Author : Bilyn Abdull ce Category : African Stories & Novels
ginine na jar
laka tamkar yanda duka gidajen ƙauyen suke. Sun ɗan jima
acan suka dawo, sun iske kaka ya dawo shima daga fitar da
yay tun ta safe gona ɗebo sassaƙe-sassaƙen magunguna. Ƙara
zaman tattaunawa sukayi iya su uku, ita dai Iffah bata cewa
komai. Daga ƙarshe ma tashi tai ta shige ɗakin kwananta.
Bata sake fitowa ba sai da kaka ya neme ta. Sassaƙe-Sassaƙen
magungunan daya ɗibo ɗazun ne a gabansa, kowanne ya
ɗauresa daban-daban. Ya turamata babban robar da suke
ciki... “Zaki fara amfani da su Iffah, bana son kiyi wasa dan
ALLAH. Waɗannan kuma hayaƙine, a kowacce duhun magriba
ki tabbatar kinyi turarensu, wannan kuma a ruwan wanka ne,
da kin idar da sallar asuba ki zubasu cikin ruwa kaɗan ki cire
kayanki ki tabbatar duk jikinki ya samu”.
“Tofa kaka wannan ɗin kuma duk na miye?”. Iffah ta
tambaya cikin nuna mamaki.
Idanu ya tsiramata na kusan mintuna uku tamkar mai
nazari, sai kuma ya ɗauke kansa da wani yanayi mai wahalar
fassara. “Faruwar ƙaddararmu bashi ke nuna baza'a sake
jarabtarmu ba. Idan jiya ta shuɗe da ɗaci zata iya yuwuwa
yau ɗinmu da dariya zata kasance, sai dai sanin mike a
gobenmu al'amarine mai girman gaske, damin gaibunmu ce
ita ALLAH ne kaɗai masanin mi zaizo.”
Kallon juna sukai ita da Hanash, Iffah ta ɗan ɗage kafaɗa
cikin yanayin ban fahinta ba, shima sai ya kaɗamata idanu
alamar shima hakan take. Atare suka maida dubansu ga kaka.
Amma sai ya kauda kansa alamar baya buƙatar kowacce irin
tambaya daga garesu. Iffah ta jinjina kai kawai alamar ko'oho.
Sai kuma ta miƙe tana mai faɗin, “Ni dama fa na yanke
shawarar zanbi Akhi mu koma. Tunda dai naji sauƙi gara naje
na koma makaranta anata wuceni a darasi”.
Ba karamin waro idanu Hanash yay ba, zaiyi magana kaka
ya dakatar da shi ta hanyar yin murmushi da kaɗa kansa. “Ita
rayuwa rubutacciya ce tunkan halitta, an rubutatane da
alƙalamin da ba'a goge rubutunsa, babu wani hannu daya isa
gogeta koda da ƙarfin iko. Dole ne sai anyi hakan, ko muna so
ko bama so mashin nan sai ya isa inda aka aikashi. Domin ita
*KIBIYAR AJALI! SULKE BAYA TARETA SAI TA GITTA*”.
A rikice Hanash ya tari numfashinsa. “Kaka bana gane
dunƙulallun zantukan nan naka, ka fito fili dan ALLAH ka
sanar mana mi kake son faɗa...”
“Hanash! Lokacin faɗar baiyiba ai, nima kurman baƙin
kawai na gani, fassarar sai UBANGIJI”.
