Author : Bilyn Abdull ce Category : African Stories & Novels
kuma zagaye da tsatstsauran tsaro”
“ALLAH ya ƙara bata lafiya, sai dai kuma banajin tanada
hannu a cikin al'amarin Mamy, dan da ganinta mutiniyar kirki
ce”.
“Gane mutanen kirki ba'a ido yake ba Ibnati musamman a
wannan masarautar da kowa kansa kawai ya sani, a mafi
yawan lokuta ma ba'a gane maƙiyi da halayya. Akwai
rikitattun abubuwa dake a matuƙar cuɗe a wannan Daular da
gani da ido bazai wadaci mai kallo ba, dan haka nakeso ki
nutsu kisa hankalinki waje ɗaya kafin ki koma sashenki ki koyi
abubuwa da yawa na salon mulki da tsarin matsayinki na
Zawjata-almilki. Saboda kunada matuƙar tasiri da girma a
tsarin ƙarfin iko na masarauta da kaikawon talakawan ƙasan
ruman. Fatana kuma kece Malikat a cikin Zawjata-almilki
insha ALLAHU”.
Sam Iffah bata fahimci komai ba ga kalaman Daneen
Ammarah, amma sai bata sake cewa komai ba dan a ganinta
tana buƙatar samun lokacin yin nazari na musamman a kansu
kafin ta fahimcesu dallah-dallah.......
★★... ★... ★★....
Ana idar da sallar asuba drivern daya kawo su Kaka jiya dan
hanashi komawa yay saboda dare ya ɗauka Iyyani da Ummu
suka wuce. Kaka da Abu Zainab kuma sukai shirin fara neman
inda zasu samo Babiy da Hanash.
Dai-dai suna shiga mota kaka ya dubi Abu Zainab da ɗan
murmushin ƙarfin hali a fuskarsa, “To Zakariyya kai ne ɗan
gari, yanzu ta ina zamu fara kenan?”.
Numfashi Abu Zainab ya furzar, tare da yin ɗan jimm alamar
tunani, “E to Baba banace ba dai, dan al'amari nada wuya,
saboda bamu da tabbacin waɗan nan jami'ai daga wane
station suke. Amma ni yanzu a nawa shawaran ina ganin
kamar mu nema gidan shi marigayi ɗin, tunda matarsa ita ta
kawo jami'an tasan daga ina suke”.
“Hakane, wannan ma shawara ce mai kyau, sai dai inda
gizo ke saƙar kai koka san ina gidan Dawood ɗin yake? Dan ni
dai rabona da shi ma kusan shekara biyar kenan tun suna tare
da Muhammad Zayyan”.
“Ito baba banace ba, dan kusan nima hakan dai take,
amma bayan tashinsa daga anguwarmu nasan inda ya koma,
sai dai bani da tabbacin ko har yanzu acan ɗin yake zaune
tunda ba wani huɗɗa muke ba gaskiya, dama dalilin Abu
Hanash ɗinne ake gaisawa sai kuma idan wani zama na
anguwa ya haɗa kafin ya tashi kenan. Amma yanzu dai bara
mu tafi can ɗin kawai rana ma nayi”.
Cikin ƙanƙanin lokaci suka iso anguwar, kasancewar ma ta
cika ba kamar da ba da kyar suka iya samo gidan. Duk da
jikinsu ya ɗanyi sanyi ganin ƙofar gidan babu alamar anyi
wani abu daya shafi mutuwa Abu Zainab yay sallama har sau
uku. Ana huɗun wani mutum ya fito. Cikin binsu da kallon
rashin sani ya basu hannu suka gaisa. Abu Zainab da shima
dai jikinsa yay sanyi ya ce, “Kayi haƙuri nasan baka sammu
ba. Muma dai munzo nan ɗinne neman wani bawan ALLAH
daya zauna anan shekara kusan huɗu haka baya. Sunansa
Dawood, amma ana masa alkunya da Abu Moosa. Matarsa
ɗaya bashi kuma da yaro ko ɗaya”.
