Author : Hadiza D Auta Category : Romance
nauyi ko kunya. Haka itama yake rungume ta Bilki ta yi musu.
Ana jibi zasu bar London Khadijah ta ce "Dady zamu je gidan Anty Ayusha fa na fad'a maka tana mini kirki, Ina zuwa na yi weekend a gidanta, k'asan idan y'an arewa muka hadu a turai duk zama muke yi dangin juna. Ita da mijinta suna mana kokari suna guiding dinmu sosai."
Ya ce"To zuwa anjima idan mun je yiwa sisters dinki tsaraba sai mu je gidan".
Sosai Khadijah da Bilki suka saba suka samu kyakkwar fahimta duk da Khadija tana yawan tuna mominsu tare da jin da yanzu itace a gefen Dady ba Anty Maigado ba. Sannan yadda yake zumudi akan amaryarsa ta gane ko momi na da rai zai iya nad'e k'afar wando ya yi zawarcinta har ya aure ta duk rikicin da za'a yi kuwa. Amma ta danne don kuwa gara ace auren ya yi da ace Babansu na harkar banza da zubar da mutuncinsa da nasu.
K'arfe biyar saura na agogon GMT Ummi ta karbi ziyarar manyan baki cikin sa'a suka tarar da Baban Husna a gida dan haka da karramawa ya karbi kwamishina a falonsu. Cikin mintina kad'an aka cika gabansu da cimaka iri iri. Sosai ya yi musu godiyar yadda suke kula da su Khadija suka basu kofar zuwa wajensu. Ya yiwa yaransu kyautar bajinta sannan suka tafi. Bilki tana yaba kirkin Ayusha da mijinta tare da yiwa Husna, Hanan da Aryan addu'ar su zama masu albarka.
Fatan alheri ga kanwata marubuciya Ummi Ayusha Muhammad da iyalinta da suke zaune a birnin London.
Washegari suka mayar da Khadijah makaranta suka yi bankwana suka rabu cikin sanyin jiki don sun ji dad'in zamansu taree que ne illa tuna mominsu shike nan su da ita sai a darussalam. Ta dinga yi mata addu'o'in neman gafara har ta samu nutsuwar zuciyarta.
Ta dauki wayarta ta shiga what'sapp ta shiga ta tura hotunansu cikin group dinsu da Aysha ta bude musu su kad'ai. Su hud'u ne a ciki Aysha Khadija Hafcy sai Bilkisu tunda itama da wayarta Amal da Noor ne babu su.
Cikin mintina kad'an Aysha ta yi tagging hoton Bilki da Babansu ta ce amma kuwa Khadija kin ci amanar momi da kika turo mana wannnan abin, na rantse tunda na zo duniya ban tab'a ganin abu mai muni a zuciyata irin wannan pic's din ba. Yanzu Dady abin da ya zama ke nan, ji yadda ya wani mak'ale ta? Ke kuma da yake sarai sunanki shine har da turo mana?"
Hafcy ma ta ce "Yaya Khadijah kam ai gabadaya al'amarinta babu kishin kai ".
Bilkisu dai stickers din dariya take ta turawa babu adadi don gabad'aya Dady ne ya bata dariya yadda yake sanye da k'ananun kaya ya dawo kamar saurayi yana ta soyewa abinsa.
Aysha kuwa ta kufula ta zazzage ta tare da fad'in zata cire ta daga group din tunda take dariya bayan abin kuka ne ya same su.
Khadija ta ce "Ya Aysha ki yi hakuri Anty Maigado bata da damuwa. Da ya auro wacce bamu santa ba ta zo ta cutar da shi muma ta cutar da mu fa? Ai gara ita duk tsiya dai y'aruwarmu ce".
Nan da nan Aysha ta danna voice na tsawon lokaci tana fad'in "Ta ina ta zama danginmu? Sun kai Baba Babba fa kotu? Sannan an ce za'a ba shi anty Laura don ta cigaba da kula da su Noor tunda sun saba da ita amma fir ya k'i ta. Sai kawai ya kwaso mana wannnan mai tafiya mazaunai na sittin, saba'in, sannan yanzu na gano tuntuni ya so aurenta tunda har mai suna ya yi mata." Ta fara kuka murya na rawa ta ce"Na tausayawa poor momi! Allah sarki ta sha wahalar haihuwa an tashi an sakawa d'iyarta sunan budurwa wohoho me za'a ce da maza ne?"