Sosai Hanash ya sake tsare fuskar kaka da idanu, kamar
yanda itama Iffah tai tsai tana kallon nasa. Su dukansu sun
jima da sanin kaka mutum ne hatsabibi, dan kuwa mahaifinsa
gawurtaccen masanine da azamaninsa akan kallesa tamkar
matsafi ko wani mai gani har hanji, sai dai kasancewar bai
ajiye buzu ya zauna akan iya wannan al'amarin ba yasa ake
shakkar faɗa, yana bada taimako na magani akan abubuwa
daban-daban musamman harkar aljanu komai ƙarfinsu da
shaiɗancinsu. Sannan yana sana'arsa ta saƙa kayan kwalliyar
doki. Kaka ya gaji abubuwa da dama a garesa, sai dai shi ya
watsar da harkar bada maganin dan shima dai a karan kansa
yana ta'allaƙa sanin mahaifin nasa da bokancin, duk da dai
bai fito fili ya bayyana hakan ba kuwa, amma rashin maida
hankali akan abinda ya shafi hakan zaisa ka zargi ko haka
ɗinne. Akwai kayan aiki na mahaifinsa da yawa a killace a
wani waje da shi kaɗai ya sani, kuma tun bayan mutuwarsa
shi ya tattare su ya killace su............✍
4
.........Iffah tayi mamaki da kaka ya bari salin alin tabi Hanash
washe gari, duk da Iyyani taso borewa ita. Amma wasu lafuza
daga cuɗaɗɗun kalamansa ya sata yin shiru ta bisu da addu'a.
Kaka yayma Iffah gargaɗi matuƙa akan abubuwan daya bata,
ya kuma tabbatar mata ko guda ɗaya taƙiyi zaiji hakan a
jikinsa.
A hankali ta murza awarwarayen hannunta da shine ya
sakamata, ta sake lumshe idanunta da sakin ajiyar zuciya.
Haka kawai takejin awarwarayen da girma da kuma banbanci
da irin wanda take sakawa a baya domin kwalliya, ko miye
dalili oho.
Daga Ummu har Babiy a tsorace suke kallon Iffah da
Hanash da suka shigo. Hanash ya girgiza musu kansa cikin
sauri yana faɗin, “Wlhy ba laifina bane Babiy. Itace ta bore
akan saita biyoni, kaka kuma ya bata goyon baya. Dan a
cewarsa _(Babu wani nisa dake bada tazarar gujema ƙaddara.
A wani ajin jarabawar data biyoka ma gara kai ka tunkareta.
Dan ba kowane kogo bane ke zama kogo ga ma'abocin gudun
ceton rai)._ Babiy na kasa fassarawa, akoda yaushe
cirkuɗaɗɗun kalamai daga bakin Kaka masu tsaurine da
wahalar fahimta. Dan ALLAH idan kun sani ku fassara mana”.
Maimakon amsa daga Babiy baya sukaga yayi tamkar zai
faɗi, sai dai cikin sa'a ya dafe gini tare da dafe kansa alamar
hajijiya. Ummu ma ƙasa takai zaune jikinta na rawa, hakan sai
ya ƙara firgitasu. Da sauri duk sukai kansu suna mai
tambayarsu suna lafiya kuwa?. Da kai kawai suka amsa musu,
Babiy harda ƙoƙarin ƙaƙaro murmushi. Cikin son kwantar
musu da hankali yake kallonsu. “Kunga karku sakama
zukatanku wata damuwa, ba maganar Baba bace ba, kawai
dai bana jin daɗine kwana biyun nan dama”.
Jimm sukai alamar tunani, sai dai kuma babu damar yin
musu ko ƙin aminta da cewar tasa. Hanash ya taimaka masa
suka koma cikin runfa, Iffah kuma tana riƙe da Ummu..
★★★
Washe gari batare da sun sani ba Babiy yay sammakon
yin tafiya zuwa ƙauyen Jumna. Ya samu tarba daga surukan
nasa ko ta girmamawa....
Ƙyaƙyƙyawan tsohon da Tattarowar fatarsa ta tsufa bai
hana bayyanar ƙyawun cikar halittarsa ba ya sake kallon
dattijon gabansa a karo na babu adadadi. Murmushi ya saki a
karon farko, cikin karyar da kai da ƙanƙan da idanu ya kai
hannu bisa kafaɗar dattijon. Numfashi yaja kakkaura da
juyowa alamar dawowa hayyaci. Ya maida kansa ƙasa ya
sunkiyar saboda girmamawa ta surukuta dake a tsakaninsu
na tsahon shekaru.
“Humm Muhammadu Zayyanu!”.
Tsohon ya kira sunan tamkar mai sake bita a ranar da aka
raɗa ga mai shi. Ɗago idanu ya sakeyi a karo na biyu sai kuma
ya risinar tare da amsawa da “Na'am Baba”.
