DINGISHIN KWADO 3 COMPLETE BY D Auta.txt

Author :  Hadiza D Auta Category :  Romance

Chapter   30 / 50

87K to 90K   out of 149K words

ya yi masa a yanzu kuma ya sake gigita Shi don Ki yake tamkar ya yi ta zunduma ihu da iyakacin k'arfinsa.
A kasalance ta koma wajen Abida. Murya na rawa ta ce "Ya hana ni fita Abida. Ko za ki masa magana?"
A zabure ta ce "Ban isa na yiwa Dady magana a yanzu ba, ai tunda na ga ya fito a gigice nasan a birkice yake haka nan tunda Bai fad'a miki dawowar Dr Sule ba nasan to kin yi saken da zai fara yi miki fitinannen fishinsa mai cunkushe mak'oshi."
Hawaye ke zarya a fuskarta wai duka aure haka yake zuwa da k'alubale. Shi ya yi mata laifi, sannan ya girke hotunan matacciya a d'akinsa da falonsa bayan haka motsi kad'an ya ce ta fita Kaza, Shai ba haka aka Saba masa, Duk bai yi tunanin yadda take jin ciwo a ranta ba,sl Sai Kuma ya gindaya gaba Mai tsauri irin haka a tsakaninsu?
Ace Sulaiman ya dawo amma ya kasa fad'a mata? Ta ce zata je ta gan shi ya ce ba zata ba don gadara da son ya musguna Mata.
Yayin da Abida ta sake tsotaya da lamarin maza wato dama har yanzu ana hana mace zuwa wajen da aka san mai muhimmanci ne a wajenta. Nan Duniya Sulaiman na cikin abubuwan da suke da daraja hadi da muhimmanci a duniyar Bilki. Ya yi shekaru kusan hud'u ba'a san inda yake ba, ya dawo kuma a hanata zuwa ta gan shi?
Ita da kanta Abida al'amarin ya girgizata tana auna tamkar itace ta ce zata je ganin oga Asad bayan an shafe shekaru ba'a san inda yake ba ace kuma miji ya ce ba zata ba.
"Tirk'ashi!
Ta fad'a a bayyane. Ganin Bilki na kuka sai ta yi maza ta had'iye kaduwar da ta shiga ta ce "Share hawayenki, idan ya yarda zan rakito shi mu zo ya ga twins."
Cikin kuka Bilki ta ce idan bai yarda ba fa?"
Abida ta ce "Zan saka Baba ya yiwa Dady magana ya bari ki zo."
Ta goge hawaye ta ce "To".
Amma k'asan zuciyarta ya yi mata nauyi tare da jin k'ololuwar gajiya da zaman gidan oga Asad kisan mummuke kawai yake yi mata.
Haka Abida ta tafi da junior.
Sai da Bilki ta shanye kukanta sannan ta fad'awa Alti Yaya Sulaiman ya dawo.
Alti murna sosia ta dinga tare da adduar Allah yasa ya dawo kenan.
Bilki ko jikinta ya sake sanyaya don kuwa Idan ba sa'a ba Yaya Sulaiman ya yiwa oga Asad wulakanci shiyasa ya dawo a firgice bai kuma fad'a mata ya dawo ba, sannan ya hanata zuwa wajensa.
A ranta kuwa ta san rikice ne zai sake tashi sai dai Allah ya shiga al'amarin kawai.
..
Sulaiman ganin Abida ta fita ya sanya ya tausasa murya ya ce "Baba ina son na wuce yau. Amma zan dawo na ji sharadina da zaka gindaya mini satin sama".
Mamaki ya tuke Baba a zaune
Ya nisa ya ce "Ina zaka ke Sulaiman"
Kansa a k'asa ya ce "Zan je Katsina Baba."
Baba ya girgiza kai ya ce "Za ka je amma ba yanzu ba".

