Author : Bilyn Abdull ce Category : African Stories & Novels
is, what you have?”.
Ya faɗa cikin katse mata tunani dai-dai yana ɗagowa.......
✍️
“Fareedatu kibar danginmu su tsinkayi yini da kwana cikin
sallama, Banda taro dutsen zuma inake ina kace nace da
dodon may...🥱🏇”.
34
........(Mi wannan mutumin ke ƙullawa?). Ta faɗa a zuciya
batare data motsa ba. (Keda ke neman kusanci da shi dama
miye matsalarki da koma mi yake nufi) wata zuciyarta ta sake
ayyana mata. tamkar wadda aka zaburar sunan Arfa da Fariha
ya fara amsa kuwwa a zuciyarta har tana jinsa yana tashi bisa
sararin samaniya.
Kaifafan idanunsa masu nuna tsaurinsa ya zuba mata ganin
ta basar da shi itama. Kusan mintuna uku babu alamar zata
tankama zancen nasa har ya fara jin haushi. Ta taɓe baki da
kauda kanta gefe, cike da dakewa ta furta, “Da gizago na
tsorata ƙwarin gwiwata da bazan amincewa shigowa ramin
zakin da ɗanyen nama shine abincinsa ba. Karka damu a
kaina ranka ya daɗe, dan a wannan gaɓar *_cuta ce ta ɗakko
cuta, ɓarawo ya ɗakko akwatin maciji”._*
Fuska ya ɗan motsa kamar zaiyi murmushi, sai kuma ya
basar. “Bana haɗa ƙwanji da mage duk da kamaninta na
yanayi da nawa matsayina na ZAKI har a hallaya. Ki kama
kanki dan kina buƙatar rayuwa mai tsaho wajen moran
ƙuruciyarki”.
Ya faɗa da muryarsa mai zurfi da ƙasaita yana miƙewa ya
zagayeta ya wuce abinsa. Shiru bata motsa ba har ta gama jin
ɓacewar sautin takunsa a wajen, ta ɗan cije bakinta “Zaki
zako ka magantu fiye da haka”. Ta faɗa a fili cike da
kwaikwayo salon maganarsa tana sakin wani lallausan
murmushi da kai kofin shayi a bakinta, duk da zafinsa ta
rumtse ido ta kwankwaɗe abinta sannan ta juya taima
hadiman dake tsaye har yanzu kallo ɗaya ta ɗauke kanta
batare da damuwar komai ba, dan tasan basuji komai ɗin ba
da suka tattauna. A yanda suke maganar ma wani sai ya
ɗauka wani zancen soyayya ne ya haɗasu. Komai batacema
kowa ba itama ta miƙe tabar wajen, duk suka bita da kallon
ƙasan ido kowa da abinda yake ayyanawa a zuciyarsa.
A tafiyar tata tana ɗan kalle-kalle taci karo da camara,
komai bataji a ranta ba, dan tayi tsammanin hakan tun farko,
saboda babu yanda za'ai sashen mutum mai ƙarfin iko kamar
Tajwar ace babu wani tsaro makamancin hakan koma fiye da
hakan. Da ƙyar ta iya gane ɗakin data kwana. Tana shiga ta
zube a kujera da sauke nauyayan numfashi, ɗakin da akaima
gyara ɗan gaske tabi da idanu, sai taga ma kamar ba'a cikinsa
ta kwana ba, ganin akwatin kayanta kawai ya tabbatar mata
da shi ɗin ne. Tunani mai ƙarfin gaske ta faɗa kusan kashi uku
zuwa huɗu musamman akan kawota da Malikat Haseena tayi,
mi tsohuwar ke nufi da haka bayan su suka sanar mata an
rasa matan baya ne a dalilin kawosu turakar Shahan-shan ɗin.
