DINGISHIN KWADO 3 COMPLETE BY D Auta.txt

Author :  Hadiza D Auta Category :  Romance

Chapter   39 / 50

114K to 117K   out of 149K words

Content Bot, [Nov 3, 2025 at 13:03]
*DINGISHIN KWADO*
*08032773332*.

Daga haka ya mike ya ce "Dama fita zan yi."
Sulaiman ya mike yana masa godiya ya taka masa zuwa waje.
Ya shiga mota direbansa ya ja suka fice.
A tunzure Sulaiman ya shiga ya sameta.
Komawa ya yi Sulaiman din da mai cike da zafin kai. Don ashariya ya danna mata tafi goma. Ya gama zage ta sannan ya moma kan y'ay'anta suma ya dinga maka musu.
Gabad'ayansu sun yi tsamo tsamo don kuwa suna yara sun san baya wasa da su.
Hamida kuka kawai take yi. Don gorin da mijinta ya yi mata na bata zaune lafiya da y'anuwanta da wan mahaifinta da ahalinsa ba shine lasisin da zata yi gaba ko ta saka ya'yanasa gaba da y'anuwansa ba. Kuma yayar tasa da suke uba d'aya tabbas bata sonta akilo take yi ma ya k'ara aure. Amma ya kafe dole ta bita tunda ba shi da uwa ba shi da uba kuma ita ce ba lbbarsu a lokacin da ya yi karatu haka ta dinga siyar da kayan d'akinta tana ba shi kud'i yana hidimar makaranta. Shi kuwa ba yadda za'a yi a shata mata layi a gidansa ko a kan y'ay'ansa. Itama Idan ta ga ba zata iya girmamata ba to kawai ta yi gaba shi bai saba ganin gaba irin tata ba.
Kukan da take yi bana korar da ya yi niyyar yi musu ba ne. A a gorin tana gaba da Baba Babba da su oga Asad ne yake saka ta kuka mai gigitarwa.
Ga Sulaiman din da suke nema ruwa a jallo ya zo gidanta ya tarar da bak'incikin da ya yi sanadin a gaban y'ay'anta yake mata cin mutunci.
Tsawon lokaci kafin ya daina cin mutuncinsu.
A sanyaye Ummu da ita ce babba ta ce "Ka yi hak'uri uncle zamu gyara."
A kufule ya ce "Kada ma ku gyara. Ai ni kam kun ba ni kunya ace wai kuna iya zagin uwarku, tana fad'a kuna fad'a, bata isa ku bita ba, sai dai ta biku?"
Hamida ta sake rushewa da kuka don al'amarin da yake matuƙar gigita ta kenan. Amma ita bata gano sakacinta da matsanancitar soyayyar da take gwada musu na kan gaba wajen halin da suke ciki, sai kawai take ganin saka mata hannu dangin miji suka yi don basa sonta.
Baffa mai bin Ummu kansa na k'asa Sulaiman ya ce "Kai zo nan".
Da sauri ya isa kusa da shi ya tsugunna. Ya ce "Dago fuskrua ba ga ni?"
Ya dago a tsorace Sulaiman ya zuba masa ido ainun cikin nazari.
Kafin ya ce "Shaye Shaye kake yi sha ko?"
Da sauri ya ce "Uncle wallahu bana sha!
Hamida ta sake kecewa da kukan bak'in ciki don kuwa tabbas yana sha.
Sulaiman ya ce "Kana fad'a mini baka sha ko?"
Gobe da kaina zan kaika wajen Ansari su auna mini kai. Idan suak gano kana sha da kansu Kuma. To zan barka a gidansa ya ci uwarka da kyau".
Hankali ln yaron ya tashi ya ce "Wallahi uncle last month na fara shan shisha, wiwi kam shekaranjiya ne kawai. Kuma Babanmu ya fad'a mini idan na cigaba da sha zai kori ni. Wallahi yau kwana biyar ban sha ba, dan allaj5ka yi hak'uri na daina na a kuma taya ni addu'a.
Zuciyar Sulaiman ta karye. Ya rasa mai zai ce. Tabbas matasa sun jefa kansu cikin gararrin Shaye Shaye. Tarbiya ta shiga cikin halin ni y'asu. Wasu laifin iyaye ne yayin da wasu iyayen sun yi iya bakin k'ok'arinsu y'ay'an ne suka bijire suka tankwabar da kyawawan dabiun da ake dorasu a kai. A fili ya ce "Allah ya shirye ka, ya shirya na dukkan y'ay'an alummar Annabi da suka karkace.
Ya kalli Ummu ya ce 'Ke kuma sai kika zabi ki ta cin mutuncin uwarki saboda kina son aure ko? To dan kan uwarki kin kawo mijin ne aka k'i yi miki? Da bakina zan faɗawa Babanki a katse karatun da kike yi tunda ba na hankali da nutsuwa kike yi ba, na raini da rashin d'a'a ne. Ban da haka kamar ki ace ki tisa uwarki a gaba saboda kina ganin kin kamo ta girma!
Da kuka sosia take bada hak'uri. Don ga ni take yi kafin ya bar gidan zai iya zaneta. Tunda mamansu ma an mata ashariya kalakala.

