Author : Bilyn Abdull ce Category : African Stories & Novels
musu. Sanin rayuwarsu akafi buƙata a yanzu sama da
mutuwarsu yasa hadiman kurkukun dake a cikin daular
ruman tsagaita musu. Amintaccen hadimin Malikat Bushirat
ya koma ya sanar mata halin da ake ciki. Shiru kamar
bazatace komaiba. Sai kuma ta dubi Jasrah da har yanzu ke
tare da ita ta ɗauke kanta.
Jasrah data fahimci mi ƴar uwar tata ke nufi takai dubanta
ga hadimin. “Ghazi! A cigaba da tsaurara musu tsaro har
zuwa gobe idan ALLAH ya kaimu”.
“ALLAH ya ƙara miki lafiya an gama”. Ya faɗa da tsantsar
girmamawa yana mai rissinawa da gyara takobin hanunsa ya
fice.......
*_ZAWJATA-ALMILKI_*
Tun Iffah na iya motsa jikinta da furta kalmar bakinta har
hakan ya gagara numfashinta ya fara neman barin jikinta. Ga
dai masu magani mata rufe a kanta mazan na daga waje suna
haɗo duk abinda ya dace amma babu alamar wani canji sai
ma ƙwaɓewa da komai ke nemanyi. Tun ana ƙirga awannin
iya shawo kan matsalar har komai ya fara firgita kowa. Daular
ruman tayi tsitt babu mai ƙwaƙwaran motsi a cikinta. Sautin
fitar kiran salla ma dan ya zama dolene. Koda aka idar da salla
ma sake komawa zaman jigum-jigum akayi domin kuwa
abinda bai taɓa faruwa a tarihin masarautar bane ya faru.
Tajwar Eshaan bai fito sallar zuhur ba yau. Hakama da la'asar.
Magrib ma ta shiga babu wanda yaji motsinsa. Zuwa lokacin
kuma akan Iffah an zubama sarautar ALLAH idone wadda ta
girma ta ɗaukaka.
Dan kuwa tana a shimfiɗene jiki duk ya ɗashe tamkar
wadda ta ƙone gurin yay ja kafin ya tashi. Kaɗan-kaɗan
numfashinta ke fita wanda shine kawai ya tabbatar da tana a
raye bata mutu ba. Masu magani kowa yayi iya iyawarsa sun
koma gefe ana jiran ikon ALLAH kuma. Ana idar da sallar
la'asar Malikat Bushirat ta bada izinin maida Iffah
sashenta.....
Kamar yanda Malikat Bushirat ta bada umarni an maida
Iffah sashenta, a kuma cikin ɗakin barcinta da babu wani
mahaluki daya taɓa shiga bayan Tajwar Eshaan da Jasrah.
Hakan ya bama dukkan hadiman sashen mamaki da tabbatar
da lallai wannan Zawjata-almilki ɗin tana da wata daraja ta
musamman ga Malikat. Dan kaf Zawjata-almilki da suka rasa
rayuwukansu a gidan babu wanda ya iya ganin makamancin
damuwar Malikat Bushirat irin ta yau. Ƙarin tabbaci har
hawaye sai da ta share na tsagwaron tausayin Iffah. Lallai
halin da Iffah ke ciki ta cancanci duk mai imani ya zubda mata
hawaye, dan sauran Zawjata-almilki na baya mutuwarsu
kawai akeji bayan kaisu turakarsa. Amma ita ko kaitanma
ba'ayiba, a kwana ɗaya tak da tai a gidan batare da an
kammala gagarumin taron bikin da aka shirya ba dominta
gata a halin da gara mutuwa da shi...
