Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dauɗar Gora Complete Hausa Novel by Bilyn Abdull Ce

Author :  Bilyn Abdull ce Category :  African Stories & Novels

Chapter   18 / 34

51K to 54K   out of 100K words

Malikat Haseena ta saki da kauda kanta. “Ni
kuma ba hakan kawai na hanga ba”.
Idanu Daneen Ammarah ta tsura mata batare da tace komai
ba. Malikat Haseena datai shiru itama kamar bazata cigaba
da cewa wani abu ba ta nisa. “A nazarin danai musu tamkar
akwai sanayya tsakaninsu kafin haɗuwar jiya”.
“Sanayya kuma Mammah? Idan da na fahimta sun san
juna kenan kike nufi?”.
“Haka”.
“Haba Mammah a ina to zasu san juna? Karki manta Abni ba
fita yake ba. Ƙaddara ma yana fita, wanda ke zagaye da tsaro
ta ina sani da mu'amula mai ƙarfi irin wadda kike hasashe
zasu ƙullu tsakaninsa da yarinya mai matsayinta. Karfa ki
manta ko'a cikin gidan nan ba kowa ya san fuskarsa ba balle
talakawan dake rayuwa a waje”.
“Wannan shine abinda ya ɗaure kaina nima. Sai dai
azuciyata na faɗamin akwai abinda yake ba daidai ba da
saninmu tabbas”.
“Kamar mi kenan Mammah?”.
“Nima amsar da nake nema kenan”.
Babu wanda ya iya sake cewa komai sukai shiru kowa da
abinda yake tattaunawa da zuciyarsa......
★★..... ★★.... ★★.....


Alhamdullah Barrister yaci nasarar gano inda su Babiy suke,
sai dai ba'a jiya ba kamar yanda ya faɗama su kaka har suka
zauna zaman jira sai da sukaga yamma tayi babu wani bayani
sannan suka haƙura suka wuce. Bai ɓata lokaci ba kuwa yay
kiran Abu Zainab ya sanar masa. Shima cike da zumuɗi ya nufi
gidan Babiy domin sanar ma Kaka. Sai dai kuma ya tarar yaje
masallaci kasancewar lokacin sallar zuhur yayi. Dole ya
shanye zumuɗin nasa shima ya tafi masallacin. Bayan an idar
da salla ƙofar masallaci ya fito ya tsaya yana kallon duk mai
fitowa.
Daga can ciki kuwa Kaka dake a cikin mutanen da suke
sahun farko sai a karshe suka sami damar miƙewa suma. Ya
ɗaga zai miƙe mutumin dake a kusa da shi ya bashi hannu
alamar suyi musabaha. Babu musu ya miƙa masa nasa yana
ɗan murmushi. Mutumin da shima murmushin yake ya tsaida
kwayoyin idanunsa a tsakkiyar na kaka, hakan yasa shima
Kaka cigaba da kallonsa dan ya fahimci akwai wani abu....
“Nasan kasan girman alkairi tsoho. To karka yarda ka
maida shi da sharri ga wanda yay maka. Dan haka ina baka
shawarar hana waɗan can mutanen biyu cigaba da shiga
abinda bai shafesu ba. Inba hakaba kuwa kai da su kuna gab
da zuwa inda surukinka da jikanka suke yanzu. Na Barka
lafiya”.
Mutumin ya kare maganar da zare hanunsa a cikin na Kaka
ya miƙe. Da kallo kawai kaka ya bisa harya ɓacema ganinsa.
Kafin yaja numfashi ya fesar tare da miƙewa zuciyarsa na
faman kaikawo tamkar zata fito. Koda ya fito da Abu Zainab
ya fara cin karo, ya tsira masa ido na wasu sakanni kafin ya
karasa garesa. Abu Zainab da shima ya hangosa cike da
zumuɗi ya tarbesa, ko gaisawa basuyi ba ya rankwafa dai-dai
kunnen kaka ya gwargwaɗa masa saƙon Barrister...
Murmushi kaka ya saki na ƙarfin hali, sai kuma ya jinjina
kansa da ambaton Alhamdullah a hankali. Abu Zainab da bai
gama fahimtar yanayin kakan ba cike da zumuɗi yace, “Baba
muje Barrister na jiranmu yanzu haka”.
Idanu kaka ya tsira masa tamkar zai ce a'a. zuciyarsa na
tuna masa girman alkairinsu garesa, tabbas bazai so saka
rayuwarsu a gariri su da iyalansu ba, idan ma yaga wani zai
zama sanadi zai bada karfinsa wajen karesu. Kalaman wancan
mutumin sun sake tabbatar masa akwai lauje cikin naɗi game
da kama su Babiy, hakama ƙin amsar Ummu a asibiti waccan
ranar. Hakan na nufin kuma duk kaikawon da suke ana biye
da su.......
“Baba kaga gashi ma yana kirana”.
Abu Zainab ya katse masa tunani. Ɓoyayyar ajiyar zuciya ya
sauke, yanda Abu Zainab ya ƙagu ya sashi fahimtar bashi da
isasshen lokacin tunani, zai bari sai ya samu nutsuwa ya bi
hanyar data dace badan masu kurarin sunfi ƙarfinsa ba. Sai
dan kawai baya son bin wata hanya daya jima da kyamatarta
a ransa, amma da su ko inda yake basu isa tunkara ba balle
jininsa.....


