DINGISHIN KWADO 3 COMPLETE BY D Auta.txt

Author :  Hadiza D Auta Category :  Romance

Chapter   33 / 50

96K to 99K   out of 149K words

k'arshen mugunta kenan. Sadda ina tare da su a port a dole take karɓar gaisuwata, idan tana falo na zo na zauna, idan ta tashi ta bar mini falon kenan. Idan kuwa ni ce a zaune to ba zata yarda ta zauna ba haka ta yi mini wannan izayar. Ni kuma ina ta kaffa kaffa kada a ce na k'i zaman gidan mijina na dawo gidan yayana zan kashe masa aure. Kai na ga rayuwa Wallahi! Yaya Sule dole ya biya ni diyya kashi kashi."
Ta kece da kuka na sosai.
Bilki ta yi sororo tana kallon yadda take kukan da ba na iyashege ba ne na tsantsan bak'in ciki ne.
Alti ma sai kawia ta fashe da kuka tana fad'in "Dole ki yi kuka Hajiya Abida ai irin wannan zaman kuttunsa yawa gare shi ka rasa inda zaka tsoma ranka."
Cikin kuka ta ce "Haka matar nan zan ji tana k'iran Maigado suna hira ita ala dole mun samu sabani bari ta had'a kai da ita ta musguna mini, bata san ko da bama mu'amala, babu tsanarku a zuciyata ba, kanta ya toshe ta kasa gane tasirin jini girma ne da shi. K'ememe ta raba ni da y'ay'an d'anuwana bata bari su zo dakina haka na zama tamkar mujiya a gidan Dady" . Save Restricted Content Bot, [Oct 22, 2025 at 11:49]
Ta sake kecewa da kuka tana fad'in "Ba wanda zan yiwa k'orafi akan tozarta ni da take yi cikin ruwan sanyi, tunda k'orafi na yi masa momi bata sakar mini fuska shine ya tafi da ni wajensa a kokarinsa na ganin na samu sauyin muhalli tunda jinina ya k'i sauka. Haka nake zaune ba um ba um y'an aikinta sun fini walwala, kanwarta ta fini sakewa a gidan dan'uwana. Na kasa cin mutuncinta ne kada ya ce laifina ne tunda uwata ma ai ba jin dad'in zama nake yi da ita.".

*Ina farincikin sanar muku da zarar na kammala wannan littafin ba da jimawa zan zo muku da sabon littafin tsohuwar marubuciya Haj Saliha A.A Zaria in sha Allah*.

*Sunan littafin Wutar jeji*.

*Sannan Duka books dinta na baya akwai Su in soft copies.*

*08032773332*
*Ku tuntube Ni*.

Alti aka face majina da tissue aka ce Dr Abida yanzu kawai ki dawo gobe don wannan hirar ba a kurarren lokaci za ki yi mata bitarta ba, don ita bata fahimci girman k'alubalen da ake hango mata ba idan ta k'i kwantar da hankalinta ".
Abida ta goge fuskarta ta ce "Anty Rukayya ta cuce ni bisa hujjar mijinta na sona da yawa. Yana mini hidimar da ta shake mata mak'oshinta alhalin bai yi mata iyaka da kuɗinsa ba.
Yanzu ai ga karshen ta nan ta bar wa Maigadon da take nunawa tata ce gida da mijin da take mutuwar so, yayin da Maigado ta washi ko sunanta mijinta ya kama . Allah ne ya saka mini. Kuma Wallahi da ace tana raye ya aure ki, da ta gane tasirin jini. Da na hutar da ita zargin bana sonta don kuwa tabbas zan nuna mata bana ko kaunar ganinta. Ta kitsawa y'ay'anta mugun abu a kaina. Su Aysha a dole suke gaishe ni, ta zo ta same mu lafiya , ta nemi jefa mana gaba. Ya ya dady zai ga farina idan ya ga bana kula y'ay'ansa? Sai da ya gane sune basa zuwa inda nake sannan ya yi mata cin mutuncin ya ce ba ni ba ko Anisa da take karama cikin kannensa idan har y'ay'ansa zasu ganta su d'auke kai, ko a hana su zuwa wajenta to shima su daina gaishe shi, su kuma daina zuwa inda yake kawai.
Sannan na samu sukuni fa".
Billki ta yi lakwas.
Tabbas suna waya da Rukayya. Ganin tana k'iranta don ta gaishe ta, ya sanya itama jifa jifa take k'iranta don ta gaishe ta.
Murya ba amo Bilki ta ce "Kafin ki tafi Abida ji fad'a masa ya cire mini waɗanccan hotunan da ya girkesu babu ko sha'awar ga ni".
Abida da Alti suka fashe da dariya.
Cikin dariya Abida ta ce "Gaskiya Maigado ko hasidim iza hasad yasan hotunan sun yi kyau sun Kuma fita. Wai me yaushe kika yi zurfi a soyayyar Yaya Asad ne irin haka? Ashe har yanzu ba zaki Daina zafaffiyar soyayya irin haka ba? Yanzu ga shi nan tun baku ko ina a zaman ba kin fara kishi mai saka ciwo a kirji da shake kofofin shakar numfashi."
Bilki ta yi shiru don kuwa Abida ba karya ta yi ba. Da ace idan ta faɗawa Abida tana jin son Baban Bilkisu ninkin na son da ta yiwa Sahal da ta fad'a mata. Sai dai ba lallai ta gamsu ba don idan akwai abin da Abida ta gasgata take sarhutu a kansa to son da yake yiwa Sahal na kan gaba.

