Author : Hadiza D Auta Category : Romance
ya ce "Ina son
kowa ya bude zuciyarsa a cikinku ya karbi gaskiya ya kuma rungumi hak'uri da afuwa.
Duk wanda ya yi imani da Allah da manzonsa to ya yi hak'uri ya huce da d'anuwansa."
Ya kalli Asad ya ga gabad'aya ya zama wani iri. Tashin hankali zane baro baro akan fuskarsa ya tausaya masa don kuwa dukkan yaran kowa ya bude baki laifinsa ne akan gaba. Bilki ma ta saya ne saboda mijinta ne.
Ya ce "Asad menene taka matsalar?"
Save Restricted Content Bot, [Nov 6, 2025 at 14:58]
*Surayya Dee*
08032773332
*Wannan littafin na kudine*
*Ga mai son biyan hak'kin wahalata 1k ne*
*2384876855*
*Zenith Bank*
*Surayya Ibrahim*
*Lame.Ng Skin Beauty and wellness*
*Duk masu son sanin mayukan da azsu dace da skin dinsu to A lame skin Beauty and wellness zaku samu.*
*07036662633*
*Ga mutanen jamhuriyar Niger ku tura 500f ga wannan lambar+227 96451253*
Mene ne taka matsalar Asad?"
Ya yi k'asa da kansa, ya dago ya kalli mahaifinsa ya ce "Ba ni da hujjar da zan gabatar don duk hujjojina sun kawo sun kuma rushe bisa hujjar arzikin Baba K'arami zasu ci. Amma abin da nake so su mini adalci daya ne. Daukarka da na yi don nema maka lafiya ba laifi na yi ba, ba kuma zan yarda na yi kuskure akan hakan ba. Duk cikin kurakuran da suka jingina mini d'aya na karba na barin Abida a gida. Shima kuma a yanzu na rushe shi. Don duk cikinsu ba wanda ya k'alubalanci Sulaiman da fantsama duniya da ya yi ya barka da ciwon rashinsa, da kuma rainin da ya yi maka, ya barta da aurenta da k'aramin ciki. Don haka idan ina da son kai da son zuciya lah shakka kun fini . Maganar ban kawo daidaito ba, na d'auke baba na dawo da shi nan, akwia wani a cikinku da ya zo ya yiwa Baba k'orafi ko ya yi yunkurin d'auke shi kamar yadda na yi masa? Gabad'aya fa shata layi kuka yi da shi? Kai Ansari da kake fad'in ka zo ka gurfana akan ya karɓa maka aure, bayan haka sai yaushe ka zo kuma?"
Ansari ya yi shiru.
Oga Asad ya ce "Buk'atar kanka ce da nemawa kanka mutunci a idon iyayen matarka ya sanya ka zo, amma ba dan yana da rigar Baba k'arami a jikinsa ba. Da na d'auke shi, me yasa baku zo kun d'auke shi ba idan har ubannku ne da gaske, kuma kuna da buk'atarsa? Akwai wanda a cikinku ya taho dan ya duba shi tun ma kafin komai ya damalmale gabad'aya? Gabad'aya kun gamsu an ci mutuncin Sulaiman saboda bamu mayar masa da Abida ba. A daa na hak'ura da dukan da na yi niyyar yi mass na wulakanci da rainin da ya yiwa Baba na shiga duniya tsawon shekaru hud'u babu wanda yasan inda yake. Abida ce ta had'a su? Wacece Abida yaushe ma aka ba shi ita?
Ba wani guda da ya yiwa Abida alkunya a cikinku. To a ina aka ce namiji ya tafi ya bar mace da ciki ba waiwaiye tsawon lokacin da wannan yaron ya yi? Wato ku mutuwar Baba gata da sangarta ta janyo muku kuna ganin baku da wani babba, komai zaku yine yadda kuke so babu mai taka muku birki. To kuwa a yanzu sai na zane shi, haka Hamida ki yi matuƙar shiga hankalinki, ki yi hankali da ni, ki kalle ni ki harare ni? Amma ai rashin kunyar karya kike yi me yasa kika gudo gaban Baba?