*_BARRISTER_*

Barrister Abdallah Aas ya ajiye wayar daya janye manne a
kunensa alamar waya ya gama. Kallonsa ya maida ga
sakatarensa dake ƙoƙarin ficewa saboda ganin yana waya.
“Suhail”.
Ya dakatar da shi ta hanyar kiran sunansa. Amsawa yay tare
da juyowa cikin girmamawa.
“Akwai damuwa ne?”.
“A'a Sir. Wani mutum ne dai ke buƙatar ganinka. Nayi
ƙoƙarin fahimtar da shi kanada uziri amma bai saurareni ba”.
Ɗan jimm yay kamar mai nazari, sai kuma ya huro iska da
kaɗa kai. “Okay ba damuwa shigo da shi kawai na gansa kona
minti goma ne dan zan fita ne”.
“Okay Sir”.

A yanayin da mutumin ya shigo ya saka Barrister tsira
masa ido, yakai zaune tun kan a bashi izini yana cigaba da bin
office ɗin da kallo tamkar mai irge kayan cikinsa. Sai kuma ya
juya ga Barrister tamkar wanda aka bama umarni ya miƙa
masa hannu. Kamar Barrister zai noƙe sai kuma ya miƙa masa
shima.
“Am sorry Barrister nasan baka Sanni ba. Na kuma shigo
kai tsaye batare da neman damarka ba” ya saki murmushi da
cigaba da maganarsa batare da ya bama Barrister ɗin damar
cewa wani abu ba. “Kar sani na ya zama damuwar abinda ya
kamata ka sani dangane da ni, mafi muhimmanci kawai kasan
miya kawo ni”. Ya kai ƙarshen maganar da ɗakko jakkar daya
shigo da ita ya ajiye saman tebirin Barrister.
“Waɗan nan kuɗaɗene da zasu isheka tsahon wani lokaci
kana amfana, ina son ka manta da zancen aikin da surikinka
ya kawo maka, idan son samu ne ma daga yau ka dakatar da
shi shiga abinda bai shafesa ba”.
“Duk akan wane dalili zanyi hakan?” Barrister da ɓacin
ransa ke yunkurowa ya faɗa cikin son dannewa.
“Ba dalilin ya kamata ka sani ba. Ƙin bin shawarar ne
matsalarka Barrister”.
Cikin bayyanar fushin Barrister gaba ɗaya akan fuska ya
yunkuro zaiyi magana ring ɗin wayarsa ya dakatar da shi
hakan. Atare suka kalli wayar sannan suka kalla juna. Wayar
mutumin ya nuna da sakin murmushi, “Bismillah”.
Barrister yaja ƙaramin tsaki da hararsa tare da kai hannu
akan wayar dake cigaba da ɓurari.........✍️

