Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dauɗar Gora Complete Hausa Novel by Bilyn Abdull Ce

Author :  Bilyn Abdull ce Category :  African Stories & Novels

Chapter   30 / 34

87K to 90K   out of 100K words

suka fice sannan itama ta fito.

★ A yanzu kam masarautar a harmutse take fiye da
ɗazun, hakan ya sake bama Iffah damar komawa sashenta
cikin matuƙar tashin hankalin abinda ya faru da zantukan
wannan mutumi. Kulle kanta tai a ɗaku ido rufe ta saka flash
ɗin a jikin laptop ɗinta da bawani amfani dake da shi ba. Abin
tamkar wani film video ya fara da shigar Babiy riƙe da Abu
Moosa cikin gidansu a waccan ranar, shimfiɗa tabarmar
Ummu da bayanin Abu Moosa da bai kammala ba har
mutuwarsa. Zuwan matar Abu Moosa da jami'an tsaro abinda
Hanash yay mata da tafiya dasu. Daga nan ya yanke. Da sauri
tai playing na gaba. A yanzu kam su Babiy ne a mawuyacin
hali duk sun rame sunyi baƙi a cikin wani ɗaki. Kan Babiy a
saman cinyar Hanash alamar babu lafiya tare da shi, Hanash
nata faman shafa masa ruwa a fuska yana kuka. Sautin dariya
ne ya fara tashi a ɗakin, kafin shigowar wani mutum da iya
jikinsa kawai ake gani babu fuska. A take su Hanash suka
zabura yayinda sautin dariya ke tashi da tafa hannayen
mutumin. Bayan anyi dariyar mai tsawo aka tsagaita, ƙirjinta
yay wata irin bugawa jin muryar Shahan-shan. “A tunaninku
bayan samun tagomashi a jinin yaronku ƴan baiwa zan
haƙura ne. Ina bazai yuwuba, dan a kaf yaran dana halaka
jinin ƴaƴankune na farko daya bani fiye da nasarar da nake
buƙata, shiyyasa na fara bibiyar ta uku daku kanku saboda
bincikena ya nuna min daga jinin ubansu ne”. Hhhhhhh!
Hhhhh!! Kune nasarata ahalin Zayyan. Kune nasarata dole ne
kuma na samu hhhhhhh!!!”.
Kuka Hanash keyi da roƙonsa amma babu alamar zai
sauraresa. Sai ma wani irin salon siddabaru da yakeyi da
hanunsa a take ɗakin ya turniƙe da hayaƙi, sai kuma wata irin
guguwa mai ƙarfi ta nannaɗe hayaƙin a tsakkiyar ɗakin. Su
Babiy dai tuni sun maƙure a bango. Sai kuma suka shiga ihu
ganin guguwar ta zama wani irin maciji daya kusa cinye kashi
ɗaya bisa ukun ɗakin, sara ya fara kaima su Babiy da suka
dunƙule waje ɗaya shi da Hanash, kafin macijin ya kafa kansa
a wuyar Hanash dake ƙanƙama Babiy. Tuni duhu ya gama
mamaye jikin Iffah dake karkarwa, ta rufe laptop dan zuwa
yanzu ma kukan ya kafe ƙaf a idanunta. Sai wani irin
mahaukacin ja da sukayi kai kace wuta aka haɗa a cikinsu.
Tun tana iya jin surutan masarautar har ta daina jin komai.
Daga haka sai farkawa tai ta ganta a gadon asibiti Daneen
Ammarah tare da ita..
Gaba ɗaya ta tsani komai daya shafi Tajwar Eshaan. Dan
