Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dauɗar Gora Complete Hausa Novel by Bilyn Abdull Ce

Author :  Bilyn Abdull ce Category :  African Stories & Novels

Chapter   10 / 34

27K to 30K   out of 100K words

ta, dan kuwa itace mafi ƙarancin girma a cikin
Zawjata-almilki da aka kawo daular ruman.

Sun mata shiri irin na Zawjata-almilki data isa a kirata da
wannan sunan. Dan ƙwalliyar tata ta dace da halittar
ƙyaƙyƙyawar surar jikinta da ƙyawunta. Ta cancanci a kirata
Malikat Fareedah bayan Zawjata-almilki duk da ƙanƙantar
shekarunta. Saboda duk da damuwar dake shimfiɗe a
ƙyaƙyƙyawar fuskarta hakan bai hana bayyanar fitar kwalliyar
ƙawata kwarjininta da cikar haiba ba. Su kansu hadiman dake
zagaye da ita sai faman satar kallonta suke. Bawai dan tafi
duk sauran Zawjata-almilki da suka shuɗe ƙyawu ba, kawai
natan ya matuƙar ƙayatar dasu ne batare da sun san dalili ba.
Ita a karan kanta kallon kanta take dajin tamkar ba ita ɗin
bace, bawai dan ƙyale-ƙyalen gold da diamonds da aka
ƙawata adon jikin nata da shi ba. Hasalima sune abu na farko
da takejin tsantsenin gani a jikinta.
Hadima Diwa data sake neman izinin shigowa ta shigo a
gabanta ta sake zubewa tana mai satar kallonta itama. Cikin
jinjina girma irin na UBANGIJI mai halittar abinda yaso a
yanda yaso ta isar da saƙonta kamar haka....
“Ya Zawjata-almilki! Yanzu shine lokacin karin
kumallonki”.
Iffah da takurar ta fara gundurarta ta saurin tarar
numfashinta, “Bana buƙatar cin komai nikam Mama”.
Tamkar hadima Diwa zatai kuka, muryarta har rawa take
wajen faɗin, “Ki gafarceni ranki ya daɗe. Wannan suna bai
dace da niba, jinsa a harshenki zai tabbatar da hukunci mai
tsanani a gareni. Hakama rashin cin abincinki a yanzu”.
(Ya rabba).
Iffah ta ambata a zuciyarta cike da takaici dajin sake tsanar
Tajwar Eshaan dama duk mai faɗa aji na masarautar. Bata
sake magana ba ta miƙe suka fito da hadima Diwa. Dan
matan da suka mata kwalliya tuni sun fice su. Babu kowa a
ƙaramin falon da Diwa tai mata jagora, inda aka shirya abinci
kala-kala kai kace su goma zasu cisa. Ita a rantama tunani tai
ko tare da Tajwar Eshaan ɗinne ma. Sai da taga har takai
zaune Diwa na ƙoƙarin fara haɗa mata abincin ta tabbatar
domin ita kawai akayi kenan. Komai batace ba, har Diwa ta
gama buɗe abincin duka alamar taga wanda take buƙata
kenan. Komai kallo ɗaya tai masa ta ɗauke kanta, da ga
ƙarshe ta nuna mata dafaffiyar madara kaɗai. Diwa tai jimm
kamar mai tunani, sai kuma ta saci kallon Iffah ɗin tai saurin
maida kanta ƙasa. Iffah da duk ke kallonta ta ƙasan ido ta
cigaba da nazarinta harta kammala zuba mata madarar.
Gabanta tazo ta ajiye, harta yunƙura zata miƙe ta dakatar da
ita.
“Bani zan sha ba ai mama naki ne”.
A wani irin matuƙar hargitse Diwa ta ɗago tana duban ta,
jikinta har wani karkarwa yake. “R....ran...ki ya daɗe
w...w..wan nan ai ba hurumina bane”.
Iffah data kafeta da idanu ko ƙyaftawa batayi ta janyesu
a hankali tana mai miƙewa abinta batare da tace komai ba.
Da sauri Diwa ta ƙara gurfana a gabanta tana hurwa. “Ranki
ya daɗe dan ALLAH karkice bazakici komai ba, dan komai
anan umarnine”.
Bata zauna ɗin ba, ba kuma tace komai ba. Sai ma ɗakin
da suka fito data nufa zuciyarta cike da nauyi. Batafi zaman
mintuna biyarba wasu mata da batako musu kallo biyu ba
suka iso da wata hamshaƙiyar riga mai kamar alƙyabba daga
Malikat. Tare da umarnin tafiya da ita. Batai musu ba, dan a
nata tunanin Malikat Bushirat suke nufi, sai dai zuciyarta ta
kasa nutsuwa. Addu'a ta shiga ambato a zuciyarta har suka
kammala saka mata ƙawatacciyar rigar alƙyabar mai tsananin
ado da ɗaukar idanu, zasu kunna mata turaren wuta da suka
shigo da shi a burner tai saurin dakatar da su.
Kallon juna sukai, kafin ɗaya tai saurin faɗin cikin ƙanƙan
da kai, “Ya Zawjata-almilki wannan umarnine daga Malikat”.
Yamutsa fuska Iffah tai tana mai kallonta, kallo irin na
wannan bata san wacece autar Babiy ba ta ɗauke kai. A karon
farko tun shigowarta gidan tai magana da harshen ƙarfin
zuciya ta ajiye rauninta a gefe. “Ni kuma wannan umarnina
ne bana buƙata. Sai kumuje umarni na gaba”.
Babu wanda a cikinsu baiji yayi sumar wucin gadi ba. Sai
dai wani irin kwarjininta da jin shakkarta ya gama ɗarsuwa a
zukatansu lokaci guda.. Iffah dake jin jininta na wani irin
tsitstsinkewa ta sake dubansu da niyyar magana, tamkar
wadda aka jefa da narkakken ƙarfe taji yafff! A ƙirjinta. Da
sauri ta dafe ƙirjin tana mai rumtse idanunta. Rawar da jikinta
ya farayi ya sata zubewa ƙasa tana mai ƙoƙarin ambaton
sunan ALLAH, amma hakan ya gagara, dan tamkar an naɗe
zuciyartane da harshenta a lokaci guda......

