Author : Bilyn Abdull ce Category : African Stories & Novels
Yanzu ma dai ɗauke kai
tai ga Iffah ta cigaba da hidimar gabanta batare data sake
magana ba. Daga baya ma saita ƙirƙiri jan Iffah da sabuwar
hira da bata da alaƙa data farko. Tun Iffah na ɗararewa har ta
saki jikinta...
★Washe gari ta ɗan danne kaso sittin cikin dari na
damuwarta dan kar Ummu ta hanata zuwa makaranta. Sai
dai koda taje makarantar ma dai zaune kawai ta kasance
badan ta nutsu a fahimtar komai ba har aka tashi. Kanta
tsaye ta fito domin samun abin hawa a bakin gate kamar
sauran ɗalibai. Da ƙyar ta samu tare da wasu da suke kusan a
anguwarsu, sai dai zasu rigata fara sauka...
A hankali wata baƙar mota dake fake ɗan nesa da
makarantar tasu ta fara bin bayan mai Mototaxi ɗin da sam
shi hankalinsa baima kai ba. Haka suma su Iffah babu wanda
ya kula da motar. Da mai motar ya fahimci zasu zargesa sai ya
canja salon bin nasu. A haka har aka sauke abokan tafiyarta.
Motar ta cigaba da binsu har titin anguwarsu, anan aka
dakata har mai Mototaxi ɗin ya shiga ya kai Iffah ya juyo zai
fita suka tsaidashi..........✍
10
........Kamar wasa Iffah na shigowa gida ta zube kwance tana
rawar sanyi, ga jikinta ya ɗauka matsanancin zafi. Ummu bata
kawo komai a ranta ba game da ciwon Iffah sai tunanin ranar
da ake ƙwallawa ce ta washeta. Da ƙyar ta tilastata tai wanka,
taci abinci kaɗan ta ajiye. Maganin zazzaɓi Ummu ta bata
tasha, daga haka ta koma ta kwanta ranar ko Islamiyya bataje
ba.
Da dare firgita data dingayi saboda munanan mafarkai ya
sa kusan kowa bai rintsa ba a gidan sai gab da asuba. Da barci
yaɗan figeta saita tashi a firgice har sai sun rufeta da addu'oi
take samun nutsuwa ta sake komawa barci. Al'amarin ya
tsayama kowa a rai, sai dai ganin ta tashi ragal da asuba tai
salla sai sukaita mamaki. Dan bazaka taɓa tsammanin itace a
daren jiya ba.
Da safe koda tace zataje makaranta hanata Babiy yayi,
acewarsa ma asibiti zasuje da Hanash. Kasancewar Iffah da
rashin son asibiti sai ta turje akan itafa ta warke, dama jiyan
rana ce (ta fake da abinda Ummu tace). Ganin harda ƴan
kwallanta Babiy yace to inhar zazzaɓi ya sake dawowa a yinin
yau dole suje asibitin nan. Da sauri tace ta yarda. Bayan
wucewar Babiy tai ta ɗan ƙarfafa kanta harda taya Ummu
aiki, duk da yanda takejin yanayinta babu daɗi haka tai
ƙudirin shirin Islamiyya idan lokaci yayi, tana ɗaki kwance
bayan idar da sallar azhar sai ga kiran malaminta Fawzan,
wayar kawai ta tsurama ido tamkar bazata ɗauka ba harta
katse, wani kiran ya sake shigowa shima harya katse bata
ɗaga ba. Duk da zumuɗin son ganin kiran nashi da take ciki a
kusan kwanaki uku sai taji hanunta ya mata nauyin ɗagawa a
yanzu daya kira... Shigowar saƙo ya katse mata tunani, ta kai
hannu kan wayar ta ɗauka kamar mai tsoro...
_“Fareedah ga dama ta biyu ta sake samuwa, Idan kinga
saƙona kiyi ƙoƙarin fitowa kafin Four”._
A zabure ta miƙe jikinta na tsuma ta hau shirin Islamiyya,
tare da tattare dukkan takardun bayanan da take ta faman
adanawa harma da waɗanda ta ƙara haɗawa a kwanaki ukun
nan.
