Author : Hadiza D Auta Category : Romance
hannunta ta gefen Ido kuwa Bilki take kallo. Haka kawai ta ji wani abu ya mintsine ta ganin yadda ta yi kyau ta haska maroon din rigar da take jikinta. Sannan cikin jikinta ya fara turowa ana ganinsa duk kuwa da ya bi jikinta. Sosia ta ji ciwon da ya ce wai k'amshin girkinta baya jinsa a ko ina sai a gunta. Wato har na mominsu kenan?
Ta yi k'aramin tsaki tabbas ba zasu shirya da Anti Maigado ba mussaman da dazu ta nuna mata iyakarta a gidan ubanta. Bari a sha ruwa itama ta nuna mata tasirin y'a a wajen uba.
Mintina shabiyar ya fito sanye da jallabiya coffee k'amshinsa ya baibaiye su tun kafin ya shigo.
Yana shigowa ana kirian sallah.
Suka yi addu'ar buda baki sannan suka hau cin dabino da inibi ga kuma kankana da ruwan roba da ya yi raba don sanyi.
Suka dan huta sannan ya jasu sallah.
Bayan sun idar suka fara cin soyayyar doya da kwai da kuma ferfesun kaji sai kunun gyada, da shayi. Ga kuma su samosa a gefe. Sai kuma farrar shinkafa aka dafa da kayan lambu irinsu kara's, pea's, da koren wake da za a ci da soyayyiyar miyar kaji. Ga hadin salad mai kyau. Ga kunun aya mai dad'in gaske.
Duk abin da kake son ci shi zaka zuba da kanka. K'ananun ne ake zuba musu zabin da suke so.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal đź«¶đź’Ťđź’›: Sannan har yanzu girkinsu suke sawa a yi musu. Basu fasa yin yadda suke so a kicin ba.
Bilki ta rasa yadda zata bullowa lamarin sai kawai ta ce a daina girki da su, ta rika dafa iya su da su Amal su kuma Jummai ta dinga dafa musu abinda suke so, hakan kuma da aka yi shike nan Bilki ta samu zaman lafiya, ba ta shiga harkansu suma ba sa shiga tata, tana zuwa wajen aikinta suma suna zuwa makarantatsu tunda dama hutun da Hafcy ta samu ba mai yawa ba ne . Bilkisu ma a sati biyu da suka shud'e ta fara zuwa makarantarsu Hafcy ta samu gurbin karatu zata karanta pharmacy, dan haka sai dare suke haduwa, idan kuma sun hadun Bilkisu za ta gaishe ta amma Hafcy matsewa take yi tamkar bata ganta ba.
Al'amarin Hafcy na matuƙar ciwa Bilki tuwo a kwarya, kawai hak'uri take yi, don ba zai yiwu ta biyewa yarinya k'ank'anuwa ba. Amma dai tabbas ta gama tabbatarwa jarabawar aurenta da Asad yaransa ne don sune zasu hana ta zaman lafiya.
Bilki bata san ce wa Hafcy lafiya ba ce sai da Aysha ta kamalla kwas dinta ta dawo gidan anan ne ta tabbatar da Hafcy ba ta yi mata komai ba. Ta dauka Aysha da take babba za ta fi su hankali mussaman yadda idan sun je hutu Funtua tana makale da ita tunda Abida bata kula yara.
Tundaa ta dawo gidan komai ya fara sauyawa, kai tsaye ba ta yi wa Bilki rashin kunya amma ta zuge yaran har da Bilkisu mai dama dama yanzu ta kasa gane kanta. Su Amal kuwa tana dawowa duk ta kwashe kayansu ta mayar dakinta ta raba su da Farha, duk Billki ba ta yi magana ba amma lamarin ya ba ta mamaki sannan ya daure mata kai.
Kuma ta koma ita ke yiwaa yaran komai.
Alti ke yi musu abin kari da wanda za su tafi da shi amma tana dawowa ta ba da Umarnin jummaia ce za ta dinga yi.
