DINGISHIN KWADO 3 COMPLETE BY D Auta.txt

Author :  Hadiza D Auta Category :  Romance

Chapter   37 / 50

108K to 111K   out of 149K words

ki d'auko mini kayansa "
Murya ba amo ta ce "Ni ban d'auke masa ba fa. Akan me zai dinga k'ala mini sata. Tun ina karama yake mini sharrin na yi mass sata kafatalin gidan nan Abida ce barauniyarsa akan me zai dinga keta mini haddi irin haka?"
Ta kece da kukan da dama bata gama yinsa ba tunda kishine ke yagalgalata.
Sulaiman ya yi mata k'uri yana kallon ikon Allah.

Har cikin zuciyarsa yake jin kukanta.
Ya masa magana don gabad'aya ya zama speechless.
Ba wani kuzari ya ce "Wallahi ke kika d'auka ba mai shiga d'akin ya taba mini kayana sai ke, ko danki ba zai je ya zabe abubuwana masu muhimmanci ya bar ni da tarkace ba, babu mai yin wannan TA'ADAr sai ke."
Baba ya kaurara murya ya ce "Tashi ki dauko mini kayansa Abida ".
Yadda Baba ya yi magana cikin sigar umarni ya sanya ta tashi ta nufi d'akinta.
Jimawa kad'an ta dawo da wayarsa da ATM.
Ta mik'a masa ya karɓa ya ce "Saura passport".
Nan da nan ta ce "Wannan kuma ban dauka ba. Ban san inda yake ba, ka dai duba a cikin kayanka".
Da hanzari ya ce "Wallahi kin dauka yana hannunki ko kaffara ba zan yi ba akan haka."
Baba ya ce ",Je ki kawo mini."
Ta fara kuka tare da cin layar bata d'auka ba iyakacin abin da ta d'auka ta fito masa da kayansa.
Juyin duniya ta k'i ta yarda ma ta dauka bare ta bayar.
Baba ya ce "To ku je ta duba maka a nutse". Save Restricted Content Bot, [Oct 28, 2025 at 11:05]
Abida ta yi maza ta mike tare da fad'in "To Baba" .
Yayin da Sulaiman ya ce "Baba baya dakin nan Wallahi. Tunda ta je yi mini shara ta d'auke kuma tun a ranar sai da na faɗa maka."
Baba ya ce "yanzu dai tashi ka je
ku duba cikin nutsuwa ba da tashin hankali ba."
Tuni Abida ta fice.
Kan dole Sulaiman ya tashi ya bi bayanta amma ya riga yasan yana hannunta ba ganinsa za'a yi ba tunda ta fice da shi tun tuni.
Yana shiga dakin kawai ya ganta a tube ta cire doguwar rigar jikinta ta wurgar kan kujera.
Daga ita sai gajeran wando skin tight iya guiwarta sai half best. Ko brexiya bata saka ba tunda kananun nono gareta da suke a makale basu zube ba.
Don haka bata cika saka bra ba Sai ta yi nishadi.
Ya yi turus zuciyarsa ya buga.
Ganin shatin nipples a cikin farar half best dinta da ta kamata.
Ya dan diririce. Murya ba amo ya ce "Ke ban son shakiyanci fito mini da abubuwana kin ji."
Gabad'aya ta tunkare shi ta ce "Caje ni, laluba ko a jikina na boye tunda baka gasgata ni ba.
Kaitsaye ta rik'o hannuwansa akan ya laluba ko zai ga ni a jikinta.
Gabad'aya jikinsa ya dauki mazari.

*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Just DM for your order @08033773332*.

