Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dauɗar Gora Complete Hausa Novel by Bilyn Abdull Ce

Author :  Bilyn Abdull ce Category :  African Stories & Novels

Chapter   14 / 34

39K to 42K   out of 100K words

Daga haka aka ƙara bata magungunan da duk suka
dace da gyara mata kwanciya a lafiyayyen gadon da yaji
shimfiɗu na alfarma. Wani irin barcine mai daɗi yay awon
gaba da ita, cikin ƙanƙanin lokaci ta fara sauke numfashi.
Daneen Ammarah dake kallonta cike da tausayawa da jin
wani ɓoyayyen al'amari akan yarinyar ta sauke numfashi
ahankali da mata addu'ar samun lafiya da fatan ya zama
kaffara a gareta.......

★★.... ★.... ★★.....

Duk wani nau'in kiranye ga uwa ta yisa tun lokacin da
labarin abinda ya faru da yarinyar can sakamakon saka riga ya
risketa, tabbas sune suka bada riga, amma abinda ya faru da
yarinyar bashine ya kamata ya faru ba akan rigar, dan shirinsu
sam bashi da alaƙa da halin da take a ciki yanzun. Hakan na
nufin kenan bayansu akwai wasu masu shiri akan yarinyar
kenan?. In dai har hakane kuwa to su ɗin su wanene? Minene
tasu manufar kuma?.
Wannan amsar take buƙatar ji a wajen Uwa, sai dai har
zuwa duhun dare babu alamar zata ziyarce ta. Tun zuciyarta
na raya mata ta jira har ta fara jin ita taje gareta mana kawai.
Amma tuna zuwa ga Uwa babban al'amari ne mai wahalar
yiwuwa gareta yasa ta kasa iya cigaba da tabuka komai har
dare ya cigaba da tsalawa masarautar ta ɗauki shiru tamkar
babu wani mahaluki mai sauran numfashi. Ta cigaba da
kaikawo a cikin wannan shiru, tare da ƙara gwada dabaru
kala-kala na kiranye ga Uwa. Dai-dai lokacin da take sarewa,
gaɓɓanta ke nuna gajiyawa mummunan sautin dariyar Uwa
mara daɗin saurare a kunnuwa ta fara mata kaikawo tamkar
tana yawo cikin iska. Ƙasa ta zube akan gwuyawunta tana mai
jan nannauyan numfashi dajin sanyi a ranta. Tarwai Uwa ta
bayyana a gabanta, akan kujerar baƙin karfenta mai adon
gwal sanye cikin jajayen kaya kamar koyaushe. Mummunar
fuskarta a matuƙar tsuke take babu alamar itace ta gama
dariyar dataita amsa kuwa a mintocin da suka shuɗe.....
“Barka da isowa Uwa mai share kukan masu kuka. Uwa
ina cikin matuƙar ruɗani, dan aikinmu yasha banban da
wanda ya bayyana ga ƴar shilar suda. Kamar yanda na riski
yinin jiya a cikin ruɗani, haka na kasance a duhun dare batare
da na rintsa ba, na kuma sake wayar gari da ƙishirwar ganinki
a yinin yau har zuwa iyanzu da daren ke ƙoƙarin zama dare
biyu da faruwar komai?. Shin kuskuren daga garemu ne?
Kokuwa kece kika canja aikin ya koma hakan? Ko akwai wasu
masu irin shirinmu ne a wannan daula batare da mun san
dasu ba? Minene manufarsu su? Wane buri kuma suke da
shirin cimmawa?. Uwa ki taimakeni nasan wannan amsoshi in
ba hakaba zuciyata na gab da tarwatsewa ne”.
“Bazan gaji da tuna miki akwai ƙalubale zagaye da cikar
matakin aykinki na biyu ba, kuma wannan ƴar shila na tare da
kaddarar ƙalubalenne, sai dai na miki alkawarin tsayuwar
daka akan hana faruwar nasarar da zatazo in har bataki bace
ba. Tabbas aikin ba namu bane, kuma rigar da aka kai mata ta
sanya ba tamu bace itama. Na gano hakane a daren jiya
bayan mutuwar waɗan can hadiman da kuma samun lafiyar
ƴar shilar.. Hakane ya sani duƙufa bincike tuƙuru domin gano
daga ina matsalar take?, wanene ya shirya aikin laɓewa
bayan namu? Har yaci nasarar kuɓutar da ita da tarkon
makircin sa cikin sauƙi haka?......”
“Uwa kin gano kenan?”. Ta-kurya ta tari numfashinta cike
da zalamar son jin amsa........✍️

