Advertisements
google.com, pub-3860387852992103, DIRECT, f08c47fec0942fa0



Follow us on social media

Facebook Telegram TikTok WhatsApp X

Dauɗar Gora Complete Hausa Novel by Bilyn Abdull Ce

Author :  Bilyn Abdull ce Category :  African Stories & Novels

Chapter   16 / 34

45K to 48K   out of 100K words

bamu san nasu shiri ba, zasu iya amfani da duk wani
yunkurinmu a yanzu. Dan haka nayi abinda ya dace bayan
barina wajen Ibrahim Askari. Akwai wani babban police dana
sani kai tsaye naje garesa, nakumayi sa'asar samunsa. Nayi
magana dashi da rokonsa ya bincika mana inda zamu iya
samun su, Alhamdullah kuma ya amsa, yanzu haka kiransa
nake jira kamar yanda yaymin alkawarin kafin cikar awa
ɗaya”.
Anan ɗin ma dai farin ciki ne a fuskokin su Kaka, sai faman
sauke ajiyar zuciya sukeyi.....
★... ★★.... ★....

Zamu iya cewa gaba ɗaya yinin yau Iffah ta kare shine a
neman number Malaminta Fawzan da abokinsa Ajmaal.
Amma abin mamaki har yamma amsa ɗaya ce layukansu not
available. Gaba ɗaya tayi firingai-firingai na damuwa, duk
yanda take ƙoƙarin ɓoyewa da danne hawayenta sai da suka
zubo bayan ta idar da salla. Bakomai yasata shiga damuwar
akan son samunsu ba sai rashin samun number Babiy da
Hanash da batai ba suma. Tana son jin wani abu game da
ahalinta, dan yawan faduwar gaban da take da mummunan
mafarki yasa tanaji a jikinta akwai matsala. Tama rasa wane
tunani zatayi, har text message ta turama Malam Fawzan
akan ya taimaketa ya duba mata iyayenta amma shiru kakeji,
bama tada tabbacin ya gani ko bai gani ba. Kuka taci sosai a
wajen kafin ta mike tana share hawaye bisa shawarar
zuciyarta. Wayar ta sake ɗauka ta sake tura sakon data
turama Malam Fawzan a layin Ajmaal abokin nasa. Tana fatan
ɗaya daga cikinsu yaga saƙon koda bata samu sauran biyan
bukatarta ba. Jikin window ta koma ta tsaya tana mai shaƙar
iskar dake busowa mai daɗi, kamar ance kalla gefe ta hango
Hadima Banou can jikin filawoyin saitin ɗakin Malikat
Haseena tsugunne kamar tana tona rami, sai faman waige-
waige take alamar rashin gaskiya. Da farko tsura mata idanu
Iffah tai, sai kuma ta zabura bisa umarnin zuciyarta. Sai da ta
tabbatar wani baiga sanda ta fito a dakinta ba sannan ta fice,
kasancewar ta naɗe har fuskarta da ɗan kwalin abayar jikinta
yasa babu wanda ya ganeta, balle abayar jikin nata ɗaya daga
cikin natane na gida data canja bayan barowarta wajen
Malikat Haseena. Da ƙyar ta gane hanyar dazata ɓulla bayan,
dai-dai Hadima Banou na ƙoƙarin maida kasar data tone
alamar harta saka abinda zata saka. Sauri-sauri takeyi harta
kammala, ta ɗago da nufin barin wajen taja ta tsaya a kiɗime
ganin mutum tsaye a bayanta. Amma kasancewar ta mai
shegen tsurin ido sai ta dake a zahiri tana kallon Iffah da har
yanzu bata janye mayafin data yane har fuskar ba....
“K! Ubanwa ya kawoki nan?”.
Ta faɗa da zaton cikin hadimai ne irinta. A hankali iffah ta
karasa takowa gabanta, tare da janye mayafin ta saka
idanunta cikin nata jajaye marasa ƙyan gani. Sosai hadima
banou ta rikice har rawar jikinta ya bayyana. Iffah ta janye
idanunta daga kanta ta maida akan ramin,
“Mi kika binne?”.
“Ranki ya daɗe babu komai, w... W... Wani magani ne kawai
da nake son yin amfani da shi.....”
“.....Shine kika shuka shi anan cikin rashin gaskiya? Wacece
ke? Mi kike kullawa”.
Tambayoyin sunma Banou yawa da tsauri wajen bada
amsa, a take ta sake gigicewa duk da tana ƙoƙarin ƙirƙirar
jarumtar dole. Wuceta Iffah tai zuwa wajen ramin, ta
tsugunna da daukar iccen datai tonan da shi ta shiga sake
tone kasar da Bismillah. Firrr wani abu kamar tsintsuwa ya
fito a ramin yay sama. Iffah ta mike da sauri ta bisa da kallo
harya bace. Juyawa tai da sauri inda Banou take, dai-dai ko
tayi shirin silalewa tabar wajen ta dakatar da ita.
Ƙasa tai da kanta jikinta na matukar rawa, Iffah ta kare
mata kallo sama da kasa na wasu sakkani, sai kuma ta girgiza
kai. “Wani asirinne haka bizne tsuntsuwa da ranta saboda
son zuciya? Ko wani ya sakaki biznewar saboda ya isa?
Kokuwa ke ɗin kina a cikin jinsin Mayu ne? Dan a cikin ukun
nan dana lissafa dole ne a samu ɗaya tattare da ke tsohuwa”.
Kuka Banou ta fashe da shi gwuyawunta a ƙasa. “Ranki ya
daɗe ban fahimci abinda kike nufi ba, nifa magani na shuka ki
yarda dani”.
“Uhhm wato magani kika shuka, tsohuwa kalleni da
kyau ki ganni banyi kama da wanda akema rufa ido ba, amma
zan baki lokaci kije, zan nemeki a lokacin daya dace. Idan kika
hangi gudu baki da wajen iya ɓoye min, idan cutar dani ne
zagaye nake da kariyar UBANGIJINA, idan yunkurin salwantar
da rayuwarkine idona biye yake dake tako ina. Shawara ya
rage gamai shiga rijiya”.
Da wani irin mummunan kallo hadima banou tabi bayanta
da shi, ta cije baki da rumtse jajayen idanunta da karfi.........✍️

