Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dauɗar Gora Complete Hausa Novel by Bilyn Abdull Ce

Author :  Bilyn Abdull ce Category :  African Stories & Novels

Chapter   31 / 34

90K to 93K   out of 100K words

zuwan
wasu baƙin. Damar shigo da su ya bada dan yasan da
zuwansu, daga haka ya maida hankalinsa kan Barrister.
Barrister yayi matuƙar mamakin ganin baƙin, sai dai ya
danne hakan dalilin kallon da suke masa matsayin Barrister
Akeem. Gaisuwa sukai ta mutunta juna, har suna tsokanarsa
da cewa shine idonsu na gari. Murmushi yayi yana rissinar da
kai alamar girmamawa. “Kar kuji komai ranka ya daɗe, a
komai muna tare da ku kuma zamu kare mutuncin ku”.
Sosai suka nuna jin daɗi da zancensa. Nan suka shiga
kwarzantashi. Shi dai nasa murmushi ne a zahiri, a kasan rai
kuma yana matuƙar mamakin abokinsa da ɓoyayyun
ayyukansa. Dan bai taɓa tunanin Barrister Akeem zai iya irin
waɗan nan ayyuka ba.....
“Barriter ina alkawarin mu?”.
Sayeed Faizul-Anwar ya katse masa tunani. Ajiyar zuciya yaja
a ɓoye, sai kuma ya muskuta yana murmushi da taɓa bag ɗin
daya shigo da ita. “Ranka ya daɗe komai yazo hannu fiye ma
da yanda kuke buƙata. Sai dai kafin mukai ga nan ina son
nace wani abu saboda wasu dalilai”.
“Faɗi kanka tsaye Barrister baka da damuwa akan
hakan”.
“Nagode ranka ya daɗe. Bawani abu bane mai girma akan
dai shi wannan case ɗinne. Komai dai gashi na gani anan
kuma na tattaro, sai dai yanda aka bani aikin a dunƙule ina
ganin ya kamata nace wani abu duk da dai naga komai a
kansa, amma saboda nasan inda duk ya kamata na toshe a
ramukan da zasu iya yunƙurin buɗewa koma su buɗe ɗin yasa
nake son bada shawara bisa wani hangena”.
Shiru kamar bazasu ce komaiba. Sai dai sun maida
dubansu ga Sayeed Faizul-Anwar, kai ya gyaɗa musu alamar
tabbatar da babu matsala, dan haka kusan a tare suka sauke
numfashi, kafin ɗaya a ciki ya shiga faɗin. “Barrister mun
yarda da kai, sai dai ka sani koda baka san komai akan case
ɗin nan ba bazamu taɓa bari wani rami a buɗe mana ba koya
buɗe maka, zamu kasance a bayanka a kowanne lungu da
saƙo na ƙasar nan.”
“Nagode da wannan karamci”. Barrister ya faɗa da
girmamawa.
“Baka da damuwa Barrister ka cancanta ne.”
Murmushi ya sake saki tare da mikewa ya kai jakar
gabansu, cike da farin ciki suka buɗe suna mai fiddo duk
takardun ciki. Bayan sun ɗan dudduba su suka ɗago fuskoki
cike da murmushi suna yabama Barrister namijin ƙoƙarin sa.
Shi dai nashi murmushi ne kawai. Ɗaya daga cikin baƙin da
ake kira da Sayeed Harun Al-rashid, babban mutum ne a
ƙasar ta ruman, dan riƙƙaƙen ɗan kasuwa ne na gwal da kowa
ya sani kasancewar sunansa yayi matuƙar shura a wannan
harkar data zama babban tattalin arzikin su na ƙasar, dan
Ruman kam bata san iya arziƙin gwal da ALLAH yay mata ba,
shiyyasa duk wani riƙƙaƙen ɗan kasuwa zaka samu gwal ɗin
ne mafi rinjayen makaminsa kamar dai Sayeed Harun Al-
rashid. Ta wani gefen kuma yana riƙe da sarauta sai dai yafi
bama kasuwancin muhimmanci matuƙa. Zamansa ya gyara
sosai yana fuskantar Barrister. “Barrister yanzu mi kake son
ka sani?”.
“Ranka ya daɗe ba komai bane dama sai akan waɗan da
naga case ɗin ya karkata. Na duba dukkan bayanan Barrister
Abdallah Aas, sai dai a yanda na fahimta kamar ya gano inda
su mutanen dake hannun naku suke, dan kafin ma ya rasa
ransa kamar ya fito da ga ƙauyen Lufana ne wajen matar
marigayin, abinda nake son cewa anan ina tsoron yazam
bayan Barrister ɗin akwai wanda yasan wannan sirrin. In
kuwa hakan ta kasance zaman mutanen a station ɗin dana
fahimci kun ɓoyesu zai zama barazana ke nan koda anan
gaba”.