21

________________________

_Innalillahi wa-inna ilaihirraji'un. A madadin ɗaukacin ɗalibai
na G.G.A.S.S D/Z. Muna miƙa saƙon ta'aziyyar ga ƴan
uwanmu da iyayenmu da yayyenmu na rasa Uwa abin
alfaharin duk wani ɗa na gari da mukai *Hajiya Ai'sha Ahmad
Tukur* tsohuwar principal ɗinmu. Ya rabbi ka gafarta mata,
ka yafe mata kurakuranta. Ka bama iyalanta da mu haƙurin
rashinta. Mu data bama tarbiyya a wani bigire na rayuwa,
ALLAH yasa muyi koyi da ƙyawawan halayenta managarta.
Dan ita ɗin abin alfaharinmu ce da bazamu taɓa iya mantawa
ba😭 , zamu tunata, zamu cigaba da tunawa da ita, zakuma mu
tunatar dana bayanmu kyawawan halayenta da alkairinta.
(ALLAH ya gafarta mata.😭 )_


________________________
...........“Ina kan ƙoƙarin yin hakan yawaitar kiranyanki ya
katse ni, amma tabbas wanda ya aikata yana a cikin wannan
daula ne, yana kuma da babban shirin daya kamata mu sani
tun a yanzu. Ina kuma ji a jikina babban yaƙine da kema ya
shafeki, kuma za'a cigaba da amfani da yarinyar ne wajen
tabbatar da shi in har tana cikin masarautar nan”.
“Shiyyasa tun farko nace a kawar da ita Uwa, dan babu
wani amfani da wannan yarinyar zatamin face cigaba da
ɗagamin hankali, gashi kuma har tana neman zama tafinta a
al'amurana dake gab da kammala bayan gumurzun yaƙin da
naci na tsahon shekaru a baya kafin zuwa lokacin tattara
ganima”.
“Abinda kike ƙoƙarin yi shine mafi girman kuskure da zai
rusa dukkan nasarorinki Ta-kurya. Domin yunƙurin kashe
wannan ƴar shilar da kike tamkar kashe rayuwarki ne baki
ɗaya. Tun farko na faɗa miki kasheta kai tsaye bashine
mafitar ba, ba kuma shine ƙarshen daƙile yunƙurinta ba ita a
karan kanta. Hasalima a yanzu rayuwarta mukafi buƙata,
zamu jefata ne matsayin dutse ɗaya dazai wargaza tsuntsaye
biyu. An wargaza mana shirin mu na farko a kanta, dan haka
zamu tafi na biyu. Yaƙinki a yanzu shine kiyi duk yanda zaki ta
baro wancan sashen daga nan zuwa cikar kwanaki bakwai.
Zakiyi yanka na baƙar babbar dabba a daren goma sha uku,
zakuma ki dawo da rigar data sanya. Kiyi duk wani ƙoƙarin da
zai hana kusancinta da Ajlaan a turaka. Dan maganar kaita
turakarsa ta rushe kuma zamu sake sabon salo ne domin
kama tsuntsu mai wayo.......”
“An gama Uwa mai share kukan masu kuka. Sai dai dawo
da rigar nan zai zama abu mai wahala kasancewar tana a
hanun Mamma (Malikat Haseena) ne a yanzu haka”.
“Wannan umarni ne Ta-ƙurya”.
“Zanyi iya ƙoƙarina Uwa. Sai kuma maganar mutuwar
Hadiman can, Shahanshan da kansa ya saka kwamitin bincike
masu tsauri da basu taɓa ƙetare nasarar cika umarnin da'aka
basu ba. Kinga akwai matsala kenan tunda waɗan can sun
laɓe ne a jikin aikinmu suka zartar da nasu, sannan suka
kashe hadiman tamkar yanda muka shirya kafin mu mu
aiwatar da hakan”.
Wata irin mahaukaciyar dariya mai amsa kuwwa Uwa ta
shiga ƙyalkyalawa, sai da ta ɗauka tsahon lokaci tanayi kafin
ta tsagaita ta tsuke fuska tamkar ba itace tayin ba. Har ta
ƙurya ta fidda ran samun amsa sai kuma Uwa ta sake
ƙyalkyalewa da dariya tana ambaton “Ajlan! Ajlan!! Ajlan!!!”
ta ƙara kwashewa da dariya tana mai disashewa a idanun Ta-
kurya da zuciyarta ta kasa fassara ma'ana ko dalilin dariyar ta
uwa...