“ALLAH sarki, gaskiya ban sanshi ba, dan nima dai ban
wuce shekara biyu da tarewa anan ɗin ba. Na kuma sayi
gidanne a hanun wani mutum Ibrahim Askari”.
Abu Zainab zai sake magana Kaka ya girgiza masa kai
alamar kar yace komai. Godiya sukai masa da sallama suka
wuce.
“Baba ban san miyasa ka dakatar dani ba. Dama zan
tambayesa ne ko zai faɗa mana inda zamu samu shi Ibrahim
Askari ɗinne”.
Numfashi Kaka yaja ya fesar, “Dalilin da yasa na dakatar da
kai kenan. Kasan shi al'amari irin wannan yana buƙatar kasan
dawa zakai maganar abu na gaba. Inaji a jikina waɗanda suka
haddasa tushen wannan matsalar dole suma zasu kasance
suna bin bayanmu domin toshe duk wata hanyar da zamu iya
bi. Dalili kuwa shine ina kallon lauje ne cikin naɗi akan
al'amarin”.
“Eh gaskiya hakane kuma Baba. To amma in har hakane
mizai hana mu nema lauya, sai nake ganin cikin sauƙi shi zai
iya binciko mana inda suke ma, kuma koma minene sai yazo
cikin sauƙi tunda ana magana ne akan abinda ya shafi shari'a
ko kuwa?”.
“Itama wannan babbar shawara ce a mahangar hankali
Zakariyya, sai dai shi lauyan ne matsala musanma irin mu
wanda muke bukata. Mai gaskiya da amana”.
“In dai dan wannan ne babu damuwa insha ALLAHU, akwai
yayan matata data rasu, kwararren lauyane kuma mai
nagarta da nasan zakaso aikinsa kuma zai taimakemu
kasancewarsa babba. A yanzu dai nasan bazamu samesa a
gidansa ba. Bara kawai muje ofishinsa”...
★★..... ★... ★★.....
Kamar yanda Iffan ta nema alfarma a wajen Daneen
Ammarah akan ɗakko mata akwatinta da aka kawo ta gidan
dashi ya iso gareta. Taji matuƙar sanyi a ranta da farin ciki.
Hadimar data kawo na fita ta buɗe akwatin ta shiga dubawa.
Alhamdullah komai yana nan yanda yake, hatta takardar da
malam Fawzan ya bata ɗinnan itama tana a inda ta ɓoye ta.
Tana idar da sallar azhar littafin data sako a kayan nata kawai
ta ɗauka da biro ta fara rubutu. Anutse take rubuta komai
daya faru daki-daki tun daga barowarta gida har zuwa
shigowarta cikin masarautar, abinda ya faru da ita dama
wanda ke kan faruwa bayan warkewarta. Da zarar taji motsi
koda ma Daneen Ammarah ne sai ta boye, a haka ta kwashe
kaf yinin har zuwa dare tana abu ɗaya. Da daddare bayan
kammala shirin barci maimakon kwanciya zaman karatun
Alkur'ani tayi, koda Daneen Ammarah ta shigo ta sameta a
hakan bata katseta ba. Tasa Hadimar dake biye da ita ajiye
mata madarar da suka shigo da ita. Daga haka ta fice taja
mata ƙofar da nufin ta dawo zuwa anjima, dan yanzu tana
son zuwa ta duba Malikat Haseena ne da yai batajin daɗi.
Iffah na ganin ta fice ta sauke ajiyar zuciya, addu'a tai ta
rufe Alkur'anin ta mike, kofar taje ta sanyama key bayan ta
leƙa babu kowa a corridor ɗin. Ta ɗan jingina da ƙofar tana
mai ambaton “Alhamdullah” da sakin ɓoyayyen murmushi.
Cikin sassarfa tabar jikin ƙofar zuwa ga akwatinta, ta buɗe
tare da ɗakko wayar Arfa da takardar da Malam Fawzan ya
bata. Number da aka rubuta ta kwashe a wayar, ta haye
tsakkiyar gadon ta kwanta tare da jan lallausan bargon ta
shige ciki har kanta sannan tai dailing number. Gaba ɗaya a
kage take da zumuɗin a ɗauka. Dan haka take bin sautin
shigar kiran da zuciyarta. Sai dai harta yanke ba'a ɗaga ɗin ba.