Kusan a tare sukai murmushi, Sayeed Harun Al-rashid ya
muskuta zamansa cikin nuna damuwa da zancen Barrister.
“Maganar ka nakan hanya Barrister shiyyasa tun kafin yau
muka gama maganin duk abinda kake gudun. Tun daga
farkon wannan case ɗin idanunmu akan komai suke, dan
haka ka kwantar da hankalinka. Su kuma tuni basa a police
station ɗin, dama mun kai ajiyar su ne domin ɓadda kama
bayan kwanaki kuma muka ɗauke su, amma kai a yanzu mi
kake son cewa?”.
Anzo dai-dai gaɓar da Barrister keson azo, dan haka ya ɗan
murmusa yana mai ƙara bama kansa nutsuwa. “Alhmdullh
kun fahimci inda nake buƙatar akai ranka ya daɗe. Abinda
nake son cewa kai tsaye shine ayi duk yanda za'ai cikin
kwanaki biyun nan abar ƙasar ruman da mutanen gaba
ɗaya”.
“Eh maganarka abin dubawa ce kam, amma kuma mizai
hana kawai a ɓaddasu a wuce wajen, dan abinda ya zama
dalilin zuwansu hanunmun ma an sameshi cikin sauƙi yanzu
haka”.
Barrister yay ɗan jimm dan bai fahimta ba, amma sai ya
dake bai sake musu wata tambaya ba gudun karsu zargi wani
abu. Sai dai ya cigaba da faɗin, “Ɓaddasu bashine mafitaba
ranka ya daɗe, dan a ɗan bincike da nayifa akwai babbar
matsala game da mutuwar Barrister Aas”.
Babu wanda zancen bai daka ba a acikinsu, Sayeed Faizul-
Anwar daya kafe Barrister da ido yay saurin faɗin, “Barrister
bamu fahimce ka ba, mi kake son cewa?”
“Ranka ya daɗe yanzu zan fahimtar da ku. Idan har kun
saurari dukkan labaran dake yawo har yanzu babu wani
tabbaci na samun alamar sassan mutum a cikin motar
Abdallah, wannan shine yaja hankalina tun a ranar farko
bayan nabar nan na fara nazari da bincike. Tabbas Abdallah
na raye, sai dai ya ɓoye kansa domin bada ƙafa. Na sanshi
nasan mizai iya fiye da tunaninku. Shiyyasa nake ganin kashe
mutanen a yanzu bashine mafita ba, muyi nesa da su da ƙasar
nan ta yanda babu inda zasuji ɗuriyarmu, sai kuma mu samo
wasu a madadinsu a buɗe shari'ar ta yanda zamu ƙona
Barrister Abdallah Aas da ransa batare daya farga ba”.
Dukansu gumi suke na tashin hanakali, sai dai babu
wanda ya iya cewa komai har zuwa wani tsahon lokaci.
Sayeed Harun Al-rashid ya nisa yana mai share ɗan gumin
daya taru masa a goshi. Ƙyaƙyƙyawar fuskarsa fara tas gaba
ɗaya ta ƙwaɓe alamar rashin damuwa. “Zartar da hukunci
bazai yuwu yanzu ba Barrister, amma kaje zuwa anjima zakaji
komai ta waya”.
“Babu damuwa ranka ya daɗe”. Barrister ya faɗa cikin
jimami shima, sai dai acan ƙasan ransa dariya yakeyi, yayinda
wani gefe na zuciyarsa ke tabbatar masa akwai wani babba
mai alaƙa da case ɗin bayan su, shiyyasa bazasu iya zartar da
hukuncin ba kai tsaye. Yau ma dai an rakosa da kuɗi masu
yawa har mota.......