🤔Ko miye naku tunanin a wannan gaɓar kuma masu
karatu???.

★... ★.★.★ ★...

*_GIDAN BABIY_*

Sun dawo har yanzu da ɗan sauran mutane maƙwafta da
aketa ɗan ƙus-ƙus akan lamarin. Cikin ƙanƙanin lokaci aka
baibaye motar, waɗanda suka shige gidaje suka fara fitowa. A
yanayin da aka fidda Ummu mafi yawansu sunma ɗauka dai
bata da rai, dan kuwa da gaske babu alamar rai tare da itan.
Kuka da salatin da mafi yawan mutane suka ɗauka na tunanin
ta mutun ne yasa Abu Zainab saurin dakatar da su.
“Dan ALLAH kowa ya kwantar da hankalinsa. Umm-Arfa
ba mutuwa tai ba”.
Badan hankalin su ya kwantaba sukai shiru, sai dai dama
kukan na wasu na munafurci ne dai. Matane suka kamata aka
shiga da ita, a tabarmar da suka samu tsakar gida suka
shimfiɗeta. Cikin sa'a Abu Zainab yaci karo da wayar Babiy
dake yashe a ƙasa. Da alama sanda jami'an nan zasu fita da
shine ta faɗi. Jikinsa har tsuma yake a duba contact ɗin
wayar, cikin sa'a ya samo number da akai saving da Baba.
Baya raba ɗayan biyu mai sunan nada babban matsayin
baban a wajen Babiy ɗin, dan haka ya danna masa kira kai
tsaye, sai dai harta tsinke ba'a ɗaga ba. Sake kiran yay yana
addu'ar dacewa sai ko gashi an ɗaga...

