DINGISHIN KWADO 3 COMPLETE BY D Auta.txt

Author :  Hadiza D Auta Category :  Romance

Chapter   17 / 50

48K to 51K   out of 149K words

falo bata shigo ciki ba".
Suka fita momi na ganin yadda fuskarta ta yi ja ga idanuwa sun yi luhu luhu zuciyarta ta harba ta tabbatar babu lafiya.
Da hanzari ta isa kusa da kujerar da take yayin da Maigado ta mik'e kaitsaye momi ta jata jikinta ta rungume. Jin haka ya sanya Maigado rushewa da sabon kuka don a yanayin da take ciki so take a ce ta je gaban mahaifi ko mahaifiyarta ta yi kukan da take ta rik'e shi a ranta. Sun jima a hakan kafin Momi ta sake ta, ta ce "Zauna Maigado sannu!.
Maimakon ta zauna kan kujerar sai ta zauna a k'asa tana fad'in "Momi ina kwana?"
"Da kin zauna a kujerar ai sai tafi miki dadi Maigado".
Murya a dakushe ta ce "Babu komai momi".
Yayin da Momi ta kalli Farouku ta ce "Sannun Farouku Ubangiji ya yiwa kokarinka albarka".


A sanyaye ya ce "Ameen momi. Baba ya tashi kuwa?"
Ta ce "Har ya karya ya yi tattaki kwanciya ya ce zai yi amma ai dole ya taso".
Ta juya don zuwa d'akin Baba.
Tare suka fito da Baban kamar kullum yana sanye da farar jallabiya mai asalin tsada.
Duk da shekaru sun ja masa ainun da dan sauran kuzarinsa, ba dan mutuwar k'aninsa da takaddamar da ta biyo ba, da yafi haka kyan gani don tun lokacin bai yi cikakkiyar lafiya ba.
Alti ta gaishe shi, ya amsa da walwala, ya mik'awa Farha hannun tare da fad'in "Zo kusa da ni Bilkisu d'iyar Bilki".
Ta tashi daga kusa da Maigado ta isa kusa da shi ta gaishe shi yana tambayar ina ta baro Amal da Noor?"
Zuciyar Bilki ta doka, sai dai bata ji a ranta zata koma gidan da za'a dinga bawa yara lasisin su dinga zaginta suna aibata mata uwa haka siddan ba.
Cikin hikima Alti ta zame ta nufi kicin da ta jiyo motsin momi.
Momi ta fito ta ja Farha zuwa d'akinta inda junior yake barci don sassafe Abida ta fita zata yiwa wata patient c.s.
A nutse Bilki da Farouku suka gaisa da Baban nasu.
Ya k'are musu kallon nazari ya ce "Dukkanku ba kwa cikin walwala menene damuwarku ne?"
Cikin nutsuwa Farouku ya ce "Bilki ce ta samu matsala da mijinta, ga kuma halin da take ciki."
Baba ya yi shiru tsawon lokaci bai ce komai ba.
Yayin da dukkansu suke dakonsa.
Ya numfasa ya ce "Yau ne karon farko da kika taba barin gidan aurenki da sunan bacin rai, ban so kika karyawa kanki record din ke ce kad'ai baki taɓa yin yaji ba tunda aka yi miki aure, sai ga shi kin fara yi a inda ban yi zaton za ki yi ba. Na kuma shaida alamarine ya kerewa haƙurinki, amma da sawa kika yi Farouku ya kai miki ni gidanki da yafi mini dad'i." Save Restricted Contents Bot, [Sep 22, 2025 at 12:31]
Bilki kanta na k'asa tana zirar da hawaye ta kasa magana.
Ya nisa ya ce "Menene matsalarki?"
Ta kasa ce masa komai, Farouku ma ya yi tambayar duniya, amma bata ce komai ba sai kuka mai tayar da hankalinsu".
Baba ya ce "Ai kin yi k'uruciya Maigado, da zaki taho da kin sa ni kin had'o da Amal da Noor amma sai kika tsame y'arki a cikin y'anuwanta alhalin ni kika saka na fad'a masa za ki je masa da ita, na fad'a masa ya kuma ce ya amince zai saka ta cikin jerin y'a'yansa, yanzu dan kun samu matsalar da ba sakinki ya yi ba sai ki watsar masa da y'ay'ansa k'ananu ki taho da taki kad'ai? Anya kuwa! Wannan ba halayyarmu ba ce, ba mu da wannan halayyar ta banbantawa."
Kukan Maigado ya tsaya cak. Domin kuwa iyakacin gaskiyarsa yake furtawa wanda ta yarda babu son kai ko na zuciya a cikinsu.
Take kuma ta gamsu ta yi kuskuren barin yaran mussaman da su basu yi mata laifin komai ba.
Ya nisa ya ce "Ki zauna zuwa yamma idan mijinki ya tuntube ni, ko Farouku to za ki koma a yau din nan. Hakan ma dan na ga yanayin da kike cikine ya sanya zan barki, ki d'an huce. Amma da yanzun nan za ki koma inda kika fito".
Ta shi ki je dakinki ki kwanta ki yi barci kafin Dr Abida ta dawo".
Ta yunk'ura da ƙyar ta tashi ta nufi ciki yayin da Baba da Farouku suka bita da kallon yadda ta aune ga ciki ya habaka tamkar a lokacin zata haihu.
Sai da ta k'ule sannan Baba ya nisa ya kalli Farouku ya ce "Ban da k'uruciya ma a wannan halin da take ciki me zai saka ta bar d'akinta?
Faruku ya ce "K'ure ta ya yi ne Baba ai Maigado mai hakuri ce kowa ya shaida hakan".
Baban ya nisa ya ce "Ai kuwa zai hadu da fishina Wallahi akan Maigado zan yi matuƙar sab'a masa, bata son aurensa amma ya dage ya matsa sai da ka shawo masa kanta shine tun auren bai je ko ina ba zai fara tayar mata da hankali?"
Baba ya yi tambayar yana kallon Farouku tamkar shine Asad din.
Farouku ya saukar da kansa k'asa ya ce "Ka yi hak'uri ni kaina ban ji dad'in al'amarin ba, zan fad'a masa gaskiya idan ya yarda shikenan, idan ya yi wasarere da matsalar kwabarsa ce zata yi ruwa."
Sai shadaya sannan Faruku ya yi sallama da iyayensa akan da yamma zai dawo.