Ko wanne irin laifi na yi muku auren Bilki da na yi bai ci ku
huce da ni ba? Don da bana sonku da ban aureta ba. Amma na fahimci ke a wajenki ma zunubine aurenta da na yi saboda kin kwashe kayanki a gaban ma'aikin Allah. Ace ta haihu cikin jinya amma ki k'i zuwa ki ganta, bare ki ga abin da ta haifa, sannan kuma kika hana Ansari da Anisa su zo saboda nine mijinta kuma uban y'ay'an da aka haifa Hamida Hamida!
Ta zumbura baki bata ce komai ba.
Ta zumbura baki bata ce komai ba.
Baba ya ce "Sassauta haka Asad ya isa haka".
Don magana yake yi cikin daga murya da matsanancin fishi".
Baba ya kalli Faruku ya ce "Yi magana Faruk ".
A takaice ya ce "Ansari abin da yasa ban shiga cikin matsalar ko yin wani yunkurin komai ba a wanccan lokacin kid'ima na yi, tare da firgicin sannan na tsorata. Baba fa shine k'at to shima ga yadda ta kasance da shi a hannunku mussaman kai, to ni kuma fa?
A wanccan lokacin kanka na zafin idan na yi magana kana iya faɗa mini komai. Sannan rashin zuwanku gaban Baba da nufin duba shi ko gaishe shi sai muka fahimci ku gabad'aya baku d'auki al'amarin Baba k'arami da muhimmanci ba kun tsaya ne a iya girman uwa da hak'kin a yi mata biyayya ta kowacce fuska, shi kuma uba ba shi irin wannan hak'kin. Bamu cire muku rigar Baba k'arami ba kune da kanku kuka cire ta kuka yiwa kanku tunbur. Duk abin da zamu yi muku ai saboda Baba ne to Baban kun nuna ba zaku bishi w ware sai mu yi ta binku don ku zo wajensa?"
Ya jijjiga kai tabbacin ba zasu yi hakan ba. Save Restricted Content Bot, [Nov 6, 2025 at 15:02]
*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Just DM for your order @08033773332*.
...
Jikin kowa ya yi tub'us da kalaman Farouku.
Hatta Hamida kuwa. Ansari kuwa tuni ya gamsu iya gaskiyar Yaya Faruku kenan.
Baba ya kalli Usman ya ce "Kai fa?"
A takaice ya ce "Ba ni da matsala da kowa. Idan mutum ya huce nima na huce".
Sulaiman ya daga hannu alamun yana son yin magana.
Baba ya ce "Muna sauraronka".
"Sulaiman ya ce" Yauwa Baba Usman ya yi mini ba daidai ba. A gabana akan idona da kuka zj ta'aziyar MAMI ya kalli Abida ya ce mata wai idan tana son tafiya da y'arta ya karbo a hannun Bilki. Bai fa tsawatar mata akan ta zauna a d'akinta ba a matsayinsa na wanta kuma dan'uwana aminina Sai yake kokarin sake tayar da wuyar rikici a halin tashin hankalin da muke ciki na mutuwar MAMI".
Baba ya ce "Assha Usman Kaine ka yi haka?"
Ba ja in ja ya ce "Na yi haka Baba, amma gani na yi sunsan girman uwa da muhimmancin bin ra'ayinta akan kowanne irin al'amarin da ta bijiro da shi. A lokacin na kalli k'wayar idon Abida na ga tana kallon Farha da wata soyayya irin ta uwa shiyasa na takaice mata wahala na tambaye ta idan tana buk'atar d'iyarta don kuwa itama uwa ce. Amma da yake ita bawa Bilki diya ne saboda alakarta da Baba K'arami ai bata karbeta ba."
Gabad'aya Sulaiman ya yi lakwas don kuwa jirwayen Usman ya dage.
Baba ya shiru kafin ya ce "Salaha fa?"
Ta ce "Duk wanda na musgunawa ya yi hak'uri ya yafe mini, Nima na yafewa kowa".
Baba ya ce "Allah ya yi miki albarka."
"Abida."
Ta nisa ta ce "Baba ina sake baka hak'urin gardamar komawa d'akina da na yi maka. Tabbas ka ce na koma na bijire, Duk laifin nan da ake jingina maka kai da daddy ni nake da alhakin d'aukarsa amma tunda na zama y'ar kuka dole ku shiga cikinsa. Ta kalli Sulaiman ta ce sun ce na koma ni na ki bisa hujjar zuciyoyinmu a tunzure suke komai zai iya afuwan marar dad'i. Allah me shaidar an yi haka.