★A lokacin da kiran Abu Zainab ya riski su kaka ta hanyar
wayar Babiy ba'a ƙaramin tashin hankali suka tsinci kansu ba
shi da Iyyani. Duk da kasancewar yamma tayi kuma yasan a
yau dole ne sai ya dangana da daular ruman dole ya bazama
neman wani yaro mai mota a ƙauyen nasu dake jigila a ko
yaushe, cikin sa'a ya samesa ya dawo kenan ma ko gida bai
shiga ba. Amma saboda mutuncinsa da ake gani yana masa
bayani babu musu ya amsa masa suka ɗauka hanya harda
Iyyani daketa faman sharar hawayen da suka kasa tsaya
mata. Ana sallar isha'i suka iso cikin daular ruman. Basu sami
mutane ba a gidan kamar ɗazun, sai Umm Yazeed da matar
Abu Zainab dake dai tare da ita har yanzun. Zuwa yanzu
Ummu ta farfaɗo, sai dai taƙi magana da kowa sai hawaye da
taketa faman zirarwa ta gefen ido, ga numfashinta baya fita
normal kamar na kowa, tana fitar da shine da fisgosa a
wahale sannan a fiffisge. Kuka Iyyani ta sake fashe da shi da
rungume Ummu a jikinta tana kiran sunanta. Kaka kam tsaye
yay kawai zuciyarsa na harbawa da ƙuna. Suna a haka Abu
Zainab ya dawo, dama sallar isha'i yaje. Cikin girmamawa ya
gaida kaka, shima ya amsa masa da kulawa da godiya. Ya ɗan
murmusa kansa a risine. “Ai ba komai baba yiwa kai ne.
Sannan mun zama ɗaya ai mu da Abu Hanash. Ko mu irin
haka ta faru da mu zai tsaya tsayin dakane a kan komai.
Ruɗanin halin da Umm Arfa ke ciki yasa su bamu bibiyesu
musan miya faru ba har yanzu gaskiya. Dan munata yawo a
asibitoci amma sunƙi amsarta, ga jikin nata kuma yana
buƙatar a duba mata shi, shiyyasa yanzu dana idar da sallar
magrib naje na samo ɗan uwana dake aikin asibiti gashi muna
tare, sai dai ba wani babban likita bane dai....”
Kai kawai Kaka ya jinjina masa da faɗin, “ALLAH ya saka
muku da alkairi, haka ake fatan zaman makwaftaka, domin ita
makwaftaka tanada ƙarfin da zata iya fin ƴan uwantaka
muhimmanci ma a wani ɓangaren. Yanzu gashi abu ya
samesu, kafin mu muzo kun basu ɗauki, da bakwa zaman
lafiya kuma hakan bazai yuwuba. Dan haka duk wani mutum
na ƙwarai daya san kansa ya dace ya rayu da maƙwafcinsa
lafiya da ƙaunar juna”. “Hakane Baba, ALLAH ya saka da
alkairi. Bara na shigo da shi”. Murmushi Kaka yayi da jinjina
masa kai. Koda suka shigo tare da ɗan uwan nasa shima ya
gaida Kaka da girmamawa, hakama Iyyani da har yanzu ke
faman sharar hawaye tana tofama Ummu addu'a. Damar
duba Ummun Kaka ya bashi dan haka ya shiga aikinsa. Ya
tabbatar musu jinin Ummu ya hau matuƙa, amma zai mata
allurar barci ta samu nutsuwa dan barinta a ido biyu akwai
haɗari komai zai iya faruwa. Sai da suka maida Ummu ɗaki
sannan ya saka mata ruwa da allurai aciki, cikin sa'a kuwa
babu jimawa barci yay awan gaba da ita. Sosai Kaka yay musu
godiya da sanya albarka, dan ko sisi ɗan uwan nasa bai
amsaba ma.......


★★.... ★.... ★★.....

