Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dauɗar Gora Complete Hausa Novel by Bilyn Abdull Ce

Author :  Bilyn Abdull ce Category :  African Stories & Novels

Chapter   27 / 34

78K to 81K   out of 100K words

da
ayanzu take ƙoƙarin janyewa a nasa ba, bai kuma janye
takobin da kallonta kawai zai iya tada tsigar jikin mutum daga
wuyanta ba ya sata ɗan shammatarsa ta goce makoshinta da
ga tsinin takobin daya ɗaura matan, sai dai a yanda ya wani
lumshe idanu da sauke takobin yasata tabbatar da ya bartane
kawai. Gaba tai yunƙurin yi, da yima hadiman da suka iso
wajen yanzu nan kallon gefen ido a kaikaice ta saki wani
lallausan murmushi mai ma'anoni da yawa a zahiri. A kuma
ƙasan ranta ko ɗar babu.
Duk wannan abun Miran Arshaan fa na tsaye a wajen ne
yana ƙarema Iffah kallo a kaikaice cike da mamakin ƙarfin
halin yarinyar, dan tunda yake a wannan masarauta bayan shi
babu wani mahaluki daya taɓa zuwa wannan wajen sai
Shahan-shan da hadiman dake kula da wajen. Amma a yau
sai ga yarinya ƙarama da babu alamar tsoro a cikin idanunta a
wajen. Sai kuma yanda tayi kamar bata gansa ba yay matuƙar
ƙona masa rai amma ya dake dan yana buƙatar ganin ƙarshen
wasan....