Bayan idar da sallar isha'i Malikat Bushirat na hakimce a
katafaren falonta na uku Malikat Ashwaq ta iso da tawagar
hadimanta duba Iffah. Malikat Ashwaq itace mace ta farko ga
marigayi Tajwar Haysam ibn Abdull-majeed. Hamshaƙiyar
mace ce data isa take kuma amsa suna Malikat. A ƙa'idar
Daular ruman matar data haifi yarima mai jiran gado a cikin
matan sarkice kawai ake kira da Malikat. Mafi yawanci kuma
ana samu ne daga matan farko. Sai dai ga Tajwar Haysam
hakan bata faru ba. Dan matarsa ta farko Ameera Ashwaq
bata taɓa haihuwa ba kamar sauran matansa, tadai taɓa
ɓarin ciki na wata huɗu daga shi kuma bata ƙara ba. A zahiri
mace ce isashiya mai baza mulkin da yafi na kowace mace a
gidan bayan malikat Bushirat, amma kuma bata da damuwa
sam. Ƙaryarka kace ga wani mugun halinta na zahiri saboda
tasan kanta. Rana ɗaya aka ɗaura aurenta dana Malikat
Bushirat matsayin Zawjata-almilki. Amma itace uwargida. Duk
da mulkinta Malikat Bushirat ta fita, ta kuma fita zafi da nuna
kishi a zahiri dan sam ita bata da haƙuri, hakan yasa ake
matuƙar jin tsoronta fiye da kowace Zawjata-almilki, dan
Malikat Bushirat ba kanwar lasa bace ƙwarai da gaske, sai dai
mace ce mai son ƙyautatama wanda yay mata da na ƙasa da
ita, hakan ya taimaka mata samun soyayyar hadiman gidan.
Haihuwar Miran (Yarima) mai jiran gado Eshaan tasa dole
sunan Malikat ya koma kan Malikat Bushirat. Wato Sarauniya
Bushirat kenan. Amma duk da haka sai Mahaifiyar Tajwar
Haysam mai suna Malikat Haseena ta bada umarnin cigaba
da kiran Ashwaq da suna Malikat Ashwaq. Hakan ya ƙona ran
Malikat Bushirat, sai dai babu yanda zatayi. Amma ta sake
tsananta kishin da takema Malikat Ashwaq ɗin fiye da da,
yayinda ita kuma Malikat Ashwaq ke nuna tamkar babu
komai a zahiri, amma a baɗini hummm....
Koda ta shigo Malikat Bushirat bata nuna tasan da
shigowar tata ba. Sai dai ta ɗagama hadimanta yatsu biyu da
ya sakasu rige-rigen fara barin falon. Zaune Malikat Ashwaq
takai bisa ɗaya daga cikin kujerun falon tanama nata hadiman
nuni dasu fita suma. Da sauri suma duk suka fice aka barsu su
biyu kawai. A hankali Malikat Ashwaq ta ɗan sakin murmushi
daya danne zafin yarfin da Malikat Bushirat ɗin tai mata, ita
ta fara gaisheta da tambayar ya mai jiki?. A daƙile Malikat
Bishirat da tai kamar zata basar ta amsa mata cike da isa.
Nanma Malikat Ashwaq dai murmushi kawai tayi da haɗiye
ɓacin ranta. Sosai ta nuna tausayi akan Iffah ta kuma mata
doguwar addu'a da bada shawarar mizai hana a kira likita ma
ya duba ta ko wani abune daban da wanda ake tunani.
Karan farko Malikat Bushirat ta ɗakko manyan idanunta
tai mata kallon tsakkiyar ido. Cikin yamutsa fuska taja
numfashi da fesarwa, “Haihuwar magajin Daular ruman daga
tsatson Malikat Bushirat rubutacciyar ƙaddara ce da duk yaƙi
da gwagwarmayar masu son daƙile hakan. A baya basuci
nasara ba, Taya suke tunanin samunta a yanzu kan
_Saifulmulk_ ɗi na?. Kamar yanda aka haifesa daga matsayin
gudan jinin Shahan-shan, Tajwar Haysam ibn Abdul-majeed.
Shima haka za'a samar da Ɗa daga gudan jininsa da izinin
UBANGIJI masu lissafi su fara...”
Muƙutt Malikat Ashwaq ta haɗiye yawun dake neman
kufce mata, a zahiri kuwa murmushi ta saki da ɗan girgiza
kanta. Batare da tace komai ba tai yunƙurin miƙewa domin
barin ɗakin tana mai ƙoƙarin danne zuciyarta dake
yunƙurowa. Har tayi taku biyu sai kuma ta tsaya, batare data
juyi ba ta saki murmushi. “Idan dai har Eshaan ya kasance
gudan jinin Shahan-shan ne babu gauraye, muma irin wannan
fatanne a bakunanmu garesa kasancewarmu uwaye a
wajensa. Fatan alkairi da samuwar lafiya ga Zawjata-
almilki.....”
