Author : Hadiza D Auta Category : Romance
ki ce yau kowa yana gaban Baba. Ice dai kowa ya yi tuba ko?"
Suka dinga dariya.
Ta ce "Baban Abida yau kana cikin alheri dumu dumu".
Ya ce "Alheri mai girma kuwa Munira."
Ta ce ",To Alhamdulillahi Baba barka, barka Allah yasa k'arshen jarabawar da zamu sake ganin kenan".
Da karsashi ya ce "Ameen Ameen Munira ina yaran da maigidan?"
"Suna makaranta shi kuma Yana wajen aiki".
"To Ki gaishe shi."
Ya ce Baba tsaya, dan Allah waye ya tuna da ni don nasan babana da baya mantawa da ni idan an hadu haka babu shi".
Baba da alfahari ya ce "Ai kuwa yanzu ma Sulaiman ne ya ce "A kamo ki".
Ta yi turus. Don jingine Abida da ya yi na shekaru hud'u ba k'aramin bugunta ya yi ba.
Ya danne ta ce "To a ba shi wayar".
Aka mik'a masa ya ce "Munee how far?"
Ta rike haba ta ce "Gaskiya Yaya Sulaiman da Babanmu na nan ba zaka fantsama duniya irin haka ba. Ya ya haka? Kasan da na kud'ire idan ka dawo sai na gurfanar da kai don bibiyar zullimin da ka jefa mu na kana Raye ko kuwa ka mace."
Ya murmusa ya ce "Double sorry Barista a yi hak'uri na dawo ba Zan sake tafiya ba".
Ta ce "To yanzu nawa Abida ta yanka maka na diyya don nasan asussunka zai san ka jingineta".
Ya yi gajeriyar dariya ya ce "Ba wannan batun ai Munira ".
Itama ta yi dariya ta ce "Ai shikenan. Na gode Yaya Sulaiman Allah ya jiƙan Babanmu da Mamie na huce da kai".
Har ransa ya ji dad'in addu'ar da ta yi mussaman da ta had'a da mami.
Ya amsa da "amin muni na gode, na gode sosai Allah ya bar zumunci. Ki gaida yara da Babansu".
Daga haka aka dinga bawa kowa suna gaisawa.
Har aka yi sallama da ita tana jin tamkar ta yi tsuntsuwa ta sauka a cikinsu don ta taya Baba Babba farincikin da yake ciki.
Abida tana son a yiwa Sulaiman batun ya bata gidan da zata zauna, tana jin tsoron kada ya yi batun da zai wargaza ta a wajen su Hamida.
Dole ta shamik'e take ta yak'e Amma gabad'aya ba a nutse take ba.
Ganin magariba ta kawo kai ya sanya Baba ya ce "Duk ku bani hankalinku nan.
Daga yau na haramta ku tattauna rikicin Ladi farm. Na hana, na haramtawa kowa a cikinku. A yanzu ba ta kowa ba ce, ku yi komai a cikinta. Ku ci duk abin da kuke so na cikinta, ayi batun kasuwanci da waɗanda suke bukatr taimako tunda wakafi ce. "
Suka amsa da fad'in"In sha Allah baba Allah ya kara lafiya ".
Ya saka hannunsa na dama a kasa ya ce "Duk wanda ya yi imani da Allah, da manzonsa da ranar lahira, ya kuma yarda ni ubansa ne to ya d'ora hannunsa ya yi mubaya'a babu sauran gilli da tashin tashina a tsakaninmu gabad'aya".
Oga Asad ya yi saurin d'ora nasa akan na Baba. Faruk ya dora. Ansari ya d'ora, Hamida da Salaha suka d'ora. Abida ta dora nata, Saddiqa da Anisa. Usman ma ya dora.
Abida tana kallon Sulaiman zuciyarta na harbawa.
Ya dora amma ba duka hannunsa iya rabi ya dosana. Ya ce Baba na d'ora, sauran sai dawo mun zauna akan alafarmar da na ce zan neman sannan komai na zuciyata zai warware".
Dan haka bai yarda ya saka dukkan hannunsa ba.
Ya bawa Faruku dariya sosai don yadda ya makale rabin hannun abin dariya ne sosai.
A hakan Baba ya sake yin addu'a soaai.
