Author : Hadiza D Auta Category : Romance
waje ita kuma ta ce ba za ta fita ba ya shigo falo.
Ya sassauta ya ce "Su Baba na ciki fa!
A gajarce ta ce"Bamu da gaskiya ne? Sannan Baba na ciki Momi kuwa ba fitowa zata yi ba".
Ganin ta dage tana jero masa hujjoji ya fahimci ba zata fito su zauna a harabar gidan ba. Dan haka ya shiga falon da shine farko a gidan.
Kunyar Baba da Momi yake ji amma tunda haka Maigado take so, dole ya bi ra'ayinta tunda shawo hankalinta yake yi.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 11:43]
Ya jima yana zaune, yana yi yana duba tsadadden agogon da yake daure a hannunsa ƙirar Rolex.
Yana tunanin yadda mata suke son shanya masoyansu da sunan jan aji.
Mintina kusan talatin yana zaune shi kad'ai yana dakonta. Ban da rashin mutuncin soyayya ya za'a yi yarinya kamar Bilki ta dinga yi masa haka. Shi da idan yana cikin kakinsa dubban zarataan maza suke kame masa tare da sara masa. Amma ita ganinsa take yi tamkar takalmin sawarta.
Ya numfasa a fili ya ce "Mata ne jarabawar mazaje a duniya". A hankali ya dinga jiyo k'amshinta na turaren oils na mkbees perfumery da baya jinsa a ko ina sai wajenta na iso shi kafin ya jiyo sautin takunta cikin nutsuwa.
K'amshin ya yi matuk'ar saukar masa da kasala da bege.
A ransa yake fad'in Ko ina take samo wadannan turarukan?
K'amshinta na sake mayar da ita yar gayu ta sosai.
Mkbees perfumery na kawo muku oils perfumes masu matuƙar dad'i da Zama a jiki.
Mkbees sun yi fice wajen sanin sirrin gayu don kuwa kamshine Kan gaba wajen mayar da mace mai aji.
Mkbees Perfumery .Kano 07032456061
A hankali ta iso ta zauna bayan ta yi masa sallama a hankali. Ba ta yi masa magana ba sannan ba ta kalle shi ba ta juyaar da fuska tana tura baki.
Shi kuma ya shagala da kallon ta domin ta yi kyau sosai sai tashin kamshi take yi.
Material din Malaysianfabrics da take gown da su suna matuk'ar yi mata kyau.
Bai san ya shagala da kallonta ba sai da ta ɗan kalle shi kafin ta ce" Ni don Allah ka daina yi mini wannan kallon bana so."
Ta faɗa cikin yar shagwaɓa kamar wata yarinya.
Gabad'aya duk ta sukurkuta shi, ya neman rasa yar natsuwan shi.
"Mai gado kin yi kyau ne. Kamar na sace ki zuwa gidana."
Harararsa ta yi ta gefen ido, tare da juyar da manya idanuwanta . Hakan ya kara masa nishaɗi. Ya yi dariya ya ce
"Ko yau Baba ya ɗaura mana aure kawai Maigado?
Ta kalle shi da mamaki amma bata ce komai ba .
"Allah Maigado ina cikin tsananin buk'atar na yi aure. Kin san ni ba yaro ba ne, na dad'e ba na tare da mace, ke ma kuma a irin takalmina kike ko?"
Ya faɗa har yana rage murya.
Kunya ya kamata ta yi maza ta yi k'asa da kanta kafin a hankali ta ce " Ni ba ruwana"
Dariya ya sake yi kafin ya ce" Da ruwan ki kuwa Maigado".
Shiru ta yi masa yana ta sakin layi, wanda mamaki yake ba ta, ko kunya ba ya ji daman haka yake? Yaya Asad ne a gabanta yana kunyata ta amma shi ko a jikinsa, kai maza da abin kunya suke.
Kan dole take zaune yana ta kunyatata.
Ita ke jin kunya amma shi ko a jikin shi.
Suna cikin haka Baba ya fito zai fita tattakin da yake cikin unguwar da yammaci, ya gansu a falo, ya kalle su ya yi dariyarsu ta manya kafin ya ce" A a garin yaya haka Asad ka zo zance gidana amma ba ka nemi izinina ba?"