Ta kammala cikin tsananin kuka.
Khadija tana kwance tana sauararen Aysha jikinta ya mutu tabbas itama ta ji babu dad'i amma kuma ya zasu yi ne tunda ba zata dawo ba, sannan basu isa hana shi yin aure ba. Kanta ya kulle mussaman ita bata ga aibun Anty Maigado ba. Sannan zuwansu duk abin da zai yi mata baya shawara da matarsa kawai bata yake yi, kuma bata ga ko a fuska Anty Maigado tana jin babu dad'i ba. To shi ke nan duk kokarinsa na ya faranta musu, sai kuma su k'i kwnatar masa da hankali ta hanyar zama lafiya da matarsa. Ta kuma fahimci Aysha tana son jagorantarsu su musgunawa matar Babansu ta yadda zamanta da shi zai gagare ta.
A sanyaye ta yi nata voice din da fad'in Momi is gone ba zata dawo ba forever. Mu yi hak'uri mu zauna da matar da Dady ya aura da girmamawa dan yasan mun gode da hidimar da yake yi da mu babu gajiyawa. Idan ya gane muna da damuwa da matarsa zai kasa samun nutsuwar da ta dace da shi. Don haka mu yiwa Momi addu'ar samun rahamar Ubangiji shine abin da tafi bukata. "
Nan da nan Aysha ta ce "Hidimar da yake da mu ashe ba Allah ne ya kallafa masa ba? Tunda ke ba kya kishin uwarki sai ki k'arata ke kad'ai sannan kada ki kuma turo mana wannnan bak'incikin!
Hafcy ta yi tagging da fad'in "Wlh kuwa Yaya Aysha duk yadda nake son matar nan yanzu haushinta nake ji, tunda ta yi kuskuren auren Dady ai ba sauran girmanta a idona tamkar mai jiran momi ta mutu ta aure shi".
Bilkisu dai bata ce komai ba sai dai ta shiga tunanin maganganun yayarsu na cewa saka mata sunan anty Maigado ma
cin amanar mominsu aka yi.
Daga haka Khadija ta sauka daga what'sapp din tare da tunanin Aysha zata d'agawa masu gidan hankali dama ita bata da dad'in mu'amala.
Yayin da Aysha ta dinga jan kunnensu Hafcy saura su ce zasu shige mata.
Tirk'ashi.
Ranar juma'a da daddarre suka sauka a birinin Abuja suka tarar da tawagar y'an sanda na dakonsu.
Har gida aka kawo su.
Ita dai Bilkisu tana kallon yadda ake ta k'ame musu tare da sarawar girma.
Wannan nau'in gaisuwar na matuƙar yi mata dad'i a zuciyarta.
A daddafe suka yi wanka da ruwan zafi sannan suka yi salla suka kwanta barci ya yi awon gaba da su don sun gaji lik'is.
Da yake asabar ce da suka yi sallar asuba sake rungume ta ya yi suka koma barcinsu. Sai wajen 12 suka farka. Suka yi wanka sannan suka nufi kicin don karyawa don kuwa a cikin katafaren kicin din dainin eriya yake.
Tuni an tanadar musu abinci kalakala na alfarma. Da kansa ya zuba mata sannan ya zubawa kansa. Ita dai cikin tsantseni take cin abincin duk kuwa da ba shi da makusa kawai ita yadda duka ba musulmai ba ne suke yi musu abinci ne ya dame ta.
A tausashe ta ce "Baban Bilkisu mu je gida anjima mu gaida su Baba daga nan mu dauko yara da Alti".
Ya girgiza kai tare da fad'in "A a Sai na gama hutuna zasu dawo".
Ta zuba masa ido ta ce "Baban Bilkisu ka ce mini fa za'a sake baka hutun tafiyar da ka yi na sati biyu. Kuma yanzu sai mu yi ta zama haka?".
Ya zuba mata ido cikin wani irin salo ya ce "Ba za su dawo su dinga katse mana amarci ba. Dan haka gobe zamu je mu gaishe su amma ba da yara zamu dawo ba".