Abida ta katse Shirin ta ce "Ba ni da k'warin guiwar da Zan tsaya gaban Dady na ce ya cire hotonsa da na matarsa a gidansa, ban isa ba, ba hurumina ba ne. Ta kama baki alamun al'amarin babba ne.
Bilki ta jijjiga kai ta ce "Amma Ina ce kin ce mu hada kaiu yako matsalarmu?"
"Saboda Allah Maigado ke ce Zaki fad'a masa. Dady fa cewa yake yi raina shi na yi da nake gaba da matarsa duk da ina gaishe ta. Ya kuma san itace ta washe ni. Amma a gabana nunawa yake yi ba ni da kunya ne isgili nake yi mata alhalin ba sa'a ta ba ce. Yanzu kuma na ce masa ya cire hotunanta me zai ce mini? Ki mini adalci fa Maigado!
A zuciyarta kuwa mamakin soyayyar da mata suke yiwa Dady take yi. Haka Rukayya ta so shi tamkar rai. Ga Maigado ma ta fad'a tsumdum. Yaya Sulaiman na cikin gidanta amma batun fishinsa take yi. Ta saki gauron numfashi ba ta furta komai. Don dama tuni tasan Maigado akwai zurfafa soyayya.
Daga haka ta d'auki Baba K'arami tana fad'in" Bari na kai masa yaran tunda ba kya farincikin zuwansa."
Haka Bilki ta d'auki Baba Babba ta bi bayan Abida zuwa falon oga Asad na k'asa. Save Restricted Content Bot, [Oct 22, 2025 at 11:52]
Are11
Abida ta ce a gaba kaitsaye ta shiga da sallama. Yayin da oga Asad ya amsa mata sallama idanuwansa na kan Maigado da take biye da ita babu kuzari. Zuciyarsa ta motsa. Duk kuttun da yarinyar take cusa masa sonta yake yi da dukkan zuciyarsa. Bai son ya ganta a iron wannan yanayin na sanyin jiki da rashin kuzari amma ta alas gane hakan.
Daidai lokacin Sulaiman ya dago fuskarsa da yake duba wayarsa. Idanuwansu suka sarke da na Maigado. Da azama ya mik'e ya k'arasa kusa da ita. Maimakon ya karbi yaron hannunta Sai kawia ya had'a su duka ya rungume. Yayin da Maigado aka bare baki aka rushe da kukan da take rik'e shi.
Sun jima a rungume da juna oga Asad da Abida suna kallonsu cikin wani irin yanayi na tausayawa.
Sulaiman ya yi jarumtar sakinta ya jata suka zauna a kujera mai cin mutum biyu.
Ya zari tissue da take kan centre table ya dinga goge mata hawayen da ya ki yankewa. Shi Dai oga Asad kallon ikon Allah da shagwaba yake yi da dukkan nutsuwarsa. Yana kuma gasgata ta fi Abida sakalci nesa ba kusa ba.
Tsawon lokaci kafin Sulaiman ya samu ta Daina kuka. Murya ba amo ta ce "Yaya Sulaiman dan Allah a ina kake tsawon lokaci, baka tuna Ni, baka tuna su Anisa?"
Jikinsa ya yi sanyi ya ce "Ina nan Bilkina! Batun tuna ku kuwa ba sai na ce komai ba, amma ina tuna ki sama da sau goma a rana, ina kuma yi miki addu'ar ki zama jaruma , duk kuma abin da zai tunkare marar dad'i Allah ya warware miki, ya had'a ki da dukkan alkairi ".
Hawaye ya cika gurbin idonta ta ce "Shikenan na huce da kam na yi fishi da kai Yaya Sulaiman don kasan ina bukatarka a kusa amma ka tafi babu waiwaiye, na hak'ura tunda Allah yasa ya ka dawo mun gana. Ya bayan rabuwa?"
Ya saki gauron numfashi ya ce "Alhamdulillahi zan ce amma ko ina babu dad'i. Duk inda aka je hak'urin nan dai shine a gaba. Ina su Amrah da Faruku?"
A sanyaye Bilki ta ce "Suna Katsina ".
Daidai lokacin Abida ta mik'a masa yaron ta ce "Ga Baba K'arami ".
Sulaiman ya karbe shi yana zuba masa ido. Ya d'ago ya kalli Abida ya ce "Sai a ce kece uwarsu. Ba su yi kama da Anty Rukayya ba fa ko kad'an".