Har tsakkiyar kai kalaman ƙarshe na Malikat Ashwaq suka
daki zuciyar Malikat Bushirat, sai dai kafin ta samu wani
damar fassarasu sallamar Ameera Danish-Ara da suka kusan
kiciɓus da Malikat Ashwaq ya dakatar da ita. Itace mata ta
uku ga Tajwar Haysam. itama da tata tawagar hadiman.
Kallon juna sukai da Malikat Ashwaq, Ameera Danish-Ara ta
saki wani malalacin murmushi a kaikaice. Sai kuma ta matso
cikin girmamawa ta gaishe da Malikat Ashwaq ɗin datai mata
kallo guda ta ɗauke kanta. Amsa mata tai cike da ƙasaita,
kafin ta matsa ta bata hanya ta shige, itama ta fice tawagarta
biye da ita.
Saɓanin Malikat Ashwaq ita ta samu tarba daga malikat
Bushirat. Dan duk da take mata itama ga Tajwar kuma
Malikat Bushirat kishiya a gareta hakan bai hanata risinawa ta
gaidata ba da matuƙar girmamawa tana mai tambayar jikin
Iffah. Malikat Bushirat dake kishingiɗe har yanzu a yanda
Malikat Ashwaq ta barta ta amsa mata da sassauci mai haɗe
da jimami. Cike da makirci Ameera Danish-Ara ke nuna
tsantsar tausayin Iffah tana mai yin ALLAH wadai ga duk mai
hannu akan waɗan nan al'amura.
Malikat Bushirat taɗan jinjina kai irin na ƙasaitattun mata
da yamutsa fuska kaɗan, a saman lips ta furta, “Nagode”.
A kaikaice Amera Danish-Ara ta ɗan saƙi murmushi tare da
harararta ta ƙasan ido. A zahiri kuwa zamanta ta gyara tare
da risinar da kanta. “Wannan abunda ya shafemune ai gaba
ɗaya ranki ya daɗe. Domin Zaki ɗammu ne, fatammu dai
ALLAH ya warware waɗannan al'amura cikin sauƙi”.
Har cikin zuciya Malikat Bushirat taji daɗin kalaman
Amera Danish-Ara, dan haka a lips ta amsa da “amin” tana
mai sauke ajiyar zuciya, dan bata cika samun damuwa da ita a
gidanba tunma sunada ƙuruciya. Amera Danish-Ara mace ce
mai tsananin kissa da ba lallai a lokaci guda ka iya gano
wacece ita ba. Duk da kasancewar ita Zawjata-almilki ce a
daular ruman zakasha mamakin irin girman da take bama
Malikat Ashwaq da Malikat Bushirat a gidan a zahiri tunda ta
shigo. Kai hatta da Amera Haifah dake amarya kuma ƙarama
a cikinsu ita bata taɓa bari saɓani ya shiga tsakaninsu ba a
zahiri. Wannan halin nata yasa sanda surukarsu Malikat
Haseena ke da lafiyar ƙafa take sonta da janta a jiki fiye da su
Malikat Bushirat. Wani lokacin har kwatance take musu da
halin Amera Danish-Ara ɗin wai suyi koyi ta fisu dattako. A
yanzu haka da take zaune babu lafiyar ƙafa Ameera Danish-
Ara ɗin tafi kowa sintirin zuwa dubata da mata hidima a
zahirance, duk da itama Malikat Bushirat na kamantawa sai
dai babu ruwanta da sai wani ya gani yace tayi.
Shiru falon ya ɗauka na wasu mintuna, Amera Danish-
Ara na son taga Iffah babu fuska ga Malikat Bushirat, dole ta
miƙe cikin ƴan kame-kame tana tambayar ko Amera Haifah
tazo kuwa?.
