Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dauɗar Gora Complete Hausa Novel by Bilyn Abdull Ce

Author :  Bilyn Abdull ce Category :  African Stories & Novels

Chapter   2 / 34

3K to 6K   out of 100K words

san akwai matsala tattare dasu. Komai ya sauya,
sauyawa irin wadda ƙaddara ta shigo cikin tarihinsu. Babu
mai walwala a cikinsu, komai na ƙarfin hali sukeyi, abinci ya
gagara ciyuwa yanda ya kamata a koda yaushe garesu, sai cin
ƴaƴan itatuwa, tunkan a sanar musu alamominsu sun
tabbatar da zaman makokinsu. A haka duhun wani dare na
cika watanni uku da kwana uku da auren Arfa ya sake
riskarsu, suka sake zama ƙarƙashin mulkin mallakar ɓarawo
mafi iya sata koda shiri ko babu wato (barci). Daren da yazo
ma Iffah da wasu irin munanan mafarkai masu firgici daban
tsoron.
Har rige-rigen fitowa suke daga ɗakunan barcinsu
sakamakon fitar sautin razananniyar ƙarar data karaɗe gidan
mai ban tashin hankali. Su duka huɗun suka rufu a kanta
kowa na ambaton sunanta da kai hannu jikinta. Duk da sanyi
da akeyi jike take sharkaf da zufa ga illahirin jikin nata daya
ɗauka zafi. Ummu ta rungumeta tana mai sakin hawayen da
ke kwance a cikin idanunta. Ta riga ta farka dan haka itama ta
ƙanƙame Ummun tana fashewa da nata kukan.
Ba yau ne karan farko da Iffah ke shiga irin wannan tsoron
ba sakamakon firgici a mafarki, sai dai na kwanakin nan yafi
razanarwa da saka ruɗani a zukatansu. Babiy ya kai hannu ya
shafa yalwataccen gashin kanta, murya a raunane yake
ambatar sunanta.. Kanta ta ɗago a hankali fuskata sharɓan da
hawaye, ta dubi mahaifin nasu da Yayansu Hanash da Fariha,
sassanyar ajiyar zuciya ta sauke tare da haɗiye sauran kukan
tana tashi zaune daga jikin Ummu ta share hawayen dake jiƙe
da fuskarta. Matsawa tai jikin mahaifinsu tana mai kamo
hanunsa.
“Babiy inajin tsoro, matuƙar tsoro a wannan mafarkin fiye
dana kullum. Babiy itama Nina Arfa kashemana ita zasuyi
kamar sauran matan daya aura?, itama zamu rasata na gani a
mafarki na...”
Da sauri Hanash da dukkan rauninsa ya bayyana a
fuskarsa ya shiga girgiza mata kansa cikin aro jarumta.
“Mafarki ba gaskiya bane Iffah, ki kwantar da hankalinki Arfa
na cikin ƙoshin lafiya tamkar mu insha ALLAHU...”
“Amma Akh Hanash nawa yasha zama gaskiya, a daren da
Nina Arfa zata bar gidan nan irin wannan mafarkin nayi a
kanta, yau ma shine na maimaita da ita babu banbanci a
cikinsa na rantse maka”.
Har ƙasan zukata zancen nata ya dake su, ganin bayyanar
rauni a fuskokinsu ya saka Babiy yin murmushin ƙarfin hali
yana shafa kanta. “Shaiɗanu zasu iya dawo miki da