Har rige-rigen fita hadiman nan sukeyi jikinsu na
matuƙar rawa. Diwa dake zaune a falo tana jiran fitowarsu ta
miƙe da sauri tana tambayar lafiya? Babu wanda ya saurareta
a cikinsu suka fice. Hankalintane ya tashi, tai kamar zata bisu
sai kuma ta fasa ta nufi ɗakin da Iffah take. Wani irin mugun
bugawa ƙirjinta yay damm. Innalillahi..... ta shiga ambata
dayin kan Iffah dake ta faman juye-juye a ƙasa, cikin ƙanƙanin
lokaci ta jiƙe sharkaf da zufa tamkar an watsa mata ruwa
koma an tsamota a ciki. Harta kusa kai hannu kanta sai kuma
taja baya da sauri cikin tsoro. Ina bai kamataba, matsayinta
na hadima hanunta ya taɓa Zawjata-almilki. A daburce tai
waje da nufin isar da saƙo ga Malikat Bushirat duk da bata da
tabbacin samun iso cikin sauƙi........✍
15


...........Ilai kuwa, duk yanda Diwa taso isa ga Malikat Bushirat
akan lokaci hakan ya gagara, dama tasan ba abune mai
sauƙiba. Amma kuma ƙin isar da saƙon a lokacin daya dace
tamkar sakacintane. Zata kuma iya fuskantar kowane irin
hukuncin da babu mai mata uziri a cikinsa...