Wajen duk da filine na karshen ginin (rufinsa kenan) ya
ƙawatu da abubuwa kashi-kashi na more rayuwa. Ga wani
ƙamashin furanni da aka ƙawata waje dana fresh air masu
narkar da jinin mutum da sanya kasala. Da sauri ɗaya daga
cikin hadiman da suka shigo wajen da abubuwa a hanunsu ya
ƙarasa ga Tajwar Eshaan dake murza goshinsa kansa a ɗan
rissine ƙasa. A gabansa ya dirƙushe yana mai miƙa masa
kufan takobin hanunsa da babu tantama anyi adon jikinsa da
gold ne. Takobin ya ɗaura masa kan dogon trayn da kufan
yake. Hadimin ya miƙe da sauri yana ja da baya. Na biyu ya
iso da sauri shima, sai dai saɓanin na farko shi bayansa ya
koma yana warware farar rigar hanunsa mai maɗauri.
Hannayensa ya ware da ɗan kai idanunsa inda Iffah ke tsaye
tana tsiyaya shayi a karamin kofi, ya wani irin ɗage kafaɗu da
juya rigar cike da salo ta rufe jikinsa tare da zarge igiyoyin
biyu akan damammen cikinsa. Hadimi na uku ya iso shima ya
durƙushe hanunsa dauke da ƙaramin farin towel. Nan ma dai
ɗauka yay ya rataya a kafaɗa bayan ya ɗan tsane zufan daya
taru masa a gefen wuya da goshi alamar dai jininsa a tsinke
yake a lokacin.
A yanda hadiman suka sani daga haka hanyar da zata
maidashi bedroom ɗin daya kwana yake bi, acan zai samu
shayinsa na ƙa'ida mai dafawa ta kai, bayan yasha zai shiga
wanka kafin ya fito inda aka shirya masa karin kummalo. Sai
dai saɓanin yau yana ɗaga ƙafa domin barin wajen bayan ya
dubi Aamin nasa ya rissinar da kai kaɗan na alamar sallama
da girmamawa a garesa Iffah dake faman baza ƙamshin da ga
Shahan-shan ɗin kawai suka sansa ta isowa wajen ɗauke da
ƙaramin kofin shayi dake tururi fari tar na glass.
Da sauri duk hadiman suka juya bayansu, dan kallon
abinda zai iya biyo bayan wanda suka gani ɗin haramunne a
garesu. Iffah dake taku a nutse kamar wata hawainiya
takalmanta da ba wani tsinin kirkine da su ba na bada sautin
isar da saƙon tahowar tata ta iso gabansa.. Ƙin yarda tai koda
wasa su haɗa idanu. Idanunsa da kallonsu ke canjawa ya
sauke akan kofin shayin da take miƙo masan. Shiru babu
alamar zai amsa, har hanunta na ƙoƙarin fara yin dayi. Sai da
ta fara ambatar sunan ALLAH kafin ta ɗago fuskarta a dake,
“Ƙin sha na nufin rauni da muhimmancin Zawjata-almilk a
gareka. Ko kuwa cigaba da tabbatarma duniya abinda suka
sani shine gaskiya ranka ya daɗe”.
Yanda lips ɗinta da suka sha pink lipstick ke motsawa ya
zubama ido, sai dai maimakon mata sharhi akan zancenta
kamar yanda taso yau gefe ya ɗan maida kansa da amsar
shayin kamar wanda ya shiga halin tarkon kasala. Karan farko
ta sakar masa wani lallausan murmushi da faɗin, “Thanks”.
Basarwa yay ta hanyar ɗan duban gefensa a takaice ya
furta,
“Aami”.
Da sauri Iffah ta duba wajen tamkar sai yanzu ne taga Miran
Arshaan ɗin, “Ya salam”. Ta faɗa a zahiri da nufarsa ta zube
ƙasa domin miƙa gaisuwa a garesa. Ya ɗan murmusa
zuciyarsa taf da al'ajabin wannan figigiyar yarinya da da
auren wuri yayi ya haifa wanda suka fita nesa ba kusa ba.
Cike da salonsa na fuska biyu ya amsa yana mai ƙare mata
kallo ta ƙasan ido. Iffah daba kula da hakan tai ba cike da
girmamawa ta miƙe da faɗin, “Uncle bara a baka shayin
kaima”.
“Zan so kasanwa na farko da zai ci abu daga hanunki
Ibnati”.
Jin daɗin kalamansa yasa Iffah sakin murmushi da ɗan
rissinawa ta furta, “Na gode Aam”. Shima dai shayin ta kawo
masa, nan ma yay mata godiya da sanya albarka yana ɗan
duban sashen da Tajwar yake tsaye dafe da ƙarfen da aka
zagaye wajen ta bakin ginin yake ya tsurama cikin masarautar
idanu yana ɗan kai shayin bakinsa tamkar bai san abinda ke
gudana a wajen ba. A hankali ya taka inda yake shima yana
shan nasa.
“Yanzu ne daular ruman ta tabbatar da samuwar Zawjata-
almilk”.
Sarai Tajwar Eshaan ya jisa. Amma halinsa na ƙasaita da
mafi yawan iyayen nasa suke ambato da girman kai yasa yay
tamkar baiji ɗin ba. Sai ma juyawa da yay bayan wasu sakkani
ya dubi Aamin nasa cikin tausasashiyar muryarsa mara
hayaniya da kamewa ya furta. “A huta gajiya”. Ya bar wajen.
Ga mamakin duk wanda ke'a wajen gaban Iffah dake ɗan
nisa da su ya isa. A bazata taji tattausan tafin hanunsa da yay
sanyi ƙalau sakamakon iskar wajen a cikin nata. Da sauri ta
rumtse idanu tana mai ambaton sunan ALLAH a zuciyarta da
ɗan dubamsa. Ba ita yake kallo ba, sai ma fara takawar da yay
wanda ya tilastata binsa tamkar raƙumi da akala. Batare da
sun luraba takun sawayensu na sauka da ɗagawa a tare
sakamakon shima tafiyar izza da ƙasaita irin na masu mulki
yasa baida garaje a tafiya tamkar wani mace. Anan ɗin ma dai
tana sanya ƙafarta na'ura ta sanar da ita wacece, haka shima.
Da sauri hadimin dake a ƙofar ya zube yana kwasar gaisuwa.
Hannu kawai ya ɗaga masa yay gaba abinsa har lokacin
hannunsa na cikin nata ya riƙe gam kamar wanda aka bama
amanar riƙon nata dan karta suɓuce......

