Author : Hadiza D Auta Category : Romance
yi mini alk'awari ko kuwa na fara fita nemansa da kaina?"
Idonta ya ciko da k'walla.
Na yi shiru amma dariyar da ban shirya ba ta k'wace mini. Na ce "Ni wacece ta ce mini ita dakhila ce ne?"
A hassale ta ce "Abida ce amma sadda na fad'a din AI ban gane kaina ba, yanzu kuma an rataue ni shekaru uku ai dole na k'osa tunda raine da ni".
Ni dai dad'in yadda aka jarrabi ta akan Yaya Sulaiman nake yi don kuwa a bayyane yake tana da tasiri a cikin y'anuwanta tunda ta sauko ta huce da mu, to fishin kowa ba zai ma abin damuwa ba tunda hatsabibiyar tasu ta yi laushi irin tub'us din nan. Sai dai Bilki ta san da sauran rikici a gaba don Yaya Sulaiman ya fusata da ita takaddama ce mai tsananin gaske zata sake Tashi. A ranta ta dinga addu'ar Allah ya shiga don kuwa ga ni take ba k'aramin jan Abida zai yi a k'asa ba.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Save Restricted Contents Bot, [Sep 19, 2025 at 11:31]
*Surayya Dee*
Hakurin nan dai shi Bilki ta bawa Abida.
Tare da adduar Allah ya bayyana shi.
Sai azahar suka tafi nasu gidan su ya'yansu.
Daga kan Bilkisu, Amal da Noor basa bata matsala don kuwa tunda ta zane Hafcy suka sake nutsuwa.
Yayin da Aysha da Hafcy har ma da Laura ido ne a tsakaninsu. Suna yin yadda suke so a gidansu. Yayin da ta koma gefe take kallonsu.
Bilki na zaune tana cin hadddedn kulikulin da ya Asad ya koya mata ci na Ummiel foods 08036355535....wayarta ta hau kuwwa. Ta dan murmusa ganin sunan Baban Bilkisu ke yawo a fuskar wayar.
Ta dauka da walwala ta ce "Baban Bilkisu ka sauka ne?"
Da take yana cikin tawagar da suka raaka Shugaban Yan sanda na k'asa (I.G). Zuwa jihar Sokoto kan sha'anin tsaro.
Jiya suka tafi, yau kuma zasu dawo.
Ya ce "Eh mun sauka sai dai zamu fara raka oga gida. Tuwo nake son ci, ki mini da kanki if possible Maigado".
Da kanzagi ta ce na shinkafa ko na semo?"
Na fi son na masalina fa".
Cikin hanzari ta ce ka samu Baban Bilkisu. Allah ya kawo ku lafiya".
Ta mike ta nufi kicin ta shiga store ta fito da garin masalina leda d'aya. Kad'an zata yi tunda yaran basa ci. Manyan kuma abin da suke so suke sawa a yi musu.
Ta bude murya ta k'ira Alti. Ta iso tana fad'in me kike so ne Mahmah?"
Daidai lokacin Laura ta shigo kicin din. Ta bude sink tana wanke hannunta.
Bilki ta ce "Baban Bilki yake son cin tuwo ya ce na yi masa da kaina."
Farinciki ya bayyana a fuskar Alti a dalilin ta fara gamsuwa Bilki ta fara son mijinta, nan gaba zata dawo da hakurinta ta yadda zata jure duk wani k'alubalen zamanta a gidan.
Don gabad'aya Alti a ankare take da ita kada ta yi musu sanadin da zasu bar wannan aljannar duniya tunda ta gane Bilki irin mutanen nan ne da basa neman hujja a so ko a kiyayya. Idan suna son mutum to suna sone da dukkan zuciyarsu duk kuma nak'asun wanda suke so zai zama an amsa uzziri. Idan kuwa basa son mutum komin kirkinsa da abin duniyarsa basa so, dole a k'yalesu.
Da azama ta ce "To da me zan taimake ki?"
"Ki fito da kaza ki wanke, ki silala mini, miyar ayayo zan yi masa ".
Alti ta ce "Yanzu kuwa. Ta bude firiza.