“Tun isowarka magana nake gani shimfiɗe a fuskarka
amma bakinka ya kasa furtawa, ko wani abu ya sami Hanash
da ƴar uwarsa ne a hanyarsu ta komawa gida jiya?”.
“A'a baba ko ɗaya, lafiya lau sukaje cikin ƙoshin lafiya
kuma, sai dai.....”
Sai kuma yay shiru ya kasa ƙarasawa. Kaka dake kallonsa yay
ɗan murmushi, “Sai dai baku so komawar Iffah ba ko?”.
“Hakane baba. Domin kuwa babu abinda ya canja a daular
Ruman, muna jin tsoron rasata itama kamar ƴan uwanta, duk
da bamu da tabbacin zasu sake waiwayrnmu, sai dai
kalamanka sun sakamu a ruɗani har muka kasa rumtse idanu
a daren jiya domin yin barc......”
“Hana ido barci bashi ke nufin damar iya sauya abinda
bakai ka rubuta ba. Muhammadu Zayyanu! Da ace
ƙaddararmu a hannayenmu take da kaf mutane bazasu zana
zaman duniya ba a littafinsu musamman idan sun san koda
daɗin busawar iskar dake cikin aljanna ce. Karka damu kanka
da sanin sirrin cikin dutsen da ko'a kallo abin firgitarwa ne.
Mumini yakan kasance mai azumtar yini daga UBANGIJI, ya
kuma sallaci duhun dare daga UBANGIJI domin yaye damuwa
ko samuwar nutsuwa a duniyarsa. Gaibu daga ALLAH take,
zahirin da yaso mu sani kawai yake iya nuna mana ta isharar
rayuwa ko canjawar tunanin zuciyo
yi”.
Nannauyan numfashi yaja ya fesar tare da jinjina kai,
bawai kwanciyar hankalin da yazo nema ya samu ba, sai dai
rashin zaɓi ko bakin zaren kamawa ya sashi fahimtar tsohon
na masa nuni da shiru ne kawai a zubama sarautar ALLAH ido
dan shine kawai gagara misali.....
_________________
★Kwanaki biyu kenan da dawowar Iffah gida, inda
dawowar tata ta zame mata tamkar wani famin ciwo a jikinta.
Dan a kullum takanyi hawaye sama da sau babu adadi akan
rashin ƴan uwanta guda biyu. Komai ta kalla nasu yakan
dawo mata da jiyansune mai cike da farin ciki da babu
tunanin yankewa. Duk halin da take a ciki Ummu da Babiy na
hankalce da ita, tausayi take basu matuƙa, wani lokacin
Ummu har hawaye takan share itama.
Yau ma tamkar kullum tun bayan dawowarta tai shirin
makaranta ta fice badan hankalin su Ummu ya kwanta ba.
Kawai dai dan ta dagene akan komawar. Sun bartane ko
komawar zaisa ta sake samun nutsuwa da farin cikin da ko'a
fuskarta yanzu baka hangosa. Sanye take cikin skirt golden
yellow da t-shirt fara da suka kasance Uniform ɗinsu, sai
hijjab fari ƙarami shima ta ɗora niƙab ta yanda ƙwayar
idanunta kawai ake iya gani. Bayanta goye da school bag. A
nutse take tafiya kanta a ƙasa tamkar bata son taka ƙasar har
ta iso bakin titi, tsayuwar da batafi ta mintuna uku ba ta
samu abin hawa kamar sauran ɗalibai daketa ɓillowa a
kowane kusurwa. Makarantarsu babbar makarantace mai
ɗauke da ɗalibai masu hazaƙa, domin kuwa an tattarosu ne
daga mabanbanta makarantu aka kawo nan saboda
hazaƙarsu. Kowa bata kulaba ta shige aji tai zamanta, saɓanin
da da kowa yasan Iffah mai tsiwa da surutu, gata ba'a kadata
a himma. Kauɗinta yasa mafi yawan malamai saninta ga
kuma ƙoƙari. Amma tunda ta dawo yanzu ta canjama kowa,
magana ma saita zo har a tashi batai da wani ba. Kamar
yanda malaman sukai mata uziri haka ɗaliban ma sukai mata,
dan kowa yasan tana cikin yanayin da uzirin kawai tafi
buƙata.