★★... BAYAN KWANA BIYU ★★....

A kwanaki biyun nan abubuwa da yawa sun faru tako
wane ɓangare, sai dai marasa daɗi sunfi masu daɗin rinjaye.
Zuwa yanzu dai da gaske ƙasar ruman da jama'arta suke basa
buƙatar Tajwar Eshaan Ibn Haysam Abdul-majeed matsayin
Shahan-shan. Dan tun tsirarun mutane na zanga-zanga a
wasu jahohi takai yanzu ƙasar ma gaba ɗaya ta ɗauka. Abu
mafi ban mamaki harda wasu a manyan ƙasar na nuna goyon
baya ga talakawa, ciki kuwa harda wasu Tajwar na jihohi.
Yayinda ta wani gefen kuma hankalin wasu manyan ƙasashen
duniya ya fara dawowa kan zanga-zangar dama dalilin yinta.
Babban abinda ke tunzura jama'a shine biris daga Shahan-
shan, yayinda kuma a cikin gida hankalin ƴan majalissar sa ya
rabu kaso biyu, wasu na goyen bayan ya saukan wasu na
buƙatar karya sauka dan shine kawai ya cancanta da kujerar a
ganinsu. A talakawan ma bai rasa tsirarun masoya ba, sai dai
basu da ƙarfin ja da masu boren shiyyasa suka koma gefe
sukai shiru matsayin masu kallo da ido.

*_IFFAH!_*

A kwanaki biyun nan yanda Daular ruman ke a hargitse
haka Iffah ke a hargitse. Kuka kam idanunta har sun daina
fidda ruwan hawaye. Cikin ƙanƙanin lokaci tayi wata irin rama
mai ban tausayi. Haukan da iyalan Sayeed Khairul-Bashar keyi
a masarautar da wanda jama'a keyi a waje sai ta ɗaukesa
wasan yara. Idan su da suka rasa uba kawai zasu harmutsa
masarautar haka ina ga ita data rasa ahalinta duka, a ganinta
ita ya cancanci ta hargitse ƙasar ruman baki ɗaya ma ai. Sai
dai yanda ƴan zanga-zanga ke daɗa ƙaruwa na saka mata
farin ciki, dan abin ban mamaki har wasu a cikin Tajwar na
jihohi suma sun ƙara tunzura wuta da bada goyon baya akan
saukar Shahan-shan ɗin, hankalin ƙasashe kuma ya fara
dawowa ƙasar ruman, da alama dai dama a jirace kowa yake
da wannan damar. Hakan na sake tunzura ƙwarin gwiwar
ƙudirinta.
Wutar wannan al'amari na ƙara ruruwane dalilin shirun
Tajwar Eshaan. Babu shi babu cewarsa, harma wasu sun fara
tunanin anya kuwa yana cikin masarautar ma ko?.... Duk
wannan bai damu Iffah ba a yanzu, hankalinta gaba ɗaya ya
tattara ne akan ta ina zata samo dafin maciji. Bata da wani
amintacce a cikin masarautar, a waje kam sir Fawzan ne
kawai, shima kuma zuwa yanzu ta fara shakku akansa saboda
tana ganin ya ɓoye mata abinda ya faru da su Babiy ne bisa
wata manufa. Idan tace zata fita a sulale daga masarautar
taya kuma zata dawo cikinta? Wannan ƙalubalen keta faman
mata kaikawo harya gagara samun mafita a kwanaki biyun
nan. Tana a bangarenta bata ganin kowa kowa baya ganinta,
waɗan da zasu iya ganinta hankalinsu a tashe yake dan kai
tsaye su abin ya shafa, shirunsu kuma sai ya bama Iffah
damar fassarashi da abinda zuciyarta ta gama tabbatar mata,
dan haka itama a yanzu ta haƙƙaƙe bata da lokacinsu.