“Ummu zan wuce Islamiyya”. Ta faɗa lokacin da take
ƙoƙarin saka takalmi a ƙafarta Ummu na tsakar gida tana
alwalar sallar la'asar.
“Ke da baki da lafiya auta”.
“Ummu naji sauƙi wlhy, kinga saukarmu ya kusa babu
buƙatar na fara wasa ai. Malam nata mana gargaɗin hak......”
Sauran maganar ya maƙale a harshenta sakamakon tashin
sautin busa mai nuni da isowar jama'ar masarautar Daular
Ruman. Tamkar an daki kan Iffah da guduma haka taji wani
dummm! A cikin kunnenta har suka ƙarasa shigowa cikin
gidansu jinta bai dawo ba. (Shin tsoro ne? Ko firgici?) bata
san wanene ya risketa ba...... Taɓata da Ummu tayine ya sata
jan kakkauran numfashi tare da kallonta. Jikin Ummu ne ke
rawa, idanunta kam tuni sun tara ƙwalla. Iffah ta shiga girgiza
mata kai alamar kar tai kuka, ta sake damƙe hanunta cikin
nata tare da maida kallonta garesu rai ɓace, dan ta ɗauka
alwashin a wannan karon komi sukazo da shi sun tara sun
samu, sai dai a kasheta...
“Mi kukazo yimana a gida kuma? Ko kun dawo muma ku
idasa kashemu tamkar yanda kuka halaka min ƴan uwana da
tsafink......”
Da sauri Ummu ta danne mata baki da tafin hannunta tun
kan ta ƙarasa faɗa. Kai take girgizamata cikin rawar jiki. Da
ace ba Ummu bace babu abinda zai hanata ta ture hanunta ta
ƙarasa abinda ta fara faɗa ko zata samu salama a ranta. Sai
dai kuma bazata iya ba, dan haka ta shiga yima Ummu alamar
roƙo da magiyar ta barta amma taƙi yin hakan...
Basamuden nan ne na kullum mai riƙe da bulala ya daka
mata tsawa. Da sauri Ummu ta sakemata baki, sai dai ta
jawota jikinta ta ƙanƙame. Iffah jitai zuciyata ta ƙara
hautsunowa, a matuƙar zabure ta sake buɗe baki zatayi
magana ya dakatar da ita...
“Ke ƴar talakawa lura da inda kike. Bakin rijiya ba wajen
wasan makaho bane. Idan taƙamarki tsageranci tamkar
ƙiftawar ido za'a sauke miki shi, a kuma shafe babinku daga
ke har iyayen naki a doron ƙasa”.
Hasala iya hasala Iffah tayi, Kukan da Ummu ta fashe da
shi ya hanata cewa komai ta juya gareta jikinta na rawar
shiga tsananin ɓacin rai, kanta take juyamata alamar karntace
komai.....
“Umm....”
“A'a Iffah! Ina umartarki karki ce komai”.
“Kibarta tace ɗinma yanzu harshenta ya zama datsatstse
a gabanki.”
Kafin Ummu dake girgiza kai tace komai Babiy ya shigo
tamkar an jehoshi, da alama dai wanine ya sanar masa da
zuwan jama'ar masarauta gidan nasa. Ko sau ɗaya basu bashi
damar cewa komaiba suka isar masa da saƙon kira daga
daular ruman.
“Innalillahi.....” Iffah ta shiga ambata ita da Ummu, dan
sunaji a ransu tarihine dai yake ƙoƙarin maimaita kansa,
hawaye masu tsananin ƙuna da ɗaci na gangarowa bisa
ƙyaƙyƙyawar fuskata Babiy da shima dai yasan labarin gizo
bazai wuce ƙoƙi ba. A gaban idonsu aka wuce da Babiy Daular
Ruman a karo na uku, tare da barin wasu dakaru a ƙofar gida
ta hanyar hana duk wani mai yunƙurin fita daga gidan. Haɗe
kai kawai Iffah da Ummu sukai suna kuka, dan shi kaɗai suke
da damar yi ɗin..