🤔 Wannan ƴa ta Babiy ƙarfin halinta da tarar aradu sun
mata yawa. Dole dai sai ta kai kanta inda za'a lamushete oh ni
Balki😜
.

24


..........Komai daya faru tsakanin Iffah da Hadima Banou akan
idon Daneen Ammarah ne, dan itama tayi yunƙurin fitowar
ne ganin Banou na tono a bayan windown Mamman sai ta
hango Iffah na tahowa. Kasancewar ta ganta da rigar jikinta a
ɗazun yasa kai tsaye ta ganeta. Da farko gabantane ya fara
faɗuwa da tunani iri-iri, shiyyasa ta tsaya domin ganema
idanunta. Sai dai kalaman Iffah da yanayin Hadima Banou ɗin
ya sata shiga ruɗanin tunani. Idan har zata auna da
hankalinta matsayin babba itama Iffah taga Hadima Banou ne
shiyyasa ta fito, a yanayin Banou kuma ya nuna akwai wani
ɓoyayyen al'amari na rashin gaskiya tattare da ita. To amma
su maiyasa a tsahon shekaru basu taɓa ganin wannan fuskar
ta Banou ɗin ba? Wacece Iffah? Anya kuwa ba akwai abinda
ya kamata ta sani dangane da yarinyar nan ba?......