Alti ta yi mata magana ta ce "Mahma kada ki bari ta raba su Amal da Farha. A sanyaye ta ce "kyale su kawai ai su gidan ubansu ne ita kuwa fa? Ubanta ya yi nisa nice nake zaman uwa da uba a gare ta dan haka ki dinga yi mata kawai". Ta kamalla maganar da kuka don gabad'aya ta fara gajiya.
Ta koma kawai ta zama yar kallo shi kuma megidan bai san wainar da ake toyawa ba. Duk tsiyar Hafcy bata taba nunawa akan Farha ba amma tunda Aysha ta zo ta tisa mata yarinyar da hantara da zare ido da dukkan alamu Aysha bata son Abida duk yadda aka yi. Idan ita basa sonta to Farha fa? Kuma idan yaran basu san ba ita ta haifi Farha ba, to Aysha ta san Abida ce ta haife ta. Abida kuwa uwarsu d'aya ubansu daya da ubansu. Amna gabad'aya ta hana su Amal kulata daga Bilki har d'iyarta Aysha ta takurasu matuk'a da gaskeq .
Tun Bilki na mamakin lamarin har ta fahimci Aysha dai kishi take yi da ita mai tsananin gaske.
Sannan dangin babarsu sun fad'a mata rabon auren Bilki ne ya kashe uwarsu. Bayan haka ya k'i auren Laura wacce ita yafi cancanta ya aura don kanwar Momi ce da ta girma a hannunta ba zata taba cutar da su ba. Sannan ba zasu zama bak'i a gidan ubansu ba.
Da haka suka sake cusa mata kin Bilki tare da kud'irewa sai sun matsa mata ta bar musu gidan. Antinsu ta shigo tunda wata kusar ai tafi wata.
Da yake da iliminta cikin ruwan sanyi ta baza makaman yaƙin musgunawa Bilki.
Ana cikin haka aka shiga watan azumin ramadan. To da wuri megidan yake dawowa in dai yana gari ya yi bude baki tare da iyalinsa da haka ya saba tun filazal.
Ganin haka da Bilki ta yi ya sanya karbar ragamar girkin buda baki sai dai a taya ta don kama wasu ayyuakan don kwadayin samun ladan ciyar da mai azumi.
Don haka tun azahar suke shiga kicin ake Fara hidimar abin shan ruwa tunda ba iya cikinsu suke yi ba har da ma'aikatan gidan.
Amma ga mamakinta sai Aysha ta saka Charity da Jummai yin wani girke-girken na daban.
Karon farko da Bilki ta taka birki akan ba za'a yi wani girki ba matuƙar tana kicin din.
Sannan abin da aka yi shi kowa zai ci.
Aysha ce ta ce "Na yi fa Anty".
Jummai ta fadaa dan tsorace.
Kaitsaye Bilki ta ce "Ki ce mata na hana ina aiki a kicin din".
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal đź«¶đź’Ťđź’›: Cikin kyawawan plates din ralzaplace suke cin abincin.08109544470
Cikin nutsuwa suke ci a hankali ya fahimci Aysha da Hafcy Basu zuba komai ba. Tun kankanar da suka sha da ruwa basu taɓa komai ba. Ya ajiye cokalin hannunsa. Da kulawa ya ce "Aysha, Hafcy bakwa cin abinci what's wrong?"
Suka yi shiru nan da nan idon Aysha ya cika da k'walla ta zuba masa ido take ya gano kuka take yi sannan bata cikin sukuni. Tausayinta ya kama shi yasan mominsu ta tuna tunda sun saba da ita suke zama irin haka, bana kuma ba da uwarsu ba dole hankalinta ya tashi. Atausashe ya ce "Menene?"
Da rawar murya ta ce "Dady kasan bama cin doya da aka soya da kwai ni da Hafcy, sannan ni bana cin kaza.
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal đź«¶đź’Ťđź’›: https://youtu.be/j7_u1udYqDI?si=Jg27RDNS9GcXtCOJ
*Dingishin KWAD'O*
*Book4*
*Na*
*Surayya Dee*
*Dan Allah masoyan rubutuna ku daure Ki cicciba mini labarin nan ta hanyar yi mini likes a YouTube.*
*Gasa ce da yawan likes da za'a fitar da gwarzon labari*.