A dai-dai lokacin da Diwa ke ƙoƙarin son isa gaban
Malikat Bushirat ƴan uwa ga Malikat ɗin na can sun doshi
sashen Iffah domin kai kayan al'ada da akema kowace
Zawjata-almilki da zata saka kafin a wuce da ita wajen taron
buɗar amarya da duk wani babba mai faɗa aji a daular ruman
zai halarta, wanda kuma akaf matan Tajwar Eshaan ɗin da
suka shuɗe huɗun farko ne kawai akaima wannan bikin sai
Iffah a yanzun. Anan zata san kowa, kowa kuma ya santa.
Tafe suke tare da rakkiyar hadimai masu ɗauke da wata
lafiyayyar rigar alƙyabba mai tsananin ɗaukar hankali da aka
ɗinkata ta musamman domin Zawjata-almilki da kuma
wannan rana. Sai sauran kayan ado irin na hamshaƙan mata
da akayisu da zallar zinare da diamond.
Sun ɗanyi mamakin rashin samun kowa a sashen, saboda
sanin tunda safe an turo hadimai da zasu mata hidima.
Yanayin tsaftar sashen kuma ta tabbatar musu hadiman
sunzo. Tunanin ko itace ta sallamesu ya sakasu ture zancen a
zukatansu suka bama cikin hadiman umarnin wata ta nema
musu iso. Har hadimar ta nufi ɗakin da aka kai Iffah jiya ta
tsaya cakk sakamakon wani irin kakari da sukeji tare da ɓarin
fashewar abubuwa. Su dukansu dubansu suka maida ga
ƙofar, da alamun mamaki ɗaya daga ciki ta sake bama wata
hadimar umarnin zuwa ta duba. Minti ɗaya baima cika da
shigar hadimar ba ta dawo a guje numfashinta na fita da ƙyar
tana nuna ɗakin da faɗin, “Z...Z....Zawjata-almilki!......”
A kusan tare suka afka ciki. Su dukansu babu wanda bai
firgita da ganin Iffah dake layi hanunta na dama dafe da
ƙirjinta tana laluben hanya dana haggu ba. A dalilin laluben
ne taketa faman zubda abubuwan da aka ƙawata adon ɗakin
da su. Sakamakon hakan kuma duk ta jima hanunta ciwo sai
jini yake yi. Da zafin nama ɗaya daga cikin matan nan ta
riƙota cikin jikinta suna mai ambaton sunan ALLAH a tare.
Ganin yanda ta jiƙe sharaf ga jikinta yayi jajur abinka da fara
sai hankalinsu ya ƙara tashi. A fisge Iffah ta damƙo hanun
matar ta haɗa da nata takai kirjinta tana fadin,
“Ummu wuta, jikina zai babbake Ummu ki sakani a
kanƙara dan ALLAH karna ƙone. Zan mutu Babiy wuta tana
cin jikina....”
Gaba ɗaya kalamanta sake ruɗasu sukayi. Duk sun
daburce sunma rasa miya kamata su mata. Dan wadda ke
rike da ita har hucin zafin takeji a nata jikin itama. Ƙaramar
cikinsu ce tai ƙarfin halin fita da hanzari tana mai musu nunin
tana zuwa. Cikin sauri tamkar zata kifa ta nufi sashen Malikat
Bushirat. A yanayin data shigo ya saka Malikat ɗaga yatsun
hanunta dake ƙawace da jan lalle da adon zabban zinare biyu.
Tamkar ƙiftawar ido duk hadiman dake zagaye da ita suka
fice. Zaune ta tashi da ƙyau, idanunta akan ƴar uwar tata.
Cike da ƙasaita ta ambaci sunanta akan lips “Jasrah!”.
“Na'am Bari-Hamshira”.
“Mike faruwa kika shigo kamar an koroki”.
“Afuwan. Duk abinda kikaga ya koro ɓera daga wuta tofa
yafi wutar zafi ne. Wai kin san kafin zuwanmu har an kai mata
rigar alƙyabbar buɗar amarya ta saka, akwai babbar matsala
Bari-Hamshira, ga yarinyar mutane can a wani mawuyacin
hali”.
“Kamar ya?”.
Malikat Bushirat ta faɗa tana mai miƙewa zaune sosai da
sake ware ƙyawawan manyan idanunta akan Jasrah.
“Bari-Hamshira ba lokacin neman ba'asi bane wannan,
lokacine na neman hanyar ceto ran yarinyar mutane. In ba
hakaba itama zasu kashe mana ita kamar sauran na baya....”
Lokaci guda idanun Malikat Bushirat suka kaɗa sukai
jazur. A kallo guda zaka fahimci ƙololuwar tashin hankalin
daya tsargata. Da ƙyar ta iya ɗaukar wayar landline dake
gefenta hanunta na rawa, ƴan danne-danne tayi kafin ta
miƙama Jasrah. Da hanzari Jasrah ta amsa. Sanin kowa
Malikat zata iya nema a yanzun yasata kai tsaye ambaton
sunansa. “Ghazi! A tattaro duk wani mai magani dake a
daular ruman dama wajenta yanzu zuwa sashen Zawjata-
almilki ta uku”.
“An gama ranki ya daɗe”. Aka faɗa daga can cike da
tsantsar girmamawa....