haka tun buɗe idon farko da tai ta ga wadda ke tare da ita
bata sake yarda ta buɗe ba. Hakan yasa Daneen Ammarah
bata san ta farka ba. Dama itama kuma tayi matuƙar nisa ne a
cikin tunani a kallo ɗaya ma zaka fahimci bata tare da
nutsuwarta. Ga wata ƴar rama ta yini ɗaya sakamakon tashin
hankalin da ake ciki tattare da ita. Dan tun kai gawar Zawjata-
almilk da Sayeed Khairul-Bashar makwanci ba daular ruman
kawai ba gaba ɗaya ƙasar ruman a harmutse take. Yau wasu a
cikin talakawa sunyi ƙarfin halin fitowa zanga-zanga a wasu
jahohin suna kiranyen Shahan-shan ya sauka ko su ɗauka
doka a hanunsu.
Fitsari daya takura Iffah ne ya tilastata tashi har Daneen
Ammarah ta farga. Da sauri takai hannu ta riƙota tana mata
sannu, dauriya kawai Iffah tai na dannewa dan tunanin datai
a ɗan farkawar nan Tata zuciyarta ta bata shawarar ɓoye
sirrin ranta domin samun cikar burinta. Dan tayi alkawarin a
wannan karon sai ta halaka Shahan-shan, ta riga ta ƙuna bata
tsoron mutuwa. In har burinta ya cika danta mutu ba komai
bane a gareta a yanzu ma tafi buƙatar mutuwar fiye da
rayuwa tunda har ta rasa sauran ahalinta kuma miya rage
mata.
“Ya akai na zo nan Mamy?”.
Ta faɗa cikin danne komai dake ɓoye a ranta. Daneen
Ammarah da farin cikin farkawar Iffah ya sata sakin
murmushi yaƙe da ita kuma Iffah ta fassara da wani abu
daban ta amsa mata da faɗin, “Sakamakon abinda muke
tunanin ya rikeki aka sameki a sume shine aka kawoki asibiti,
amma Alhamdullah tunda gaki kin farka”.
Maimakon ta amsa mata wannan zancen sai ta jefa mata
tambaya. “Mamy da gaske ta mutu ko?”.
Take idanun Daneen Ammarah suka cika da hawaye.
Cikin ɗaci tace, “Sun kasheta Ibnati, sun sami damar da suke
buƙata akansa. Gaba ɗaya ƙasa ta harmutse da bore akansa
kamar yanda dama suke son cimma buri”.
Iffah ta ɗan lumshe ido ta buɗe zuciyarta na karajin tsanar
Daneen Ammarah ɗin da mamakin salon yaudararsu, amma a
zahiri sai itama ta marairaice fuska. “Mamy ban fahimta ba?”.
Hawaye Daneen Ammarah ta share, “Ibnati a yau ruman
baki ɗaya a harmutse take, talakawa nata zanga-zanga a
wasu jahohin akan sai Abni yayi murabus a kujerar Shahan-
shan inba hakaba zasu ɗauki mataki. Gashi tunda abin nan ya
faru babu wanda yaga idonsa ya kulle kansa a ɗaki anyi-anyi
ya buɗe yaƙi”.
Iffah ta rumtse idanu da karfi tana taune lips ɗinta,
yayinda take faɗi a zuciyarta da kakkausar murya. (Ni zan
ƙarasa musu aikin da kawo musu ƙarshen matsalarsu. Dan ba
murabus kawai ya cancanci yi ba mutuwa gaba ɗaya yabar
duniyar ya cancanta da shi ba kujerar Shahan-shan da ƙasar
ruman kawai ba)..........✍️
45



