DINGISHIN KWADO 3 COMPLETE BY D Auta.txt

Author :  Hadiza D Auta Category :  Romance

Chapter   31 / 50

90K to 93K   out of 149K words

dadynsa ne yake saka shi a school ".
Ya nisa ya ce "Hakane ".
"To ka ta shi mu je ka saka ni a makarantarsu pls".
Sulaiman ya ce "Zamu je amma ba yau ba".
Junior ya yi shiru ba dan ya ji dad'i ba.
Ya sauka daga gadon ya nufi Abida fuska a kwakkwabe yana son yin kuka.
Ta yi maza ta ja shi jikinta ta ce "Shhhh shima baya son kuka irin Baba. Zai saka ka fa, amma kana bude bakinka ka yi kuka to ba zai saka ba."
Nan da nan kuwa ya had'iye kukan.
Sulaiman ya bisu da ido yana mamakin yadda Abida ta k'ware a tarairayar yaron har cikin idonta yake ganin soyayyar yaron. Ya tuna yadda ta bar shi da rainon Farha. Matuƙar yana gida to fa shine mai raino duk juyin da zai yi kuwa.
Tsakaninta da yarinyar ta bata nono amma canja diaper ma sai ta so matuk'ar ta k'yalla ido ta ga yana gida.
Abida ta yi sharafinta iya sharafi don tana rayuwa ne akan uwa da uba duka sun yi tarayya akan raino da tarbiya ba wai uwace kawia mai lura da wannan b'angaren ba. Ga mamakinsa sai ya ji tausayin yadda ta yi fama da goyon ciki da haihuwa hadi da rainon yaron da babu wata kamarta da ya d'auka ko kad'an. Take kuma ya fahimci ita da yaron a takure suke rayuwa don tana cewa baya son kuka irin Baba nan da nan yaron ya kama bakinsa da hannuwansa.
Wani sashe na zuciyarsa ya kore tausayin da ya taso masa tare da hujjar ita ta so hakan ta faru da ita.
Tunda idan ya zo da bukatarsu bata yi masa k'wange ko raki.
Haka nan idan suka fita asibiti har su dawo girmamawa mai yawa take yi masa a idon jama'a. Amma suna dawowa gida zata nade a gado da sunan ta gaji sai ya yi mata tausa. Kafin a samo Mata yar aiki raba musu aiki take yi shi da ita. Ba k'aramin jarumta ya gwada ba kafin ta daina cewa idan ta yi wanke wanke yau, gobe shi zai yi.
Sai da ya yi da gaske ya yi rantsuwar ba zai yi wanke wanke ba sannan ta hak'ura akan dole take yi kullum. Amma sauran ayyuka tare suke yi.
Rainon Farha kuwa ba k'aramin wahala ya sha ba, don idan ranar dutinsa ce komin kukan yarinyar ba zata karbe ta ba. Matuk'ar ta bata nono to fa sai sai dai ya yi ta fama da ita. Ganin ta bar masa kaso mai yawa na hidimar yarinya sanya ya tubure akana a raba. Don haka rana rana suke yi wato kowa da ranar da zai kula da yarinyar a tsakaninsu.
Bai samu kansa ba sai da aka kaiwa Bilkisu ita wanda sau uku suna saka ranar da zasu kaita suna d'agawa don tsananin alhini. Abidar ce ta fishi jarumta a ranar da suka yi shahadar kaita don ita ce ta kafe a ranar kuwa zata tafi, alk'awarin da ta d'auka na bawa Bilki ita sai ta cika don ko mutuwa ta yi sai an bawa Bilki ita.

