Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dauɗar Gora Complete Hausa Novel by Bilyn Abdull Ce

Author :  Bilyn Abdull ce Category :  African Stories & Novels

Chapter   13 / 34

36K to 39K   out of 100K words

Mikewa tai itama ta
hau shirin fita fadarta. Sai dai komai tana yinsa ne a tsanake
amma yanayinta tattare da matsananciyar damuwa.
Fitowarta dai-dai da shigowar Ghazi, ya zube ƙasa yana mai
miƙa gaisuwa a gareta. Hannu kawai ta daga masa bayan ta
kai zaune. Jasrah ma dake zaman jiran fitowar tata tai mata
sannu da fitowa. Kai ta jinjina mata da maida hankalinta ga
Ghazi dake gurfane kansa a risine. Itama Jasrah hankalinta ta
maida kansa.
“Ghazi ya naganka kai ɗaya?”.
“Ranki ya daɗe an samu matsala ne”.
“Matsala kuma? Kamar ya kenan?”.
Ɗan jimm yay na jimamin faɗar abinda ke bakinsa. Sanin
Malikat Bushirat bata buƙatar kawane-kwane a magana ya
sashi girgiza kansa idanunsa na canja kala zuwa ja sosai.
“Ranki ya daɗe gawar uku daga cikinsu kawai muka samu,
tare da hadiman dake tsaron inda aka killace sun su duka
biyun. Diwa da ta rage ma bana zaton zata kai labari, kuma
da alama yanzu-yanzu aka aikata ta hanyar madarar da aka
basu matsayin abincin rana.
Ba ƙaramar zabura Jasrah tai ba, yayinda Malikat ta
rumtse idanu da sauri ƙirjinta yay wata irin harbawa da ƙarfi
tamkar zai buɗe dan firgici. Amma a zahiri miskilancinta da
ƙasaitar mulki bazai taɓa haska maka komai ba daga yanayin
nata.....

★Kamar yanda labarin mutuwar hadiman nan ya isa
kunnen Malikat Bushirat haka ya karaɗe kunen kowa a
masarautar. Yayinda likitoci suka rufu akan Diwa da itama
gab take da rasa tata rayuwar. Wasu kuma sun duƙufa ne
akan binciken madarar da suka sha ta ƙarshe duk da kowa ya
san daga cikinta ne akama zuba musu ko minene.......