........Daneen Ammarah dake tunanin yanayin ma Iffah
tashin hankaline kawai sai ta shiga rarrashinta. Dole Iffah ta
cigaba da pretending da matsawa a sallameta taji sauƙi.
Daneen Ammarah na rakata sashen ta wuce dan jikin Malikat
Haseena ma dai babu daɗi sam. Dama Daneen Ammarah ɗin
ta zauna da Iffah ne domin saka ido kar wani ya cuta mata
itama. Hakan yama Iffah daɗi, dan ya bata damar nutsuwa a
kallon videon data ɗauka ɗazun. Sosai tai zooming gawar
Zawjata-almilk tana kai bin jikinta ta inda yake a waje daki-
daki. Wata irin zabura tai ganin abinda take ma ɗin kuwa a
saitin wuyan gawar ta gefen kunenta na haggu. Wato alamar
ɗigon sarin maciji har biyu. Innalillahi wa inna'ilaihirraji'un
take ambata wata irin zufan na keto mata, dan kuwa tabbas
zancen mutumin can ya zama gaskiya. Amma duk da haka
tana buƙatar sake tabbatar wa. Cikin rawar da jikinta ke mata
ta shiga laluben number ɗin Sir Fawzan. Bugu ɗaya kuwa ya
amsa kasancewar dama a jirace yake da kiran, dan ya nemeta
amma bai samu ba. Yaci kuka har ya godema ALLAH dan
zatonsa ma ita suka rasa. Cikin rawar murya ya ambaci
sunanta duk da yaji muryarta. Amsawa tai da kuka, bata jira
cewarsa ba tace, “Sir kaji tsoron ALLAH ka sanarmin gaskiya
akan iyayena. Na rokeka karka ɓoyemun komai”. Zufa ce ta
shiga karyo masa tako ina, dan baiyi tunanin jin wannan
tambayar bazatanba a bakinta.
Shirunsa ya sake tada hankalin Iffah, ta cigaba da masa
magiyar da dole ya faɗa mata gaskiyar data buƙata. “Tabbas
na ɓoye miki Iffah, amma tun bayan barinki gida baifi da
kwanaki ba aka rasa ɗan uwanki da Babiy sakamakon......”
Ya zayyane mata labari tiryan-tiryan kamar yanda ya
bincika. Babu kuma banbanci da abinda ta gani a wancan
video ɗin na farko. Ya kare da faɗin, “Wlhy har yanzu akan
binciken inda aka kaisu ake amma babu labarinsu. Nima
kuma a yanzu haka ina yin nawa ta ƙarƙashin ƙasa amma har
yanzu ban samu wani bakin zaren ba....”
Kukan data fashe masa da shi ne ya katsesa daga jawabin
nasa. “Ba zaku gansu ba, ba zamu ƙara ganinsu ba, sun rabani
da su kamar yanda suka rabamu da ƴan uwana. Wlhy nima
sai na kasheshi kamar yanda ya kashesu. Na rantse bazan
barsa ba, bazan taɓa barinsa ba. Yanda ya halakasu da
macijin tsafi sai na halakashi da dafin maciji na gaskiya. Shima
sai ya ɗanɗa......” kuka ya sarƙeta ta kasa cigaba da magana...
Cikin tashin hankali daga can Sir Fawzan ke faɗin, “Iffah
ban gane ba. Dan ALLAH ki daina kuka kimun bayani, kaina ya
kulle dan ALLAH kiyi shiru kinji, wlhy na miki alkawarin
taimaka miki akan koma minene, koda kuwa nima zan rasa
rayuwata ne.....”.
“Babu wannan lokacin sir, bani da shi. Kai dai kawai ina zan
samu dafin maciji mai haɗarin gaske?”.
“Ya ALLAHU! dan ALLAH ki faɗamin mike faruwa? a yanda
zan fahimceki”.
“Idan bazaka samamin abinda nake buƙata ba na Barka
lafiya”.
Yana hello-hello bata sauraresa ba ta yanke wayar, koda ya
sake kira bata ɗauka ba, da taga zai dameta ma sai ta jefa shi
a black list. Kaikawo ta cigaba dayi a ɗakin tana kuka. Komai
ya cakuɗe mata, zuciyarta ta gama ƙeƙashewa da bushewa.
Ta sallama duk wani ɗan sauran rangwamenta. Abinda kawai
idonta da zuciyarta ke gani gawa huɗu ta ahalinta kwance
duk a dalilin mutum ɗaya tak, lokaci yayi da zatai abinda ya
kawota itama dan bai cancanci cigaba da rayuwa ba mutumin
nan sam, tayi alkawarin tare zasu mutu, amma sai ta kasheshi
ta kuma bayyanama duniya wanene shi.
Yanda taci kuka ta fita hayyacinta dole ta bama duk wani
tausayi, da ƙyar ta iya zaman rubuta komai da ya rage, ta
tattare ga Ajmaal, a ganinta ta gama tattare dukan abinda ya
dace ta tattare masa. Hatta ƙudirinta na kawar da Shahan-
shan ta hanyar dafin maciji bata ɓoye masa ba. Ta kwashe
videos ɗin dake wayar zuwa wayarta ta turama Ajmaal ɗin,
takumayi gajeren video da kalaman masu girgiza zuciya har
biyu. Ɗaya na Ummu da su Kaka ta roƙa ya bamawa, ɗaya
kuma na al'ummar ƙasar ruman ne baki ɗaya. Shima tai masa
godiya da fatan alheri da nasara har ƙarshen rayuwa.......


