Author : Bilyn Abdull ce Category : African Stories & Novels
“Na'am Baba”.
Ta amsa akan laɓɓanta.
“Damuwa ko ƙuntata kai bata sauya ƙaddarar bawa.
Juriya da tsantsar jarumta baya hana ƙaddarar zuwa. Haƙilo
ko nuna ƙarfin iko baya ture ta a lokacin da aka so. Rauni ko
rashin tawwakali bazai dawo maka da abinda dama can ba
naka bane ba. Haƙuri shike samar da komai koda kuwa a
zahiri yafi ƙarfin ƙarfinka”.
“Hakane Baba”.
Ta faɗa cikin rawar murya.
Murmushi ya saki da matsawa kusa da ita sosai. Ɗa a gaban
iyayensa baya girma koda ace yayi furfura a saman kai. Kaka
ya riƙo hanun Ummu cikin nasa, ɗayan kuma ya shafa kanta.
“ALLAH yayi miki albarka. Yasa ƙaddarar su ta zama kaffara a
garemu baki ɗaya.”
“Baba mun rasa su suma ko?”.
Ummu dake dubansa idanu cike da ƙwalla ta faɗa.
Murmushin ya sake sakar mata. Sai kuma ya girgiza kansa da
kwanto da kanta bisa kafaɗarsa. “Bamu rasa su ba, ba kuma
mu fidda rai da samunsu ba”.
A hankali hawayen da suka kasa fita a idonta tsahon
kwanaki suka fara sauka a kafaɗarsa.......
★★.... ★★.... ★★.....
Mummunan mafarkin da ALLAH ya bata ikon cin galaba a
cikinsa ta farka a zabure, cikin amincin UBANGIJI harshenta
ya ambato addu'ar tashi daga barci kamar yanda musulinci ya
ɗoramu akai. Ajiyar zuciya ta sauke da saka gefen bargon
data lulluɓa ta yarce gumin da yay ma goshinta jalab, sai
kuma ta sake lumshe idanu jin sautin kiran salla da take
ƙyautata zaton a masallacin cikin masarautar ne. Hasken
ɗakin ta kai hannu ta ƙara, ta bi ko'ina na cikinsa da kallo
tamkar zataga munanan halittun data gani a cikinsa a
mafarki. Rashin ganin komai a zahiri ya bata ƙarin gwiwar
sakkowa a gadon ta nufi toilet. Bata damu da rashin ganin
Tajwar Eshaan a ɗakin ba duk da taji Malikat Haseenat ta
ambata nan ɗin matsayin ɗakin barcinsa na daren jiya.
Ƙarancin shekarunta da wautarta yasa bata ɗauki tsallakewar
komai ba. Abinda kawai zuciyarta ke mata kaikawo a rai shine
ta tsallake daren na jiya dai koma yaya ne, ta tsallake tarihin
mutuwa a daren kwana turakar dodon matsafa. Dalilin
tsallakewar, ko barinta da yay da ranta ne bata sani ba, ba
kuma tasan tayaya ya kamata ta sani ba. Abinda kawai take
da damar yi shine buɗe kunne da idanuwa taga mizai biyo
baya ga kowa da kowa. A yanzu ɗin ma tayi zaton ganin jinin
kamar jiya dai, sai dai babu alamar hakan har ta kammala
uzirinta tayo alwala ta fito. Tana idar da salla wani irin
nannauyan barci ya dinga fisgar idanunta. Dakewa tai cikin
dauriya tai zaman yin azkar, da ƙyar ta iya kammalawa barci
yay mata baban fisga a wajen dole takai kwance tana
ambaton sunan ALLAH. A hankali ta fara sauke numfashi
alamar barcin nata mai nauyi ne....
★★.... ★★.....
A cikin masarauta tako ina an gama baza kunnuwan jin
fito da gawar Zawjata-almilk. Hatta da Malikat Haseena bata
tare da nutsuwarta gaba ɗaya. Tun ana ƙirga sakanni a bayan
sallar asubahi har aka koma mintuna, mintuna suka koma
awanni babu wani labari. A take aka koma ƴar ƙus-ƙus tun
daga kan hadimai har manyan masu faɗa ajin masarautar.