*Lame.Ng Skin Beauty and wellness*
*Duk masu son sanin mayukan da azsu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.*
*07036662633*

*Ga mutanen jamhuriyar Niger ku tura 500f ga wannan lambar+227 96451253*

Ya yi shiru ya ce "To Baba zan dan shiga cikin gari gobe zan dawo in sha Allah".
Ran Baba ya yi k'ololuwar b'aci ba zato ya suri robar ruwan Eva da ba'a bude ba, rab'a ta lullube robar saboda sanyin ruwan.
Da dukkan k'arfinsa ya kantaraqa Sulaiman a gadon bayansa.
Babu zaton Sulaiman ya ji saukar dukan ya karade jikinsa a gigice ya mik'e yana waiwaiye tare da tunanin oga Asad bai tafi ba ne, don bai taba tunanin Baba ne ya kwada masa abu haka ba. Don kuwa suna k'ananu ma bai tana dukansu ba.
Murya ba amo Baba ya ce "Ni ne na kwada maka ba kowa ba, matso nan".
Sulaiman ya tsugunna nesa da shi don gabadaya ya rikice.
Muryar Baba na rawa ya ce "Matso nan Wallahi Sai na Ƙara maka."
Da sauri Sulaiman ya rarrafa gaban Baban kansa a kasa don ya kubutar da shi daga yin kaffara.
Baba kuwa ya cire tausayi da rauni ya shiga kantara masa jarkar nan har a kansa ya dinga maka masa.
Momi ta fito ganin Baba na dukan Sulaiman da iyakacin k'arfinsa l, shi kuma yana durk'ushe yana dan karewa da hannuwansa idan za'a kwada masa a kansa.
Da hanzari ta iso ta janye shi tana fad'in "Yi hakuri, ayi masa nasiha dai ai ya wuce duka Alhaji".
Hawaye na zuba a idon Baba ya ce "Da yake idan mutum ba shi da mahaifa sai gata ya yi masa yawa, sannan babu mai iko da shi ko?"
Momi ta fashe da kuka tana fad'in "A a ba haka bane Alhaji".
Yayin da Sulaiman yake durk'ushe hawaye na tsere akan fuskarsa wanda na tausayin Baba ne, ba na dukan da ake yi masa mai shiga kansa ba.
Da rawar murya baba ya ce "Duk wulakancin da wannan yaron ya yi mini na jure na karbe shi, shine ya samu kuzarin fad'a mini zai tafi ya samu masauki saboda nan ba gidan ubansa bane! Da ace ubanka na da rai da ka ga yadda zan saka a zane mini kai, amma tunda babu shi, sai na yi maka iya yadda zan iya don wataƙila idan na saka guda cikin yayunka su lallasa mini kai, za ka yi zaton na saka ya'yana sun ci zarafinka tunda ni na haifesu.!
Hankalin Momi ya yi tashin gauron zabi a dalilin yadda ta ga Baba ya shiga matsanancin b'acin rai.
Ta dinga ba shi hak'uri tare da kokarin kwantar masa da hankali.
Yayin da Sulaiman yake kuka marar sauti.
Daidai lokacin Abida da junior suka dawo.
A guje ya shigo sai dai ya yi turis ganin Momi da Baba suna kuka.
A sanyaye ya ce "Menene?"
Kafin su ba shi amsa Abida ta shigo.
Ganin suna kuka bai bata mamaki ba.
Sai kawai ta durk'use kusa da Sulaiman da kansa ke k'asa.
Ta tausasa harshe ta ce "Ka yi hak'uri Baba! Dan Allah dan Annabi ka yafe mana ka cire mu a cikin sahun waɗanda suke tayar maka da hankali.
Ni dai na bi Allah na bika, na yi kuskuren bijirewa umarnin da ka ba ni, akan na koma d'akina, yanzu kuwa tunda Allah ya sa ya dawo to zan tabbatar na gyara kuskuren da na yi, zan bi umarninka, zan bi shi duk inda za shi zan kuma zauna lafiya da shi".
Baba ya ce "Ke ma ban isa da ke ba, bare shi da yanzu ya tabbatar mini ni ba ubansa ba ne, alhalin ubansa ma ni ubansa ne".
Sulaiman ya dago da fuskarsa da ta yi face face da hawaye ya ce "Wallahi Baba ba hakan nake nufi ba".
Dak'uwa Baba ya yi masa tare da fad'in ka ci ubanka! Me ka ke nufi to? Matso nan".

