DINGISHIN KWADO 3 COMPLETE BY D Auta.txt

Author :  Hadiza D Auta Category :  Romance

Chapter   11 / 50

30K to 33K   out of 149K words

Duk yadda take danne al'amura a ranta tare da jin kai matakin Yaya Sulaiman ya yi matuk'ar bugunta ta yadda ta fara sauke al'amura masu yawa. Ta tabbatar saukowar da ta yi take mu'amala da ita da kyau har da soyayyarsa da son sanin inda zata gan shi ko ta samu wani bayani gamshasshe.
Da ƙyar ta shawo kanta ta yi shiru.

Tsawon lokaci suna zaune jugum jugum don sosai suka shiga alhini.
A sanyaye Abida ta shiga bayi ta wanko fuskarta ta fito ta shafa hoda sannan ta fita dan gaida Yaya Asad. Suna gidan aka yi sallar magariba da isha.
Basu bar gidan ba sai da Bilki ta damkawa duka yaran tsarabarsu kowa da ledarsa tunda ga kan Amal har zuwa kan Noor. Yan aikin gidan mata ma duk ta bisu da turare.
Abida kuwa gwangwajeta ta yi da haddun materials din Malaysianfabrics....07020695644
Wanda take ta yi mata nacin tana so saboda kyaunsu da rashin nauyinsu.
Suka tafi baba da Momi suna ta saka musu albarka.
A hanya ya kalli yadda ta takure ta kasa sukuni.
Ya tausasa harshe ya ce "Sarauniyar shaiba ya dai?"
Ta yi shiru bata ce komai ba. Ya yi shiru don ya riga da ta gane ta idan ta shiga yanayi irin haka tafi son shiru.
Maimakon ya sake yi mata magana da baki sai kawai ya kunna musu karatun alkur'ani suratul Maryam ta fara tashi da muryar sheik Afif.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: https://t.me/+us5UdbOzEc5iNWVk
Kada a manta yau ma a daure a Danna mini likes din nan.

Sosai karatun ya daidaita mata rud'un da ta shiga na ina Yaya Sulaiman ya shiga tunda Abida ta kore mata tunanin ko ya hadu da ajaline.
Suka isa gidansu da y'ansanda suka yi masa k'awanya.
Ya kammala daidaita parking. Ta ga bai motsa ba. Sai kuma can ta ga ya sauke gilashin danƙareriyar motar, y'ansanda sun fi goma gabad'aya sun k'ame tare da sara masa. Hannu kawai ya daga musu suka sake sake sarawar sannan suka bar jikin motar kowa ya koma inda yake tsarewa a kusurwaowin gidan. Ta saka hannu da nufin ta bude murfin k'ofar sai ta ji ta a rufe.
Ta kalle shi amma ta kasa ce wa komai. Sai ta ga ya bude ya fita. Ya kewaya ya bude mata k'ofar da kansa sannan ya yi mata irin gaisuwar da ta ga yaransa sun yi masa yanzun nan. Har cikin ranta tana matuƙar jin dad'in sarawar da yake yi mata. A duk sadda ya yi mata hakan har zuciyarta take jin lallai ita din sarauniyar zuciyarsa ce.
Ta murmusa ta ce "Na gode Baban Bilkisu!
Daga haka ta dan yi gaba ta bar shi yana rufe motar tare da magana da wani d'ansanda da bata ji me suke ce wa ba.
Kaitsaye d'akinta ta nufa ta fara rage kayan jikinta. Daga nan ta fad'a bayi don ta yi maza ta yi wanka kafin ya shigo don sai ya ce shima wankan zai yi su yi tare.
Duk saurinta ya shigo d'akin kafin ta kammala wankan. Abin da take zaton shine ya afku don kuwa bayin ya shiga babu jin nauyi. Ya tube kan dole sai da suka yi tare. Daga suka fito kuma abin da ya biyo baya masu nauyi ne.