Sai kuma akan Tajwar Eshaan ɗin, na farko waccan fuskar
data gani a waje kafin shigowarta masarautar matsayin
matarsa. Na biyu wannan fuskar ta yanzu da bata da
banbanci da waccan ɗin, na uku hanyar da ya kamata ta
cigaba da bi domin sanin ainahin wanene Tajwar Eshaan Ibn
Haysam Abdul-majeed a baɗini da zahirin rayuwa. Domin da
gasken gaske tana a cikin ruɗani akan fuskokin nan biyu data
gani a mabanbanta muhallai. Su ƴan biyu ne? Kokuwa shi
ɗinne ke ɓadda kama yana fita?. Abu na uku kuma abinda ya
faru a daren jiya da sai a yanzu yake bata matuƙar mamaki,
tun a jiyan bawai ta ajiyesa a gefe bane dan bashi da
muhimmanci ga haɗarin da tasan ta kawo kanta ciki, kawai
dai bata san dalilin da yasa bataji ko ɗar ba a zuciyarta na
tsoro, kuma har yanzu batajin tsoron sam, dama kuma tun
asali bata da tsoron. Dan Iffah irin mutanen nan ne masu
ƙesashiyar zuciya mai iya tunkarar komai koda yanada haɗari
a garesu, tanada naci da zama kaifi ɗaya akan zimma da
cimma buri duk da ƙarancin shekarunta. Na ƙarshe
tattaunawarsu ta yanzu da shi da girman kalaman da yay
amfani wajen jifanta da su. Ta ɗan murmusa da cije lips ɗinta
tana mai lumshe idanu a hankali......
★★.... ★★.....
Zuwa yanzu tako ina maganar tsallakewar Iffah ce ke
kaikawo a cikin masarautar. Kowa ya nutsu wajen tattauna
abinda ke bakinsa da abokin maganarsa. Wasu jin daɗine
game da hakan, wasu ko baƙin cikine a ransu, dan mutuwar
Zawjata-almilk ɗin kamar wani makamine a hannayensu na
dukan nasarar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed ɗin.
Tsallakewar Iffah kuma zai kasance kamar damar
ƙalubalantarsa da suka riƙe ya kuɓuce musu kenan. Ita kuma
yarinyar kimarta da nunawa duniya tafi ƙarfin masu ƙarfin zai
yi tasiri a zukatan jama'a.....
★Komai dake faruwa yana isa da shiga a kunnen manyan
masu faɗa aji ta bangaren iko da kusanci da Tajwar Eshaan
ɗin. Wato Malikat Haseenat da Malikat Bushirat. Sai dai sunyi
biris babu alamar zasu tofa nasu akan hakan bayan bayyanar
farin cikinsu akan fuskokinsu daya gaza boyuwa ga kowa. Dan
a dalilin wannan al'amari Malikat Bushirat har ƴafiya tayi ga
wasu firsinoni dake a cikin kurkukun masarautar akan wasu
laifuka nasu da basu kai sun kawo ba. A cikin sunne kuma aka
sallami harda Diwa a dalilin bincike daya tabbatar da bata da
hannu game da abinda ya faru ga Iffah a waccan ranar.
★A ɓangaren Malikat Haseenat kuwa maimakon bama
abinda ke zuwama kunenta muhimmanci hankalinta ta maida
wajen tantance hadiman da zasu koma aiki a karkashin Iffah
ne bisa taimakon Daneen Ammarah da farin cikinta itama
yake a bayyane. Dan itama dai har kyaututtuka na
musamman yau ta bada ga hadimai tare da sakawa a tattaro
mata dukkan malaman masarautar zuwa sashen Iffah da
bukatar suyi saukar Alkur'ani mai girma. Ta kuma miƙe da
karfin jikinta wajen shirya lunch na musamman ga Tajwar
Eshaan da amarya Iffah Zawjata-almilk...
*_★BARRISTER★_*
Abubuwan da suka faru sun sakashi dakatawa a zahirance
bisa shawarar Kaka. Sai dai yana cigaba da gudanar da wani
binciken sirri dan yayma kansa alƙawarin binciko duk mai
hannu akan wannan al'amarin nasu Babiy da ma inda aka
ɓoye su.