★Iffah da al'amarin wannan masarauta ya fara ruɗama
tunani tana shiga ɗakin dake matsayin nata yanzu ta murza
key. A jikin ƙofar ta jingina da lumshe idanunta tana sauke
numfashi. Ita kanta taga ƙarfin halinta yau, dan zata iya
rantsewa bata san a ina ta samo wannan jarumtar ba. Idanun
ta buɗe tare da riƙe ƙugu ta karyar da kai alamar nazari. In fa
har ta canka dai-dai tabbas wannan hadimar mayya ce. Dan
bata manta da wani labari da Iyyani ta taɓa basu ba na mayya
yar Danƙo datai zamani a kauyen jumna shekarun baya. Babu
banbanci da abinda taga matar nan tayi yanzu, dan da alama
kurwar wani ta laso tazo ta boye a wajen. “Bahun ubancan,
eh da gaske dai ashe lamushe ƴaƴan mutane ake a
masarautar nan tunda ga alama harda su bayi an barbaɗa
musu muguwar tambaya. Shi baƙin babban dodon nasu
nacinye mutanen gari su kuma bayi nacinye junansu a cikin
gida”. Tai maganar a fili cikin ƙankance idanu na alamar
tunzuruwa...
Murmushi Daneen Ammarah dake bakin ƙofa tsaye ta
saki, dan nutsuwar da zuciyarta ta kasa mata ya sata biyo
bayan Iffah, har ta kai hannu zatai knoking sai kuma ta fasa
da tunanin inhar Iffah nada wani mugun nufi a kansu to baro
can zata samu wani abun take aikatawa a yanzu. Dan haka ta
ɗan kara kunenta kaɗan jikin ƙofar, cikin Sa'a kuwa ta jiyo mi
Iffah ta faɗa saboda yanda tai maganar da ɗan zafi sai ta fita
da ɗan karfi kaɗan. Ƙofar ta fasa bugawa ta koma ɗakinta da
baya. Itama dai ƙofar tata ta sanyama key duk da tasan babu
wanda zai shigo mata. Kai tsaye wadrob ɗin ta ta nufa, a cikin
wani akwatin ƙarfe karami mai ƙyau ta fiddo waya bayan ta
danna madannan sirri ya buɗe. Wayar ta shiga ƙoƙarin
kunnawa tana mai rufo windows ɗin ɗakin nata. Sai da tai
danne-danne kusan na mintuna biyu alamar text ta tura. Kira
ne ya shigo, sai a ring ɗin karshe ta ɗaga, batare da jiran wani
gaisuwa daga wancan ba cikin bada umarni tace,
“Daga yanzu zuwa safiyar gobe idan ALLAH ya kaimu ina
buƙatar sanin komai akan Zawjata-almilk ta uku. Idan nace
komai yana nufin komai da komai”. Kitt ta yanke kiran tana
wani irin murmushi tun kan ma ta samu amsar data bukaci
sani. Wayar ta kashe gaba ɗaya ta sake maidata inda ta
dakkota......

(🤔Wai su kowa da tasa manufar ne????)