Ya yi maza ya tsalla gefe. Da haki ya ce "Abida you are trying me fa".
Kallonsa kawai ta gane sakonta ya bige shi.
Ta daure fuska ta yi juyi tana fad'in "A a to indai ba a cikina na boye ba ina zan ajiye?"
Ya zagaye ta ya zauna a bakin gado daga k'arshe ya juya mata baya Yana kallon window.
Ta jijjiga kai tasan ba k'aramin jarumta ya yi da bai kai hannunsa kan nipples dinta ba mussaman da suka fito sosai irin yadda yake son ya gansu, alamun tsosto suke so.
Ganin ta birkita shi Sai kawai ta d'auki rigarta ta sanya. Ta isa kusa da shi. Ba wani Dogon turanci Kawai ta zube a gabansa.
Murya cike da rauni ta ce "Yaya Sule Ga ni na durkusa on my kneel ka karya mini Duk wata fiffika to ka yafe mini haka nan mussaman ma da ya kasance sharrin marab'ai na hadu da su. Amma Duk da haka na yarda na bata maka, ka yi hakuri."
Daidai lokacin wayarta ta hau kuwwa.
Tana durk'ushen ta d'auka ganin sunan Dady ne.
Ta dauka.
Tun kafin ya amsa gaisuwar da take yi masa ya ce "Ki kaiwa Sulaiman wayar".
"Ga Shi ma".
Ta mik'a masa.
Ya karɓa yana fad'in wanene ne?"
Yana jin muryar oga Asad ya daidaita ya ce "Yaya barka da yammaci ".
"Yauwa Dama zan tambaye ka zaka zo me ko kuwa ita ta zo gobe?"
"A a zan zo in sha Allah wajen 2 haka".
"To shikenan sai ka zo".
Ya kalli Bilki da take kallonsa.ya ce "Ya ce zai zo".
"Tom shikenan Allah ya kaimu".
Sulaiman ya mik'awa Abida wayarta.
Ta karba ta had'a da hannunsa ta rik'e.
Ta marairaice ta ce "Ka yafe mini Yaya Sulena?"
Ya harareta ya ce "Ai na ga alamun da isgi6ma kike bani hak'uri. Yaya Sule, Yaya Sule tamkar kina son na ji baush6ne tunda ai idan kin so yi mini Ta'adi me kike fad'in Sule."
Ta yi maza ya ce Dr yaya Sulaiman, mijin Abidan Baba, Baban junior. Allah ya taya ni baka hak'uri. Allah na son mai afuwa ka yafewa k'anwarka masoyiyarka. Ni fa Sai yanzu na gane ashe tun da can ma Yaya Sule kwamushe zuciyar Abida ya yi shiyasa take ganin sauran maza a ragwage ashe dr take Kira. Shiyasa yana tayawa Kara karbe shi babu gardama. Wataƙila fa da ka yi nauyin baki na rigaka furtawa tsabagen ka tafi da ni. ".
Bai san sadda gajeriyar dariya ta k'wace masa ba tare da fad'in "Da dai ba Abida ce ba".
Itama ta murmusa ta ce "Da gaske fa Baban junior ka ga yadda ka hadu ne? Ga ka dogo wankan tarwada ga hanci ga ka namiji a tsaye. Ga ilimin addini ga na zamani. Ga hak'uri da yafiya, ga girmama iyaye, ga son y'anuwa, ga adalci ga iyalinsa. Idan harkar odafare ne ba sauki sai an k'ure Abida. Ya ya kuwa ba zan mace a kanka ba Dr Baban junior?" Save Restricted Content Bot, [Oct 28, 2025 at 11:10]
"Ya mike tare da fad'in "Allah ya shirye ki".

Itama ta mike tare da bude masa dukkan hannuwanta alamun ya zo ta rungume shi.
Shi gabad'aya sai ya ga tamkar da jinnun a tare da ita da gaske.
Ta ce "Zo mana tunda dai mun shirya ka kuma gane sharrin jinnu ne masu son ganin bayan aurena".
Hawaye ya k'wace mata.
K'warai da gaske ta kife shi. Yaa rasa mai zai ce don kuwa tsakaninsa da Allah ta kunna shi tunda ta yi masa sanadin ganin k'ananun kirjinta da suke motsa shi.
Ya yi jarumtar cewa "Yanzu za ki ba ni passport din, ko ba za ki ba ni ba?"
Ta zuba masa ido, yayin da shima ya zuba masa nasa idanuwan. Tsawon dakika goma suna kallon junansu.
Sulaiman ya gama gamsuwa Yana son Abida har yanzu.
Shi ya fara janyewa daga kallon.
Ita kuma cikin rashin kuzari ta ce "Ba zan baka ba, don kuwa ina da hak'kin kulawa da tarbiyarka. Ba zai yiwu na yi sakacin da zaka sake tserewa ba. Ko ina zaka tafi, kafata kafarka matuƙar da aurenka a kaina".
Da mamkin kulawa da tarbiyarsa da ta ce.
Ya ce "To kuma idan babu auren fa?"
Zuciyarta ta harba ta ce "Ai nasan zaka yafe mini, ba zai yiwu na yi zaman jiranka a banza ba".
"A takaice ya ce "ai kuwa kin yi ma".
Nan da nan ta hauro.
Ta ce "Yaya Sulaiman tsakanina da Allah Ina son ka yi hakura ka yafe mini, na fi son ka huce, ina son ka hak'ura Allah me shaidar Hakan. Amma fa gaskiyar magana na fara gajiya, don laifin nan ba da gayya na yi ba. Sharrin jinnul Ashiq ne amma ka cije ka kafe gaskiya kuma na fara kaiwa gejin rarrashinka ya ya haka ne?"
Ya hassala ya ce"Abida ki fa bini hankali, ki fa shiga taitayinki."
Idonta akan fuskarsa ta ce "Har a sannu na bika, yanzu muka a guje zan n bika don Wallahi na gaji. Ina da bukata mahaifata na buk'atar jin ruwa na gaji ko ka zuba mini, ko ka raba ni da zaman zullimi haba dan Allah shekaru hud'u ai ba watanni ba ne."
Ya girgiza kai ya nuna mata k'ofar fita tare da fad'in "out".
Ta rausayar da kai ta ce "Yaya Sulaiman tsakanina fa da Allah na gaji. Ko dai ka yi hak'uri ka yafe mini, ko ka gajarce mini zullimin da nake ciki akanka. Fito kawai ka fad'a mini makomata."
Ya sake girgiza kai ya damko hannunta ya ce "na damka miki damar aurenki a hannunki, idan kin so ki rike, idan kin ga hagu ki tankwabar da shi.
Ta yi maza ta fizge hannunta ta damke hannuwanta da kyau.
Murya na rawa ta ce "Na damke shi da kyau."
Hawaye ya k'wace mata.
Ta ce "A ina zan zauna ina son komawa gidana".
Kaitsaye ya ce "Ban da shi a yanzu".
Daga haka ta ce "Ya yi kyau na gode sai anjima."