Laifi nasan na yi laifi, na janyowa Baba da Dady ma. Amma ina bada hak'uri, kowa ya yi hak'uri Allah ya kiyaye gaba."
Gabad'aya jikin kowa ya yi sanyi don a yadda Abida take ba wanda ya zaci zata bude baki ya bada hak'uri a cikin taro iron hakan.
Baba ya ce "To Alhamdulillahi Ina fatan kowa ya gama fad'ar abin da yake ransa?"
Aka yi shiru.
Ya sake maimatawa suka amsa da fad'in"eh.
Amma oga Asad kala bai ce ba.
Ya nisa ya ce "Alhamdulillahi ni yanzu a matsayina na uba na yafewa kowa. Allah ne shaidar da dukkan zuciyata na yi wannan kalamun. Amma fa Sulaiman ka yi mini laifin da ya mini ciwo, kukan da na yi a Kanka ban yi akan kowa ba, ba dan komai ba sai dan ka nuna mini k'arshen iyakata, ka nuna mini Abida na haifa ba kai ba. Tabbas na yafe maka sai dai mantawa Sai a hankali Idan ka tsaye kai da fata ka yi kokarin toshe kofofin da zan dinga tunawa. Tafiyarka ta sake rub'anya damuwa da b'acin rayuka da yawa. Tafiyarka ta cakalkala al'amura masu yawa.
Amma Alhamdulillahi ka yi sa'a ka dawo ka tarar da sauran rayuwata ba dan haka ba da nadamar da zaka yi ba y'ar kad'an bace.
Hankalin Sulaiman ya tashi daga Baba har su yayyensu suna k'alubalantar ya tafi ya bar Abida don Basu isa ba.
Ta ya ya zai bude baki ya fadi abin da ta yi masa?
Idan bai fad'a ba shikenan ya tabbata ya raina ubansu ya wulakantasu. Har su koma ga mahallici ba zasu daina kallonsa da wannan tabon ba.
Amma kuma ya yi imanin idan ya fada su Hamida suka ji babu sauran sulhu. Zasu yi komai, zasu bantse matuƙar suka ji ta taɓa alafarmar MAMI ne."
Ya numfasa ya ce"Baba ka yi hak'uri. Amma dare ko gobe dan Allah zamu zauna tare da kai da Yaya Faruku da yaya Asad". Save Restricted Content Bot, [Nov 6, 2025 at 15:05]
Baba ya ce "Allah ya kaimu ko yaushe ni inan ku daidaita lokacin had'uwar a tsakaninku.
Abida ta yi wuki wuki tasan laifinta zai fad'a don ya fita dava zargin ya rataye ya saboda ya raian Baba a idanuwansu. Hankalinta ya tashi amma ta samu salamar su Yaya Hamida ba su ji ba, ba kuma zai fad'a a gabansu ba.
Zuciyarta ta yi nauyi, ko su Baba ma ba zata so su ji wannan katobarar ba. Kaifin harshe ya janyo mata nadama da kubucewar al'amura masu yawa a wajen Sulaiman. Ya janyo mata nadamar da har ta mutu ba zata daina kokawa ba don ta tabbatar lokaci zuwa lokacin Idan ya tuna ba dad'insa zata ji ba. Don ta riga ta gane Su suna da rik'o da kullaci kuma sun fi son uwarsu akan komai. A yanzu ma kunyar baba da tsoron abin da zai biyo baya ya hana dankara mata saki. Tunda ya tafi Kano bai nemeta ba Har ya dawo ta tabbatar asarar da ta yi babbace.
Dan haka ta kud'iri aniyar yin hak'uri da duk abin da zai yi mata. Amma dai a yanzu zata daure ba zata dinga bibiyarsa ba. Idan Allah ya tarfawa garinta nono ta koma d'akinta ta yi ta bibiyar har ta shawo kansa.
Sulaiman ya ce "Baba muna sake rokawa MAMI gafara dan Allah, dan Annabi ka yafe mata."
Dukkansu suka Matso kusa da Baba suka hade waje d'aya suak maimaita kalaman Sulaiman Har da Bilki.