Kamar yau ma tun jijjifin safiya ya fito daga gida. Kai tsaye
hanyar jihar Hubab ya nufa inda bincikensa ya tabbatar masa
nanne ainahin jihar da matar Abu Moosa ta fito. Jihar Hubab
makwafciyar Dahab city ce (Daular ruman kenan) dan haka a
cikin ƙanƙanin lokaci ya isa. Bai tsaya sanyaba ya ɗauka
hanyar ainahin kauyensu kuma. Kasancewar anan ma
hanyace shimfidaɗɗiya a kanƙanin lokaci ya isa. Da farko ya
sha wahalar binciken inda gidansu yake, sai da yay dabarar
nuna hotonta sannan.
Kusan mintuna goma bayan isar da saƙon tanada baƙo
gareta ta fito cikin irin shigarsu. Tayi ɗan tsamm alamar shan
jinin jikinta kafin ta ƙaraso a yanayin son basarwa. Barrister
shi ya fara gaidata, tare da sanar mata sunansa. Lokaci ɗaya
ruɗani ya bayyana akan fuskarta ta shiga waige-waige irin na
rashin gaskiya da ƙoƙarin ja baya daga garesa...
“Bawan ALLAH ina baka shawara ka taimaki kanka ka bar
ƙauyen nan, babu wani abu da zaka iya ji a gareni dan ban
san komai ba”.
A fusace Barrister yay tsalle gabanta yana huci. “Baki san
komai ba amma akaje da ke har gida aka kamasu. Karki sha
mamakin bayan sanin inda kike har wasu abubuwa na sani a
kanki Mss Farishta. Rashin bani haɗin kai kuma na nufin na
tonasu kowa yasan ke ɗin wacece har ma da dalilin auren
Dawood, sani kankine wannan babban koma baya ne a gareki
kuma harma da zuri'arki”.
Yayu ta haɗiya masu kauri tana kallon Barrister, sai kuma
ta sake wawwaigawa tabbacin dai akwai abinda take shakka.
“Naji Barrister zan baka dukkan bayanan da kake buƙata,
amma ina roƙonka kabar wajen nan, idan ma zai yuwu
kauyen nan gaba ɗaya nake son ka bari. Wlhy na maka
alkawarin zan zo na sameka na kuma faɗa maka komai da
kake buƙata harma wanda baka sani ba”.
“Miyasa bazan sani ba a yanzu?”.
“Saboda zamanka anan yana da matuƙar haɗari”.
“Taya zan tabbatar da zaki zo ɗin?”.
“Na baka dama kabi duk hanyar da zata bibiyi al'amarina”.
Kafaɗarsa ya ɗan ɗage sama da faɗin, “Okay inaga bana
bukatar hakan, kije kawai ni na san ta hanyar daya dace na
bibiyekin. Amma yaushe ne zamu haɗun?”.
“Inasha ALLAH a daren yau ka sameni a ƙauyen Jumna”.
“Garin su Abu Hanash da Dawood kenan?”.
“Insha ALLAH”.
Tafiya yake zuciyarsa na faman masa kaikawo akan
haɗuwar tasa da Farishta (matar Abu Moosa datazo har gida
da ƴan sanda aka kama su Babiy. ALLAH yasa kun gane🥱). Duk
da yasan zata iya ƙin aikata abinda ta faɗa na haɗuwar tasu a
garin Jimna ya zaɓi barinta su haɗun can bisa lumana. A cikin
Hubab ya tsaya yaci abinci tare da sallar azhar. Ya fito
masallaci idanunsa suka sake sauka akan wata mota da tun
fitowarsa ƙauyen su Farishta ya lura da ita tana biye da shi,
sai dai duk da ya ganta suna tafiya kafaɗa da kafaɗa bai kawo
komai a zuciyarsa ba. Janyewa yay cike da rashin bama abin
muhimmanci ya shige motarsa da zummar zai cigaba da
tafiya kawai yaga an zagaye motarsa da bindigu.......
★★★.... ★★.... ★...
