DINGISHIN KWADO 3 COMPLETE BY D Auta.txt

Author :  Hadiza D Auta Category :  Romance

Chapter   44 / 50

129K to 132K   out of 149K words

ce mu yafi juna, ai komai sai ya wuce a tsakaninku mana".
A nutse Sulaiman ya ce "Ai saboda matsalata da ita ya sanya ban d'ora dukkan hannuna akan naku ba. Ni yanzu kai da oga nake jira da Usman mu zauna da ita a gaban Baba. Idan aka yi sannan ne zan samu sassauci a zuciyata ".
Yaya Faruku ya ce "Ni kam da so nake yi komai ya wuce . Na kashe koma menene dukkanku kowa da inda ya yi kuskure. Dan haka na kashe batun."
Nan da nan ya girgiza kai tare da ce wa "A a bai kasu ba gaskiya. Ai tunda a farkon al'amarin aka zuba mata ido ta yi yadda take so, to nafi son a baje maganar a faifai don kowa ya huce gabad'aya. Idan na yadda aka tafi a dukunkune to fa zan rayu ne kuna mini kallon na ci mutunci baba ta hanyar jingine Abida a gabansa. Ni kuma na san ita ta jingine kanta".
Yaya Faruku ya zubawa Sulaiman ido yana aiyyana shima kaffaffe ne tabbas.
Ya numfasa ya ce "Sulaiman ya kamata ku fuskanci gaskiya fa. Ka janye wannan maganar kasan ba k'aramar magana ba ce idan aka fasata ta ya ya zaka ce ka bar mata yaron da kowa ya ganka ansan kaine ubansa" Save Restricted Content Bot, [Nov 10, 2025 at 09:47]
"Yaya na sa ni mana. Ni ban ce mata ba d'ana ba ne ai, na ce na barta mata ne kawai".
Faruku ya numfasa ya ce "Yanzu Sulaiman ace sulhun da aka yi jiya bai wanke komai ba?. Tunda ka iso hankalinsa bai kwanta ba, idan ita mace ce bata da hankali sai kuma ka biye ta ku sake tayar masa da hankali gabad'aya?"
Yaya Sulaiman ya d'ago idanuwansa ya zubasu kan na yaya Faruku, ya ce "Abida fa har yau din nan bata gama risina ba. Yau ta bani hak'uri gobe ya yi watsi da ni, sannan har ta samu kuzarin ce mini na biyata makudan milyoyin kudi."
Faruku ya ce "Ai yarinya ce ka yi hak'uri ".
Wani abu ya tokarewa Sulaiman. Abidar ce yarinya?"
Ya bude baki zai ce ba wata yarinya Sai ya tuna irin haka ya faɗawa oga Asad akan Bilki. Abida kuwa ai k'anwarta ce. Kan dole ya had'iye raddinsa ya yi shiru.
Ya fesar da iskar b'acin rai ya ce "Tsakani fa da Allah an yi mini ba daidai ba Yaya Faruku. Ni fa kawai shiru na yi amma kai ma na jin zafinka akan wannan al'amarin. Me yasa a wanccan lokacin baka motsa mata k'wanjin ta dawo d'akinta ba? Me yasa baka nuna mata girman hakkina a kanta ba? Ban mata komai ba, ita ce ta mini laifuka masu ciwo da wuyar mancewa. Ko ban cin arzikin komai ba a wajenta sai na ci na jini. Amma ta iya tsayawa a gabana tana fad'a min dama ba sona take yi ba, auren cimma manufa ta yi da ni, mafi munin kuskuren da ta yi mini da ta furzar da munana maganganu akan uwata! Ai mami uwartace aurena da ita kuma ya sake kara darajarta a wajen Abida. Amma tsabar tsaurin ido da tink'ahon yadda take so haka ake yi mata, ta zage mini uwa akan idona sannan ta kwashi jiki ta tafi gida, aka kuma bata mafaka, bayan ta sha magani don ta cire ciki bisa hijjar bata son had'a zuri'a da uwata. Sai kuma Allah ya nuna mata iko ta haife shi ".