Abida bata dawo ba sai azahar. Junior da suke wasa da Farha ya ruga ya rungume ta. Yayin da Farha ta yi mata sannu da dawowar ba tare da bar wasan da take yi ba.
Ta kalle ta ta ce "Ke da wa kuka zo?"
"Da Mahma tana ciki tana barci".
Abida bata kawo koami ba, tunda Maigado na da ciki don ta yi barci ba komai ba ne.
Ta leka d'akin Momi ta fad'a ta dawo sannan ta shiga dakin Maigadon.
Ta idar da sallar azahar tana ninke sallaya.
Ta ce "Maigado kin ga yadda fuskarki ta yi kozai kozai kuwa, me ya same ki haka?"
Ta yi k'arfin halin ce wa "Ba komai.
Jikin Abida ya yi sanyi a dalilin ta gane ba k'alau ba.
A sanyaya ta ce "Bari na je na yi sallah na dawo ".
Da ta yi sallar ta dawo ta tisa ta a gaba da tambayar menene matsalarta. Haka siddan Bilki ta ji ta kasa fad'a mata. Kan dole Abida ta numfasa ta ce "Indai da dama ki yi hak'uri ki koma dakinki Bilki, ki dubi halin da kike ciki mana, ki cire b'acin rai tun ba ki yiwa kan ki da abin da za ki haifa illah ba. Menene abu mai dad'i ne a zaman gida? Babu dad'i fa Maigado, Wallahi babu dad'i, kin ga dai a gaban Momi nake ko? To Wallahi kullum dare sai na yi kuka, ba zan so mu yi kuka tare ba Maigado. Yaya Asad na sonki, lallaba ki koma dakinki, ki daure har Allah yasa ki shawo kan matsalar da ta dame ki".
Cikin kuka ta rattabawa Abida halin da take ciki da yara da kuma yadda Babansu yake fad'in yara ne hak'uri kawai yake bata. Sannan ta gano Laura da uwarta sune suke yiwa yaran famfo ta ce masa ta koma gida ya ce ba zata tafi ba saboda alfarmar Rukayya."
Abida ta yi shiru can ta nisa ta ce "Ai kuwa sai ta tafi ko sama da k'asa zata hade. Dama ni ba son tsohuwar nan nake yi ba tunda take taya Rukayya kishi da ni, ko tunanin yana rik'e da d'iyarta a gidansa basa yi, sun dauki tsangwama sun dore mini duk abin da yayana zai yi mini na kan idon Rukayya. Allah dai ya jiqanta amma ai ta mutu da kuttuna a ranta. Save Restricted Contents Bot, [Sep 22, 2025 at 12:38]
Kuma na ga take taken Aysha gaisuwar da take yi mini tabbas uwarta ta cusa mata k'ina zan ko ci uwarta Wallahi ".
Bilki ta rik'o hannun Abida ta ce "Ni dai kada ki taso da wani batu akan matsalata, kawai ni dai ba zan koma gidansa ba matuƙar Laura tana nan, ko Baba ya mayar da ni, to kada ku ga laifina akan na bijirewa Baba Wallahi yana tafiya zan gudu, ba zan zauna ba".
Abida na jin haka ta mike ta fice, kaitsaye d'akin Momi ta shiga, ta fad'a mata komai na matsalolin Bilki. Yayin da itama ta nufi d'akin Baba ta rattaba masa batu.
Ta kara da fad'in "Kada a mayar da ita tunda ta fad'a masa Laura ta koma gidansu, ko ita ta tafi nasu gidan, tunda yafi buk'atar zaman yarinyar to sai ta yi ta zama".
Baba ya ce "A a zata koma kuwa daga nan zuwa dare, ai itama ta yi rashin alkunya. Idan kin ga bata koma yau ba to sawunta ne bai biyo ba, Laura kuwa tunda uwarta da ranta sai ta koma gabanta idan aurenta ya zo sai ya yi mata duk abin da ya kamata. Batun Aysha kuma ai k'alilan ne da anzo batun neman aurenta ba za'a saka dogon lokaci ba tunda itace fitananniya idan aka kawar da ita an karya lagon sauran yaran ".
Momi ta ce "To shikenan Alhaji yadda ka ce hakan za'a yi".
Farouku tunda ya fita yake neman dukkan layukan C.P amma basa tafiya ga shi har yamma ta yi.
Yayin da shi kuma maigirma C.P. aiki ne ya yi masa yawa da yamma kuma suka shiga meeting da Mr President da sauran masu rik'e da madafan iko. Sai wajen takwas na dare ya samu kansa. Kaitsaye gida ya dosa a lokacin tara har ta gota. Ya tarar da yaran su kad'ai a falon da suka fi zama. Suka dinga welcoming d'insa. Ya zuba musu ido sosia yana nazarin waye babu a cikinsu. "Noor Ina Farha?"
"Mun tashi tun safe bamu gansu ba, mun hau saman Mahmah duk bamu gansu ba".
Nan da nan ransa ya sosu. Ya ce "Alti na nan?"
Bilkisu da tafi takura da rashinsu ta ce duka fa basa nan tun safe, na k'ira mahman wayarta a kashe".
Ya numfasa ya ce "Kun ci abinci ne?"
Hafcy ta ce "Ga shi can jiranka muke yi".
Murya ba amo ya ce "Ku je ku ci, mun yi dinner tare da Mr president tea kawai zan sha".
Aysha ta ce "Anty Laura ta kawo maka ne?"
Takaicinsa ya kamata. Bai amsa mata ba ya ce "Hafcy ta kawo masa saman Mahmah ".
Takaici ya shak'e Aysha da Hafcy yadda yake fad'in Mahmah a gabansu shi ala dole so yake su dinga k'iranta da Mahmah su kuwa ba zasu ce Mahmah ba sai Anty Maigado hakan ma don ba yadda zasu yi ne.