27



.......“Assalamu alaikum”.
Ya faɗa a daƙile saboda rashin sanin wanene. A maimakon
amsa masa sallamarsa aka ambaci sunansa tamkar a lokacin
ake raɗa masa shi.
“Barrister Abdallah Ibn Adam Aas! Kar kayi taurin kai, dan
zaka iya rasa kanka dama waɗan da kake yunƙurin
taimakawar. Ni umarni nake baka ba shawara ba kamar shi,
domin hatta iyalanka ba zasu tsira ba daga tarko na”..
Ɗan zabura Barrister yay tamkar wanda cinnaka ya ciza.
Daga can aka cigaba da magana cike da isa. “Suna hanyar
zuwa gareka, ya rage naka tun yanzu ka raba gari da su, ka
kuma gargaɗi surikinka. Na barka lafiya”. Yana kokarin yin
magana ƙitt aka yanke kiran. Ciro wayar yay da sauri daga
kunensa, ganin ta yanke yay ƙoƙarin kiran number...
Mutumin dake tare da shi ya miƙe yana dariya. “Barrister
shawara karma ka wahal da kanka dan basake samunsa zakai
ba har abada in har a wannan layin ne. Na barka lafiya”.
Da ƙyar Barrister ya kwato numfashinsa gab da mutumin zai
fice. Cikin jarumtarsa ya dakatar da shi a ɗan tsawace. “Ni
kurari ko gizago basa firgitani ai. Dawowa ka ɗauka trash bag
ɗinka zai fi maka alkairi fiye daka barta anan ta zamewa
rayuwarka BAYA DA ƘURA. wannan shawara ce”.
Har cikin rai maganganun Barrister sun sokesa. Amma
kasancewar sa ɗan hannu a iya bariki sai ya saki murmushi.
Batare da yace komai ba yay salute ɗin Barrister dake masa
kallon ƙasƙanci yay ficewarsa.
Baya Kaka da Abu Zainab dake yunƙurin shigowa office ɗin
suka ja dan kaɗan ya rage suyi gware. Suna masa sallama bai
ko amsa su ba yay musu kallon ƙasa da sama yay wucewarsa.
Basu damu ba, dan daga ganinsa kaga babban mutum.
Barrister da aka bari da juyawar kai ya amsa musu sallama
cike da son danne ɓacin ran dake a fuskarsa. Sun gaisa da
mutuntawa kamar yanda suka saba. Fuskar Kaka da ɗan
murmushi ya ce, “Ashe kuma an dace da sanin inda suke?”.
Murmushin ƙarfin hali Barrister yayi da jinjina kansa, ya
jawo wani file dake gefensa. “Nima banyi tunanin abin zai zo
mana da sauƙi haka ba Baba. Amma Alhamdullah addu'a bata
faɗuwa ƙasa banza. Inaga muyi azamar zuwa ma kar'a samu
wani tazgaro kuma kasan halin ƙasar tamu”.
Daga Kaka har Abu Zainab sunyi na'am da hakan. Duk suka
miƙe babu ɓata lokaci suka fice kowa da abinda ke masa kai
kawo a cikin rai musamman Kaka da Barrister.....

*_MASARAUTA. (MALIKAT BUSHIRAT_*

Cikin zumuɗin son jin yaya haɗuwar Shahan-shan da
Zawjata-almilk ta kasance a jiya Malikat Bushirat tai shirin
ziyartar sashen Malikat Haseena a yau. A ƴan rakkiyarta har
da Jasrah dake son sake duba jikin Iffah. Tuni ƴan leƙen asirin
cikin hadimai sun kwasa zuwa sassan iyayen gijinsu kuwa.
Dan wannan ya zama kamar al'ada a masarautar kowane ɗan
leƙen asiri kan kai wa uwargijiyarsa ko uban gidansa duk wani
motsin wani babba a daular. Ta wannan hanyar ne a mafi
yawan lokuta abubuwa ke yaɗuwa kunnen duk wani mai faɗa
aji na gidan musamman abinda ya kasance na sirri.
Malikat Bushirat ta samu tarba ta girmamawa ga surukar
tasu a fadarta. Tuni hadimai sun cika gabansu da kayan motsa
baki. Kasancewar ganawar ta shafi wani yanki na ɓoyayyen
sirrinsu duk wani hadimi aka sallamesa. Katafaren falon ya
kasance daga Malikat Haseena sai Malikat Bushirat da Jasrah
sai Daneen Ammarah. Tattaunawar ta jasu tsahon lokaci kafin
Malikat Haseena ta aika amintacciyar hadimarta Banou kiran
Iffah....