Sai da ya wanke su tas sannan ya sallame Su tare da gargadin ya dawo Kano gabad'aya. Kada Su fasa rashin tarbiya da cin mutuncin uwarsu da yan uwan ubansu.
Suna fita ya kalli Hamida da take kuka tamkar ta fito da zuciyarta. Save Restricted Content Bot, [Nov 3, 2025 at 13:06]
Ya tausasa harshe ya ce "Hamida" .
Ta kasa amsawa don kuwa kukan da take yi mai nauyi ne ainun.
Ya yi shiru yana kallonta amma zuciyarsa tamkar ya rushe da kukan shima don zuciyarsa ta yi masa nau yi k'warai da gaske.
Tausayinta ya mamaye takaicinta.
Ya zuba mata ido yana ganin kammanin Maminsu sak a tare da ita. Dama ita kam komai na uwarsu ne hatta tafiyarsu iri daya ce.
Ba yaudari kansa ba har halayyar ta kwashe. Don kuwa suma sun rayu ne tana fad'a musu y'anuwanta da y'anuwan Babansu basa sonta.
Ya nisa ya ce "Kukan ya isa y'aruwata, share hawayenki ko kowa baya sonki, ai kinsan lina da ni, ba wanda nake so kaf cikinku irinki. Ni na saki nono kika kama. Ki yi hakuri".
Nan da nan kuwa ta share hawayenta. Idonsa ya ciko da k'walla. Haka MAMI take yi Idan ta zaunar da Shi tana fad'a masa mutanen da suke kewaye da ita basa sonta duk munafukanta ne. Da zarar ya ce mata mu muna sonki MAMI. Irin son da zamu sadaukar miki da komai. Nan da nan sai ta wartsake su yi hirar arziki. Amma idan ya yi mata nasiha tare da fad'in ta daina damuwa irin haka ai sai ta harzuk'a ta hau fadan baya kishinta tunda baya sonta daga nan zaman ya watse. Amma da ya fahimci rarrashi da zuga take so sai yake yi mata hakan cikin siyasa, ya samu su rabu k'alau.
To yau ha Hamida ma ta nuna masa haka take..