★★..... ★★......

A ɓangaren Barrister kamar yanda mutanen can suka sanar
masa hakance ta faru. Sunyi amfani da kamannin da mutane
suka daɗe da sanin sunayi, wanda shine ma tushen
zamowarsu abokai, aikinsu kuma ya maidasu aminai. Sai dai
muryarsu ta banbanta da wasu abubuwa na ɗi'ar yau da
kullum. Akan wannan ne mutanen suka bashi training na dole
dalilin barazana da sukai masa akan iyalinsa dama kashe
Barrister Akeem ɗin da yake gudun cin amana. Bayan
kimtsawarsa da shiga irin ta Barrister Akeem da bashi wasu
bayanai akan aikin da zai musun suka bashi key ɗin motar
Barrister Akeem. Sun sanar masa dukkan motsinsa akan
idonsu ne, kuskure ɗaya akan ganganci fansar rayuwar ɗaya
daga cikin ahalinsa ne kona Barrister Akeem. Dole Barrister
ya kwantar da hankalinsa dan ya fahimci mutanen sunfi
ƙarfinsa, gashi koba komai yana buƙatar kuɓuta kodan tarin
ayyukan dake gabansa musamman akan aikin da ayanzu ya
tasa a gaba da alƙawarin cika alƙawari.
Su da kansu suka bashi address ɗin inda zaije, yayinda ya
hau titi kuma sai ya fahimci suna biye da shi a mashina wasu
a mota. Ya ɗan rumtse idanu da jan kakkauran numfashi ya
fesar lokacin da ya gama dai-daita parking a inda suka
umarcesa zuwa. Sai da ya karanto addu'ar neman ɗauki ga
ALLAH sannan ya fito riƙe da brefcase ɗin Barrister Akeem a
hannu. Ƙaton gidan ya ɗan ƙarema kallo kafin ya nufi inda
suke sanar masa yabi ta hanyar bluetooth ɗin kunnensa.
Kansa kawai yaɗan gyaɗa tamkar yana gabansu ya nufi
ƙofar......

★★★....... ★★.....

A cikin masarauta kam kusan ƙarfe tara da wasu mintuna
labari mai razanarwa na rashin ganin Sayeed Khairul-Bashar
(Aami gasu Miran Arshaan. Kaka kuma ga Tajwar Eshaan.
Shine wanda yay maganar jiya a ɗakin tattaunawa bayan
tashin Tajwar Eshaan). Zancen rashin ganin nasa ya fito ne
daga iyalansa, da farko an ɗauka yana cikin masarautar ne
dan sun tabbatar daga sallar asuba bai dawo ba. Amma ganin
har lokacin shigarsa gida ya wuce ƴaƴansa kuma sun bincika a
inda suke tunanin ganinsa amma babu shi sai suka fitar da
maganar. A take sojojin gidan masu bada tsaro dama hadimai
suka bazu lungu da saƙo amma babu alamar hakan. Anbi
diddigin wasu daga cikin cctv footage amma fitowarsa kawai
aka gani daga sashen nasa babu komawarsa. Hakan ya
matuƙar bama kowa mamaki da ɗaure kai. Dan ta ko'ina
masu tsaron ƙofofi sun tabbatar basuga fitarsaba sukam.
Gashi kuma an duba lungu da saƙo na gidan amma babu wata
alamarsa.....

★★......