★Sam Iffah dake cikin wani yanayi na tsananin faɗuwar
gaba da sanyin gaɓɓai sakamakon mummunan mafarkin da
tai akan su Babiy a barcin zuhur daya figeta bata san mi ake
ba saboda bata fita ko'inaba yau iyakarta ɗakinta. Yanzu
hakama da aka idar da sallar la'asar tana tsumayen Daneen
Ammarah ne kamar yanda ta saba, dan duk yinin yau ma
basu haɗu ba tun bayan idar da sallar asuba dai data fita ta
gaishesu kamar yanda ta saba ita da Malikat Haseena.
Hadimai dai sun kawo abinci tare da saƙon gaisuwa daga
Daneen Ammarah ɗin ɗazun da rana akan cewar tana nan
tafe. Malikat Haseenah ma kullum da kanta takan zo ta duba
ta, kasancewarta tsohuwa mai dattako da iya zama da
mutane tuni ta shige zuciyar Iffah itama, dan duk da bata da
sakewa da yawan fara'a har dan jan Iffah take da hira.
Sallayar datai sallar ta linke har yanzu jikinta a sanyaye ga
damuwa fal ranta akan iyayenta, acan ƙasan zuciyarta takeji
akwai wani mummunan abu dake sake tunkarota koma ya
riga ya iso garetan ta hanyar iyayenta batare data sani ba.
Yanayin ɗan zafi da ake ya sata yaye mayafin abayan data
naɗe kanta da shi ta ajiye, ɗaurarren dogon baƙin gashinta
dake reto a tsakkiya ya bayyana. Abincin da aka shirya mata
tun ɗazun da bata ci ba ta nufa, ta bubbuɗe taga komai,
batama jin cin komai har yanzun, dan haka ta tsiyayyi madara
kawai da shanta tamkar al'adar ƴan ƙasar ne. Tana buƙatar
fara canja kayanta zuwa marasa nauyi, dan haka ta ajiye kofin
madarar a bedside drawer. Toilet ta fara shiga ta fito sannan
ta shirya cikin wata yar yololuwar rigar mara nauyi mai zubin
shimi. Iyakar rigar gwiwar ta ne, gata kalar fari da adon
jajayen firanni. Ta matuƙar haskata da fidda ƙuruciyarta
tamkar ƴar budurwar balarabiya. Turarrukan da Daneen
Ammarah ta tule mata ta zaɓa kusan kala uku ta fesama
jikinta. Cikin nutsatstsen takunta ta dawo saman gadon tana
mai kallon fatar hanunta dake jajir saboda saɓar da tayi.
“ALLAH dai ya isana wlhy” ta faɗa cike da halin tsiwarta tana
jan bargo ta rufa iya cinyoyinta bayan ta jingina jikinta da
fuskar gadon. Littafin da take rubuce-rubucenta na duk
abinda ya faru ta ɗauka ta buɗe ko zata ji sassaucin tunane-
tunen da zuciyarta ke mata marasa daɗi akan iyayenta, dan
sam mafarkin nan yaƙi barin ranta koda na sakan ɗaya... A
zahiri rubutun tai shirin fawara, dan yanda ta tsurama littafin
ido da riƙe biron da nutsuwa matuƙa zai saka ka hasashen
haka. Sai dai sam ko kalma biyu ta kasa rubutawa tamkar ma
an mata wankin ƙwaƙwalwa komai ya gudu, hasalima nisan
da tai a tunani yasa bibbiyu take ganin rubutun baya da
tayi....
Knoking ƙofar da akai ya sata jan numfashi ta fesar, sai
kuma taja mayafin dake gefenta ta yane jikinta har saman
kanta tare da amsawa da “Yes! Kowaye ya shigo”.
A ɗarare hadima banou ta shigo, tsananin tsoron Iffah
shimfiɗe akan fuskarta ya kasa boyuwa. Daga bakin ƙofar ta
zube muryarta na ɗan rawa kamar yanda jikinta ke tsuma.
“Amincin ALLAH da lafiya su tabbata ga Zawjata-almilk”.
Harara Iffah dake kallonta ta zabga mata. “Ina tare da
masu lashe kurwar mutane irinku lafiyar zata tabbata a
gareni? mtsoww!! Malama faɗi abinda ya kawoki bana son
gulma”.
Ƙasa Banou ta sakeyi da kanta muryarta na rawa, dan
harga ALLAH tana shakkar wannan yarinya da ko magana
gatsau take yinta babu alamar shakku tattare da ita. “Uhm
uhm dama Malikat ce take buƙatar ganinki”.
Hannu kawai Iffah ta ɗaga mata, dan har cikin rai ta
tsani matar nan matuka. Sai da ta miƙe zata buɗe ƙofa
sannan tai magana a gadarance. “Ki jirani a ƙofa, saura kuma
kafin na fito ki lashe mun hadimai azzalumar bamza”.
Da rawar jiki data harshe Banou tace, “Hakan bazata faru
ba ranki ya daɗe”.
“Uhm munafuka kamar gaske”.
Iffah ta faɗa tana sauka a gadon cikin mita......