Kamar yanda ta tsara bayan sallar la'asar ta shirya tsaf
cikin abaya data amshi jikinta, dan ma ta rame ga idanunta
da suka ɗan kuklumburo amalar taci kuka bana wasa ba. Duk
da masarautar a harmutse take haka ta keta cikinta
hadimanta na take mata baya har sashen marigayi Sayeed
Khairul-Bashar. Tayi matuƙar mamakin tarbar data samu dan
batai zaton irinta ba, sai dai abinda bata sani ba shine su
kallon tausayi suke mata da tabbatar da itama bawai ta tsira
bane a hannun azzalumin. Dan malamin duba da matar
Sayeed Khairul-Bashar ɗin ta ziyarta tun lokacin daya ɓata
kafin aga gawarsa ya tabbatar mata akwai ƙulli mai girma da
Shahan-shan keyi game da rayuwar Iffah shiyyasa itama bata
mutu ba a sanda aka kaita sashenshi. A ranar bata ɓoyema
ƴaƴanta komai akan zancen nan data jiyo ba, sun kuma yi
niyyar samun Iffah har sashenta da batun washe gari aka
tashi da wannan tashin hankali. Wannan shine dalilinsu na
mata tarbar data bata mamaki. Ita kuma kasancewar
zuciyarta a kusa take tana musu ta'aziyya tana share hawaye
da handkherciff. Sai hakan ya ƙara mata kima a idon iyalansa.
Yayinda ƴan uwansu kuma da basu san komai na ke jin zafin
ganin Iffahr da fassarashi matsayin leƙen wani asiri dan a
yanzu wasu a cikin ahalin masarautar su kuma suna ma Iffah
kallon wata ƴar kaɗafin Tajwar Eshaan ce tunda har ta tsira
daga kisan gillarsa..........✍️
47


.........Kamar yanda Iffah tai tunani labarin zuwanta sashen
Sayeed Khairul-Bashar ta'aziyya har ya isa kunnen surukarta
dama na jikin Tajwar Eshaan irinsu malikat Haseenat da su
Daneen Ammarah. Dan tana fitowa kiran Daneen Ammarah
ya shigo wayarta. Bata ɗaga ba, aka kuma sake kira nan ma
dai ta share kamar bataji ba. Sai da ta koma sashenta da
kusan mintuna goma sannan tai kiran Daneen Ammarah ɗin
back. A bugu biyu ta ɗaga, Iffah ta taɓe baki cikin rashin
damuwa tai sallama da fara gaishe ta. Da kulawa Daneen
Ammarah ta amsa. Iffah na jiran jin ta mata batun fitarta sai
Daneen Ammarah ta jeho mata tambayar da bata da alaƙa
ma da fitar.
“Ibnati na kiraki ne akan Abni, shirunsa na tadamin
hankali matuƙa, gashi yana ƙara harzuƙa mutane ƙasa, kinga
dai yanda ƙasar nan ke sake rikicewa. Mu dukanmu mun
nemesa a waya amma bamata shiga, na fara zargin anya ma
yana cikin masarautar nan?”.
Murmushin takaici Iffah tayi, amma a zahiri sai ta danne ta
fara magana cikin kwantar da murya. “Wannan shine tunani
na nima Mamy, sai dai ban san yanda zanyi ba ganin ku
manya bakuce komai ba.”
“Shirun na dole ne Ibnati, bazaki gane babbar sarƙaƙiyar
dake cikin masarautar nan ba ne. Amma tabbas akwai
matsala, akwai kuma gagarumin al'amarin dake ɓoye amma
yana son bayyana kansa a wannan gaɓar.....”
Cikin zumuɗi Iffah tace, “Mamy minene shi dan ALLAH?”.
“Humm Fareedah kinyi ƙarama da yawa ba yanzu ba. Ke dai
kawai abinda nake so da ke shine ki taimaka ki bincika min
idan Abni yana a gidan nan...”
“To Mamy, amma dai zaiyi wuya tunda kunce idan yana
cikin damuwa kulle kansa yakeyi baya kuma sauraren kowa.
Sai nake ganin ni taya zai saurare ni”.
Murmushi Daneen Ammarah tayi mai sauti. “Rashin
saurarenmu bashi ke nufin kema bazai saurareki ba Ibnati. Ke
dai gwada sa'arki mu gani”.
Iffah dai ta jita ne kawai, amma sai bata sake musawa ba
sukai sallama.....