★★..... BARRISTER ★★.....

Barrister dake jin kamar ya ƙwaɗa wayar da ƙasa ya
rumtseta a hannunsa da masifar ƙarfi, a karo na farko wasu
zafafan hawaye suke silalo masa. Jarumar zuciyarsa zugasa
take kada ya yarda ya amince koda zai rasa rayuwarsa,
yayinda wani ɓangaren kuma ke haska masa iyalansa da yafi
so fiye da komai a duniya a halin yanzun. Wannan shine
tashin hankalin mafi ƙololuwar girma daya taɓa cin karo da
shi a rayuwarsa....

Washe gari da safe wujiga-wujiga ya wayi gari, amma
hakan bai saka ko gezau ga mutanen ba. Sai ma duk wani
details daya shafi case ɗin da suka dire masa. Mamaki da
tsoronsu ya sake mamayesa ganin duk wani abinda ke
hannunsa ne. Kuma ya adanasu ne a mabanbanta wajeje.
Akwai wanda a gidansa suke, akwai wanda a office suke,
akwai na mota ma. Amma abin mamaki gasu duk a gabansa
sun tattaro sun kawo masa. Tabbas ya sadaƙar, dan mutanen
nan hatsabibaine na innanaha. In har zasu iya hakan a
kankanin lokaci bayaji idan ya bijire musu iyalansa zasu tsira
kuwa....
“Barrister baka da lokacin dogon tunani, ka shirya dan a
yau oga ke son ka tattaro masa duk bayanin da yake buƙata a
wajen mutanen can. Ciki har da sanin su wanene ainahin
masu aikin, da inda suka ɓoye Abu Hanash da ɗansa”.
Karan farko Barrister ya dubeshi a razane, har ƙoƙarin
taune harshe yake wajen faɗin, “Kana nufin dama baku bane
ke riƙe da su Abu Hanash ɗin...?”
Saurayin yay ɗan waige-waige alamar baya son wani
yaji, cikin raɗa-raɗa yace, “Bamu bane Barrister. Muma
kuɓutar da su muke son yi har ma da kai kanka. Sai dai ban
san miyasa oga bai son ka sani ba ya zaɓi baka aikin a kife”.
Ba ƙaramin zabura Barrister yay ba jikinsa har rawa yake ya
matsa gab da saurayin. “Dan ALLAH kada ka yaudareni ka
faɗa min gaskiya”.
Da sauri saurayin ke masa nuni da yay ƙasa da murya kar
wani yaji, “Barrister wlhy kaji na rantse maka abinda na faɗa
maka shine gaskiya. Na kuma sanar maka ne saboda ka bani
tausayi. Amma iyalanka kansu suna zagaye da tsaro ta yanda
wani bazai taɓa iya samun damar cutar da su ba, kai kanka
kusan sati uku fa muna tare da kai batare daka sani ba. Oga
ba azzalumi bane ba, amma ban san miyasa bai son kasan
taimakonku zaiyi ba. ya kamata kaima ai ka gane hakan tun
farko musamman aikin daya baka ɗin, taya wanda zai cutar
da kai zai kuɓutar da kai?, taya wanda zai cutar da kai zai
ɗauraka akan hanyar abinda kake nema ya baka bakin
zarensa haka cikin sauƙi?”.
“Hakane wlhy ɗan uwa hakane. Kaina ne ya kulle a ruɗani
nake gaba ɗaya. Nagode nagode yanzu kam ka bani ƙwarin
gwiwa, insha ALLAHU kuma sai na bada mamaki. Dan a
wannan gaɓar sai su Abu Hanash sun fita da izinin UBANGIJI,
zan kuma gano koma wanene da hannu a kan ɓoyesu”.
“ALLAH ya baka nasara. Ni bara naje kar wani ya fahimci
ina anan har yanzu”.
Kai kawai Barrister ya ɗaga masa yana murmushi. Wannan
tattaunawa ce ta bama Barrister duk wani ƙarfi da sabuwar
himma na musamman, a yanzu kama baka iya ganin komai
sai murmushi tare da shi, lokacin da aka kawo masa abincin
rana ya buƙaci takarda da abin rubutu. Takardu aka kawo
masa bama takarda ba, hakan ko ya masa daɗi, dan ya
kwashe sauran wannan yinin da dare wajen tsara duk abinda
ya dace. Washe gari har ya fisu zumuɗin son fita ma, sauran
da basu san miya faru ba canjawar Barrister ɗin taita basu
mamaki.....