★Tunda suka shigo ko sau ɗaya Iffah bata iya ɗaga kai ta
kalla ko ɗaya a cikinsu ba. Saɓanin su da duk suka zuba mata
ido cike da jin ƙaunarta a rayukansu. Cike da nutsuwarta ta
karasa garesu, maimakon kujera da duk suke zaune sai ta kai
ƙasan lallausan dardumar...
“Haba Ibnati tashi ki hau sama mana”.
Jasrah tai yunƙurin dakatar da ita. Kai Iffah ta girgiza da ɗan
murmushi a fuskarta, “A'a nanma ya isa”. Cike da sha'awa da
jin daɗi duk suke dubanta. Ta juya ta gaishe da Malikat
Haseena, da fara'a da kulawa ta amsa mata tana mai sanya
mata albarka. Cikin jin daɗi ta juya gasu Malikat Bushirat ta
gaidasu suma. Suma da kulawar suka amsa mata, dan duk
ƙasaita da jin kan Malikat Bushirat sai ta tsinci kanta da
murmushi da sauƙaƙawa akan yarinyar saboda kwarjini da tai
mata. Shiru na wasu ƴan sakkani ya biyo baya, kafin Daneen
Ammarah ta katse shirun ta hanyar kiran sunan Iffah.
Ta amsa mata da girmamawa sai dai bata iya ta ɗago
kanta ba. Daneen Ammarah ta sake kiran sunanta da faɗin,
“Kinga ɗago ki kallemu”. Da ƙyar ta iya dauriyar bin
umarninta. Dan duk rashin jin Iffah tana da wani hali na
girmama duk mai nuna mata ƙauna koda bai cancanta ga
sauran mutane ba. “Ibnati nasan nan zuwa yanzu duk kin
sammu ko?”.
“Eh Mamy”.
“Amma baki san matsayinmu ba?”.
Nanma tace “Eh Mamy”.
“To Alhamdullah yau duk zaki sani. Ina son ki bani dukkan
hankalinki nan ki kuma saurare ni yanda ya kamata”.
Ta jin jina mata kai.
“Kamar yanda nasan kikaji Mamma a garemu mahaifiya ce,
itace ta haifi Hama (Suruki) ɗin ki, da ni dama wasu biyu da
zaki sani anan gaba sai dai ɗaya ya rasu”.
“ALLAH ya gafarta masa”.
Ta faɗa cike da rauni. A tare suka amsa mata da Amin.
Daneen Ammarah ta ciga da faɗin, “Wannan da kike jin ana
kira Malikat Bushirat itace Hamah (Suruka) ɗinki data haifi
Shahan-shan na yanzu kuma mijinki da yazo nan jiya......”
A razane Iffan ta waro idanu ƙirjinta na wani irin harbawa
kamar zai wantsalo. Cikin subutar baki ta ce, “Shahan-shan!
Na jiy.....” sai kuma tai shiru ta haɗiye sauran maganar
saboda tuna a inda take...
“Kin sanshi ne kafin jiya?”.
Malikat Haseena dake nazartarta ta jeho mata tambayar a
bazata. Da sauri Iffah da zufa ta jiƙema dukkan jiki, ta girgiza
kanta. Kasancewar ta gwanar wayo tai saurin faɗin, “Mamma
ina mamaki ne dai, ban zaci ganin Shahan-shan ɗin nada
sauƙi kamar haka ba”.