Kallon ƙasan ido Malikat Bushirat tai mata tana ƙara tsuke
fuska, dan ita duk yanda take da zafi babu wanda zaice ga
ranar data zauna maganar wani a cikinsu koda da su Jasrah
ne kuwa. A ganinta idan tai hakan sunma isa kenan a
wajenta. Murmushin yaƙe Amera Danish-Ara tayi cike da
basarwa. Sai dai ƙasƙantaccen kallon da Malikat Bushirat tai
mata ya matuƙar sokar mata zuciya. Taɗan risina da faɗin,
“Na barki lafiya ranki ya daɗe”.
Kai kawai Malikat Bushirat ta jinjina mata batare data ko
ɗago ba. Amera Danish-Ara ta cije baki da ficewa hadimanta
dake jiranta daga falo na biyu suka take mata baya.
Sam Amera Danish-Ara bata gaban Malikat Bushirat,
kalaman Malikat Ashwaq ne keta faman mata kaikawo a
zuciya musamman na ƙarshe. (Fatan alkairi da samuwar lafiya
ga Zawjata-almilki) waɗan kalamai bakwai a cikin tarin
kalaman Malikat Ashwaq sunfi komi tsayawa Malikat Bushirat
a zuciya. Dan kuwa tana fassarasu ne da wani abu daban ne.
Haka manyan mutanen masarautar suka cigaba da shigowa
duba Iffah daga sassa daban-daban na gidan. wasu iyaye ne,
wasu yayu, wasu ƴaƴa harma da kakanni maza da mata duk
da basu samun damar shiga ciki iyakarsu wajen Malikat
Bushirat. Bata damu kanta ba sai da dare yaja. Koda
hadimanta suka dawo sallamarsu tai dan tafi buƙatar kaɗaici
a yanzu saboda son ƙara tunani akan kalaman Malikat
Ashwaq da suka gagara haɗiyuwa a gareta. Da kuma nazartar
kowa daya shigo sashen nata domin duba Iffah. Tun tana a
zaune har takai ta miƙe tsaye hannayenta goye da bayanta
tana faman kaikawo tamkar mai safa da marwa..........✍
17
...........Dare yayi nisa, bakajin motsin kowa a daular ruman sai
sassanyar iskar dake kaɗa bishiyoyi kaɗan-kaɗan. Sai kuma
Hadiman da ake kira Ghazi a masarautar ne kawai ke faman
kaikawo domin bada tsaro ta kowacce kusurwa ta gidan
musamman a sashen Tajwar Eshaan.
Iffah dake kwance samɓal a katafaran gadon alfarma na
Malikat Bushirat idanunta a rufe kai kace batama numfashine
ta fara zabura a hankali kamar wadda ake mintsini. Jasrah ce
kawai tare da ita a ɗakin, tana daga gefe barci ya ɗan figeta
mai cike da wani irin mummunan mafarki. Wata gigitacciyar
ƙara da Iffah ta fassa tare da girgizar data saka gadon shima
rinƙa girgizawa yasa Jasrah farkawa a kiɗime. Tsalle tai gefe
jikinta na rawa ganin yanda Iffah da gadon ke girgiza, hatta
shi kansa ɗakin ji Jasrah keyi na mata rawa shida fitulun da
suka haskesa, dan sai daukewa suke suna kawowa. Wani irin
tari Iffah ta farayi mai tahowa da aman jini ta baka ta
hancinta harda ta kunne. Jasrah ta fara ƙwala kiran sunan
Malikat Bushirat a matuƙar firgice tana sake manne jikinta da
bango hanunta na laluben ƙofa amma ta kasa buɗeta...
Malikat Bushirat da dama ba barci take ba saboda tsabar
damuwa ta buɗe idanunta a hankali jin sautin muryar Jasrah
tamkar a sararin samaniya tana yawo. Cigaba da jin sautin ya
sata miƙewa zaune ta sauka a gadon baki ɗaya. Babu wani
hadimi dake da damar shigowa sashen ɗakunan barcinta sai
masu gyarawa kawai suma da safe ne, hakan ya sata ɗora
abaya kawai a saman kayan barcinta ta fito.... Jasrah da ta
gama fita hayyacinta gaba ɗaya ta faɗa jikin Malikat Bushirat,
rungume ƴar uwar tata tayi, a hankali ta shiga hura mata iska
a kunne tana bubbuga bayanta. Jasrah da ƴar nutsuwa ta fara
zuwa mata tai lamo tana sauke numfarfashi a jajjere, sai
kuma ta ɗago a hankali hawaye wanke da fuskarta...