Laura ta fice tana jin takaicinsu gabad'aya ya kamata. Tare da tunanin yadda zata b'ata girkin tunda kishinta take yi sosai, so take a ce itace a gidan tana bada umarni ayi ko a bari. Amma ya tashi ya dauko bazawara yana b'are b'are a kanta. Ta fice ba wanda ta yiwa magana illa tafiyar tak'ama da take yi. Bilki ta jijjiga kai tana ayyana al'amura masu yawa, idan su Aysha suna yin dibar karan mahaukaciya da ita tana hakuri tare da zuba ido to lah shakka Laura ta yi kad'an. Amma dai zata sake daurewa tunda idan ta yi magana Alti balbale ta zata yi da fadan ta koyi rashin kawaici.
Sai da Alti ta dora ta ce "Da su Amrah nake yin waya, d'an nawa ya ce mini suna tafe cikin satin nan".
Bilki na dauraye tukunya ta ce "Haka suka ce mini dazu, zasu biyo matar k'anin babansu zata zo wani aiki, wai da motar ofis zata zo kuma zata yi kwanaki biyar."
Cikin nutsuwa da k'ware wa suka shirya masa tuwon da lafiyayyar miyar ayayo da aka burge gudar kaza a cikinta.
Ta hada masa salad don ya samu daidaito a cikinsa.
Ta shirya masa a falon saman da suke shan ruwa. Sannan ta zarce nata saman don yin wanka da kintsawa.
Ta bata lokaci tana shiryawa sosai ta yi kyau. Farha ta kalle ta ta ce "Mahamah kina da kyau fa! Kuma na ga fuskata irin ta ki ce, nima zan yi kyau kenan?"
Ta murmusa tare da fad'in "U are so beautiful Farha, kina da kyau ma fiye da ni".
Dad'i ya sanya Farha yin dariya har da tafi. Bilki ta kalle ta ce "Ki je wajen su Noor Dady yanzu zai dawo kada ya yi fadan bai gan ki a gunsu ba".
Ta fice a guje don kuwa ya fad'a mata idan bata zama a samansu to babu ita a zuwa London wajen Yaya Khadija.
Sanye take cikin super wax karshen tsadar, doguwar riga free size haka ayi ta babu ado illa tsadaddun stones da aka watsa a rigar. Save Restricted Contents Bot, [Sep 19, 2025 at 11:35]
Ta yi kyau har ta gaji, ta yi fari, fata ta yi taushi k'warai da gaske. Zai yi wahalar gaske ka kalle ta sau daya baka sake na biyu ba.
Tana tafe k'amshi na alfarma na biye da ita. Gabad'aya samanta ya karade da k'amshinta.
Cikin nutsuwa take sauka zuwa inda tasan zai yada zango. Sai dai turus ta yi cikin tsananin alajabi a dalilin yadda ta tarar da Hafcy da Laura suna zaune suna cin tuwon da ta ajiyewa maigidan. Aysha na gefensu tana cin salad a bowl.
Bak'inciki ya turniƙe ta. Daidai lokacin kuma aka bude gate din gidan tabbacin ya iso kenan.
Da tsananin b'acin rai ta ce "Wa ya baku izinin taɓa abincin nan?"
Kaitsaye Aysha ta ce "Abinci a gidan nan kuma har sai mun nemi izni?"
Yayin da Laura ta ce "Mun dauka namune tunda daddy yana son mu dinga cin wanda kika saka aka dafa."
Yayin da Hafcy uffan bata ce ba.
Bilkisu tana d'akinta yayin da su Amal da Noor da kuma Farha suka yi waje don taro Dady.
Bilki ta kalli Laura ta ce "Ke ki tsaya a matsayinki kada ki yi kokarin wuce iyaka, idan su sun xama dole su zauna ke fa? Babu dalilin zamanki tare da mu".
Aysha ta ce "Ai kuwa zamanta daram don a tare da mu ta rayu".
Yayin da Laura ta fara kukan an mata gori. Daidai lokacin kuma ya iso inda suke shi da yaran.