Momi ta ce "A a Alhaji ai ya daku bar shi haka dan Allah!
Yayin da Sulaiman ya yi k'asa da kansa yana fad'in "Ka yi hakuri Baba dan Allah".
Junior ya yi tsuru tsuru.
Abida ta yafito shi tare da fad'in "come to Dady junior".
Ba kuzari ya isa kusa da ita ya tsaya a dalilin ya ga kan Sulaiman a k'asa yana kuka yana goge fuska da hankici.
Abida ta zaunar da shi a jinyarta.
A ladabce ta ce "Baba ina sake baka hak'uri, sannan Allah shine shaidar na yafewa Dr yaya Sule tafiya da ya yi ya rataye ni. Don haka ka daure ka yafe mana ka saka mana albarka komai ya wuce. Kawai ya d'auke mu yi tafiyarmu".
Kansa na k'asa ya ce "Baba ka fad'a mata ba da ita kake magana ba, ta daina saka baki idan kana mini fad'a ".
Momi ta ce "ina zata yi shiru kuwa".
Abida ta yi maza ta kame bakinta.
Baba ya ce "Kada ki sake bude baki ki yi magana, tashi ki shiga ciki ma".

*Contact Bojuwa herbs@ 08032773332 what'sapp only*
*For all your kayan mata gangariya*
*Bridal package*
*Maijego package*
*Uwargida package*
*Bazawara package*
*Kazar sababi ta amare da uwayen gida da masu jego*
*Ciccibin garari*
*Tsumin saiwowi*
*Hakkkn daka emergency*
*Gumbar ridi*
*Gumbar saiwowi*.
Save Restricted Content Bot, [Oct 18, 2025 at 11:02]
*Wannan littafin na kudine pay* *1k via 2384876855*
*Surayya Ibrahim Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wadannan lambobin*
# 08032773332#
# 09069067488#


*DINGISHIN KWADO 4*

*BY*
*SURAYYA DEE*

*MARUBUCIYAR*
*HALIN YAU*
*SABO DA KAZA*
*BAK'AR TA'ADA*

Ta tashi a sanyaye.
Baba ya kalli Sulaiman ya ce "Kana sane ai ban huce da kai ba, amma tunda mukaa sauka kake ta bata mini rai. Ga ka, ga yayanku ka kasa bude baki ka yi masa magana? Wanne irin al'amarine haka Sulaiman? Kullum addu'ata Allah ya bayyana mini kai, ta dalilinka zumunci zai daidaita sai kuma ka dawo da dabi'un jahilai?"
"Ka yi hakuri Baba". Sulaiman ya fad'a a hankali.
Baban ya nisa ya ce "Ya kamata kasan ka girma kuma dole ka yi hak'uri da sha'anin rayuwar nan mussaman a al'amarin zumunta. Yanzu ka kalli yaro an haifa maka har ya girma baka san shi ba, bai sanka ba, wanne irin Bakar Ta'ada haka ka yi?"
Ya kasa magana wato cikin Abida bai zube ba kenan?"
Baba ya zarce da fad'in zan "hak'ura na huce ne idan ka je ka tattaro mini y'anuwanka ka kawo mini su gabana don tunda ka tafi idan ka d'auke Bilkisu. Ansari da Saddiqa kad'ai na sanya a idanuwana suma zan iya lissafa maka.".
Murya ba amo Sulaiman ya ce "Da ikon Allah zan kawo su Baba amma ka dubi Allah duk uzziri da alfarmar da zamu nema ka yi mana".
Baba ya ce "Zan muku Sulaiman indai kun yarda ni din ubanku ne to menene ba zan yi muku ba?"
Sai kuma kuka ya k'wace masa.
Sosai hankalin Sulaiman ya yi tashin gauron zabi.
Ya dinga bawa Baba hak'uri cikin rauni.
Yanzu ka je d'aki ka yi wanka, Idan muka yi sallah sai mu dan kwnaata kafin laasar mu dan huta."