*A daure a mini like an saki episode 1-3 wadanda suka yi Allah ya saka musu da ALHERI, waÉ—anda Basu yi, a daure a yi, Ubangiji ya taimakemu gabad'aya.*
Kuma duk abincin akwai kaza a ciki."
Da sauri ya ce "Hakane to ai da kin fad'a mata tunda bata sa ni ba ".
A nutse kuma a hankali ta ce"Na saka Charity ta yi an ce ba zata shiga
Cigaba
kicin ba, na tura jummai tunda ita mai sallace an ce ba zata yi ba, dole abin da aka girka shi zan ci, alhalin mu ba haka muka saba ba."
Ta fad'a tana goge hawaye da tissue hannunta.
Ya juya ga Bilki ya ce "Maigado ki dinga bari ana yi musu duk abin da suke so. Yanzu charity da Jummai ai kusan zamansu suke yi tunda sun san me suke so. Mun Saba rayuwa kowa yana cin abin da yake so ne ba takura ".
Mamaki ya hana Bilki magana.
Ya tashi daga kusa da ita ya koma kusa da Aysha da Hafcy da suka koma gefe. Ya dinga rarrashi tamkar yara k'ananun akan su yi hak'uri su ci snacks kafin charity ta yi musu abin da suke son ci kada yunwa ta illata su.
Idonsa ya yi ja tamkar ya taya su kukan.
Bilki ta sandare tana kallonsu gabad'aya ma ta rasa me zata ce.
Ya danna k'ira shashin ma'aikatan. Charity din ce ta dauka. Cikin harshen turanci ya ce "Ta zo yanzun nan".
Mintina uku ta iso ta gurfana gabansa. Ya ce "Me zaku ci?"
Hafcy ta ce "Fried yam da onion soup ma is ok. Tunda yunwa muke ji. Aysha da ƙyar ta ce "Ki yi mana dambun kuskus da zamu ci anjima".
Ta amsa a ladabce ta mik'e. Abincin da bai ci ba kenan don yana kusa da su har aka kawo musu farar doya soyayya da miyar albasa.
Daidai lokacin kuma an fara k'iran sallar isha.
Amal da Noor suna ta kallonsu tare da Farha. Bilki ta yi sukuri tana kallon uba da ya'yansa yana ta yi musu sannun jiran da suka yi don ga ni yake yi yunwa ta ci ta cinye su.
Bilkisu junior kam ta ci abinda da Bilkin ta girka babu musu ko inkari ita bata da matsala kawai yayyen nata ne suke tursasata akan ta bijirewa Bilki.
*Pay1k via* 2384876855
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank*
08032773332
*Don smaun cikkaken labarin a telegram*
[10/3, 4:03 PM] Mrs awwal đź«¶đź’Ťđź’›: [Sep 17, 2025 at 11:27]
49
Bayan sun idar da salla sundawo Aysha ta ce "Dady na san kana son kuskus na zubo maka kadan tunda dazu baka wani ci abinci ba".
Zuciyarsa d'aya ya ce "Zubo mini Aysha". Ta tashi ta zubo masa daidai cikinsa. Ya ce kawo wani spoon din zan je mu ci da Antinku a ido ma ya yi kyau."
"Kai Dady ka zauna ka ci anan idan zaka tafi sai na zubo maka nata. Ita ai ta nadi doyar nan ba kad'an ba".
Ya zauna kuwa ya cinye suna hira tana babshi labarin Enugu da mutanen garin da irin banbancin da ta gani na aladun inyamurai da kuma na yarabawa da ta ga ni a Lagos. Har shadayan dare kafin ya yi musu sallama ya haye saman Bilki.