★Bayan cikar awanni biyu da tafiyar Babiy sai gashi ya
dawo, dawowa irin wadda ya saba a duk lokacin da
makamancin kira irin wannan ya samesa daga daular Ruman.
Yanda ya kafe Iffah da idanunsa dake zubda hawaye ya saka
Ummu zubewa ƙasa cikin kuka. “Abu Hanash itama zamu
rasata ko? Itama ka ɗaura mata aure da Tajwar.....?”
Hawayene masu ɗumi da ƙuna suka ziraro a idanun
Babiy, ya girgizama Ummu kansa a hankali alamar a'a, tare da
girgiza kan nasa kuma alamar tayi shiru. Hawayen nata ta
share kamar yanda ya buƙata, sai dai jikinta bai bar tsuma ba.
Kamar yanda Iffah data kafesa da idanu bata iya ko ƙyaftawa
ba. Ummu ta sake gyara zamanta da fuskantar Babiy da
ƙyau....
“Idan ba abinda muke tunani bane to minene ya faru?”.
“Ki kwantar da hankalinki babu komai f.....”
“Bazan taɓa yarda babu komai ba. Sai dai idan kana so ka
rufeni ne. Hakan kuma shine mafi ƙololuwar kuskuren da
banajin zan iya yin afuwa gareka a kanshi. Dan inaji a jikina
zuwanka masarauta nada nasaba da rayuwar yarinyata data
rage min, idan har zuciyarka ta iya ɓoyewa ƙwayoyin
idanunka basu lulluɓe komai ba, garama ka sanar min”.
Babiy ya fahimci idon Ummu ya rufe ta manta Iffah na
wajen, dan haka ya cigaba da ƙoƙarin ganin ya kufcema faɗar
abinda yazo da shi har sai sun keɓe amma ta dage akan itafa
ya faɗa mata a yanzu. So yake ya buɗe ido amma bashi da
sauran ƙarfin zuciya a yanzu, dan haka a sanyaye ya rumtse
idanunsa da launinsu yay matuƙar komawa ja. “Ba'a ɗaura
mata aure da shi ba. Sai dai....” ya kasa ƙarasawa.
“......Sai dai me? Dan ALLAH ka faɗa min”. Ummu ta faɗa
tana mai sake fashe masa da kuka mai matuƙar sake ɗaga
masa hankali. Miƙewa yay yunƙurin yi tai saurin riƙe masa
ƙafa. Babiy ji yake shima kamar ya fashe da kuka ya huta
kawai. Ya dawo ya durƙusa gaban Ummu tare da riƙo mata
hannu, “Akan abinda suka faɗa munada mafita tunda yasha
ban-ban dana baya Jumaima. Dan haka na gama yanke
shawarar zamu bar garin nan dama ƙasar gaba ɗaya a daren
yau insha ALLAH. Dan sun buƙaci izinin neman auren Iffah ne
a gareni, sun kuma bani damar zuwa nai shawara daga nan
har zuwa ƙarshen makon nan”.
Kafin Ummu ta samu damar cewa wani abu sulalewa da
faɗuwar Iffah a lokaci guda ta riski kunnuwansu. A tare suka
zabura kanta jikunansu na matuƙar rawa da tsuma. Ummu ta
fashe da kuka dai-dai tana ɗago Iffah dake wanwar a ƙasa
taga ta koma yaraf alamar babu rai a tare da ita.....
.....Sosai kukan Iffah ya sake ɗaga hankalin Babiy. Dan
tunda aka zuba mata ruwa ta farfaɗo ta haɗe kai da gwiwa.
Suma idanu kawai suka zuba mata suna hawayen zuci, rikicin
yana a kantane kawai, amma sune suka fita jin raɗaɗin a
zuciya saboda ita akwai ƙuruciya tare da ita. A ganinsu bai
zama lallai ma tana hange irin wanda su suke matane ba.
Kusan mintuna talatin suna a haka, kafin Babiy yay ƙarfin
halin miƙewa suma yay musu umarnin su tashi su koma ciki.
Sai da taimakon Ummu Iffah ta iya miƙewa, har sun kusa
shiga ɗakin ta tsaya, ɗagowa tai ta dubi Ummu ta juya ta dubi
Baby hawaye na sauka da gudu bisa ƙyaƙyƙyawar fuskarta.