*Umm Aslan&Asalah Egyptian Items*
*Egyptian abayas*
*Egyptian nighties*.
*Bags and jewelries*
*Dukkansu a sassuakan farashi da ya dara na saura, don kuwa a can take zaune tana turosu Kano kaitsaye, daga nan sai a turawa kowa inda yake a fadin tarayyar Nigeria*
*Tuntube ta a wadannan lambobin dan ganin kayayyakinta na alfarma*.
# +201121544627
# +2349162662750
*DINGISHIN KWAD'O 4*
*BY*
*SURAYYA DEE*


*PAY 1K VIA*
2384876855
*SURAYYA IBRAHIM DAHIRU*
*ZENITH BANK*
08032773332.

Cikin gaggawa ta fice ta bar masa d'akin tare da kudirin ba zata sake nemansa ko ba shi hak'uri ba.
Ta yi iya yinta ta jure komai. Ta ba na shi hak'uri irim hak'urin da bata yi zaton zata bawa namiji irinsa ba. Don haka enough is enough ba zata sake bibiyarsa ba zata kame.

Yayin da ya bita da ido, tare da ayyana ta yi fishi don ya ga yanayinta ya fita daga yanayin salamar da ta aro ta tafawa kanta tunda suka yi arba.
Gabad'aya sai yake jin wata irin damuwa ta yi masa k'awanya tunda ga k'asan zuciyarsa.

Kaitsaye ɗakinta ta shiga ta dinga kuka tamkar hawayenta zasu kafe. Ita kam ta gaji ba zata sake zuwa yana disgata ba.
Idan Allah yasa an daidaita haka take so. Idan kuma ya gama yanke shawarar ba zai sake zama da ita ba, Kawai ya fito ya furta ya sahale masa idan ya so ya biyata basukan da take binsa ta cigaba da aikinta da addu'ar ta samu nutsuwar zuciya.
Junior ya yi lakwas Yana kallon tana kuka wiwi.
Murya ba amo ya ce "Ammi Ki Daina kuka. Ba kin ce Idan Dadyna ya dawo ba zamu dinga kuka ba, ba zamu dinga zama a d'aki ba?"
Ta kasa bashi amsa a dalilin haka ta dinga fad'a masa a lokutan baya kafin bayyanar Sulaiman. Ga shi ya dawo kukanta na na neman ya zarta sadda ba'a gan shi ba. Gabad'aya ya taurare ya murd'e ya k'i barin komai ya wuce a tsakaninsu.
Cikin Kuka ta ce "Ya k'i ya dauke mu, mu tafi gidanmu junior
"
Ya ce "To zan je na tambaye shi"

Ta kasa cewa komai.
"Ammi na je?"
"Je ka".
Ya sauka da gudu ya fice zuwa d'akin babansa.