Kusan a tare suka saki murmushi saboda hango tsantsar
ƙuruciya a maganar tata. Sai dai malikat Haseena tsaf ta
gama karantar Iffah waskewa tai. Amma kasancewar ta
tsohuwa mai dattako sai ta dake itama ta shiga jerin ƴan
murmushin.. Daneen Ammarah ta cigaba da faɗin, “Wannan
ƙanwa ce ga Malikat Bushirat, Khaalah (Aunt) ga mijinki. Na
baki ne a dunƙule iyamu da muke anan saboda muhimmancin
abinda zakiji a yanzu”.
Kai Iffah ta jinjina mata da alamun gamsuwa. Jasrah ta
cigaba daga inda Daneen Ammarah ta tsaya.
“Ibnati dalilin miki wannan dogon sharhin a kammu
shine fara aikinki matsayin Zawjata-almilk a wannan
masarauta. Alhamdullah tunda kinji sauƙi zaki koma sashenki
kamar sauran Zawjata-almilk guda biyu, sai dai zaki samu
horo daga wasu amintattunmu matsayinki na Zawjata-almilk.
Mun zaɓeki ne saboda nutsuwarki da tarbiyyarki. Basai mun
zaman sharhi akan abinda ya faru ba a baya kasancewar
kema ƴar kasa ce kin san komai na dangane da mutuwar
matan Shahan-shan da suka gabata.”
Iffah ta haɗiye kududun baƙin cikin daya tokare mata
maƙoshi akan famin rasa ƴan uwanta da tai da ƙyar ta jinjina
kanta.
Malikat Bushirat ta amshe da cigaba da faɗin, “Ibnati
kece zaki zama mutum ta farko a rayuwa da zan nema
alfarma a gareta, hakan kuma ta faru ne saboda jinki da nake
a cikin raina da kallon da duk muke miki anan matsayin wani
haske da insha ALLAH zai haska mana duhun da muke ciki.
Muna son ki shiga jikin Saiful-malik domin binciko mana
ainahin minene matsalar, saboda dukkan waɗan can matan
da aka rasa daga kaisu turakarsa ne ake samun matsalar.
Mun miki alƙawarin baki dukkan kariyar da bazamu bari ki
cutu ba....”
(Kariyar UBANGIJINA zata kasance tare da Ni). Iffah ta
ayyana a zuciyarta.
Malikat Haseena ce ta cigaba da faɗin, “Zamu fara ne da
matakai da hanyoyin dinga haɗuwarku daga nan zuwa wani
lokaci, fatanmu ki zama mai saka ido a dukkan wani motsinsa,
a karan kansa, da duk wasu wanda zasu mu'amulancesa har a
cikin hadimai. Kiyi takan tsantsan, dan mutum ne shi mai
wayo matuƙa, sannan mai wahalar sha'ani da fahimta. Ba'a
gane mi yake nufi ko minene a ransa akan fuskarsa, kar ki
yarda ki bashi wata damar da zai iya zargi a kanki. Fatanmu
dai ki zama jaruma a dukkan al'amuransa dama na kowa dake
a wannan masarauta, duk abinda kikaci karo da shi ba dai-dai
ba kiyi maza ki sanar da ɗaya daga

18 / 34