Yayinda suma Hadiman sashen Shahan-shan suke zaune
jigum-jigum na jiran tsumayen abinda kowa keda tabbacin zai
kasance. bakunansu cike yake taf da abubuwan faɗa akan
abinda suka wayi gari da shi mai matuƙar rikitarwa da zai
maimaita faruwa bayan ya faru ga duk wata Zawjata-almilk
data kwana ta tashi a wannan sashen. Duk ɗunbin yawan
abin cewar iyakarsa zukatansu dan ko'a tsakaninsu bai
faɗuwa balle gulmantawa a waje saboda tako ina camara ce
zagaye da su.....
*_★MALIKAT BUSHIRAT★_*
Ba'a safiyar yau ba, ita tun ma a daren jiya tai hanun riga
da nutsuwa. Gaba ɗaya a daren ko sau ɗaya bata iya ta rintsa
ba. A maimakon barci ma idanunta akan sashen Shahan-shan
da kowa ke iya gani daga nasa sashen a cikin masarautar suka
kwashe mafi yawan awannin daren na jiya. Tayi yunƙurin
kiransa amma wayar a kashe, hakanne ya sake ɗaga mata
hankali da jin zafin wannan hukunci na Malikat Haseenat a
karo na farko. A ganinta ganganci ne miƙa nagartacciyar
yariya irin Iffah hannun gudan jinin nata bayan Mamma tasan
minene makomar yin hakan ga rayuwar yarinyar. Duk
jarumtarta a duk sanda ta tuna zuwa safiya gawar yarinyar ce
zata fito takanji ƙwalla sun cika idonta. Amma takan danne ta
hanasu fitowa har garin ALLAH ya kammala wayewa...
Tun idar da sallar asubahi bata iya ta motsa ba, ƙirjinta ne
ke matuƙar bugawa da jiran tsammanin mummunan labari.....
*_★DANEEN AMMARAH★_*
A ɓangaren Daneen Ammarah itama a kwatankwacin irin
halin da Malikat Bushirat ta kwana ta tashi take ciki. Dan ita
kwana tayi ma tana hawaye. Har ƙarƙashin zuciya takejin
matsanancin ƙaunar Iffah. Tana jin yarinyar a matsayin cikon
wani gurbi data rasa irin na kowace uwa mai shekarunta. Sai
gashi Mamma da ta fara bata tsoro a daren jiya ta rusashi da
maye gurbinsa da fargaba mai matuƙar tsanani da razani.
Wani mutum saɓanin jininta bai taɓa mamaye zuciyarta da
ƙauna mai ƙarfin haka ba kamar yanda yarinyar tayi mata.
Sosai take jinta a rai da jinin jikinta. Itama dai tun daga sallar
asuba bata sake iya kataɓus ba tai zaman jiran tsammani irin
na duk wanda ya kwana ya tashi a cikin masarautar.......
★★... ★★.... ★★....
Harya gota ɗakin cikin shiga ta blue ɗin jallabiya mai
tsananin ƙyau da ƙyalli mai ɗaukar ido da nuna taushinta a
zahiri dake nuna daga masallaci yake ya tsaya cak. Kamar
bazai motsa ba sai kuma ya juya kansa a sannu yana kallon
ɗakin. Kallon kusan minti ɗaya da wasu sakanni ya motsa
gaɓɓansa cikin takunsa na izza da kame kai ya tura kai ciki. Da
farko rashin lura da ita ya sakashi yin tsamm, sai dai fuskarsa
ta nuna dakewa kamar koyaushe. Ya ɗaga ƙafa da niyyar
juyawa ya fita idanunsa suka sauka a kanta. Yay tsai yana
kallonta na tsahon mintuna kusan huɗu tamkar mai rarrabe
ita ɗin ce ko wata? Dan a kallo ɗaya zaka fahimci salla ta idar
a wajen barci yay awon gaba da ita. Ya ɗan furzar da
numfashi da kauda kansa gefe ya sake bin ɗakin da kallo kai
kace baƙonsa ne har ya sake direwa akan fuskar Iffah dake ta
barcinta numfashinta na fita a hankali.........✍️
33
.........Ƙarfe takwas da rabi dai-dai agogon ƙasar ɗaya daga
cikin amintattun Hadiman dake gyara ɗakunan barcin na
Tajwar ta iso cikin faɗuwar gaba hanunta ɗauke da akwati da
aka kawo yanzun nan daga sashen Malikat Haseenat
matsayin kayan da Iffah zatai amfani da shi. Zuciyarta har
wani zallo take na fargabar abinda take da tabbacin tozali da
shi kamar yanda sukayi a baya ga sauran Zawjata-almilk da
suka shuɗe. Ta tura ƙofar cikin sanɗa tana mai ambaton
sallama da rawar harshe badan tana tunanin samun amsa ba.