“Bazamu gudu ba Babiy, zan aure shi....”
Kaɗan ya rage Babiy yaci uban tuntuɓe saboda firgitaccen
furicin Iffah mai kamanceceniya da gawurtaciyar sautin
saukar aradu cikin tsakkiyar duhuwar dare. Ummu ma dai da
taima Iffah sakin bazata ƙirji ta dafe dukanin idanunta na
firfitowa.....
Iffah ta share hawayenta da sakin murmushi a karo na
farko. “Ummu! Babiy! ku kwantar da hankalinku, kar kuma ku
ɗauka ba'a cikin hayyacina nake ba. Nasan burinku shine ku
kuɓutar dani daga mutuwa, sai dai kuma a duk inda zanje ku
sani tana tare da nine. Wannan azzalumin ba guje masa ya
kamata ayi ba, tunkararsa ya kamata ayi. Kamar yanda kaka
ya faɗa, a wasu lokutan gujema ƙaddara ba mafita bace sake
kirawowa kai halaka ne. Amma tunkararta gaba da gaba
ƙarfafa imani ne sannan jarumtace. Shin idan mun gudu
kunada tabbacin zamu iya tsere musu bayan ƙasar a hanunsu
take? Sannan idan mun tafi ina zamuje bayan babu inda
muka sani sama da ƙasar Ruman. Fir'auna ma da yay nasa
zamanin mulkin da ko kama kafarsa wannan shaiɗanin
baiyiba UBANGIJI maida ANNABI MUSA (A.S) yay cikin
gidansa ya rayu bisa ƙudirarsa da tabbatar masa shine mai iko
akan kowa da komai. Azzalumin nan ba gudun masa ya
kamata ayi ba, daƙilesa ya kamata ayi, domin idan ni kun
kuɓutar dani, su sauran iyayen da zasu iya fuskantar
makamancin halin da kuke ciki fa bayanku?. Babiy zanyi
biyayya kamar yanda ƴan uwana sukayi, kuma ku sani da
iznin ALLAH nice zan kashes........”
Cikin rawar jiki Ummu ta zaburo tare da toshe bakin Iffah.
Sai faman waigen bayansu take domin sanin dakarun Daular
Ruman na ƙofa gidan har su biyar. Babiy ma gaba ɗaya
kalaman Iffah sun sake rikitashi. Sai dai kafin wani cikinsu ya
samu damar cewa wani abu ta shige cikin ɗakin. Idanu suka
tsirama juna shi da Ummu harna tsahon mintina biyu, kafin
Babiy yay ƙarfin halin janyewa yana mai jan nannauyan
numfashi da barin wajen ya shige ɗakinsa. Da ƙyar itama
Ummu ta sauke numfashin, har zatabi bayan Iffah sai kuma ta
fasa ta nufi ɗakin Babiy ɗin itama.
Shigowarta dai-dai dayin sallamarsa waya manne a
kunensa. Zaune takai a bakin gadon dake ɗakin dan inba haka
ba zata iya zubewa ƙasa saboda yamutsawa da jininta ke
mata. Jin sunan Baba da Babiy ya ambatane ya sata maida
hankali garesa itama. Komai sai da Babiy ya zayyanema Kaka
kafin yay shiru alanar saurarensa.
Daga can Baba yaja nannauyan numfashi bayan gama
sauraren surukin nasa mijin ƴarsa tilo data rage masa a raye.
Sai kuma yay murmushin ƙarfin hali mai sautin daya isa har
cikin kunnen Babiy. “Ni ma ina goyon bayan maganar
Fareedatu. Da ace wani rai nada ikon hana tabbatuwar wasu
daƙiƙu na gaban rayuwarsa masu tafe da ƙaddara da mutane
da yawa sunyi rigakafi kafin cikar adadin waɗan nan daƙiƙu
Muhammadu Zayyanu. Amma inaso ku tuna muɗin
talakawansu ne, masu rayuwa a ƙarƙashin mulkinsu, bamu da
wani ƙarfin iko akan hukuncinsu garemu ko kan ƴaƴanmu.