makamancin sa ai Ibnati, dan haka ki kwantar da hankalinki
Arfa na lafiya a gidan aurenta”.
Bazata cigaba dayin jayayya da su ba, amma tana cikin
matsanancin damuwa tamkar yanda take hango tasu akan
fuskokinsu. Maimakon komawarsu barci sai duk suka miƙe
zuwa tsakar gida, alwala suka ɗauro, suka koma can runfar
dake matsayin falon iyayensu suka fara salla da miƙa kukansu
ga UBANGIJIN talikai da fatan hana tabbatuwar abinda
zukatansu ke cikin tsananin fargaba. Haka suka kasance har
sallar asubahi gaban mahaliccinmu, bayan idar da sallar
asubahi maimakon kwanciya sai suka riski kansu a zaman
jugum-jigum na jiran tsammani. Har fitowar rana babu wani
yunƙuri daga ɗayansu. Sai ko ga isowar abinda suke fargabar
ya riskesu ya iso garesun. Shigar bugun gidan a cikin
kunnuwansu ta sakasu miƙewa a zabure gaba ɗaya kuma a
lokaci ɗaya, kowanne cikin rawar jiki da fidda tsammani.
Babiy ne yay jarumtar ƙarasawa ga soro cikin jan ƙafa. Tunda
yay tozali da hadiman masarauta zuciyarsa tai wata irin
masifar wulƙitawa.....
“Kun kasheta itama ko?!”.
Da shi da hadiman suka riski muryarta a cikin kunnensu a
bazata. Sam babu tsoro ko shakka irin wadda akema duk
wani mai alaƙa da masarauta a ƙasar cikin idanunta a yau.
Sun soye sunyi jazur irin na tashin hankali. A harzuƙe cikin
hadiman ɗaya ya daka mata tsawa da faɗin, “Hattara ɗiyar
talakawa, bakin rijiya ba wajen wasan yaro bane”.
“Idan yaron ya kasance rago ba!!”.
Ta bashi amsa itama a tsawace. Shimfiɗeɗiyar bulalar
hanunsa ya ɗaga zai zuba mata Babiy ya kare cikin rawar jiki
yana mai zubewa ƙasa a kan gwiyawunsa. Sosai a zaba ta
ratsashi, ya rimtse idanu cikin aro dakiya da jarumtar dole, “A
gafarceta ita ɗin yarinyace masu nasara”. Ya faɗa cikin rawar
murya saboda azabar tasirin shigar bulalar.
Ƙasa Iffah takai durƙushe gaban Babiy tana mai fashewa da
kuka, kafin ta ɗago ta dubesu zatayi magana Babiy yasa
hannu ya rufe mata baki jikinsa na tsuma. Jikin nata itama
tsumar yakeyi, sai dai ita bana tsoro bane na tsananin baƙin
ciki ne da bushewar zuciya. So take ta amayar da abinda ke
bakinta an hanata. Batare da hadiman sun sake bi takantaba
suma suka isar da saƙon dake tafe da su.
“Kasancewarka mai biyayya da bin umarnin masarauta a
karo na biyu an sake baka damar halartar jana'izar ɗiyarka kai
da zuri'ar ka. Mun barka lafiya”.
Innalillahi wa-inna'ilaihirraji'un. Babiy ya shiga ambata,
kusan a tare Ummu da Fariha suka saki razananniyar ƙara
wadda ta jawo hankalin maƙwafta da mutanen dake tsaitsaye
a ƙofar gida tun wucewar hadiman masarauta. Dan sun san
dai labarin gizo bazai wuce na ƙoƙi ba........