“Mike faruwa?”.
Malikat ta faɗa a hankali. Ɗakin Jasrah tabi da kallo, kafin ta
fara mata bayanin komai har yanzu hawayenta sun kasa
tsayawa. Sosai hankalin Malikat ya ƙara tashi, sai dai
kamewarta yasa ba lallai ka fahimta a kan fuskarta ba. Cikin
takunta na ƙasaita ta isa gaban gadon inda Iffah take. Kwance
take samɓal tamkar ba itace ta gama buge-buge ba yanzun.
Idanu ta tsura mata a karan farko, yarinya ce ƙarama sosai
kuma ƙyaƙyƙyawa matuƙa, duk da halin ciwo da take ciki da
canjawar fatar jikinta ƙyawunta da kwarjininta basu gushe ba,
tausayinta mai tsanani da ƙaunarta suka sake ratsa zuciyarta.
Zaune ta kai gefen gadon ta kai hannu ta shafa yalwataccen
gashin Iffah daya gama bajewa a kan filon.
“Ibnati kiyi haƙuri zaki samu lafiya bazasu taɓa samun
galaba ba kinji”.
Iffah da sarai take jin maganar Malikat dan ba barci take ba
azaba ce kawai ke ratsata tai murmushin ƙarfin hali a
zuciyarta, a karan farko taji ƙaunar matar a ranta da sake
ganin kima da girmanta.......
★★_______★★
“Sun jiƙa mana aiki! Sun ɓata mana shiri! Ya ƙwace mana
damarmu wadda sake samun samuwarta a garemu cikin
sauƙi haka zata iya zame mana mai wahala!!”.
Kakkausar muryar Uwa mai matuƙar rashin daɗin saurare
ta fara karaɗe ɗakin cikin amon sauti mai tashi sama. A firgice
ta miƙe a zabure tare da zube gwuyawunta ƙasa jikinta na
tsuma dan dama zaune take ido biyu tana jiran tsammani. “A
gafarce ni uwa ba laifina bane, ni kaina ina cikin damuwar
tangarɗar da aka samu”.
“Bana buƙatar jin komai daga gareki Taƙurya. Domin
sakacinki ne ya jawo hakan. Nasha faɗa miki ki san suwa zaki
bama aikin da ke bazaki iya yinsa kai tsaye ba. Su kuma
waɗan can sakarkarun barinsu sukai wayewar gari tamkar
rasa sauran damar data rage miki ne....”
Ɗan zabura tayi da nufin cewa wani abu, sai dai tamkar
walƙiya Uwa ta ɓace a ɗakin. Hakan na nufin ranta a ɓace
yake. Itama kanta ta dafe nata ran na suya da ƙara girmamar
baƙin cikinta. Miyasa kowa bai bata matsala ba sai wannan
ƴar shilar yarinyar da bata wuce sauron gidanta ba da feshi
ɗaya take kawar da shi. Zuciyarta ta fara raya mata Uwa
kodai tsoron yarinyar nan takeyi, yo inba tsoro ba taya zata
dinga wani gewaye-gewaye bayan bai wuce da ƙyaftawar ido
kawai ta shafe babin rayuwarta ba. Dama mutum na gagarar
aljani ne banda ta fara maidata susu......
WASHE GARI..
Duk wanda ya kwana ya tashi a masarauta a yau ya tashi ne
da tashin hankalin da yafi na jiya sakamakon mawuyacin
yanayin da Iffah ta wayi gari. Dole tun gabatowar sallar asuba
aka maidata cikin clinic ɗin dake a masarautar saboda
ɓallewar jini ta kowane sashe na jikinta. Da farko aman jini ta
fara, sai kuma ta hancinta, sai gashi ta ido da kunne harda ma
ramin cibiyarta. Hankalin Jasrah da Malikat dake tare da ita
ya kai matuƙar ƙololuwar tashi. Duk da kowa yasan ciwo ne
bana asibiti ba haka likitoci suka rufu a kanta domin ƙoƙarin
ganin sun tsaida jinin amma abu na neman gagara. Har kusan
goma na safe a gogon ƙasar babu wani cigaba, jikin Iffah ma
ya fara saki alamar jininta yayi ƙasa matuƙa....