Ya fada yana mai bayyana murnar ganinsu har a saman fuskarsu.
"Baba Faruku ne ya ba ni izinin zuwa, har aurenma ya ce ya ba ni."
Baba Babba ya yi dariya kafin ya ce" To to haka aka yi? Lallai kuwa tunda Faruku ne ya baka to Bilkisu ta badu babu tantama. Dole kuwa ka ce masa Baba ".
Shi da Yaya Asad suna ta dariya Bilki ta yi gum fuskarta a k'asa nan Baba ya fita haraban gidan ya bar su. Ya Asad na cigaba da zolayarta idan ta turo baki sai ya ji ya fara mazari kamar ya kamata ya matse ya tsotsi bakinta amma ba hali sai dai yana fatan lokaci kaɗan ne zai yi hakan ta halastaciyar turba.
Haka dai aka gama zancen tana ɓata fuska da zai tafi ya ce su je mota ya bata sako, dole ta bi shi ya bata leda cike da kayan kwalliya da dogayen riguna, ta karba tana godiya ya shiga mota yana fadin" Maigado ki bar tura baki kwana nawa ne? Ni fa ko yau aka daura na shirya "
Nan ta bar shi yana ta kiran sunanta ta yi bakam ta wuce cikin gidan, don tasan yana yanko mata zancen da sake kunyata ainun.
Da daddare tana kwance Farha na gefenta tana barci. Ya k'irata ta saka hannu ta dauka tare da sallama.
A hankali ta ce "Ka je gida lafiya?" Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 11:53]
A sanyaye ta ce"Hakane Baba amma dai ka sanar masa din zan fi samun nutsuwar zuciya."
"To Zan fad'a masa a yau din nan Maigado ".
Ta Numfasa ta sake ce wa "Sannan dan Allah Baba zan je Katsina na bar kayayyakina masu muhimmanci a can, ina son na je na harhadasu tunda muka taho gidan a rufe yake".
"To shike nan zan yi magana da Faruku sai ya kai ku tare da Alti ku yi kwanaki biyu ko uku".
Daga haka sallame ta yana cigaba da yi mata addu'o'i masu dadi da sanya farinciki.
Kwance yake kan tafkeken gadonsa yana waya da babbar diyarsa Aysha da take shirin kammala Bar school ta Enugu.
Cikin nutsuwa ya sanar mata upper week zai tafi America daga can zai biya London ya ga Khadija.
Juma'a mai zuwa kuma zai daura aure.
Zuciyarta ta harba da tsananin gaske.
"Aure Daddy! Da wa kuma?"
Ta tambaye shi a rude don har cikin zuciyarta ta ji wani irin kishi mai tsananin gaske ya shak'e ta gabad'aya.
A hankali ya ce mata da "Anti Maigado ".
Ta yi shiru tabbas watanni biyu da suka shud'e ta tarar da ita a gidan Momi. Ashe aurenta ne ya mutu ba wai jinya kawia take yi kamar yadda Anti Abida ta fad'a mata ba?
A sanyaye ta ce "Amma Dady su Mama ba sun ce sun baka Anti Laura ba?"
Da sauri ya ce "Ai na fad'a musu ba zan iya aurenta ba domin kallonta nake yi tamkar yarinyar da na haifa. So ba zan iya aurenta ba".
Ta kasa magana amma tabbas ba ta ji dad'in hakan ba. To Akan me ma zai sake aure yanzu shekara d'aya kacal da mutuwar mominsu!
Kan dole ta ce "Allah ya sanya alheri. "
Ya amsa da "Ameen"
Ya numfasa ya ce "Ina fatan babu matsala ko damuwa?"
A hankali ta ce "Babu komai Dady".
"Stay blessed sai mun sake magana".
Da ga haka ya katse wayar.
Jikin Aysha ya yi mugun sanyi bata san dalilin da ya sanya ta ji wani abu ya soke ta da ya ce 'Anti Maigado zai aura ba'.