★★_________★★

Ƙarar marin da azabarsa ya saka hadimar zubewa ƙasan
lallausan carpet ɗin dake katafaren falon. Sosai jikinta ke
tsuma tamkar mazari. Ga hawaye har rige-rigen sauka suke a
fuskarta. Kanta ta shiga girgizawa da sake gurfana a gabanta
sosai tamkar mai neman gafara...
“Ki gafarceni uwar-gijiya. Wlhy nayi iya yina domin ganin
mun mata turaren amma ta nuna sam bata aminta ba.
Wannan ba irin waɗan can na baya bane, akwai wani sirri mai
razani a cikin ƙwayar idanunta da taurin ka....”
Saukar wani sabon bahagon marin ya hanata ƙarasawa.
Ƙara dafe kuncin tai da hannu bibbiyu. “Ina neman gafara a
gareki bisa kuskurena Uwa- gijiya...” hadimar ta faɗa da sauri
tana mai ƙoƙarin gumtse kukan dake son kwace mata dan
harga ALLAH marin ya shigeta matuƙa.
Matar dake harɗe bisa kilisa tana cin inibi cike da ƙasaita
irin ta masu isa ta ɗaga idanu kaɗan ta dubi wadda ke tsaye
kusa da ita tana faman hura hanci, wanda marin ma itace ta
yisa daman. ƙyawawan idanunta ta juya a fuskar amintacciyar
hadimar tata, sai kuma ta janyesu ta maida a yanda take
tamkar batasan mike faruwa a wajen ba. Cike da girmamawa
hadimar ta ranƙwafa. “An gama Uwar-gijiyata. Umarninki
wajibine a garemu”. Kamar yanda bata motsaba a yayinda
hadimar ke kashe fuskar waccan da mari da neman afuwa a
yanzu ɗinma haka. Ga hadimar tata hakan ba sabon abune a
gareta, dan haka bata damu ba. Sai ma nuna waccan hadimar
dake gurfane tana sharar hawaye tai da ɗan yatsa da
kakkausan harshe.
“Shugabata bata yafiya, bata ɗaukar kuskure koda zaka
shekara dubu kana mata hidima kuskurenka ɗaya bazai taɓa
fansarka ba”.
“Innalillahi wa-inna ilaihirraji'un” Hadimar dake a
gurfanen ke faɗa cikin rawar jiki, ta sake kaiwa gurfane gaban
Uwar-gijiyar tasu tana kuka da hurwa irin ta masu neman
afuwa. Amma ko kallo bata ishetaba. Sai ma amintacciyar
hadimar nan tata ce ta kora ta waje tana mai sake kaimata
mari......

★★......

Cikin ƙanƙanin lokaci duk wasu masu ƙarfin faɗa aji akan
magani suka rufu a sashen Iffah da komai ke ƙara rikicewa.
Dan takai ƙoƙarin ma yaga kayan jikinta take saboda azabar
da takeji a jikin. Matan nan dake matsayin ƙanne ga Malikat
Bushirat sai faman zuba mata ruwa mai azabar sanyin da
taketa ambata suke suna hawaye amma tamkarma basa zuba
matan. Fatarta kam tayi wani irin masifar ja kai kace za'a
taɓata ta ɗashe ne da kanta. Dan tayi wani luguf-luguf tamkar
an dafa ganda taji wuta. Abin tausayi duk yanda Iffah ke son
ambaton sunan ALLAH bisa a zabar da takeji hakan ya gagari
harshenta. Sam ƙwaƙwalwarta da zuciyarta ma sunƙi
connecting wajen taimaka mata. Sunan Ummu da Babiy
kawai take ambata akan su zo su taimaketa zata ƙone......