Ga shi dai sadda ta yi alak'awarin bawa Bilkisu d'iyarta shi baya k'asar bai kuma k'ulla soyayya da ita ba.
Amma q hakan da ta yiwa Bilki ya k'ara masa sonta tare da kaita matsayin a zuciyarsa.
Duk da shi din ba k'aramin takura ya yi da rasnin Farha ba a lokacin .Ya Dade yana kokawa da zuciyarsa kafin ya hak'ura.
Da kansa ya yi amannar kaf duniya Bilki zai iya yiwa hakan.
A yanzu kuma ya rage Jim zafin da ta ce don ta bawa Bilki Farha ya sanya ya aure shi, don Idan ba shine uban Farha ba ai kyautar zai zama ba irin yadda take a yanzu ba. Don uban yarinyar da danginsa ma sun dinga yin abin da kowa zai gane ba ita ta haife ta ba. Save Restricted Content Bot, [Oct 18, 2025 at 11:07]
Ya kuma gasgata dukkan zuciyarta take son Bilki tamkar yadda yake sonta. Don ya dan rage jin zafinta kad'an ne a lokacin da Usman ya ce Wai ko zata tafi da d'iyarta?
Wannan kalmar tana yawan fad'ar masa da gaba. Wai Usman nasa da suka taso tare ne ya yi masa irin haka akan laifin da ba shi ya yi ba? Bai taimake shi akan ya daidaita aurensa da kanwarsa ba.Sai ma yake bata kariya akan izgilin da take yi na na zata zauna da shi ba, tare da son ya nukurkusa Bilki da bak'incikin rabata da d'iyar da ta k'wallafa rai a kanta. Duk sadda Sulaiman ya tuna wannan batun yana yawan tambayar kansa ko dai Usman ya manta shine uban Farha ba wani ba? Shi kuwa a duniya ba zai taba yiwa Bilki gayya da abin da ya haifa ko ya mallaka ba.
Wallahi ya so a ce Abida ta ce zata karbi y'arta da kuwa ya nuna musu lallai MAMI ce ta haife shi kuma nononta da ya sha bai furzar ba, yana kuma alfaharin kasancewarta uwarsa.
Don sai ya yi wulakancin da zai sake girgiza gidan gabad'aya.
Sai kawai suka yi sa'a daga ita har Usman din ta ce 'wai munafuki ne yake magana biyu.' Hakan da ta fad'a sai jikinsa ya mutu fishinsa ya sauka, sannan bak'inta ya ragu da kad'an a zuciyarsa.
A fili ya furta "Dole sai an zauna".
Abida ta ce "Me ka ce ?"
Ya yi shiru tare da rufe idonsa alamun barci zai yi.
Kan dole ta sunkuci junior da yake ta gyangyadi a jikinta.
Ya bi bayanta da ido har ta bude k'ofar ta fita.
Kukan Baba ya karya masa lagonsa kwarai da gaske har yake jin Idan ya ce ya saki Abida Baba zai tabbatar lallai baya ganin mutuncinsa ne.
Amma ya ya zai yi da bak'incikin maganganun da ta yi akan uwarsa.
Ko lokacin da ta yi eannan BAK'AR TA'ADA din ta zube jini ya tsinke mata ne. Ya kaita asibita da zummar jdan ta warke ta dawo sai ya yanke Ma3ta hukunci. Sai kuma bata dawo ba ta tafi.
Ana cikin haka mamin ta rasu amma zuciyarta bata risina ba a cikin gayya ta yi masa gaisuwar, ta sake saka k'afafuwanta ta bi iyayenta duk kuma ana kallonta alhalin sun sa ni ba sakinta ya yi ba. Hawaye ya k'wace masa yana jin lallai ya hak'ura da ita shine ya zama d'an kirki, nakudar da mami ta yi kafin ya iso duniya bata yi a banza ba. To amma ya zai yi ne da Baba?
Lallai tsugunne bata k'are musu ba. Don kuwa la shakka duk matsanancin son da yake yiwa Abida. Ya fi son MAMI. Sannan mami tana da alfarmomin da duk wanda yake k'arkashinsa sai ya girmamasu bare kuma ace wai matarsa ce zata keta mata alfarma cikin isgili a gabansa to ba yi wannan lalacewar ba kuwa. Mami ba zata yi wannan arahar ba ila yaumil qiyama ko me ta yi na kuskure kuwa.

*Duk girman rikicin da zai gitta da mijinki kada ki yi gangancin zagin iyayensa matuk'ar ba shi da dabi'ar zagin iyayenki, basa manta zagin da macen da aurensu ta yi musu cikin sauk'i*.
*Shawara ce kyauta*.