Ganin Iffah kwance a saman gado, lulluɓe da lallausan bargo
baisa taji ƙwarin gwiwa ba. Tai yunƙurin ajiye akwatin
hanunta, cak ta tsaya dukkanin idanunta na fitowa waje dan
firgici ko sumar tsaye sakamakon juyi da Iffah tai alamar
gyara kwanciya. Akwatin ta saki ƙasa ta shiga jan jikinta dake
ɓari baya-baya harta dangane da ƙofa gab.....
Iffah dake ƙoƙarin gyara bargo idanunta rufe ta buɗesu da
sauri saboda jin ƙarar bigewar hadimar. Da mamakin jinta
kamar a gado ya sata shashshafa hannunta. (Tabbas
gadonne) ta ayyana a zuciyarta tana sake buɗe idanunta da
ƙyau tana mai yunƙurin tashi zaune. Tuni hadimar nan ta sake
firgicewa, da lalube ta murɗa handle ɗin ƙofar ta fita a guje.
Kallon ƙofar Iffah tayi, sai dai hadimar ta gama ficewa
bayanta kawai ta ɗan gani kaɗan da wulgawar mayafinta. da
sauri ta yaye bargon da bata san ya akai yazo jikinta ba. Ta
dire ƙasa mamakin duniya na cigaba da dabaibaye ta.
“Wacece wadda ta fita? Mi tazo yi? Wai ta yaya ma na dawo
saman gadon nan bayan a ƙasa na kwanta?”. Ta shiga jerama
kanta tambayoyin da bata san inda zata samu amsarsu ba. Sai
kuma ta ɗan kamo rigar jikinta ta kai hancinta. “Ya ALLAH, da
gaske fa wannan mayataccen ƙamshin a jikina ne?”. Ta sake
faɗa a fili tana sake shinshinar rigar......
A ɓangaren jama'ar masarauta dake a zaman jigum-jigum
kam fitar hadimar nan ya isar da saƙon Zawjata-almilk na
raye. Da farko duk wanda zancen yaje kunensa ɗaukewar
numfashi na wucin gadi ne ke riskarsa, sai kuma rashin
gaskatawa a zahiri ya biyo baya. Hatta da Malikat Bushirat da
Daneen Ammarah yanayi da ruɗanin jin hakan bai tsallakesu
ba suma. A kusan tare suka ɗauka wayoyinsu domin neman
Iffah ko zasu samu jin gaskiyar zance. Cikin Sa'a kuwa ta
Daneen Ammarah ta fara shiga....
Iffah na zaune har yanzu cikin ɗaurewar kai akan wanda
ya maidata saman gado da wulƙawar fitar wadda bata sani ba
wayarta ta katseta. Numfashi taja ta fesar da ɗan ƙarfi tana
kai hannu akan wayar. *_Mamy_* ta gani rubuce ɓaro-ɓaro.
Ganin zata katse tai ƙarfin halin ɗagawa ta kai kunne tana
faɗin, “Assalamu alaikum. Amincin UBANGIJI da rahamar sa
su yalwatu a gareki Mamy barka da safiya”.
A matuƙar razani da motsuwar zuciya Daneen Ammarah
taja numfashin dake neman ƙwace mata. “Ibnati!”. Ta
ambata cikin son tabbatarwa.
“Na'am Mamy”.