Kira ta sake yi, nan ma dai shiru, bata gajiya ba ta cigaba da
kira har fin sau goma kafin a ɗaga a karo kusan na goma sha
biyar. Nannauyar ajiyar zuciya ta sauke tamkar wadda aka
tsamo daga cikin ƙanƙara. Sai kuma tai saurin faɗin,
“Assalamu alaikum”.
“Wa'ake nema?”.
Aka faɗa daga can maimakon amsa sallamar tata. Da lafiya
lafiya ne sai tayi mitar ƙin amsa sallamar, amma sai tai saurin
faɗin, “Sir Ajmaal”.
“Wa'ake nema?”.
Aka sake maimaita mata tambayar.
Zuciyarta ta ɗan fara zabura amma sai ta danne ta sake
maimaitawa itama.
“Sir Ajmaal”.
“Wa'ake nema?”.
Still aka sake faɗa kamar dai ba'ama jita ba.
Wayar ta janye a kunenta ta tashi zaune ta ɗauka
takardar, number dai dake a jikice dai-dai batai mistake ba.
Sake maida wayar tai kunne aranta tana faɗin (bara naga
ƙarshen ku dai) ta sake amsawa da “Sir Ajmaal”.
“Kin saɓa lamba”.
Aka bata amsa da yanke wayar lokaci guda batare da anjira
cewar ta ba......
★★..... ★... ★★.....
Kasancewar Abu Zainab suruki ga barrister cikin sauƙi suka
samu ganinsa ta hanyar kiran waya. Har office yasa
masinjansa daya fita yay musu iso ya shiga da su. Ganin
lafiyayyen office ɗin nasa dama hukumar tasu ya sake
tabbatar ma da Kaka babbane gaskiya. Sun gaisa cikin nuna
sanayya shi da Abu Zainab. Ya kuma gaida Kaka da
girmamawa kasancewar tsoho dama zai iya haifarsa. Basu
saurari lemo da aka kawo musu ba Abu Zainab ya shiga masa
bayani dalla-dalla. Sai da ya gama tsaf Barrister Abdallah dake
rubuta wa ya ajiye biron yana jinjina kansa. Kaka ya fuskanta
cikin son ƙarin bayani....
“Baba kaima kasan shi Dawood ɗin kenan?”.
“Tabbas na sanshi yaro. Hasalima ga gidan mahaifin shi
Muhammad Zayyanu gana mahaifin Dawood. Sannan ta
ɓangaren mahaifiyata ma munada alaƙar jini da mahaifin
nasa. Shine kuma yay sanadin zuwan Muhammad Zayyanu
garin nan, shi kuma Muhammad Zayyanu ya koya masa
noman zuma daya gada ga mahaifinsa”.
“Eh lallai sanayya ce babba kam. Sai dai kuma inaga ya
kamata nasan miya rabasu? Dan yanzu hujjojin hanunmu
sune zasu taimaka mana wajen kubutar da su saboda wannan
case ne babba kuma da alama shiryayye”
“To nidai kai tsaye banace ga abinda ya zama sanadin
rabuwar kawunan nasu ba. Dan shi Muhammad Zayyanu
mutum ne mai zurfin ciki da rashin kwaramniya. Amma dai
lokacin da naga bana ganinsu tare na tambayesa ko akwai
matsala? Shi da abokin nasa. Sai ya sanar min shi dai a
saninsa bai masa komai ba ya janye daga jikinsa, ya kuma
bisa ya bisa babu adadi danya faɗa masa amma yaƙi, daga
karshe ma ya tattare kayansa da iyalinsa sukabar anguwar,
bai kuma sake ganinsa ba har watanni sunja a lokacin. Na
bashi shawarar ya ƙara nemansa dai, da muka sake haɗuwa
na tambayesa sai yace ai yama bincika yabar gari. Iyakar
abinda na sani kenan gaskiya”.