Sannan ya ce "Alhamdulillahi ko yanzu na mutu ban bar baya da k'ura ba. Allah ya sake had'a zuciyoyinku ya rufa muku asiri duniya da lahira."
Gabad'aya suka ce "Ameen Baba".
Faruku ya yiwa hannuwansu a yadda suke hotuna.
Sannan kowa ya cire nasa hannun. Daidai lokacin oga Asad ya ce da Bilki ta tashi ya mayar da ita gida saboda yara yini guda basu sha nono ba.
A hankali ta ce "Baban Bilkisu ko James ya dauko su tare da Alti?"
Ya girgiza kai ya ce "A a mu tafi kawai ai an gama komai magharib ta kawo, yini guda su kad'ai".
Kan dole ta bishi suka tafi. Don yadda ake hada hada ba zaka so tafiya ba.
Magariba ma tare suka sake yi.
Hamida da ta zo da ƙyar sai gata ta bugawa mijinta waya da kanta akan ya yi mata hak'uri zata kwana a gida. Save Restricted Content Bot, [Nov 7, 2025 at 19:17]
Gobe Idan zasu tafi a kawo ta.
Dad'i ya lullube shi ya ce "To yanzu dai mun fita da Justice Yunusa muna kusa da wuse din zan biyo na gaida Baba tunda jirgin sassafe zamu bi".
Ta ce "Baban ummu da zaka lamince mini ba gobe zan tafi ba. Ina son na dan kwana biyu Salaha tana gari itama ta zo."
Kaitsaye ya ce "Na baki sati guda ki yi zamanki tare da y'anuwanki. Amma ya ya za ki yi batun kaya? Kin ga irin gaddamarki dai da na ce ki debi kaya da dama kika ce kala biyu sun isheki tunda ba dadewa za ki yi ba.".
Ta ce "Babu damuwa sai na saka na Salaha kasan itama ba auki gareta ba. Ko kuma na je boutique a aljihun Yaya Asad ".
Ya ce "Ho Hamida tun yanzu za ki fara yi masa lissafi?
Ta yi dariya ta ce Baban ummu da makudan kudade fa zan dawo, shekaru hud'u bai bani kudin kayan sallah da na azumi da ya saba bamu ba, ba zan bar Abuja bai lissafa abuna ya bani ba."
Ya yi dariyar k'arfi halinta.
Ya numfasa ya ce "Yanzu me kika siyawa baba da kudin da na baki ki yi masa tsaraba?
Ta fara dawurwarar ai ta mance su a Kano gabad'aya ta shafa'a."
Ya ce "Allah ya shirye ki kawai. Yasan tunda tare suka zo ba zata
ba sai dai ya siyo da kansa kud'i kam sun zama nata.
Amma tunda ta sauko ta rungumi sulhu ba abin da ba zai mata ba. Haka nan zai dage ya saita yaransu da suke kokarin bijire mata. Tunda shi suna shakkarsa.
Kayan abinci da ruwa da lemo mai yawa ya kawowa Baba da rafar yan dubu dubu guda biyu.
Baba ya dinga yi masa godiya da fatan alheri. Bai tashi ba sai da ya sake jaddada ya k'ara hak'uri da Hamida. Ya kuma gode da yadda yake rik'e da ita.
Tana gefe tana jin tamkar an tsumduma ta a aljanna yanzu kam sai ya samo wani abin da zai fad'a dan ya musguna mata ba dai ta watsar da ubanta ba.
Da zai fita ta bishi tana raragefe. Haka ya d'auki rafa guda ta dubu ce "Ga pocket money. Saura ki boye ki dinga jiran sai an yi miki".
Ta marairaice ta ce "Baban ummu kana bada ni akan kud'i ".
Ya murmusa tare da fad'in"Ai kin bari na gama gane ki. Ke da kanwarki Abida bansan me zaku yi da kud'i ba".
Ta yi dariya ta ce "A a wannan ta kere ni a son kud'i tun tana karamarta ta tara abin duniya. Labari idan Abida ta bayar sai an biyata.
Ya jijjiga kai ya ce "sai dai ku yi taya amma batun ta kere ki bai taso ba."
Ta kwashe da dariya daga haka suka yi sallama ya tafi.