Iffah ta amsa kanta tsaye babu alamar irin fargabar dake
harshen Daneen Ammarah ɗin a tattare da ita. Dan ita wanda
ya ɗauketa daga ƙasa ya maida saman gado da fitar macen
data ganine kawai damuwarta a yanzu. Daneen Ammarah da
taji al'amarin tamkar a mafarki ta lumshe ido hawaye na
silalo mata saman ƙyakykywar fuskarta a hankali. Ƙasa takai
durƙushe tana mai godema UBANGIJI ta hayar kai goshinta
ƙasa tai sujjadar shukur...
Iffah da mamaki ta cigaba da ambaton “Hallo Mamy!
Mamy kina jina kuwa?”. Shiru babu alamar za'a amsa. Yanke
wayar tai da yunƙurin sake kira a zatonta matsalar network
ce sai ga kiran Malikat Bushirat ya shigo shima. Ɗan jimm tai
tana kallon wayar, sai kuma ta ɗaga takai kunne da sallama
nan ma. Malikat Bushirat da idanunta ke cikowa da ƙwalla
sakamakon jin muryar Iffah tar-tar a kunenta ta kai zaune
tana ambaton sunan ALLAH. Iffah na son tambaya tana jin
nauyi, sai kawai tai shiru tana sauraren kalmomin godiya ga
ALLAH da Malikat Bushirat ɗin ke ambata daga can.
(Ya rabbi! Wai mike faruwa ne haka?) Ta ayyana a
zuciyarta da al'ajabi. Knocking ƙofa da akai ta hanyar danna
alerm a dai-dai lokacin ya katse tunanin nata. Ta kai dubanta
ga kofar babu alamar zata tanka har aka sake danna alerm
ɗin sannan tai ƙarfin halin amsawa da bada umarnin shigowa
tana gyara mayafin data yanama kanta.. Hadimar ɗazun ce
dai ta shigo ɗauke da ƙaramin tray mai ɗauke da butar shayi.
Kanta a ƙasa ta ajiye a inda ya dace tana mai zubewa ƙasa
durkushe. “Amincin ALLAH da tsahon rai mai albarka su
kasance tare da Zawjata-almilk Barka da safiya”.
Iffah da ke kallonta ta amsa cikin motsa lips ɗinta kaɗan.
Sabo da hakan yasa hadimar bata damu da rashin amsawar
Iffah ba. Cikin sake rissinar da kai tace, “Ya Zawjata-almilk
yanzu lokacin wankanki ne, bayan nan karin kummalo na
jiranki tare da Shugabana”.
Yanzu ɗin ma kamar Iffah bazata amsa ba sai kuma ta
jinjina kanta. “Kije abinki zan fito”.
“Umarninki shine abin jirana. Amma a gafarceni zan haɗa
ruwan”.
“Kije abinki zan yi komai da kaina”.
Babu yanda hafimar ta iya dole ta miƙe domin bin umarni
shine kawai huruminsu. Da kallo iffah ta bita abubuwa masu
yawan gaske na son fara mata kutse a ƙwaƙwalwa da zuciya.
Ƙwarin gwiwar da take bama kanta akan turesu ya sata
miƙewa ta nufin toilet tana mai ambaton addu'ai a bakinta
saboda tuna abinda taci karo da shi a daren jiya a toilet ɗin.
Ko'ina tsaf, kuma cikin ƙamshi irin na daren jiya. Sai da ta
ƙarema komai kallo fiye da jiya kafin ta ɗage kafaɗa irin na
koma miye ta shirya masa. Tsabagen rigima da wuce wuri ko
tsageranci za'ace ta haɗa ruwanta mai ɗumi da zuba duk
wani nau'in turaren wanka da aka jera domin Shahan-shan ta
shige cikin kwamin wankan tai luf. Sai da taji ko'ina nata ya
miƙe yanda take buƙata sannan ta fita a ruwan domin fara
wanka...