Da safe Bilki zaune gaban madubi daga ita sai tawul iya cinya tana k'arewa kanta kallo don gabad'aya bata yarda da kanta ba. Maganganun Abida na cewar tana da ciki sun yi matuk'ar tsaya mata a zuciyarta.
Zuciyarta ta harba ganin yadda breasts dinta suka cika suka tsaya sannan ya k'ara gari tamkar mai shafa mai. Haka nan ta ciko. Ta gasgata cikine da ita don kuwa rabonta da period tun wanda ta yi satin da za'a daura Mata aure. Ga shi wata na biyu ke nan. Ta furta 'Tirk'ashi ' a bayyane don gabadaya al'amarin wani iri take ganinsa. Wai itace d'auke da cikin Yaya Asad? Duk yadda ta gama fad'in bata sonsa shike nan sai a ji ta haihu wata tara da aure don kuwa tabbas kwanakinta a gidansa kwanakin cikin jikinta.
"Wanne irin rabo ne na gaggawa haka?"
Ta fad'a a fili .
Yara basu dawo ba sai da ya cinye sati biyunsa da ya fad'a. Soyayya da riritawa ba wacce bata ga ni ba. Ita da kanta idan yana yi mata wasu abubuwan sai ta ga kamar ya wuce ya yi su.
Bata fad'a masa batun cikinta ba shima kuma ya kife ta a baibai bai nuna mata ya gano ba.
Alti Jummai da yaranta uku Amal Noor da kuma Farha sun dawo gidanta wanda Abida ce ta kawo mata su.
Da farko Bilki tana zaune lafiya da Amal da Noor. Komai tare suke yi da Farha sannan bata banbanta su akan komai. Tana jinsu tamkar ya'yan cikinta. Yaran sun saba da ita tun a gidan Momi. Mahma sama Mahma k'asa kamar yadda Farha ta ke k'iranta.
Sosia take jin dad'in zamantakewarsu. Tuni ta koma aikinta, kullum Kuma suna waya da su Amrah mutanen Katsina. Hankalinta ya kwnaata tabbas yanzu ne ta yi aure a da kam ba wani abu da zata idar na jin dad'i ko na nutsuwar zuciyarta. Har dinga ganin ba zata samu wata a gidan Yaya Asad ba don kuwa ta yi amannar yana matuƙar sonta k'warai da gaske.

*Bayan wata d'aya*
Yana kishingide gefen gadonta ta shigo d'akin hannunta rike da bowl fari kal mai dan zurfi ta zauna gefe daga k'asa kan kafet. Tana cin abinta cikin nutsuwa.
Ya zura mata ido yana nazarin yadda ta zama mai ciye ciye sannan ta ninka farinta, haka nan ta zama mai kwadayi.

"Madam ko dai na yi ajiya ne ba a faɗa mini ba?".
Ya fad'a da wata irin murya mai kashe jiki.
Ta matse ta ce "Ajiya a ina ke nan?"
Ya yi murmushi mai sauti ya ce a cikinki mana ".
Yadda ta kalle shi tana tura masa ɗan bakin nan nata ne yasa ya san cewa tabbas ya yi ajiyar bakin shi ya ƙi rufuwa saboda murna nan da nan ya ta so daga inda yake kwance ya rumgume ta yana sumbatar ta, cikin tsananin farinciki da murna.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Yayin da ita kuma take jin wani iri takura da zullimin yadda cikin ya yi mata shigar sauri. Amma kuma soyayyar da yake gwada mata tare da yin bare bare akan sha'aninta yana matuƙar k'warara ta.

