen haka
ta dinga jarumtar son dannewa a zahiri. Sai dai duk ƙanƙantar
motsi yakan saka zuciyarta harbawa da tunanin anzo
kashetane.
Tana idar da sallar asubahi barci yafa ce ya shirya, dan duk
yanda take faman turesa da son ƙin yinsa sai da yakaita ƙasa,
dole takai kwance kan lafiyayyen kafet ɗin dake gaban gadon
kafin ƙiftawar ido ta fara sauke numfashi....
Barci sosai Iffah tasha na tsahon lokaci mai tsayi da har
sai da aka tadata ta fahimci hakan. Ƙyawawan idanunta dake
cike da barci ta buɗe da ƙyar akan matar dake tsaye a
gabanta kanta a rissine. Babbar mace ce mai shekaru sosai,
sai dai shigarta ta tabbatar da cewa ita ɗin bakomai bace sai
hadima a masarautar. Amma kuma da alama hadima ce mai
babban muƙami da matsayi....
“Barka da safiya ya Zawjata-almilki”.
Ta katse tunanin Iffah ta hanyar gaisheta. Yunƙurawa tai ta
tashi zaune idonta na a kanta, kanta ta gyaɗa da faɗin,
“Mama ina kwana”. Dan shekarun girma na matar ya wuce ta
zauna saita gaisheta. Sosai ta ga ruɗewa da kiɗima a idanun
matar. Cikin yin waige-waige na tsoron kar wani yaji ta zube
ƙasa da rawar harshe. “Ranki ya daɗe na roƙeki dan ALLAH
wannan sunan yabar fita a bakinki. Kece uwa a garemu, ke
kika cancanta mu kira da sunan bani ƙasƙantacciyar baiwa
mai miki hidima ba. Sunana shine Diwa, zaki iya kiran Ama
(baiwa), ni shugabar hadimai masu kula da tsaftar sashen
Malikat ce. An kawo miki abin karin kumallone tare da wanda
zasu shiryaki da hadiman da zasu kasance masu hidima a
gareki”.
Idanu kawai Iffah ta tsura mata cike da tausayawa. Sai dai
komai bata iya cewa ba ta kauda idanunta zuciyarta na ƙuna
na raɗaɗin ƙasƙancin da su talakawan ruman ke fuskanta a
ƙarƙashin waɗannan masarautu. Hadima Diwa miƙewa tai da
sauri ta fita. Mintuna kaɗan sai gata ta dawo tare da wasu
mata guda biyu.
“Ranki ya daɗe, waɗannan matan sune zasu shiryaki a
yanzu”.
Yanzun ma iyakarta ɗago ido ta kallesu kawai, sai dai batayi
musu ba wajen basu damar fara aikinsu. Amma a zuciyarta ta
cigaba da yin addu'a sakamakon harbawa da ƙirjinta keyi da
sauri-sauri tamkar mai tsoron tunkarar wani abu. Tsaf suka
kwance kitson dake kanta, dogon gashinta da mafi yawan ƴan
ƙasar ta Ruman keda ya bayyana.
“ALLAH ya ƙara miƙi tsahon rai da lafiya, wannan lokacine
na wanka”.
Komai Iffah batace musu ba ta miƙe, dan tanabin huɗubar
Kaka ne daki-daki. Da zata shiga bayi dakatar da su tai daga
ƙoƙarin binta da suke.
Hadima Diwa dake gurfane gefe tai saurin faɗin, “Ranki ya
daɗe ki basu dama dan ALLAH, dan zasu nuna miki yanda zaki
amfani da kayan wankan da aka shirya dominki a ciki, su
kuma gyara miki kai kawai su fito”.
“Karki damu zanyi da kaina”.
Ta faɗa tana mai shigewa kafin ma ta sake cewa wani abu,
sai dai bakinta ɗauke yake da addu'a. Wani irin harbawa
zuciyarta tayi, tareda sarawar kai lokacin da take sanya ƙafa
cikin toilet ɗin sai kace ba dashi tai amfani ba da asubahi,
yanzu kuma da su Diwa suka shikago sun gyarasa da ajiye
kayan wankan da suka shigo da shi tare da matan, hannu
takai saman kanta tana karanto addu'a bayan ta shiga toilet
da tayi sannan ta ƙarasa shiga. Shi kansa bayin abin kallone a
yanzu fiye da ɗazun, dan yanzu an ƙawatashine da wasu irin
fure da candles ta gefen jakuzzie ɗin. Sai wasu nau'inkan
ruwan turare da aka ajiye domin tai amfani da shi, sam
zuciyarta taƙi aminta da hakan, atake ta dinga ɗaga tasoshin
da suke a ciki tana maidasu gefe guda ta hau wankanta tana
mai zubda hawayen tausayin kanta dana iyayenta da batasan
halin da suke ba a yanzun suma....
Koda ta fito da tunanin samun matan data bari sai taci
karo da akasin haka. Domin kuwa wayam ɗakin babu kowa,
sai ƙamshi mai daɗi na turaren wuta da aka ajiye ke tashi.
Numfashi ta sauke a hankali, badan samun nutsuwa na
abinda ke gudana ba. Sai dan samun sassaucin nauyin da
zuciyarta tai mata. Kusan mintuna biyar da fitowarta ta
gagara tsinana komai, hasalima bata san ta ina zata fara ba.
Knocking ƙofar da neman izinin shigowa ya sakata ɗaga
idanunta manya takai dubanta, kafin ta bada izinin shigowa
tana mai janye idanun nata. Hadima Diwa ta shigo sallama
kanta a ƙasa, tun'a bakin ƙofa ta zube bisa gwiyawunta. Cike
da tsantseni irin na tsakanin yaro da uban gidansa murya cike
da rauni tace, “Ya Zawjata-almilki! Yanzu lokacine na
shiryawarki da taimakon waɗan nan mata”. Ta ƙare maganar
da nuna bayanta.
Iffah dake saurarenta tare da zuba mata ido kallonta ta
kai bayan nata, kamar zatai magana sai kuma ta fasa. Tai ɗan
shiru na wasu sakanni tamkar mai tunani kafin taja numfashi.
“Ai zan iya shirya kaina su barshi kawai”.
Ƙasa Diwa ta sake yi da kanta da sake gurfana ƙasa sosai.
“Ki gafarceni ya Zawjata-almilki. An basu umarnine, saɓawa
kuma a garesu tamkar bijirewa ne?”.
Tsantsar tausayinsu da takaici mai gimtse maƙoshi ya
sake baibaye Iffah, ta nisa tare da haɗiye abinda ya tokare
ƙirjinta tana mai jin-jina kai wa hadima Diwa kawai. Tamkar
ƙyaftawar ido matan suka shigo su biyu. Suma dai kallonsu
kawai Iffah take cike da tausaya wa. dan cike da girmamawa a
gareta suka zube gwiyawunsu a ƙasa domin gaisuwa a gareta
kasancewar bana ɗazun bane.
“Dan ALLAH ku miƙe”.
Ta faɗa cikin wani irin yanayi daya saka matan ɗan ɗagowa
suka dubeta. Su ɗin ababen tausayine, amma sai sukaji itace
suke tausayi fiye da kansu. Umarninta sukabi duk suka miƙe
ɗin, suna maiji da kallonta da matuƙar girma a idanunsu duk
da ƙanƙantar