*_ZAWJATA-ALMILKI_*
Yayinda ake tsaka da jimamin rasa hadiman da sukai
sanadin shigar Iffah a mawuyacin halin da take ciki, ita kuma
waraka ALLAH ya saukar a gareta bayan duƙufar Baba yaro
akanta da maganin da aka amso a wajen Kaka. Tun a mata
hayaƙin farko jinin dake fita a jikinta ya tsaya. Hakan ya basu
hope ɗin cigaba da bin dokokin da kaka ya kafa na maganin
daki-daki har ALLAH yasa aka dace ta kawo wani nannauyan
numfashi da ambaton sunan ALLAH.
“Ruwa!”.
Shine abinda ta ambata na biyu. Cikin sauri Daneen Ammarah
ƙanwa ta biyu ga marigayi Tajwar Haysam da ayanzu ke tare
da ita ta zabura da kanta ta ɗauka ɗaya daga cikin bottle
water dake a ɗakin ta ɓalle murfin ta kafa mata a baki. Cikin
mawuyacin hali Iffah take zuƙar ruwar, sai dai kasancewar
shine abinda tafi buƙata a ƙanƙanin lokaci ta shanye sa tas.
Yumma da itama dai uwa ce gasu Daneen Ammarah ɗin,
sannan matsayin Kaka ga Tajwar Eshaan dan ƙanwace ga
Malikat Haseena ta sake ɓalle wani ta zuba a hanunta ta
shafa a goshin Iffah dake jiƙe sharkaf da gumi. Ajiyar zuciya ta
sake ja a hankali tare da buɗe idanunta da sukai mata
matuƙar nauyi. Kaɗan ta buɗe ta maida ta rufe. Alhmdllh
suka shiga ambata da mata sannu, yayinda Daneen Ammarah
cike da zumuɗi tai kiran Malikat Bushirat. Ita ta fara sanar
mawa kafin mahaifiyarsu Malikat Haseena duk da tana cikin
halin ciwon ƙafa da bata iya ko miƙewa sai da taimakon
wheelchair dama ga tsufa.....
Cikin abinda baifi mintuna goma ba ɗakin da Iffah ke
kwance ya cika da wasu a manyan masarauta. A fuska dai
suna nuna farin cikin farkawar tata ne, amma a ƙasan zuciya
mafi yawansu kowa da irin tasa manufar. Malikat Bushirat
kuwa harda hawayen farin cikinta, farkawar yarinyar da a
kallon farko ta gama shiga ranta ya goge mata sauran
damuwar abinda ya faru game da kashe Hadiman da aka aika
suka aikata sherin daya jawo komai. A take Malikat Bushirat
ta bada ƙyauta mai tsoka ga Baba yaro. Hakama wasu a cikin
manyan sun masa ƙyautar. Daneen Ammara ce ta biyu, itama
kuma ta bada mai tsoka daya bama kowa mamaki.
Ana ƙoƙari daukar Iffah zuwa sashen Malikat Bushirat
kamar yanda ta buƙata sai ga saƙo da ga Malikat Haseena
cewar akai Zawjata-almilki sashenta. Take fuskokin mutane
da yawa ya canja a wajen, saɓanin ta Malikat Bushirat data
nuna tsantsar farin ciki da jin ƙaunar surukar tata. Dan dama
zuciyarta cike take da fargabar sake kasancewar Iffah babu
tsaro. Duk da sashenta ma bazai iya zama kanwar lasa ba ga
wani mahaluki a zahiri, sai dai yaƙin sunƙuru. To amma idan
ta danganta da abinda zuciyarta ke rawa a kai komawar Iffah
sashenta kamar an gudu ba'a tsira bane. Sashen Malikat
Haseena kuwa sunyi imanin ko ifiritu da kansa zaiji tsoron
gittawa kai tsaye balle wani shiryayye dake a masarautar....
Rashin ƙarfin jiki da rashin dai-daiton tunani yasa Iffah
ba fahimtar komai take ba, hasalima tun yunƙurin farko bata
sake gwada buɗe idanunta ba suna a lumshe. Sai dai tana jin
komai dake gudana har ɗaukarta da akai akan keken asibitin
zuwa waje. A mota a ka sakata Daneen Ammarah tare da ita.
Sai Malikat Bushirat da tabi bayansu a tata motar da ake
tuƙata. Ganin haka sauran ƴan son ganin ƙwaf suma duk suka
bisu can dan babu mai fatar yin laifi ga Malikat Haseena.......