Kwanci tashi har aka yi hutu. Hafcy da take hostel a Skyline University ta kammala aji d'aya zata shiga biyu. Bilkisu kuma ta kammala sakandire. Aysha ta kammala da Enugu ta dawo gida Sai Dai kwanakin sati ta yi ta wuce Lagos yin wani kwas na watanni uku zuwa yanzu ta cinye wata guda. Tun a kwanakin da ta yi Bilki ta gane Aysha tsagera ce, Sai dai bata nuna mata ma ta gane tana mata kallon riani ba.
Yaran Basu Dade da dawowa gidan ba yaran ta fahimci halin kowacce daga cikin su. Bilkisu ta fi sauƙi sauki, kullum tana gaishe ta da safe, amma ba ta sake mata kamar da, duk da tana kokarin jawo yaran a jikinta. Hafcy kuma ba ta da kunya idan ta ganta sai kallon sama da k'asa tana tabe baki ko ta yi mata dariya, abin ya fara damunta amma ba ta nuna ba, kuma ba ta taba yi mata magana ba.
Amal dai da Noor sune nata komai itace ke yi musu tare da Farha. Abu daya ne yake bata mata rai da Hafcy ko ba ta ci darajan matan ubanta ta gaisheta ba, to ta ci darajar ita kanwar uban su ce su girmamata amma yarinyar nan sam ba ta ganin girmanta da mutumcinta kamar za ta yi mata magana sai kuma ta fasa, ta zura mata ido kawai ta ga iya gudun ruwanta amma idan ta zauna shiru ko a wajen aiki ne sai ta yi ta tunanin kar dai ta baro gidan Sahal a dalilin rashin adalcin miji yanzu kuma ta faɗo l gidan da ya'yan miji za su tayar mata da hankali domin ga Hafcy nan ta dau hanya. Hafcy dai tata da suke son Juna. Duk shekarar Duniya Sai ta yi mata dinkin sallah, haka nan lokacin uwarsu na da rai akai akai take k'iranta ya gaishet Konda aka yi rikicin Ladi farm bata fasa k'iranta ba hakan ya tabbatar lwa Bilki ba'a hana yarinyar mu'amala da ita ba. Amma tunda ta dawo ta tarar da zama matar Babansu Shike nan take yi mata abubuwan Raini iri iri.
Ko abinci aka dafa a gidan ba ta ci sai abin da taga dama zata bawa umarni Jummai ta yi mata ko Charity.
Kullum za'a yi girkin gida amma Hafcy zata bada umarnin ayi musu nasu daban. Koada yaushe abinci kibikibi Kuma ba'a iya cinyewa haka aka barinsa ya lalace.

"Mahma anya ba za ki yiwa yaran yaran nan togaciyar girkin da suke Sawa ana yi musu wanda ya wuce bukartarsu ba? Abin da suke yi bai kyautu ba, idan megidan ya ga ni ba zai ji dadi ba."
Alti take wannan batun da taa ga almobazarancin ya yi yawa .


Balki ta yi shuru kawai tana jin Alti na kora mata jawabi, yau ma hadaddiyar fried rice da coslow Ga Kuma pepper chicken aka dafa, amma Hafcy ta sanya aka dafa musu brown superghetti da pepper fish wai k'awayenta zasu zo. Har dare ba Wanda ya zo Kuma abincin gal warmers ko ta kansu bat sake bi ba.

"Mahma bai kyautu ba gaskiya. A matsayinki ta uwa a gare su ya kamata ki tsawatar musu."

Bilki ta jinjina kai, tasan gaskiya Alti ta fada, uwa take a wajensu kuma hakkinta ne ta gyara musu idan taga an yi ba daidai ba.
Duk da ba ta so ta yi magana ba, amma ya zama dole tun kafin Megidan ya ga ni ransa ya baci kuma daga karshe laifi ya dawo kanta.

"Haka ne Alti je ki abin ki zan yi musu mgana in sha Allah"
Ta tashi ta tafi ta bar Balki na nazarin yadda za ta tari yaran da magana, da ƙyar dai ta yi kundubslan tashi ta nufi dakin yaran har Farha duk suna cikin dakin tare da su, da yake suna da tibi a dakina suna ta kallon cartoon su kuma manyan na saman gado kowacce na latsa wayarta.
Shigowar Balki ya ba su mamaki, domin ba ta taba shigowa dakin su ba.
Tana shiga ta kalli su Amal ta ce
"Ku je falo ku ce Alti ta kunna muku cartoon din a can Farha."
Ta fada tana kallon ta da sauri ta yi gaba tana fadin" To Mahma Noor mu ku zo je."

Sai da suka fice sannan Balki ta mayar da hankalinta wajen manyan tana kallonsu.

"Sannu da gida Anty."[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: In ji mai sunanta Bilkisu.
"Ya hutu?"
Ta fada tana kallonta.
Sai ta amsa da lafiya lau, da ma ita suna gaisawa marar kunyar ta k'arshe Hafcy ce.
Yanzu ma ko kallon Bilki ba ta yi ba, hankalinta na kan wayar hannunta
Stool din madubi Bilki ta jawo ta zauna lokaci daya tana fadin" Sannu Hafsat."
Da gayya ta yi mata sannu domin ta ji kunya, idan ita ba za ta gaisheta ba, ita bari ta watsa mata kunyar gabadaya.