Tsaf ta kammala shirinta cikin doguwar rigar material sky
blue da akaima ɗinkin daya fidda ainahin halittarta tamkar
ƴar tsanar roba. Rigar ta zauna mata ɗas, siririn mayafin da
aka haɗa rigar da shi ta naɗa tamkar yanda larabawa keyi, ta
ɗakko after dress shara-shara mai kamar alƙyabba ta ɗora a
sama kalar blue sosai. Ta ɗanji babu daɗi na rashin
turarurrukanta tare da ita, dan ko waɗan nan kayan ganinsu
kawai tai, cikin ɗan taɓe baki da ɗage kafaɗa a zahiri ta dinga
kwasar turarrukan da taci karo da su a ɗakin cikin wani
ƙyaƙykyawan glass dake kusa da mirror ta dinga zazzagama
jikinta har sai da ta gamsu ƙarfin kamshin zai kai duk inda mai
rai ke numfashi a sashen sannan ta haƙura. Idanunta ƙyam a
mirrorn ta saki ƙayataccen murmushi da kanne ido ɗaya a fili
ta furta “Irin wannan haɗuwa haka autar Ummu”. Tai salute
ɗin kanta....
Sautin ƙarar takun takalman ƙafarta da mayataccen
ƙamshin tiraren da shi kaɗai aka sani da shi ya sashi tsayawa
cak daga ƙoƙarin kai hannu a abincin da aka gama haɗawa
gabansa. Fararen idanunsa tar-tar tamkar madara ya ɗago ya
sauke a kanta. Hakama hadiman dake a tsaye ta gefe da
gefensa kawunansu a ƙasa cikin yanayin mutuwar tsaye data
rikesu suka zube ƙasa kan gwiyawunsu illahirin jikkunansu na
ƙyarma akan dalilai guda biyu. Na farko ganin tabbatar da
wadda suka gama fidda rai da jiran tsammanin ganin an shigo
fidda gawarta tamkar Zawjata-almilk na baya dai na raye ɗin
kamar yanda Hadimar ta gano. Na biyu ƙamshin turaren
jikinta da ga mutum ɗaya tak ake iya jinsa a duk faɗin ƙasar
ruman ma bawai a daular ruman ba...
Tamkar Iffah bata fahimci halin da suke a ciki ba ta ƙaraso
cikin katafaren falon batare data dubi ko ɗaya a cikinsu ba
balle mai gayya mai aikin. Cikin sauri ɗaya daga cikin hadiman
ya miƙe ya gyara mata kujera, zaune ta kai tana mai dubansa
a karo na farko. Tuni shi kuma ya maida kansa ga abinda yake
yi tamkar bai san da zuwan tan ba. Ta taɓe baki da juya
idanunta ta maida ga hadimar dake ƙoƙarin fara haɗa mata
abincin. Nunin abinda take buƙata tai mata da ɗan yatsa.
Hadimar na kammalawa ta koma cikin ƴan uwanta ta tsaya
itama kanta a rirrine.
Gaba ɗaya jinta take a takure, kwarjininsa ya cika ko'ina a
falon. Cikin dakewa da kaucewa gizago sa ta ɗan ɗago ta ɗan
saci kallonsa da nufin gaishesa idanunta suka shige cikin nasa
da ya ɗago da nufin kallon nata...
“Who are you?”
Ya fara faɗa cikin basarwa yana kaɗa idanusa da har yanzu
ke cikin nata tamkar bashi yay maganar ba. Badan a idanunta
tausasan lips ɗinsa suka motsa wajen ambaton wacece itan
ba zata iya gaddamar hakan. Kaifin idanunsa sun neman sage
duk wani ƙwarin gwiwarta. Ƙoƙarin fara sassauta nata idanun
tai yunƙurin yi cikin ƙanƙance su sannu a hankali. Shima sai ya
kankance nasa kamar yanda takeyi, fuskarsa na sake tsukewa
babu alamar sassauci tattare da ita. Nata ta fisga da ƙarfi ta
lumshe su, sai kuma ta buɗe a kansa tana mai sake tsuke tata
fuskar itama, bazata iya jure salon nasa ba dake neman ƙone
ƙudirinta, dan haka ta kauda kanta gefe babu alamar zata
bashi amsar da yay yunƙurin ji daga garetan..
“Barka da safiya”.
Ta faɗa a ƙoƙarinta na basar da tambayarsa ta farko.