Ganin da ya yi Sulaiman ya kai kololuwar fusata ya sanya ya sanyaya murya ya ce "Da kasan dalilin da yasa aka barta ta zauna din da ka gane ba mafaka muka bata ba, aurenku muka bawa kariya. A lokacin cikinta k'aramine ya zo ya fara kokarin faduwa ga jininta ya hau. Ta kuma ce idan aka tilasta mata ta koma hankali ba zai taba kwanciya ba. Ga likita ya ce tana buk'atar nutsuwar zuciyata saboda cikin jikinta ya zauna sosai , mu kuma muka tsareta tare da bawa cikin kariya. Ga Sulaiman nan tamkar ka yi kaki ne, lamarin mata ba'a biye su yanzun nan sai su yi abin da zasu jefa kansu cikin *Fargar Jaji (Janafty)*. Yanzu tunda kai ne babba kuma namiji ka yi hakuri komai ya wuce dan Allah Sulaiman ka ga dai yadda hankalin Baba ya fara kwanciya dan Allah kada ku tayar masa da hankali.
Yaya Sulaiman ya numfasa ya ce "Wai yanzu so ake yi na je na tare ta na bata hak'uri ta dawo ta zauna da ni?"
Cikin rarrashi Yaya Faruku ya ce "Maganar zaman da za'a yi zaka janye, sai ka sake daurewa ka d'auke ta zuwa gidanka shike nan maganar ta wuce, ina tabbatar maka Abida ta yi laushi Sulaiman ".
Sulaiman ya ce "ka yi hakuri amma ba zan dauke ta da kaina na mayar da ita ba. Yadda ta fito da kanta, da kanta zata koma matuk'ar tana son zama da ni".
Da hanzari Yaya Faruku ya ce "To ina ne gidan da zaku zauna ni sai na kaita da kaina inace shike nan?"
Murya ba amo ya ce "Inda ta baro, Funtua zata zauna!
Yaya Faruku ya yi shiru yana jin matuk'ar basu bi Sulaiman a hankali ba rikici ne zai sake barkewa a tsakaninsu bayan wanda aka yi akan Ladi farm.
Ya riga ya gane Sulaiman bai fahimci da kyakkwar manufa suka bari Abida ta zauna a gida ba. Don haka zai iya yin komai tunda yana ganin basu yi masa kara ba.
Tunda y'anuwansa ma sun kalubalance su da rashin yi masa adalci.
Ya nisa ya ce "Aikinta fa Sulaiman? Inace kai ma kana shiga specialist Hospital na nan Abuja".
Ya murmusa ya ce "Ko ina zan iya aiki ai Yaya Faruku ba ni da matsala akan hakan".
Yaya Faruku ya ce "To ku zauna a gidana na Gwarinfa kafin zuwa lokacin da zaku koma Funtua. Ai yanzu gyaran da yake gidan ba kad'an bane tunda ya dade a rufe". Save Restricted Content Bot, [Nov 10, 2025 at 09:50]
Gaskiya fa Yaya Funtua zata tafi, ni na riga na saka an gyara gidan gabad'aya dan haka ta koma can ta zauna, da amarya zan zauna a nan.
"Sulaiman!
Yaya Faruku ya k'ira shi da muryar gargadi.
Bai amsa ba amma ya sha mur. Ya ce "So kake Baba ya sake rafkewa ko? Idan an bata maka ba zaka yi hakuri ba? Hankalin mace da na namiji ba daya bane ai."
Ya za'a yi da sha'anin mata dole sai hakuri. "
Sualiman da sauri ya ce "Yaya Faruku idan hakurin ba zai zama akwai wulakanci a cikinsa ko cutarwa ba. Amma Wallahi ta daina yaudarar kanta da ce wa zan nemi sulhu da ita."
Da azama Yaya Faruku din shi ma ya ce "Dama tunda ita ta fara tsokanar ai ba zaka bata hak'uri ba. Amma idan ta k'ira wayarka ko ta yi maka message ka dinga amsawa. Tabbas ta yi laifi, Kuma ko Ni nan Sai na Mata ba dad'i, ka yi hak'uri, amma kaima hukuncin da ka d'auka ya yi tsair6da yawa shine ya bani kuzarin sake baka hak'uri akan ka bata dama ta gyara kuskuren ta."
Ya ce "Gaskiya ka yi hak'uri mu zauna da ni da ita da ku. Idan ba haka ba zuciyoyi ba zasu huce ba".