Kafin Sulaiman ya yi magana Abida ta fito daga dakin mami hannunta d'auke da mukullin guest room, da confidence ta zo ta d'auki jakar Sulaiman ta rataya, ta ja trolley yayin da junior yake rik'e da tsintsiya da parker da detergents.
Sulaiman ya ce "Ajiye mini ina da hannu".
Abida ta d'auki salati mai tsananin gaske ta ce "Yaya Sule yanzu duk nasiha da Baba ya yi maka baka risina ba, ina jiye maka ya sake tunzura to ni dai kam darajar Baba na yafe komai. ba kuma zan sake yarda da fishinsa mai yawa ba a kaina ba."
Ta kalli Baba ta ce "ka shaida na huce na yafe masa, ina kuma neman shiri saboda na riga na gaji da wannan danbarwar".
Sulaiman ya yi shiru a ransa kuma mamakinta yake ba zata taɓa canjawa gabad'aya ba. Wato ta nan zata bullo masa?
Kwatsam ya ji Baba yana saka mata albarka har da fadin tabbatuwar aurensu na cikin abubuwan da suke da muhimmanci a zuciyarsa, dan haka ta cigaba da juriya in sha Allah zata yi albarka, don yiwa miji biyayya da hak'uri da shi, alamun mace na kan turba madaidaiciyane. Gabad'aya Sulaiman ya ji duk wani azancinsa ya k'wace Abida ta binne shi da ransa. Baba kuma ya tula masa k'asa cikin girma.
Yana ga ni ta fice da jakunkunansa wanda ya yi amannar sai ta bude masa kafin ya je d'akin tunda haka dabiarta take.
Ya bi yaron da bai bar komai na halittarsa ba da ido da ya bita a baya da kaya a hannunsa yana ja.
Cikin lokaci k'alilan ta karkade Dakin da kanta ta share, ta shi ga bandakin ta wanke toilet din da k'ura ce kawai a cikinsa.
Sannan ta koma ta dauko bedsheet dinta wankakke goggage da blanket ta hado kuma ruwan moping.
Baba yana ganin yadda take ta safa da marwa cikin rawar jiki da falli.
A ransa dariya ne fal akan lamarin Abida sai dai ba ya so ya yi a gaban Sulaiman don ya lura gabad'aya Sulaiman din ya zama wani iri ya kasa katabus.
Baba fad'i yake yi a ransa ja'irar yarinya ta ji jiki iya jiki, ta yi laushi tub'us ya kuma gane sulhu take so ko na dolen doliya ne.
Mintina biyar suka ga ta shigo da sauri sosai ta yi d'akinta. Zuciyar Sulaiman ta harba ya ce "Baba k'irata na tabbatar ta ɗauko mini wani abu" .
Baba ya ce "Haba Sulaiman ai yanzu ta yi hankali ba zata dauki wani abunka dan ta boye ba. "
Sulaiman ya yi shiru ba don ya gamsu ba, sai dan ba zai yiwa Baba gardama ba. Amma tabbas ta d'auke masa wani abu.

Ta fito fuska ba walwala hannunta d'auke da burner da kwalbar turaren wuta mai kyau.
Ta wuce tana fad'in to na gama gyara maka da kaina Dr yaya Sule ". Save Restricted Content Bot, [Oct 18, 2025 at 11:04]
*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Sanyi flusher kuwa best seller ne*
*Just DM for your order @08033773332*.