An wayi gari da samun canji sosai a yanayin Iffah, dan
zuwa yau kam Alhmdllh. Sai dai jikinta dake wani irin saɓa
saikace wata macijiya. Sai kuma rauni data tsinci kanta a ciki
sakamakon mummunan mafarkin datai akan su Babiy daya
haddasa mata matsanancin faɗuwar gaba da akai-akai. Gata
dai iya gata tana gani wajen tsohuwa Malikat Haseena duk da
bata da lafiyar ƙafa sai a wheelchair take komai. Hakama
Daneen Ammarah tsaye take kan Iffah, yanda take kula da ita
yasa Iffah jin ƙaunarta batare data san dalili ba, ganinta take
tamkar Ummu. Yanda ake tsaye kanta da gata da kulawa yasa
ko damar yin ƙwaƙwaran tunani bata da shi, dan da tayi shiru
Daneen Ammarah zata nuna damuwa taita jera mata
tambayar mike damunta? Ko tamanin wani abu ne a jikinta
har yanzu?. Dole take sassauta damuwarta, sai dai tayi
matuƙar dagewa wajen ambaton UBANGIJI kamar yanda
Babiy da Ummu suka dinga jaddada mata a nasiharsu ta
ƙarshe gareta. Labarin mutuwar hadiman da suka kai mata
rigar nan ta saka yazo kunenta itama, sai dai jin sanadin
mutuwar tasu ya tsaya mata a rai matuƙa, harma ta rasa yaya
zata fassara al'amarin...
Bayan idar da sallar isha'i tana zaune tayi tagumi gaba
ɗaya hankalinta ya tattara ga tunanin iyayenta da
mummunan mafarkin daren jiya a kansu Daneen Ammarah ta
shigo hadimai uku biye da ita. A bakin gadon takai zaune tare
da kai hannu ta janye tagumin da Iffah tai. Nannauyan
nunfashi ta sauke da ɗan ɗagowa ta kalla Daneen Ammarah
ɗin, sai kuma ta maida kanta ta risinar da mata sannu da
zuwa. Daneen Ammarah dake kallonta cikin damuwa taja
numfashi ta fesar batare data amsa ba. Dai-dai nan Hadiman
da suke tare suka zube gaban Iffah bayan sun ajiye kayan
hanunsu. Gaisheta suke da tsantsar girmamawar da ko iya
ɗaga kawunansu basayi su dubi sashen da take. Sam Iffah
batajin daɗin yanda suke matan saboda bata sababa, a ranta
gani take kamar ƙasƙancine. Hannu Daneen Ammarah ta
kaɗa musu alamar suje, zumut suka miƙe tamkar ƙyaftawar
ido suka fice. Iffah ta bisu da kallo cike da jin raɗaɗi a
zuciyarta.
“Ibnati!”.
“Na'am Mamy!”.
Iffah ta amsa cike da girmamawa ga Daneen Ammarah. Sosai
sunan da Iffah ke kiranta da shi ke raunanata da sake jin
ƙaunar yarinyar, dan a bakin mutum ɗaya tak take jinsa kafin
ita. Taja numfashi da haɗiye hawayen da suka cika mata ido
ta maye gurbinsu da murmushi.
“Ibnati bana son cigaba da ganin damuwar nan a fuskarki,
ki kwantar da hankalinki insha ALLAHU babu abinda zai sake
samunki. Wanda ma ya sameki ki ɗauka kaddararkice kinji,
amma inaji a jikina insha ALLAH kece mabuɗin nasararmu, ke
ce hasken da zata haska mana duhun da muke a ciki a Daular
nan kinji”.
Kai Iffah ta jinjina a hankali, haka kawai take jin matuƙar
nutsuwar kasancewa da wannan baiwar ALLAH, sam batajin
irin zafi da tsanar da takema duk wani mai alaƙa da
masarauta a kanta. Kallonta take tamkar wata katanga ta
wani babban al'amari dake tunkarota. “Mamy bana tare da
damuwa in har kina a kusa dani, duk abinda ya sameni kuma
dama ALLAH ya ƙaddara sai ya sameni koda banzo nan ba. Ina
tunanin su Ummu ne da jin tsananin kewarsu saboda
mummunan mafarkin danai akansu jiya, ina tsoron kar wani
abu ya samesu ne suma?”.
Cike da jin tausayita Daneen Ammarah ta shafa kanta,
“Duk ɗa na gari dolene ya kasance cikin kewa a lokacin da yay
nesa da ahalinsa, da ace inada dama da a yau sai na kaiki
kinga su Ummunki. Amma dokar masarauta ce Zawjata-
almilki tana fitane kawai bisa ƙwaƙwaran dalili, zuwa gidansu
kuwa tana yinsa ne sau biyu tak a shekara, ɗaya a sirrance,
ɗaya a bayyane tare da rakkiyar hadimai. Shiko mafarki ai na
gaskiya bane Ibnati, MANZANNI ne kawai idan suka yisa yake
gaskiya a garesu, amma mu namu yakanzo da wasu sigogi ciki
harda sheɗanu”.
A hankali hawaye suka silalo a kumatun Iffah, bawai
lokacin ziyarar bane yay mata nisa, rashin tabbacin kaiwa
lokacin ziyararne ya sata zubar hawaye. Ita dake zaman jiran
ƙaddarar mutuwarta taya zatai tunanin zuwan waɗan can
damarmaki guda biyu na ganin su Babiy, maganar mafarki
kam ta san gaskiya Mamyn ta faɗa, itama kuma ba tana
dangantashi da zama tabbaci bane, kawai tana matuƙar jin
tsoron faruwar wani abu ne a dalilin mafarkanta na baya....
Ganin hawayen Iffah ya matuƙar tada hankalin Daneen
Ammarah, a rikice ta shiga tambayarta kamar yanda ta saba
in har ta ganta a makamancin damuwar nan. Hannu Iffah tasa
ta share hawayen nata da ƙirƙiro murmushi.
“Mamy ki kwantar da hankalinki hawayen sunzo ne kawai
da kansu babu dalili”.
“Haba Ibnati, dama ana kuka babu dalili ne? Ko baki faɗaba
nasan kinada dalilan yin kuka, amma idan kika zama mai
haƙuri da juriya wataran ke zakiyi dariya a gaban waɗanda
suka cancanta suyi kuka.” (ALLAH ya tabbatar da wannan
ranar) Iffah ta faɗa a zuciyarta, a zahiri kam sai ta goge
hawayen tana murmushi. Hakan yasa Daneen Ammarah yin
murmushin itama, kafin kuma ta mike tsaye da kama Iffah
suka koma kan dardumar da aka shirya abinci acan gefe na
ɗakin, dan ɗakine ƙaton gaske mai dauke da komai na jin
daɗin duniya. Tare sukaci abincin, Daneen Ammarah har tana
bama Iffah wani lokacin a baki, jitake inama Iffah ɗiyartace,
dan da'ace tana gidan aurenta har yanzu ɗiyarta ta fari zata
iya kasancewa dai-dai da shekarun Iffah ne. Kulawar Daneen
Ammarah ta sake saka sassauci a zuciyar Iffah harta ɗan saki
jikinta. Bayan sun kammala ta sakata shiga bayi tai wankan
maganin da take amfani da shi, data fitoma da kanta tai mata
hayaƙin turare. Iffah ta hau gado ta zauna, Daneen Ammarah
a gefenta da littafin tarihin annabawa acewarta zata dinga
karantama Iffah har sai taga tayi barci domin ɗebe mata
kewa.
“Yauwa Ibnati kin shirya dai ko?”.
Fuskar Iffah da ɗan murmushi tace, “Eh Mamy na”
“Masha ALLAHU ashe dai Habibty na tare dani”.
Hannu Iffah tasa ta rufe fuska tana murmushi, itama dai
Daneen Ammarah murmushin take. Ta fara buɗe littafin. Iffah
dake kallonta tai dauriyar finciko ɗaya daga ɗunmbin
tabayoyin dake cin ranta ganin zata fara karatun...
“Mamy dan ALLAH na tambayeki wani abu?”.
“Oh Ibnati tambayeni mana kanki ma tsaye kuwa.”
Iffah ta jinjina kanta da sauke ajiyar zuciya..........✍️