Ta yi k'asa da kanta don har zuwa lokacin nauyinsa da kunyarsa basu gama barinta ba. Ya cigaba da kallon yadda ta sake yin fari, fatarta ta yi wani irin smooth na ban mamaki. Zuciyarsa ta harba da sauri don kuwa ta sauya sosai wanda bai lura da hakan ba sai a lokacin.
Zuciyarsa ta amince masa cikine da ita don gabad'aya ta danyace ta sake zame masa yarinya sosai.
Ya tafi lissafin aurensu idan har daidaine suna cikin sati na bakwai don anyi bikin da sati biyu suka tafi America. Sun shafe satika biyar kafin su dawo, ke nan suna daf da shiga watanni biyu. Zuciyarsa ta cika da farinciki a duniya yana son yara yana son ya'ya da yawa. Tun kafin ya tabbatar da zatonsa ya ji son abin da yake cikinta yana ratsa shi ta ko ina.
Ya tausasa harshe ya ce "Me yasa kike son su dawo tun yanzu?".
Cike da tab'ara ta ce "Gaskiya ban son abincin wannan matar na fi son na Alti".
Ya yi shiru tare da tunanin yadda shi da iyalinsa suke son girkin charity mussaman ya rabota da hotel d'in da take aiki ta dawo zama a gidansa gabad'aya. Tana da d'akinta a sashin y'an aiki. Ya numfasa ya ce"To kafin su dawo ki dinga yi mana dan gaskiya ba zan yarda hankalinki ya kasu biyu ba a wannan kwanakin. Kawai ki bari na kammala cikace su".
Ta rausayar da kai ba tare da ce masa komai ba domin duk zalamarta akan al'amarin yayan nata ya k'ure ta. Matuk'ar ya mu'amalance ta sai ya gurje ta da kyau.
Ta fara jinsa cikin zuciyarta, duk wani kallon da ta dinga yi masa a baya na baibai ya fara gushewa daga idanuwanta. Ta gasgata Abida da take yawan fad'a mata bak'in namiji ba shine muninsa ba, sannan yayansu ba mummuna bane kawai dan ta rufe zuciyarta akansa ne. Yanzu kam ta amince ba mummuna bane sannan tabbas jarimi ne ko cikin jarumai.
Washegari sai yamma lis ya dauke ta zuwa gidansu, da ledar tsarabar mutanen gidan. Da kansa yake tuki, yayin da take gefensa a zaune. Gabaɗayansu sun yi kyau na ban mamaki. Sassanyen k'amshi na tashi a jikin kowannensu.
Da farinciki sosia Baba Babba ya gaisa da su yana jin auren Asad da Bilki ne tsanin yin sulhu a zuri'arsu don kuwa ya lura ya'yan Baba k'arami gabad'aya basa iya yin mu'amala mai yawa da shi da ya'yansa dama Bilkin ce tafi sassauci. Yanzu kuwa saboda ita zasu yi mu'amala da gidan Asad daga haka kuma har komai ya warware albarkacin addu'ar da yake yi a kullum na kada zumuncinsu ya waste gabad'aya.
Ya dinga sanya musu albarka tare da nasiha mai ratsa jiki. Yayin da tausayinsa ya kama Bilki ya tsufa sosai gabad'aya rauni ya baibaiye wanda ba na rashin gata ba ne illa na rashin cikakkiyar lafiya da kuma rauni irin na gajiya da duniyar da tashin hankalin da yake cikinta.
Suka ajiye masa tasa tsarabar wnada jallabiyoyine fararen sai turaren alfarma.
Haka momi ta dinga yi musu addu'a cikin bayyananen farinciki.
Ta yunk'ura a hankali ta yi ciki wajen yaran tare da adduar Allah yasa Abida na gida.
Dakin Abidan ta fara shiga ta tarar da ita kishigide a gadonta junior na kwance jikinta yayin da Farha ke can gefe a zaune tana cin cookie's. Amal da Noor kuma na kan kafet suna game a tablet.
Farha na ganinta ta zabura ta mik'e ta nufe ta a guje. Yayin da Bilki ta yi yunkurin d'agata amma ga mamakinta sai ta kasa. Mamaki ya rufe ta don ba wani girma Farha ta k'ara ba haka nan ba nauyinta ne ya k'aru ba. Kan dole ta hak'ura ta rungume ta tare da jan hannunta suka zauna bakin gado. Ta kalli yarinyar ta ga idanuwanta sun cika da k'walla ta ce "Menene?"