Bai amsa ba bare ya motsa. Ganin haka ya sanya Baba mikewa da ƙyar.
Sulaiman ya yi maza ya mike ya rik'e shi har zuwa bak'in k'ofar d'akinsa.
Sannan ya bar shi Abida ta yi maza ta fice kan dole ya bi bayanta. A harabar hate don ya hango junior na buga ball. Ba dan sadda ya bar k'asar Farukun Bilki ya fi shi shekaru Banda ya ce shine don tsananin kamarsu. Ba tantama dansa ne don ga shi nan sak shi tamkar kakinsa ya yi.
Ba ya inkarin jininsa ne amma sai ya yamutsa Abida. Kuma tunda Baba ya yi masa fahimtar tafi ne don bai d'auke shi ubansa ba, to kuwa sai sun gurfana shi da ita a gaban Baba an baje komai a faifai da ya huce duk da dabararta kuwa. Sai tula masa k'asa take cikin dabara.
Momi kad'ai ba Baba ba, kunyarta yake ji akan Abida. Dole ya hak'ura amma sai sun sake yinta da wajewa. Ba zai sake d'aukar wulakanci irin wadda ta yi masa ba.
Don haka ba zai bata fuska da wuri ba.
Suna shiga ta wuce bayi, tuni ta kai masa brush da makilin d'insa da ta ga ni cikin jakarsa Hadi da soso da sabulu.
Sai da ta had'a ruwan wanka ta fito tare da fad'in "Dr , Yayana, mijin Abida, kuma Baban junior with dew respect nake sanar maka na had'a maka ruwan wanka, mu je na taimaka na dunduma maka kanka na ga gefen can ya dan kunbura kad'an. Gaskiya na tausaya maka Yaya Sulena ka bugu a hannun Baba".
Sai hawaye shar shar a idanuwanta.
Ya zuba mata ido yana ganin yadda hawaye ke tsere, hannunta rike da tawul dan k'arami da ya gamsu da gaske take yi dundumen zata yi masa. Ya rasa ma ajin da zai ajiye ta.
Ya matse bai ce komai ba, jakarsa ya bude ya fito da tawul da jallabiyar sannan ya ce"kauce Malama! Don ya gama gasgata bai gama karantar halayyarta ba .
Ta kuwa yi maza ta kauce din sai dai bata yi shiru ba.
"Ba damuwa sai na yi maka dundumen da daddare."
Yayin da ya wuce yana ayyana ai yasan duk juyin da zai yi ba zata yarda ta yi fishi ba a yanzu.
Ya fito daga wanka sanye da jallabiyar.
Sai da ya fesa body spray mai dad'in k'amshi sannan ya kwanta.
Ta tausasa harsehe tare da fad'in "Yaya Sule na yi maka irin tausarrr nan da ka ke yi mini idan mun dawo daga asibiti?"
Ya yi mata shiru. Ta sake maimaitawa
Ya kaurara murya ya ce "A a ".
"To yaya Sule bari na cire maka dattin kunne ka ga ma cotton buds din na d'auko, nasan zuwa yanzu datti ya cika maka kunne tunda baka iya cirewa da kanka".
Kaitsaye ya ce "To idan kuma a can din ina da matar da take cire mini fa?"
Zuciyarta ta buga don tasan wataƙila hakan zai iya kasancewa.
Amma ta aro jarumta ta cije ta ce "Tunda yanzu ni ce tare da kai, ka bari na cire maka mana. "
"To ba zan bari ba".
Ya fad'a a takaice.
Ta cuna baki tana kunkuni. Shi kuma ya yi kamar bai ji ba.
Can ta nisa ta ce Yaya Sule na yi kewar chest dinka, na zo na kwanta zaka yi hugging ɗina da tausayawa?"
Ya kasa ce mata komai don ya ga so take ta shashantar da shi ta rubta shi ya fad'a tarkonta.
Daidai lokacin junior ya turo k'ofa ya shigo.
Abida ta yi maza ta ce "koma ka yi sallama, ka jira a amsa maka".
Ya koma din.
Ya dinga knocking tare da fad'in assalamu alaikum cikin muryar yara.
Ta amsa masa da fad'in walaika salam shigo Habibina".
Sulaiman ya zuba mata ido shi gabad'aya mamakinta yake yi.
Jiniyo yhigo ya isa kusa da ita.
Ya ce "Ammi dadin nawa bai yi mini irin yadda Dady oga yake yiini ba".
Ta murmusa ta ce "Ba shi da lafiya ne. Idan ya warke fiye da Dady zai dinga yi maka." Save Restricted Content Bot, [Oct 18, 2025 at 11:05]
Sulaiman daga kwancen ya mik'a masa hannu ya ce "zo mu gaisa."
Junior ya isa gare shi ya hau Gadon ya zauna Yana kallonsa.
Yayin da Abida take mamakin tsananin kamar da suke yi da juna.
Farha da junior da kuma Farukun Bilki ba inda suka bar Bilki da Sulaiman kwabo da kwabo kuwa.
A hankali Sulaiman ya ce "ya sunanka?"
Da hanzari junior ya ce "Sulaiman Sulaiman. Junior ake ce mini".
Ina ne school dinku?"
Ya ce "Ba'a sa ni ba, amma ammi ta ce mini zaka saka ni a makarantarsu Yaya Noor da Yaya Farha ".
Zuciyarsa ta harba a dalilin suanar Farha da ya ji. Idan kuma har ba mancewa ya yi ba to Noor itace last born din oga Asad.
Yasan Bilki na Abuja tunda an fad'a masa ta bar Katsina. Don haka idan makantarsu Noor aka saka Farha ba zai yi mamaki ba.
Ya ce "Amminka ce zata saka ka ka ji".
Junior ya ce "Amma fa Yaya Noor ta fad'a mini kowa

30 / 50