Kamar yadda Baba ya fad'a yaya Farouk ya kaisu Katsina. Farha tana ta murnar zata ga su yaya Farouk. Kaitsaye gidanta suka yada zango. Komai tsab sai dai gidan ya yi kura. Cikin gaggawa Alti ta hau gyaran gidan tamkar ba gajiyar tafiya a tare da ita. Sai da komai ya yi daidai sannan ta D'ora girkin abin da zasu ci. Nan da nan gidan ya kaure da k'amshi. Daidai lokacin Yaya Farouku ya dawo daga masallaci. Ya zauna a falon ya bude murya ya ce "Alti saboda Allah da wanne irin abu kike girki ne? Gabadaya layin ya cika da k'amshin girkin dan Allah fad'a mini abin da kike zubawa Idan kina girki dan na siyawa Jamila, don k'amshi da nake ji a gidana idan ana yin girki bai haka dad'i da k'arfi ba, tunda na doso kusa da gidan fa hancina yake shakar k'amshin dad'i ".
Ta fito da robar curry da spice's din Amreesh spice's Kano ta ce "Ga wasu da Ga cikinsu tafi da su a fara yi maka don nasan Mahma zata siya amarya package".
.......
Ya kwashe da dariya yana fad'in "Ashe haka Alti ta iya turanci ban sani ba?"
Ta koma kicin ta kawo musu abinci falo sannan ta shige d'akinta don ta yi wanka da sallah.
Cikin nutsuwa Bilki ta zuba masa ta saka cokali ta ba shi sannan ta zubawa kanta. Farha tuni ta yi barci don Indomi aka fara dafa mata tana ci kuwa bata jima ba ta yi barci.
Ya kammala cin abincin da ya yi masa kyau a ido, ya cika hancinsa da k'amshi, ya yi masa dad'i a baki. Ya nisa ya ce zan saka kudin spice's din nan a asusunki sai ki yi muku order tare da Jamila."
A nutse ta ce "To". Ko godiya ta kasa yi masa don haka siddan ta ji wani irin abu ya turnike ta mussaman da yake ta ambaton sunan matarsa da son sai dandanon girkinta ya yi irin nata.
Daga haka ya mike ya yi mata sallama zai tafi masaukinsa ya huta shima.
"Idan Alti ta fito ki ce mata na tafi sai gobe zan zo da rana dan haka kada ta yi abin karyawa da ni".
"Allah ya kaimu ka huta gajiya". Bilki ta fad'a a takaice tana jin haushin Jamila da na Yaya Asad na kutsowa tunda ga k'asan zuciyarta. Don tabbas sune mutane biyu da suka yi mata shamaki da samunsa. Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 11:55]
Ya fita bai sake ce wa komai ba don ya lura so take ta hargitse tunda suka iso komai yake neman k'wace mata.
Tana jin sautin takunsa a kafar bene ta ja dogon tsaki tare da fad'in "Yan ta'adda kawai masu son kansu"
Daidai lokacin k'iran gogan nata ya faɗo wayarta. Tana kallo har ta katse bata d'aga ba don sosai ta ji haushinsa ya dirar mata. Sai dai cigaba da kiran ya yi, akan dole ta dauka ta yi sallama murya a mak'oshinta.
Yayin da hakan ya jefa Asad cikin wani irin yanayi.
Ya yi k'asa da muryarsa ya ce"Ba ki da lafiya ne?"
ke nan?".
"Lafiyata k'alau".
Ya nisa ya ce Saboda Allah Maigado za ki yi tafiya sai dai na ji a bakin Farouku. Da safe ma mun yi waya na ji alamun a mota kike, na tambaye ki, inda za ki je kika ce wajen aiki, ashe Katsina za ki tafi shine ban isa ki fad'a min ba ko? Amma ni da zan taho Lago din nan sai da na fad'a miki tun ana gobe zan tafi, ina cikin jirgi kafin na tashi ma sai da na sanar da ke ".
Haka kawai ya fad'a ta ji ta harzuk'a tunda dama haushinsa da na Jamila ke ciciiyarta a daidai lokacin.
Dan haka ba tare da ta tauna kalamanta ba ta ce "Amma ai ban rok'e ka, ka fad'a mini ba, sannan akan me duk abin da zan yi sai na fad'a maka?".