*_GIDAN BABIY_*
Tun bayan barin Iffah gidan ɗan sauran kakkaɓin farin ciki
da ƙwarin gwiwar da su Fareeha suka barsu da shi ya ida
kakkaɓewa. Ummu bata da aiki sai kuka. A kwana uku kawai
duk ta rame saboda ko abinci bata ci yanda ya kamata.
Hanash kam ba'a magana dan makamancin irin ciwon Iffah na
damuwa ne ke neman bugarsa (Depression). Shi kansa Babiy
dake dauriya duk ya zuƙe a tsaye wani lokaci har yi yake
kamar zai faɗi. Komai ya tsaya musu cak, kunnuwansu ne
kawai a buɗe na jiran kiran jana'izar tilon ƴarsu mace data
rage. Dan gushewar kwana uku bai sa sun saka ran ta tsallake
ba. Suna tsaka da wannan zaman jigum-jigum akai sallama da
Babiy ƙofar gida. Kamar bazai fita ba sai kuma ya miƙe cikin
ƙarfin hali ya zura takalma ya fita. Ɗan turus yayi idanunsa
kafe akan wanda yay sallamar da shi... Abu Moosa da shima
ke kallonsa ya iso gabansa da ƙyar yana tangaɗi. Riƙesa Babiy
yay da sauri da faɗin, “Subahanallahi Abu Moosa!”.
Bai iya ya amsa masa ba saboda halin da yake ciki. Riƙesa da
ƙyau Babiy yay suka shiga ciki yana jera masa sannu. Zai
zaunar da shi a soro ya girgiza masa kai cike da ƙarfin hali.
“Kamin alfarma mu shiga ciki”. Ya faɗa da ƙyar tamkar
numfashinsa zai rabu da gangar jikinsa. Cikin sauri Babiy ya
cigaba da riƙesa suka shiga cikin gidan, shigowarsu yasa
Ummu miƙewa da sauri ta ɗakko tabarma ta shimfiɗa a ƙasan
bishiyar dake tsakar gidan...
“Ku bani ruwa dan ALLAH”.
Abu Moosa Ya sake faɗa da ƙyar yana fisgar numfashi. Ruwan
Ummu ta kawo masa, dai-dai da fitowar Hanash daga ɗaki
saboda jin maganganu na tashi a gidan nasu. Da ƙyar ya iya
maƙwarwa uku saboda numfashinsa fisga yake. Babiy ya ajiye
ruwan da sake tallafosa jikinsa. “Abu Moosa mike faruwa ne
haka? Daga ina kake?”.
Da ƙyar ya iya ɗaga idanunsa dake zubar da hawaye ya
kalla Babiy. Sai kuma ya girgiza kan yana jan numfashi da
shashsheka. “Abu Hanash ka gafarceni dan ALLAH, nasan
wannan yana cikin numfashin bankwana da nakeyi”.
“Babu abinda kamun nikam, dan ALLAH kuma ka daina
faɗar wannan magana bara mu kaika asibiti”. Riƙo hanun
Babiy dake yunƙurin tashi yay yana girgiza masa kai da ƙyar.
“Babu buƙatar hakan, domin ban cancanci kwatankwacin
wannan adalcin daga gareka ba, kayi haƙuri ka zauna ka
saurari abinda zan faɗa maka da yafi kaini asibiti
muhimmanci, nasan kuma insha ALLAHU zai maka amfani da
kuɓutar da yarinyarka dama sauran yaran da zasu iya biyo
baya a makamancin halin data tsinci kanta”. Numfashin dake
neman kufce masa yaja da ƙyar kafin ya cigaba da faɗin, “Abu
Hanash ka gafarce ni nine nai sanadin shigar ƴaƴanka wannan
halin, dan nine nai shunensu ga masarauta”. Da ga Babiy har
Ummu da Hanash wani irin zabura sukai mai bugawa da
bugun ƙirji. Ya cigaba da faɗin, “Nayi hakane dan son zuciya
da shegen son abin duniya. Sai hassadarka data daɗe a
zuciyata saboda sana'armu ta kasance iri ɗaya, ada tare ake
amsar zumar mu a masarauta amma daga baya aka koma
amsar taka kawai saboda gaskiyarka da rashin algus.
Maimakon na gyara nima na zama mutumin kirki kamarka sai
na kasa hakan, shaiɗan ya dinga tunzurani akan kayi sammu
ne shiyyasa. Tun daga wancan lokaci naketa ƙulla hanyoyin
ganin bayanka a matsayin ɗaukar fansa, sai dai duk wadda na
ƙulla sai ALLAH ya kuɓutar da kai, hakan ya cigaba da ƙaramin
tsanarka, dan haka na cigaba da kutsa kaina cikin masarauta
dan kawai naga na ɓataka an wulaƙantaka, nan ma banci
nasara ba dai. Kwatsam sai aka samu canji gwamnati, ni kuma
nai amfani da wannan dama wajen sake cusa kaina cikin
tsakkiyar masarauta harna samu nasarar amsuwa, nasan
komai game da mutuwar Zawjata-almilki, dan ina gaba-gaba
a hadiman da ke aiki ga masu aikatawar”. Yaja numfashinsa
da ke fisga da ƙyar. “Lokacin da aka sakamu aikin binciken
yara mata guda biyu masu hankali dan a aurama Tajwar naji a
raina lokacin nasarata a kanka ya yi, dan haka na bada
sunanka da adireshin gidanka. An ɗauka tsahon kwanaki ana
bibiyar yaranka da kai kanka kafin azo gareka. Ko bayan
mutuwar ta farko ni na ƙara ƙulla aka sake dawowa ta biyu
dan burina kawai naga na durƙusar da kai ƙasa. Ka gafarceni
Abu Hanash dan nayi nasara, sai dai ramin muguntar dana
gina daga ƙarshe ni na afka ciki......”
Babiy da hawaye suka gama wanke masa fuska ya share
yana duban Abu Moosa “Kenan kai ne ka ƙulla na uku ma?”.
“Wlhy a'a bani da alaƙa da wannan, hasalima ban san
ƴar wajenka bace sai ranar da aka kawo kuɗin aure”.
“Waye ya kashe min ƴaƴa? Kai kuma miya faru da kai?”.......