A firgice ta farka a ɗan barcin daya figeta bayan ta idar da
sallar azhar. Ta dafe kanta dake sara mata. Irin mafarkin da
tai da dare ne dai babu banbanci. Huci ta furzar da faɗin,
“Wace madara ce haka? Tabbas kodaga ina zata fito babu
alkairi a cikinta tunda har mafarkin nan ya sake maimaita min
kansa. Ya ALLAH”. Ta furta a fili zuciyarta duk babu daɗi, dan
zuwa yanzu Iffah ta fahimci wani ɓoyayyen al'amari game da
ita, tabbas in har zatai mafarki taita kuma maimaita irinsa sai
wani abu ya biyo bayansa mai taɓa zuciya, ta gane hakanne a
ɗan zamanta cikin masarautar nan, sai kuma auna abubuwan
da suka faru a baya kafin yau ɗin. Sai dai tana ƙoƙarin ƙin
gasktama kanta hakan dan kar zuciyarta ta shagala kan
abinda zai sakata kaucema umarnin mahaliccinta kuma. Ga
kanta jingim kamar yanda yakeyi a duk lokacin datai mafarki
makamancin haka, sai zufa data jiƙeta sharkaf tamkar wadda
tai wanka. Shigowar saƙo a wayarta da ke gefenta ya sakata
tsurama wayar ido na kusan mintuna biyu, kamar wadda aka
zaburar wani abu data shafa'a kuma sai ta jawo wayar. Data
ta kunna a take tai downloading WhatsApp app..., Bayan ta
kammala dai-daita komai tai searching number Sir Fawzan da
zuciyarta ke ayyana mata ta fara nema, cikin rashin sa'a taga
kusan kwana uku ma baya online ta hanyar lastsin ɗinsa. Duk
da hakan bai mata daɗi ba batai wani yunƙurin kiransa ba ta
maida akalarta kan number abokinsa Ajmaal. Cikin sa'a
shikam dai yana online. Sallama tai masa a taƙaice ta tura, sai
dai har kusan mintuna biyu babu reply (yana aiki) zuciyarta ta
ayyana mata. Aminta da hakan ya sata cigaba da ajiye masa
saƙo kawai a kan duk abinda ya sake faruwa bayan wanda ta
tura masa ranar. Daga karshe ta aika masa da roƙon ya
bincika mata iyayenta dan har yanzu hankalinta ya kasa
kwanciya dangane da su. Ta haɗa masa da adireshin gidansu,
da faɗin (In har kaci amanata ko yaudarata na barka da
mahaliccin rana da wata yay maka hukunci da alhakin dukkan
al'amuran ƙasar ruman da zalincin mulkin wannan shaiɗanin
dodo ke tafin hanunsa). Daga haka ta fito shima Sir Fawzan
ɗin ta tura masa gajeran saƙo ta goge WhatsApp ɗin gaba
ɗayansa ta ajiye wayar.
Da ɗan layin nauyin jikin dake tare da ita ta miƙe, tana
ƙoƙarin shiga toilet taji kamar an gitta mata ta baya. Idanunta
ta ɗan rumtse sai kuma ta waigo. Komai babu dai a zahiri dan
haka ta kaɗa kanta kawai ta shige bakinta da addu'a....
Fitowarta kenan bayan ta watsa ruwa alerm ɗin ƙofar yay
ƙara alamar ana knocking. Sai da ta zira doguwar rigar abaya
data ɗakko cikin kayanta sannan ta ƙarasa ƙofar ta buɗe.
Hadimar dake tsaye ta zube ƙasa cikin girmamawa tana
kwasar gaisuwa. Amsa mata Iffah tai, zuciyarta babu daɗi
akan yanda suke ƙasƙantar da kansu, ta amsa cikin sauƙin
muryarta dake a sanyaye sakamakon mafarkin da duk ya
sakar mata kasala..
“Wani abu ya faru ne?”.
Ta tare hadimar tunkan tace komai. Kai ta gyaɗa mata tana
sake rissinar da kanta. “A gafarceni ya Zawjata-almilk. Dama
abinci ne aka kawo daga sashen mai Babban ɗaki”.
Iffah tai ɗan jim tana hasashen wace kuma mai babban
ɗaki? Kamar hadimar ta fahimta tai saurin mata fashin baƙi
da “Malikat mai babban ɗaki”.