*_WASA FARI GIRKI_*

Dole ne zuri'ar mal. Zayyan su ambaci rasuwar Arfa da
kalmar WASA FARIN GIRKI a jerin zaren ƙaddarar da ta kutso
a rayuwarsu mai ɗauke da almakashin da ya datse farin
cikinsu. Sun rasata tamkar labarin hikayoyin marubuta ko
wasan kwaikwayo na film. Ta tafi tafiyar da bazasu sake
ganita ba, tafiyar da babu wanda aka bawa damar yin
cikkakkiyar sallama da ita a cikinsu hatta mahaifansu. Ta
shuɗe a ƙaddararsu tamkar yanda ruwan damuna kan tafi da
duk wani yayin dakan tare masa hanya a lokacin wucewa.
Komai ya faru tamkar ba'aiba. Babu mai iya koda tari balle
bin ba'asi. Iyakarsu kukan idanu dana zuci wanda muryarsu
kan tsayane kawai iya filin gidansu ko katanga basu isa bari ta
haura ba. A yau ma dai Babiy da Hanash ne sukaje domin
jana'izarta. Suko aka barsu da amsar gaisuwa a cikin gida
wadda mutanensu talakawa na zuwa musu itane a
ɗarare.......
Kwanaki sun cikagaba da shuɗawa tamkar ba'ai komai
ba, yayinda ɗayar matar Tajwar da aka aura masa tare da
Arfa itama dai ta mutu bayan wasu watanni. Bayan su Arfa
ba'a sake jin Tajwar yayi wani aure ba, sai dai mutane na
raɗeraɗin a duk randa aka kaisu domin ziyartar turakarsa
babu fashi gawarsuce take fitowa. Hakan yasa kowa ke
danganta mutuwar matan da tsafi yakeyi dasu.
Wata huɗu da sati ɗaya cif tarihi ya sake maimaita kansa,
dan kuwa Fariha ta sake faɗowa a jerin matan da aka
ɗaurama Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdul-majeed aure da
su. Batare da wani shawara ba a safiyar alhamis suna zaune
kira ya riski Babiy daga masarauta, babu wanda bai shiga
tsoro da firgici ba a cikinsu, sai dai babu wanda ya isa hana
hakan a duk faɗin ruman. Sunaji suna gani babiy yay shiri ya
amsa kiran. Tafiyarsa da awanin da basu gaza biyar ba sai ga
hadiman masarauta sunzo sunma Fariha ɗaukar amarya
itama babu wani bayani daga garesu. Ranar dai kam Iffah
bata gazaba kojin tsoro wajen gwada musu hauka, dan bata
bari an fita da Fariha ba har sai da basamuden nan ya zabga
mata bulalar dorinar hanunsa data sakata zubewa, bata tashi
dawowa hayyacinta ba sai bayan wucewarsu da kusan awa
guda. Zuwa lokacin har Babiy ya dawo. Kamar dai Arfa itama
Fariha an ɗaura mata aure da sarkin da kowa yake masa
inkiya da fir'aunan wannan ƙarnin. Sai dai a ɓoye wannan
suna ke fita a bakunan talakawan gari irinsu Iffah. Sakamakon
bulalar da aka zabga ma Iffah bayanta yay mugun fashewa
har akan mazaunanta, ga wani raɗaɗi mai azaba na ratsata
har ta kasa riƙewa sai da ta saki ƙara. Babiy da Ummu suka
rufu a kanta, hawaye suke suna jeramata sannu, Hanash na
gefe zaune idanunsa jajur alamar tsananin ɓacin ran da babu
ƙarfin ɗaukar mataki......
Tayi jiyya ta kwanaki uku, wajen ya warke, daga haka
kwanaki suka cigaba da tafiya, inda a cikar watanni biyu
itama Fariha mutuwarta ta riskesu tamkar ba'ayita ba. Sun
sake rasa Fariha a dalilin auren Tajwar Eshaan ibn Haysam
Abdul-majeed........✍😭



*_Hummmm!!😕_*

3

_____________

MAAB LUXURY HOME!! Sabuwar duniyar hamshakan mata da
ƴaƴan gata.💞

GIDAN ƙawa da ƙawata gidajen da suka cika gida.

SABUWAR DUNIYAR Amare da uwargidan data amsa sunanta
ƴar gaban goshi.

MAAB LUXURY HOME wata duniya ce ta ƙawa da ƙawata
gidajenmu da kayan ƙyale-kyale na burgewa da ɗaukar
hankalin duk wani mai kallo.

SUNYI FICE Fice irin na ɗaya a cikin tsara, sune na farkon fari,
a farin da za'a kira fari a kowace irin duniya.

A GAREMU ba sitturu na alfarma da kawa ne kawai ke
tabbatar da mu hamshakai ba. Sai mun haɗa da ƙawata
gidajenmu da kayan MAAB LUXURY HOME zamu kasance
cikakkun ƴan gata ababen kallo da nunawa sa'a koda a cikin
dubun da sukafi dubu.

MAAB LUXURY HOME sun takaita mana dukkan wahalar
nema ko order a kasashen ketare ta hanyar wadatamu da
galla-gallan kayayyakin adon gidajenmu

MAAB LUXURY HOME. Duniyar kayan Kitchen da decoration
din gida na keta raini.

INA UWARGIDA INA AMARYA!!?* Ku ziyarci shagon mu dake
No 22 Ahmadu Bello Way, Kano state. Ko kuyi order daga
shafin mu na Instagram @maabluxuryhome. Ko Facebook
@maabluxuryhome. Ko Ku nememu a lambar waya
*08034631010*.