Jikinsa ya yi sanyi k'alau tare da tunanin ko ya yi mata wani abu ne?
A sanyaye ya ce "Me yake faruwa ne Maigado?".
"Kamar na me fa?"
A hankali ya ce "Sai da safe".
Ba tare da ta amsa ba ta yi maza ta riga shi katse wayar.
Yana kwance shi kad'ai kan makeken gado na alfarma cikin tsadadden hotel a birinin na Ikko.
Ya yi sororo da waya a hannunsa a fili ya ce "Tooh! Zuciyarsa na bugawa tare da kitsa masa ta je Katsina ta ga mijinta da ya'yanta shine zata birkice ta nemi juyawa maganarsu baya? Ban da haka bai ga dalilin fishi da fisgar da ya ji a tare da ita ba.
A fili ya ce "Allah ka k'addara mini auren yarinyar nan, Allah ka sa rabona ce".
Don gabadaya hankalinsa ya yi mugun tashi. Tunda yasan ba sonsa take yi ba komai na iya faruwa.
Tun Daren suka yi waya da su Amrah ta fad'a musu ta zo garin.
Sassafe Babansu ya dawo daga masallaci Amrah ta tsaya a falo. Ta gaishe ta ce "Dady dan Allah anjima ka kaimu wajen Mahma ta zo kuma ta ce ba zata dade ba, zata juya".
Daidai lokacin Faruk ya shigo falon.
Da sakakkiyar fuska ya ce "To ku shirya tunda hutu kuke yi anjima zan kai ku ranr da zata tafi sai ku dawo".
Dad'i ya kamasu suke ce "Mun gode".
Ya haye sama don yanzu kan dole idan ya dawo masallaci yake hawa saman tunda Hawwah ta kafe kwana Kawai zata yi a k'asa amma ba zata yarda ta dinga biyo shi da abinci ko wani abu daban k'asa ba tunda bata d'aki a gun. Dan haka ya amince dan ra'ayinta tunda ya kafe k'asa na y'ayansa ne ba mai takurasu kuma ba zasu dinga kwana su kad'ai ba. Dan haka itama ya lallaba yake bin ta saman da zarar ya dawo daga masallaci da asuba don su samu daidaita a tsakaninsu.
K'arfe takwas sun gama shirya ko barcin safe basu koma ba. Gabaɗayansu zumundin ganin uwarsu ya dabaibaye zuciyarsu. Farouk ya kalli Amrah ya ce ",Yaya ai dai bana yi miki rashin kunya ko?"
Dariya kad'an Amrah ta yi ta ce "Yaushe rabon da ka ce mini Yaya Farouk?"
Ya yi dariya kad'an ya ce ",Saura ki je Ki faɗawa uwata zancen da zai dame ta".
Amrah ta kalle shi ta ce "Me zan fad'a kuwa da zai dame ta ?"
Ya make kafada tare da fad'in "Idan kika ce bana magana da anty ta yi mini fad'a Allah muka dawo ke ma daina kula ki zan yi".
Ta jijjiga kai tare da fad'in"Tun yanzu daina kula ni kawai".
Ya yi dariya ya ce "Don dai bana son ki yi kuka ne".
Itama dole ta dara don ya bata dariya sosai.
Ta shiga dakinta ta fito da yar jaka Karama mai kyau d'auke da kayanta set biyu ta ce "Za ka dauko kayan naaka na saka maka ko kuwa?"
Ya make kafaɗarsa ya ce "Ki je d'akin nawa ki dauko mini idan ba haka ba, da iya na jikina zan je sai na ga wa za'a yiwa fad'a a tsakaninmu."
Ta kalle shi ta ce "Allah ya shirya ka Farouk ". Save Restricted Contents Bot, [Sep 12, 2025 at 11:58]
Sannan ta wuce zuwa d'akin nasa don idan bata d'auko masa ba haka zai tafi, kuma ita Mahma zata yiwa fadan ba ita ce babba ba. Yayin da shi kuma yake tsaye rungume da hannuwansa yana yiwa kansa waka wai shi Yayan Mamah mai kafaciti dole a bi shi".