Ta mike ta shiga kicin ta hado masa abinci.
Yana ci suna hira ya bata labarin komai har zamansa a gidan yari don yasan ba zata fad'a ba.
Cikin dabara ya ce "Zan dai hutar da ke gorin mijinki na kina gaba da Baba. Zan zo da kaina na tafi dake ki gaida Baba gobe kuma sai ya samu wani abin fad'a.
Amma lallai ki shiga hankalinki, idan kika yiwa kanki sanadin da aurenki ya k'are za ki shiga garari mai yawa. Mijinki mutumin kirki ne, mai addinine to ki yi maza ki gyara tun ba ki janyowa kanki sanadin wahala ba. Duk son da nake yi miki ba zan iya cike miki gurbinsa ba. Idan kin yarda da maganata idan ya dawo ki ba shi hak'uri, ki gyara mu'amalarki da y'anuwansa, ki kuma gyara kuskuren da kike yi akan tarbiyar yara".
A sanyaye ta ce "To."
Ya kalle ta ya ce nan da sati biyu zan n koma Abuja tare da ku zamu tafi gabad'aya.".
Ga mamakinsa ya ji ta ce "To".
Wani abu ya tsirga masa don ya yi zaton sai ya kai ruwa rana da ita kafin ta amince don kuwa ita din kafaffiya ce ta gaske.
Amma tunda ta amince to kowa ma zai amince babu dogon turanci, don ita da Ansari shawararsu d'aya sune kuma yake fargaba akansu.
Hamida da Ansari sune sak MAMI kuma sune aminanta. Saddiqa bata da wata matsala.
Anisa kuwa ra'ayin Hamida take bi akan komai bisa hujjar ita ce babbarsu, to itace uwarta a yanzu. Shiyasa da ta ce mata ta tafi Maiduguri ta tafi babu musu.
Daidai lokacin ya k'ira abokinsa akan ya zo ya d'auke shi.
Ya dinga yi mata nasiha tare da rarrashi.
Har abokin nasa ya iso ya mata sallama akan zai dawo, amma gobe sammako zai yi zuwa Funtua, kafin ya fara hidimar ayyukan asibiti.
Bak'in ciki ya hanata yin magana amma da tambaye shi me zai yi a wannan garin?
Da abokinsa ya dauke shi bai zame ko ina ba, sai office din Julius Berger.
Ya gama tattaunawa da su, suka yi gobe zasu tafi Funtua da wakilansu.
Washegari sassafe kuwa suka tafi a motar kamfanin.
Kaitsaye gidansu da yake a garkame suka isa.
Ba maganar neman makulli. Don haka aka yanke Shi.
Gabad'aya k'ura da karashiya shin yiwa gidan k'awanya sosai.
Sashin Baba Babba suka fara shiga kujeru da abubuwan bukata duk suna nan Sai dai kam ba ko dad'in kallo a dalilin yadda suka dade a haka.
Suka shiga d'akinsu Abida Hatta gadajensu uku duk suna ciki.
Ya daure suka Ga ko Ina a Shashi sannan suka wuce zuwa sashin MAMI.
Nan kam ba kaya tunda komai nata sun sun bayar, wasu sun sadakar wasu kuma k'annensa mata sun dauka.
A yanzu b'angaren MAMI zaman Ansari yake yi.
Shima suka duba suka yi aune aunensu.
Suka isa shashin yan aiki.
Shashinsa ne na k'arshe. Save Restricted Content Bot, [Nov 3, 2025 at 13:08]
Shima komai na nan.
Kurace dai kawia ta lullube komai.
Amma har kayan Abida na wadrof duk suna nan da akwatinanta.
Ba wani gyara ne sosai a nasa b'angaren ba, a dalilin lokacin aurensu Sai da aka canja fasalin ganin ya banbanta da na su Baba.
Suka gama ganin ko ina suka fito harabar suka tsaya.
Sulaiman idanuwansa sun cika da k'walla a dalilin memory dim da suka shud'e Yana ta dawo masa.
Wai gidansu ne ya zama kufai, gidansune ya zama matattarar tururura da kwazazzabai da karashiyoyi.
Hawaye ya k'wace masa.
Ma'aikatan jikinsu ya yi sanyi don kuwa Su kansu yadda suka ga girman gidan da kuma alamun da an yi rayuwa a cikinsa Sai suka tausaya masa a dalilin sun yi tunanin ko duk iyalin sun rasu ne.
Suka gama ya rufe gidan da Sabon kwadon.
Tare da su suka rankaya gidan sarki.
Ya yi gaisuwa tare da sanarwar ya dawo, a kuma kowanne lokaci zai iya buk'atar Ladi farm.
Mai girma hakimi ya tabbatar masa babu damuwa ko yanzu idan yanzu so zai ba shi.
Suka yi sallama suka fito suka d'auki hanyar Kano.
Bai bar office din ba sai da ya cake musu milyoyin kudin da suka caje shi akan gyara da canja fasalin gidansu gabad'aya da yake su yi masa cikin k'ank'anin lokaci.
Duk da milyoyin kudine masu yawa haka ya musu transfer ta dala account d'insa.