🤔Ikon ALLAH, wannan duniya ina zaki kaimu, baka damu
da kowa ba amma kana barcine da rashin barcin wasu, kana
ci ne da rashin cin abincin wasu. Kana numfashi ne da burin
ƙaruwar na wasu. Kana farin ciki da gushewar farin cikin
wasu. Kana shiga tarkon wahala da dariyar bakunan wasu. Ya
ALLAHU ka ɗoramu akan maƙiyammu, ka hanemu yin
hassada da zaluntar wani koda ace shi ɗin ya zaluncemu.
ALLAH sarki Babiy namu

20
........Abu Moosa dake sonyin magana ya dafe ƙirjinsa da
numfashi ke kokawar kufcewa, tari ne ya suɓuce masa sai ga
jini. Hankalin Babiy da Ummu ya tashi, amma Hanash ko'a
jikinsa. Da ƙyar tarin ya lafa, Babiy dake riƙe da shi yace, “Kayi
haƙuri muje asibiti, aman jini fa kake yi”. Murmushi yay mai
ciwo da kaɗa ma Babiy kansa da ƙyar. “Abu Hanash zuwa
asibiti bazai canja komai ba, dan gubar da aka shayar da ni
bata da makari a ko'ina sai a wajensu.”
“Ya ALLAH! Guba kuma?” “Wannan shine hukuncin daya
dace da masu irin halina ai karka damu, kai dai kawai ka
saurareni zan gaya maka ta hanyar da zaka kuɓutar da
yarinyarka, ina fatan hakan ya zamar min aikin alkairin dazan
samu sassauci a kabarina”. Babiy zai yi magana ya dakatar da
shi. “Ka saurareni kawa Ab.....” ya kasa ƙarasawa saboda
sabon tarin daya sake sarƙesa. Sosai Babiy ya rikice ya shiga
ƙwala kiran Hanash duk da yana a kusa da shi. Hanash dake
jin tamkar yasa wuƙa ya ƙarasa numfashin wanan shegen
tsoho ya amsa da ƙyar.
“Kaga kamashi maza muje asibiti”. “K...k...karku wahal da
kan.. Ku. ka saurareni kawai”.
Abu Moosa ya tari numfashinsu da ƙyar yana dafe ƙircinsa
da tari ke yunƙurowa. Babiy ya buɗe baki zai yi magana cikin
taresa shima sai kawai sukaga yarab alamar rai yayi halinsa.
Salati suka ɗauka a tare, wanda yay dai-dai da shigowar
jami'an tsaro dake na ƴan sanda a ƙasar, bayansu wata mata
ce ke rusar kuka... “Ranka ya daɗe dama na faɗa muku, na
faɗa muku mutumin nan baya ƙaunar mijina, yanzu kun gani
da idonku gashi nan ya kashe mini shi, dama kullum yana
faɗa min neman rayuwarsa yake yi, ashe dai shine ɗin zai
zama ajalinsa.....” ta zube ƙasa tana cigaba da kuka harda
kururuwa.......