(Malikat Haseenat) shine abinda zuciyarta ta ayyana mata.
Ta kaɗa kanta da faɗin, “Okay ba damuwa zan fito”. Daga
haka ta maida ƙofar ta rufe. Ciki ta koma, sai dai maimakon
zama sai ta koma kaikawo kamar mai Safa da marwa
abubuwa masu yawa na faman mata kaikawo. Ta jima a haka
sosai kafin ta sake kimtsa jikinta cikin wata tsadadiyar abaya
mai adon stones dake ta ƙyalli da ɗaukar idanu. (Wannan
yana cikin horon Daneen Ammarah data tabbatar mata koda
wasa karta zauna da kazamar shiga ko fitowa da ga ɗaki a
raguwar kwalliya. Dolene inhar zata bar cikin ɗakinta ta
tabbatar komai na jikinta ya isa a kalleta da shi. A tsarin
masarautar hakan ba fariyya bane mutunta kaine ga kowa. A
kuma ɗan zaman Iffah cikinsu ta fahimci hakan sarai). A yanzu
ma kamar ɗazun turarrukan sa ta baza har ƙamshinsu na rige-
rigen fita kafin ita ta fita. Ta fito cikin takunta na nutsuwa da
ƙasaita kamar wata budurwar macen ɗawisu (lol)..........
😉 ✍️
35
........Hadiman sashin gaba ɗaya kamshin turaren da sukaji ya
sakasu tunanin Tajwar Eshaan da bai jima da shigowa ba daga
fada ne ya sake fitowa. Sai kuma sukaga saɓanin haka lokacin
da Iffah ke ƙarasowa cikin katafaren falon mai ɗauke da duk
wani nau'in kayan more rayuwa irin na wanda suka isa. A
kujerar da ko ba'a faɗaba tsarin zubinta ya isa tabbatar ma
mai kallo Shahan-shan ne kawai ke zamanta ta kai zaune da
bismillah a bakinta. Ƙafa ɗaya kan ɗaya ta harɗe fiye da salon
sarauniyar Ingila tana kallonsu. Cikin rawar harshe dajin
kwarjininta ya cike falon tsaf suka shiga zubewa suna
gaisheta. Yatsu biyu ta ɗaga musu cike da ƙasaita batare data
amsa ba dan haka kawai yanayin da ta tashi da shi taji bata
buƙatar magana. Basu iya sun motsa ba har ta gama zuƙar
iska da fesarwa tamkar mai lissafin kaɗawarta sannan ta
dubesu, sai kuma ta maida ga tarin abincin da aka shirya
yanzu akan wata lallausar darduma saɓanin na ɗazun akan
teburin cin abinci. Akan farin tambulan na gilashi mai ɗauke
da madara fara ƙal-ƙal ta sauke idanun nata (mafarkina ya
zama gaskiya kenan ko saɓaninsa) zuciyarta ta ayyana har
lokacin idanunta tsaye akan tambulan ɗin..
Hadiman da basu fahimci ma'anar kallon da takema kayan
abincinba cike da girmamawa a gareta ɗaya ke faɗin, “Ya
Zawjata-almilk abincine daga saken mai babban ɗaki, an
shiryashi ne matsayin liyafa gareki ke da shugaba”. A hankali
Iffah ta janye idanunta daga wajen ta maida kan hadimar na
tsahon wasu sakkani, acan ƙasan zuciyarta kuwa nanata
sunan Malikat Haseenat take tamkar mai bitar karatun
hadda. Batare da tace komai ba kuma sai ta kaɗa kanta. Shiru
ya sake biyo baya kafin Iffah ta katseshi da duban hadiman da
har yanzu dai ke tsaye da alama zaman jiransu sukeyi kenan,
dan ta fahimci idan zaici abinci haka suke zagayesa. Kanta ta
kauda da faɗin,
“Maleek fa?”.
Kai tsaye duk suka fahimci wa take nufi, tunda dai duk sun
san minene ma'anar kalmar Malik ɗin. Cikin tsantsan da kai
ɗaya daga ciki ta amsa mata da “Yanzu ya shigo daga fada”.