Ya tarar da ita tana kwance ta lullube Rabin jikinta da bargo idanuwanta a lumshe. Ya shiga bayi ya sake wanka ya yi brush sannan ya kashe fitilar dakin Ya laluba da taimakon hasken da yake shigowa ta windo ya Isa gadon ya kwanta a bayanta ya saka hannunsa ya rungume ta sosai. Bata motsa ba, dan kuwa kuka take yi na sharb'e. Ta rasa ta yadda zata bude baki ta yi masa k'orafi akan ya'yansa. Sannan shi kansa yana yin abubuwan da suke musgunawa ne a gareta. Sai ya kai kusan shabiyun dare tare da su a falo da sunan hira. Sannan k'aida da su zai karya ko da ace ba zai fita da wuri ba to Duk abin da yaran suke son karyawa da shi Idan an yi musu Sai su yi masa waya wai suna jiransa Su karya haka zai katse barcin ya fita. Sai idan zata karya sai ya zauna da ita suna hira yana bata a baki sannan ya dan taba kad'an. Ta taba yi masa maganar da ita ya kamata ya dinga karyawa fa. A tausashe ya bata amsa da fad'in "Ki yi hak'uri ni so nake ma ki dinga shiga cikinmu muna karyawar da abin da suke so din, tausayinsu nake ji mun riga mun saba tare muke karyawa, so ina matuƙar jin tsoron kada damuwar rashin mamamnsu ta yi musu yawa. Shiyasa nake yi musu komai kada su dinga ganin dan sun rasa uwa sun rasa gata."
Tunda ya fada mata haka ta debi ido ta zuba musu.
Yanzu kuma me zata ce masa?"
Ya gama lalubeta ta yi bakam. Ya hura mata iska a kunne tare da murza kirjinta nan da nan jikinta ya amsa k'iran nasa. Ta kasa cigaba da share shi. A kunne ya rada mata kina iya yin barci ba a k'irjina ba ne? Nasan idonki biyu. Babyna ba zai bari ki yi barci ba tare da na zo na tabo shi na zuba masa ruwan dumi da zai kara masa kuzari ba".
Haka ya dinga rura mata jiki har sai da ta sakar masa jiki yadda yake so, ya cudata sosai sannan suka yi wanka suka kwanta barci mai dad'i ya sure ta, ta manta takaicin yara.
Tun ranar bata sake hana ayi musu girki ba. Don cewa ya yi a dinga yi musu nasu a kicin din samansu.
An kai azumi goma suna buda Baki Aysha ta ce "Dady Anty Laura zata zo mana hutu ".
Ba tare da tunanin komai ba ya ce "Ah ta zo mana itama ai nan gidansu ne".
Nan da nan zuciyar Bilki ta motsa. Lauran da ake ta yi masa tallan ta aura ne za'a turo fa gidan ta zauna?.
Ta hadiye tunda maigidan aka faɗawa shi kuma ya bada damar ta zo har yana fad'in gidansu ne. Ta jijjiga kai wataƙila dai hak'urin da take ta yi da shi da ya'yansa ya kusa k'arewa dan kuwa idan har Laura ta ce zata yi mata shakiyancin da yaran suke yi mata lallai zai sha mamakinta tunda ya amince da zuwanta ba tare da ya shawarce ta ko tunanin komai ba.
Laura ba ta zo gidan ba sai ranar azumi na shaa bakwai. Ta kammala digiinta a B.u.k
Tunda Laura ta dawo gidan sai aka canja salo don kuwa daga ita har Aysha yamma na yi suke yin wanka su kece da kwalliya yadda suka ga Bilki na yi. Sannan a gabansa mutuntunta suke yi suna fad'in "anty sannu da shan ruwa, sannu da aiki." Gabadaya Laura ta sake koyawa Aysha da Hafcy dabarun yin kisan mummuke. Ta yadda idan ma ta kai ƙararsu za a ga itace bata da hakuri.
Idan ba ya gidan kuwa mp ce dasu su mai tsada mai fitar da sauti mai k'arfi yini suke yi suna kunna wakokin gwanja na habaici kalakala su kure volume duk tazarar samanta da nasu sai ta jiyo. Abubuwan suka fara yi mata tsauri. Mafi tayar mata da hankali cin zalin Farha da suke yi, sannan sun hana su Noor kulata. Idan yana nan bai ganta a gunsu ba ya ce ta je wajensu sannan ya yiwa Bilki fad'a tana makale da yarinya ba zata barta ta shiga wajen yara ba.
Ta kasa bude baki ta ce masa zalinta suke ci tare da zare mata ido da razanata.
Ranar asabar ya je Ilorin, kwana d'aya zai dawo.