Muryarta na rawa ta ce "Mahma na dauka nima guduwa mini kika yi kamar yadda muka gudo muka bar su Yaya a Katsina".
Jikin Bilki ya yi sanyi. A tausashe ta ce "Amma ai na sha fad'a miki ce wa "Duk inda zan je da ke zan tafi mutuwa ce kawai zata rabamu".
Ta goge hawayen idonta tare da rik'o hannun Bilki ta ce "Dan Allah Mahma to zan biki yanzu ni dai na gaji".
Ta fashe da kuka sosai.
Bilki ta jata jikinta ta ce"Zan zo na d'auke ku tare da su Noor next week inji dadynsu ke ma yanzu shine dadynki".
Ta yi shiru can ta ce "To dadynmu na Katsina fa?"
A hankali ta ce mata "Dadynki ne mana. Amma tunda zamu koma gidansu Noor to ba uncle za ki ce dinga ce masa ba sai Dady".
A hankali ta ce "To! Amma dai Mamah yau zan biki gaskiya. Junior ya yi ta tsokanata amminsa ta hana ni dukansa, su Noor ma su dake ni Ammi sai ta ce ",Ni na tsokanesu na rufe bakina na dame ta da kukan shagwaba. Alti ce kawai take kula ni".
Na jijjiga kai na ce ki yi hak'uri idan kuka dawo gida ba zan bari su dinga dukanki ba, amma ke ma ban da rashin kunya tunda basu Yaya Amrah bane da basa iya dukan ki".
Abida ta jijjiga kai ta ce "Duk yadda ake kaffa kaffa da ita ki ji sharrin da take hadawa?".
Bilki ta yi murmushi kad'an ta ce "Ke dai Abida ki yi shiru amma Farha bata karya kawai kina bawa d'anki kariya idan ya tsokane ta.
Abida ta jijjiga kai tabbacin mamakin yarinyar ya yi matuk'ar kamata.
Daidai lokacin su Amal suka iso kusa da ita suna fad'in "Mahma sannu da zuwa, ina yini tare da Dady kuka zo?"
Ta mik'a musu hannunta suka rik'e ta amsa da fad'in "kuna lafiya? Dady na falo".
Suka fice da azama ta bude hadaddiyar jakar hannunta da ta siya wajen umm asalan Egyptian items.....
Ta fito da tissue ta gogewa Farha hawayen idonta cikin rarrashi ta ce "Oya je ki gaida Dady ki yi masa welcome kada ya hana ki tsarabar da muka siyo miki ".
Ta sauka da sauri ta fice.
Sai lokacin ta mayar da hankalinta ga Abida da ta lura ta kafe ta da kallon k'urillah.
Murya ba amo ta ce "A a Abida wanne irin kallo ne haka ne?"
Da dariya ta ce "Ga ni na yi tamkar cikine da ke Maigado".
Zuciyarta ta tsinke don kuwa ita da kanta tana k'alubalantar sauyawarta tashi guda. Sannan kasala ta dabaibaye ta. Kasa d'aga Farha d'azu ya sake jefa mata shakku a zuciyarta. Duk da bata da tabbas din cikin ne.
Ta nisa ta ce "Daga dan zamanmu ne har za ki fara yi mini batun cikin Abida? Inace ban gama rufa watanni biyu da auren ba?".
Abida ta watsa mata wani irin kallo ta ce "ko jiya kuka tare sai ciki ba zai shiga ba? Wannan gagarumar sauyawar da kika yi fa, ko duk vitamin A-z din da yake zuba miki a baki ne?" Save Restricted Contents Bot, [Sep 15, 2025 at 22:07]
Wata irin kunya mai yawa ta dirar mata.
Ta yi maza ta yi k'asa da kanta tare da fad'in "Allah ya shirye ki kawai".
Abida ta kyalkyale da dariya tana fad'in ".Yaya Asad ya hada wata da aiki nan da watanni zamu ga sakamakon da zata ba shi.
Kafin Bilki ta ce komai, Alti ta turo kofar da hanzari bakinta d'auke da sallama.