*
A zaune ta tarar da Baba bai shiga ciki ba. Ta isa kusa da shi ta kwantar da junior. Ta koma gefe tana dan haki.
Ya kalle ta ya ce "Ina fatan baki fesa masa Bilkisu na tare da yayanku ba?"
Murya a sanyaye ta ce "Tun a Saudi da ka ce kada na fad'a ban fada din ba Baba."
"Madallah!
Baba ya furta hakan a takaice.
Ya ce "To anjima zaki kai Shi ya gaida yayanku daga nan sai ya ga twins kalarsu Baban Munira".
Abida ta murmusa. Ta ce "Zai yarda na kai shi ne?"
Ya ce "umarni zan ba shi ai, ke dai ki shirya kawai "
Dad'i ya kamata. Da walwala ta ce "To Baba ".
Daga haka Baba Babba ya mike ya nufi d'akinsa.
Abida ta ciccibi yaron zuwa nata d'akin.
*
Bilki na zaune a d'akinta. K'ofar d'akin a bude kuka take yi k'asa k'asa yayin da Alti take fad'in "Abin da na yi ta guje miki kika ji. To wai menene ba za ki bude baki ki fad'a masa ba kya son hotunan ba?"
Cikin kukan ta ce "Bai ba ni dama ba Alti. Tunda na zo gidan nan fa bai taɓa ba ni damar da zamu tattauna ba. Komai za'a yi mini kalmar d'aya ce 'ki yi hak'uri yara ne."
Daidai lokacin oga Asad ya sauko basunji Shi ba. Save Restricted Content Bot, [Oct 18, 2025 at 11:09]
Kunnensa ya jiyo Bilki na fad'in "An zage ni, an zagi uwata ya ga ni bai ce komai ba illah k'uruciya da ya jingina musu. Amma ni da na zagi maimurabus da uwarta ai laifi na yi, laifin da ya zama sanadin da ya yi mini hukuncin da sai da na shafe sattitika a gadon asibiti. Duk ana ga ni an kasa tsawatar masa. Ke ma yanzu da nake ganinki ina jin dad'i ya k'wace mini ke kin koma bin bayansa to Allah dai yasa ni ce ta ki, ba shi ba. Yanzu ban da ya riga ya kud'iri aniyar sai ya kunsa mini bak'inciki ace Yaya Sulaiman din da ake nema ruwa a jallo ya dawo ace an shata mini layi da zuwa wajensa?"
Kuka mai cin rai ya k'wace mata.
Alti hankalinta ya tashi ta ce "To ki ba shi hakuri mana. Indai kina son zuwa ki gyara barakar da ke tsakaninku. Yanzu ki saka direba ya kai ni, na gaishe shi a madadakinki. Anjima ki je masa kwana ki ba shi hak'uri ku shirya gari na wayewa da kansa zai kai wajensa".
Bilki bata ce komai ba.
Illah gunjin kuka.
Yayin da Oga Asad ya dinga istigifari tare da wanke Alti daga zargin da yake yi mata na bata faɗawa Bilki gaskiya.
Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:04]
*Surayya Dahiru*
08032773332.
*Littafin kud'i akan manhajar telegram*.
*1k*
*Via*
2384876855
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank*

*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*Ki zo ki saka order din ciccibin garari ko kazar sababi ki gode mini domin saiwowin da nake amfani da su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Sanyi flusher kuwa best seller ne*
*Just DM for your order @08033773332*.