A bakin k'ofar ya tsaya ya dinga bugun.
Dr Sulaiman cikin kasala ya ce " shigo".
Junior ya shiga.
Ya tsaya ya ce "Ammi na kuka, zamu tafi gidanmu".
Sulaiman ya mike ya isa kusa da yaron ya d'auke shi ya daga sama.
Ya zauna bakin bada ya rungume Shi a jikinsa. Yaron ya dinga sakin ajiyar zuciya.
Haka kawai tausayi mai tsananin gaske ya shake Sulaiman jin yaro na ta sakin ajiyar zuciya jikinsa.
Jini ba k'arya ba ne.
Ya shafa kansa ya ce "Sulaiman".
Junior ya kalle shi ya ce "Ammi fa ta hana su Farha da Noor ce mini Sulaiman ta ce sunan babana ne".
Sulaiman ya murmusa ya ce "Ta ce " maka sunan dadynka Sulaiman"
Kai junior ya daga masa.
Ya ce "ka ce qwa Ammi ta daina kuka idan na dawo daga Kano zan d'auke ku mu tafi gidanmu ".
Junior ya fara tafin murna ya ce "Zaka saka ni a school din su Farha"
Sulaiman ya girgiza kai ya ce "Dadynsu mai kudi ne kai kuma dadynka mai allura ne. Zan saka ka a wacce zan iya idan muka tafi garinmu".
Junior ya yi shiru ya ce "Ina ne garinmu?"
Har Sulaiman zai ce Funtua sai ya yi maza ya ce Katsina ".
"Ya ce "to yaushe zamu tafi?"
Sulaiman ya dinga mamakin surutun dan yaron.
Ya numfasa ya ce "Idan na dawo daga Kano".
Ya mik'a masa hannu ya ce "promise?"
Dariya ta kubucewar Sulaiman ya ce "promise". Suka k'ulla alk'awari.
Yaron ya juya a guje don ya faɗawa uwarsa zasu koma gidansu ta daina kuka.
Ya je ya fad'a kuwa.
Ta daure ta daina kuka amma ta yanke shawarar ba zata kuma bibiyarsa ba. Za ta dinga addu'a tare da buga masa wuridin da zai kasa shareta. Amma ta gaji da yadda yake wulakantata.