*_MALIKAT BUSHIRAT_*

Diwa da jikinta ke tsuma kamar mazari ta zube gurfane
agaban Malikat Bushirat data saka aka nemota tun kafin a
sanar mata dalilin kiran. Gaisuwa ta mika cike da tsantsan da
kai. Sai dai daga Jasrah dake faman kai kawo a falon har
Malikat babu wanda ya amsa mata. Sai tarar numfashinta da
Jasrah tayi tare da jeho mata tambayar data nema sakata
sakin fitsari a bujenta.
“Bisa umarnin wa kuka aikata, kuma ke da su wanene?”
Kanta ta shiga girgizawa jikinta na rawa. “Wlhy ranki ya
daɗe bansan komaiba, taya za'a haɗa baki dani a aikata
wannan kuskuren. Sam ban san badaga nan aka turasuba, kai
tsaye ma suka shiga wajen Zawjata-almilki batare da sun jira
na musu iso ba saboda bana kusa. Amma wlhy wlhy banida
wani alaƙa ko sani akan wanda ya turasu, hasalima nayi iya
ƙoƙarina na ganin na kama ko ɗaya a cikinsu amma hakan ya
gagara saboda hankalina ya kasu biyu gashi sai ni kaɗai a
wajen”.
“Ƙarya kike yi? K kina ina suka shigan?”.
“Na rantse da UBANGIJI mai zartar da mutuwa akan kowa
iya gaskyata kenan ALLAH ya baki yawan rai, ina kan tattare
abincin da aka shirya mata ne da bata ci ba ma”.
“Zaki iya gane hadiman?”.
“Sosai ALLAH ya taimakeki”.
“Kafin cikar awa biyu muna buƙatar ku anan”.
“Da ikon ALLAH hakan ce zata tabbata”. Hadima Diwa ta
faɗa tana miƙewa da rawar ƙafa ta fice. Sai lokacin Malikat
Bushirat ta ɗago idonta, dan tunda Diwa ta shigo bata sake
motsawa a yanda take ba, duk maganar da sukai da Jasrah
ne.
“Bari-Hamshira! Karsu kashe yarinyar mutane itama. A
daren jiya harna fara murnar ALLAH yasa zuwan wannan
yarinya alkairine garemu, ALLAH yasa itace zata zama mana
hasken da zai haska duhun dake zagaye da mu saboda ganin
rashin tsoro a ƙwayoyin idanunta, Amma yanzu a wani
ɓangaren inajin matuƙar tsoron kar muna akan dokin zaton
wuta a maƙera ne kamar yanda mutanen gari ke ma Zaki. dan
gaskiya a yanzu gaba ɗaya komai neman ƙwacemun yake....”
Wani irin rumtse idanu Malikat Bushirat tayi mai nuna
alamar jin ɗacin zancen, sai dai kuma a duba na gaskiya ƴar
uwarta gaskiya ta faɗa, kuma da itane kawai take iya tattauna
irin waɗan nan matsalar tata taji sauƙi a ranta duk da ba ita
kaɗai bace ƴar uwarta mafi kusaci. Sai dai Jasrah itace
autarsu, ta kuma rayune a hanunta tamkar itace ta haifeta,
dan haka tasan bazata taɓa jifan tilon ɗanta da sharri ba
domin taji daɗi kamar yanda maƙiyansu keyi. Ita a karan
kanta mahaifiyarsa a kullum zuciyarta takan ɗarsa mata kodai
gaskiyane da sanin bahagon ɗan nata mai wahalar sha'ani da
fahimta ake kashe yaran mutane? Saboda al'amarin akwai
matuƙar rikitarwa da ban mamaki a cikinsa, amma a yau tana
fatan a wannan gaɓar su samu wani haske.....