Hankali tashe su Babiy ke kallon wannan mata da jami'an
tsaron, ba shigowarce ta tada hankalinsu ba da farko, dan
tunaninsu ya basu duk wanda ya bama Abu Moosa guba
shine yasa suka biyo sa. Furicin wannan mata da kai tsaye
Babiy ya gane matar Abu Moosa ce ya firgitar dasu. Cikin
ƙarfin hali Babiy yace, “Yallaɓai taya daga taimako kuma zan
zama mai kisa? Abu Moosa abokina ne tun ƙuruciya kowa ya
sani, ban kashesa a da da muke tare ba sai yanzu da a ƙalla
nama kai shekara biyar kenan ban sakashi a idona ba sai
yanzu dana gansa ayam cikin gidana babu zato.....”
“......Shiyyasa akaga gawarsa a cikin gidanka yanzu daka
samu damar ganin nasa ko?”. Jami'in ya tari numfashin Babiy
da sauri yana wani makirin murmushin ƙeta...
“Allahumma ajirni fi musibati wa'akhlifni khairin minha”
Babiy ya faɗa a zahiri gumi na karyo masa. Duban jami'in yay
zaiyi magana matar ta taresa tana cigaba da kukanta mai cike
da bori.... “Ƙarya yake wlhy yallaɓai, shekaran jiya jiyan nan
sai da yaje har gidanmu ya faffaɗa masa magana mara daɗi
da tabbatar masa shine ajalinsa, idan ya ƙaryata ai munada
shaidar hakan”.
Hanash da zuciyarsa tazo ta tokare maƙoshi a hasale
yayo kan matar, wata shegiyar shaƙa yakai mata saiga
idanunta tamkar zasu fito waje. “K! baƙar matsiyaciya, dan
kawai anga gawar mutum a waje sai ya tabbatar masu wajen
suka kashe shi!!”. Idanuta ta rumtse da ƙarfi jikinta na ɓari, ta
fara kakarin azaba dan da gaske ta shaƙu. Tuni jami'an tsaron
duk sukai kansu da ƙoƙarin ɓanɓare hanun Hanash a wuyanta
amma sun kasa. Ummu kuka ta sanya, yayinda Babiy keta
kiran sunan Hanash da faɗin ya saketa amma sam babu
alamar yana ma jinsa. Da ƙyar aka iya ɓanɓare Hanash, ta
zube gefe tana sauke nunfashi da ƙyar hanunta riƙe da
wuyanta. Sai da suka bata ruwan da suka fita suka ɗakko a
mota da sauri tasha ta samu dai-daiton numfashi.
Cike da gadara ogan tawagar ya bama yaransa umarnin
kama Babiy da Hanash. Sosai Ummu ke kuka da roƙonsu
amma babu wanda ya saurareta, har ƙofar gidansu daya cika
da mutane tun isowar jami'an tsaron ta biyosu amma
kamarma basu san tanayi ba. Haka aka saka Babiy da Hanash
a mota, sai gawar Abu Moosa a Ambulance da sukazo da ita
(Alamar akwai dai lauje cikin naɗi kenan. Inba hakaba miye
na zuwa da Ambulance ɗin?🤔).
Matan anguwar ne suka rufu kan Ummu data yanke jiki ta
faɗi bayan wucewar motocin. Amma koda suka zuba mata
ruwa bata farfaɗo ba. Hankalinsu ne ya sake tashi,
makwafcinsu ya bada umarnin a sakata a motarsa a kaita
asibiti. Da taimakon matan aka sakata a mota, matarsa da
wata mata dake anguwar itama mijinta ya rasu suka shiga. Sai
lokacinne mutane suka samu bakin magana. Wasu na nuna
tausayawa ga wannan ahali, wasu na jin farin ciki badan sun
taɓa musu komaiba, sai dan kawai dalilin hassada na rashin
dalili.
A asibiti kam har an amshesu za'a fara dubata sai sukaga
Doctor ɗin ya dakata sakamakon kiran wayarsa da akayi.
Kansa ya girgiza musu ya nufi barin ɗakin yana sanar musu
yanada uziri. Hankali tashe makwafcin nan nasu da ake kira
Abu Zainab ya shiga roƙonsa amma bai sauraresu ba. Sun fara
neman taikon Nurses suma sai zuƙewa suke saboda gargaɗin
da Doctor yay musu. Al'amarin kamar wasa anƙi taɓa Ummu,
dole suka ɗauketa suka bar asibitin zuwa wani, sai dai acan
ɗin ma har an amshesu aka koresu. Basu gajiyaba suna kuka
suka nufi privet ko acan za'a dace tunda aikin kuɗine. Anan
sun amsheta, amma sun sara musu maƙudan kuɗaɗe kafin su
taɓata, acewarsu dokarsu kenan. Matar nan da mijinta ya
rasu ta fashe da kuka tana girgiza kai. “Suma basa son su
amshemu ne kawai, shiyyasa suke mana kora da hali. Inba
kora da hali ba ai banajin Abu Hanash ya mallaki koda kwatar
waɗan nan kuɗaɗen da suka ambata inba dai kaddararsa zai
saida ba”.
“Hakane Umm Yazeed maganarki nakan gaskiya, kuma
tabbas na fara ji a jikina akwai lauje cikin naɗi a wannan
lamarin, da alama hanasu amsarmu akeyi”. Abu Zainab ya
faɗa ransa a ɓace.
Matar Abu Zainab dake share hawayen itama ta ce,
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'un. Wannan wace irin masiface
haka? Mi bayin ALLAH nan suka tarema wani da zafi haka?”.
“Sanin gaibu sai ALLAH, inaga inada mafita ɗaya, mu
ɗauketa mu maidata gida sai a sanar da ƴan uwansu ko?
Tunda mudai munyi iya ƙoƙarin mu...”
“Da hakan kukai tun farko da baku wahal da kanku ba”.
Wata murya ta faɗa a bayansu. Da sauri suka juya su duka,
sai dai bayan mutumin kawai suka iya gani. Da gudu Abu
Zainab ya bisa, amma kafin yaƙarasa garesan harya shige
mota sai ƙura ya bulesa da shi.......