Mai azama shi za'a kira dana farkon fari😉. Bara nai sauri
nawa suzo hannuna kafin a kwashe😁♀️

______________

.........A wannan gaɓar haukane kawai ya rage wannan ahali
suyi, dan duk dauriyar Babiy ya kasa danne raɗaɗi da zafin da
yakeji. Itako Iffah kalaman dake fita a bakinta kausasa sun
saka kowa ke ɗaukar tama zare kawai. Daga ƙarshe maganin
barci aka ɗura mata. Bata tashi farkawa ba sai a ƙauyen da
kakanninsu ke rayuwa. Wato iyayen Ummu. Rayuwa a
ƙauyen Jumna a gareta tamkar mai gushewar hankali ya
zame mata. Domin bata gane komai sai sambatu da kalamun
ɗaura ɗammarar ɗaukar fansa ga duk ahalin Daular Ruman.
Ba ƙaramin dagewa da jajircewa kakannisu da su Babiy sukai
ba a kanta wajen ganin ta samu lafiya ta dawo hayyacinta. A
cikin watanni takwas ta rasa yayunta guda biyu, wannan
babban tarihine da bazai gogu a zuciya da ruhinta ba har
karshen rayuwarta. Bayan jiyyar watanni kusan uku ta dawo
hayyacinta. Sai dai ta daina fira'a da kowa, an daina ganin
dariyarta ko farin cikinta. Babu abinda ke'a ranta sai buri da
ƙudirin ɗaukar fansa. Tama kanta alƙawarin ita da hannunta
zata kashe *_Tajwar Eshaan ibn Haysam Abdull-majeed_*.
Bayan nan idan itama an kasheta burinta ya cika na kawar da
azzalumin sarki mai mulki irin na fir'auna a ƙasarta a cikin
al'ummarta....

*_(Babbar magana. Tayaya wannan buri naki zai cika Iffah
😱? Sarki mai cikakken iko irin Tajwar Eshaan, mai amsa
sunan Shahan-shan da ko fuskarsa babu wanda ya iya sani a
cikin kasar Ruman har yanzun. Anya kuwa....? To mudaije
zuwa wai mahaukaci ya sai kura😬🤧🚴🏼)_*