“Shi kuma Dawood ɗin baka sake ganinsa ba kaima?”.
“Eh to gaskiya ban sake ganinsa ba. Dan ko'a rasuwar
mahaifinsa sai wai-wai mukaji yazo yay gaisuwa ya tafi kawai.
Daga nan kuma dai bamu sake jin ɗuriyar tasa ba dan dama
mahaifiyarsa bata raye tuni”.
Barrister dake faman kaɗa kai ya sake ajiye bironsa.
“Uhhm yanzu to inaga mataki na biyu shine musan wane
station suke. Ko kuma inda ita matar tasa take”.
Cikin damuwa Abu Zainab yace, “Munje inda muke tunanin
samun nata bamu sameta ba. Sai dai an ambata mana sunan
wanda ya saida gidan ga wanda ke ciki yanzu”.
“Miye sunan”.
“Ibrahim Askari”.
“Badamuwa kuje abunku, insha ALLAHU daga nan zuwa gobe
za'a nema mana Ibrahim Askari ɗin. Suma kuma zan ɗan
bincika ta hanyar jami'an dana sani a mabanbanta station na
garin nan”.
Sosai kaka ya dinga ma barrister godiya. Hakama Abu
Zainab. Shi dai faɗa musu yake karsu damu. Aje a cigaba da
addu'a komai zai zama labari insha ALLAHU......
★★..... ★★.... ★★.....
Iffah kamar zatai kuka ta ƙara dailing number amma sai ma
aka sanar mata switch up. Wani irin zafi da lugude ƙirjinta ya
shiga yi, ta shiga neman number Malam Fawzan cikin rawar
jiki tunda dai shine ya bata number..........✍️
23
........Itama ɗin dai switch up. Wasu zafafan hawaye suka
silalo a kumatun ta. Ƙoƙarin sake kiran waccan number ta
gwadayi knoking ƙofar da akai ya katseta. Da sauri ta yanke
kiran da kashe wayar ma baki ɗaya ta ɗaga gadon ta tusasu
har da takardar gaba ɗaya sannan ta sauka dan tasan bazai
wuce Daneen Ammarah ba...
“Ibnati baki barci ba kenan?”.
Kan Iffah a ƙasa tai ɗan murmushi. “Yanzu zanyi Mamy
karatu na kammala”.
“Masha ALLAH, ya kamata ki kwanta to dare yaja, nima
zuwa zanje na kwanta”.
“To Mamy ALLAH ya tashemu lafiya”.
Koda Daneen Ammarah ta wuce Iffah ba kwanciyar tai
ba, sake ɗakko wayar tayi ta cigaba da neman wancan layin
da a yanzu ake cemata not available saɓanin switch up na
ɗazun. Hakama number Malam Fawzan har yanzun. Daga
ƙarshe dai barci ɓarawo gwanin iya sata ne ya saceta akan
dole ta haƙura, sai da asuba ta tsinta wayar a ƙasa yashe....
Yau dai kam ta ƙudiri niyyar fita gaida tsohuwa Malikat
Haseena da kanta, tunda dai jikinta Alhamdullah hatta saɓar
ma sai inda ba'a rasa bane bai gama ba. Bayan hadimar dake
gyara ɗakin ta kammala ta fita key ta sama ƙofar sannan ta
shiga wanka. Dan duk da tausayin hadiman da takeji a yanzu
batajin zata sake yarda da waninsu. Ta fito tana tsaka da
shiryawa cikin ɗaya daga kayanta na gida akai knoking.
Karasa saka abayar tayi sannan taje ta buɗe, a tare suka
sakarma juna murmushi, tai ƙasa da kanta tana faɗin, “Barka
da safiya Mamy”.
Daneen Ammarah takai hannu ta taɓa kanta da faɗin, “Kin
tashi lafiya?”.
“Alhamdullah”.
“Haka ake so. Ga kayanki nan na amfanin yau, mun zaɓi yin
hakane saboda gudun abinda zai iya zuwa ya dawo Ibnati,
amma insha ALLAH kayanki na amfani na gab da kammaluwa,
saiki shirya ni zanje sashen Umm Jasrah. Ki tabbatar kinci
abinci sosai yanzu zan dawo ba jimawa zanyi ba”.