(🤔????)

*_MASARAUTA_*

Babban ɗaki na musamman aka warema Iffah a sashen
Malikat Haseena. Tare da amintattun hadimai biyar da zasu
dinga mata hidima. Sai Ghazi biyar suma da zasu dinga bata
tsaro duk da dama sashen zagaye yake da masu tsaron,
amma an ware biyar ɗinne na musamman domin kula da duk
wani motsin shiga da fitar mutane da zai shafi Iffah. Hakan ya
sake saka Malikat Bushirat a farin ciki matuƙa. Yayinda
sabanin haka ya bayyana a fuskokin munafukai, sai dai wasu
sunyi jarumtar dannewa baƙin cikin nacin zukatansu tamkar
wutar daji. Malikat Haseena data zartar da hukuncin batama
nuna tasan sunai ba. Ita kuwa Daneen Ammarah damar
nutsuwar nazartarsu ta samu ɗaya bayan ɗaya dalilin wani
ɓoyayyen al'amari dake ajiye a zuciyarta tsahon shekaru.

Daneen Ammarah ta kasance ɗaya daga cikin ƴaƴan
Malikat Haseena da Tajwar Abdul-majeed Ibn Aliy. Su huɗu
suka haifa. Tajwar Haysam shine babba, (sarkin daya shuɗe
kuma mahaifin sarkin yanzun). Sai Daneen Waheeda tana
auren wani babban sarki a yankin larabawa. Sai Daneen
Ammarah, itama tayi aure sai dai auren bai jimaba
sakamakon wani ɓoyayyen al'amari dake tattare da ita,
wannan ne sanadin dawowarta gida take zaune kusan
shekara goma sha tara kenan bata kuma sake wani auren ba.
Ƴar uwarta da mahaifiyarsu Malikat Haseena da marigayi
Tajwar Haysam da mahaifinsu daya bar duniya da tabon
damuwar ƙaddarar ɗiyar tasa ne kawai sukasan wannan
sirrin, al'amarin ya sameta tun tana ƙarama dan bata wuce
shekara 14 ba, shiyyasa ta jima batayi aure ba, bayan ta samu
tai auren kuma bata jimaba suka rabu da mijin dan auren
baifi wata takwas ba ma. Manyan masarauta sunta ƙananan
magana akan hakan da fassara al'amarin na Daneen
Ammarah ta siga daban-daban amma su Malikat Haseena
sukai biris dasu. Sai auta Miran Nayyar nada shekara bakwai
ALLAH yay masa rasuwa.

Bazamuce Iffah tayi garau ba kam a wannan yini. Dan har
yanzu ko idanunta bata iya ɗagawa ta kalla kowa. Sai dai
daidaituwar fitar numfashinta ya saka nutsuwa a zuciyar
kowa. Koba komai dai an samu sassauci ai. Daneen Ammarah
itace da kanta ta gogema Iffah jiki ta canja mata kaya, itace
kuma da kanta tai zaman bata abinci daya kasance mai ruwa-
ruwa.

13 / 34