Daga nan ya wuce zuwa gidan Hamida.
Anan ya ci abincin dare.
Bai fad'a mata kudirinsa ba.
Daga nan ya shiga aiki a asibiti ka'in da na'in.
Satinsa guda bai ga k'iran wayar Abida a wayarsa ba.
Abin na mintsininsa sosai, sai dai matsanancin ayyuka da matsalolin da suka dabaibaye shi ya sanya shi mantawa da wannan matsalar.
Sati biyu ya kammala contract din asibitin.
Ya samu kuɗadensa.
Ya koma Funtua ya tarar an kammala gyara shashinsa kamar yadda ya bukat su fara da nan.
An wanke shi tas.
Ya fito ya dawo tamkar yanzu aka gina.
Kayan Abida da aka yi mata masu k'arshen tsada ba abin da suka yi.
Amma ya tarkata su bayan ya k'ira kafinta ya kunce ya goge Su.
D'iyar goggonsu ya kaiwa wacce da babarta da su Baba babba ubansu d'aya.
Ta dinga yi masa godiya da fatan alheri.
Ya tarar duk goggonin nasu sun rasu.
Zuciyarsa ta harba. Ko ya ya y'anuwa Maminsu?
Take ya wuce ainihin gidansu ya gaida yayyenta da kanneta da suke rayuwa a cikin gidan.
Ya yi musu alheri suna ta yi masa nasiha tare da fad'an ya yi wauta da ya tsallake ya bar y'anuwansa da danginsa tsawon lokaci.
Kawu Bala da suke daki d'aya da mami ya tambaye shi akan Ko ya je ya gaida Alhaji Babba?"
Sulaiman da k'warin guiwar ya ce" A wajensa ma na sauka".
Dad'i ya kama dattijon ya dinga yi masa addu'a tare da ba shi umarnin lallai ya dinga saka y'anuwasa akan hanya. Bilki ce kawai take yi musu waya har ma da aiken kayan abinci da kud'i, sai kuma Ansari da Shima yake kamantawa. Amma sauran kam ko gaisuwar wayar ma ta gagara.
Haka Sulaiman ya tafi cikin murnar sa'ar da ya yi ba wanda ya mutu a cikinsu Allah ya k'addara zasu sake ganawa.
Yana tafe a k'afa yana sake fahimtar irin koma bayan da ya same shi a dalilin tafiyar da ya yi. Nadama kam dama ya jima da yinta mussaman da ya yi rayuwar prison.
Amma halim da kannensa suke ciki ya yi matuƙar dama masa lissafi. Idan auren Hamida ya mutu a yanzu ba ita ba shi kansa ya shiga uku ai.
Ba zai iya daukar matsalarsu shi kad'ai ba.
Matsalar da kud'i zata magance zai iya amma matsalolin da kud'i ba zai magance su ba, ba zai iya ba. Tabbas yana bukatar Asad da Faruk har ma da Usman.
Matsalar Hamida kad'ai ta hana shi sukuni to ina ga ta Anisa da take k'aramarsu yake jin tausayinta fiye da kowa.
A duk sadda ya samu zama ba abin da yake bijiro masa irin kannensa. Ko tunanin Abida da ya'yanta ba ya yi a dalilin yasan suna amintaccen hannu.
Bilki ce kawai bata da damuwa idan ma tana da ita to tana da Baban da zai tsaya mata.
Ya numfasa yana ganin girman k'alubalen da yake gabansu.
Maimakon ya zauna ya huta kawai sai ya yi Katsina. Save Restricted Content Bot, [Nov 3, 2025 at 13:11]
Ya dira gidan Anisa.
Bai wani tarar da tashin hankali irin yadda ya yi hasashe ba. Rikici ne irin na sabanin fahimta, har abin ya yi tsananin da ta bar gidan.
Ta yi murnar ganinsa kamar me.
Idanuwansa suka kada a dalilin irin murnar da ya ganta a ciki lallai ya yi kuskuren tsallake su.
A ranar ya juya Kano.
Yana tunanin gobe zai je Kaduna wajen Saddiqa.
Ansari waya suke yi da shi, da har zai zo Kano wajensa ya ce ya bari nan gaba kad'an sai ya zo.
A maimakon sati biyu ko uku sai da ya shafe wata guda a tsakanin Kano da Funtua.
Ya sabunta gidansu an sake masa fasali na ban mamaki.
An had'a sola a kowanne b'angaren.
Ya yi furnishing din bangarensa sosia komai na garari ya zuba.
Haka b'angaren Baba babba ya zuba musu komai na bukata sababbi na alfarma.
Gadon Abida da yake d'akinsu na b'angaren Baba babba da kullum take fad'a masa tana son abinta har yanzu, ya saka an gyara mata ya kai mata bangarensu iya na Bilki da na Munira ne a d'akin yanzu.
Bangare MAMI kuwa da yake zaman Ansari labule da kafet da talabijin da firij ya saka sai katifu a d'akuna biyu. Ba kowa ya yiwa hakan ba sai y'anuwansa idan sun zo su zabi duk inda suke so su sauka, wala gunsa ko gun Baba ko kuma ainihin wajensu.