Dan haka ku bita da addu'a kawai itama.”
Tamkar yana gabansa ya jinjina masa kansa, tare da
ƙoƙarin danne hawayen da yake na zuciya da ƙunarsu gara
ace a zahiri suke zuba bisa ƙyaƙyƙyawar fuskarsa. “Shikenan
Baba, amma furucin Iffah ya girgizani, ina tsoron kar zuciya ta
ingizata tai yunƙurin aikatawa. Kisa fa! Koda bata aikata ba
fitar wannan furucin zuwa kunen wani bayan mu ba ƙaramar
magana bace”
“Kar komai ya dameka Muhammad Zayyan. Ta faɗane
kawai saboda raɗaɗi da takeji da kuma ƙuruciya, kai dai ka
sanar dasu ka amsa daga nan zuwa kwanaki uku. Zan zo a
amsa kuɗin auren da ni dama wasu a cikin zuri'an ka insha
ALLAHU.........✍
11
..........Iffah taci kuka matuƙa da ko maƙiyinta ya dubeta sai ya
tausaya mata. Sai dai kuma iya juyawa su Babiy sun mata
akan su gudu ta kafe akan itafa ta yarda zata aura *_Tajwar
Eshaan ibn Haysam Abdull-Majeed_*. Sosai hankalinsu yake
ƙara tashi da tirjewarta. Gashi gaba ɗaya ta bikice musu ko
isashen lafiya babu a tare da ita. A cikin wannan halin Babiy
ya sake samun saƙon kira daga masarauta. Yana shirin tafiya
sai ga Kaka. Duk sunyi matuƙar mamakin zuwan nasa, dan
abune mai wahalar gaske a garesa zuwa inba da wani dalili
ba. Sun tarbesa kamar yanda suka saba matsayinsa na uba.
Bayan gama gaisawa ya kai dubansa ga Iffah dake kwance
cikin bargo duk ta rame ta sake komawa fayau da ita, dama
tun rasa ƴan uwanta ɗan jikinta ya zube, dan sam ba siririya
bace. Iffah nada jiki murjajje daba za'ace mata siririya ba
kuma babu mai sakata a sahun masu ƙiba. Duk da shekarunta
har yanzu sunada ƙaranci ALLAH ya bata jiki na manyan mata
da'a yanzu komanta yake ciff dai-dai da halittarta. Kaka ya
ɗauke idanunsa a hankali tare da maidasu ga Babiy.
“Muhammadu Zayyanu ka sakama ranka nutsuwa ka cire
batun barin gidan dan bashine mafita ba. Hasalima tun randa
ka amsa kiran masarauta wannan gidan zagaye yake da
dakarun daular ruman harta inda baka zata ba. Ko'a
tunaninka zasu tunkareka da wannan maganar su baka
damar kanka sannan su koma gefe da tunanin kai bazakayi
wani yunƙuri ba”.
Daga Babiy har Ummu da Hanash kallon tsoro da mamaki
sukema Kaka. Ya ɗan jinjina kansa alamar tabbatarwa. “Karku
damu da yanda akai nasan wannan, kai dai kawai kaje ga
kiran da sukai maka. Karka kuma nuna wani ja'inja kace ka
amince musu suzo neman auren”.
Kuka Ummu ta fashe da shi tana kallon mahaifin nata. Yay
ɗan murmushi da ɗauke kansa tamkar bai fahimci mitake nufi
ba. Ganin haka Hanash da idanunsa sukai jajur cikin
cinkushewar harshe yace, “Amma kaka miyasa ka zaɓa itama
mu sake rasata? Wlhy nayi alƙawarin in har itama ta salwanta
sai na salwantar da ran Shahan-shan da wannan hanun nawa
wajen ɗaukar fansa koda nima za ai gunduwa gunduwa da
naman jikina!!”.
“Ba kai ne zaka salwantar da ruhinsa ba, ni nan Fareedah
bint Zayyan nice zan karya ƙarfin ikon azzalumi da hannuna,
zan masa shaƙa irin wadda har sai ya mutu yana mai kallon
tsakkiyar cikin ƙwayar idanuna Hanash Akhi”.