Oga Asad ya yi shiru tare da tunanin bai san Rukayya ta rasu ba, bai san kuma Bilki ce ta haifesu ba. Kamar zai yi magana sai ya yi shiru yana cigaba da kallon k'annem nasa gabad'aya.
Abida cikin gigighiwa aka ce "Baka Ga junior da ita yake kama ba. Nima wadannan share mini zuciyata suka yi. Duk da daka khadija ma muna kama."
Sulaiman bai gano manufar Abida ba.
Yaron ya fara kukan neman nono tunda wanka aka yi musu, Sai sun sha nono Sai a kwantar da su Su yi barci. To yau Basu sha ba.
Abida ta karbi yaron ta ce "Maigado ba Shi baba Babba da bai Fara kukan ba ki ji da wnanan".
Ba musu ta mik'a masa ya karɓi yaron yana kura masa ido don ya ga banbancinka da d'anuwansa don kuwa tabbas yan biyu ne masu kama da juna (Identical twins).
Ya cigaba da kallon yaron da ya idanuwansa suke a bude tarr. Gaban Sulaiman ya fadi a dalilin ya ga k'wayar idon yaron irin tasu ce. A kallon da ya yiwa junior d'azu ya ga kammanin idonsu d'aya ne. Haka kuma idanuwan Farha suke tana jinjira.
D'ayan da ya karbe shi idanuwansa a rufe suke shiyasa bai ga idonsa ba. Tabbas da oga Asad suke kama da Abida amma idanuwansu ba irin nasu bane. Irin nasa ne.
Ya d'ago da niyyar yin tambihi game da tasirin jini kawai ya ga maigado na shayar da yaro.
Kansa ya kulle. Ya kalli oga Asad ya ga shima kallonsa yake yi. Ya yi masa kwarjini ainun ya kasa bude baki ya tambaye shi. Ya fara bitar kalaman Baba 'ka je ka gaishe shi ka ga tagwayem da aka haifa masa'.
Ya koma ga Abida ya ce "Uwar yaran matsala ta samu ko kuwa?"
Kaitsaye Abida ta ce "Kamar ya ya kana ganin ya ras a gabanka?"
A dimauce ya ce "Abida Maigado Matar Yaya Asad ce ko kuwa shayar da yaran take yi?"
A takaice ta ce "Matarsa ce ita ta haifi yaran".
Bai musa ba don kuwa idon yaran ya tabbatar masa na Bilki ne. Save Restricted Content Bot, [Oct 22, 2025 at 11:55]
Ya kalli Bilki ya ce "Yanzu Maigado idonki da kwalli like Kishi da Anty Rukayya?"
Ta daure fuska sosia ta kasa magana. Oga Asad Yana lura da ita.
Abida ta ce "Anty Rukayya kam tuni ta yi kwanciyar manya".
Sulaiman ya sake shiga rudu yayin da oga Asad ya rasa gane iskancin Abida na fad'in wai kwanciyar manya ta yi".
A daburce Sulaiman ya ce "Kina nufin ta rasu ne?"
Abida ta tattaro alhini ta ce "Shekaru biyu kenan. Plastic surgery ta yi, ya yi failing ".
Hankalin Sulaiman ya sake tashi.
Cikin damuwa yake yiwa oga Asad ta'aziyar rasuwarta. Har cikin zuciyar Asad ya ji dad'in damuwa da kaduwar da ya gani a fuskar Sulaiman da gangar jikinsa da kuma yana k'asar ya shaida zai zo masa gaisuwa. To me ya yiwa Sulaiman kenan? Shi ya d'auka rashin zuwa yi musu ta'aziya ne laifinsa. A ransa hake ayyana ko da sun huce to akwai buk'atar su tattauna don dukkan kullikan da suke zuciya su warware.
Falon ya yi tsit kowa Maigado yake kallo yadda ta yi kicin kicin da fuskarta tana shayar da yaro.
Abida ta dinga mamakinta. Tana yi kuma tana ganin yadda duk motsin oga Asad ita yake kallo baya ko gajiya.
A ran Abida take ayyana idan namiji ya so mace ta huta kawai. Itama irin haka Sulaiman yake sonta. Duk iyashegenta haka yake jurewa baya kuma son su yi fad'a.
Save Restricted Content Bot, [Oct 23, 2025 at 20:06]
*Surayya Dee*
08032773332.