Haka ya wuce su zuwa masallacin don yin sallar laasar. Kukan Bilki ya taba shi sosai. Amma shi so yake yasan me ya yi mata ne a yanzu?
Me yasa zata kafe ba zata je d'akinsa ba?
Kansa ya kulle ainun amma ya fi gamsuwa y'anuwanta da suka d'ora masa k'ahon zuk'a ne behind everything. Ko kuma ya ce Hamida kaitsaye. Kuma yanzu ya sake gasgata Sulaiman ma zai d'ora nasa famfon tunda daga dirarsa k'asar ya tabbatar masa shima gabar yake yi da shi.
Ban da darajar idon Baba, da ba sai ya wulakanta Sulaiman ba. Idan juninsa zafin kai ne, da ya nuna masa bai iya komai ba, ya saka kafa ya bar mace da aurensa a kanta har da ciki shekaru hud'u ba kad'an. Sannan akan dole ya dawo, sai da aka yi masa tilas kuma duk wannan wulakancin da ya yi musu da ubansu har yana da kuzarin da zai sake yin wani sabon wulakancin da raini daga dirarsa?
Ya hurar da iskar b'acin rai.
Yana jin Baba babba ne cikas d'insa akan kudirinsa na cin mutuncin Hamida da Sulaiman. Sai dai kuma matuƙar Hamida bata kiyayi shiga tsakaninsa da iyalinsa tare da yi mata famfo a kansa ba, tabbas sai ya wulakanta ta idan ya so su sake shata layi da shi tunda shi kad'ai suka wasa, ko kad'an basu tisa Faruku a gaba da bala'i kamarsa ba.
Tun lokacin aurensa da Bilki da ta zugata tare da ankarar da ita bai je gaisuwar mami ba yasan ta washe shi. Yanzu kuma rashin zuwa ta ga twins ya sanya har zuciyarsa ya washe ta don ya tabbatar shine bata so ba Bilki ba.
Yana tafe yana sake saken yadda zai bullowa lamarin har ya iso gidan.
Ya tarar Alti na falon k'asa.
Ta yi masa barka da dawowa ya amsa ya wuce. Ita kuma ta shige d'akinta da a cikin falon yake.
Kaitsaye d'akin Bilki ya yi burki. Ya tarar ta idar da sallah. Ya kalle ta zuciyarsa ta tsinke a dalilin yadda ya ga ta rame Ga fuskarta ta yi kuyes idanuwanta sun jan sun fito gwara gwara.
Ya ji ba dad'i.
Ya had'iye fishinsa ya ce "Me yake damunki.
Ta girgiza kai ta ce "Ba komai".
Ya ce "To kukan na menene?"
Ta suake ajiyar zuciya bata ce uffan ba.
Ya jijjiga kai ya isa gadon da yaran suke shimfide. Idonsu biyu dukkansu sai shure shure suke yi tabbacin a kwashe Duke. Sun yi bul bul da su tamkar sun kai watanni hud'u alhali kwanakin baya kad'an suka cika watanni biyu.
Ya zauna ya dauki kowanne ya yi masa wasa sannan ya kwantar da su a hankali. Ita mamaki yake bata yadda yake yi musu tamkar k'wai. Idan aka ga yadda yake b'arin jiki a kansu sai a zaci gabad'aya bai samu haihuwar ba ne sai a yanzu da shekaru suka fara tura masa. Wani zubin ita da ta haifesu ganin gazawarta yake yi akan kula da yaran. Komin dare idan ya jiyo kukansu sai ya zo ya tambayi ba'asin kukan ko ya ce a daren zai kaisu asibiti a duba lafiyarsu.
Da Alti ta gane shi sai take ce masa ai kukan ne alamun suna lafiya, sannan alamun zasu yi kwakwalwa ne.
Tunda ya ji hakan kuma sai ya koma tambayar yau kuwa sun yi kuka da ba nan? Alti yau basu yi kukan dare ba fa? Ko dai basu da lafiya ne?"
Aysha da kullum ita take gida tana kallon ikon Allah.
Tasan dadynsu na sonsu k'warai da gaske. Amma da wayonta da hankalinta aka yi goyon Amal da Noor tabbas bai yi irin haka ba. Sannan ba ya taya Momi rainon yara, abin da ta san baya damuwa akan abinci ne, ta bude ido ta ga da daddare idan ya dawo zai bada order chep ta yi masa abin da yake so. Amma tun zuwan anti Maigado ta ga ya canja, matuƙar ta ajiye masa abinci sai ya ci. A yanzu baya iya saka chep ta yi masa sai ya dinga raragefe kafin ya sanya a yi masa abin da yake so. Save Restricted Content Bot, [Oct 20, 2025 at 14:07]