Amrah ta fito ta ce"Ka daina cika bakin dole na bika. Kawai tausayinka nake ji".
Ya k'yalkyale da dariya yana ce wa "Yayan Mamah ba abin tausayi ba ne Haj Amrah".
Dolenta ta k'yale shi don masu gidan ma hakuri suke yi da shi, don su ba ya kula su, tsakaninsa da su gaisuwar safe, sai ko idan zai faɗawa Babansu zai sayi abun makaranta. Amrah dai yake mu'amala da ita kawai.
Basu da wata babbar matsala a gida don su kad'ai suke rayuwa a wajensu, da daddare kuma iyayen su sauko su kwana. Sun sake samun saukin matsala ne da mijin Alawiyya ya dawo da ita cikin Katsina.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Kuma basu da nisa da unguwarsu. Dan haka duk sati suke zuwa gidanta Su yini, mamarsu ta turo musu ita da Amrah su yi samosa da springrols da numa meatpie sai Su tafi da shi su saka a fridge. Duk sadda suke so sai su soya abinsu. Sosai Alawiyya take kulawa da su dan har gidan take zuwa jifa jifa tana yiwa wajensu kyakkwan gyara. Dan haka basu wani tagayyara da yawa ba, mussaman da Hawwah ta kasa samun tasirin da zata
dakile hankalin ubansu a kansu. Tun Bilki bata dad'e da barin gidan ba ta fara cin karo da matsaloli da ashe zaman Bilkin a gidan ne ya hana ta lura da su.
Lafiya take zaune da mijinta amma kuma babu wannan rawar jiki da tarairayar da ya dinga yi mata a watannin farkon na zamansu. A da kafin ta bukaci wani abu sai dai ta ga ya kawo, yanzu kuwa sai ta yi ta fad'a kafin ya samu sukunin siyowa. Sannan su yaya Turai sun koma suna jan kunnen mijinta akan lallai ya saka ido akan ya'yansa kada ya bari su yi kukan rashin wani abu tunda uwarsu da take nan ba abin da bata yi dan ta rufa masa asiri ba. Tuni sun fahimci Bilki ce ta sanya gidan Sahal ya zama gidan masu wadata ta yadda zaka ci abinci laifayye ka k'oshi. Amma tunda ta bar gidan ba dama ka je a baka abinci sai dai ruwan pure water. Idan kuwa yini zaka yi to abincine dai ga shi nan amma ba wani sha'awar da zai baka. Sun sa ni kuma iya k'arfinsa ke nan tunda Hawwah bata da shi dole iya yadda ya bata haka zata yi.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: *Kun tuna Umm Nihla mai yadinkan Yan gayu da Yabin Bulkacuwa ta yi ta kece raini da su?*
*Tana nan tana kawo muku su zuka zuka, na alfarma, amintattu, akan farashi mai rahusa*
*Malaysianfabricsng*
07020695644.
Haba ba sai sai kuma suka koma suna son ya'yan Bilki ba. Hawwa kullum cikin kuka take tunda yanzu ita aka saka a gaba ana fadin itace farar k'afa ba Bilki ba. Sannan iyashegen da Faruku ya tisa ta a gaba da shi cikin lumana kad'ai na matuƙar damunta. Tsiyataku iriiri yake yi sannan ba dama ya ga Amrah ta hau samanta zai k'ira ta ya dinga yi mata sababin ta tafi neman suna ta bar shi, shi kad'ai. Ba yadda ta iya da shi tunda ubansa ma rarrashinsa yake yi da son ganin dariyarsa.
Da kanta ta fahimci babu riba ko kad'an idan har kishiya ta tafi ta bar maka ya'yanta gara ku zauna kowa ta rik'e ya'yan har Allah yasa su girma. Yanzu ba abin da take so irin ace Bilki ta dawo d'akinta ko dan mijinta ya samu nutsuwa sannan ta tabbatar idan tana nan wulakancin Faruk ba zai yi tasiri ba. Sannan hankalin Sahal ba zai zama kacokan akan su Amrha ba. Yana son d'iyarta tabbas tunda ba abin da ba ya yi mata amma sai take ganin ba kamar manyan ba. Idan zata kwnaa tana Kiran Faruku ba