Amma yarinyar nan ba ta ji kunya ba sai ma ɗagowa da ta yi, ta sakar ma matw wani kallo kafin ta amsa da lafiya kawai ta cigaba da latsa wayarta. Ta ji wani iri amma sai ta danne ta numfasa ta ce
"Bilkisu da Hafsat me ya sa ba kwa cin abincin da na saka ake dafa mana gabadaya?"
Ta tambaye su tana kallonsu.
"Muna ci mana."
Bilkisu ta amsa amma ban da Hafsat..
"Ba kwa ci, sai dai ku saka Jummai ta yi muku naku daban. Kunsan kuma ba yadda za'a yi a dora tukunyar abinci a gidan nan a hanaku. Sai mu yi d'aku ku k'i ci, ku saka a dafa muku fiye da cikinku, abincin yana yin yawa da safe sai an zubar me ya sa haka?"
Bilkisu ta yi shuru domin ita ko tana son ci sai Hafsy ta hana ta.
Hafcy kuma ko nuna ma tana jin su ba ta yi ba.

"Ba zan takura muku sai kun ci abincin da na saka aka dafa ba. Amma ina so ku sani in har ba za ku ci ba, ku fada min, sai na fad'a mata ta daina sanwa daku idan jummai ko charity kuke son su dinga dafa muku ya wadatar ba sai an yi barna da yawa ba."
Suka yi shuru ba wacce ta yi magana.
"Ina fatan kun fahimta?
"E Anty"
Bilkisu ta fada kafin ta cigaba da fadin" Ki yi hakuri Anty."
Bilki ta mike tana fadin" ba komai ni dama saboda b'arnan abincin ne ya sa na yi magana."
Har ta kama hanyar fita ta ji Hafcy na magana cikin gunguni
"Ai ko mun yi b'arnar Daddynmu ke kawowa ba wani ba "
Ta fada tana hararan ta gefen ido.
Bilki ta juyo tana kallonta da kamar za ta ce mata wani abu sai kuma ta kasa hadiyewa ta ce" Haka ne shi yake kawo wa."
Daga haka ta fice daga dakin nasu, ta koma nata ta dade a gefen gado tana fama da zafin zuciya, yarinya karama take yi mata rashin kunya amma ta kasa daukan mataki.
Ta dade zaune tana tunanin kafin kiran sallar mangariba ya tashe ta, ta shiga tiolet ta dauro alwala amma a ranta ta kud'iri niyyar ko mai za su yi ba zata sake yi musu magana ba, kamar yadda suka fada gidan ubansu ne, su yi yadda suka ga dama.