Faruku ya rasa yadda zai yi da shi. Ya ce "To ai shike nan ku da Babanku ni kam na gaji gaskiya!
Ya sassauta ya ce "Dan Allah yaya Faruku ka fahimce ni, ina son a huce ne gabad'aya."
Ya ce "Na fahimce ka da dukkan zuciyata."
Washegari sassafe Sulaiman ya kai Ansari airport ya tafi Maiduguri. An rabu lafiya da shi, ya kuma karbu sulhu da yafiya da dukkan zuciyarsa.
Save Restricted Content Bot, [Nov 11, 2025 at 13:19]
*Dingishin kwado*
*Surayya Dee*
08032773332.

*Bojuwa herbs*
*Oder your kayan mata for women of class*
*Our products are healthy and original*.
*Tested and trusted*.
*Sanyi flusher dinmu zai raba ki da dukkan nau'in infection, ya kuma sabunta ki*.
*A zo a saka order din ciccibin garari ko kazar sababi don ko zaki gode mini domin saiwowin da nake amfani da Su na yi imanin ba kowa zai iya zuba kudi ya sarosu ba*.
*Duk wadda ta ci ciccibi sai tasan ta ci abu gangariya haka ma kazar sababi*
*Just DM for your order @08033773332*.

Karfe sha d'ayan safiya duk suna hallare gaban Baba. Oga Asad, Yaya Faruku, Usman, Sulaiman da Abida.
Cikin nutsuwa Sulaiman ya rattabo irin halin tsaka mai wuyar da ya shiga a lokacin ake danbarwar Ladi farm. Zullimi da rud'anin da ya shiga bai samu sassauci da rarrashi daga Abida ba. Haka ya zama desperate gida da waje ba nutsuwa a tare da shi. Duk irin rarrashi da kwantar da kan da ya dinga yi mata bai saka ta samar masa da nutsuwar da ta dace da halin da yake ciki ba.
Zaman wurinsu ma ta daina yi barci zai kawo ta shima yana shiga dakinta zata rufe k'ofar. Ana idar da sallar asuba zata sake ficewa. Duk ya yi hak'uri akan hakan tunda yasan MAMI ta yi ba daidai ba.
Ya dago kansa ya ce "Sai kuma ta kasa gane irin hak'uri da taka tsantsan din da nake yi don kada komai ya sake k'wacewa. Ta tsaya a gabana ta zagi MAMI irin zagin tsamar nama da babu tarbiya da mutunci a cikinsa.
Ganin idona na ga maganin lalata ciki a bakinta wanda hakan ya sanya jini ya balle mata. Duk izgilin da ta yi mini na zagin uwata hakan na kwashe ta zuwa asibiti da kaina duk da zuciyata na ingiza ni na mata dukan kawo wuka sai ta yi jinyar da hujjar.
Amma saboda kai Baba sai ban yi hakan ba.
Duk hidimar asibitin ni na yi alhalin nasan ita ta janyo ciwon da kanta. A hakan na daure nake ta zarya. Sai kuma na ji daga asibiti ta taho Abuja.
Zuciyata daya na gamsu akan nasan zaku korota tunda ban sake ta ba, ban yi mata komai ba. Sai kawai na ga an barta, a yiwa Allah a duba wannan batun ya ya zan ji ne a zuciyata?Dole na zaci dukkanku da kuke da iko da ita kun gamsu na yi laifin da ya cancanci na rasa y'anci akan aurena. Shiyasa ban zo ba.
Zagin mami kuma da ta yi ban sake ta ba. Billahillazi lah illah ha illah huwa nauyinka na ji Baba. Don kuwa babu macen da zata yi mini hakan a duniya na cigaba da zama da ita".
Hawaye ya k'wace masa.
Daga oga Asad har Faruku jikin kowa ya yi sanyin. Hatta Usman da yake da ra'ayi irin nata jikinsa ya mutu tub'us.
Usman ya fara cewa "Lallai ta yi ƙaton laifin da yake da ciwon gaske ".
Baba kuwa ya ce "A a lallai Abida ta kerewa tunanina Ai ba matar zama ba ce. Ni kaina ba zan zauna da mai zagin iyaye ba don mace ta gari ba zata yi wannan jahilcin ba".
Abida ta rushe da kukan tashin hankali.