Su duka zuba mata idanu sukayi, dan a yanda take maganar
babu alamar tana a cikin hayyacinta. Babiy zaiyi magana Kaka
ya girgiza masa kai alamar kar yace komai yaje kawai....
★Kamar yanda Kaka ya umarci Babiy ya amsa kiran
masarauta kasancewar a wannan karon an bashi damar zuwa
ne shi kaɗai batare da dakaru sun taho da shi ba. A yanda ya
samu tarba zai tabbatar maka dama a jirace ake da zuwansa.
Kamar ko yaushe a wannan karon ma baiga Tajwar ba, amma
dai a karon farko na tarihin rayuwarsa an kaisa har cikin fadar
Shahan-shan. Inda yaga tsantsar dukiya da ainahin karagar
mulki ta Shahan-shan da akayita da zallar zinare. Hakan
ba'abin mamaki bane ba, saboda girman Shahan-shan koda
da diamonds akai kujerar mulkinsa bazai zama wani babban
al'amari ba, sannan zinare arziƙin ƙasar su ta ruman ne da
bare ma kanzo ya ci balle su ƴan ƙasa musamman Shahan-
shan. Karo na farko da Babiy yaga karramawa daga dattijan
daular ƙasar ruman. Waɗan da ko'a mafarki bai taɓa tunanin
gani ba dan su ɗin ma ba'abune mai sauƙi ga duk wani talaka
ganinsu ba kai tsaye haka. Duk da a birkicen da yake ALLAH
sai ya saka masa nutsuwar yi musu bayani babu ko rawar
harshe a tare da shi. Sun masa godiya da tabbacin a gobe
idan ALLAH ya kaimu masu neman aure zasu zo. Karramawar
da sukai masa ta matuƙar basa mamaki da tsayawa a ransa,
sai dai ta wani gefe na zuciya ya tabbatar da sabuwar hanyar
yaudarace kawai. Cikin danƙareriyar mota aka maidasa har
gida badan yaso haka ba, yayi shiru ne kawai domin bin
unarnin mahaifin matarsa, dan duk da bai taɓa ambatawa ba
ga kowa ya jima da tsanar duk wani abu daya shafi
masarautar daular ruman..
★A wannan dare Babiy yayi zaman kuka irin wanda ake
kira kuka a zahiri da baɗinin rayuwa. Har yanaji bazai iya
cigaba da yima kaka biyayya ba shikam, zai ɗauke Iffah su
gudu daga ruman koda daga shi sai ita ne. Sai dai wani
ɓangare na zuciyarsa na tunatar da shi maganar Kaka, yasan
gaskiya ya faɗa, dan daular ruman bazata zuba ido na barinsa
sakakai ba. Ajiyayyun dakarun dake a ƙofar gidansa ma kawai
tabbaci ne....
A ɓangaren Ummu ma bata runtsa ba, sai dai saɓanin
Babiy ita kwana tai tsaye tana gayama UBANGIJI damuwarsu
da roƙonsa kariya da kuɓuta ga yarinyarta. Shi kuwa Hanash
kwana yay ƙulla ta yanda zai halaka Tajwar Eshaan ibn
Haysam Abdul-majeed da kansa. Hakama Iffah nata shirin
nada alaƙa dana Hanash. Ta gama yankema kanta koda zata
mutu itama sai dai su mutu tare da Tajwar Eshaan. In yaso a
binne gawarta a tsakiyyar ruman matsayin tarihin da za'a
dinga tunawa.......
*_WASHE GARI_*
Washe gari data kasance safiyar laraba da misalin ƙarfe
biyar na yamma sai ga manyan baƙi daga masarauta ruman.
Baƙi masu ban mamaki, dan kuwa wasu manya ne a cikin
dattijai masu faɗa aji a daular ruman. Sannan iyaye ga
Shahan-shan ta ɓangaren jini makusanta sosai ga mahaifinsa.
Tamburan masarauta da ɗunbin tawagar hadimai da jibga-
jibgan motoci da suka ƙoshi ne suka tabbatarma da jama'ar
anguwa dama maƙwaftan anguwar wace tawagace. Tuni
mutane