Tun daga ranar ta kawo ido ta sanya musu, duk sun manta da tara sun da mahaifinsu ya yi farkon dawowarsu gidan a gaban Bilki ya ce su yi mata biyayya su darajata idan har suka yi mata rashin da'a shi suka raina ba ita ba, amma duk Hafcy ta manta da wannan karatun, shi kuma baya yini a gidan bai san abin da yake faruwa ba, da daddare yana tare da yaran sai sun kwanta sannan yake zuwa wajen Bilki.
Ita kuwa tana zaune tana zaman jiransa wani lokacin ma barcinta take yi tunda ta fara fahimtar Kakar hak'urin da zata yi a nasa gidan.
Wani dare ya shigo d'akinta ya tarar tana ninke sallaya da alama shafa'i da wuturi ta idar. Ta cire ƙaton hijab dinta na gunis collection . Sanye take cikin rigar barci ta garari fara kal wacce umm asala mazauniyar Eggypt ke kawo su Nigeria....
Cikinta ya fara turowa ta sake budewa ta kasa. K'amshinta na mussaman na tashi ko ya ya ta motsa. Shima ya yi wanka sanye yake cikin hadaddiyar jallabiya ruwan madara. Kamshinsa ya cika mata kofofin hanci.
Ya matsa daf da ita ya rungume ta a hankali ya ce
"Maigado ki rika zama tare da yaran nan da haka ne za su shaku da ke.".
Ba ta ce masa komai ba illa to domin ita bata son ta fara magana ahalin yanzu, ga cikin jikinta ba ya son hayaniya yanzu abu kadan zai bata mata rai, ta fara jin za ta yi kuka, sannan yana saka ta hassala nan da nan amma duk da haka tana ta daurewa.
Tunda ya yi mata magana ta ke dan fitowa suna zaman hiran amma ba mai sako hira da ita to gwara ma Bilkisu, amma Hafcy yi take tamkar bata san da ita a wajen ba, da ubanta kawai take hira.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal 🫶💍💛: Har suka kammala ayyukan Bilki na zuba idon ganin Aysha ta fito ta tanka ko ta ce sai an yi mata girkin dole. Sai ta ji shiru. Ta dinga ganin ashe ma rashin motsa kwanjine ya sanya suke yi mata cin kashi.
K'arfe shida sun kammala komai an shirya abinci abinci a saman tsakiya inda suke shan ruwa gabad'aya. Bilki ta fito a wanka ke nan ta ji ana bude mass get. Gabadaya gida ya kaure da k'amshin spice's din girki na Amreesh spicy Kano....
Ga kuma k'amshin tuararukan Dubai masu tsada na tashi sannu a hankali cikin burner.
A takaice dai gidan tamkar aljannar duniya ne.
A takaice ta shirya cikin bubu abaya ta elsisi Mai zuwa da mayafinta wacce itama dai a wajen mazauniyar Eggypt din nan uwar Yan biyu ta yi order din ta Umm Asalan da asala mai rigunan kasaitaaccun Mata.....
Ta saka hularta da ta ce da rigar. Ta ajiye mayafin akan gado. Ta dauki sallayar tare da mayafin ta sauka zuwa inda zasu sha ruwa don da shi da ita da yaran Syke Shan ruwa gabad'aya tunda aka fara azumi yaunkuma na biyar zasu kai.
Abin jin dad'i Shi yake jansu sallah.
Sallar Isha da asham kuwa a can k'asa suke yi ya jasu tare da dukkan ma'aikatan gidan maza da Mata.
Zamanta da shi ta gane ba shi da girman kai ko kad'an sannan Yana da kyakkwar mu'amala da na kasa da Shi. Rashin faraarsa ba ya hana shi kirki da saukaka mu'amala da jama'a.
Kawai inda take ganin rauninsa ta fahimci tamkar yana cikin mutane masu tsananin son ya'ya.
Amma sai bata wani ganin laifi tunda bata ga wani abu da zaisa ta tuhume shi akan son ya yi yawa ba. Dama ba yadda za'a yi ka haifo d'a ace baka sonsa.
Ta sauko daga samanta, shi kuma ya hawo dan haka suka hadu a tsakiya. Ya cire hularsa ya sara mata da taushin murya ya ce "Ranki ya dad'e sarauniyar shaiba ya ibada?"
Ta murmusa tare da mika masa hannunta na dama ta ce "Alhamdulillahi, ya aiki dafatan dai yau baka ji k'ishin ruwa sosai ba?".
Ya sumbaci hannun sannan ya ja ta zuwa tafkeken falon da suke zama.
A ciki ya tarar da yaran har kananun. Ganinsu bai saka ya sakar mata hannu ba sai da ya kaita kujera ta zauna. Ya dunkule hannunsa na dama alamar jinjina ya ce "Sannu da k'ok'ari Maigado gabad'aya k'amshin girkinki na daban ne wani irin k'amshi yake bayarwa da ba'a jinsa a ko ina sai a girkinki."
Dad'i ya ratsata don kuwa tana matuƙar son ta ji yana yabon ta, sannan shi a gaban kowa yaba mata yake yi ba ruwansa da yara
Sai da ya ga ta zauna sosai sannan ya juya ga yaran ya karbi gaisuwarsu. Ya kalli agogon hannunsa ya ce "Ku bani mintina goma na watsa ruwa".
A ranta kuma tasan spice's din Amreesh babu na biyunsu wajen k'amshi da fitarwa girki dandano na mussaman.
Aysha na kishigide wayarta na

11 / 50