★★.... ★.....

Miran Jasim ya sauke wayar dake a kunnensa bayan gama
sauraren abokin wayar tasa, yanda fuskarsa ta canja daga
farin cikin dake shimfiɗe a kanta kafin wayar yasa Miran
Arshaan sake maida hankalinsa garesa. “Wani abu ya sake
faruwa ne?”.
“Zai dai faru”.
Cewar Miran Jasim ɗin a fusace yana miƙewa. Miran Arshaan
da maganar ta dakesa ya miƙe zumbur shima. “Ban gane mi
kake son cewa ba Jasim Akh?”.
Kamar bazai tanka masa ba sai kuma yaja kakkauran tsaki.
“Harun Al-rashid ne dai akan waccan maganar banzar ta
ranar, duk yabi ya tashi hankalinsa yana cigaba da damuna
nima, tun abin bai tasiri a raina ba har ya fara, wai Barrister
da suka bama aikin can kan ɗan iskan can ne ke cigaba da
musu bayani dai kan Barrister Abdallah bai mutu ba dai da
gaske.”
“Wai suna nufin shi ya tabbatar da hakan kenan?”.
“Abinda ke cazamun kai kenan, na rasa wane shirme ne
kuma hakan? Taya wanda bomb ya tashi da shi ace bai mutu
ba?”.
“To amma fa kuma maganarsu fa abin a duba ce Jasim Akh.
Dan koni naji shakku a randa bomb ɗin nan ya tashi amma
jami'an tsaro suka tabbatar babu wani alamar an rasa rai......”
“Amma shine kai shiru?!”.
Miran Jasim ya katsesa a zafafe. “Mi kake so nayi bayan
wanda nayi to? ina son ka tuna tun a ranar na kawo maka
wannan zancen amma ka nuna min cewar zata iya yuwuwa
ƙarfin tashin nakiyar ya cillashi wani waje ne shiyyasa basu
gansa ba. A kuma shekaran jiya da suka kawo maganar na
kuma ƙoƙarin maka nuni ka kalli zancensu a shirme”. Shima
Miran Arshaan ɗin ya karɓa masa a nasa zafin.
Shiru Miran Jasim yayi da dafe kansa yana murza goshinsa
dan ya tuna tabbas anyi hakan. Amma wannan aikin na cikin
gida da rashin sanin mi Tajwar Eshaan ke ciki ya ɗauke
hankalinsa bai nutsu yayi nazari kan batunba kasancewar
akwai abubuwa da yawa da bawai yana buɗema Miran
Arshaan ɗin bane, kamar yanda shima Miran Arshaan ɗin ba
komai yake yarda ya buɗe ma Miran Jasim ɗin ba. Sai dai a
yanzu dukansu sun fahimci yin kuskure, dan haka kowanne ya
ajiye ɓoyayyar manufarsa suka fuskanci juna.
“Ni ina ganin in har an yarda da aikin Barrister ɗin nan
shawararsa ba abar yardawa bace. Sannan dole ne fa mu
gaggauta ganawa da yarinyar can in ba hakaba aikinmu zai
iya buɗewa. Dan idan ya kasance Barrister Aas na raye bazai
samu ɗaki bane ya kulle kansa domin hutu kaima ka sani”.
Miran Jasim ya gyaɗa kai da faɗin, “Hakane maganarka na
kan gaskiya. Yanzu minene abinyi?”.
“Abinyi ɗaya ne bama Barrister Akeem damar shigewa
gaba kafin kwana biyun nan na cikar aikinmu abar ƙasar nan
da mutanen. Bayan ka haye karagar mulki shi kuma shegen
duk inda yake zamu nemishi ne ya ɗan-ɗana kuɗarsa”.
“Ina sake godema ALLAH da kasancewar ka kusa da ni, dan
kana farkar da ni a duk sanda kaina ya shiga duhuwa ɗan
uwana”.
Murmushi Miran Arshaan ya saki a zahiri, a zuciya kam faɗi
yake, (Banza ka gama cusamin ƙayar a rumbu na rufeta da
ɗan boto ina daga kwance).
Ɗaukar wayar Miran Jasim dai-dai da kammala wayar Iffah
da Daneen Ammarah daga can......