Da daddaren ranar tana kan sallayarta ta kalli agogon bango ya nuna mata k'arfe uku da rabi na dare. Ta sake kai ganin ta ga gadonta Farha ke barci cikin nutsuwa.
Zuciyarta babu dad'i amma ta dukufa addu'a don kuwa al'amarin yaran kullum kara tsananta yake yi.
Washegari lahadi k'arfe d'aya na rana da y'an mintina Farha ta shigo d'akinta a guje sannan a matuƙar tsorace ta dumfare ta, ta makale a bayanta jikinta na b'ari.
"Wa ya biyo ki?"
Kafin ta bude baki ta yi mata magana Hafcy ta shigo d'akin a matuƙar fusace. Ba jin nauyi ko kunya ta finciko ta a bayan Bilki ta faffala mata mari har guda biyu masu zafin gaske.
Wani irin fishin da Bilki take yawan addu'ar Allah ya tsare ta da shi ya taso mata, hak'urinta ya k'wace. Ta yunk'ura ta mike daidai lokacin Hafcy ta juya da nufin fita daga dakin yayin da Farha take daderen kuka rike da fuskarta.
Da azama Bilki ta finciko ta da k'arfin gaske ta dawo da baya ta fadi kan hannunta. Bilki bata lura da hakan ba ta yi maza ta rufe kofar d'akinta ta cire key din dakin ta jefa kan gado. Cable din jikin standing fan ta ciro irin wacce ake cajin ta.
Ba tunanin komai ta isa ta dinga labtawa Hafcy ta koina babu tausayi ko kad'an. Ihun Hafcy ya tsananta Aysha da Laura har ma da Alti suka dinga bugun k'ofar amma bata k'yale ta ba sai da ta yi mata ligi ligi. Bayan ta jiyo kukan Alti tana fad'in kada ta bari zuciyarta ta rinjaye ta, ta yi aikin da zai zama Fargar Jaji.
Ta wurgar da wayar gefe ta shiga bayi ta wanko idonta don kuwa hawaye ke zubar mata tamkar famfo. Ta dauki key ta bude k'ofar d'akin, gabad'aya suka shigo d'akin da gaggawa suka nufi Hafcy da take kwance tana kukan neman agaji don kuwa sosai jikinta ya karbi kebra.
Laura da ta ga jikin Hafcy ya yi rudu rudu wani gefen har jini ya kwanta. Ta ce "Kan uban nan wanne irin duka ne haka tamkar an samu jaka?"
Bilki tana tsaye bata ce uffan ba.
Aysha kuwa ta saki ashariya tare da fad'in "Ai kuwa ko sama da k'asa zasu hade ba zan yarda ba, zan ga inda aka bawa wata banza lasisin cin zarafin d'anadam haka siddan. Daga kaidojojin addini har na constitution ".
Bata Ankara ba Bilki ta d'auki cable din ta shimfida mata a gadon baya da iyakacin k'arfinta. Tsananin azabar da ta ratsa ta ya sanya ta girba a guje ta fice don kuwa gabad'aya ta kidime.
Laura ta yi wuri wuri a tsorace ta ce "Anty lafiya kuwa?"
A sanyaye Bilki ta ce ", Lafiyar ce ta kawo haka. Ki kama hanya ki fice mini a d'aki. Don idan kika yi kuskuren zagina a dakin nan Billahillazi ba za ki sake tako k'afarki da sunan kwana gidan nan ba. Ba zan doke ki ba, amma za ki ga yadda zan saka a yi miki korar kare tunda dai ke ba dolen gidan ba ce. Su kuma kada su fasa taɓa ni, ba a haifi wacce zata shigo dakina ta yi mini cin mutunci na bar ta salin alin ba. Komai zasu yi mini a waje zan yi hak'uri don nasan komai lokacine, wata rana ba zasu yi ba, dan haka zan yi hak'uri har komai ya wuce, amma ba zan yi hak'uri idan aka tako har cikin d'akina aka taɓa ni ba tabbas. Sannan zan gargade Ki da babbar murya ki bi a sannu don ke ma ina da kalar na ki hukuncin, akan idonki kin ga yadda na zane su ko? To ki taka a hankali " .
Ta kasa magana ta