*Kun tuna Umm Nihla mai yadinkan Yan gayu da Yabin Bulkacuwa ta yi ta kece raini da su?*
*Tana nan tana kawo muku su zuka zuka, na alfarma, amintattu, akan farashi mai rahusa daga Malaysia*
*Malaysianfabricsng*
*What's only*
07020695644.
*Ana yawan ce mini layin baya shiga, iya whtsapp ne don a Malaysia take zaune*.

Bangaren yan aiki da yake mallakin Baba Babba ne an yi gyara ya zama iri d'aya da sauran b'angaren ammaa bai zuba komai ba. So yake idan Ubangiji ya taimake shi akan niyyarsa Yaya Faruku ya dawo su zauna tare da Baba tunda a Funtua Yaya Faruku ya rayu. Ya sha cewa ba inda yake jin dad'insa a duniya irin Funtua. Idan hakane to kuwa lokaci ya yi da ya kamata ya dawo gida.
Ya shiga b'angarensa ya ga yadda aka kawata wajen ya tabbatar wajen zai burge Abida tunda y'ar gayu ce ta soaai.
Yana kwance akn kujera yana hasashen kuɗaden da suka narke wajen gyaran gida. Tabbas zasu gina masa sabbin gidaje biyu.
Amma kuma kowa ya ga gidan sai ya sake kallonsa.
An sake masa fasali gabad'aya.
Ya sha fenti da fitilu tamkar wata masarauta ko fad'ar gwamnati.
Tun baba bai dawo ba yake jin dad'i a k'asan ransa yana jin tamkar komai ya wuce ne.
Yanzu abin da ya rage masa ya tattara kan k'annensa su je su gurfana a gaban Baba.
Ba ya jin fargabar faɗawa Baba kudirinsa na son ya dawo Funtua don ya tabbatar idan Baba ya gane hakan yake so zai yarda. Kawai wasu daga cikin y'ay'ansa ne zasu iya yin bara'a. Anan ne kuma yake tunanin rikici zai sake ballewa don shima ba zai yarda ba. Ko suna so ko basa so Baban ba nasu bane su kad'ai.

Ansari ya Isa Kano da sassafe Sulaiman da kansa ya dauko shi a airport tunda ya sayi tsaleliyar mota da tsayawa fad'in kudinta kauyanci ne.
Suna tafe suna tattaunawa cikin shauki da mararin juna.
A hakan Sulaiman ya kutso masa da buk'atar gobe zasu tafi Abuja tare jibi kuma Hamida da Anisa zasu biyo su a jirgi.
Ya yi magana da Saddiqa tana Abuja wajen mijinta dan haka zasu sameta a can ne, maimakon su tsaya su d'auke ta a Kaduna.
Ansari ya yi shiru don bai gamsu da zuwansu gabad'aya ba.
Sulaiman ya yi turus don bokarewar Ansari na nufin bokarewar Hamida da ya samu ta amince babu qabali da ba'adi.
Cikin damuwa Ansari ya ce "Allah ne shaidar bana fishi da Baba don kuwa ina gaishe shi from time to time. Amma hakan ba yana nufin kuma na gamsu ya yafewa MAMI bane."
Sulaiman ya ce "To yanzu mu je mu nema mata yafiya ta gaske Ansari.
Ansari ya jijjiga kai ya ce "Yaya Sulaiman gaskiya ni ba zan je ba.
Baba K'arami ne d'anuwansa ba MAMI ba. Har kuma Baba k'arami ya bar duniya ba shi da ra'ayin kansa mun sa ni sarai. Komai Baba Babba ya ce bai taɓa inkari ko yi masa gardama ba. Save Restricted Content Bot, [Nov 3, 2025 at 13:14]
To idan hakane ya kamata ya tattara ya barmu gabad'aya? Idan ya bar su yaya Hamida bisa hujjar sun bar shi to ni da Saddiqa da Bilki da muke gaishe shi fa?
Har Anti Bilki ta gama rayuwarta a Katsina nai taɓa sawa an bibiyeta ba, duk kuwa da yasan tana mak'onsa tana mak'on ya'yansa. Duk satin duniya sai ta gaishe shi, amma kafin ta bar Katsina ba wani abu da ya yi mata da zata gane shi ubanta ne.
Mami ce ta yi laifi sai ta yi mutuwar fuju'a ashe bai kamata ya tausaya mana ya danne laifin uwarmu ya rungume mu ba mussaman da muka rasa uwa da uwa a cikin shekara guda?
Da ɗansa ya d'auke shi ai mutuwar MAMI kuma sai ta saka ya dawo ya gyara barnar da ta yi a matsayinsa na babba kuma namiji mai hankali.
Duk bai yi ba haka ba. Da ya zo ta'aziya bamu ci arzikin Baba k'arami ya zauna

39 / 50