Oga Asad ya katse shirun ta hanyar cewa "Kun ga yadda take kumburin nan to fa a haka nake da ita. Gabad'aya ta murd'e ta k'i dad'in kasafi. Ba dama na shigo ta faranta mini kullum cikin fishi da bijire mini take. Da kuma zan kaita k'ara kowa cewa zai yi Bilki mai hak'uri ce, bata da hayaniya alhalin ni kad'ai nasan yadda nake zaune da ita."
Sulaiman ya yi shiru. Bai k'arya ta batun oga Asad ba. Amma tabbas yasan ba haka kawai ta sauya ba. Ya zuba mata ido haka nazarinta. Can ya nisa ya kalli Abida ya ce "Kamar fa tana da damuwa ya kamata ta ga likita".
Abida ta fara ambata scientist word6da likitoci ke fahimtar yaren. Take ya fahimci ciwon damuwar da ta yi ne ya sauya ta. A yanzu ma akwai alamunsa a tare da ita.
Ya tausasa harshe ya ce "Ka yi hak'uri Yaya Asad zata daina yarinya ce."
Bilki ta kalli Sulaiman tana kallo yadda kaunarta da tausayinta ya cikasu. Tana kuma ganin da dukkan zuciyarsa ya bawa oga Asad hak'uri tare da gabatar da uzzirin yarinya ce ita. To ashe Baban Bilkisu da yake fad'in ta yi hak'uri da su Aysha ashe ba wulakanci bane ya sanya yake fad'in su yara ne ba. Tunda gata da ta girme musu nesa ba kusa ba, yayanta yana fad'in a yi mata hak'uri yarinya ce ita.
Oga Asad ya ce "Hak'uri ya zama dole ai, amma idan na ga bata gane hak'urin da nake yi ba ai zan nemarwa kaina mafita."
Bilki aka sake daure fuska ba'a tanka ba.
Yayin da Abida take mamakinta matuk'a da gaske.
Sulaiman kuma gabad'aya mutuwar zaune ya yi tare alajabin zamowar Bilki matar Yaya Asad. A ransa yake fad'in fad'a ya k'are a tsakaninsa da yayan nasu tunda ya auri Bilkisu. Ya Kuma gamsu Asad ba ya k'insu saboda baya son uwarsu kamar yadda suke zaton. Don da yana k'insu ba zai auri Maigado ba.
Ya saki ajiyar zuciya mai nauyi.
Ya mike yana fad'in Yaya Asad Allah ya raya su Baba. Allah ya jiqan anty Rukayya. A mini hak'uri dan Allah."
Oga Asad ya mik'e ya mik'a masa hannu tare da fad'in "Ameen Ameen. Na gode sosai. Yanzu zuwa nan da ka yi nawa ne. Ya kamata ka samu lokaci ka dawo sai ya zama zuwan Maigado ne. Ko gobe ka zo ku yi lunch tare".
Sulaiman ya ce "Zan dawo amma ba gobe ba. Kafin dai na wuce in sha Allah".
Ya kalle ta ya ce "Bilkina zan tafi".
Ta murmusa ta ce "Ka ji yara sun dawo bari su shigo ku gaisa".
Bai musa ba, ya koma ya zauna.
Mintina biyu suka ji Shigowaesu suna wucewa zuwa sama.
Abida ce ta fita ta kirasu.
Farha ta kalleta ta ce "Ina junior?"
"Da walwala ta ce "Yana gida barci yake yi."
Suka shiga falon.
Ganin Dady ya sanya suka tsugunna suna gaishe shi.
Sulaiman ya bi yaran da ido
Zuciyarsa ta harba da suka had'a ido da Farha kowa ya ganta ya ga Bilkinsa.
Ya kalli Noor ya ce "Noor ya school?
Ina Amal da Bilkisu?"
"Ta ce sun hau sama yanzu zasu sauko."
Ya ce "Farha ya karatun Ina Su Faruku?"