Su oga Asad da su Abida suka bisu da ido suna kallon yadda suka hade da junansu tamkar sardine matan sun kewaye Ansari da Sulaiman.
Baba ya ce "Na yafe mata tun ranar da ta rasu, ina kuma nema Mata rahamar Allah. Amma alfarmar ma'aiki ba zamu tsaya a gaban Ubangiji ba, na yafe mata duniya da lahira.
Sulaiman ya dauki file din gabansa mai d'auke da takardu da mukullai. Sauaran suma kowa ya saka hannu suka rike.
A hakan suka ce Baba idan ka yafe mata, to ga Ladi farm mun dawo da ita, ba tamu ba ce, ita da kanta da ka sadaukar Amma jikinta ya yi sanyi ta ce bamu ci gonar gabad'aya ba ta hanamu rabata. A yau kuma mun dawo maka da ita cikin gasgata kasonka ne yafi yawa a ciki, sauran kason ma da muke da hak'ki a cikinsa mun yafe maka duniya da lahira bamu da alaka da ita don munsan taka ce ".
Idanuwan kowa sai da ya cika da k'walla hatta oga Asad kuwa.
Yana kallon Bilki da ta ke safare a jikin Sulaiman.
Ta ki shiga cikinsu ta k'alubalence shi ko ta k'alubalenci Baba Babba. Amma a yanzu ta shiga cikinsu tana nemawa uwarsu yafiya tare da mayarwa Baba Ladi farm cikin y'anuwanta.
Yadda ya ga sun yi a gaban Baba gabad'aya sai suka bashi tausayi jarabawarsu akan uwarsu mai girma ne.
Ba dan tasirin Baba k'arami ba da tabbas ko kallon inda suke ba zasu yi ba. Haka ma dangin uwarsu tasirin jini ne kawai ya sanya suke sonsu amma mami al'amuran da ta cakalkala masu yawa ne. Allah ya jiƙanta ya yi mata rahama kawai.
Mafi munin jarabawar da namiji zai shiga rashin dace da mace ta gari. Mai take gaskiya, wacce bata siffantu da ilimin addini da aiki da shi ba, mai kuma tsananin kishi da hassada. Don sannu a hankali zata wargaza masa gida ta rushe ginin da yake tsakaninsa da y'anuwansa, ta jefawa y'ay'ansa rud'anin kowa baya sonsu ciki kuwa har da shi kansa ubansu. Duk juyin da za'a yi da irin wadannan matan ba zaka ga yadda kake so a cikin gidanka ko a tarbiyar yara ba.
Shiyasa idan za'a yi aure a duba tarbiyar uwa a duba d'ab'iar yarinyar ba wai fara mai kyakkwar fuska ba. Kyakkwar zuciya da dabiun addini sune zasu daidaita maka al'amura. Ba dan Allah ya so Baba k'arami da rahama bata danne shi ba, da tun da ransa za'a yi wnanan tawarwatsen gidansa kuma sai ya gagari danginsa shiga ba kuma yadda za'a yi dole a hak'ura a sallama shi.
Allah ka shirye mu kasa mu wanye lafiya.
Save Restricted Content Bot, [Nov 7, 2025 at 19:13]
*Surayya Gwaram*
08032773332.
Baba cikin jarumta ya ce "Ina sake jaddada muku na yafe mata Allah ne shaidar hakan. A wannan lokacin Munira ta sadaukar muku da Ladi farm ba tare da nemi yardata ba, ni Kuma na amince da hukuncinta cikin gasgata ta yi abin da ya kamata.
A yau kuma da kuka dawo mini da ita cike da yaƙinin kunsan tawa ce to ni kuma na bar miki ita duniya da lahira Har cikin zuc6na baku ne saboda mu ya'yana ne a yanzu kuma da rayuwata ya zo gargada ba ni d a bukartata. Idan Har akwia wanda ya dace ya mallaki Ladi farm to Faruku ne da mahaifinku, to shi mutuwa ya d'auke shi, Faruku kuma ya ci girma ya bar muku, ba kuma gillin komai a cikin bar muku Wallahi ".
Sulaiman ya kallesu ya yi kasa da kansa a hankali ya ce "Ya zamu yi?"
Suka yi magana kasa kasa.