Lokacin da labarin rashin ganin Sayeed Khairul-Bashar ya
iso kunnen Miran Jasim da Miran Arshaan dake tare kallon
juna sukai, sai kuma duk suka kauda kawuna suna murmushi.
Cikin son basar da zancen Miran Jasim ya cigaba da magana
kan zancen da Miran Arshaan ya kawo masa dangane da Iffah
“Lallai wannan yarinyar hatsabibiya ce, aini tun isowar
labarin kasancewarta raye a safiyar jiya al'amarin ta kemun
kai kawo. Zancen ka na yanzu kuma ya sake tabbatar min da
shirinta ta shigo masarautar nan.”
“To ai ta tara ta samu, dan dama mu irinta muke nema”.
Cewar Miran Arshaan yana ɗan murmushi.
Miran Jasim ya jinjina kai shima yana murmushin nasa na
izza da ƙasaita. “Hakane kam ta kawo kanta inda ake jirace da
zuwanta. Dan kam zamu sauke ƙuruciyar dake izata a tunanin
yin rawa da bazarta dake ɗawainiya da ita. Zata ƙarasa mana
aikinmu cikin sauƙi batare da ita kanta tasan a cikin tarko
take ba”.
Nan ma murmushi Miran Arshaan yay idonsa akan ɗan
uwan nasa. “Zuwa yaushe aikinmu zai fara?”.
Miran Jasim ya ɗan ɗage kafaɗa da taɓe baki. “Bazai
ɗauka lokaci ba. Sai dai muna bukatar wani point ne dole”.
“Wanda yake hannunmu fa?”.
Cewar Miran Arshaan da mamaki.
“Kai wannan bashi da wani ƙarfin da zaiyi tasiri ita a
gareta, duk da dai zai iya zama kamar share mana fage ne.
Zaren da nake ganin zamu ja ya kaimu gareta ɗaya ne, duk da
dai har yanzu babu wani shaida dangane da tsallakewarta
itama. Amma zamu yi amfani da damar, a wannan karonma
matarka ce zata mana aikin”.
“A wannan gaɓar fa ya kamata mu canja salo, Jasrah nada
matuƙar wayo, kar yawan bugar cikinta fa yasa ta fara
fahimtar wani abu”.
“Sai idan kaine ka bada ƙofar hakan Arshaan. Shekara nawa
muna amfani da itan bata fahimtaba sai yanzu. Ka dai kawai
ka kasance mai lura”.
Kai kawai Miran Arshaan ya jinjina batare daya ce komai
ba......

★★★......

Suna yin ɗan nesa kaɗan da masu tsaron ƙofar Iffah ta zare
hannunta da sauri tana ɓata fuska. Bai ko juyo ya kalleta ba
balle ya nuna alamar yasan mitayi yay gaba abinsa cikin
takunsa na nutsuwa da tsantsar ƙasaita tamkar baya son taka
kafafun nasa. Da ƴar hararar ƙasan ido ta bisa tana ƙunƙuni a
zuciyarta. (A haka dai kamar na wani limamin masallacin
Saudiyya, sai dai zuciyar ko kafiran farkon ƙarni haka suka
gansa suka barsa. Wanda duk zai iya salwantar da rai yay
barci lafiya babu ko ɗar ai ya dace ka kirasa da duk sunan
daya zo maka a rai dan ya cancanci haka). “Ni zanyi
maganinka da izinin ALLAH”. Ta faɗa a zahiri fuskarta na nuna
gaskiyar ɗacin da zuciyarta ke mata.......✍️
41
.......Shiru yay yana kallon inda ya saba iske shayinsa, wayam
babu komai, ya kai zaune a kujerar cikin alamun gajiyawa, a
gefe kuma tsaurin idon yarinyar da ƙarfin halinta na masa
kaikawo. Shan wannan shayin ya zame masa jiki da in bai sha
ɗin ba sam bama yajin daɗi, har ma yakan tsinta kansa a wani
yanayi da shi kaɗai ya barma kansa matsayin sirri duk da
abun na matuƙar damunsa. Har yayi yunƙurin dauriyar
sharewa tunda ya ɗan sha wani amma jin abinda yake gudun
na taso masa ya sashi furzar da zazzafar iska, babu shiri ya
danna alerm ɗin dake isar da saƙon kira ga amintattun
hadimansa. Cikin mintunan da basu wuce uku ba ko sai ga
ɗaya daga cikin su ya iso. A gabansa ya zube cikin tsumar jiki
yana mai ambaton...
“ALLAH ya ƙara ma Shugabana tsahon rai da ingantacciyar
lafiya, umarninka shine abin jirana”.
A zuciya ya amsa da Amin, a zahiri kam babu alamar zai
tanka kamarma bashi ya bukaci ganin hadimin ba. Tsahon
mintuna uku ƙasaita da izza irinta saraki na dawainiya da shi
kafin ya motsa lips ɗinsa a hankali cikin bada umarni.
“Miya hana a kawo shayi?”.
Hadimin ya ƙara ƙasa da kai jikinsa na ɗan rawa. “Umarni ne
daga Zawjata-almilk”.
(Umarni?!) Ya maimaita kalmar a zuciyarsa cikin ƙara
ƙanƙance idanunsa. (Shi kam ya zaiyi da yarinyar nan ne? Mai
kama da alja.....) Ya sake ayyanawa a zuciyarsa batare da ya
ƙarasa ba. Sai kuma ya kalla hadimin ya ɗauke kai. “Ina
buƙatar waninsa”.
Da sauri hadimin ya ƙara gurfana yana amsa masa ransa fal
mamaki da al'ajabin wannan sabon al'amari.
Fuskarsa gwanace wajen shanye sirrin dake bayyane,
amma yanda ya yatsinata da lumshe idanu a yanzu zai
tabbatar maka akwai magana tattare da shi.....