Bata amsa ba, sai ɗan jimm da tai na tunani akan ambatar
fada da hadimar tayi, amma a zahiri ta basar abinta.
★Kasancewar saƙon haɗa liyafar cin abincin na Malikat
Haseenat da tai akan iya shi da wadda ake kira matar tasa ya
riskesa tunma kafin Iffah, dan kusan shine ma yay sanadin
barowarsa fada duk da Aaminsa Miran Jasim (Aami.
Kawunsa)ya buƙaci zaman tattaunawa da shi. Badan son
ransa ba ya kimtsa ya fito cikin shiga mai sauƙi ta zaman gida.
Kamshinsa da takun sawayensa dake tabbatar da girman
ikonsa tuni ya iso a kunne da hancin Iffah dama hadiman
dake zagaye da ita. Tuni hadiman duk sun zube bisa
gwiwunsu kawuna a ƙasa dan kallon shugaban nasu kai tsaye
haramunne garesu bisa al'adar masarautar, idanma hakan ta
faru gaban Ghazi zaka iya fuskantar tsatstsauran hukunci a
dalilin hakan. Akanta dake harɗe kan kujerar da bayan shi
babu wani mahaluki daya iya kwatanta zama kanta ya fara
sauke ƙasaittun idanunsa. Dai-dai itama ta ɗago nata
sakamakon jin takun sawayensa da zubewar hadiman. Cikin
ido suka kalla juna, hakan yay matuƙar tsikarar zuciyar Iffah
da abinda take faman hasashe da neman tabbaci a kwanakin
nan ya tabbata ɗin yau a idanunta. Dan tabbas shigar jikinsa
ta yanzu ta sake tabbatar mata da waccan fuskar... Shine ya
fara janye nasa kausasan idanun batare data iya tsinto komai
a cikinsu ba. Kamewa da gagara fassara abinda ke kan
fuskarsa kuma ya taka rawar gani wajen ɓoye ainahinsa. Sai
ma kallonsa da ya maida kan ƙaton agogon dake kafe a falon
cike da basarwa kai kace bai ganta bane. Ita madai basar da
shi ɗin tayi kamar ma bata san da fitowar tasa ba, sai
zuciyarta dake faman kai kawo a ƙirjinta cikin sauri-sauri. So
take ta gaskata shi ɗinne kota ƙaryata amma zuciyarta taƙi
bata haɗin kan karkata akan ko ɗaya a cikinsu. Sai ma neman
jefata a ruɗani takeyi......
*_BARRISTER_*
Duk yanda Barrister yaso sanin suwaye su? Mi kuma yay
musu basu saurareshi ba suka turasa cikin jibgegiyar baƙar
motarsu, yayinda ɗaya daga cikinsu kuma ya shiga motar
Barrister ɗin ya fiddo komai na ciki a cikin wata ƙatuwar jakka
suka bar wajen.. Suna ɗan matsawa a wajen wani abu mai
masifar ƙara ya ziyarci kunnuwan kowa. A take aka fara
gudun ceton rai dan duk wanda yasan bomb yasan shine a
yanzun ma.
“Innalillahi wa inna'illaihirraji'un”. Barrister ya faɗa idonsa
nabin motarsa da tai sama ta shiga dawowa pieces ƙasa
alamar dai bomb ɗin daga cikinta ya tashi. Duk da ya firgita
da mutanen yay jarumtar dubansu fuska a dake. “Ku su
waye? Miyasa kuka aikata min haka?”.
Babu wanda ya tanka masa a cikinsu, kamarma basu jisa
ba sukayi. Hakan sai ya ƙara tada hankalin Barrister, dan ya
fahimci ya shiga hannun mugayen mutanen nan kenan.
Yunƙurowa yayi da nufin ƙara magana suka jefa masa
handkherciff a fuska, daga haka bai sake sanin inda yake ba
sai buɗe idanu yay ya gansa a wani ɗaki da bai san inane ba...
Gaba ɗaya jihar Hubab da ƙasar Ruman a rikice ake akan
tashin wannan bomb, dan abune da bai taɓa faruwa da