“Adawo lafiya Mamy a gaisheta”.
“Zataji, amma ki tabbatar kin canja waɗan nan kayan”.
Kai kawai Iffah ta jinjina mata. Amma a ranta tana mamakin
minene aibun abayar tata? Tana cikin sabbin kayantama da
take matuƙar ji da su. Shigowar hadimai biyu da kayayyaki ya
katse mata mitar tata, sai dai batace komai ba bayan amsa
musu gaisuwa. Fita ɗayar tai aka barta da wadda tafi yawan
kasancewa da ita, tazo gabanta ta zube kanta a rissine. “Ya
Zawjata-almilki bisa umarninki za'a shirya kayan”.
Karo na biyu Iffah ta amsa neman izini da umarni ga
hadimai a gidan. “Ba yanzu ba, zaki mun rakkiya ga Mamma
ne, ki jirani a waje”.
“Umarninki shi nake zaman jira ya Zawjata-almilki”.
Hadimar na fita ta taka inda kayan suke tana dubawa.
Tunda ta samu lafiya kullum da safe za'a kawo mata kaya kala
uku, washe gari za'a kwashesu koda daya kawai ta saka a
sake ajiye mata wasu. Da farko ta ɗauka ko haka tsarin
masarautar yake. Sai a yau bayanin Daneen Ammarah yasa ta
fahimci ita akema hakan saboda tsaro. Waɗanda ranta yafi
kwantawa da su ta dauka ta saka. Ta koyi ƙyau sosai
musamman da suka kasance bakake da adon stones masu
sheƙi da ɗaukar idanu. Ga farar fatarta data koma ja ƙaɗan
saboda saɓar datai tamkar ta larabawa ta sake fitowa.
Ɓoyayyun turarenta na wajen Kaka ta ɗakko ta saka, wani irin
ƙamshi mai daɗi da saka zuciya nutsuwa ya fara ratsa ɗakin...
Sosai murmushi ya bayyana a fuskar tsohuwa Malikat
Haseena saboda ganin Iffah akan kafafunta, takuma ji daɗin
wannan ziyarar bazata data kawo mata duk da kuwa suna a
sashe ɗaya ne. Iffah data kai zaune gefenta bisa tattausar
dardumar da aka ƙawata falon da shi ta risinar da kai tana
gaisheta da tambayarta yaya jiki?.
“Alhamdullahi ƴar albarka. Yaya naki jikin?”. Malikat
Haseena ta amsa da kulawa har yanzu murmushi ƙawace da
fuskarta.
“Naji sauƙi ai Mamma” (kamar yanda taji Daneen Ammarah
na kiranta.
“To Alhamdullah ALLAH ya ƙara kiyaye gaba”.
Da amin duk hadiman wajen suka amsa. Malikat Haseena
sallamar duk Hadiman tayi, tare da bada umarnin a shirya
mata breakfast da Iffah. Hakan ya bama hadiman mamaki
sosai, dan duk wanda Malikat Haseena zata buƙaci zaman cin
abinci da shi ba karamin mai sa'a bane ba. Cikin ƙanƙanin
lokaci kuwa aka kammala shirya komai, ita dai Iffah na kallon
ikon ALLAH da tsagwaron mulki wajen wannan tsohuwa. A
ranta kam tunani take shin wai idan haka matan suke waishi
babban dodon nasu yaya za'a gansa kenan?. Bisa umarnin
Malikat Haseena Iffah ta mike suka nufi wajen da aka shirya
abincin. Zamansu dai-dai da shigowar amintacciyar hadimar
Malikat ɗin ɗauke da wani ƙaramin kwano...