Duk wanda ya shigo yakan miƙa mata hannu su gaisa,
itama babu musu take miƙawa tare da amsa sallamar da
sukai mata. A haka har duk ɗaliban ajin suka kammala
shigowa malamin farko ya shigo musu. Da farko ta nutsu
wajen fara fahimtar darasin da yake musu, a hankali kuma
tunaninta ya fara janyewa zuwa ga abinda taketa faman
shiryawa da zuciyarta a kwanakin nan har malamin ya
kammala ya fita babu abinda ta ɗauka. Haka na bayansa suka
cigaba da shigowa basu darasi daban-daban, wani hankalinta
na kai wani harya fita babu abinda zatace ta saurara. Ana
tashi tana a ɗalibai sahun farko da suka fara fitowa, jitai
kawai tana sha'awar yin tattaki da ƙafafunta yau, dan haka
bata tsaya neman abun hawa ba ta miƙo titi da ƙafa ta fara
tafiya kamar wasu tsirarun ɗalibai irinta da gidajensu ke kusa
da makarantar. Tafiya tayi mai nisa sosai batare da nuna
alamun gajiyawa ba, harta kusa isowa roundabout ɗin daya
raba hanyar gidansu da ainahin titin hanyar masarauta daular
ruman. Daga roundabout ɗin ana iya hango ƙaton tambarin
ƙosashen zaki da akayisa da gold na tambarin Masarauta.
Iffah taja wani kakkauran tsaki da ɗauke kanta zuciyarta na
mata zafi. Harta kusa tsallakawa ta hango wata tsohuwa dake
riƙe da wani yaro da Uniform a jikinsa da alama titin take so
su tsallaka amma sunata inda-inda. Karan farko murmushi ya
suɓuce mata ganin yanda yaron ke jan hanun tsohuwar sai
sun tafi kamar zasu tsallaka saita fisgo yaron su dawo baya
tana masifa. Sallama tai musu, tsohuwar ta amsa mata. Ta
gaisheta da girmamawa tare da faɗin, “Ammi kuna so ku
tsalla ne?”.
Amsawa tsohuwar tai da “Eh Ibnati ”.
Iffah ta sake murmusawa daga cikin niƙab ɗinta, kafin takai
hannu ta riƙo na tsohuwar dake riƙe da yaron ita kuma. Suna
gab da kaiwa tsakkiya yaron ya fisge hanunsa ya koma baya
da gudu yana faɗin yabar abunsa a baya. Tsohuwar zata fisge
itama tana masifa da kiran yaron ya dawo Iffah ta riƙeta gam
suka karasa tsallakawa. “Ammi yi haƙuri barsa naje zan sake
tsallako miki da shi. Rufe bakin Iffah yay dai-dai da taka wani
bahagon birkin daya bada sautin ƙuuuuuu!!!. Sai sautin fitar
ƙara mai razanarwa ta biyo bayansa.
Wani irin zabura Iffah tai na juyowa dan ƙarar har
tsakkiyar kanta ta jita. Ai batama san sanda ta yaye niƙab ɗin
fuskarta ba da waro manyan ƙyawawan idanunta waje gaba
ɗaya ba tana mai ambaton sunan ALLAH ganin yaron nan
tsaye cak a tsakkiyar titi hancin wata mota gab da shi allamar
kaɗan ya hana ayi ɗanyen aiki. Kusan a tare suka isa kansa ita
da tsohuwar data fashe da kuka da ƙwala kiran sunan yaron a
matuƙar firgice.
Iffah da jikinta ke ɓari ta riƙo yaron jikinta tana
duddubashi da sauke ajiyar zuciya a jajjere, ganin babu ko
ƙwarzane a jikin nasa. Saurin sakin yaron tai ga tsohuwar
tasha gaban motar ranta a ɓace ganin mai motar ko fitowa
baiyiba ya ɗan leƙone kawai, ganin baima yaron komaiba ya
maida kansa yanama ƙoƙarin barin wajen. A fusace ta buɗe
murfin, ba saurayin daya kasance drivern motar ba hatta
wanda ke gefensa hankalinsa akan lap-top dake saman
cinyarsa sai da ya ɗago suka zuba mata idanu. Gaba ɗayansu
ta haɗa ta dallama harara da manyan idanunta masu matuƙar
haske tamkar madara.