A saman Bilki ya yada zango tunda anan yake kwana. Kaitsaye d'akinta ya shiga ya fad'a bayi. Ya fito da alwallah. Ya idar da sallar kenan Hafcy ta kwnakwasa kofar d'akin. Yana Kan sallayar ya ce "Come in".
Ta shigo da sallama sannan ta ajiye masa tare da fad'in "Dady gaskiya ka gaji, ya kamata ka kashe wayoyinka ka yi barci, kada stress ya yi maka yawa.
Murya ba amo ya ce "Je ki k'ira mini yayarku, ku zo tare".
"To Dady".
Ta juya ta tafi, yayin da ya bita da ido.
Suka shigo a nutse bayan ta yi sallama, k'asa suka zauna kusa da shi.
Cikin nutsuwa Aysha ta ce "Dady ga mu'.
Ya nisa ya ce "Wayarki za ki ba ni".
Kaitsaye ta mik'a masa. Bai karɓa ba ya ce "cire mini password din".
Ta cire don yana yawan yi musu irin haka, ya gama bincike ya basu amma baya taba shiga groups dinsu na whtsapp. Contact yafi dubawa da waɗanda suke magana ta pc.
Kaitsaye whtsapp ya shiga ya yi searching sunan group din we are one da ya ga ni ta vedio record.
Ai kuwa ya shiga ya ga maganganun da suka tayar masa da hankalin Bilki.
Daidai inda Laura ta ce kudi ko mukaminsa baza su amfane shi ba idan ya ce zai jewa Bilki ta baya. Ya tsaya ya mayar mata da wayar. Ta karanta ta ji zuciyarta ta buga, hankalinta ya tashi. Murya na rawa ta ce "Dan Allah ka yi hak'uri Dady duba ka ga duk mun yi mata ca akan wannan batun da ta yab'a maka".
Murya a dakushe ya ce "Dama kuka bata shiyasa ta zage ni, kin bude group kuna zagina a fakaice ita kuma tunda ni ba ubanta ba ne sai ta zage ni a bayyane akan idanuwanku da kunnuwanku". Save Restricted Contents Bot, [Sep 22, 2025 at 12:41]
Hankalin Aysha ya kai k'ololuwar tashi ta ce Wallahi Dady bama zaginka a fakaice. Duba ka ga ni".
Ta fad'a a rude matuk'a da gaske. Yayin da Hafcy ta yi wuki wuki tana jin kunyar duniya na kamata duk kuwa da bai ambace ta ba.
Ya yi murmushin da ba shi da alaka da nishadi ya ce"Duk wanda ya zagi matarka ai kaitsaye kai ya zaga, ke ce babba kina da ilimi har kin zama Barista, makarantun da kika yi tun daga matakin nursery har jami'a duka na alfarma ne. Ba abin da ban yi miki ba na gata da soyayya tunda aka haife ki. Amma wai yau ke ce kike yak'ata kike son ki nukurkusa ni da bak'inciki!Kina tunanin ko uwarki na da rai zan kasa yin aure ne? Tunaninki bai alamta miki cewar auren da na yi rufin asirinku ne ba? Da ace Babanku ya yi aure bayan mutuwar matarsa da ace Babanku na yin lalata da yara sa'aninku wanne yafi muku?".
Gabad'aya Aysha ta ji ta muzanta hankalinta ya rub'anya tashi, kuka ya k'wace mata saboda ta ga b'acin rai mai tsanani a fuskarsa da muryarsa gabad'aya.
Murya na tawa ta ce "Dan Allah Dady ka yi hak'uri!
Ya numfasa ya ce "Ke ce da hak'uri Aysha. Ni dai nasan ke na ke bi ba shi, ba ni kike bina ba. Ruwanki ne ki bar ni na samu nutsuwar da ta dace da ni, ruwanki ne ki cigaba ta tayar mini da hankali, idan na fad'i na mutu sai ki ji dad'in jagorantar kannenki yin duk abin da kuka ga dama. Idan an raba gadon y'anuwana sun baku naku sai ku ci duniyar da tsinke tunda dai mu dai mun ga ayar da ba zamu sake barin gado ba tare da an raba shi da wuri ba".
Hafcy ma ta fara kukan don kuwa yanayin Dadynsu ya yi matuk'ar tayar musu da hankali.
Hafcy da kuka sosia ta ce "Ka yi hak'uri Dady".
Ya ce "Kune fa da hak'uri don idan kun zauna lafiya da matata kune da riba don hankalina zai kwanta na yi ta binku da fararen addu'o'in da zasu yi tasiri a kanku.
*Ralzaplace suna da plates na alfarma na gidan yangayu.*
08109544470