★★

Duk yanda taso nuna halin ko'in kula kan abinda ya farun
yanzu hakan ya gagara. Dan mayataccen ƙamshin turarensa
daya bambanta da wanda ta saka duk da suma nasa ɗinne ya
mugun addabarta. Takai hanunta kan hanci yafi sau biyar, sai
ta shinshina sai kuma ta janye tana laɓe baki. Hakan kuma bai
hana anjima ta sake maidawar ta shinshina. Daga ƙarshe da
taga abin na neman zama mata ɗan kaɗafi sai ta faɗa toilet ta
wanke hanun da sabulu, amma dan mayata yaƙi ya daina sai
da ta ɗauka ɗaya a cikin turarrukan datai amfani da su na
ɗakin tasa a hannun sannan ta daina ji.
Littafinta ta ɗauka domin cigaba da nazari, sai kuma ta
tsaya cak, wani tunani ne yazo mata a zuciya, dan haka ta
miƙe zaraf tana ɗaukar wayarta data gani tare da littafin
alamar duk ma wanda ya kawota tare da su ya kawotan.
Kamar yanda ta saba idan zasuyi magana tai dawnlording
sabon WhatsApp app, sai da ta daidaita komai sannan ta
lalubosa. Baya online gashi kuma tana buƙatar yau suyi
magana ne bawai saƙo take son ajiye masa ba. Sai hakan ya
sata jin babu daɗi har walwalarta ta ɓace. “Kona masa
flashing?”. Ta faɗa cikin sigar tambayar kanta. Kan ta daga
alamar gamsuwa, ta fito a watsap ɗin. A karo na farko tai
dailing number ɗin cikin shakku. Harta katse ba'a ɗaga ba,
damuwarta ta kara bayyana. Harta sake komawa watsap ɗin
ta fito ta sake danna kiran. A hankali ta sauke ajiyar zuciya
har ana iya jinta daga can. Tai sallama cikin yar muryarta
dake nuna zumuɗin jin an ɗaga, sai dai ba'a amsa mata ba
gashi kuma tanajin alamar ana saurarenta.
Danne takaicinta tai ta sake sallamar, nan ma shiru dai
babu ma alamar za'a amsa. Cikin suɓutar baki taja tsoki da
faɗin. “Nifa a rayuwa na tsani walakanci wlhy, shiyyasa komai
nafi yarda naima kaina. Yanzu haka wani ɗan iyan dake
ƙarƙashin sa ya ɗaga kiran kamar waccan ranar dana fara
kira, ƴan hana ruwa gudu kenan. Nima badan ƙaddarar
faɗawa hannun wannan Dodon ba da yanzu ina can ina
karatuna na jaridar a daina yarfani. Kai insha ALLAHU kafin
naga bayan a azzalumin nan ko sau ɗaya ne sai na hau kujerar
karagar mulkin nan nayi tankaɗe da rairaya cikin duk ƴan
jaridar ƙasar nan da jami'an tsaro aikin banza......”
Jin kamar sautin fitar murmushi a kunenta ya sata saurin
ciro wayar ta kalla. Dai-dai ana yanke wayar. Ido ta kwalalo
waje da dafe bakin. Sai kuma ta janye da faɗin, “Kai kamarfa
daga cikin wayar ne sautin nan ya fito wlhy. Kai ina”. Ta sake