***
Washegari sassafe ya dawo daga motsa jiki ita kuma zata tafi asibiti suka hadu a harabar gate din.
Fuskarta ba walwala ta ce Yaya Sulaiman ina kwana?"
Daga haka ta shige motarta bata jira komai ba.
Hakan ya bata masa rai ya sanya shi jimami. Ya kud'ire kuwa zasu zuba ne don ba zai sauko ya bita ba.
K'arfe Uku Yana gidan Bilki. Suna zaune kan daining suna yin lunch daga shi sai ita.
Alti na can da tagwaye, yaran kuma duka basa nan.
Hira sosai suke yi. Ya bata labarin ibtilain da ya shiga bayan tafiyarsa. Sannan ya bata labarin irin kuɗaden da ya samu a yanzu.
Ta jinjina kai ta tausaya masa. Ta yi masa jaje ta kammala da murnar ya zama kasurgumin attajiri.
Ya nisa ya ce "Ina son na yi aure Bilki. Yarinyar yar Kano ce amma tana karatu a Jeddah."
Kuka kawai Bilki ta rusa tana fad'i "Ka yiwa Allah Yaya Sulaiman kada ka yiwa Abida haka. Ta sha wahalar rashin ka.
Laifinta bai kai haka ba dan Allah."
Ya yi shiru yana jin ba zai iya faɗa mata abin da ta yi masa ba ko da kuwa bata roke shi arzikin kada ya fad'a musu ba.
Cikin kuka ta sake fad'in "Baba ba zai ji dad'i ba. Dan Allah ka yi hakuri a shirya haka nan. Lokacin aurena da maigidan nan irin murnar da Baba ya yi sai da ya bani tausayi Wallahi yana son a shirya, ka ga mune k'ananu kuma shine uba mu kuma y'aya'."
Sulaiman ya ce "Wallahi kuwa matuƙar yana Abuja ba za'a shirya gabad'aya ba. Sai ya yadda na d'auke shi na mayar da shi Funtua ta yadda kowa zai shiga gidan kansa tsaye. Sai ya yarda na mayar da shi inda duk zamu zama ya'yansa kamar yadda Yaya Asad ya dauko shi ya dawo da shi nan. Matuƙar yana Abuja to shi da iyalinsa ne kad'ai. Mu bamu da inda zamu fake."
Ya fad'a idanuwansa sun kada.
Jikin Bilki ya yi sanyi lallai akwai sauran rikici.
Ya kalle ta ya ce "Ya ya aka yi aurenki da Yaya Asad?"
Ta ba Shi labarin komai, har hard aurenta da Sahal ya k'are
Cikin tashin hankali ya ce "Da Baba na Funtua Sahal bai isa ya yi miki gorin ba ki da inda za ki je ba. Anisa ta yi rikici daijinta Sai jiya ta koma gidanta. Maiduguri ta tafi wajen Ansari. Hawaye ya k'wace masa tamkar mace.
Ya girgiza kai ya ce "Yanzun kina sonsa ko kuwa?"
Ba noke noke ta ce "Ina sonsa, ina son zama da shi".
A fili ya ce "Ila yaumil kiyamati ma huce da shi, rikicina da shi ya k'are.
Amma fa batun a shirya a hade tamkar da sai an yarda na yi iko da Baba kamar yadda maigidan nan ya yi.
Ya matsa da kujerarsa kusa da tata kujerar.
Ya rike hannunta.
Ya ce "Bilkina akwai yiyuwar rikici zai sake barkewa amma duk juyin da za'a yi kada ki shiga. Tun filazal ke a wajen Baba Babba kika girma. Yana sonki, yana ganin mutuncinki, ki yi kokarin tabbatar da wannan soyayyar.
Mu da muke da laifi kan laifi barmu mu yi rikicin. Ki bi mijinki. Ba zan iya yi miki abin da yake yi miki ba. Ya fini iko akan ki ".
Da rawar murya ta ce "Wallahi idan ban bi bayanka ba Yaya Hamida da Ansari da Anisa sake kullata zasu yi".
Hawaye ya k'wace mata.
Ya zari tissue ya ce "Zan wanke ki da kaina. Zan musu bayanin ni na baki umarnin yin hakan. Duk basu da hankali ne. Kubucewar oga Asad a hannunki ba k'aramin asara zamu tafka ba.
Idan yana hannunki mun ringa mun zargo su gabad'ayansu dole su karbi dukkan uzzirn da zamu gabatar musu. Ga wacccar zakwakurar tasu ta yi laushi.".
"Amma Yaya Sulaiman ka bar batun karin auren nan dan Allah ".
Bilki ta fad'a cikin firgicin don sosia ta ji tana taya Abida kishi na ban mamaki.
"Aure zan k'ara tabbas, don Wallahi ba dan na tarar kin zama matar Yaya Asad ba, da sakinta zan yi. Amma yanzu na yi imanin idan na sake ta komai zai sake cakalkalewa ne, mafi tayar da hankalina rasa aurenki ko rashin samun nutsuwa cikin auren ki. Don tabbas Oga Asad sai ya yi mini gayya ko bai sake ba to kuwa zaman naku ba zai yi wani armashi ba. Don haka zan yi hak'uri don aurenki ya tsira, na kuma gama lissafina aurenki da shi babbar nasara ce wajenmu, aurena da Abida kuma shine makullin rufe dukkan sabani."
Bilki ta numfasa ta ce "Gaskiya Yaya Sulaiman bana son ka ƙara aure, ba zan so wata matar ka ba alhalin ina ina ganin Abida".

*Contact me 08032773332 what'sapp only*
*For all your kayan mata gangariya*
*Bridal package*
*Maijego package*
*Uwargida package*
*Bazawara package*
*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*
*Ciccibin garari*
*Tsumin saiwowi*
*Hakkkn daka emergency*
*Gumbar ridi*
*Gumbar saiwowi*


Sulaiman ya nisa ya ce "Bilkina wato saboda Abida sai ba zaki yiwa iyalina adalci ba. Wannan ai son kai ne
Matsayinta daban, matsayin abida daban, ko ba zaki so ya ba, to ki yi mata adalci. Yarinyar tana da kirki ba sakaliya ba ce, ba ta kuma da girman kai".
Wani irin Malolo ya tokarewa Bilki.
Murya na amo ta ce "kai ta zo wa a hakan. Amma baka da tabbas akan badinin halayyarta ".
"A a Bilkina da gaske tana da kirki kuma yarinyace akanku ba zata fi Anisa ba fa ".
Ta kasa jurewa kawai sai ta kece da kuka wiwi".
Don kuwa a yanzu ta fahimci alfarmar k'uruciya, wato wacce tafi Abida k'uruciya

37 / 50