Ta koma ciki ta wuce baba da mazan a falo. Zuciyar Baba fes yau shine rayuwa ta dawo masa daidai. Y'ay'ansa dana d'anuwansa suna shige da fice a gabansa cikin walwala. Motsi kad'an yake fad'in Alhamdulillahi ba kakkautawa.
Bayan magharib Usman ya yi sallama ya fara tafiya.
Faruku ma ya yi sallama akan sai da safe.
*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Just DM for your order @08033773332*.
Saddiqa ce kawai ta tafi, mijinta ya zo ya d'auke ta.
Salaha Hamida Abida Anisa kwanan zaune suka yi. Hira soaai suka yi mai sanya nishadi.
Washegari suna karyawa abida ta d'auke su a motarta suka rankaya gidan Bilki.
A farfajiyar gidan suka tarar da oga Asad cikin kakinsa.
Yana ganinsu ya juya da sauri ya koma ciki.
Da azama Bilki ta gan shi ya dawo. Ya saka hannu ya dauki baba K'arami.
Ya kalleta ya ce "Yi maza ki kawo mini na hannunki".
Ba sukuni ta ce ", Lafiya kuwa?"
Ya ce "Ki dai biyo ni da shi
yanzun nan".
Ta saba yaro ta bishi.
Ya karbe shi ya kwantar da shi kusa da d'anuwansa akan doguwar kujera.
Ya kalleta ya ce "Da Hamida da Ansari ba zasu gansu ba sai sun biya kudin ganinsu, tunda Basu komai ba laifina ya hana Su zo su ya ya'yansu.. Na ga su Hamida sun zo shiyasa na dawo dan na boyesu." Save Restricted Content Bot, [Nov 7, 2025 at 19:19]
Bilki ta murmusa tare da fad'in "Amma dai an yi mubaya'a a gaban Baba. Kai ka fara aminta tunda kai ka fara d'ora hannunka akan na Baba. "
Ya ce "Hakane to d'auke daya mu sauka".
Ya saba Baba Babba a kafaɗarsa, ya fara fita, ta bishi a baya tana d'auke da Baba K'arami.
Daidai lokacin sun shigo cikin falon.
Asad ya bawa Hamida na hannunsa, Bilki kuma ta mik'awa Salaha na hannunta.
Hamida ta zubawa yaron ido tana ganin fuskar oga akan fuskar yaron.
Haka kawai ta tsinci kanta da jin kunyar Bilki da oga Asad na rashin zuwanta ganin yaran.
Amma haka ta matse ta waske.
Suka gaishe shi ya amsa sannan ya fice.
Daidai lokacin da junior ya fito daga wajen Alti don jiya da suka zo tare da Salaha kin bin ta ya yi saboda Farha da Noor.
Ya zubawa Hamida ido. Sai kuma ya kalli Abida ya ce "Ammi kamar Maman Kano".
Abida ta ce "Ai kuwa ita ce junior".
Gaban Hamida ya yanke ya faɗi da ta ga junior. Ba buk'atar a fad'a mata dan Sulaiman ne don kammaninsu guda.
Kunya ta rufar mata fiye da kunyar rashin zuwa ganin twins.
Inama lokacin haihuwarsa ta yarda sun taho tare da Bilki?
Shi ya santa amma ita bata san shi ba.
Murya ba amo ta ce "Zo a ina kasan ni?"
Ya je kusa da ita ya ce "Ammi tana nuna mini pics dinki ta ce "Ke ce maman Kano ce kuma sister din Dadyce kuma sister dinta ce".
Hamida ta ji tamkar ya doka mata guduma.
Ta yi dif ta kasa magana.
A ranta kuma fadi take yi wato Abida tana nunawa d'anta su tunda dan yaro irin haka duk ya gane su.
Ta kasa cigaba da yi masa magana tsabagen an kashe ta da kunya.
Save Restricted Content Bot, [Nov 10, 2025 at 09:41]
*Dingishin kwado*
*Surayya Dee*
08032773332.
*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*A zo a saka order din ciccibin garari ko kazar sababi don ko zaki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Just DM for your order @08033773332*.
Sai kuma ya koma kusa da Abida yana fad'in "Zan biki ammi".
Abida ta ce "Tare zamu tafi, Dady ma ya dawo".
Ya ce "To yau zamu tafi gidanmu ne?"