Idan kuma kun cigaba da zaginta, kun ga ai nima zata cigaba da gigita mini nutsuwata kuma ko ban ce muku komai ba ai ba zaku ga daidai ba tunda kun jefa ni cikin b'acin rai da tashin hankali. Ace kuna y'ay'ana ban isa da ku ba, ban isa ku mutunta iyalina ba, ta ya ya wacce na auro zata ga k'ima ta, tunda ta gane ban isa da ku ba, sannan baku da tarbiya! Shi yasa ba abin da ba zan yiwa Khadija da Bilkisu ba, don sun yarda na isa da su, kuma sun gamsu ni ubansu ne da zasu taya ni mutunta abin da nake so, su kuma taya ni k'in abin da bana so".
Kuka sosia Aysha da Hafcy suke yi suna ba shi hak'uri.
Ya nisa ya ce "Zan hak'ura ne kad'ai idan kun daina cin mutuncin Maigado don kuwa ko ban aure ta ba ai uwarku ce, sai kuma k'arfin k'addara ya sanya ta zama matata, kenan tudu biyu ne da ita a wajenku. Idan ta haihu ashe haka zaku dasa mini y'anubanci a gida tunda ni ba kwa sona uwarku kawai kuke so ko?"
Ya yi musu tambayar yana kallonsu gabad'aya.