Cikin kuka ta ce "A yiwa Allah a yi mini hak'uri a kuma fahimce ni. Ba kowacce mace ce zata iya tsallake halin da nake ciki ba. Ace uwar miji da mijin da y'anuwansa sun dunkule suna k'alubalantar uban mace da zalunci har a maka shi a kotu? Dan Allah a duba da kyau. Amma na janye kalamaina, na bada hak'uri kuma ni bansan ma sadda na fad'a ba. Wallahi jinnul Ashiq ne da suka hana ni aure suke shafata lokaci zuwa lokaci."
Tausayinta ya kama oga Asad yasan jiki ta ji shiyasa ta jinginawa jinnu alhakin laifin da ta yi.
Faruku ya ce "Ai kad'an ma kike ganin tunda ke jununki kaifin harshe".
Baba ya ce "Yanzu na gane kana da hujjojinka masu k'arfi. Kuma na gode da ka ga girmama ni amma fa ka sani kana da dama da y'anci a cikin aurenka. Ni dai ka wanku tas a zuciyata. Idan kana sonta a haka zaka iya danne laifinta ka yi mata adalci to hakan nake so. Idan ba zaka iya ba to kada ka yi mata rokon da zaka zalunci kanka Allah ya kama ka da laifinta to ka sahale mata kuma ba zan ga laifinka ba".
Abida ta fashe da kuka tana fad'in "A duba nadamata Baba. A duba shekarun da na shafe a rataye alhalin Annabi ya ja kunnen maza akan kada su bar mata a rataye su ba sakakku ba, su ba masu aure ba. A duba zaman goyon ciki da raino da na yi, a duba bak'incikin zura mini ido da kuka yi kai da momi. Gaskiya Baba ka yi mini adalci ". Save Restricted Content Bot, [Nov 11, 2025 at 13:22]
Usman ya mike ya yi kanta yana fad'in Baban kike ce wa ya yi miki adalci? You are very stupid!

Ya mike ya yi nufin kai mata duka Sulaiman ya tare shi tare da fad'in kada ka dake ta. Ba usman din da aka tare ba, kowa sai da mamakin Sulaiman ya daskarar da shi. Ganin hakan oga Asad ya samu kuzarin fad'in "Baba mu yi alkalanci na gaskiya a tsakaninsu.
Abida ta yi laifi mai suna laifi. Lallai ta yi rashin tarbiya da rashin mutunci wanda ba gani ta yi ana yi a gidanmu ba. Ita tasan inda ta ga ana zagin miji da manyansa. Ko ba Sulaiman ke aurenki ba ai MAMI ta wuce ki zage ta don kuwa ta haifi waɗanda suka fiki bayan haka kuma matar Babanmu ce. Da ace a lokacin da kika yi wannan rashin tarbiyar mun ji da ni da kaina na saka Sulaiman ya rabu da ke don kuwa ba zai zauna da wacce bata tarbiya ba. Amma tunda shima ya taka alfarmar sharia wajen yin hukunci to shikenan, Sai a yi hukunci na gaskiya.".
Ya nisa ya ce "Sulaiman tsakanina da Allah nake batuna, ba wani bangaranci ko son zuciya. Ba zan maka dole akan ra'ayinka mussaman akan aurenka. Kai kake da cikakken iko akansa haka kaine kake da da damar cigaba da rik'e aurenku ko ka gutsire shi. Amma abin da zan fad'a maka ka fahimce ni da kyau. Ka take dokokin sharia Sulaiman. Ba addinin da ya ce ka bar mace shekaru hud'u ba tare da tasan makomar aurenta ba. Hukuncin ya yi tsauri matuƙa da gaske.
Kenan kai da ita duk kun yi laifi babba.
Ita ta zagi uwarmu don itama MAMI uwarta ce. Kai kuma ka bijirewa kaidojojin sharia. To idan a mahangar addinin musulunci za'a yi alkalancin to gaskiya ka yafe mata ku cigaba da zama kaima sai Allah ya yafe maka d'ora ra'ayinka akan na shari'a da ka yi yayin hukunci".
Abida ta rrarafa ta fad'a jikin oga tana kuka sosai.
Don ya faɗi abin da ya yi mata dad'i bai ce a saketa ba.