Ta girgiza kai ta ce "A a".
Ya ce "Ya ce fa yana dawowa".
Tace "Idan mun je Sai ka tambaye shi".
Alti ta shigo musu da kayan motsa baki. Ta zauna ana hira mai dad'i tamkar komai bai faru ba.
Sai yamma Salaha da Abida suka tafi suka bar Hamida zata kwana, gobe Abida zata dawo ta dauke ta.
Bayan sun tafi Alti ma ta kauce ta basu guri.
Hamida ta ce "Maigado ikon Allah yawa ne da shi. Allah dai ya yi Yaya Asad Sai ya aure ki.
Ni dai yanzu na huce da kowa, na yi taubayan nasuha. Ki bi mijinki, nima yanzu zan gyra kurakuran da na rayu akansu. Tunda Allah yasa baba ya yafi kowa to duk wanda Zan faɗawa ya ji to muma mu yafe keta da warakin da suka gwada mana saboda babu idon ubanmu. Yadda ya yafewa uwarmu haka nake son Duk mu yafe masa gorin da ya janyo mana.
Maigidan nan ma na yafe masa Har cikin zuciyata.
Shiyasa na zo masa kwana."
Bilki ta murmusa tare da fad'in "Oh ba ni kika zo wa ba kenan?"
Da azama ta ce "A a gunsa na zo, kafin na tafi zan dawo na ki zuwan".
Bilki ta sake murmusawa har cikin ranta ta sake samun gamsuwar rikicin gidansu ya k'are.
Don bangrensu Hamida da Ansari ne masu kafiyar masifa kuma suna da tasiri a cikinsu.
Idan har yadda ta sauko haka Ansari ya sauko ya karbi sulhu to tabbas babu saurin rikici don Abida ta yi rauni. Yaya Usman kuma Baba zai danne shi tunda suma sune kaffafu a nasu b'angaren.
A farfajiyar suka tarar da Sulaiman yana zaune. Ansari ya fita da motarsa.
Salaha ta wuce bayan ta ce "Yaya Sule wai ina tsaraba ta ne?"
Ya murmusa ya ce "Salaha ai ba haka tsakaninmu mu bar wannan batun kawai.".
Ta wuce tana fad'in "To shikenan, an bar shi".
Abida da junior suka nufi inda yake.
A hankali ta ce "Yaya Dr Baban junior kwana biyu".
Ya d'auke kai ya ce "Kwana goma ma".
Ta yi dariya kad'an ba ta ce komai ba.
Junior ya ísa kusa da shi ya ce "Dady ka dawo, yaushe zamu tafi gidanmu to?"
Ya yi masa murmushi ya ce "Ammi zaka tambaya. Ita ta dawo da ku nan, bansan sadda zata mayar da ku gidanmu ba".
Zuciyarta ta harba. Murya ba amo ta ce "Ina ne gidan, a wacce unguwa ne?"
Ya kalleta tare da mamakin yadda take ganin zai zauna a Abuja.
Tsakaninsa da Abuja ya shigo ya yi uzzirin da ya kawo shi ya juya. A yanzu ma don Baba ne kawia ya sanya shi zuwa har da yin kwanaki.
Ya d'auke kai ya ce "Junior shiga ka yi alwallah ka zo ka mu tafi masallaci."
Ya juyawa kuwa ya tafi yin alawala.
Ta ce "yaron nan ya isa a saka shi a makaranta, sa'anin haihuwarsa tuni an saka su, shima ya matsu a saka shi. Don Allah ka cire yaron nan a cikin matsalarmu".
Kansa tsaye ya ce "Wai ban ce miki na bar miki shi ba ne?"
Gabad'aya ta ji numfashi na neman gagararta zuk'a.
Ta jijjiga kai ta ce "Baba ya yafewa kowa dan haka nima za'a iya yafe mini.
Baba ya ce wanda ya yi imani da Allah da manzonsa kowa ya huce ya yafewa d'anuwansa ashe kai baka d'auki wannan batun ba?"
Ya ce ban dauka ba tunda suna mini kallon na jingine ki ne saboda na wulakanta baba. Dole su san abin da kika yi don su gane ban raina baba ban kuma wulakanta aure ba".
Idonta ya ciko da k'walla.