★★... KAUYEN JUMNA ★★....

Tun kammala bayanin Abu Zainab ga su Kaka jikkunansu
duk yay sanyi, Ummu ma hawaye takeyi, Barrister shine hope
ɗin su a yanzu bayan UBANGIJI masanin abinda ke fili da
ɓoye. Gashi a dalilinsu an rasashi. Idan har aka cutar da shi ta
dalilinsu bazasu yafema kawunansu ba.
Kaka dai jinjina kai kawai yake amma komai ya kasa
cewa, sai Iyyani ce cikin ƙarfin hali da sharar ƙwalla ta dubi
Abu Zainab da damuwa ke shimfiɗe a fuskarsa. “Zakariyya
kuyi haƙuri dan ALLAH, mun jefa rayuwarku a haɗari, ya
ALLAH ka bayyana Abdullahi da gaggawa”.
Ɗan murmushin yaƙe Abu Zainab yayi, cikin danne abinda
ke masa kaikawo yace, “A'a mama ai mutum baya taɓa wuce
ƙaddararsa, kuma har yanzu bamu tabbatar ba ko akan
wannan case ɗin bane muka rasa shin, dan Barrister da kike
ganinsa nan shima hatsabibin kansa ne, gaskiyarsa da
tsayuwa akan ganin tabbatar da ita yasa yanada maƙiya da
yawa akan cases daban-daban hatta a cikin abokan aikinsa
ma. Kinga kuwa zama ta iya yiwuwa ba'akan wannan ɗin
bane.....”
“Dole ya zama akan wannan ne”
Kaka ya faɗa cikin katse Abu Zainab. Duk kallonsu suka maida
a kansa. Ya jinjina kai batare da ya kallesu ba. “Ban san gaibu
ba, amma inaji a jikina akan su Muhammad Zayyanu ne, sai
dai kuma tabbas koma a ina yake har yanzu yana raye insha
ALLAHU. Inajin wannan ƙwarin gwiwar ne a zuciyata”.
Ba ƙaramin mamaki kalaman kakan suka basu ba, sai dai
kowa ya gagara cewa komai sun dai zuba masa ido. Kusan
mintuna biyu gidan shiru kafin kaka ya miƙe, babu jimawa ya
dawo da jakka a hanunsa. Su dai duk suna kallonsa kawai.
Takardar daya zaro ya miƙama Abu Zainab. “Ungo duba
wannan”.
Da sauri Abu Zainab ya amsa ya fara karantawa. Bakinsa
cike da magana ya ɗago yana duban kaka da ke kallonsa.
“Baba wannan kuma fa?”.
Murmushi Kaka yayi da kauda kansa kamar bazaice komai
ba. Sai kuma ya ɗan taɓe baki da fara basu labarin yanda duk
a kai a randa zai dawo. Ya ɗora da faɗin, “Saurayin daya
kawoni gidan nan zuciyata ta bani ba haka nan ya kawoni
ba....”
“Amma baba shine ka amince harma da nuna masa
gida?”.
Kaka yay ƴar dariyarsu ta manya. “Zakariyya kenan, to idan
baka iya kama ɓarawo ba ai shi sai ya kamaka. Ka ganni nan
barni kawai inda ka ganni. Idan na nuna nasan yanada
manufa a kaina tun farko kamar yanda naso nuna masa a
tasha ai bazan san sirrin zuciyarsa ba. Amma dana bashi
dama fa? Yanzu a tafin hannuna yake, kuma jirace nake da
zuwansa dan na tabbatar zai dawo, na masa talalar da tabbas
sai ya dawo da izinin UBANGIJI”.
Abu Zainab kam a yau Kaka ya fara bashi tsoro. Sai dai
ya danne bai yarda ya nuna ba. Kaka ma ya fahimci haka
amma ya kanne, sai jakkar ya tura ma Abu Zainab yana faɗin,
“Wannan sune kuɗin dake tare da takardar”.
Nan ma dai da mamaki Abu Zainab ke kallon kuɗin, kuɗine
masu yawa sabbi ƙal sai ƙamshi suke na sabunta. “Baba
waɗan nan mutanen kuwa anya....”
Kaka yay murmushi mai bayyana haƙora. Sai kuma ya
ɗan kalli sashen da Ummu ke zaune. Tuni ta tashi batare da
sun farga ba har Iyyani..........✍️