Duk abin da ta girka haka yake ci, babu musu wanda lokacin mominsu shine yake da lasisin zabar abin da zai ci bayan ya dawo har da tsirfar baya cin abincin da ya shiga warmers. Gara ma a kwanakin nan ta ga chep angela ke yi masa.
Takaici ke cinta me yasa yake rianon wadannan, ko ita kanta jele take yi tsakanin samansu da saman anti Maigado da Kuma saman Dady ba don komai ba sai don ta kaisa masa yaran, ko ya ce ta je ta karbosu a wajensa suna jin yunwa. Kuma yaran da zata iya hadesu ta d'auke su sai ya ce da d'aid'ai zata kai su ko ta sauko da su. Idan kuwa ta d'auke guda a cikinsu ya dinga fad'in "Aysha handle them with care. Ki sauka a hankali ban da garaje!
Me yasa yake wannan barin jikin akanasu, shin dan sun kasance maza ne ko kuwa don sun kasance y'ay'an Maigadon da yake so kuma Abida da mominsa suke sonta?
Kullum sai ta yi kuka a d'akinta wanda na kishin yadda yake son wata macen alhalin uwarsu na kushewa. Gata da riritawa ba wanda ba ya yi musu amma gabad'aya zaman gidan ya yi mata tsauri so take ta barwa Maigado da Abida guri su cinye gidan ma gabad'aya.
Tunda ta gama gamsuwa ya fi son Maigado akan mominsu. Ya dinga ganawa momi azaba da fishinsa akan ya'yan da ta haifa. Amma wata katuwa ta zo ta zanesu ya yi muk'us bai yi mata azababben fishinsa da yake sanya mominsu yini tana goge k'wallar bak'inciki. Amma wannan ko kwakkwaran motsi kasawa ya yi sai ma kwasarta shopping da ya yi suka raba dare a waje.
Idan ta ga hips din Maigado har kan harshenta take jin ciwo tunda a dalilin momi na son ta zama irin yadda yake so ta salwantar da rayuwarta. Ga shi ya samo wacce take da su natural ba artificial ba yana sharafinsa yadda yake so. Sune kad'ai suka yi asarar rashinta sai ko danginta.
Wadannan dalilan ya sanya Aysha ta kasa sakewa da Maigado amma kuma ko kallon banza ba ta yi mata.
Ya mike ya fice ba tare da ya ce mata kanzil ba. Yayin da ita kuma kuttunsa ya zo mata har wuya. Idan har yana da imani ya tambayi ba'asin kukanta? Ya kumshe a gida yana faman Hana Mata azaba. Ace Sulaiman Yana Abuja a hana ta zuwa wajensa? Da ace maimurabus ce yama isa ya fara yi irin wnanan kama karyar?
Oh namiji dai baya fita a wajen mace, baya gwaninta ko wacce ga ni take yi yafi son wata a kanta.
Yan shiga d'akinsa wayarsa da layin da iya family ne suke da Shi ya hau kara.
Ya duba ganin Baba ne ya sanya ya zauna sannan ya amsa cikin girmamawa.
"Baba dafatan ka kwanta ka yi barcin gajiya?"
Baba ya amsa da fad'in "Na dan yi. Sai dai ban wani jima ba a dalilin zuciyar babu dad'i".
Ran oga Asad ya baci a ransa ya ce "Ina zuciyarka zata yi dad'i ka k'wallafa waɗanccan ja'iran a ranka."

A fili kuma ya ce "Ayyah sannu Baba ka Ƙara hak'uri ka kuma dinga yawan istigifari.".
"Ina yi, amma zan dage da yi. Ina son ka bude kunnuwanka da zuciyarka ka saurare ni da kyau".
Zuciyarsa ta buga don kuwa la shakka al'amarin da za'a bijiro masa mai nauyi ne!
"Asad Asad Asad! Baba ya k'ira shi har sau uku cikin dakakkiyar murya.
A sanyaye ya ce " Na'am Baba".
Anjima ka shirya tarbar Sulaiman a gidanka. Zai zo ya gaisheka daga nan ya gaisa da Maigado ".
Tamkar an kwada masa guduma haka ya ji wannan batun na Baba Babba.
Murya ba amo ya ce "Wallahi k'arya yake yi ba dan ni zai zo ba Baba wajen kanwarsa zai zo".
"Wallahi bai san Maigado iyalinka ba ce bai san komai ba".
Nan da nan Asad ya gamsu don kuwa baba ba

31 / 50