Murya a snayaye ta ce "Shan can gidanmu da dadynmu na Katsina. Ni ma Mahmah ta ce ana yin hutu za'a kai ni".
Ya yi murmushi ya ce "Hakan ya yi. Yana ayyana bata son shine Babanta ba.
Ta kalli Maigado ta ce "mahmah yayanki ne na Hoto da kika.ce na dinga addu'ar Allah yasa a ganshi ko?"
Bilki ta ce "Shine fa Farha g ashi Allah ya karbi addu'armu ya dawo."
Oga Asad ya yi shiru wato ma ta dauka wanccan sahalallen ne ubanta kenan?"
Yayin da Abida take kallonsu. Amma tana mamakin yadda Farha take ganin soyayyarta a idanuwan Farha kamar hadd5taoe ganin soyayyar Bilki. Haka nan ita da junior son juna suke yi kamar me.
Daidai lokacin Amal da Bilkisu suka shigo Har sun cire uniform. Suak gaida duka iyayen nasu. Sualiman ya mik'awa Bilkisu hannu ya ce "Zo nan Bilkina haka kika girma?"
Kunya ya kamata.
Ta karisa kusa da shi ta durk'usa.
To Noor da Farha da Amal duk ku matso mu yi selfie."
Suka matsa ya dinga yi musu hoto da wayarsa yayin da Abida ta mike tana yi musu a tata wayar.
Ya ce "next Zan zo mu je shopping tunda na dawo babu tsaraba". Save Restricted Content Bot, [Oct 23, 2025 at 20:11]
Dad'i ya kamasu suka dinga yi masa godiya. A gidan suka yi sallar magharib.
Daga suka yi sallama suka tafi. Oga Asad ya nisu Har harabar adana motoci.
Amal da Bilkisu suka d'auki twins suka koma sama da Bilki.
Alti ta ce "Ba Dai sun tafi ba?"
A snayaye Bilki ta ce sun tafi Alti Amma zai dawo".
Cikin walwala oga Asad da sualiman suka rabu.
Abida ce take tukin.
Sun fara nisa a Kan titi ta ce "Ogana yanzu ina muka nufa?"
Bai kalle ta ba ya ce "Ind kike so".
"Yaya Sule inda nak so fa ka ce? Ni fa na dauka ganin maigado da na kaika ka yi zaka huce ka yafe mini tunda na baka hak'uri a aikace, na yi nadama, na baka hak'uri baki da baki, na cire girman kai haba yaya Sule ka yi hak'uri ka yafewa masoyiyarka dan Allah".

Ya numfasa ya ce "Me kike son na yafe miki zagin mami ko cire mini ciki da kika yi ko kuwa nuna mini iyaka da kika yi na ban isa da ke ba?"
Zuciyarta ta yi nauyi. Hawaye ya k'wace mata ta rage gudun da yake yi.
Da muryar kuka ta ce "Ka yafe mini maganganun da na yi akan mami, ba a hayyacina na yi su ba. A lokacin marab'aina ne suka motsa, su suka bude mini baki da kunne har nake jin lallai na yi b'aranbarama amma ba daga k'asan zuciyata kalaman suka fito ba. Ban tab'a yin abin da ya sanya ni nadama irin maganganun da jinnu suka furta ya bakina. Allah ne shaidar na yi tuba, na kuma gamsu ban kyauta ba, amma ni ma da sharrin jinnu na h'adu, ka yiwa Allah ka bani dama ko da kuwa shine last chance".
Ya yi shiru bai ce uffan ba.
Jikinta ya yi mata nauyi na gaske.

Gabad'aya ta ji ta rasa kuzarinta don sosai ta ga fishi a tare da shi. Hakan ya sanya ta gangara gefe sosia ta yi parking gudun kada ta je ta bugawa wasu.
"Yaya

33 / 50