Shigar ƙamshin turaren Iffah hancin Hadima Banou ya saka
jikinta fara tsuma. Hanunta na ɗan rawa ta sunkiya zata ajiye
kwanon suka haɗa ido da Iffah. Zabura tayi da sauri ta miƙe
kanta a sunkuye. Iffah ma dake jin jikinta na wani irin
yamutsawa ta sake kallonta da kyau, haka kawai matar batai
mata ba, gata wata irin doguwar mace gandaƙaiƙai kamar
namiji babu wani fasalin mata tattare da ita... Malikat
Haseena da rawar jikin Hadimar ya bata mamaki itama ta
tsura mata idanu. Sai dai mulki da kasaita baisa ta tanka ba.
Hadima Banou dake jin kamar ta zura a guje saboda yanda
take jin jikinta ta zube ƙasa, cikin rawar hannu ta fara
yunƙurin haɗama Malikat Haseena abinci.. Iffah dake mata
kallon nazari ta dakatar da ita. “Kinga jeki kawai”.
Ai kafin ma ta rufe baki tuni ta mike zaram kamar wadda ke
akan wuta. Iffah da gaba ɗaya abin ya gama ɗaure kanta ta
fara haɗama Malikat Haseena abincin da kanta. Itako Malikat
Haseena komai bata kawo a ranta ba game da yanayin
Amintacciyar hadimar tata, saboda takan ganta a wasu
yanayi daya fima hakan, dan haka ta jima da sakata a jerin
masu aljanu...
Hadima Banou na fita a falon ta sauke wani irin nannauyar
ajiyar zuciya da kai hannu ta yarce gumin dayay sharkaf a
goshinta kamar wadda ta tiƙi surfen gero. Gaba ɗaya manyan
idanunta masu saka tsigar jikin mutane tashi sunyi jazur. Gefe
ta koma ta zauna a ranta tana fatan ALLAH yasa har Iffah ta
tafi Malikat Haseena bazata nemeta ba. A ganinta ma tai
zamanta anan koda an nemetan ai sai an ganta. Wannan
shawarar data yankema ranta ya sata cigaba da zama a wajen
har lokacin jikinta bai gama komawa dai-dai ba....
Gaba ɗaya Iffah kasa sakewa taci abincin tai saboda
kunya, ganin haka cikin hikima Malikat Haseena ta cigaba da
ɗan jan ta da hira domin jan ra'ayinta, itako tana amsa mata
a kunyace da tsakurar abincin. Suna a haka Daneen Ammarah
ta shigo, itama dai ta nuna jin daɗinta na ganin Iffah ɗin tare
da jin kaunarrta har cikin rai. Zama tai itama aka ɗora cin
abincin da ita suna yar hira jefe-jefi da Malikat Haseena.
Iffahn dai nata saurare kawai, sai kuma murmushi. Rabin
hankalinta kam nacan wajen tunanin hadima banou da
yanayin ta....
★★.... ★.. ★★....
Kamar yanda Barrister yayma su kaka alƙawari ya samo
Ibrahim Askari ta hanyar mutumin nan da suka fara zuwa
wajensa. Fuskarsa cike da murmushi yake dubansu, dan tun
yana can ya sanarma Abu Zainab su haɗu a office. Sai gashi
kafin ya iso ma su har sun iso. Ko cikakkiyar gaisuwa basuyi
ba ya fara musu bayani.
“Alhamdulh an samo Ibrahim Askari, ya kuma bani
cikakken adireshin Dawood ɗin, hasalima yace shiyya sayar
masa da gidan daya koma ɗin. Ga adireshin gidan ya bani”.
Sosai farin ciki ya bayyana a fuskar Kaka. Ya dinga jerama
Barrister addu'a da fatan alkairi. Shima dai Abu Zainab yayi
masa godiya, tare da ɗorawa da faɗin, “Barrister yanzu mune
zamuje can ɗin? Kokuwa kai ne?”.
“Mu duka babu wanda zai je Zakariyya”.
Kallonsa sukai su duka, ya jinjina musu kansa da buɗe wani
littafi a gefensa ya yago takarda, ɗan rubutu yay da sake
ɗagowa ya dubesu. “Kamar yanda na faɗa muku mu duka
babu wanda zaije. Domin ita Shari'a takanzo saɓanin hankali.
Sannan