*_MALIKAT BUSHIRAT_*


Zaune take hakimce kamar ko yaushe cikin kwalliya mai
matukar ɗaukar idanu. Ga wani sihirtaccen ƙamshi mai ratsa
zuciyar duk wani mai shaƙa na tashi. Shi kansa falon
kamshinsa na musamman ne. Gefenta na dama Jasrah ce
itama cikin kwalliyar, zuwanta kenan sashen sakamakon
aiken data samu daga ƴar uwar tata. (Itama dai Jasrah anan
cikin masarautar take aure, tana kuma auren ƙanin marigayi
Tajwar Haysam ne da suke uba ɗaya. Dan kamar yanda
Tajwar Haysam suke su huɗu a ɗakinsu suna kuma da ƴan
uba har su kusan tara, sai dai mata sunfi yawa a ciki. Su
tarannan kuma ƴaƴan mata uku ne. Mijin Jasrah shine babba
a cikin ƴaƴan amaryar Tajwar Haysam da ake kira Ameera
Aasfah a masarautar. Mace ce mai kirki da sanin ya kamata,
jininsu kuma yay matuƙar haɗuwa da Malikat Haseena. Dan
idan ka gansu bazaka taɓa ɗauka kishiyoyi bane a sanda tana
raye. Yaranta biyune ita kacal, Miran Arshaan shine babba,
shine kuma ɗa na takwas a wajen Tajwar Abdul-majeed, a
maza kuma na uku, shine mijin Jasrah a yanzu, sai ƙanwarsa
Daneen Fu'ada, a yanzu haka tana aure itama. Ƙaunar dake
tsakanin Malikat Haseena da Ameera Aasfah yasa shaƙuwa
sosai a tsakanin ƴaƴansu, hakan yasa Tajwar Haysam ke
kallon Miran Arshaan tamkar ƙaninsa Miran Nayyar daya
rasa, shine ma da kansa ya aura masa Jasrah. Wannan kenan,
ALLAH yasa kun gane🥱).
“Akia kince nazo amma kin kasa cewa komai? Wani abun
ya sake faruwa ne?”.
Numfashi Malikat Bushirat ta sauke a hankali tana kallon
ƴar uwar tata da takema kallo tamkar first born ɗin ta. Kamar
bazatai magana ba sai kuma ta nisa cike da kasaita. “Komai
bai sake faruwa ba, sai dai ina gudun sake faruwar. Sanin
kanki ne Jasrah ba lallai kosu waye su haƙura ba dan yarinyar
nan ta kuɓuta a yanzun, sannan ma bayan ita akwai sauran
yaran biyu da har yanzu fargaba ta hanamu kaisu turakar
Saifulmalik. Kin san kuma rashin kai su zuwa nan da ɗan
lokaci sai kinji an fara kace-nace”.
“Hakane Akia. Amma ke mikike son cewa?”.
“Zancen dai ɗaya ne shine inajin tsoro, na biyu kuma da
gaske yarinyar nan ta shiga raina fiye da duk matan da aka
kawo gidan nan matsayin Zawjata-almilk”.
“Wlhy nima har cikin rai yarinyar ta shiga raina. Gata da
tarbiyya daga ganinta, sannan itace mafi ƙanƙanta a duk
matan na Son”.
“Wannan yana ɗaya daga cikin abinda ya sake jan
hankalina a kanta Jasrah, shiyyasa yanzu da wani tunani yazo
min nace bara nai shawara da ke. Shin kina ganin naima
Mamma (Malikat Haseena) magana gobe idan ALLAH ya
kaimu da Saifulmalik zaije gaisheta a kusanta shi da yarinyar
nan suga juna? Sai nake ganin hakan zai canja wani babban
al'amari da masu mana yankan baya ke ƙullawa. Tunda kinga
dai duk matansa sai an kaisu turaka yake da damar ganinsu
kamar yanda kowa yasan dokar kenan ga duk Zawjata-almilk
tun ƙarnin baya”.
“Eh gaskiya kuma wannan tunani ne mai ƙyau Akia inhar
Mamma zata amince ɗin. Dan Kinga muma a karan kammu
wata hanya ce da zamu fuskanci wani abu akan shi kansa..”
“Wannan gaskiya ne. Dan da gaske Jasrah a yanzu har shi
kansa zuciyata rawa take ga al'amarinsa, dan abinda ke
faruwa dole ne kowa ya zama abin zargi har mu kammu, ke
nama takaice miki zance ni kaina yanzu ban yarda da kaina
ba”.
Murmushi Jasrah tai har haƙoranta na bayyana. Tace, “Kai
Akia kinada abin dariya wlhy wani lokacin. To inke baki yarda
da kanki ba mu kuma dawa zamu yarda kenan?. Kawai dai
inaji a jikina koma minene ya kusa zuwa ƙarshe ta silar
yarinyar nan tunda har ALLAH ya fara nuna musu iyakarsu
suka gaza cin nasara a harin farko da suka kai mata. Yanzu dai
bamu da lokaci, ki tattauna da Mamma ɗin kawai. Hukuncin
data yanke sai mu karɓa kawai”.
Malikat Bushirat ta jinjina kai kaunar ƴar uwar tata na sake
ratsata. Koba komai idan ta tattauna da ita takanji sanyi a
ranta.......