46


..........Lokacin da kaka yayi ma Abu Zainab rakkiya sukejin
halin da ƙasar ke ciki, dan shima Abu Zainab kasancewar
fitowar sassafe yayi sannan komai bai fasu ba. Hankalinsu
yayi matuƙar tashi dan basu san wacece a cikin matan sarkin
ta rasu ba.
“Zakariyya zama bai ganni ba, dole ne mu wuce tare
kenan, kayi haƙuri kaɗan jirani anan ina zuwa”.
Kaka bai jira cewar Abu Zainab ba ya koma gida da sauri,
koda su Iyyani sukaga a yanayin da ya shigo suma hankalinsu
ya tashi, amma tambayar duniya yaƙi ce musu komai kan
abinda ya farun, sai cemusu da yay shima zaije Daular ruman
ne.”. jin wannan furucin nasa yasa jikin Ummu fara rawa, a
hankali ta zube ƙasa dan zuciyarta ta gama bata kodai ta rasa
Iffah ko su Babiy. Dama yau kusan gabbanin asuba tayi
mafarkin Iffah na kuka da kiranta tazo ta ceceta, sai kawai ma
zuciyarta tafi karkata akan Uffan..

Su Kaka sun iso daular ruman a harmutse, dan ƴan
zanga-zanga nata da ɗa karuwa harma abin na bama mutane
mamaki. Yayinda jami'an tsaro tuni sun fito ta kowane titi na
masarauta sun tare. Da ƙyar suka samu ƙarasawa gida,
kasancewar ana aikowa gidan domin halartar jana'iza yasa
Kaka yay tunanin wannan ma indai Iffahr ce zasu aiko. Dan
haka suka shiga tambayar ƴan anguwa amma kowa na
tabbatar musu babu wanda yazo. Hankalin Kaka ya tashi fiye
da farko, dan kuwa dai bayan wannan hanyar babu wata mai
sauƙi da zai iya ji sai abokinsa dogon yaro da ke cikin
masarauta. A yanda kuma garin yake hakan abune mai
wahala a garesa kenan......

★ BARRISTER ★

Yanayin da aka wayi gari a ƙasar bai hana su Barrister
fitowa ba, sai ma lokacin shi yasan abinda ke faruwar,
al'amarin ya taɓa masa zuciya, dan ta wani fannin case ɗinsa
tamkar kacokal yanada alaƙa mai ƙarfi ne da abinda ke
faruwar. Har yaji yana tsoron ace yarinyar ce ma ta rasa ran
nata. Dan dole dai ya daure ya isa inda ya nufa. A yau dai bai
samu Sayyid Faizul-Anwar a falon ba, sai dai kasancewar an
san da zuwansa ya samu tarbar data dace. Bayan zaman
kusan mintuna arba'in Sayeed ya fito cikin shigar jallabiya,
cikin girmamawa Barrister ya gaidashi, ya amsa masa da
kulawa shima yana masa barka da zuwa. Suna tsaka da
gaisuwar cikin yaran Sayeed ya shigo ya isar da saƙon

30 / 34