Kuka kawai take yi wanda babu shegantaka ko shakiyanci don hankalinta ya tashi ainun sannan ta muzanta sosai.
Ya kasa ture ta a jikinsa don tausayinta ne ke kekketa shi. Zullimi da firgici ya bayyana mata barobaro mussaman da Baba ya yi kalamansa da yake nuni ba zai yiwa Sulaiman tilas ya zauna da ita ba.
Sulaiman ya nisa ya ce "Shikenan na yafe mata amma gaskiya kada ta sake yi mini irin haka. Sannan ta fara yi mini bincike a wayata to ta bari, wayata ba huruminta ba ne. Ina neman aure ba ruwanta da batun karin aurena idan an k'addara mini zan k'ara to zan yi, idan kuma ba'a k'addara mini ba to shikenan amma kada ta fara saka mini ido tare da bin diddigin halin da nake ciki ".
Abida ta dago daga jikin oga idanuwanta jage jagee da hawaye ta ce "Ba ruwana da wayarka. Aure kuwa da ikon Allah ba a k'addara maka ba. Baba babba da Baba K'arami matansu d'aya. Ga yayyenka nan duk matansu d'aya don haka kaima d'ayan ce".
Oga Asad ya bige mata baki ya ce "Wai ke wacce irice ne? Ba za ki yi godiyar ya yafe miki ba, sai kawai ki hau raddin batun da ya ce bai shafe ki ba. Ina ruwan ki da Ƙarin aurensa?"
Cikin kuka ta ce "Ayi hak'uri na yi shiru."
Baba ya nisa ya ce "Na huce da kai Sulaiman na kuma fahimce ka, ba da gayya ka yi abin da ka yi ba. Na yafe maka b'acin ran da na shiga a dalilin tafiyarka. Allah ya yi maka albarka".
Sulaiman ya amsa da ameen Baba na gode Allah ya kara lafiya da nisan kwana mai albarka."
Dukkansu suka amsa da "Ameen".
Abida ganin za'a tashi ba'a yi batun inda zata zauna ba.
Ya sanya ta ce "Yaya Sulaiman ya bani inda zan zauna ".
Ya yi shiru.
Baba ya ce "Sulaiman ka ji rok'onta?"
Ya yi k'asa da kai ya ce "Na ji Baba. Da na gama gyara mata gidanmu na Funtua don can zan koma. Sai kuma jiya ta gabatar mini da lissafin bashin da ta ke bina tun bayan tafiyata. Na gama lissafina ban ga ta yadda zan bata milyan dari uku da sittin da ukun da ta ambato mini ba. Dan haka ta zauna zuwa sadda zan hado mata kuɗaden sai ta koma".
Ta yi fit ta ce "Ba zan jira ba. Ka bayar abin da ya samu a hankali sai ka dinga biya". Save Restricted Content Bot, [Nov 11, 2025 at 13:25]
Ya yi maza ya ce "Kin manta babu bashi a tsakaninmu ne?"
Ta goge hawayen idonta ta ce "Sai mu fara yanzu".
Ya ce "Abida Wallahi ba za ki bini bashin kud'i ba."
"To shikenan ka ba ni milyan sittin da ukun albarkacin yafiyar da ka yi mini, na yafe maka milyan dari ukun.
Ya jijjiga kai ya ce "Na gode amma ki mini lamini zuwa na samu sararin samunsu idan na kawo sai ki koma d'akinki don kuwa ba zan yarda ki koma da sharadin kina bina bashi ba".
Ta yi shiru amma yadda ta ga ba wanda ya tsoma musu baki ya sanya ta fad'in "Yanzu nawa zaka iya ba ni to?"
Iya na magani da hidimar junior zan iya baki kawai. Amma bayan wannan duk wani lissafi ban karɓe shi ba, don kuwa ban ce ki bar d'akinki ba, ke ce kika tafi don rad'in kanki don haka kwabona ba zan bayar ba".
"To yanzu nawa zaka iya ba ni?".
Ta tambaya cikin rauni.
"Milyan d'aya."
Ya amsa a takaice.
"Ta fashe da kuka sosai tana fad'in "Na rantse na kashe ninkin ba ninkin wannan kudin da ka ambata ka dai sake dubawa".
Dariya ta k'wacewa Yaya Faruku. A ransa yake ayyana Abida

44 / 50