★★.... ★.... ★★.....
“Wai nikam ɗazu ina ƙoƙarin shiga fada naga kamar motarki
ta gitta, kinje wani waje ne?”.
Shayin da take ƙoƙarin zuba masa ta karasa tare da miƙa
masa. Sai da ya amsa ta koma ta zauna tana mai ɗan ɗage
kafaɗunta. “Kaima kasan fita ta bata wuce wajen Akia ai Abu
Harith, wlhy itace fa tai min kiran gaggawa shine ka ganni na
fitan. Amma lafiya kuwa har irin wannan lokacin kuna a
fada?”.
“Uhm to lafiya lau za'ace, anyi baƙin bazata ne kawai ga
Shahan-shan ya rigada ya shige kuma. Dole mu mukai zaman
tarbarsu. Amma kiran gaggawa wata matsalar ne ta sake
faruwa? Ko jikin Zawjata-almilk ɗinne dai?”.
“No akan dai wadda ake cikine. Jikinta kuma Alhamdullah,
idan ma ka ganta yanzu bazakace wani abu ya faru ba. Kawai
dai Akia ce ke ganin ya kamata idan Shahan-shan yaje gaida
Mamma gobe idan ALLAH ya kaimu Zawjata-almilk ta
ziyarcesa ko hakan zai kawo wani sauyi kan abinda har yanzu
muka kasa sanin kansa”.
“Amma baƙwa ganin hakan wani ganganci ne? Sannan
dokace fa Shahan-shan baya ganin matansa sai a turaka”.
“Eh muma mun duba wannan ɗin, dan haka ma bamu
wani yanke shawara ba akace sai an sanarma Mamma. Amma
kai ya kake gani akan hakan. Abu Harith wlhy Akia na bani
tausayi matuƙa, a yanzu har takai da kanta itama zarginsa
take shi yake ɓarnar nan”.
“Ya ALLAH wannan wace irin magana ce haka? Miyasa zatai
irin wannan tunanin akan ɗanta. Bana jin Eshaan zai taɓa
aikata makamancin hakan. Kawai dai akwai abinda yake ba
daidai ba”.
“Sosai kuwa. Amma insha ALLAHU ta sanadin yarinyar
nan kowa sai yaci ƙaniyarsa. Dan haka kawai nakeji a jikina ita
ɗin haske ce a wannan daula. Tunda har gashi ta karya tarihin
farko na azzalumai”.
“Haka muke fata, dan muma an tattauna akan hakan sosai
jiya da yau a fada. Kusanma issue ɗin da ake kai kenan kawai
yanzu a majalissa. Sai na kisan hadiman can”.
“To ALLAH ya dafa mana mu da ku, ya kaimu ranar da
zamu ga iyakar wannan al'amari”.
“Amin my meera”.
Yay maganar da wani salon kashe ido mai cike da soyayya da
kaunarta. Murmushi tayi itama tana miƙewa, “Bara na kimtsa
kafin ka kammala ko”.
Kai ya gyaɗa mata idanunsa narke a kanta.. Tana juya
baya ya bita da wani irin matsiyacin kallo mai ma'anoni da
yawan gaske yana tsuke fuska da jan tsaki......


🤦Jasrah kamar yanda ƴar uwarki ta faɗa miki kowa ba
abin yarda bane yanzu🧐.

★★.... ★★.....

Kamar yanda Malikat Bushirat suka tattauna da Jasrah batai
ƙasa a gwiwa ba tana idar da sallar asuba ta fita daga
sashenta cikin badda kama zuwa sashen Malikat Haseena.
Kasancewar ta sanarma Daneen Ammarah tare suka nufi
ɗakin Malikat Haseena ɗin. Itama tasan da zuwan Malikat
Bushirat ɗin. Dan haka basu ɓata lokaci ba suka fara
tattaunawa dan ta samu ta koma kafin gari yay haske. Da
farko dai malikat Haseena ta kakkawo musu dokokin
masarautar masu tsari dangane da haɗa Shahan-shan da
Zawjata-almilk kai tsaye ba'a turakarsa ba. Sai dai bayanin da
sukai mata da nusar da ita abinda suke son tabbatarwa yasa
itama ta amince. Sai dai da sharaɗin komi ya biyo bayan
hakan laifinsu zata gani. Cike da yaƙinin fatan karma wani abu
ya faru suka amince. Dan haka tai musu sallama ta koma.
Daneen Ammarah da tunaninta nada banbanci da na Malikat
Bushirat akan wannan haɗuwa tai murmushi a ranta tana mai
addu'ar samun nasara. Domin wannan yaƙi kamar natane ita
kaɗai sakamakon itace kawai tasan ɓoyayyen sirrin daba
kowa ya sani ba sai UBANGIJIN talikai. Fatanta shine komai
yazam yana gangarowane ga faɗan karshe akan maƙiya koda
ita zata rasa rayuwartane a yayin gumurzun...