Bilki na ganinta ta yi karfin halin mikewa da sauri suka rungume juna.
Abida ta kallesu tana jin babu yadda za'a yi ta yarda ta had'a jikinta da na y'ar aikinta duk da dai Bilkisu ta yi matuk'ar yiwa Alti wanka babu wani abin aibu ko na k'yama a tare da Altin.
Sakwanni biyar suka saki junansu dukkansu fuskokinsu d'auke da bayyananen farinciki.
Alti ta zauna a gefen kafet yayin da Bilki ta zauna a inda take zaune.
Suka gaisa cike da karrama juna. Jimawa kad'an Alti ta fice.
Jummai wacce yar kabilar Nufe ce ta shigo d'auke da tiren ruwa da lemo ta dire a gaban Bilki sannan ta durkusa cikin gurbatacciyar hausarta ta ce "Anty barka da yanzu, sannu da zuwa".
Bilki ta amsa da fad'in "Ba hausa mun same ku lafiya?"
Ta murmusa ta ce "Lafiya kalau Alhamdulillahi Anty.
Sannan ta fita. Jummai zata yi shekaru ashirin da biyar ta taba aure har da yaranta biyu suna can garinsu a Bidda a wajen Babansu, tunda suka rabu. Tun kafin a yi mata aure take hannun marigayiya Rukayya sosai ta iya gyara babu gajiya, haka nan ta iya girkin gargajiya daban daban dan idan tana yin sakwara sai ka zaci ba da hannu ake yi ba. Sannan ta iya rainon yara da juriyar fitinarsu. Amal da Noor sun yi matuk'ar shak'uwa da ita. Shiyasa har yanzu take nan tana kula da su.
A zuciyatar Bilki ta kudire Alti da jummai kawai sun ishe ta amma charity sai ta bar gidan ba zata zauna ahalil kitabu na yi mata girkin abinda zata ci ba.
A matuƙar sanyaye Abida ta ce "Yanzu Maigado ba za ki tausaya mini ki fad'a mini gaskiya akan Yaya Sulaiman ba. Ke ko tausayina ba kya ji. Dubu yadda vitamins din da ake zuba miki na watanni biyu kacal ya mayar da ke amma ni kullum k'ara baki nake yi ina yamushewa, sai na bude baki na fad'a miki ina da buk'atar a zuba mini ne?"
Dariya ta subucewa Bilki ta sosai. Ta numfasa ta ce "Allah Abida kalamanki na kashe ni da kunya. Amma fa watannin baya na yi miki rantsuwar ban san inda yake ba. Wallahi tunda ya tafi ban sake ji daga gare shi ba."
Hawayen nadama suka k'wacewa Abida babu zato. Cikin rishin kuka ta ce "Na gaji Bilki, Wallahi na gaji, ni kam na shiga ukuna".
Tausayinta ya kama Bilki sosai ta matsa kusa da ita ta rik'e ta. Murya a dakushe ta ce "Sannu Abida ki k'ara hak'uri mu cigaba da addu'a da ikon Ubangiji idan yana raye zai bayyana.".
Cigaba
Ta d'ago idanuwanta hawaye na tsere duk wata izza da jin kai sun k'wace mata ta ce "Wallahi yana nan da ransa, Wallahi bai mutu kawai tsabagen wulakanci da zalunci ne".
Bilkisu ta kasa ce wa komai. Can ta numfasa ta ce "Abida tunda dai kad'an ya rage ki cika shekaru hud'u a dakon dawowarsa kawai ki yi gaiba idan kin samu miji ki yi aurenki tunda har kika furta mini kin gaji na tabbatar kin kai k'ololuwar gajiya ne tabbas".
Takaicinta ya shake Abida a zafafe ta ce "Ce miki na yi ina marmarin wani rijalun ne bare ya biya mini nasa littafin ra'asin? Yaya Sulaiman din nake kewa kuma gangar jikina take mararinsa ba waninsa ba. Kawai idan za ki taimake ni, ki taimake ni, idan kuma ba wani taimakon da za ki iya yi mini to yaune rana ta k'arshe da za ki ce na yi gaiba don kuwa daga nan har mahdi ya bayyana zan jira shi ".
Ta fad'a cikin kuka na sosai.
Maigado ta kasa ce wa komai don sosai Abida ta bata tausayi