“Kai malam baka san darajar mutane bane?....” Zazzaƙar
muryarta mai taushi da nutsuwa a cikinta ta daki
kunnuwansu cikin faɗa babu ko ɗigon tsoro a tare da ita.
Batare data damu da yanda suka zuba mata ido ba ta
murguɗa musu bakinta da sake dalla musu harara ta cigaba
da masifarta, “Ka kusan bige yaro amma tsabar kanka ba'a
daidai yake ba shine koka fito kaga yaya yake ma saboda ku
masu kuɗin nan ɗaukar talaka kuke baida banbanci da titin da
kuke gurza tayoyin banzayen motocinku da kuka saya da
kuɗinmu”.
“Kai!”.
Drivern ya faɗa da maɗaukakin mamaki Iffah.
Harara ta sake dalla masa da zira hannunta ta zare key ɗin
motar daya riga ya kashe tun ɓuɗe musu murfin da tayi.
“K! K! Dalla bani key kajimun fitsararriyar yarinya kinga
mun taɓashi ne?”.
“Anƙi a bakun, wlhy duk sai kun fito kun dubashi kun bama
kakarsa haƙuri zan baku key ɗin nan, inba hakaba sai dai mu
kwana anan.”
Hannu saurayin ya kai da nufin warto key ɗin taja baya, sai
dai duk da haka saida yaɗan taɓa skirt ɗinta kaɗan. Cikin
matsanancin ɓacin rai ta jinjina yatsarta a kan fuskar
matashin tamkar zata tsone masa ido. “Idan hanunka ya sake
gigin taɓa koda hijjab ɗin jikina ne sai na karyashi, Sannan
koda Shahanshan ne yay wannan aikin bai isa barin wajen
nan ba balle kai shashasha driver”.
“K!!”.
Na gefensa ya faɗa cikin matuƙar waro idanu. A karan farko
wanda ke hakimce zaune a sit ɗin bayansu lap-top a cinyarsa
da tarin takardu a gefe da gefensa ya ɗago ƙyawawan
idanunsa dake tattare da matsananciyar gajiya da ƙosawa
yana yamutsa fuska. Baya ganin yarinyar, sai dai duk abinda
take faɗa raɗam a kunensa zazzaƙar muryarta ke sauka. Baiko
kalla yaran nasa ba ya sauke Lap-top ɗin dake cinyar tasa tare
da kai hannu ya buɗe murfin. A tare suka zabura, sai dai kafin
suyi wani yunƙuri harya fita a motar. Dolo suka fito suma da
sauri...........✍
5
........Kama hanun yaron da Iffah tai da nufin subar wajen duk
da key ɗin motar mutanen har yanzu na'a hanunta yay dai-
dai da isowar wani nutsatstsen taku mai tafiya da sassanyan
ƙamshin turare tamkar shi kaɗai iska ke tsintowa tana
busawa a hancinan mutane. Kamar wani magic wajen yay
tsitt na wasu sakkani, tsirarun mutanen da suka taru a wajen
tun furuwar abun duk suka zuba masa idanu. Ita kanta hajiya
Iffah mai masifar ƙirjintane yay wata irin harbawa lokacin da
mutumin ya sauke nasa lulu idanun cikin tsakkiyar nata. Da
ƙyar ta iya fisgar su daga cikin nasa tana ɗan murguɗa baki da
sauke niƙaf ɗinta cike da dakiya.
Idanun nasa ya janye daga kanta shima da matsawa gaban
yaron ya kai tsigunne dai-dai tsayinsa dan ya fara ɗauka
yarinyar nan aljanace ma dai kawai. Cikin sassanyar muryarsa
mai zurfi da nutsuwa ya motsa lips ɗinsa kaɗan tamkar an
fisgo maganar.
