Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dauɗar Gora Complete Hausa Novel by Bilyn Abdull Ce

Author :  Bilyn Abdull ce Category :  African Stories & Novels

Chapter   34 / 34

99K to 100K   out of 100K words

yanzu
na sashe na ka kwashe sa, amana ko kai na haramta maka
ganinsa ka ajiyesa gareni, idan kuma na rasa raina ka
damƙashi ga Zawja Fareedah....”
Bai bada damar cewa komai ba ya yanke kiran, da ƙyar
ya maida akalar wani zuwa Malikat Bushirat....

*_MALIKAT BUSHIRAT_*

Yanayin tashin hankalin da masarautar ke ciki koma a ace
ƙasar baki ɗaya dan yau mutanen da suka fito zanga-zanga
akan murabus ɗin Tajwar Eshaan sunfi na kullum yasa ko fita
batayi. A kallo ɗaya zaka iya ƙirga damuwarta saman
ƙyakykywar fuskarta data koɗe matuƙa a cikin kwanaki ukun
nan. Tayi duk wani ƙoƙarin ta iya iyawa domin ganin gudan
jininta amma al'amarin ya gagara. Kuka bata san iya adadin
da tayi ba ba kuma ta san wanda zatayi a gaba ba, dan anzo
gaɓar da ko'a mafarki bata taɓa sakata a lissafin ƙaddararta
ba.....
Shigowar kira a landline ɗin ɗakin barcin nata ya sata
zabura dan yazo mata ne a bazata, dole ta ambaceshi da
bazata dan Tajwar Eshaan ne kawai ke da wannan hurumin.
Har tuntuɓe taci amma bata damuba ta caɓi kan wayar
tunkan ta karasa gareta da ƙyau. Rawar jikinta dana harshe
na faruwa ne a lokaci guda, sai dai muryar data doki tsakkiyar
dodon kunnenta ta saka numfashinta tsaiwar wucin gadi....
“Ammie!...”
Aka faɗa da ƙyar cikin kuma rawar harshe mai fidda sautin
nakasashshiyar murya mai tabbatar da amon razani ga mai
saurare.
“Saiful-malik!!...”
Ta ambata itama tare da fisgar numfashinta dake kaikawo
a iya maƙoshinta zuwa cikin baki kawai. Shi bai sauka a huhu
ba, bai kuma fita ta hanci ba. Bata ma san ta saki wayar ba ta
fice...
“Ya ALLAH Akia!...”
Jasrah dake shigowa ta faɗa da sauri tana riƙo Malikat
Bushirat da gaba ɗaya idonta ya rufe da ruɗani. Son ƙwacewa
take tana ambaton “Eshaan.. Jasrah Eshaan.. Eshaan zasu
kashe min shi”.
Sam Jasrah bata fahimci inda ƴar uwar tata ta dosa ba,
dan haka tai saurin katseta da faɗin, “Na shiga uku Akia dan
ALLAH nutsu kimin bayani, mi ya dakesa?”.
Ina Malikat Bushirat ta kasa amsata, dan numfashinta ma
har ya fara fisga. Bata haɗa soyayyar Tajwar Eshaan da komai
ba a duniya. Tana masa wani irin makahon so mai wahalar
fahimta. Duk yanda Jasrah taso tanƙwarata ta kasa, sunan
Eshaan kawai take ambata da son fisgewa ta fita. Bazai yiwu
ta barta ta fita a haka ba, dan haka tai saurin danna ƙofar
bedroom ɗin da ƙafa. Hankaɗata Malikat Bushirat tayi, duk
da taji zafi dama gata ba wani ƙwarin jikin take ji ba amma
haka ta daure ta murza key. Da ƙyar ta iya zarewa ta sake riƙo
Malikat Bushirat tana mai fashewa da kuka. “Akia dan ALLAH
ki sanar min, fitarki a haka ba itace mafita ba, idan ma akan
masu zanga-zanga ɗin nan ne ki kwantar da hankalinki
jami'an tsaro bazasu barsu su ɓalla koda gate na farko
ba........”
“Jasrah ki fahimceni.....!!!”
Malikat Bushirat ta katseta cikin ƙaraji sai kuma ta fashe da
kuka. Tabbas babu lafiya, ƴar uwarta a haka lallai akwai
matsala. Har taune harshe take wajen ambaton, “Zan
fahimceki faɗamin ko a taƙaice ne Akia dan ALLAH”.
Da ƙyar Malikat Bushirat ta sanar mata a dunƙule, nan fa
hankalin Jasrah ya tashi itama babu shiri ta zabura ta buɗe
ƙofar......