(Daneen Ammarah kin fara bani tsoro fa).
😞

*_SHAHAN-SHAN_*

Yau ɗin ce dai ta kasance rana da yake zuwa gaishe da
kakarsa Malikat Haseenah. Irin wannan rana kuma tana
zuwane sau ɗaya a kowanne wata. Sai dai idan ita ke buƙatar
ganinsa ta samesa a sashensa. Amma a kowane wata yanada
ranaku biyu na ziyartar kakar tasa da mahaifiyarsa. Malikat
Haseena yake fara dubawa a farkon wata, Malikat Bushirat a
tsakkiyar wata. Duk da fitace ta dare da ba lallai kowa ya
gansa ba ya kasance cikin shiri mai ɓoye ainahinsa, ga wani
ƙamshi na isassun da suka isa na tashi tattare da shi. Takunsa
da ƙarfin izzarsa ya isa tabbatar maka eh lallai Shahan-shan
ne da kansa. Ƙasaita jinin jikinsa ce, kamewa da isa adonsa
ce, kwarjini da nutsuwa halittarsa ce....
Duk da farkon dare ne dan kwata-kwata ƙarfe takwas ne,
amma masarautar tayi tsit kowa ya nutsu a inda ya dace
saboda sanin wannan rana ce da Shahan-shan ke fitowa zuwa
sashen Malikat Bushirat. Babu wani Hadimi dake kai kawo sai
Ghazi da masu tsaro da suka tsare ko'ina fiye da kullum.
Hakama sauran jama'a in ba babba mai faɗa aji ba babu
wanda keda hurumin wani kaikawo a irin wannan daren dake
zuwa a wannan rana saboda fitowar Shahan-shan...........✍️


********************************************
Visit http://novelselite.com.ng for more books

About Novels Elite
Novels Elite is a website consisting of Hausa Novels Books
such as Text, Documents, Audiobooks, and Videos, the
purpose of creating this site is to Entertain, Motivate and
Educate our readers.


Novels Elite provided so many kinds of Hausa Novels of any
type, Such as Adventure, love, romance, fiction, non-fiction,
mystery, fantasy, action e.t.c.

We provided a new and old novel as softcopy from our
Authors with their permission

Zaku iya samun mu a kafafen sada zumuunci kamar haka:

Facebook: Novels Elite
Youtube: http://youtube.com/@novelselitetv
***********************************************
25


.......Turus Jasrah tayi ganin babu Abu Harith a inda ta barsa.
Sai kuma ta nufi ɗakin barcinsa da tunanin koya shige. Nan
ɗin ma dai babu alamarsa har cikin bathroom. Batare data
kawo komai a ranta ba ta ɗan ɗage kafaɗa ta fito.

★Shi kuwa da tun bayan ficewarta ta ɗazun da kamar
mintuna uku ya fice cikin ɓadda kama ya nufi sashen Miran
Jasim. (Miran Jasim ɗane a wajen Ameera Banafsha, matar
Tajwar Abdul-majeed ta biyu, shine ɗa na huɗu a wajensa, a
maza kuma na biyu. Miran Arshaan ke bi masa. Sam babu
jituwa tsakanin Ameera Banafsha da Malikat Haseena, ko
mutuwar Miran Nayyar an dangantata da Ameera Banafsha a
wancan lokacin. Sai dai da yake yaƙin sunkuru ne tsakanin
matan biyu duniya bata san da haka ba. Burin Miran Jasim
shine mulkar kujerar Shahan-shan tun

16 / 34