★★...
“Bari-Hamshira! Inaga ya kamata a bama masu maganin
dake waje dama suma suzo su gwada sa'arsu tunda ba'a dace
dana cikin masarauta ba.”
Malikat da damuwar duniya ta tattaro a kanta yau ko
fadarta bata iya fitaba tana cikin ɗakin barcinta har zuwa
yanzu ta ɗago idanunta dake jajur ta sauke akan ƙanwarta ta
uku mai suna Zaimah, cikin nuna sallamawa ta jinjina kanta.
“Wannan ma shawara ce mai ƙyau Akia, ruɗewa tasa sam
wannan tunanin bai zomin ba. A sanar da Ghazi su faɗama
Baba Yaro. Sai dai komai ya kasance cikin sirri da amana dan
kar maƙiyanmu suyi amfani da wannan damar wajen ruguza
ɗan sauran ƙwarin gwiwar mu akan wannan yarinya”.
Kai Zaimah ta jinjina mata, sai kuma ta miƙe da hanzari
domin isar da umarnin.....
*_ƘAUYEN JUMNA_*
Tafiya saurayin yake tamkar zai tashi sama dan gaggawa,
wani lokacin har tuntuɓe yakanci sai dai kafin ya kai ƙasa yay
azamar taro kansa ta hanyar dafe duk abinda ke kusa da shi.
Wurjanjan ya isa ƙofar gidan Dattijon da kowa yafi sani da
suna Abu Huzaifah ya kwaɗa sallama da iya ƙarfin muryarsa
har sau huɗu babu ko jiran a amsa masa.
Dattijo Abu Huzaifah Da mukafi sani da Kaka ya dakata
da ga ɗinkin kwalliyar doki daya duƙufa yi ya dago suka kalla
juna da Iyyani dake shara a tsakar gidan. “Kamarfa sallama
naji Abu Jamaima a ƙofar gidan nan”
Kafaɗa yaɗan rausayar gefe da ajiye zungureriyar allurar
da yake ɗinkin da ita. Kafin ya ce wani abu aka ƙara zungura
sallamar a jajjere tamkar yaƙi. Kansa ya ƙara jijjigawa ya miƙe
dajan tsaki. “Kai wasu dai mutanen sam basu da lissafi, irin
wannan ai saka ɗauka tashin hankali ne”. Kaka ya faɗa cikin
mita yana gyara takalmansa. Iyyani da takaici ya ƙulle itama
ta bisa da kallo harya fice a soron gidan...
“Ayyub! dama kai ne kake ƙwaɗa irin wannan sallama
haka? Lafiya dai ko?”.
“Da sauƙi dai Baba, amma amin afuwa bani da wani zaɓi
bayan hakan. Saƙone daga Baba yaro”. Ya ƙare maganar da
miƙama Kaka takardar hanunsa. Kaka ya amsa takardar yana
ɗan juyata, sai kuma ya nuna hanyar shiga da faɗin, “Kaga
shigo daga ciki”.
A tare suka shiga cikin gidan, Kaka ya buɗe takarda yana
dubawa, yayinda Iyyani ta kawoma baƙo dake gaisheta ruwa.
Kaka ya ɗan murmusa bayan gama karanta takarda tare da
girgiza kansa. “Ayyub naga saƙo, sai dai kuma inaga basai
naje da kaina ba. Zan baka saƙo ka kai masa nima. Ita kuma
ALLAH ya bata lafiya yasa ya zama kaffara a gareta”.
Ɗan jimm Ayyub yayi, sai dai kafin yace wani abu Kaka ya
miƙe. Ɗakinsa ya shiga, kusan mintuna ashirin sai gashi ya fito
da wata jakkar fata. “Kayi maza ka kai masa wannan. Kace
kuma ina gaishesa”.
Cike da girmamawa Ayyub ya amsa da faɗin “Angama
Baba. A huta lafiya”. Kai kawai Kaka ya jinjina masa yana
murmushi. Sai da ya rakasa har ƙofar gida sannan ya dawo.
Iyyani da duk ta shiga damuwa ko zama baiyiba ta jeho masa
tambaya, dan