★★.....

Tana ajiye wayar wani kiran ya sake shigowa, kamar zata
share dan bata san number ɗin ba sai kuma dai ta ɗauka da
tunanin ko Sir Ajmaal ne kasancewar a saƙonta na ƙarshe ta
roƙesa idan ya gani ya kirata. Daga can aka amsa sallamarta
kai tsaye, hakan ya sata Ciro wayar a kunenta ta kalla tamkar
mai son gano muryar. Miran Jasim da kamar yana ganinta yay
gyaran murya, hakan ya sata sake maida wayar.
“Kina magana da Jasim Ibn Abdull-Majeed Aliy”.
Kai tsaye Iffah ta ganesa, dan haka ta fara gaidashi da
girmamawa. Hakan ya masa daɗi, dan yanda yake amsa mata
da kulawa zai baka tabbaci. Shiru ne ya ɗan biyo bayan
gaisuwar, kafin ya katsesa da faɗin, “Ibnati inata zaman jiran
ji daga gareki amma shiru. Ko baki amince da abinda kika gani
bane ba dai?”.
Iffah da ke jin an taɓo mata inda ke mata ƙaiƙayi hawaye
suka shiga rige-rigen sakko mata. Hannu tasa ta sharesu da
ɗan jan hanci. “Ba yarda ne banyiba ranka ya daɗe, kawai dai
zuciyata na kaikawo ne na son sanin dalilinka na yin hakan a
gareni. Idan ban manta ba kai fa Ammi ne garesa, mizaisa ka
zaɓeni sama da shi? A barshi ma zaka iya hakan kasancewar
ka mai gaskiya ko ƙyamar abinda yake. Amma miyasa su na
baya da aka rasa bakuyi wani yunƙuri ba sai ni a kaina bayan
akwai ƴaƴan Tajwar mafi rinjaye a cikin wanda ya halaka?”.
(Kaga ibilishiyar yarinya) ya ayyana a zuciyarsa. A zahiri
kam sai yay gyaran murya cike da dattako yana kallon Miran
Arshaan da shima ke sauraren komai. “Wato Ibnati duk yanda
zan miki bayani a wayar nan ba lallai ki fahimta ba. Amma zan
tura miki lokaci da adireshi mu haɗu zai fi”.
Jimmm Iffah tayi kamar mai shakku, sai kuma ta nisa
cikin gyaɗa kai tace, “Okay babu damuwa ina jira”. Daga haka
sukai sallama kowa ransa na masa kaikawo...

★★....

Cikin ƴar dariya Miran Arshaan yace, “Amma shegiyar
yarinyar nan fa da zata samu dama a masarautar nan ba
ƙaramin hatsabibiya za'ai ba. Kaji murya cauy-cauy bata ko
tsallaken kalma ga shegen wayo”.
“Shiyyasa dolene tana kammala aikin nan a kaudata
kawai, ai tunda har tana da ƙarfin halin shigowa masarautar
nan da ƙudiri irin na kashe Shahan-shan dama nasan zamuga
fiye da hakan tattare da ita. Irin waɗan nan yaran masu taurin
zuciya a cikin mata basu da yawa, amma kuma kasancewar su
mata ga mai mulki ba karamin ƙara samun power bane.
Badan-badan ba babu abinda zai hanani tabbatar da ita
abokiyar tafiyata. Dama yarinyar ga shegen ƙyau da ƙira
tamkar ita ta zana kanta...”
Ƙaramar dariya Miran Arshaan yay idonsa akan ɗan uwan
nasa. “Wato dai Jasim Akh har yanzu bazaka canja ba,

31 / 34