Ganin Laura na kuka su kuma sun yi cirko cirko ya sanya shi tambayar ba'asi. Hafcy ta yi fit ta zayyane masa kanun labari ta sigar da ba zai ga laifunsu ba. Ya kalli Bilki ya ce "Kada ki damu don sun ci, idan sun rage zan ci sauran, idan kuma babu bari na saka charity ta yi mini wani abin, kada wannan cin abincin ya zama abin damuwa. Takaici ya mak'ure ta. Ta kasa ce wa komai a dalilin sun cinye gabad'aya tunda dama dauri uku ta yi, ta saka masa guda biyu ta zubawa Alti d'aya tunda itama masoyiyar tuwon ce, kuma tun lokacin ta zauna a kicin din ta ci bare ta dauko masa na Altin.
Murya babu amo ta ce "Sannu da dawowa."
Ya amsa da fad'in "Sannu sarauniyar shaiba ya gida da yaran?"
Ya zuba salad din ya fara ci kana ganinsa ka san ya kwaso gajiya da yunwa.
Ta had'iye kukanta ta shiga kicin ta yi maza ta d'ora ruwan tuwo tunda da miyar a tukunya.
Tana cikin aikin charity ta shigo ta yi mata sannu ta fara hidimar abincin da ta tabbatar shi ya bada umarnin ta yi masa. Bata hana ba. Ta kammala ta shirya a tray ta kinkima ta nufi inda ta bar shi. Yana ganin ta da tray ya zabura ya mik'e ya karbe ta yana fad'in kina ganin halin da kike ciki mai zai saka ki dauko da kan ki?"
Ita dai bata ce uffan ba. Ya kai
ya ajiye ya zuba tuwon yana fad'in "Sannu da aiki Maigado "
Ta isa ta zauna amma ta kasa amsawa. Daidai lokacin k'iran Amrah ya faɗo wayarta.
Ta dauka ta kara a kunnenta. Ta ji muryar yarinyar a sanyaye tana ce mata "Mahmah zuwan namu ba zai yiwu ba sai next time , an daga zuwan Antin da zamu biyo, lokacin fa5 zata zo din kuma hutunslku ya k'are ga yayanki ki masa magana tun dazu yake mini kuka, abin da ba ya yi, amma yau ko abinci ya k'i ci duk ya tayar mini da hankali".
Ba kuzari ta ce"ba shi wayar".
Murya a dakushe ya ce "Mahma!
Bilki ta aro jarumta ta ce "Yayana ya da haka kuma, ina ce wanccan hutun kun zo? Ka yi hak'uri idan ka daina kuka to ana yin hutu zan turo a d'auko ku. Ku yi duka hutunku anan tare da su Farha ".
Murya ba amo ya ce"To".
Yauwa Yayana ka daina kuka ai ka girma, ina kanwarku?"
Kaitsaye ya ce "Tana can tare da uwarta".
Billki ta yi maza ta ce "Tana wajen anty dai ko".
Bai amsa ba ya ce "Ki aiko mini kayan da kika ce kin siya mini, ina Alti, ina Farha?"
"Duk suna lafiya anjima zan kiraku sai ku yi magana da su."
Suka yi sallama.
Ya kalle ta ya ce "Farouku rigima".
Ta yi yak'en dole ta kasa cewa komai. Ta tafi tunanin yadda take gwagwarmaya da su Hafcy haka Hawwah take gwagwarmaya da Faruku don kuwa Amra mai sanyi hali ce irinta.
Yana cin tuwon ya ce "Na ji dad'in tuwon nan gobe ma ki yi mini irinsa, thank you". Save Restricted Contents Bot, [Sep 19, 2025 at 11:46]
Kafin ta amsa masa ta ga Aysha ta mike ta fice Laura da Hafcy ma suka tashi suka bi bayanta.
Daga su sai k'ananun kan dole ta hak'ura ta sakar masa fuska amma abin da suka din ya yi mata ciwo tunda dai da gayya suka yi hakan sannan su ba cin abincinta suke yi ba, sawa suke yi a yi musu, shine yau suka shammace ta suka yi mata haka ta kuma tabbatar Laura ta ji lokacin da take faɗawa Alti Baban Bilki ke son cin tuwo.
Zaman yarinyar a tare da su ya fara gundurarta don ta fahimci ita ta take sake koya musu wasu shakiyancin tunda ta fisu shekaru da budewar ido, bayan haka ta fahimci son Baban Bilkin ta fara yi, don rashin kunya da rashin mutunci, shiyasa take ganin kishinta a fuskarta muraran.