★★________________★

Kai tsaye sashensu na hadimai Hadimar nan ta tasa
ƙeyarta, sai dai suna gab da shiga ta hango Diwa da wasu
hadimai maza masu ƙarfin faɗa aji a cikin dogaran sashen
Malikat Bushirat suna tattaro hadimai. Da sauri taja burki tare
da damƙo hanun hadimar baya. “K dakata, bana raba ɗayan
biyu ku ake nema kuwa”. Sake ruɗewa hadimar tayi, jikinta
sai faman rawa yake gab-gab abin tausayi. “Shugaba Azwa ki
taimakeni”.
“Na taimakeki ni kuma na tozarta. Kinga Jaza babu
wannan maganar, ki ƙarasa garesu zanyi duk abinda ya dace
naga kin ƙuɓuta, sai dai ki sani zaki bani wani kaso a cikin
dukiyarki. Kiyaye harshenki akan amsa laifin dake kaɗai ya
shafa shine tseratar da kanki. Kuskuren ambaton sunana
kona uwar-gijiya shine mutuwarki”.
“Na yarda wlhy, zanma iya mallaka miki komai da nake da
su shugaba Azwa”. Jajayen haƙwaranta ta washe. Tare da
kaɗa kai tamkar ƙadangaruwar data hango mage. “Baki da
matsala, hatta ga uwar-gijiya ma zaki iya tsira, dan haka
faɗamin inda kike ajiya”. Sosai Jaza ta aminta da maganar
Azwa. Dan tasan ita ɗin amintacciyace ga uwar-gijiyar tasu.
Domin duk wani aikin sharri sune suke mata shi a cikin Daular
Ruman. Sai dai bata raba ɗayan biyu akwai ire-irensu da yawa
a ƙarkashin ikonta.....
“Yauwa ga ɗaya nan a cikinsu”.
Cewar Diwa data hango Jaza na rabe-raɓe. A take hadiman
maza suka tasa ƙeyar Jaza tare da Diwa dake biye da su. Kaf
hadiman da abin ya faru a gaban su duk da basu san ainahin
abinda ya faru ba tausayin Jaza da sanin ta shiga uku ne keta
musu kaikawo a cikin zukata......

*_MALIKAT BUSHIRAT_*

Bayan wasu mintuna da batako nuna alamar tasan da
isowar su Diwa ba ta ɗago ƙyawawan idanunta da tsantsar
damuwa ta bayyana a cikinsu. Da sauri Diwa da hadima Jaza
suka sake risinar da kawunansu jikunansu na tsuma. Kallonsu
take tamkar mai neman amsar abinda ke ranta a cikin jikinsu,
kusan minti guda da wasu mintuna ta janye a hankali ta
maida ga Jasrah, sake janyewa tai ta sake maidawa ga
amintaccen hadiminta dake buƙatar umarninta.
“Bayan mintuna goma, a tabbatarmin da abinda nake
buƙatar ji daga garesu”.
“An gama Uwa goya marayu”.
Ya faɗa da tsantsar girmamawa yana mai zabga ma su Diwa
shimfiɗeɗiyar bulalar hanunsa a gadon baya. A zabure suka
miƙe su duka suna mai sosa bayan nasu kowanne idonsa cike
taf da ƙwalla. Ƙeyarsu ya tusa suka fice, Diwa na kuka da
rantsuwar bata san komaiba ita..........✍

16


........Cikin ƙanƙanin lokaci labarin abinda ke faruwa da
Zawjata-almilki ta uku ya gama gauraye daular ruman. A take
ko'ina yay tsit sai ƙus-ƙus da maganar ido kawai. Sauran
Zawjata-almilki kuwa guda biyu dake gidan dama kafin kawo
Iffah tuni sun sake shiga tsantsar tashin hankalin da yafi
wanda suke ciki. Su dai dama rayuwa suke cikin jiran
tsammanin isowar mutuwarsu. Ko lokacin da aka sanar musu
sake ɗaura auren Tajwar da wata matar tsantsar tausayin
kansune kawai ya baibayesu, yanzu kam jin halin da matar da
aka kawo jiya take ciki ya tabbatar musu suma mutuwarsu
tunkarosu take sakeyi kenan.......

Duk wata tuhumar data dace akan hadima Jaza da
sauran hadimai biyu da sukaje ɗakin Iffah suma da aka gano
anyi amma sunƙi faɗar gaskiyar wanda ya sakasu, sai cewa
suke Diwa ce. Yayinda Diwa ke rantsuwa da ALLAH tana kuka
akan ƙarya suke mata ita bata san komai ba. Iya jigatuwa sun
jigatu har takai numfashi da ƙyar sukeyi saboda azabartawar
da ake

10 / 34