★★★

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un” bakinta ke ambata cikin
firgici da rawar jiki sakamakon farkawar da tayi daga
mummunan mafarkin daya risketa a cikin barcinta. Ta dafe
kanta dake wata irin sarawa na ciwo tamkar ana mata
luguden taɓaren daka a tsakkiyarsa, gaba ɗaya jikinta ya jiƙe
da zufa tamkar tayi wanka. Kusan watanni biyar kafin
mutuwar ƴan uwanta da fara canjawar salon mafarkainta
saɓanin na baya, abu mafi tsoratarwa kuma kusan mafarki
ɗaya ne ke maimaita kansa a kowane barcinta idan ta
kwanta. Sai dai mafi tashin hankalin a yau yayi
kamanceceniya da na wasu dare da tarihi bazai taɓa
mantawa da shi ba a cikin rayuwarsu ita da ahalinta.
“Nina Arfa! Nina Fariha!”.
Ta ambata a zahiri zuciyata na ƙara ƙarfin gudu, yayinda
hawaye suka shiga rige-rigen sauka a kumatunta. Tabbas irin
wannan mafarkin tayi a daren da suka rasa Arfa, hakama
daren mutuwar fariha. Yau kuma gashi ta maimaitashi akan
kanta. Itama kenan zasu rasata?. Kai ta shiga girgizawa wani
kuka masu ƙarfi na sake tahomata, hannu tasa ta toshe
bakinta gudun kar sautinsa ya kai ga kunnen kakanninta. Sai
dai aikin gama ya gama. Dan kuwa muryar kakanta takeji jikin
ƙofar ɗakin nata a hankali yana ambatar sunanta. Da sauri ta
shiga goge hawayen, kafin ta tashi daga shimfiɗar barcin nata
wadda karan gado ne da katifar rimi. Mayafi ta ɗauka ta
yanama jikinta, ta ƙarasa ga ƙofar ta buɗe...
“Kina lafiya kuwa ɗiyar nan?”.
Ya faɗa cikin kafeta da idanu. Kanta dake rissine ta jinjina
masa, cikin son danne kukan dake yunƙuromata ta bashi
amsa.
“Ina lafiya Kaka”.
Jin shiru bai sake cewa komai ba ta ɗago ta dubesa a karon
farko. Shima dai kallon nata yakeyi tamkar mai nazari. Sake
maida idonta tai ƙasa, hawayen da take faman riƙewa suka
ɓalle mata da gudu. Bata san ta ambaci “Kaka nima zasu
kashe muku ni ko?. Inaji a jikina nima zaku iya rasani nan kusa
tamkar yanda muka rasa su Nina Arfa”. Rawar da jikinta ta
fara ta sata zubewa a gabansa kuka na ƙwace mata. Kusan
minti biyu baice da ita komai ba, ita kuma ta kasa tsaida
kukan.. Jin saukar hanunsa saman kafaɗarta ya sata haɗiye
kukan, ya ɗagota tsaye yana ɗan murmushi dake sake
bayyana tsufansa. Gefen mayafin jikinta ya kama ya shiga
goge mata hawayen. “Fareedatu! Ki kwantar da hankalinki,
insha ALLAHU babu abinda zai faru da ke, mafarki ai ba
gaskiya bane ba. Suma su Arfa kwanansu ne ya ƙare, koba
komai kuma sun rasu a gidan aurensu. Wannan kawai ya
ishemu farin ciki”.
Kanta ta jinjina masa tana sauke ajiyar zuciya a jajjere. Ya
cigaba da shafa kanta a hankali har zuwa wani ɗan lokaci.
“Kije kiyi addu'a ki kwanta abinki da safe zamuyi magana”.
A hankali tace, “Kaka ina son zuwa naga su Ummu gobe to
dan ALLAH”.
Da sauri ya girgizamata kansa. “A'a bazai yuwu ba Iffah,
iyayenki sun kawoki nan ne domin kuɓutar dake, taya kike
tunanin zan barki komawa cikin daular Ruman?. Tun ina
ƙanƙanin yaro nake bauta wa masarautar Ruman, bayan
mutuwar mahaifina na cigaba da bautar saƙa kayan doki a
garesu kamar yanda mahaifina ya barmin gado, a haka na
haifi ƙanin mahaifiyarku shima ya mayeni, gashi har girma ya
riskesa shima yana bauta musu. Mun rasa ɗan uwan
mahaifiyarku a yaƙin kare daular Ruman, mun rasa Arfa, da
Fariha. Ke ɗaya da kika rage mana da yayanki wajen
mahaifiyarku kuma sai muyi wasa da rayuwarki? Bazai
yuwuba jeki kwanta...”
Batare daya sake bata damar yin magana ba ya juya ya
koma bayan ya jamata murfin kofar. Da kallo kawai ta bisa
hawaye na silalo mata. Duk yanda taso komawa barcin bayan
tafiyarsa hakan ya gagara, zuciyarta ta kasa fita da ga ƙangin
fargaba, da gaske tanajin matuƙar tsoro bayan rasa Fariha da
Arfa da sukai watanni ƙalilan da suka shuɗe itama su rasata,
tanaji zuciyar ahalinta bazata iya ɗauka ba idan itama suka
rasatan. Wasu zafafan hawaye suka sake silalo mata masu
raɗaɗi da saka ƙuna a ƙirji......