Bilki ta numfasa tana jin idan yarinyar ba ta bar gidan ba, ba zata taɓa daidaito da su Aysha ba. Gara ta koma gaban uwarta ta zauna amma ba a gidanta ba.
Sai da suka kwanta yana ta damƙarta cikin rawar jiki. A tausashe ta ce "Baban Bilkisu ina ganin Laura ta koma gidansu hutun nata ya isa haka".
Da azama ya ce "Ki yi hakuri ya za'a yi bata ce zata tafi ba, ace mata ta tafi, k'anwar Rukayyace fa, kin san kuma a hannunmu take tun tana da shekaru goma."
Kaitsaye Bilki ta ce "To da yake ai yanzun ba Rukayyan ba ce matar gidan, na gaji da zamanta a cikin gidan nan gaskiya".
Ya yi shiru yana ayyana yadda Bilki ta ce Rukayya gatsal duk kuwa da mutumiyarta ce ta sosai don ya sha jin suna waya sannan yadda take nan nan da Bilkin bata yiwa Abida haka.
Ya nisa ya ce "Yanzu dai bari na gaisa da unborn na kuma yi barci ma tattauna daga baya".
A wannan ranar a dole ta biye masa, don gabad'aya zuciyarta ta yi nauyi ainun. Don haka babu wani aramshin a zo ga ni a had'uwar.
Washegari sassafe ya fita office ko karyawa bai yi ba, tunda zai dawo. Tana barci bai tashe ta ba, k'arar bude gate ya tashe ta. Ganin bakwai bata cika ba ma ya sanya ta koma ta kwanta don ta san sai wajen shadaya da ya dawo, a kuma wajen yaran zai yada zango su karya.
Bata tashi ba sai wajen goma da rabi. Kaitsaye wanka ta shiga, kafin ta fito tuni Rahina sabuwar yar aikin da ta dauka matashiya ta gyara d'akin sosai.
Tana fitowa kuma ta fad'a toilet ta yi wanka.
A nutse ta shirya duk yadda zuciyarta ta yi mata nauyi kwalliya ta yi sosai ta fece tamkar zata je babban taro.
Ta fita falonta daidai lokacin Alti ta shigo ta zauna suka gaisa. Ta ce "Na yi miki kunun gyada na kuma soya doya, na yi ferfesun naman rago".
Da girmamawa ta ce "Sannu Alti zuba ki bawa Rahina ta kawo mini, su Farha sun karya ne?"
Ga su can a saman tsakiya suna karyawa da Bilkisu ".
Ta ce "To sannu da aiki Alti. A ranta kuma ta gasgata mutanen da suke fad'in suna na tasiri. Gabad'aya Bilkisu yanayin halayyarta ne da ita. Shiru shiru babu hayaniya bata da matsala sannan aminiyar yara ce.
Cikin nutsuwa take karyawa tana tunanin Baban Bilkisu da ya fita bai karya ba. Ta ja k'aramin tsaki a dalilin ko yana nan ma tasan barinta zai yi ya tafi wajen ya'yansa su karya tare. Ta kammala Rahina ta kwashe kayan, tana zaune tana nazarin rayuwarmu da bata zuwa mana yadda muka zace ta, kira ya faɗo wayarta.
Da hanzari ta dauka murya a sake ta ce "Maman Abdul me ya samu wayarki ne? Na yi ta k'iranki har na gaji".
Ta amsa da fad'in "Ke dai bari Maman Amrah sace mini aka yi, kin san kuma yanzu tashin hankaline idan ka rasa sim dinka. Har na ce na hak'ura zan siyi sabo to kuma komai nawa da layin na bude shiyasa na daure na dawo da shi ".
Bilki ta ce "Haba na yi nema har na gaji, jiya na ce wa Alawiyya ta fad'a mijinta ta je ta dubo mini ke, amma muna gama wayar nan zan k'ira na fad'a mata na same miki".
Basma ta ce "uwargida kuma amaryar Yaya Asad kina tafe kina amon bullet".
Dariya ta kama Bilki ta ce "Amon bullet ki ce na zama fasa taro kenan?"