★★....

Suɓucewar kan wayar a hannun Tajwar Eshaan dai-dai da
sake faɗowar Iffah ɗakin a birkice. Gaba ɗaya ma ta mance
matsayinsa da nata, tai kansa babu alamar hankalinta na tare
da gangar jikinta. Tana zubewa gabansa yana faɗowa jikinta
hannunsa dafe da kansa yana ambaton “Ammie...” a hankali,
ga wata irin zufar da tai masa sharkaf kai kace wanka yay a
lokacin.
“Na shiga uku ni Fhareedah!”. Da Iffah ta faɗa cikin kuka
ya saka shi ɗago idanunsa dake matukar jazur zattashin
hankali. Akanta ya tsaidasu a wani irin bahagon yanayi, ya
lumshesu da ƙyar ya sake buɗewa a kanta. Lips ɗinsa da suka
koma jajur saɓanin pink a da suna motsa a hankali ya saki
wani wahalallen murmushi da har Iffah ta koma ga ALLAH
bazata taɓa mantawa ba, dan ya zauna a allon zuciyarta
tamkar rubutu akan dutse. kafin idon nasa ya koma ya
lumshe gaba ɗaya tattausan hanunsa na dama saƙale cikin
nata da bata san sanda ya riƙo ba...........✍️

*_ALHAMDULLAHI!!🙏_*

Ina godiga ga ALLAH daya bani ikon kawo ƙarshen littafin
DAUƊAR GORA CIKI KA SHATA kashi na farƙo. Ina roƙon
UBANGIJI ya bani tsahon rai da lafiya ni da ku har zuwa bayan
salla da zan ɗora kashi na biyu insha ALLAHU. Ina mai baku
haƙuri da ƙari saman haƙuri da tangarɗa da jinkiri da aka
samu duk da Alhamdullah ban taɓa fashin posting ba, sai dai
labarin yayi tafiyar hawainiya saboda yanayi, hakan ta
samune dalilin babban dalili daya shafi uzirin rayuwata. Insha
ALLAHU bayan salla zakuga canji ayi haƙuri amin afuwa dan
ALLAH yau da gobe kenan kun san Bilyn taku ba haka takeba
a da.🙏🥲.

Himmm!! Ban san ma mizan ce mukuba daga ƙarshe,
amma ku sani DAUƊAR GORA part 2 zai zama na musamman
ne da salo mai..... (🤭hummm badai sai nace komai ba..)

★Yaya kuke tunanin rayuwar Iffah zata kasance ne?.

★Mizai faru da Tajwar Eshaan zai mutu ne kokuwa?.

★Waye saurayin daya kwamushe su Kaka?.

★Taya Tajwar Eshaan ya zama Ajmaal?.

★Wacece ta ƙurya?.
★Miran Jasim da Miran Arshaan zasu ci nasara?.

★Anya ƴan ƙasar ruman akwai mai iya kwantar da fushinsu a
wannan gaɓar?.

★Yaya makomar su Babiy da Barrister?.

Kai tambayoyin da yawa suke karna cikaku da zance Ni
ban baku cigaba ba. Kudai kawai muyi addu'ar ALLAH ya
kaimu a gama azumi lafiya. Ya rabbi kasa muyi karɓaɓɓiyar
ibada.

Ina ƙaunarku masoya, zan cigaba da ƙaunarku kuma. Duk
wanda ya soni domin ALLAH shima ALLAH ya soshi haka😭 😍
😍😘 .

Taku Bilyn Abdull ce😉😄.

09032345899

********************************************
Visit http://novelselite.com.ng for more books

About Novels Elite
Novels Elite is a website consisting of Hausa Novels Books
such as Text, Documents, Audiobooks, and Videos, the
purpose of creating this site is to Entertain, Motivate and
Educate our readers.


Novels Elite provided so many kinds of Hausa Novels of any
type, Such as Adventure, love, romance, fiction, non-fiction,
mystery, fantasy, action e.t.c.

We provided a new and old novel as softcopy from our
Authors with their permission

Zaku iya samun mu a kafafen sada zumuunci kamar haka:

Facebook: Novels Elite
Youtube: http://youtube.com/@novelselitetvß
***********************************************

34 / 34