faɗa tana ɗan wawwaigawa babu dai alamar wani a ɗakin sai
itan kaɗai. “Oh ni Iffah anya bakin nan nawa bazai yankani ba
wataran, yanzu hakama shine yazo ya amshi wayar inata zuba
ban sani ba”. Tai tagumi cikin takaicin kanta. Kamar kuma
wadda aka ɗan zabura sai ta sake ɗaukar wayar. Cikin sa'a tai
tozali da ganinsa online har an amsa mata sallamarta ma. Sai
kuma ta shiga kokwanton tayi magana ko kawai ta share.
Wata zuciya ta amsa mata da (Kema kin san bashi bane ya
ɗaga miki waya. Ki basar kawai). Da alama ta gamsu da
shawarar, dan haka ta saki murmushi da buɗe saƙon.
“Sorry kin kirani bana kusa yarona ya amsa”.
Amsar data samu kenan bayan sallamarta da aka amsa. Har
cikin rai taji daɗi, dan haka a fili ta furta “Alhamdullah dama
naji haka a jikina”. Shi kuma ta bashi amsa da “Babu damuwa
Sir”.
“kina da fahimta Shahrbano”.
“Bankai nan ba😣”.
Ta bashi amsa da emojin yamutse fuska. Sharewa yay da
faɗin,
“Ta samu ne?”.
Itama sai ta share da bashi amsa da.
“Kusan haka. Sai dai a wannan gaɓar lamarin akwai ban
tsoro Sir Ajmaal. Da gaske mutanen nan matsafa ne kuma
suna aiki da aljanu”.
“Ya arrahaman! Kamar ya? Har kimsa na tsorata fa”.
“Tab tunma kan na faɗa kenan. To kama cire dan wlhy ba
aljanu ba ko bataliyar ifiritai ce sai naga bayan mutumin nan.
Wai fa jiya da dare nabar sashen nasa na koma inda sukace
nawa kawai yau na wayi gari na ganni an sake maidoni
sashen Dodon nan. Ɗakin dana kwana kuwa duk da
haɗuwarsa na rantse maka a harmutse kamar anci dambe”.
“Dambe fa?”.
Ya share zancen farko ya amsa na ƙarshe.
“Wlhy kuwa Sir! Sai dai fa ni wannan bai damenba. So nake
nasan ta yaya aka ɗakkoni aka maido ni inda ba nan na
kwanta ba”.
“Kina da gaskiya dan akwai alamar tambaya kam.
Amma ke yanzu wane mataki kika ɗauka?”.
“Komai banyiba har yanzu, nadai fara bincika irin kamshin
da naji jikina nayi, inma shine ya aika aljanunsa suka ɗakkoni
dan ya kashe ni”.
“🤭”.
Ya bata amsa da emojin rufe baki alamar tare dariya.
“😞Bafa abin dariya bane wannan, abin a dubane. Idan
kuma aka halakani kafin ƙwato muku ƴancinku ku kukayi
asara Sir Ajmaal”.
“Eh gaskiya hakane kuma ranki ya daɗe. Yanzu dai ƙarasa
bani labarin dan in san ina zan kama. Saboda na gama shirye-
shiryen buɗe wani sashe na shiri na musamman akan wannan
case ɗin, sai dai komai zai kasance cikin hikima”.
“Aiko da naji daɗi Sir, dan gara kam a fara kafin ma na
mutu na dinga ji. Dama inason maka

27 / 34