Bai motsa ba, babu alamar kuma zai amsa ta. Hakan sai ya
sake sukar zuciyarta harta ɗan saci kallonsa, da sauri ta kauda
idanunta, dan da gaske fuskarsa ruguza mata lissafi take, da
gasken gaske shi ƙyaƙyƙyawa ne, irin ƙyawun dako a cikin
ƙasar tasu ake yabawa da shi, koda yake batai mamakin
hakan ba, dan Malikat Bushirat ba'a magana, duk da girma ya
fara zuwa gareta tsantsar ƙyawunta a bayyane yake. Hakama
Malikat Haseena dake matsayin kakarsa data haifi babansa
tunda ita dai bataga baban nasaba ko'a hoto har yanzun,
amma zubin Malikat Haseena dana Daneen Ammarah ya
tabbatar mata shima ɗin dai zai kasance ƙyaƙyƙywan ne......
“What is your goal in life?”.
Kalmomi guda shida suka katse mata tunani a bazata. Ta
kallesa tana ƙoƙarin danne mamakinta kan waɗan nan
tambayoyi da yake faman yanko mata kai tsaye. Ganin yanda
ya zuba mata ƙasaitattun idanunsa masu firgita mara gaskiya
ta janye nata tana yamutse fuska. (Damarki ce wannan) wata
zuciya ta ayyana mata. Cike da gamsuwa ta sake kauda kai
gefe dan har yanzu tanajin kaifin idanunsa a kanta. “Ni ban
kasance kowa ba sai talakar dake a ƙarƙashin mulkinka ranka
ya daɗe. Abinda nake son cimmawa kuwa a rayuwata irin
abinda shugaba ke fatan cimmawa ga talakawan ƙasarsa ta
hanyar mulkarsu da fuska biyu ne”.
Yanda tai maganar kanta tsaye babu ko ɗar ya sashi jin
mamakinta. (Tabbas wannan abar ba mutum bace) zuciyarsa
ta tabbatar masa. A zahiri sai ya ɗauke kansa cike da
basarwa. Shiru babu alamar zai sake tankawa har Iffah tama
fidda rai ta cigaba da tsakurar abincinta kamar yanda yakeyi
shima.
“Wasa da rayuwarki kuskurene ga ƙarfin halinki, ƙin
kasancewar ki tarihi a wannan safiyar bashi ke tabbatar miki
nasarar tsallakewa ba”.
A yanzun kam zantukansa sun zama masu matuƙar tasiri a
fitarsu da saurarensu gareta, jin bazata iya dannewa ba ta
amsa batare data ɗago ta kallesa ba,
“Hakane shugabana, sai dai fa _Fate is some thing
undeniable”_
Ya basar babu alamar yanzu ma zai amsa, shayin sa ya
kai baki cike da ƙasaita. Itama sai bata sake cewa komai ba ta
cigaba da cin abincin tana mai kallonsa ta gefen ido, sannu-
sannu tabi sautin motsa plate ɗin gabansa da kallo har kan
lallausan farar fatan hanunsa masu ɗauke da tsaftatattun
fararen dogayen farce, baya tai ƙoƙarin jan jikinta batare data
yarda idanunta sun wuce kallon hanun nasa ba. Yanda ya
basar da ita ɗin kuma sai yay matuƙar sukar zuciyarta, dan
bata buƙatar tattaunawar tasu ta tsaya iya haka. Amma sai
bata yarda fuskarta ta nunaba. Sai ma mamakin ƙasaita da
tsantsar izzar wannan bawa da zuciyarta ke faman yi. A wani
ɓangaren ita kanta dakewa kawai take, amma kwarjininsa da
gizago na firgita ta matuƙa. Tana ƙara tsarkake sunan ALLAH
akan yarda da jinin mulki gaskiya ne. Duk da ta shigo daular
ruman da wani ƙudiri a ranta hakan bazai hanata girmamashi
ba, koda ace tayima yunƙurin hakan kwarjinsa bazai bata
damar yin saɓanin girmamawar da kowa ke masan ba. So
take taji tsanarsa a ranta kamar yanda takeji kafin ganin
wannan fuskar matsayin shi amma zuciyarta taƙi bata haɗin
kai. Numfashi taja a hankali ta fesar a ƙasan maƙoshinta.
“Kokawa da ƙaddara a fuskar iyawa na nufin faɗuwa!
Kinga ko what you get