Basma ta yi dariya ta ce "Zan so na gan ki Bilki nasan yanzu kin dawo sarauniyar shaiba ta gasken ba wacce dan tsakon nan ya ajiye ba. To ya ya yanzu dai babu matsalar oza room ko?". Save Restricted Contents Bot, [Sep 19, 2025 at 11:49]
Bilki ta numfasa ta ce "Babu Basma, duk matsalar da ta dame ni a gidan Sahal yanzu ba ni da ita, amma kuma na sake faɗawa wata matsalar mai zafin gaske har nake jin tamkar na girgije na bar zaman".
Salati mai tsananin gaske Basma ta saka tana fad'in "Eh hakane wato hakurine ba za ki yi a inda ake sonki ake daraja ki ba? Aurenki da Yaya Asad fa al'amura masu yawa yake nufi a cikin gidanku. Idan kin kwantar hankali kin jure, komai zai daidaita muku gabadaya. Idan kuma kin kasa jurewa to ina tabbatar miki komai zai sake k'wacewa ne, ku sake jefa Baba Babba cikin tahsin hankali. Haba Bilkisu menene ba ki yi hak'urinsa ba a inda ma bai kamata ki yi hak'urin ba, amma kin yi. Yaya Asad ai alfarmarsa yawa ne da su a gunki ko bai ci arzikin jinin da ya gaurayaku ba, to lallai ya kamata ya ci na dakon soyayyar ki da ya wanzu yana yi, ya kamata ki ba shi hadin kai ya daidaita ahalin gidanku waje d'aya!
A sanyaye Bilki ta ce "Ni fa babbar damuwata da shi akan yara ne, baya kaunar abin da zai sosa musu rai, kirikiri suke musguna mini amma ba zai dauki mataki ba, ina son mu dinga karyawa tare amma sai ya tafi gunsu su karya, da daddare kuwa wani lokacin sai na yi barci kafin ya zo d'akina, yana gunsu fa".
Tsaki Basma ta yi ta ce",Eh lallai kin samu guri dole ki yi shanya, to dan yana sonki sai ya k'i kula ya'yansa? Wai yaushe kika zama hakane?".
Murya ba amo Bilki ta ce ba za ki gane pain din ba. Amma ai bai kamata yara sai abin da suke so za'a yi musu ba. Dan dai ba ke kike gidan ba ne. Sannan ga k'anwar matarsa ta kammala B.U.K. Tana nan tare da mu tana sake koya musu dabarun musguna mini."
A sanyaye Basma ta ce"Ki yi hak'uri ai tunda aka yi sa'a mata ne to matsalar gajeriya ce kamar yau duk zasu bar gidan kowacce ta je ta fara fuskantar nata k'alubalen auren. Abin da nake so dake ki dinga binsa kuna karyawar tare, zai ji dad'i sannan za ki daina ganin hakan a matsayin laifi. Da daddaren ma ki dinga shiga cikinsu ana yin hirar da ke".
Ta ce "Basa saka ni a ciki, shine yake kula ni sai ƙanƙananun yaran kawai".
Basma ta ce "Tunda yana kula ki ai shikenan sai ki yi da shi da k'ananun yaran, da lokacin barci ya yi sai ki tura yaran su kwanta, ke kuma ki fara gyangyadi da ya ga haka zai sallami manyan".
Bilki ta numfasa ta ce "Hmm amma zan yi trying".
Basma ta nisa ta ce "Ni fa Duk wannan ban d'auke su matsala ba, ban yi zaton kema zasu zame miki matsala ba don kuwa kin fuskanci wadanda suka fi haka tsananin gaske kin kuma hak'ura. Me yasa ba kya zuwa d'akinsa sai dai shi ya zo?"
A sanyaya ta ce "Hoton tsohuwar matarsa ya girke a d'akin da kuma gefen gado, ni kuma Wallahi ba zan je na kwanta alhalin da hotunan a d'akin ba".
Basma ta ce "Da kin iya, kin kwantar da kai da tuni bai cire ya saka su cikin shirgi ko a saka su saman yaranta da dakunansu! Bilki Bilki, ki sauya takunki, ba shine kawai yake da laifi ba. Ni gaskiya ma nafi ganin aibinki. Shi Sahal da yake kina sonsa kin jure kin cinye dukkan tuwon iskanci da wulak'ancinsa ko?"
Bilki ta yi shiru ta