★★★

“Iffah! Iffah!!.....”
Sautin ƙwala kiran sunanta daga muryar kakarsu da suke kira
Iyyani ya sakata fitowa daga banɗaki data zagaya domin yin
fitsari. Turus ta tsaya tare da haɗiye maganar da zatayi tana
mai kallon ɗan-uwanta Hanash dake zaune gefen kakar tasu a
ƙarƙashin bishiyar ɗoruwa da take a tsakar gidan. Murmushin
da yakemata ta maida masa, kafin ta ajiye butar hannunta ta
ƙarasa garesa. Dab da shi ta zauna tana mai ɗan rungumesa
ta gefe da faɗin, “Ina kewarku Akhi”.
Murmushinsa ya sake faɗaɗa yana mai kallon fuskarta.
Ya kai hannu ya shafi yalwataccen gashin kanta da mayafin ya
zame mai tsaho da santsi. “Muma muna kewarki Little angel.
Gidan duk ya sake zama mana babu daɗi”.
Yanda maganar tasa ta ƙare cikin rauni itama sai idonta ya
cika da ƙwalla. Amma sai ta dannesu da murmushin mai ɗaci
tana kaɗa kanta kawai.
“Tashi ki bashi ruwa mana, k haka ake tarbar baƙo a
garinku”.
Baki ta ɗan tura gaba da kallon Iyyani mai maganar, tayi
hakane danta katse raunin data hanga a fuskokinsu. Ta miƙe
tana bata amsa cike da shagwaɓa. “Iyyani laifinkine fa, ban
taɓa ganin matar da bata tattalin mai gida ba irinki, dole
Yayana ya miki kishiya”.
Daƙuwa tamata cikin gatsina fuska. “Ungo naki nan
Fareedah, yo bandama lalacewa mizanyi da wannan faratun
mai kama da jar tsada tuzurin banza”.
Hanash ya tsuke fuska yana kallon Iyyani. Murmushi
Iffah tayi tun kafin ya faɗi abinda ke bakinsa. Dan dama inhar
suka haɗu da Iyyani sai ta hasalashi take jin daɗi shi da Arfa
akan ƙinyin aure, duk da bawani shekarune da shi ba, dan
ashirin da shida ne kawai, Arfa nada ashirin da uku, Fariha
nada ashirin da ɗaya. Iffah nada goma sha takwas....
Iffah ta dire masa abinci da ruwa ta sake kaiwa zaune
kusa da shi sannan ta dubesa. “Akhi yasu Babiy suke?”.
Ya nisa a hankali bayan ya dire moɗar ruwan daya sha.
“Duka lafiya suke. Suna gaisheki ke da su kaka. Duk da suma
dai nan da kwana kusa zamu ma dawo nan ɗin muma. Yanzu
haka nazo duba can tsohon gidanmu ne dan asan gyaran da
za'ai masa”.
Sosai ta kafesa da ido ita da Iyyani. Kafin cikin ƙarfin hali
Iffah tai magana. “Amma Yaya su Babiy basa ganin rayuwa
zata mana wahala anan sakamakon bamu sababa sam.
Sannan ayyukansu dake acan miye makomarsu? Da
karatunmu muma?. Abinda ya faru ya riga ya faru, tunda
hannayenmu bazasu iya maidosu ba, mi zaisa zukatanmu
bazasu cigaba da haƙuri ba. Barowarmu cikin Daular ruman
tamkar munji tsorone, ko sake sakin rayuwarmu a hanun
waɗanda kansu kawai suka sani.......”
“Tsoro halak ne Iffah. Bama muba mafi yawan masu yara
mata sunata barin daular ruman a yanzu domin tseratar da
ƴaƴansu daga auren jeka nayika. Karatun ƴammata yana
neman tsayawa cak, kowace na tsoron fitowa ta zama nama
a hanun hadiman daular ruman. a yanda lissafin yake a yanzu
an rasa mata goma sha huɗu fa, a tunaninki kafin ƙarewar
wannan shekarar ba'a rasa fin hakaba duk da bawai ya cigaba
da auren bane.”
Wasu hawayene masu ɗaci da ƙuna suka silalo ma Iffah,
tai saurin saka gefen mayafinta ta share tana murmushin
takaici. “Niko a ganina gudu bashine mafita ba, muryoyinmu
ya kama mu ɗaga wa duniya kowa yasan halin da muke ciki,
idan har a ƙasar Ruman babu wani sama da nasa mulkin ai a
sauran ƙasashen duniya akwai wanda suka fisa...”
“Humm Iffah ke yarinya ce har yanzu.”
“Sosai kuwa Hanash. Shiyyasa bata gane komai sai abinda
yanzu take zuwa da shi”.
“Humm Iyyani kenan”.
Iffah ta faɗa a yanayin jin raɗaɗi a maƙoshinta. Su duka
kallonta sukai, sai dai ta ɗauke kanta gefe tamkar bata gansu
ba. Daga haka babu wanda ya sake cewa komai har tsahon
wani lokaci. Iyyani ce ta canja hirar da wani abu daban har
Hanash ya kammala. Tare da shi suka fita wajen duba tsohon
gidan da kakaninsu da suka haifi Babiy ne suka rayu a ciki,
dan sudai tunda suka taso a cikin birinin daular ruman suka
san kansu duk da a ɗan gefen gari suke acan ɗin ma. Sai dai
su shigo cikin ƙauyen Jumna a matsayin duba kakannin nasu.
zuwa yanzu su duk sun rasu, shiyyasa gidan ya kasance babu
kowa. Duk ma ya rusa ya fita hayyacinsa dan

2 / 34