*Soraye Herbal and more*
09033336330
*Masu son gumba gangariya da ciccibi da Kaza Har ma tsumi gangariya.*
*Suna da sabaya mai tada komadar mace tare da gyaran nono.*
*Hakan nan suna da kayan kicin daidai da Farashin talaka. Bayan haka suna Sayar da pads akan sari ko siyan daidai.*
*Yan yankin rijiyar lemo free delivery za'a yi muku. Ana Tura Kaya ko ina cikin k'asar nan.*


*Littafin nan na kud'i ne ga masu son biyan hak'kin wahalar rubutu*
*1k*
2384876855
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank*.

08032773332.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Save Restricted Contents Bot, [Sep 23, 2025 at 15:23]
*Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
# 09069067488#
*Littafi na d'aya zai zo kyauta a WhatsAp yayin da na biyu da na uku zai zo a Telegram da arewa ga wadanda suka biya kudin karatu*.

*Umm Aslan&Asalah Egyptian Items*
*Egyptian abayas*
*Egyptian nighties*.
*Bags and jewelries*
*Dukkansu a sassuakan farashi da ya dara na saura, don kuwa a can take zaune tana turosu Kano kaitsaye, daga nan sai a turawa kowa inda yake a fadin tarayyar Nigeria*
*Tuntubeta a wadannan lambobin dan ganin kayayyakinta na alfarma*.
# +201121544627
# +2349162662750



Hak'uri kan hak'uri suke ba shi don kuwa ba k'aramin muzanta suka yi ba. Kalamansa sun yi matuƙar bugunsu. Kunyar ganin tattaunawarsu a group dinsu da ya yi ta kannade su.
Nadama mai tsananin gaske ta shige su.
Ya kalle su ya ga yadda suke kuka sosai, hakan ya tausasa masa zuciyarsa. Ya nisa ya ce "Abin da nake so ku fahimta guda d'aya ne ko mominku na da rai ba zan kasa auren Maigado ba. Kuma tabbas da ace Maigadon ta amince mini a farko da a gabanta zaku girma don kuwa da tuni na aure ta. Da bata amince mini ba a dalilin ta yiwa uwarku alkunya, ai na hak'ura, yanzu kuma da na samu damar aurenta na aure ta din, na tabbatar Kuma ta amince ne saboda babu ran uwarku da Kuma tausayinku. Sai ga shi kun nuna mata halin tsiya, halin rashin tarbiya. Ku bude kunnuwanku da kyau ba zan rabu da ita saboda ku ba, ku bini a hankali mu rabu lafiya, ku bini a hankali mu rabu lafiya Aysha da Hafcy!
Ya fad'a cikin sigar gargadi.
A tare suka ce "To Dady ! Cikin kuka sosai.
Hakuri kan hak'uri suke ba shi tare da alak'awarin sun canja zai kuma ga canjin a aikace.
Ya sallame bayan ya ce "Zai huce da sune idan ya ga sun canja da gaske".
Bayan sun tafi ya sauke gauron numfashi yana jin ya samu sauk'in matsaloli da kaso saba'in cikin dari.
Ya fad'a tunanin ta inda zai bullowa Bilki. Don kuwa itama ta yi masa laifin da

17 / 50