Sai suka mike suka tunkari Faruku suka tsugunna a gabansa suka had'a baki wajen cewa "Yaya Faruku ka duba alafarmar maaikin Allah da girman mahaifanmu, ka karbi kyautar da muka yi maka. Baba ya bamu mun karɓa da godiya, mu kuma mun baka da dukkan zuciyarki don munsan ba abin da kake so ka k'arar da dukkan dabarar wajen ganin ta kafu irin Ladi farm to a yau mun dawo maka da itaa matsayin taka halak malak.
Bai ce komai ya saka hannu ya karɓa hawayen da suke idanuwansa suka zubo akan fuskarsa. Bilki ta saki ajiyar zuciyar nutsuwa don kuwa tabbacin ya huce ne.
Da jarumta ya ce "Na gode muku Allah ya saka da alheri. Zan cigaba da kula da ita da dukkan iyawata, sai dai ban karɓa a aml matsayin tawa ba, na karɓa don ba kula da ita. Amma bata kowa ba ce, ta zama wakafi Ga baba Babba da Baba K'arami. Duk kuma wanda yake son wani abu a cikinta kaitsaye zai zo ya co ko ya sha amma ba ta kowa ba ce, ba mai gadonta ila yaumil kiyama za'a yi ta juya kud'in da zata dinga samawar wajen yiwa marayu d addini hidima da niyyar Allah ya kaiwa iyayenmu."
Kowa ya amince da hukuncin Faruk.
Wani irin abu da ya tokare zuciyar Bilki ya fad'a mata.
Haka sauaran ma sai suka ji nauyin zukatansu ya warware.
Baba ya dinga fad'in " Alhamdulillahi, Ubangiji na gode maka da na ga wannan rana, Allah ka saka k'arshen waki'ar da zan sake ga ni kenan. Allah ka jefa soyayya da tausayin juna a zukatan dukkan yaran nan. Allah ka kore shaidanun da zasu shiga cikin zumuntarsu.
Allah ka saka albarka a cikin dukkan zuri'arsu da dukiyarsu, ka Basu lafiya ka saka su rayu cikin Salama ka azurta mu da zama yanki daya cikin aljanna.
Allah ka jiƙan Isa da Habiba.".
Kukan da Baba yake yi bai boye farinciki da jin dad'in da ya ji ba.
Daidai lokacin ya ce a kira Momi.
Ta zo ta ya fad'a batun Ladi farm da matsayar d saka cimma.
Murna kan murna ta yi tare da addu'ar Allah ya yiwa kowa albarka tare da jaddada muhimmancin hak'uri da yafiya.
Suna cikin haka aka fara kirayekirayen sallah.
Anan falon suka yi sallah gabad'ayansu. Baba ya ja su sallar da suka idar suka mike suka yi nafila.
Addu'a saosia Baba ya yi a bayyane suna amsawa da amin.
Bayan an idar matan suak shige daki.
Salaha da Hamida aka shiga hirar yaushe rabo.
Hamida aka warware tamkar ba itace ta taho a dole ba.
Bilki da Abida su dama tuni suka yi nasu sulhun.
Saddiqa da Anisa suka samu aminci.a zuciyarsu tunda Yaya Hamida ta warware to sun suma suka saki ransu tamkar suna gida Funtua.
Baba da mazan suna falo.
Sai da aka yi sallar la'asar. James ya kawo abinci kala kala da Bilki ta saka Angela da Alti su yi kafin su taho.
Baba da dukkan y'ay'ansa suka ci abincin.
Aka yi hotuna da vedios tamkar ba za'a daina ba. Zuciyar kowa ta warware salama da soyayyar juna suka maye zafi da ƙullaci.
Sulaiman ya ce "Bilki kamo mana Munira".
Baba Babba ya ce "Allahu Akbar! Babanku kad'ai ke tunawa da ita yau kuma kaine ka tuni da ita lallai Babanku guda".
Bilki ta k'irata vedio call. Cikin sa'a tana kwance akan gadonta ita kad'ai.
Maimakon Bilki ta yi magana sai kawia ita da Abida da su Anisa suka jingina a jikin Baba ana haska mata fuskokin kowa. Save Restricted Content Bot, [Nov 7, 2025 at 19:15]
Ta zabura ta tashi daga kwanciyar da take.
Cikin mamaki ta ce "Kai Kai Maigado kina da babban tukuici