“Kana lafiya?”.
Kai yaron ya gyaɗa masa.
Ya ɗan ɗage gira da motsa bakinsa kamar zai taɓe. “Uhhm!
minene sunanka?”.
“Amjed”.
Yaron ya faɗa cike da kwarin gwiwa.
A hankali ya sake kaɗa fararen idanunsa tare da jinjina
masa👍🏻 ya saki wani sassanyan murmushi a karon farko da
jan kumatun yaron. “Oh my Friend! nice name. Kana sona da
aboki?”.
Da sauri yaron ya jinjina kai yana washe baki. Idanunsa ya
ɗan sake fiddowa suka ƙara girma tare da ƙara sakin
murmushi. Ya riƙo hannu yaron alamar suyi musabaha.
Al'amarin ya birge mutane da yawa, duk da babu wanda
yasan wanene shi, amma ko makaho ya kalla wannan mutumi
yasan babban mutum ne. Suit ɗin dake jikinsa farare tas ma
kawai abin kallone. Balle shi a karan kansa daya kasance
ƙyaƙyƙyawan gasken fatarsa da gogewarta har ɗaukar idanun
mai kallo take. Ga wani ƙamshi na musamman mai saka
nutsuwa ga mai shaƙa, yanayin kamewarsa da cikakkiyar isa
irin ta manyan mutane ke ƙara kawata kwarjininsa da cikar
kamala ga duk mai kallonsa.
A karo na biyu suka sake haɗa ido da Iffah dai-dai ya gama
gaida kakar yaron nan da keta faman washe baki da jera
masa godiya dan kuɗine dunkulallu sabbi ƙal ya damƙa a
hanun Amjed. Harara ta balla masa da janye idanunta da
sauri saboda wani abu mai tsananin sanyi taji yana tafiya
daga ƙafafunta har saman kanta. Cike da takunsa na nutsuwa
da ƙasaita shima ya juya ya bar wajen kai kace akan dole yake
taka ƙasar saboda takun zaratan maza masu cikakkiyar isa da
lafiya ce tattare da tafiyar tasa. Iffah ta jefama ɗaya daga
cikin samarin nan biyu key ɗin motar, dan ɗayan ya tafi da
hanzari ya buɗema ogansu ne. Dai-dai zai shiga ta ballama
wanda ta jefama key ɗin harara da faɗin, “Daga yau ko daga
nesa kuka hangoni to ku canja hanya koda a jirgi kuke kuwa”.
Shigar maganar tata a cikin kunensa dai-dai zai shiga
motar da aka buɗe masa ya ɗan ɗago idonsa, sai dai wadda
ya ɗago da nufin kallar da mamakinta ke cin ransa tuni ta nufi
barin wajen tamkar ba ita ta haɗa dabar wajen ba... Suna
ƙoƙarin shan shataletalen titin idanunsa ya sake sauka a
kanta ta miƙe titi tana tafiyarta a nutse, sai dai fuskarta a rufe
take da niƙab data saki tun bayan haɗa idonsu na farko....
🤔Wannan ƴa ta Babiy wataran sai ta saka an mata
dukan sakwara a titi in har bata canja hali ba😬🚴🏼.
★★......★
“Badai a ƙasa kika tahoba auta? Na ganki a gajiye tamkar an
koroki”.
Zubewa tai a taburmar da Ummu ke zaune, tare da ɗora
kanta a cinyarta tana ƙara narke fuska. “ALLAH a ƙasa na taho
Ummu. Haka kawai naji ina son na taho a ƙafan”.
“Ai gashi nan duk kin gajiyar da kanki, dama keba wata
isashshiyar lafiya ba. Tashi kiɗan watsa ruwa dan sai warin
rana kikeyi”.
“Kai Ummu warin rana fa?”. Tai maganar a shagwaɓe da
kamo rigarta ta kai hancinta. Miƙewa tai tana tura baki gaba
da faɗin, “ALLAH Ummu kinso dai yarfanine amma ƙamshin
ma turare nakeyi”.
Murmushi kawai Ummu tai da girgiza kanta, ita kuma ta
shige ɗaki