22
.......Iffah ta jinjina kanta da sauke ajiyar zuciya, “Immm
Mamy dama...” sai kuma tai shiru dalilin gargaɗin da
zuciyarta ke mata tunda har yanzu fa Bama wai tasan
matsayin Daneen Ammarah ɗin bane a masarautar.
“Dama mi? Kinga karkiji komai kimin duk tambayar da
kike buƙata, insha ALLAH zan kasance mai baki amsa, idan
kuma bata dace ba zan baki shawara kodan nan gaba”.
Kai Iffah ta jinjina “Dama dan ALLAH zance ne yanzu
mutuwar su hadiman can shikenan ta tafi a banza baza'ai
wani bincike a gano ba?”.
Kallo na kusan sakan biyar Daneen Ammarah taima Iffah
da har tama ɗauka tai laifi, amma sai taji taja numfashi da
maida kanta kan littafin hanunta. “Mutuwarsu bazai tafi a
banza ba saboda dalili mai ƙarfi Ibnati. Dan duk wanda ya
kashesu yana gudun tonuwar asirinsa ne akan cutar da ke da
akai yunkurin yi. A yanzu haka Shahanshan ya saka kwamitin
bincike, muna fatan kuma ta wannan hanyar za'a gano koma
wanene ya saka ki a halin da kika tsinci kanki. Kuma dama
kema ana jiran ƙara samun lafiyarki ne aji ko akwai wani abu
da kika sani, ko kuma bayan su ukun can da ɗayar da aka
samu nasarar ceto ranta ko akwai wasu..”
Da sauri Iffah ta dubeta. “Mamy akwai wadda bata mutu
ba dama?”.
“Eh akwai amintacciyar hadimar Umm-Jasrah (haka take
kiran Malikat Bushirat) mai suna Diwa. Ita an kaita asibiti
kafin gubar da suka sha ta karasa katsa ƴan hanjinta.
Alhmdllh kuma an dace dan yanzu haka tana kan shan
magani, tana

14 / 34