Ta ce "Ka fad'a musu babu damuwa. Amma ka tabbatar ko da ka bar mini junior to dawainiyar da na yi, da wadda na yiwa kaina ban bar maka ba". Save Restricted Content Bot, [Nov 10, 2025 at 09:44]
Ya ce "Ke ce kudi suke gabanki, fad'a mini nawa kika kashe?"
Ta ce "Bari na d'auko littafin."
Ta juya da sauri ya bita da kallon mamaki.
Zuciyarta d'aya fa lissafin take yi da gaske.
Bata jima ba ta dawo bayan ta ce da junior Dady ya ce ya jira sai ya K'ira shi.
Kusa da shi ta zauna ta mik'a masa littafin.
Ya karɓa yana bin rubutun daki daki.
Ya kalli jimillilar lissafin.
Ya dago a kidime ya ce "Wai ke lafiyarki k'alau kuwa?"
Ba alamun kaduwa ta ce "lafiya sumul kuwa?"
Da mamaki ya ce "Kina nufin kin kashe zunzurutun kud'i har milyan dari uku da sittin Abida?"
Da dukkan gaskiyarta ta ce "Wasu ai diyya ne, wasu na kwanakin da na shafe cikin kewa ne, wasu na kuttun da aka dinga kunsa mini ne a inda kake ganin ba a yi maka alfarma an mayar maka da Ni ba, saboda sun haife ni, duk zaman nan na yi ne cikin taka tsantsan da zullimi ga kuma rashin fuska a wajen Baba da Momi saboda sun ba ni umarnin na koma d'akina na taurare.Wasu na yadda bamu da y'ancin yin walwala ne Ni da junior a gidan nan. Wasu na yadda na zama marar daraja ne a gidan yayana. Kuma ba kowa ya janyo mini ba sai kai. Wasu na wahalar raini da tarbiya ne da na yi ni kad'ai ".
Ya mike tare da mik'a mata littafin ya ce "To bari sai na fara fashi da makami."
Ta karɓa ba tare da ta ce komai ba.
Ta juya ta tafi.
Shi gabad'aya ma mamakinta ya kashe shi tabbas bai zaci ta kai nan ba duk inda yake zatonya ta kerewa tunaninsa.
Yo ko milyan sittin din kai ta ambato mass ai ya yi mamaki bare wannan zunzurutun manyan kuɗaden. To wai me ma zata yi da su ne haka?
"Dank'ari".
Ya furta a bayyane.
Yayin da Abida ta kasa cigaba da jarumta. Kuka take yi sosia a d'akinta.
Ta kira Faruku a waya.
Cikin kuka ta ce "Yaya Farouku ka yiwa Allah ka shiga tsakanina da Yaya Sulaiman. Ta tsara masa komai da suke tunda suka dawo.
Ya rarrashe ta akan ta kara hak'uri.
Da iyakacin gaskiyarsa ya ce " Amma ba zan tilasata shi ya zauna da ke akan dole ba. Idan yana sonki zai d'auke ki ne ku tafi. Idan kuma ba ya sonki hakan ba shine k'arshen farinciki ba sai ki yi hak'uri.
Tana son ta faɗawa Faruku abin da ta yi masa amma harshenta ya yi mata nauyi.
A daren wannan ranar Faruku ya zo gidan. Kaitsaye
d'akin da Sulaiman yake ciki ya nufa. Cikin sa'a shi kad'ai ya tarar da shi Ansari bai dawo ba ya yi nisan kiwo.
Da girmamawa Sulaiman ya dinga fad'in "Yaya Faruku sannu da zuwa. Barka da dare, ya ya iyalin?"
Ya amsa da walwala sosai tare da zama a gefen gadon.
Faruku ya ce "Zamu yi magana.
Ka yiwa Allah ka fahimce. Duk runtsi ba zan k'i ka ba. Ba zan bi bayan karya ba".
Sulaiman ya ce 'To na kuma gode".
Faruk ya ce "Wai ka ce ka bar mata junior?"
"Tabbas na fada mata kuma itama ta san ina da hujjar da zan fad'a mata hakan akan yaron"
Sulaiman ya fad'a kansa a k'asa.
Yaya Faruku ya ce "Yanzu tunda Baba ya yafe mana, ya